Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiyar dan haka sai kaje ka ƙara sa aikin ka kai ɗaya!'cikin tashin hankali nanu ya kwanta a ƙasa yana mai neman afuwar shugaba,nasan nayi kuskure amma ayi min afuwa!' shugaba yace"tabbas yanzu yarinyar nan zata dinga bibiyar ka ta muryar ka, don kuwa ka riga ka buɗe mata hanya da ace kayi haƙuri ka barta a iya tsoron da muka dasa mata da yanzu bamu da wata matsala yanzu ka riga ka rusa komai!'yanzu lalata wannan shirin yana da matukar wuya, saboda muryar ka ta riga ta zauna a cikin ƙwaƙwalwar ta,cikin ƙara yin ƙan da kai yace"yanzu meye abinyi shugaba?yace"dole sai mun nemi taimakon dodo jack dan haka yanzu kaje za muyi magana bayan na gana dashi!'nanu dai ya haƙora ne amma ba dan ransa yaso ba dan sai yanzu ya ankara da babban kuskuren da yayi baya son wannan abin da yayi ya zama shine sanadin tonuwar asirin sa, duk yadda zaiyi da yarinyar nan sai yayi dan samun cikar burin sa da kuma rufuwar asirin sa,


Nafisa dai tana cikin tsaka mai wuya ta rasa inda tunanin ta zai tsaya maganganun Bintu ne suke ta kaiwa da kawowa cikin ƙwaƙwalwar ta,anya kuwa tana da wannan ƙwarin gwiwar a wajen Umar?duk da tana da tabbacin bai san komai akan abinda ta aikata ba,amma bata tunanin akwai wannan yardar da Bintu take faɗa a tsakaninsu,haka kawai take jin bata yadda da kanta a wajen Umar ɗin ba,to ko gwadawa zatayi ta gani ko zata dace?goge zufar dake ta tsatstsafo mata tayi,a fili ta furta,zan gwada Bintu zan ga yadda Umar ya ɗauke Ni da kuma kallon da yake min zan tambaye shi abinda yake damun sa zan gani ko zai gaya min indai kuwa ya faɗa min to tabbas zan ƙara kwantar da hankali na saboda na yadda ya amince dani ba kuma ya zargi na da aikata masa babban laifi.


Abdallah ya samu duk wasu bayanai daya buƙata a kan Alhaji Rufa'i kuma ya gamsu da gaskiyar sa,yanzu yana tunanin kiran sa dan su tattauna akan batun Alhaji Shamsi tunda har yana tunanin shi Alhaji Shasin zai iya sanin kome ne ake rigima da neman sa ta kowace hanya,yinin ranar bai samu sukuni ba saboda yawan aiyukan da ya aiwatar a ranar duk wasu baya nai da yake bukata na mutanen da yake da alama akansu ya samu,dan haka ba tare da wani ɓata lokaci ba ya fara baza ma aikatan sa dan soma bincike akan su,


Bai samu shigowa gidan ba sai misalin goma na dare,a gajiye ya shiga ɓangaren sa,kai tsaye ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shaya,sai da ya shirya tsaf kana ya nufi dinnin dan samawa cikin sa wani abun,

Tun ƙarfe takwas take duba agogo da leƙen window ko zataga dawowar sa amma shuru bai dawo ba ga yanayin garin da hadari alamu ya nuna dai yau zasu iya samun ruwa,dan ma dai damunar batayi nisa ba,
hakan ne yasa taji duk ta damu da rashin dawowar tasa ko lafiya yake?ta riga ta daɗe da sanin baya wuce wannan lokacin,shi yasa duk tabi ta damu,dan hararar hanyar tayi tare da cewa ko me yasa ma na damu bayan ko ya dawo ba lallai ne yayi min magana ba!'ta faɗa tamkar yana kusa da ita har da dan murguɗa baki,sai dai kuma duk da hakan ta kasa haƙurin shi yasa tana jin karar mota tayi saurin bude labilan tana leƙawa,wata sassanyan Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ta tabbatar da cewa shine ya shigo, komawa tayi ta zauna abakin gadon tana tunanin ta yadda za ayi taje ɓangaren nasa tunda bata da sauran wani abu da zatayi acan ɗin,ta gumi ta zuba,can kuma sai ta miƙe, toilet ta shiga tayi brosh tana fitowa ta saka wata rigar bacci wadda ta tsaya iya cinyoyin ta daga nan tayi kwanciyar ta dan ta rasa hanyar da zatabi dan zuwa ɓangaren nasa,kalan ma inje ya koroni ta faɗa tana tura baki tare da shigewa cikin ɓargonta saboda yanayin iskar da ake ga dukka nin alamu dai ruwa zai iya zuba ako wane lokaci.


Abdallah ma dai a gurin sa kusan hakane,aiki yake amma hankalin sa yana kan duban hanya,tunanin zuwan ta yake akoda yaushe,sai dai har zuwa wannan lokacin baiji motsinta ba,ɗan tsaki yayi tare da janye laptop ɗin dake gaban sa,tashi yayi ya shiga toilet Jim kaɗan ya fito,ya ɗanyi abinda ya zama al dar sa,kana ya kwanta bayan yayi addu'oin sa,so yake ya kwanta ya ɗan rage bacci kafin ajima ya tashi yayi nafilfilu,sai dai kuma hakan ya gagara a wajen sa,mamakin yadda akayi ya kasa samun sukuni saboda yarinyar yake,ta wani bangaren kuma yana mamakin yadda ta iya kwanciya ita ɗaya,ya santa da tsoro gashi kuma yana gani kamar a kwai abinda yake damunta a kwanakin nan,lumshe idanun yayi yana jin wani irin yanayi a can cikin jikin sa,iska ce ta fara kaɗawa mai ƙarfi wadda take tasowa da ƙura,da sauri ya tashi ya kuma gyara windows ɗin ɗakin,duk abinda yakeyi zuciyar shi na wajen ta, gani yakeyi tausayin Bintu zai iya saka shi a wani hali,duba da yadda ya kasa sukuni ganin yau gaba ɗaya bai ganta ba,ga yanayin tsoronta dayake taɓa masa zuciya, ji yake tamkar yaje ya dubata,kasa zama yayi a ɗakin ya fito falo saboda yana ganin kamar zaifi samun kusanci da ita.


"Can cikin baccin ta ta dinga jin kamar ana ta shinta a matukar firgice ta farka tana son yin addu'a amma hakan ya gagara saboda yadda taji tamkar an rufe mata baki, cikin zuciyarta ta ta dinga ƙoƙarin yin addu'ar yayin da duk jikin ta rawa yake,ga wata irin walƙiya da ake yi da tsawa saboda ruwan da akafara tamkar da bakin ƙwarya,kuka ta saka tana laluben hanyar da zata sauka daga gadon dan ta kunna hasken ɗakin,da ƙyar ta samu ta lalubo wayar ta ta kunna tare da saukowa daga kan gadon hasken ɗakin ta fara kunnawa,raɓewa tayi a can lokon ɗakin babu abinda jikin ta yake sai rawa saboda tsananin tsoro,ji take kamar ba ita kaɗai ce acikin ɗakin ba, zuciyarta kamar zata faso kirjin ta haka take ji,

Gaba daya ya kasa samun sukunin zuciya ba ma kamar yadda yaga an tsuge da ruwa wanda yake tafe da tsawa da walƙiya,baya jin zuciyar shi zata barshi ya nutsu ya aiwatar da wani abu ba tare da yaje yagano amanar da Alhaji Baba ya bashi ba,cikin wani irin zafin nama ya miƙe tare da fita daga ɓangaren nasa,kai tsaye ya nufi ɗakinta yana kusanta ɗakin yanajin bugun zuciyar shi na ƙaruwa,a can lokon ɗakin ya hango ta a rakuɓe kamar wata ƙadangaruwa,tanajin buɗe ƙofar tasa ta ƙara ƙarfin kukan ta,tare da runtse idanun ta,cikin ta kun shi na zaratan maza ya nufo inda take,yayin da zuciyarta take ci gaba da wani irin bugu jira kawai take taji yadda Ubangiji zai yi ikon sa akanta,lokacin da ya ƙaraso kusa da ita sai taji yanayin bugun zuciyar ta ya sauya wani irin sanyi taji yana shigarta haka kuma hankalin ta yana kwanciya zuciyar ta na fita daga cikin mugun firgicin da ta shiga,zuba mata ido yayi batare da yayi mata magana ba,A hankali ta shiga buɗe idanunta saboda sassan yan ƙamshinsa da ƙofofin hancinta suka fara shaƙa wanda ya riga ya zama hadda a cikin hancinta,idanun ta ne suka sauka akan kyawawan ƙafafunsa da suke kwance luf cikin tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin,cikin wani irin sauri wanda yake gauraye da wani irin shauƙi ta faɗa jikin sa tare da ƙankameshi tana kuma sakin wani marayan kuka mai cike da ban tausayi,riketa yayi sosai tare da ƙara gyara mata kwanciya,yana ɗan shafa bayanta wanda hakan yake nuni da calmin ɗin ta da yake son yi, bai ce mata ko mai ba sai ɗan sunkuyawa da yayi ya ɗauki wayar ta datake yashe a ƙasa,kana ya jawo hannun ta suka fita daga ɗakin,suna gaba da shiga falon sa,suka juyo muryar inno,ɗan tsayawa yayi saboda ƙarasowar innon gaban su,cikin yanayin damuwa tace"me yake faruwa ne Abdallah,me yasa mu Batular?ta jero masa tambayoyin tana riƙon Bintun da har yanzu hawaye basu daina saraftu akan kyakykyawar fuskarta ba,

Cikin yanayin sa na ƙoƙarin ɓoye damuwar dake cikin zuciyar sa ya ɗan karyar da kan sa tare da cewa"inno tsoro ne kawai da ita san nan kuma,,sai ya ɗan yi shuru kamar yana lalubo abinda zai cewa innon,kana ya cigaba da cewa, sannan tana yawan tsorata ko mai tsoro ne yake bata,kamar dai bata jin daɗi!'ya ƙarasa maganar da ɗan kallon Bintun,inno cikin damuwa da tashin hankali tace"subhanallah me yake tsorata ki Bintu?ta juya tambayar ta kan Bintu, Bintu dai ta kasa magana sai hawaye,dan bata san mai zatace da inno ba,inno tace"anya ba makaraine suke san shafar ta ba?tayi maganar tana duban Abdallah,yayin da shi kuma ya zubawa Bintu idanu wanda maganar inno tayi saurin hasko masa wani abu makamancin abinda ta faɗa,(idan baku manta ba Abdallah yayi ilmin addini mai matukar zurfi,so dan haka yana da ilmin sanin sihiri ko jinnu saɓanin wasu ƴan bokon da zaku ga sam basu yadda da irin wannan abun ba, Abdallah yasan cewa sihiri gaskiya ne haka jinnu ma gaskiya ne,dan haka bai jahilci maganar inno ba)tsai yayi da ransa yana mai hasaso al al'amarin Bintu tabbas tana buƙatar addu'a,amma dai bai kawowa ranshi ga wanda yayiwa Bintu wani abu ba kawai dai yasan Bintu al'amarin ta yana buƙatar addu'a duba da yadda gaba ɗaya ta birkice ko addu'a bata son yi wanda shi kansa shaida ne akan Bintu ba haka take ba tun kafin suyi kusan ci da juna yasan tana da matukar riƙoda ibada,shi yasa yanzu bai sha wahalar gano yadda take sakaci da addu'a ba.

A hankali ya ɗauke idon sa daga kallon da ya ƙure Bintu da shi,ya maida kan inno tayi zukuɗi tana jiran amsar sa,sai da ya ɗan huro iska daga bakin sa kana yace"hakane inno addu'a ya kamata ayi mata,insha Allah gobe zamu fita akwai wani malamina zamuje gurin sa!'murmushi inno tayi dan da tayi tunanin Abdallah ba zai yadda da abinda tace"ba,yauwa hakan yayi Allah Ubangiji ya kareku daga sharrin mutum da aljan ya tsare bayanku da gaban ku yasa kusa zama abin kallo da tsoro a idon maƙiayan ku,Amin Abdallah ya amsa yana mai juyawa dan shiga falon sa,yayin da inno ta bar zuciyar Bintu cikin wani irin hali na tunani da,tsoro mai tsanani,a hankali ta ta taka tabi bayan sa,tana waiwayen inno da take ta Binta da wani irin murmushi mai cike da ma anoni masu tarin yawa,a haka ta shige falon wanda shine sanadin rabata da kallon inno,tana rufe ƙofar ta zame ajikinta tare da saka wani irin kuka mai taɓa zuciya wai ya zatayi idan akace yau binciken ta ya gano mata inno cikin mugayen da take zargi,ya zatayi da rayuwar ta idan akace yau macen da take ƙauna,takewa kallon tafi kowa ƙaunar ta,a cikin gidan nan, tabbas wannan fargabar ita zata jefata cikin wani mugun hali na damuwa,jin an kamota yasa ta ɗaga jiƙaƙƙun idanun ta tana kallon sa wanda shima ɗin kallon idanun take bayan ya samu nasarar ɗagota daga zaunewar da tayi,cikin neman agajin makusancin ta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kukan da take jin ta fara shi kenan har sai zuwa ranar da gaskiya ta baiyana,idan kuma gaskiyar ta baiyana a gaɓar da bazataso ba tabbas hawayenta bazasu taɓa daina zuba ba,tana ƙaunar inno har cikin ƙashi da jinin ta,kamata yayi suka fara tafiya har zuwa ɗakinsa zama yayi da ita ajikin sa,yayin da zuciyar sa take san gagarar ɓoye damuwar sa a wannan karon,wanda yake tunanin girman damuwar wannan lokacin ne yayi mata yawa,jingina yayi ya ɗan kashin giɗa ya kasa ce mata komai har yanzu dan bai san ta ina zai fara ba,

Cikin tausayawa kanta da rayuwar da zata fuskanta nan gaba ta fara bashi labarin yadda sukayi da Dije,ba tare da ta ɓoye masa ko alif ba,ta gama maganar tana mai cusa kanta cikin jikinsa tana murzawa wanda hakan ne yake nuni da tsananin damuwar da take ciki,cikin muryar ta da ta dashe tace"Yahh Abdallah,yaya zanyi da wannan aiki da ya ɓullo min?kagayan ta ina zan fara bincikar matan da suka fi nunamin ƙauna ta gaskiya a cikin wannan duniyar,su kaɗai ne matan danasan sun fara ƙaunata bayan ƙaunar mahaifiyata,su kaɗai ne matan da suka karɓeni batare da ƙyama ba su kaɗai ne matan da suka fifita ƙaunata akan ƙaunar jikokin su batare da sun san Ni ɗin jinin su bane,su kaɗai ne matan da suka fara yarda dani alokacin da narasa yadda da amincin kowa a cikin gidan nan,sun maida Ni mutum sun maida Ni jikar su sun yi faɗa da jikokin su akaina,to kagayamin me yasa ba zan shiga wani hali ba duk ranar da akace wannan ƙauna ta munafunci ce ta yaudara ce ta ha inci ce,me kake tunanin zanyi a ranar, wallahi ba zan iya ɗauka ba,Ni bazan iya ba!'ta faɗa tana bugun ƙirjin shi tare da ƙara sakin wani marayan kuka mai ƙun tata zuciyar maiyin sa da kuma mai sauraren sa,hannun ta ya kama duka ya riƙe kana cikin wata irin murya da ta saukarwa da Bintu nutsuwa da kasala yace"Bint!'shiru tayi tare da yin luf tamkar wadda bata numfashi,hannu yasa ya shiga gyara mata lallausar sumar kanta wadda duk ta bar baje,kana yaci gaba da cewa',Bint injin ke musulma ce?jin jina kan ta yi batare da ta ɗago ba,yace"yauwa to kinga kuwa dole ki amshi ƙaddararki duk yadda yazo miki domin wannan shine cikar imaninki da cikarki musulma,kuma bawa baya taɓa tsallake wa ƙaddarar sa to ki ƙaddara haka taki ƙaddarar tazo kuma bazaki taɓa iya sauya ta ba,ko baki ga yadda Ni nake rayuwata ba?Bint kin san rayuwar da nayi kuwa kin san rayuwar ƙuncin da danayi kin san yadda aka ƙuntatawa rayuwata,kin san yadda nayi rayuwa a hannun kafurai alhalin Ni ina cikakken musulmi?kin san yadda zuciyata takeyi aduk lokacin da aka ƙuntatawa rayuwata da yin ibadar da batawa ba kuma addinin da ban yadda dashi ba, Bint amsar itace duk baki san wan nan ba baki san meye abinda na fuskanta a cikin rayuwata ba, taki kawai kika sani,dan haka ina so kiyi haƙuri,mu fuskanci abinda ke gaban mu abinda Dije ta gaya miki gaskiya ne,baka taɓa gane munafukin ka sai da dabaru,kuma baka taɓa gane masoyin ka na gaskiya sai kashi ga halin rayuwa,ɗago kanta yayi,yana kallon fuskar ta sauri tayi ta rufe idon ta saboda wani kallo da taga yana mata mai shiga cikin jiki da jini,ɗaga mata gira yayi cikin wani irin salo da shi kansa bai san ya iya shi ba, hakan ne ya bata kunya har ta maida kanta ta sunne ajikin sa,

Ɗaga ta yayi tare da cewa bamu ga ta bacci Bint muna da babban yaƙi agabanmu muna da buƙatun da muke nema Allah ya biya mana,dan haka dole mutashi mu roƙe shi kiyi haƙuri ki Kore duk abinda ke kawo miki farmaki da wasu wasi cikin zuciyarki kinji ko!'ya faɗa cikin matuƙar nuna kulawar sa gareta,

Kallon sa kawai take cike da mamakin sa,dama haka yake da matukar tausayi, tabbas tayi mamakin yadda akayi ya tsaya yana nuna kulawar sa akan ta kamar haka,mutumin da tasan baya yin shiri da duk wani abu da zai saka shi yin surutu mai tsayi,ta shi tayi kamar yadda ya Umar ce dan yan zu ya riga ya karya mata zuciya da kalaman sa, sai taji tana matuƙar san jin labarin sa dan ga dukkanin alamu ya sha gwagwarmaya da ƙalubale a cikin rayuwar sa.


Sun daɗe suna salloli duk da dai Bintu dauriya kawai take yi, amma sam bata jin daɗin jikinta da dukkanin rayuwar ta,amma cikin taimakon jarumin mijinta mai tsananin riƙo da addinin sa mai kishin addinin sa ta samu ƙwarin gwiwar ganawa da ubangijin ta,cikin ƙarfin hali da miƙa lamuran su gare shi,basu suka kwanta ba sai misalin ƙarfe uku na dare,daga nan suka sami yin Bacci cikin salama da nutsuwar zuciya,


A cikin wannan safiyar kuma da ta waye Abba Umar ya dawo daga ƙasar Italiya,wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Anty Nafisa ba, tunda ta riga ta sakawa ranta zata yi abinda Bintu ta shawar ta mata,hakan ne yasa tayi masa shirye-shiryen da ta daɗe bata yi masa irin sa ba,shi kansa sai da yayi mamakin hakan,amma dai bai kawo komai cikin zuciyar sa ba,lokacin da ya gama shirin sa ya fito tsaf dashi dan zuwa gaida mahaifinsa da iyayen sa mata har ta gama yi masa duk wani shiri,sai dai yace tayi haƙuri yaje ya gaida iyayen sa,dole tayi masa fatan dawowa lafiya duk da zaƙuwar da tayi suyi maganar datake cin ranta,

Sai da ya fara zuwa ɓangaren Hajjah kana ya fito ya shiga ɓangaren inno,wanda a daidai lokacin ne kuma Bintu da Abdallah suka fito dan zuwa gurin malamin sa malam Nuhu da yace zasu je,tunda ta doso falon ta dinga jin zuciyar ta na wani irin bugu wanda har saida ta dafe ƙirjinta, cikin kulawa Abdallah ya ruƙota ganin tana ƙoƙarin faɗuwa,kallon sa tayi idanun ta cike taf da ƙwalla, ɗan girgiza mata kai yayi kana yasa hannu ya goge mata wadda ta fara zubowa kan fuskarta,tare da jan hannun ta suka fito falon tare da ƴar guntuwar sallama saman leban sa,


A can ɓangaren Dije kuwa tun bayan rabuwar su da Bintu uwar ɗakinta tayi mata waya da ɓoyayyar nomba kamar yadda ta saba,ta sanar da ita a safiyar yau ɗin tana son su haɗu, sai dai bata gaya mata inda zasu haɗu ba, tasan dai sai tabar gidan zata faɗa mata kamar yadda ta saba yi,shi yasa tunda ta tashi take sauri dan tana son haɗuwa da Bintu,saboda tunanin da tayi,akan haɗuwar su da Hajiyar yau,zata gayawa Bintu ta yi ƙoƙarin biyota a baya,tunanin ta anan kuwa,tasan Bintu tana da tunani da wayo,idan taga koda bayan matar zata iya ƙoƙarin shaida ta aduk inda ta ganta, shi yasa take son lallai Bintu tabi ta ayau, tana ganin hakan ma kamar wata hanya ce zata sauƙaƙa musu aiki,cikin hanzari ta gama duk aiyukan ta,tare da kimtsawa ta fita dan zuwa sashen inno,

A can ɓangaren inno kuwa,cike take da farin cikin ganin Umar ɗin,sai da ta cika gaban sa da kayan taɓawa,kana ta samu guri ta zauna,tana cewa Umari na saukar sassafe kenan kayo mana?ya buɗe baki daniyar bata amsa wayar sa ta fara ringin,dan haka ya fasa faɗar abinda zai faɗa tare da zato wayar,ɗagawa yayi duk da cewa ɓoyayyar nomba ce aka kirashi da ita,karawa yayi akunnen sa tare da yin sallama cikin kamilalliyar muryar shi,daga can ɓangaren akace, ina fata dai da Umar Balarabe nake magana?Abba Umar yace"nine Ina sauraren ka!'daga can aka kuma cewa,yauwa to ba komai ne yasa nakiraka ba sai kawai ɗan na tambayeka shin ka shirya haɗuwa da iyalansa da karasa su tsawon shekaru....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 44 ```



Wata irin zabura Abba Umar yayi tare da miƙewa tsaye,cikin tashin hankali da rawar baki yace"waye kai?sai dai ina kafin ya kuma cewa wani abu tuni ankashe wayar ɗif, Abba Umar gaba ɗaya ya ruɗe ya kasa yarda ma wayar ta mutu sai nanata hello yake, sai da inno ta tashi ta kama hannun sa tare da zaunar dashi cikin nuna kulawa tace"Umarina me yake faruwa ne?ka nutsu ai ina tunanin ankashe wayar,waye yakiraka a waya,yake son tada maka da hankali?hannu yasa ya goge zufar da take sauko masa kamar wanda aka sheƙawa ruwa,ya kasa amsawa inno tambayoyin ta,gaba ɗaya antayar masa da tsohon mikin dake dan ƙare cikin zuciyarsa,inno karki damu wata ƴar matsala ce daga wajen aikin mune!'to dan Allah ka kwantar da hankalin ka kar kace zaka saka yawan damuwa aranka kaji ko!'murmushi yayi wanda kana gani kasan na yaƙe ne,yace"shike nan inno,bari na wuce wajen Hajiya Babba,daga nan zan ɗan shiga na kwanta, sallamar Abdallah ce ta katse shi daga sallamar da sukeyi da inno, yana tafe hannun sa sarƙafe dana Bintu,inno tace"yauwa Abdallah zo ku gaisa da Abban ku Umar shine kuma ya baka auren Bintu!'ta faɗa tana kallon Bintu da ta rakuɓe a bayan Abdallah,tunda inno ta ambaci sunan Abba Umar ta shiga wani Irin yanayi na matuƙar shauƙi da ƙauna, A hankali ta fito daga bayan Abdallah tana takawa har zuwa gaban Abba Umar tare da durƙusawa kamar yadda taga Abdallah yayi,ƙasa tayi da kan ta tana sauraren bugun da zuciyarta keyi.


Abba Umar kuwa tunda ya zubawa Bintu da Abdallah ido ko ƙiftawa ya kasayi,kuma baya fatan abinda zai rabashi da kallon waɗan nan yara da yake kallon su tamkar wasu taurari acikin idaniyar sa,muryoyin su ne da suka gaida shi atare suka yanke masa tunani da ɗimuwar da ya shiga,cikin wani irin fillin da zuciyar shi ta shiga ya dora hannayen sa duka biyun a kawunan su,yana wani irin murmushi mai ɗauke da wani irin yanayi na tsananin tausayin kansa,yace"sannun ku ƴaƴana tunda kuke cikin gidan nan bamu taɓa haɗuwa ba sai yau,ko da yake Allah ne bai nufa tun can zamu gana ba sai yau ɗin,ina fata dai kuna lafiya? gaba ɗaya suka amsa atare har ɗan duban junan su sukayi saboda yadda suke yawan haɗa baki gurin faɗar abu alokaci guda, Abdallah ne ya fara tashi ganin Abba Umar ɗin yayi hanyar fita,itama tashi tayi tabi su A baya Abdallah yace"inno zamu tafi sai mun dawo!'tace"to Allah ya kiyaye ya bada sa'a ya amsa da Amin kana suka fita gaba ɗayansu.


Suna tafe da Abdallah da Abba Umar suna taɓa hira,tunda yake cikin gidan bai taɓa yin hira ko wata doguwar magana da ƴaƴan Alhaji Baba ba,Amma ƙaunar Baffan nasa da ban take azuciyar sa,ji yake tamkar da mahaifin sa yake magana,shi yasa yakejin wani irin nishadi da farin ciki mai yawa a zuciyar sa,Bintu ma dai tana cikin shauƙin ƙaunar mahaifin nata ji take tamkar taje ta rungume shi tace Abbana ina sonka,acikin wannan hali Dady Habib ya same su,shima cikin biyayya suka gaida shi,am sawa yayi fuska cike da fara'a yace"kai kam Umar kaci sa ar ƴaƴan naka har rakiya suke maka,mu da muke tare da su kullum har yanzu sun kasa sakin jiki damu kamar waɗan da zamu cinye su!'ya fadi maganar cikin yanayin zolaya,ɗan ƙasa da kai Abdallah yayi bai ce komai ba haka nan fuskar sa ba yabo ba fallasa,Abba Umar yace"kasan haɗuwar jini ya faɗa shima cikin zolayar yana miƙawa ɗan uwan nasa hannu dan su daɗa gaisawa,daga nan dai sukayi sallama ya wuce part ɗin Hajiya Babba Dady Habib ma ya shiga falon inno,


Abdallah ya kalli Bintu lokacin da yaga tabi bayan mahaifin nata da kallo,kamo hannun ta yayi cike da tausayi, suna ƙoƙarin shiga motar da Yahya tuni ya buɗe musu yana jira su shiga ya ja,sai ga Dije da sauri har da ɗan hakinta daga Ni dai tayi gudu kafin ta cimma su,tsayawa sukayi gaba ɗaya suna kallon ta sai da ta samu daidaituwar numfashin ta kana suka gaisa da Abdallah Bintu ma gaida ta tayi,Dije tace"ko zaku bani minti biyu zan ɗan yi magana da Bintu? Abdallah ya saki hannun Bintu tare da cewa babu damuwa!'motar ya shiga,ita kuma Bintu suka keɓe da Dije,duban Bintu tayi cikin nutsuwa tace"Bintu ko da hanyar da zaki bi dan bin sahu na A yau? Bintu tace"ban fahimta ba!' ɗan numfasawa Dije tayi tare da ɗan duba hagu da daman ta kana tawa bintu bayanin abinda take nufi da kuma manufar ta naso ta bi bayan nata a yau,sai a san nan Bintu ta fahimci Dije da manufar ta,cikin fargaba da sanyin jiki tace" anya kuwa Mama Dije babu matsala?Dije tace"Bintu wai me yasa kwana biyu naga gaba ɗaya baki da ƙwarin gwiwa ne? mai yake faruwa dake?ko tun maganar mu ta juya ne ya sauya ki haka?wato dai nasihuna basu shiga kunnan ki ba ko? Bintu ta goge hawayen da suke ƙoƙarin zubo mata tace"mama Dije kiyi haƙuri zanyi duk abinda kika Umar ce Ni,amma zan fara gaya masa sai musan shirin da

Please Login or Register in order to submit comment