Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamewa daga jikin sa,sakin ta yayi kana ya ɗanja da baya batare da ya ɗauke idonsa akanta ba,Anty Nafisa datayi mutuwar tsaye daƙyar ta iya ɗaga kafafunta tare da kama hannun Bintu suka fara tafiya dan shiga falon inno, Anty Nafisa ta shiga tsananin mamaki da irin wannan soyayyar da ta hango cikin idanun Abdallah da Bintu,anya kuwa soyayya zata bari Bintu tayi mata abun da ya dace akan wannan al'amari?to amma dai bazatayi saurin karaya ba tunda wannan tunanin tane ba tunanin Bintu ba,da haka suka dan gana har zuwa cikin ɗakin Bintu batare da kowa ya gansu ba saboda basu tarar da kowa A falon ba, inno tana sashen Alhaji Baba ita kuma Taufiƙa sun ƙule cikin ɗaki tana nemarwa kanta mafita,shi yasa suka shigo ba tare da kowa ya gan suba.



Suna shiga ɗakin Anty Nafisa ta maida ƙofar tare dasa mata key,zama tayi gefan Bintun wadda ta shiga duniyar tunani, gaba ɗaya tunaninta yana kan wannan ɗakin itafa tasha alwashi ko zata rasa rayuwarta sai tagano sirrin ɗakin nan, wannan abin da akayi mata ba komai bane ba kuma ba zai sa taji ta karaya ba,ji tayi ma tamkar an zaburar da ita akan al'amarin,dafata Anty Nafisa tayi tare da cewa Bintu wai mai yafarune? tun ɗazu nake jiranki ganin bakizo bane yasa na biyo bayanki!'Buntu tace"ba wani abu bane ba fa Anty, A hanyar zuwa wajenki ne fa na ɗan samu tsautsayi,sauri tayi ta kawar da zan cen da cewa Anty Nafisa me yake faruwa ne kike nemana haka da gaggawa?take fuskarta ta sauya saboda motsuwar abinda yake ranta,cikin kama hannun Bintun tace"haƙiƙa ina cikin tashin hankali mara adadi,a hankali ta shiga zaiyanawa Bintu duk abinda ya faru ta ɗora da cewa,tashin hankali na bai wuce yadda zanyi nasan abinda Umar yake shiryawa ba,ban san me yake nufi da mallakawa, gaibu dukiyar sa ba,na shiga matuƙar ruɗani tare da duhun da naka sa ganin haske ko yaya yake!'tun da Bintu ta fahimci inda labarin Anty Nafisa ya dosa ta manta inda take saboda ruɗewa da tunani,me yake shirin faruwa ne?ba dai mijin Anty Nafisa shine mahaifin ta ba?wata irin zufa ce ta shiga keto mata,yayin da ƙwaƙwalwarta ta cigaba da yin zagaye tana auna abinda sa hannun yake nufi da labarin rayuwar ta,da kuma sunan mahaifinta da fafi ya gaya mata cikin labarinta wanda duk ta mantasu Abaya sai yanzu komai yake dawowa cikin ƙwaƙwalwar ta,ga sunan da ta ambata yayi dai dai da sunan da mutumin nan ya ambata, hakan yana nuni kenan mijin Anty Nafisa ita ya mallakawa dukiyar sa?to yasan da ita ne?kuma waya bashi labarin an haifeta,?tunanin tane ya kai kan matar Baffan ta fafi da mahaifiyar su,to ko mahaifinta ya same su dan ta hanyar sune kaɗai zai iya samun labari akan su ta hanyar sune ka ɗai zai san cewa Laila ta haifa masa ɗaya mace,to hakan yana nuni da cewa suna raye?idan suna raye to suna ina?Bintu fa ta ruɗe lallai tana buƙatar waɗan nan amsoshin a kusa,to amma ai zata iya samun wasu amsoshin wajen Anty Nafisa duk da tasan baza ta gaya mata ko mai ba,amma tabbas tana da yakinin Aunty Nafisa tasan wani abu akan mahaifiyar ta Laila,idan ba haka ba me yasa ta tashi hankalinta, saboda sa hannun?wata zuciyar tace Bintu ki nutsu kar Nafisa ta ganoki dan agurinta zaki samu,rabin amsoshin ki dan kuwa tasan abinda ke baki sani ba wanda kuma zai iya kasancewa wani ɓoyayyen sirri da batason kowa yasani,tabbas dole kiyi ƙoƙarin binciko wannan sirri, Anty Nafisa ta zaman miki tsanin hawa wanda zaki taka dan cimma kyakkyawar manufarki, da wannan tunanin ta juyo tana daɗa fuskantar Anty Nafisa wadda ta zuba mata ido ba tare da ta katse mata tunani ba dan atunanin ta ita take lalubowa mafita, ɗan numfasawa Bintu tayi tare da cewa"gaskiya wannan al'amari yana buƙatar dogon nazari!'cikin yanayin damuwa tace"haba Bintu Ni da nake ta sauri dan zuwa gareki ki bani shawara amma sai kice sai Anja lokaci,idan wani can shawarar baibgagareki ba me yasa wannan zai gagareki?kai tsaye Bintu tace"saboda ban san makamar zaren ba,bani na fara labarin ba dan haka ƙarƙareshi zaiyi min wuya!'cikin tashin hankali Anty Nafisa tace"me kike nufi Bintu?kai tsaye ta kuma cewa ban san ko mai akan batun yarinyar da aka mallakawa dukiya ba,ballantana nabaki shawarar yadda zaki ƙwaci dukiyar da A kasa hannu domin shaidar ta zama tata!'

Wani irin gumi ne mai tafe da wani irin yaji ya shiga sauko mata tako ina,gaba ɗaya miyan bakinta ya ƙafe har wani ɗaci-ɗaci take ji saman harshen ta,hannu tasa ta ɗan share gumin kan goshin ta,kana cikin sarkewar da harshen ta yayi tace"yanzu kina nufin in dai zaki warware min wannan matsalar sai na gaya miki wani abu daya dan ganci yarinyar?jinjina kanta Bintu tayi cikin bata tabbaci,Anty Nafisa ta kuma cewa to idan kuma ban san komai ba fa?wani irin kallo Bintu ta wurga mata a fakaice,kana tace"ai nasan ba zai yiwu ace baki sani ba,kinga fa Anty Nafisa Ni taimakon ki nake yi kuma ina nema miki hanyar da zaki samu abinda kike nema batare da kinsha wahala ba,idan kina ganin wannan ba hurumi na bane babu wata damuwa sai mu canja shawara!'ta faɗa tana mai fargabar kar ta ɗauki maganarta ta ƙarshe,ai kuwa cikin sauri Anty Nafisa tace"gaskiya Bintu gwara mu canja shawara,saboda Ni kaina ban san komai game da wannan al'amari ba,kawai ki taimaka ki kawo shawarar yadda zan ɓullawa Umar ya faɗa min wani abu da yake ɓoyemin!'Bintu dai ba dan ranta ya soba Amma tasan a sannu zata samu abinda take so gurin Anty Nafisa,kuma ko ba komai itama samun bayanai daga wajen Abba Umar ɗin zaiyi mata amfani,dan haka cikin nutsuwa tace"shike nan amma ki ɗan bani nan da zuwa gobe,gaggawa bazai mana amfani ba a wannan gaɓar amma kiyi haƙuri zuwa goben idan Allah ya kaimu!'Anty Nafisa dai ba dan ranta yaso ba haka ta haƙura...


Tana fita Bintu ta ƙwatar da kanta jikin gadonta tare da lumshe idanun ta,tana mai tasbihi ga Ubangiji tare da ƙara gine masa akan baiwa da Ni imar da yayi mata,ita da kanta tana mamaki idan ta duba taga yadda take juya rayuwar Anty Nafisa,duk da ba ason ranta ba,amma Allah mai ƙudura ya ɗora mata shakkar Bintu tare da bin duk abinda ta faɗa mata cikin hikimar sa tasan fidda gaskiyar mai gaskiya,gashi dai yabata ƙwaƙwalwa da tunanin abinda ta tsarawa Nafisan kuma har hakan ya zamo mata alheri,tunda gashi ta sanadin shawarar da tabawa Anty Nafisa ta san abubuwa da yawa wanda su yakamata tasani tuntuni amma bata sani ba saboda wani abu da Ubangiji ya ɓoye wanda babu wanda yasan shi sai shi mai kowa da komai,sai kuma wani irin farin ciki da ya mamayeta saboda kasan cewar ta samu mahaifin ta a raye, kuma wanda ya kasance kamili cikin wannan har gitsatstsen family mai abubuwan al ajabi iri da kala.


A hankali Hajjah ta ɗora hannun ta saman kan ɗan nata, tare da cewa Habibu me yake damun kane? tun ɗazu kazo ka sanyani gaba da tagumi idan da wata matsala ba sai ka faɗa min ba!'ta ƙare maganar cikin yanayin damuwa da da muwar ɗan nata,ɗagowa yayi kana yace"wallahi Hajjah ba komaine yake damu na ba sai lamarin Yaya Mansur,na rasa me yasa idan zaiyi abu baya tunanin mai zai je ya dawo?cikin san jin abinda ya aikata Hajjah tace"me kuma yayi sababben?cikin jin takaicin abun yace"zuwa yayi har sashen Baffa Hashir ya ci masa mutumci wai yasan sune suka ɗauke masa Sayyid, to maza suyi gaggawar fito masa da ɗan sa ko ya ɗauki matakin da bazai yiwa kowa daɗi ba!'ya ƙarasa maganar yana ɗan huro iska ta bakinsa,shuru Hajjah tayi saboda tsabar takaicin halin ɗan nata,Dady Habib ne ya kuma cewa Ni abinda ya bani mamaki ma bai wuce yadda ya ɗorawa ɗan uwan mahaifin namu sharrin satar mutum ba,ko ta ina hakan zata faru?kuma duk yara sa wanda zai ɗauka sai Saiyyid ɗan Mansur mutumin da kusan shine ya raineshi da hannun sa,Hajjah da sai yanzu ta iya furta wani abu tace"anya kuwa Mansur baya shaye-shaye?idan kuwa har baya shan komai to tabbas yana da taɓin hankali,saboda abin nasa ya wuce makaɗi da rawa,kuma wan nan magana har gaban Alhaji dan wannan hauka ne da rashin kamun kai!'Dady Habib yace"nima abinda nayi tunani ke nan shi yasa na fara sanar dake dan kar yaje yayi abinda zai ɓata musu zumunci!'hakane Habibu Allah yayi maka albarka ya kuma shiryaku baki ɗaya kai da ƴan uwanka,da Amin ya amsa cikin jin daɗin addu'ar mahaifiyar tasa.


Kallon ta take ta cikin miƙab ɗin dake sanye a fuskar ta,kallon da take mata kallone na tsana da ƙyashi, da kuma uwa uba baƙin cikin da take son yi mata na toshe mata hanyar samun burinta,tunda taƙi gaya mata inda Abubakar yake wanda ita kuma tayi yaƙinin cewa Laila tasan inda Abubakar yake kawai dai taurin kaine ya hanata faɗa mata,wanda tasan a ƴan kwanakin nan zata sauke mata shi,sunkuya wa tayi ta danƙi gashin kan lailan tare da cewa zaki iya gaya min ko har yanzu baki shirya ba?karfa ki manta kece kika dawo dani kan hanyar da da na kauce mata,wanda dama shine sanadin satoku daga wan can gurin amma sai wani dalilin ya sha kaina na sauka daga kan hanyar da nake da farko, amma sai gashi cikin tabbatuwar samun nasara ta sai ya zamana ke ɗin ke kika dawo da tunani na,to amma me yasa bazaki yi min abinda nake so ba?nace miki in dai kika gayamin suwaye mutanen dasuka ɓoyeku da kuma inda suka ɓoye Abubakar,to nayi miki alƙawarin zan kula da rayuwar Bintu ba zan bari wani abu ya cutar da ita ba!'tana direwa Laila ta ɗauka da cewa ke baki isa ki kare rayuwar wasu ba,tun da kema baki iya kare taki ba,kuma Bintu bata buƙatar kariyar wani bawa kariyar ubangiji take buƙata kuma ta riga tasamu,dan haka sai ki bi wani sarkin Bintu ta riga tafi ƙarfin shu'umancin ku gaba ɗayan ku macuta azzalumai insha Allah ƙarshen ku yana nan zuwa,Ni na gaya miki sai kun to zarta ke da duk wani mai kwatankwacin irin mugun halinki!'kafin ta gama rufe bakin ta matar ta ɗauke ta da wani mahaukacin mari,tana wani irin huci kana tace" ki kiyayeni Ni ba A faɗa ina faɗa,sai kinyi nadamar waɗan nan kalaman naki,dani kike zancen,daga haka ta fita daga ɗakin tamkar kububuwa,tana mai jin baƙin cikin yadda takasa samun abin da takeso,duk faɗi tashin da tayi kuma take kan yi,ko a iya binciken neman Abubakar ta tsaya ya isa a jinjinawa namijin ƙoƙarin da tayi,saboda ita farko neman ABUBAKAR takeyi amma sai tayi kacibus da su Laila,wanda sam da farko batayi niyar ɗauke su ba,amma sai ta canja shawara ta yaudaresu da nufin taimakon su zatayi sai da suka bata labarin su kaf ba tare da sun ɓoye mata komai ba,tun alokacin ta so su gaya mata ko waye ya ɓoye su sai kuma tayi rashin sa a suka gano nufinta,shine dalilin da yasa ta kwashe su gaba ɗaya ta killace da nufin zata iya gane ko waye ta hanyar neman su Lailan da zaiyi,amma sai taji shiru wanda hakan ne ya kuma tabbatar mata da cewa wannan mutumin baƙaramin shu'umi bane,saboda ya kulle duk wata hanya da zata sa agane shi, wannan shine dalilin da yasa tasan tarihin Laila da fafi kuma shine dalilin da yasa take faman ajiye dasu tsawon shekaru,gane Bintun bai yi mata wahala ba tunda tayi binciken ta yadda ya kamata,to kuma sai gashi itama Bintun tana yaƙin neman mahaifiyar ta,abu ɗaya ne yasa ta rabu da Bintu shine tana so ta gano musu wannan mutumin,da zarar tasame shi ita kuma lokacin zata samu kyakkyawar dama akan su su duka,dole tana buƙatar sanin waye wannan mutumin saboda shi kaɗai ne yake da fawar riga ta samun abinda take nema kuma tana ganin kamar Abubakar yana hannun sa,shi yasa take da tabbacin su Laila sun san inda yake tunda sun zauna tare da mutumin,duk da cewa ita bata yar da da wani zuwa wajen boka ba tafi yadda da kaifin basirar ta to amma alokacin sai da ta dangana da wani hatsabbin boka wanda shine ya bata tabbacin anan aka ɓoye Abubakar sai kuma gashi a maimakon ta samu Abubakar sai ta samu su Laila,wan nan abin shi yake matuƙar ci mata rai, kuma tana da tabbacin sun sani amma shegen taurin kansu ya hana su faɗa mata gaskiya,amma babu komai tunda ta haifi ɗiyar da zata nuna mata komai, batare da tasha wahalar da tasha a baya ba,



Tun da ya shiga office ɗin bai huta ba,saboda aiyukan da ya tarar,sai dai lokaci lokaci tana yawan faɗo masa a rai,da tunanin ko ya take?ko wane hali take ciki yasan ta da shegen tsoro,shi yasa duk yake jin damuwa aransa,yana fatan dai Allah yasa bata cikin firgici, wayar dake salular dake cikin office ɗin ce tayi ringin ɗaga wa yayi tare da amsawa da ok ya ƙara so!'ajiyewa yayi tare da cigaba da duba wasu manyan fayal dake gaban sa,sallama akayi tare da turo ƙofar officce ɗin, Abdallah ya amsa sallamar yana mai ƙurawa mutumin da yashigo idanu dan san tuna inda yasan shi,har mutumin ya zauna Abdallah bai ɗauke idanun sa daga kansa ba,cikin tsuke fuska Abdallah yace"me ya kawoka officce ɗina? ƙoƙarin tashi yake ya bar officce ɗin saboda fes ya tuna fuskar mutumin idan bai manta ba wannan mutumin yana daga cikin tawagar su Alhaji Nasir,to me yake nufi da zuwa har cikin officce ɗin sa?Alhaji Rufa'i kamar yasan tambayar dake zuciyar Abdallah yace"Abdallah ka tsaya ka saurare Ni a kwai tarin manufofi da kuma ma ana da muhimmanci cikin wannan ziyarar tawa, wanda banyi wannan ziyarar kai tsaye ba har sai da na nemi izinin Dadyn ka jafar!'tabbas kuwa Abdallah sauraran Rufa i Abune mai matukar mahimmanci,dan haka ina baka umarni daka tsaya ka saurari abinda yazo dashi!'Dady jafar ne yake wannan furucin a yayin da yake sako kansa cikin Officce ɗin na Abdallah,zama yayi ba tare da yayiwa Dadyn nasa musu ba sai dai zuciyar sa cike take da mamakin yadda akayi zai samu wani abu mai muhimmanci daga bakin ɗaya daga cikin abokan gabarsa, wanda shi dai baya raba ɗayan biyu cewa yaudara ce,amma dai bari ya saurare shi ɗan yaji shi kuma da wace irin al mara yazo ko kuma tatsuniya...


Tuna sarwa Alhaji Rufa'i shine babban yaron Alhaji Baba dake kula da kasuwan cin sa na Kano,kuma shike auren daya daga cikin ƴaƴan Alhaji Baba wato sakina,kuma ɗaya daga cikin ƴan kungiyar su Alhaji Nasir,

To gashi dai yayi tattaki yazo har inda Abdallah yake, kome yakawo shi? Wannan duk sai mun haɗu cikin nest page....

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 40 ```


Shuru officce ɗin ya ɗauka na dan wani lokaci,kana daga bisani Alhaji Rufa'i ya ja doguwar ajiyar zuciya tare da maida duban sa kan Dady jafar,yace" jafar akwai al'amari mai matukar ruɗarwa a cikin rayuwar iyalan mai gida,ɗan gyara zaman sa yayi tare da ƙara fuskantar Abdallah ya cigaba da cewa,tun a shekarun baya na fuskanci yadda al amuran ahlin ALHAJI BALARABE yake sauyawa da wani irin san zuciya da san duniya,kasan cewar Ni ba mazaunin Abuja bane ballantana na sa ido akan wasu miyagun abubawan da suke faruwa cikin ESTATE ɗin,to kuma ina cikin taraddadi da tunanin hanyar da zan ɓullowa al'amarin kawai saiga tayin da su Alhaji Hashir suka kawo min na san in shiga cikin su saboda sun san nima zan taimaka, kuma akwai manyan kadarorin Alhaji Baba A hannuna,ganin wannan ma wata dama ce na samu ta samun zaƙulo abinda ake ta ɓoyan sa da kuma makircin da ake son ƙullawa uban gidana kawai sai na amshi wannan tayin cikin nuna farin ciki,nan kuma aka shiga gwagwarmayar dani da faɗi tashin yadda za a samu wannan ajiyar da kowa yake harinta, A lokacin na samu na tara wujjoji masu yawa akan su Alhaji Hashir,sai dai har kawo rana irin ta yau na kasa gano abin da ake nema,duk iya bincikena da bin diddigina amma hakan ya gagara,kuma abinda na fahimta kamar dai nine kawai acikin su ban san wannan sirrin ba Ni kaɗai suka rufewa wanda nakasa gano dalilin haka, har ma na fara tunanin ko sun harbo jirgina ne nasan tona musu Asiri,sai kuma na lura sam ba haka bane kawai dai har yanzu basu gamsu dani bane,ba yanzu suka shirya sanar dani ba har sai sun gamsu da gaskiyata acikin su,kuma ina zargin Alhaji shamsi yasan ko mai akan abinda suke fafutukar nema, wanda shine baya cikin wannan kungiya tasu hasali ma nuna musu yake baza a haɗa baki dashi aci amanar ALHAJI BALARABE ba, duk da cewa zargina bai tsananta A kansa ba amma ya kamata abi sahunsa dan ina da tabbacin zamu sami wani abu daga ɓangaren sa!'yana tsayawa nan A bayanin sa Dady jafar ya ɗauka da cewa, Alhaji Rufa'i duk wan nan bayanan dakayi mana kamar tuni ne a wajen mu sai ɗan abinda ba A rasa ba,da kuma manufar ka ta shiga cikin su Alhaji Mansur,saboda ba a zaune muke ba kuma in Sha Allah muna gab da tonawa kowa asiri!'miƙewa Abdallah yayi tare da duban Dady jafar,gane abinda yake nufi da yayi ne yasa yace"Abdallah baka ce komai ba kuma kana shirin tafiya,ko baka yadda da gaskiyar Rufa'i ba?ɗan jim Abdallah yayi tare da cewa zan neme shi idan na tabbatar da abinda ya faɗa gaskiya ne!' daga haka ya fita daga officce ɗin ya barsu,Dady jafar yace" da Alhaji Rufa'i kar ka damu nasan zaiyi nazarine akan maganarka,saboda Abdallah mutum ne da bayayin abu cikin gaggawa komai yana yinsa cikin nutsuwa ne shi yasa ba zai saurin baka yarda nan take ba!'Alhaji Rufa'i yace" wannan shine halin manya,kuma hakan Abune mai kyau kayi dacen haihuwa yaron ka yana da ƙwazo da himma da kuma uwa uba san tabbatar da gaskiya, murmushin jin daɗi Dady jafar yayi,batare da yace komai ba,kana yaji daɗi da Alhaji Rufa'i bai san matsayin Abdallah a gurin sa ba,hakan yana masa nuni da cewa har yanzu su Alhaji Hashir basu san waye Abdallah ba,kuma hakan yana nufin sune da nasara akansu Alhaji Nasir ɗin.


Fitowar sa daga officce ɗin kai tsaye mota ya shiga Yahya yajashi zuwa asibiti,duk da yadda ƙwaƙwalwar sa ta ɗauki zafi da wannan al'amari hakan bai hanashi nutsuwa ya duba marasa lafiyar da suke buƙatar sa ba,duk da a can ƙasar zuciyar sa ji yake kamar ya koma gidan awan nan lokacin ko dan duba lafiyar Bintu, sai dai kuma hakan ba mai yuwuwa bane dan da akwai ayyuka da yawa da suke gaban sa,wayar sa ya zaro daga gefan aljihun rigar sa, danna wa yayi tare da ɗora ta akunnen sa,ba ayi minti ɗaya ba aka daga wayar,cikin lafiyayyar Muryar shi yace"sani idan kana cikin Kano ina so kayi min wani aiki A nan!'banji mai akace ta ɗaya ɓangaren ba naji dai Abdallah ya ɗora da bashi bayanai akan Alhaji Rufa'i,ya ɗora da cewa inaso bayanan shigo da da sauri,ok kawai yace"tare da kashe wayar ya turata ma zaunin ta..


Dije kin san dalilin da yasa nace ki dawo ko?ba tare da ta jira amsar Dijen ba ta cigaba da cewa,gagarumin aikine ya taso min wanda dole sai da mataimaki,dan haka ina so ki maida hankali kan abinda zan sanar dake, ban ɗaukoki dan kici amanata ba ɗauko ki nayi dan kiyi min aiki,Dije lallai ina buƙatar ki shiga jikin Bintu ba dan kanki ba sai dan kaina da biyan buƙatata,danƙo kunnen Dijen tayi cikin ƙara yi mata kashedi da gargaɗi tace"wallahi wallahi wallahi Dije in dai na sameki da kuskewa daga kan maganata ko cin amanata to ki tabbatar da cewa ƙarshen rayuwar iyalan ki yazo ke nan,ke kuma sai na ƙarar da rayuwarki ta hanyar gana miki azaba iri iri wadda ita kaɗai ta ishi mai irin halinki na cin amana izina,salon da kika fara dashi nakeso ki ɗora ki barta a yadda tasan ki,sonake ki lulluɓeta da kalaman yaudara ki nuna mata kinatare da ita, ki tayata yaƙin nemo wancan shu umin,ni kuma abinda nake buƙata ke nan daga gareta tunda ita da mijinta suna da baiwar gano mugu to Ni kuma da ita zan jingina dan cimma burina!'babu abinda Dije take sai kuka wanda yake tafe da wani irin baƙin ciki na kasancewar rayuwar ta a haka, tabbas da tana da damar canja ƙaddarar ta ta zuwa aƙasan wannan shu'umar mata,sai dai ina, bakin alƙalami ya riga ya bushe Allah da yayo rayuwarta ahaka shi yasan dalilin haɗa ta da wannan mata,insha Allah sai ta zama sanadin bankaɗuwar asirin wan nan makirar mata,duk duniya babu abinda yafi ƙarfin Ubangiji dan haka bazata karaya da waɗan nan mugayen kalaman nata ba,ta riga tayiwa Bintu alƙawari kuma tayi alƙawari ita da Ubangijin ta saita tona asirinta,koda kuwa shine abu na ƙarshe da zatayi arayuwarta,wata gigitacciyar tsawa ta dakawa Dijen wadda har sai da ta toshe kunnuwanta,tare da runtse idanun ta tana kuma mai fatan Ubangiji ya bata dama da nasara akan wannan azzalumar mata,koma wacece,matar tace"kinaji na kina kumajin alwashina akanki dan haka ki tabbatar da cewa ba asamu matsala cikin wannan aikin ba domin shine kwanciyar hankalin ki da rufuwar asirinki da cigaban rayuwar zuri arki!'ki tashi yanzu ki koma cikin ESTATE ki gayawa uwar ɗakin ki cewa kin dawo daga zaman jinyar da kika tafi,daga karshe ina mai kuma tunasar dake muhimmancin amanata!' cikin sanyin jiki da kuma ƙwarin gwiwar rusa rayuwar ta, Dije ta miƙe tare da kama hanya ta fita daga gurin wanda kullum zasu haɗu sai ta canja gurin haɗuwar tasu kai wannan mata ta iya takunta.


Dide ta dawo cikin ESTATE da kyakykyawar niya,da kuma burin hada hannu da Bintu dan su cimma kyakykyawar manufarsu wadda abaya ta dakatar dasu,zasu ɗora daga inda suka tsaya, saboda yanzu tana da cikakken ikon tarayya da Bintun zasu kashe su binne batare da tasani ba ta yadda ita take yiwa aiki amma ta wani gefan aikin rusa rayuwarta da farin cikin ta zasuyi ita da Bintu,cikin ƙudurar Allah gashi ita da kanta ta bata damar fallasa sirrinta da kuma rusa duk wani shiri da takeyi dan cimma mummunar manufar ta,ita da kanta ta bata lasisin tarayya da Bintu,tabbas lokacin karya alƙadarin waɗan nan azzalumai yayi lokacin banƙaduwar sirrin su yayi,zatayi abinda ya dace dan kuɓutar da bayin Allah da basuji ba basu gani ba,ko dan haka tasan Allah bazai taɓa bawa wannan tsohuwar azzalumar ikon cutar da ita ba,dan haka da ƙwarin gwiwar ta ta koma aikin ta ka in da na'in.



Baƙaramin mamaki Bintu tayi ba lokacin da tajiyo Muryar Dije a falon inno,cikin sauri ta ɗauraye hannun ta datayi kwaɓin alkubus,haka kawai taji tana sha awar yiwa Oga Abdallah alkubus,duk da tasan ba gwanin ta ake masa ba amma tunda yana son waɗan nan nau'ikan abincin wataƙil idan yaga dama yaci batare da ya gwasaleta ba,fita tayi daga kiching ɗin cikin wani irin farin ciki dayakasa ɓoyuwa daga zuciyar ta har saman fuskarta,cikin wata dariyar farinciki ta zube A gaban Dijen tare da kama hannun ta,inno tarike baki yayin da taga itama Dijen fuskarta ta cika da farincikin ganin Bintun,tace"kai Bintu irin wannan farin ciki haka,Dije tayi saurin cewa ai inno Bintu tana da shiga rai saboda biyayyar ta ga manya kinga dai ba wani haduwa muke sosai ba amma mun shaƙu da juna!'inno tace"Dije haka maganarki take kuma kema ɗin Dije ai akwai daɗin zama kin san ance sai hali yazo ɗaya ake kulla abota shi yasa kuka shaƙu da Bintu!'Bintu da bakinta yaƙi rufuwa tace"Allah mama Dije nayi kewarki gashi kuma na rasa wanda zan tambaya ina kike,kullum sai nayi cikiyarki a raina nace Mama Dije balakuro babu sallama!'dariya sukayi gaba ɗaya inno tace"ai bakin kine balakuran!'ɗan tura baki tayi cikin yanayin ta

Please Login or Register in order to submit comment