Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke dai kinsha babu abinda yay miki zafi da wanda za azarga,maza ki tashi kije kar inno taga kin jima abinda kika zaɓa kiyo min test ba sai kinzo ba!nuna mata banɗaki tayi tare da cewa maza shiga ki wanke fuskar ki karki sake ki bar wata alama da zatai nuni da damuwarki!'cikin sanyin jiki Bintu ta tashi ta shiga banɗakin bata jima ba ta fito,batare da ta cewa Aunty Nafisa ko mai ba ta buɗe ƙoafar ta fice daga ɗakin,da wani irin murmushi tabita tana ji kamar burinta ya gama cika...


Tun da tashiga ɗakin ta tarufe kanta take kuka har sai da ya saukar mata da mummunan ciwon kai,ko kiching bata jin zata iya shiga, )su Oga Abdallah yau fa sai haƙuri dan baza ka samu haɗaɗɗen girkin Bintu ba)shin yaya zatayi da wannan babban tashin hankalin da ya kuma dannowa cikin rayuwar ta? gaskiya A wannan karon bata da wata dabara ko mafita dole tana buƙatar shawarar wani,to tayaya kenan? bayan ta yi mata gargaɗin kar ta faɗa wa kowa,to hakan yana nufin duk wanda na gayawa shima sai ta kashe shi? runtse idanunta tayi yayin da hawaye suka ƙi dai na zuba mata,ita kanta tasan tana cikin tsaka mai wuya,domin baza ta taɓa iya kashe koda kiyashi ba balle mutum sukutun guda,idan kuwa hakane dole tayi gaggawar neman wa rayuwarta mafita,harma da wanda Anty Nafisa take shirin cutarwa.

Ranar yini tayi A ɗaki tana fama da tunani da matsanan cin ciwon kai.

Inno duk ta shiga damuwa ta rasa yadda zatayi ta duba Bintu, can sai wani dabara ya faɗo mata duban su siddiƙa tayi waɗanda suke ta buga game cikin ƙwarewa da nishaɗi yayin da Taufiƙa take can tana zurfafa tunani akan neman cikar muradinta,cikin haɗe fuska inno tace" dasu Farida wai ina yarinyar nan ta shiga ne ban ji alamar tafito shiga kiching ba? Siddiqa ta taɓe baki tana cigaba da sha'anin gabanta,Farida tace"yo inno kika sani ko yajin aiki ta tafi,yau tana muradin ɓatawa Yah Abdallah rai,miƙewa inno tayi ranta A ɓace ta nufi ɗakin bintu,dariya Farida da Siddiqa sukayi har da tafawa,

A hankali ta tura ƙofar tare da sallama,cikin sauri ta ƙara sa gaban gadon,ta riƙo hannun Bintu,cikin tashin hankali tace" subhanallah Bintu baki da lafiya amma baki sanar dani ba? duba jikin ki kamar garwashi!'ɗago kan Bintu tayi ta ɗora kan cinyarta ta shiga shafa lallausan gashin kanta da ya baje har bayanta,cikin tausayi tace" sannu kinji Bintu tun ɗazu nake son dubaki amma ina tunanin ta ya zanyi hakan saboda yaran nan suna tare dani!'Bintu ta kama hannun inno cikin ƙarfafawa kanta gwiwa tace" inno karki damu ai naji sauƙi jiki nane kawai babu ƙarfi shi yasa kika ga ban fito ba!' inno tace" a'a Bintu ga jikin ki nan da zafin zazzaɓi amma kice min lafiya kike bari na duba ko Abdallah ya shigo nace yazo ya dubaki ya baki magani!'ai da jin haka Bintu tayi wata iriyar zabura sai gata zaune tana rarraba ido cikin rawar baki tace" Ni dai inno karki gaya masa naji sauƙi bari ma ki gani miƙewa tayi ta shiga dan tsalle,inno sakin baki tayi tana kallon Bintu cike da mamakin wannan tsoron da takewa Abdallah,kawar da tunanin tayi da cewa ke kam Bintu ban san wace irin matsoraciya bace!' ma rai raicewa tayi tare da cewa Wallahi inno zuwa zaiyi yamin allura gashi kullum fuskarsa A haɗe babu fara'a Ni kawai ki bani magani xan ji sauƙi!'numfashi inno taja kana tace" ai shikenan bari na kawo miki maganin kisha sai ki kwanta idan kika samu bacci zazzaɓin zai sake ki,shi kuma Abdullah bari naje nasamar masa wani abu da kaina ke ma sai ki ɗanci kafin kisha maganin! to inno na gode amma da baki wahalar da kanki ba zan yi masa da kaina!' inno ta miƙe tare da cewa a'a Bintu bana son gaddama ki kwanta ina dawowa!' daga haka tasa kai ta bar ɗakin.a hankali Bintu ta koma ta jingina da window tana mai jin ƙaunar inno har cikin ranta da kowa na gidan nan halinsu yayo ita da sauran kishiyoyin ta da kuma mai gaba ɗaya wato Alhaji Baba da tabbas sun zama abin koyi,wannan shi ake kira da ƘUDURAR ALLAH,


Duk abinda ya kamata inno tayi mata sai da tayi mata ta kuma kaiwa Abdallah haɗaɗen jalof ɗin da tayi masa wanda yaji uban kifi sai gashin kaza da tayi masa mai shegen ɗaɗi,dan haka yaci abincin duk da dai bakinsa yaji cewar ba Bintu ce tayi ba, dake ya riga yasan ɗan ɗanon girkin inno sai bai damu ba amma ya ɗan yi tunanin abinda ya hanata yin girkin.


Dole washe gari ta sawa kanta ƙarfin jiki ko dan saboda damuwar inno,da kuma gudun allurar Oga Abdallah,sai da ta gama kimtsa masa ko mai kana ta bar falon batare da ta bari sun haɗu ba tun da tasan shi tamkar Aljani yake wajen gano mutum baida lafiya, Abdallah ganin tayi masa karin kumallo yasa ya dai na tunanin komai,cikin sauri ya kammala saboda shima kwana biyu yana cikin busy,


Aunty Samira tace"sir me yasa aka fasa miting ɗin jiya kamar yadda kace? cikin yanayin nutsuwarsa yace"Samira jiya an sanarwa dasu Alhaji Nasir zamuyi mitin hakan ya ƙara tabbatar min da akwai munafiki A cikin mu,dan haka yanzu inaso duk ki kira minsu a kwai binciken da zanyi akan ko wannen mu! ok sir Bari na sanar dasu!'


Kallon su yakeyi ɗaya bayan ɗaya gaba ɗaya su goma ne suke ƴan team ɗin sa, sune Amin tattun da ya zaɓa dan yin aiki dasu sai dai bai san a cikin su wanda ya ke kware masa baya ba, amma dai yana da yaƙinin A cikin ƴan mintuna zai fito da ko ma wanene,ɗan gyaran murya yayi tare da gyara zamansa cikin haɗaɗɗiyar kujerar sa, kana ya fara magana cikin ƙasai tacciyar muryarsa wanda kana ji kasan babu wasa cikin dukan Al'Amuransa,yace"abinda yasa nace A yimin kiranku shine jiya nace zamuyi mitin amma hakan bata samu ba dalilin cin dunduniya da muka samu ɗaya daga cikin mu nayi mana!'shuru yayi tare da zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya yana mai karan tar yanayin su,ci gaba yayi da cewa amma kusani na riga da na gama bin cikena A kan wanda yake fitar mana da sirrin mu na kuma gano kowanene!kallon kallone ya shiga giftawa tsakanin su kowa na tunanin waye? yayin da me aikata laifin ya fara fidda kansa wanda dama wannan duk shirin Abdallah ne yayi niyar kama kowaye A hannu shiyasa yay musu wannan hikimar,kuma Alhamdulillah yasamu abinda yakeso dan cikin hikimarsa da basirar da Allah Ubangiji ya fuwace masa ya gano mai laifin a cikin mutanen goma da ya amince dasu,ya ɗan daki table ɗin gabansa cikin wasu sakanni office ɗin yayi tsit,razanan nun idanunsa ya ɗora kan fuskar safyanu yana mai san ƙara tabbatar da zaton sa,mara gaski ance ko A ruwa gumi yake tuni safyanu ya shiga rawar jiki,cikin tashin hankali ya sauƙa ƙasa idanun sa na fitar da hawayen na dama yasan in dai a wannan harkar ne Oga Abdallah baida sassauci yana matuƙar girmama amana da gaskiya,cikin rawar baki ya buɗe baki zaiyi magana amma hakan bata samu ba saboda jin yadda wasu manyan ƙarti majiya ƙarfi suka da baibayeshi tare da sa masa sarƙa,ko su jabir baza suce ga lokacin da suka ga Abdallah yayi waya ba balle shigowar su Majid, kallon su Abdallah yayi fuskar nan babu alamar sassauci yace" ku tafi dashi karku saurara masa har sai na neme ku!'hankaɗa shi sukayi waje suka yi gaba dashi.

Dukkansu nutsuwa sukayi dan babu wanda jikin sa baiyi sanyi ba,sun riga da sun san hukun cin Oga Abdallah ba mai sauƙi bane,sai da yaga ma shaƙar ƙamshin sa kana cikin kakkausar murya yace" ina so duk wanda yasan zai ci amanata A wannan tafiyar salin alin ya fita daga office ɗin nan idan kuma ba haka ba duk wanda na kama da makaman cin abinda safyanu yayi hukuncin sa sai ya nunka nasa sau goma!'shiru yayi yayin da office ɗin ya ɗau shiru na wani ɗan lokaci kowannen su zuciyar sa cike take da tsoro sai dai kuma akwai sadaukar wa tsakanin su saboda suna san ogan nasu,shima safyanu dan badashi aka fara tafiyar bane bai san irin gwagwarmayar da ogan nasu yayi dasu bane,shi yasa har yaci amanarsa.

Dukkanin su sunyi alƙawari da kuma rantsuwa bazasu ci amanarsa ba, kuma zasu tsaya akan tabbatar da gaskiya ko mai runtsi komai wuya,daga nan ne kuma ya sallame su tare da sanar musu lokacin da zasuyi mitin ɗin ƙarfe shabiyu na daran yau in Allah ya kaimu da haka suka rufe tattatunawar.


Haka nan taji tana buƙatar ganin Dide ko da baza ta iya gaya mata halin da take ciki ba to tasan zata iya samun shawara cikin hikima,fita tayi can wajen, lokacin ƙarfe takwas na dare dan saida ta kammala wa Oga Abdallah girkinsa kana ta fito,

A hankali take takawa tana ɗan waige waige wanda har bata ankara ba sai jitayi an fincikota tare da toshe mata baki,A lokaci ɗaya kuma ana shiga da ita ta wani ɓangare wanda A halin da take ciki baza ta iya fahimtar inane aka nufa da ita ba....


Comments.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 26 ```



Kiciniyar ƙwace kanta takeyi amma hakan ya gagara ƙarfin ba ɗaya bane,ji tayi an wulla ta saman gado bayan an shigo da ita ɗakin, ɗagowa tayi hankali A matuƙar tashe, Sayyid ta gani tsaye A kan ta riƙe da ƙugunsa yana binta da wani shu'umin kallo mai dauke da tarin manufofi,cikin ƙarfin hali ta miƙe A fusace tana nuna shi da yatsa cikin ɓacin rai da tsoron da ke cike taf A ranta, tace" wai me kake nufi dani? me zan maka da kakawoni nan?wani kallo ya bita da shi batare da ya bata amsaba yayi kanta gadan gadan,wani irin tsalle Bintu tayi ta yi hanyar ƙofa sai dai bata samu nasarar fita ba taji ya cafko gashinta, ƙara ta saka kafin kace meye sun fara dambe A cikin tsakiyar ɗakin,tun Bintu tana samun ƙarfin ƙwatar kanta har ya kai gacewa ta kasa kataɓus,har sai da ya samu nasarar kamata ya shinfiɗe ta asaman gadonsa, cikin dariyar mugunta yace" to yarinya me bakin fitsara ya kikaga wannan salon yau zan kwashe duk wani abu da kike ta ƙama dashi,babu mai ƙwatarki A hannun Sayyid Mansur Balarabe!'ya ƙarashe maganar da ɗage mata gira,yana mai ƙoƙarin zare rigar saman dake jikinsa wani irin ƙarfi ne yazo wa Bintu ta samu damar ture sa kana ta miƙe cikin hanzari har garin sauka a gadon tana bige ƙafar ta hakan yasa takasa tashi dan sosai ta bugu,shi kuma hakan ne ya bashi damar kusanto inda take tare da ɗauke fuskar ta da wani gigi taccen mari wanda har sai da bakinta ya fashe kuka tasa mai ƙarfi tare da fara masa magiya, Sayyid dan Allah kayi haƙuri kar ka ɓata min rayuwa Ni marainiya ce duk abinda kake so zan yi maka amma dan Allah kabarni da mutuncina!' jan yo ta yayi tare da hankaɗata saman gadon yana cewa dama kin san bada haƙuri?bakin rashin kunyar har ya mutu ne?to yau saina cimma burina ko mutuwa zakiyi!'kuka take tana yakushin sa da duka ta ko ina amma ina Sayyid yayi nisa baya jin kira ƙoƙarin sa kawai yaga ya cimma mummunan nufinsa A kan Bintu,duk yabi ya gajiyar da ita har yanzu ya kasa samun dama A kan ta amma hakan baisa ya saduda ba tun kukan ta na fita har ya zamana Muryar ta ta dashe baka iya jiyo sautin ta sosai,sun kai kusan awa ɗaya suna abu ɗaya.


Tun da ya dawo ya ci abinci ya shirya,yake jin zuciyarsa na wani irin bugawa,komai yanayin sane cikin sanyin jiki har sai da yasamu ya ɗan yi karatun ƙur'ani kana yaji sanyi a ransa, amma duk da haka ji yayi gaba ɗaya gidan yayi masa zafi,dan haka tun kafin lokacin miting ɗin su yayi ya gama shirinsa tsaf ya zari key ɗin mota ya fita.

Duk takun da zaiyi sai yaji bugun zuciyarsa ya ƙaru, yana kusan tar wajen ajiye motocin yana jin jikin sa na wani irin rawa da sanyi tamkar ana zuba masa ƙanƙara, A hankali yasa hannu zai buɗe motar amma sai yaji ya kasa, haka nan zuciyarsa ke sanar dashi da wani mummunan abu na shirin faruwa,to A ina kuma A kan waye? ɗan jim yayi yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,waywayawa yayi yana fuskantar ɓangaren su Sayyid kasan cewar ataɓangaren gurin ajiye motoci ɗakunan su suke,hakanan yaji kamar ana ingaza zuciyar sa da ya shiga ɓangaren, A hankali yake takawa yayin da duk taku ɗaya bugawar zuciyarsa ke tsanan ta,bai tsaya ba har sai da ya dangana da ƙofar ɗakin ɗaya daga cikin samarin,har ya ɗora hannun sa kan mariƙin ƙofar sai kuma yashiga tunanin abinda zai kaishi me zaiyi A wajen idan yashiga mai zaice da mamallakin ɗakin? dan haka zuciyarsa ta umarce sa da barin gurin.


Bintu kuwa ta gama yin laushi ta kuma sadaƙar yau ƙarshen rayuwar tane yazo, dan tabbas Sayyid ya ɓata mata rayuwa baƙin cikine zai sa ta haɗiyi zuciya ta mutu,duk yaji mata ciwo ya kuma yayyaga mata kaya,lokacin da hannunsa ya taɓa lallausar fatar jikin Bintu ji yayi ya kuma ruɗewa idanunsa sun riga sun rufe baya sauraren kalaman Bintu na magiya wan da suke shige da waƙe saboda yawan jaddadawa,numfashin ta sai ƙoƙarin kumcewa yake saboda tsananin jigata da wahala da kuma yawan kukan da tasha,wani irin murmushi yayi na ganin yana dab da cimma burin sa.

A dai dai lokacin kuma da Abdallah yake ƙoƙarin juyawa dan barin wajen,tamkar mayen ƙarfe haka yaji an fixgi zuciyar sa zuwa ga ɗakin da yake kusa da wanda ya fasa shiga.

Yana gab da san cin ma manufarsa yaji tamkar duniyar tana juyawa dashi, yayin da kuma ya kasa tan tan ce duniya da lahira saboda wani irin mummunan naushi da ya bakunci fuskarsa wanda take haƙoran sa guda biyu suka biyo bayan naushin, kafin ya dawo haiyacin sa ya kuma ji anyi sama dashi tamkar ƴar tsana an wurgashi kusuwar ɗakin in da ya faɗo ƙasa tamkar kayan wanki, Abdallah dukan Sayyid ya shigayi tamkar ba ɗan Adam yake duka ba,hatta Bintu da bata hayyacin ta sai da taji tsoron kar Oga Abdallah yaje yay kisa, Sayyid ɗin ma ya daina motsi amma yaƙi daina dukan sa, A hankali ta rarrafa jiri na san yadda ita,tana kusan tar inda yake jiri ya ɗebeta ta tafi luuu, zata faɗi, babu shiri yay wurgi da Sayyid dake hannun sa ya tafi ya tarota, waɗawa tayi jikinsa numfashin ta na ƙoƙarin ɗaukewa,rigarsa ya cire ya rufa mata kana yay mata ɗaukan jarirai yabar ɗakin da ita.

Cikin mota ya sakata ya kwantar da ita kana ya shiga ya figi motar da gudu kamar zai tashi sama,har yanzu bayajin yayiwa Sayyid hukuncin da yakamata,zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinsa haka yake ji saboda tsananin ɓacin rai,tabbas ba iya abinda ya kamata yayiwa Sayyid ba kenan dole ne yasa ayi masa horo mafi muni A rayuwar sa wanda sai yaji dama ba A haife shi ba.

Da wannan tunanin yazo haɗaɗɗan gidan sa wanda yake A area 2, unguwar kanta abin kallo ce balle kuma gidajen dake cikin ta,guri ya samu yayi pakin bayan sojan mai gadin ya ɓuɗe masa get,buɗe bayan motar yayi ya ciro Bintu da har yanzu bata farfaɗo daga suman wahalar da ta tafi ba,ɗaukar ta yayi A kafaɗarsa ya nufi cikin gidan da ita.

Duk kansu A falon ya samesu shi ko kula da motocin su baiyi ba saboda baya cikin nutsuwarsa,gaba ɗaya binsa sukayi da kallo batare da kowannen su ya iya yi masa tambayar dake zuciyar saba,har sai da ya shige ɗakin dake cikin falon da ita, kana suka shiga kallon junansu amma duk da haka basuce komai A junansu ba suna dai jira su gane koma meye dan sun san dai da wuya Oga Abdallah yayi musu bayanin abinda bai shafe su ba.

Sai da ya fara shafa mata ruwa ta farfaɗo daga suman da ta tafi, kana ya saka mata ruwa saboda ƙwarin jikinta ya dawo duk da sai da sukayi artabu duk tabi ta cukwikwiye ta wahal dashi kafin ya soka mata allurar ruwan, saida yaga bacci ya ɗauke ta kana ya canja wasu kayan ya fita falo dan tattauna wa da yaran sa, bai ce musu komai akan Bintu ba dama suma basu sa ran zai faɗa ɗin ba,sun tattauna abubuwan da suka shafe su da kuma yadda zasu fuskanci wannan gagarumin yaƙin da suka tasa A gaba, kowa ya bashi ɓangaren da zai fuskanta yayin da ta ɓangaren Alhaji Salisu shima suka canja tsari dan yanzu A maimakon bibiyar Alhaji Salisu zatayi, yanzu Alhaji Sama'ila zata bi dan ƙulla alaƙar soyayya,duk da cewa yasan su Alhaji Nasir basu san da wannan shirin ba tunda daga shi sai Samira sukayi maganar A wan can ranar cikin office dinsa batare da sauran yaran nasa ba,sallamar su yayi batare da yayi musu ƙarin bayani a kan Bintu ba.

Nabil ne yazo zai shiga ɗakin sa ya hango Sayyid A sheme kamar matacce da gudu ya ƙarasa cikin ɗakin ya ɗagoshi cikin tashin hankali, ya shiga jijjiga Sayyid da ko motsi baya yi dan kuwa matuƙar buguwa ya bugu,da gudu ya fita bai tsaya ko ina ba sai sashen Dady mansur,kiran da sukaji Nabil ɗin na kwarara musu shi ya fito da su A tuɗe kowa da irin tambayar da ya kewa Nabil, bai tsaya basu bayani ba kawai yaja hannun Dad suka fita yayin da mama ta shiga binsu Abaya cikin tashin hankali,

Lokacin da suka ga halin da Sayyid ya ke ciki gaba ɗaya ruɗewa suka kuma yi,dan ita mama ta kasa daurewa kuka ta saka tana faman sanbatun tambayar waye yay mishi haka waya keson kashe mata yaro? haka dai take ta jefo zantuka cikin fitar hayyaci, Dady Mansur kuwa saɓa shi yayi A kafaɗarsa ya nufi wajen mota dashi cikin tashin hankali mara misaltawa duka nufi asibiti.

Inno ta shiga ɗakin Bintu yayi sau ashirin, tun tana kasa magana har ta fito da tashin hankalin ta A fili bata san sanda ta fara tambayar su Taufiƙa ko sunga gilmawar Bintu ba,amma duk cikin su babu wanda ya bawa tambayar muhimmanci, saima cewa Taufiƙa tayi inno ki daina neman yariyar nan,dan ba yau ta fara wannan halin ba ke ce dai sai yau kika lura!' wani irin kallon takaici inno tabi Taufiƙa dashi batare da ta iya furta mata komai ba, ta ɗaga wayarta dan ta kira Rahima ta tambaye ta ko suna tare da Bintun.

A hankali take buɗe idanunta da sukayi mata nauyi,tun tana ganin dishi dishi har suka buɗe tarwai,wata gigitacciyar ƙara ta saka tana ƙoƙarin fizge ƙarin ruwan dake hannun ta,gaba ɗaya ta fita haiyacin ta, A tsorace take gani take kamar har yanzu tana dakin Sayyid,A hankali ya turo ƙofar ɗakin ya shiga waya saƙale A kunnensa da ga dukkanin alamu da inno yake wayar dan naji ya na cewa ta farka karki damu idan mun dawo zanyi miki bayani!' daga haka ya katse wayar yana mai ɗora mata rikitattun idanun sa masu saukarwa da mutum nutsuwa,aiko take Bintu ta nutsu ta daina ihun da takeyi amma ba ta daina kukan ba,zare mata ruwan yayi kana ya juya da niyar barin gurin,riƙo hannunsa tayi gami da ƙara sakin wani marayan kuka,ɗan tsaiki yayi gami da juyowa A matuƙar fusace dan dama har zuwa lokacin bai gama hucewa ba,cikin tsananin fusata da ɓacin rai yace"meye ne kuma zan miki Ni nakai ki ɗakin nasa da zaki na cikan kunne da ihu?idan da banzo ba me kike tunanin zai faru?duk wannan tsoron naki amma bai hanaki shegen shige shige har sai kin kai kanki inda ake neman rayuwar ki!' cikin kukan tace Ni bani naje ba jana yayi ta ƙarfi ina cikin tafiyana!'ɗan tsuka yayi gami da zare hannun sa daga nata,cikin shagwaɓaɓen kukan nata ta kuma cewa dashi Ni dai yunwa nakeji!'sai ki tashi ki girka!' ya faɗa yana mai kawar da kansa gefe,tura ɗan ƙaramin bakin ta tayi tare da cewa" to ai Ni bani da lafiya!' bai saurareta ba ya fita daga ɗakin,shiru tayi cikin mamakin Al'Amuransa meyasa duk sanda take buƙatar taimako shi yake zuwa ya taimake ta? wani lokaci me kirki wani lokacin kuma akasin haka, tana cikin wannan tunanin har ya dawo hannun sa riƙe da take away miƙa mata yayi, hannu tasa ta karɓa tare da tashi zaune cikin sanyin murya tace" na gode!'bai dai tan ka matan ba ya kuma fita daga ɗakin,baki ta taɓe tare da buɗe take away ɗin ta.


Inno ta samu kwanciyar hankali jin Bintun tana tare da Abdallah,sai dai zuciyarta da take tayi mata saƙe saƙe akan bintun, ko me ya faru da marainiyar Allah? ko ma dai meye dole ta ajiye ta barwa safiya.

Sayyid kuwa yana can hannun likitoci suna kula dashi yayin da Alhaji Mansur yake Allah Allah Sayyid ɗin ya farka domin yaji uban da yayi masa wannan mummunar rauni har da cire haƙora, tabbas ba zai taɓa yadda ba dole sai ya ɗauki fansa wanda zata kasan ce ta ramuwar gayya.


Washe gari Bintu garau ta ta tashi (yarinya taji hannun likitoci,)ko da ta farka banɗaki ta shiga tayi wanka tare da brosh,tana fitowa kuma taci karo da haɗaɗɗiyar doguwar riga A kan gado,dan haka ta shirya A nutse kana ta ɗauki rigar ta saka,masha Allah tubarakalla maƙi gani ya kau da ido tabbas Bintu kyakykyawar yarinya ce ta ajin farko Allah Ubangiji ya hore mata ƙira mai kyau da jan hankali duk sutturar da tasaka sai kaji kamar ka saceta,turarukan da ta gani ta ɗauka ta feshe jikinta dasu kana ta nufi bakin ƙofar da nufin fita,tana ɗora hannun ta kan mariƙin ƙofar, taji ana ƙonƙosawa A hankali,dan haka kawai sai ta ƙara sa buɗewa,wani irin wal hasken fatar sa ya haske mata idanuwa,babu shiri ta shiga rage girman idanuwanta A kan sa,yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta ƙananan kaya fuskar sa sai fitar da wani haske take da kwarjinin sa, ganin ta shirya kawai sai ya juya batare da yace mata komai ba,da sauri ta bi bayansa dan tasan tafiya gida zasuyi maganar ce dai ba zai iya ba saboda tana masa wahala.

A can asibiti kuwa Sayyid ya samu farfaɗowa, Dady Mansur kuwa ba tare da wani jinkiri ba yashi ga watsawa ɗan nasa tambayoyi A kan wanda yaso kashe masa shi,gyara zama Sayyid yayi ya shiga sheƙa musu karya abinda ya faru da ban abin da ya faɗa musu da ban, Dady Mansur ya miƙe A matuƙar fusace yace" kai tashi mu tafi gida ai banga ta zama ba,ashe da ɗan ta adda muke rayuwa bamu sani ba!'batare da ya jira sallama ba ya tasa ƙeyarsu sai estate.

Kamar tare suke lokaci ɗaya sukayi pakin suka fito gaba ɗayansu,Bintu tana arba da Sayyid kuwa ta zunduma wani uban ihu tare da komawa bayan Abdallah ta ruƙunƙumeshi,so sai fa Bintu ta firgita da ganin Sayyid dan A haƙiƙanin gaskiya ya dasa mata mugun tsoron sa,wani mugun kallo Abdallah ya shiga aika musu gaba ɗayansu kamar yadda Dady Mansur yake auna masa nasa mugun kallon tamkar idanun sa zasu waɗo, A hankali ya juyo da ita gaban sa tare da saka yatsansa guda ya ɗauke mata hawayen da suke ta gudu kan kyakykyawar fuskarta,cikin nutsuwa yace" mata, ke ki nutsu babu abinda zai sameki ina tare da ke!' daga haka ya janyo hannun ta suka wuce su Dady Mansur sake da baki,ɗaga murya yayi yace" Ni ba sa anka bane wannan maganar bazan ƙyale ta ba tunda ba jaki kasamu ba anjima kuzo falon Alhaji Baba kai da kilakin taka!'ko juyowa Abdallah baiyi ba balle yasa ran cewa yaji abinda yace masa,fuuu ya ja hannun Sayyid mama ta mara masa baya.


Tunda suka shiga falon babu abinda Taufiƙa ke yi sai kallon hannayen su da

Please Login or Register in order to submit comment