Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wane irin zanuɓi ba,Bintu rayuwarki ishara ce ga mutane masu san zuciya kuma abar koyi ce,ƙaddararki ƙaddara ce wadda take cike da darussan rayuwa ga mutumin da ya gane,dan haka na tuba na janye duk wani batuna zan auri Sayyid dan uwana tunda shi Allah ya zaba min matsayin abokin rayuwa!'cikin farin ciki Bintu tace"Alhamdulillah masha Allah Allah shine abun godiya,kana ta ɗan gyara zamanta tana cewa Anty Taufiƙa ki sani cewa duk wanda yayi imani cewa a kwai wuta kuma akwai aljanna dole ne ya kiyaye kansa daga fadawa daga halaka ta sharrin shaidan wanda zata kasance masa azaba a gurin ubangiji,muna aikata kuskure mai girma a cikin rayuwar mu wanda sam hakan bai kamata ba,duk wanda ya dauki burin duniya ya saka a ransa to kuwa tabbas yayi ƙawance da shaidan,domin shi shaidan babu abinda yake so irin yaga ana aikata saɓo,manzan Allah s.w.a ya tambayi shaidan cewa shin mai yake sawa ƙashin bayansa ya karye? sai yace,yaga ana tuba dan komawa turbar gaskiya,

San nan a kwai lokacin da mala'ika jibrilu yazo yana bawa Annabi a,w,a labarin jahannama har yazo kan ƙofar wuta ta bakwai,irin azabobin da Annabi yaji za ayiwa waɗan da suka kasance a cikin wannan ƙofa sai da ya suma,bayan ya farfaɗone yake cewa da maka'ika jibrelu dama akwai wata al umma ta da zasu shiga cikin wuta? shin zaka bani labairin waɗan da zasu shiga cikin wan nan ƙofa?sai mala'ika jibrelu yace"masu manyan zunubai ne wadan da suka koma ga ubangiji basu tuba ba sune zasu shiga wannan kofar wutar!'wa iya zubilla alla ka kiyashemu da ita,dan haka duk wanda ya tuba daga wani aiki na saɓo da yake aikatawa ba ƙaramin rabone dashi ba,kin ga yanzu ke kin dace muna fatan dacewa har acan ƙiyama!'cak taji an ɗaga ta sama,ƙamshinsa da taji ne ya kuma tabbatar mata da cewa shine,duk da tasan shine kadai zai iya yi mata haka, yace"princess mun gode da wannan ta ƙaitaccen wa"azin haɗe da tunatarwa Allah yasaka da Alkhairi ya bamu dacewa da kuma babban rabo na Alkhairi,yanzu muje ki karya ki bar amaryar Sayyid itama taje gida ta fara shirin sabuwar rayuwa mai cike da daɗi da sirrika da kuma ɗumbin lada gurin Ubangiji!'sai kuma Taufiƙa taji duk tana jin kunyar Abdallah dan haka ta miƙe cikin sanyin jikin da kalaman Bintu suka ƙara saukar mata, cikin nutsuwar da da bata da ita, ta ce dan Allah ya Abdallah ka yi hakuri ina fata zaka dinga kallona kamar Rahima dasu Shakur!'jinjina kanshi yayi cikin jin dan tausayin Taufiƙan yace"kar ki damu Allah ya kaimu ya kuma yafe mana baki ɗaya!'suka amsa ita da Bintu daga nan ta fita daga falon Bintu ta ɗan daga murya tana cewa sai munzo shan biki dan nima ban yafe nawa ba sai anyi mun!'tana dariya a hanyar ta ta ƙarasa fita tace"ai ke angama da babinki tunda komai yayi daidai,shine ƙarshen maganarta da ta faɗa ta kai waje,


Zaunar da ita yayi kan cinyar sa ya fara bata abincin,ganin kamar bata son ci,sai kawai ya shiga ɗurawa abakin shi sai ya tauna sai ya ɗura mata,tamkar dai cin abincin tsuntsaye,(wai ko Ni nan Fatima ƴar uwar Bintu ban taba tunanin Abdallah ya iya irin wannan salon soyayyar mai kashe gaɓɓai ba sai yau)a haka suka gama daga nan kuma ya sunkuceta suka koma daki,


Inno tayi matuƙar mamaki da yadda taga yanayin taufiƙa,ta shigo cikin fara a da walwala,dan haƙiƙa ita kanta tafi jin sakewa da rashin nauyin zuciya a yanzu da ta sauke nauyin damuwarta ta kuma nemi gafarar Bintu,zama tayi gefan inno da take Binta da kallon mamaki,cikin sanyin murya ta gayawa inno abinda ya faru da kuma hirarasu da Bintu ta ɗora da cewa inno dan Allah kema ina neman yafiyarki san nan zanje na gayawa Alhaji Baba da kaina cewa na haƙura da auren Ya Abdallah a ɗaura da Sayyid ɗin!'inno ɗaga hannunta sama tayi tace"Allah na gode maka da wannan hasken Alkhairin da yake ta shigowa zuriyar mu,duk a sanadin su Bintu wan Nan shi ake kira da ɗan Hakin da ka raina, Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a mai albarka ya kuma ciga ba da nuna mana hanya mai kyau, ya bamu ikon binsa cikin tafarkin musulunci,Amin Taufiƙa ta amsa zuciyarta fes babu sauran damuwa.


A cikin wannan kwanakin ne ake ta shirye shiryen auren jikokin Alhaji Baba,yayin da su Bintu suna can suna shan soyayya duk da dai har lokacin Abdallah bai kuma neman wani abu a gurin ta ba,saboda so da tausayi,ita kuwa sai zuba sangarta da taɓara takeyi, amma fa Abdallah yana da burin maida Bintu makaranta,in Sha Allah,babu abinda yafi burge shi a gurin Bintu sai irin tsananin ibada da miƙa lamura ga Allah duk abinda zatayi sai ta saka Ubangiji a ciki, komai zata aiwatar sai kaji tana addu'a ko tasbihi da ya riga ya zauna abakinta,to dake shima Abdallah ba baya bane sai suka haɗu suke raya rayuwarsu da yawan ibadu ga sadaka da taimako,wan nan duk halinsu ne wanda suka koya daga gurin iyayensu,


Yau ake ɗaura auren su Taufiƙa da su Hauwa'u,abin yayi amarshi sosai,kaf iyalan Alhaji Baba babu wanda babu,a ranar da yamma akayi ƙayatacciyar walima,Amare sunyi kyau har ba a magana, Bintu tamkar ka saceta ka gudu fans din ƙudurar Allah kuwa kamar kiyashi haka suka cika babban holl ɗin ESTATE duk wanda ka kalla bakinta har kunne sunci atamfarsu mai zaiba sai wawar kajin walima suke su maman hamra da su Ummu banat kai harda su saudee iyayen rawar ƙafa,su Maryam cika ga su fati nan duk anci gayu an ƙafe aguri ɗaya ana muzurai,gasu nan dai da yawa mutanen idan nace zan lissafo su abun zai ci lokaci, Allah sarki yayata maman nuur tana wajen su Ummi Laila ana shirin kai Amare da ita,kai abu dai yayi kyau haka taro ya watse lafiya,daga nan kuma su Alhaji Baba suka wuce gidan su Anty Samira a ƙa ɗauro aurenta da Dady jafar,Ni kaina bazata akayi min wannan abu baƙaramin daɗi yayi ba, Abdallah zan iya cewa yafi kowa farinci,ikon Allah ya wuce da haka to mu dai sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya ya kawo ƙasantar dakuna,


Tsit kake jin estate din tayi,kowa yana ɓangaren sa ga kuma ƙaruwar Amare da aka samu duk da cewa suna da tazara sosai tsakanin su da iyayen nasu, haka tsakanin su da juna ma a kwai tazara me yawa,dan haka za kayi tsammanin kowa a guri daban yake,tamkar yadda a kayiwa kowacce amarya itama Bintu haka akayi mata basuyi duba da cewa ita ta daɗe da aureba,zaune take bakin haɗaɗɗan gadonta da yasha shimfiɗu na alfarma kai kace gadon sarautane,sallama yayi tare da shigowa ɗakin fuskarsa tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu,kana kallon sa kasan cewa yana cikin farinciki mara misaltuwa,takowa yayi cikin nutsatstsan takunsa mai cike da iko kamar wani saraki,zama yayi a gefan ta tare da dage mayafin lafayar da aka yane dukan fuskarta,cikin taushin muryarsa yace"Alhamdulillah!'kana ya sunkuyo da fuskarshi daidai saitin tata,yana binta da wani narkakken kallo mai cike da shauki,cikin sanyi da lallaɓa ya janyota cikin jikinshi yana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya,tallafeta yayi gaba ɗaya cikin jikinshi yana bin ko ina na jikinta da sunsuna,shigewa jikinshi ta kuma yi tana matsarshi saboda yanayin da take tsintar kanta aciki aduk lokacin da ya kusanto jikinta,ɗago kanta yayi mata ana bin lumsassun idanunta da eye lashes ya kwanta yayi zara zara,har shensa ya kai saman idanun ya shiga lasa tamkar ya samu alewa,wani irin numfashi taja tamkar wadda zata shiɗe,bata gama da wannan yanayin ba,ta tsinci bakinshi cikin nata,yana yi masa wani irin tsotsa tamkar wanda yake shirin tsinke harshen gaba ɗaya,sai ga Bintu na tallafar ƙeyar Abdallah domin taimakawa bakunansu wajen daɗa kusantar juna,a hankali ya shiga ware lafayar jikinta yanayi yana scuizin ɗin jikinta da tafukan hannunshi,saida ya warwareta gaba ɗaya kana ya buɗe idanunshi da suke lunshe tare da zare bakinshi daga nata,kallon shigarta data ɗimauta shi yake,wata fitinanniyar rigar bacci ce wadda akayi mata ado da bakin less baƙa kuma iya kacinta cinya,abunka da fara sai ga Bintu na walwali cikin rigar,wanda take Abdallah ya kuma rikicewa tsumammiyar ƙaunar ta ce takuma tashi tare da shawa awa da ɗokin kasancewa da ita,yana kwadayin kara zuwa wannan burnin na fadama,yana son ƙara zuwa gurin nan da tunda ya shige shi har yau daɗinsa bai bar cikin ƙwaƙwalwa da gangar jikin shi ba,duk da cewa bai je ko ina ba, bai kuma kai inda ya kamata ace ya kaiba,amma dai a yau yana fatan zuwa ƙoramar Bintu mai wuyar mantawa, cikin kunnenta ya shiga raɗa mata wasu kalamai wadanda suke neman zautar da tunaninta kalaman da bata taɓa tunanin zata jisu daga gwarzon maza irin Abdallah ba,kalaman da bata taba sanin cewa Abdallah zai iya fadawa wata mace su ba,lallai ta taki sa a ta zama mace mai sa a arayuwarta,da abun yayi mata yawa kawai sai ta yi masa wata irin runguma da ita kanta bata san taya tayi hakan ba ji take yi kamar ta maida shi cikin zuciyarta kowa ya huta,tana sonsa tana kishinsa tana kuma mararinsa,

Da ƙyar suka iya control ɗin kansu,ya tashi ya zare kayan shi,daukarta yayi cak sukayi toilet,wan Nan wanka kam ya ajiye wa rayuwarsu tarihi domin kuwa sun wanzar da wata irin ƙauna mai tsayawa azuci,tun Bintu na kunya da sunkui da kai har dai ta bada kai bori ya hau, Abdallah yayi mata cuɗin kauna itama haka ta dage ta murje masa jikinshi da tausasan tafikan hannun ta,daga nan suka ɗauro alwala suka fito,sallah suka fara gabatar wa sukayi karatu kamar yadda suka fara sabarwa kansu,


Tana ganin fitarshi tayi saurin tashi ta goga turaren da Inno ta bata na humra,kana Takoma kan gadon tayi luf tamkar mai bacci,A hankali ya ƙaraso bakin gadon yana magana cikin nutsuwa,yace"my ukty ba dai bacci kikayi ba?a hankali ta ɗan buɗe idanunta tayi masa alamun irin ta fara baccin nan,ya durƙuso kanta yana cewa tashi kici wani abu kinji ukty!'ɗan tura baki tayi hade da janyo hannun shi ta rungume a ƙirjinta,tana cewa Ni dai bacci zanyi ya Akiyy!'lumshe ldanunshi yayi saboda saukar da hannunshi yayi akan na shanunta, cikin san fita daga hayyaci yace"umm ummm ki tashi kici wani abu karki min musu kinji ukty,tashi tayi zaune amma bata sauka akan gadon ba,hakan da tayi ne yasa ya ɗauko plat din da ya shigo dashi ya hauro kan gadon yana cewa, kinga irin naman da kikeso ne zakiji dadinshi!'ba tace komai ba ta fara karbar wanda yake kaiwa bakinta,tana taunawa sai ta fito dashi akan harshenta tana tura masa,a hankali ya kai bakinsa kan harshen ta ita kuma sai ta tura masa naman da ta tauna,da wan Nan salon kaunar suka gama cin naman ya bata tatatacciyar madarar shanu tasha,daga nan suka sake yin brush,


Fitar da yayi ta sakanni kafin ya dawo har tayi bacci,a hankali ya hauro saman gadon kamar wanda yake tsoran tayar da ita,kashe fitilar dakin yayi kana ya kwanta ajikin ta,kanshi ya ɗora saman ƙirjinta,kana ya shiga yawo da hannunshi cikin jikinta,jin kamar anayi mata tafiyar tsutsa ne yasa ta ɗan buɗe idanunta kaɗan duk da dai dama baccin baiyi mata nisa ba,sai dai batayi motsin da zaisa ya gane idanun ta biyu ba,zame ƴar karamar rigar jikinta yayi tare da ɗora fuskarshi da hannunshi saman na shanunta, wanda hakan yasa ta motsawa ba tare da ta shirya ba,dama abinda yake buƙata kenan dan haka ya kai bakin shi kan na shanunta,wani irin zullo Bintu tayi tare da bankaro ƙirjinta tana wani irin shan yaji,kamar zata shiɗe,lokaci ɗaya Abdallah ya burkita mata lissafi da salon soyayyar sa mai tsayawa a rai,a hankali yake bin jikinta yana mata wani irin lasa yana tsotse duk inda yaci karo dashi ajikinta,cikin yanayin da ya gama saka ta aciki ta fara maida masa martanin salon da yake koyar da ita,wanda a take anan taso zautar da tunanin sa akan abinda shi ya koya mata, cikin nutsuwa ya nufi hanyar da yake ta ɗokin zuwa bayan ya gama rikita lissafin ta da ƙauna mara algus, wanda har bata san ya kai ga wajen da take ta kaffa kaffa dashi ba,runtse idanunta tayi yayin da taji Abdallah ya ratsata ratsin da baiyi mata shi a wan can ranar ba,kuka ta farayi a hankali tana son tureshi ɗaga jikinta,cikin wata irin murya can kasan maƙoshin sa yace"my ukty kiyi haƙuri ki barni daga yau bazaki kuma jin zafi ba,kar kiyi min shamaki da wannan jin daɗin da bazan sameshi a jikin kowa ba saike,karki hanani zuwa garin daɗin da nake mafarkin zuwa tun ranar dana fara ɗan ɗanashi,ya faɗa yana jan wata irin shaahsheƙa kamar wanda yake shirin shiɗewa, cikin rawar murya tace"na bari my Akey,na bari amma kar kabari naji zafi,kar kayi min da zafi,kar ka bari naji ciwo,kaji my hubby!'ta ƙarasa faɗa tana tallofo kanshi tare da shafa kyakykyawan sajenshi da yake matukar burgeta,haɗe bakinshi yayi da nata yana mai shigewa jikinta a hankali dan kar taji zafi,duk da cewa Bintu taji zafin sosai sai dai tayi matuƙar dauriya dan Abdallah yayi tattalinta ya kuma nuna mata tsantsar ƙauna wadda babu surki a cikinta,

Bai bari sun kwanta da najasa ba,sai da ya dauketa sukayi wanka tas, kana ya dawo suka koma bacci mai daɗi,wanda yake cike da mafarkai masu dadi da Alkhairi.


A ɓangaren su Sayyid da Taufiƙa ma an samu zaman lafiya, dan Taufiƙa da gaske ta saduda tayi nadama,hakanne yasa ta karɓi mijinta suka raya daren da soyayyar da basu san suna yiwa junansu ita ba,

Haka a bangaren Dady jafar ya samu Anty Samira yadda yake so matarsa ta kasance,dan haka sun fara ƙoƙarin shimfida kyakykyawar rayuwa me cike da amana da fahimtar juna.



💕ƘUDURAR ALLAH💕

NA

FATIMA Y ADAM

PG 64 AND 65

Momy Abigirl dai taga ishara dan daga yawan bara a can garinsu a ka markaɗe mata ƙafa,yanzu haka tana nan tana fama da ƙafa daya wadda aka rasa yadda za ayi ma a sai mata maganin da zai dinga rage mata raɗaɗi,to dai ga yadda karshen masu zalunci ya kasance.


Anty Nafisa ma dai ba acewa komai dan rayuwarta abar tausayi ta zama ga wanda bai san tsiyar da ta shuka ba,da ƙyar ta samu aka shawo kan mahaifinta yace ya hakura amma ba dan ya haƙora ta dawo masa gida ba,yace sai dai idan zata fidda miji yayiata aure amma bazatazauna masa a gida ba,dole uwar naƙi ta hakura ta kawo wani musakin bazawarinta da shi kaɗai ne me dan dama cikin zawarawan nata,matansa uku,ita ta zama ta hudu,gashi ba wani dukiya gareshi ba sai dai ɗan rufin asirin sawa ana bakin salati,haka nan ta haƙora ta zauna acikin ƙazaman matansa,idan ta zauna tana tuna baya sai tayi ta kuka,gashi nan akan kishiya guda ɗaya ta biyewa san zuciyarta har ta kasance yau itace da kishiyoyi uku,garin san dukiya ta biyewa shaidan yau itace a gidan da ko ƙofa mai kyau babu bare kuma a kai ga gyata gyatai,ai dama Nafisa duk wanda ya daka ta kaɗan sheɗan to tabbas zai kaishi ga ramin danasani,


Dady Mansur sunje sun fito da Dady Habib,sai dai kuma labari ana cikin wani hali na rashin lafiya da kuma haukan da ta soma ta azzara a gurinshi, Alhaji Baba kuka yayi da idanun shi saboda tausayin halin da Habib yake ciki haka sauran ƴan uwan shi babu wanda bai tausaya masa ba,ganin halin da yake ciki ne yasa sukayi tunanin kaishi gidan mahaukata dan abashi kulawa ta musamman, Sa dai kuma kash laifin shirka da haƙƙin ɗan adam su suka hana Dady Habib samun nutsuwa duk da cewa kulawa ake bashi sosai,amma a banza saboda akwai haƙƙin mutanen da bai nemi gafarar su ba,a kwana na biyu ne bayan uwar wahalar da ya sha duk yajiwa kanshi ciwo hatta da kunnen shi zubar jini yake saboda abubuwan da yake ji cikinsu,daga ƙarshe dai yace ga garinku nan, Allahu Akbar, tabbas duk wanda baiyi ƙoƙarin gyara rayuwarshi ba yana tare da yin mutuwar wulaƙanci ga dai yadda rayuwar Dady Habib ta kasance nan,duk abinda ya tara ya tafi ya barsu,kuma yaje ya tarar da ubangiji sai yayi bayanin yadda akayi ya tarasu,gashi kuma bai moresu ba,saboda tsoro da gudun tonuwar asirin sa,to Allah ya shiryi bayin sa waɗan da suke da rabon shiryuwa.

Da ƙyar da sidin gishi da lallami da naci da ƴaƴan Hajja su dasu inno da Hajiya Babba suka saka Alhaji Baba ya sauko daga kujerar nakin da ya hau,ya hakura ya dan sake da ita amma dai ƙimarta ta riga ta zube a idanunsa da kuma kishiyoyinta kai harma da ƴaƴan cikinta,ga dai abin da take gudu nan ya faru zubewa kuma da mutunci, Allah ya ganar damu gaskiya ya rabbil alamin,

Katsam kuma sai ga kira daga Alhaji Baba,ba kowa yakewa kiran ba sai Amare da angwayen jikokin sa da ya aurar,nan yake sanar dasu cewa bizar su ta fito na tafiya Saudiya,sunyi murna sosai kuma sunyi godiya,haka suka tattara suka fara shirin keta birnin Madina,


Tafe yake yana waya akan hanyar su ta dawowa daga ɓangaren Alhaji Baba,sai dai kuma hankalinshi na kan ƴar lelanshi ta gaban goshi wato Bintu, cikin tura baki tace"Allah Ni dai kam ka daina kallona sai kaje ka fadi!'dan murmushin gefan baki yayi kana ya kuma maƙale hannun ta cikin nashi,sauke wayar yayi daga kunnen shi yana cewa idan ina tare da ke banaso idanuna su dauke daga kallon baby face ɗin ki!'ya faɗa yana dage mata gira,rufe fuskar ta tayi tana dariyar ta mai kyau,wash ya Akey na gaji ka goyeni!'tsugunawa yayi a gabanta ita kuma ta haye gadon bayanshi tana ƙyalƙyala dariya,a Hankali yake takawa,sai da suka shiga katon falonsu wanda yake cike da kayan ado marasa yawa sai ƙamshi yake zabgawa saboda ya gamu da masu tsafta,sauketa yayi yana ɗan rike bayanshi,alamar dai ya gaji,zuwa tayi ta zagaya hannunta ta bayanshi tare da kwantar da kanta akan tsakiyar gadon bayan shi, tace"wai ka gaji ne my hubb? bani da nauyi fa!'juyowa yayi ta koma Cikin ƙirjinshi yayin da yasa hannunshi da jikinshi gaba ɗaya yayi mata mamaya, kana yace"wannan goyan fa sai an bani tukyicin sa!'ya faɗa yana yi mata raɗa cikin kunnenta,take ta shiga buga ƙafar ta aƙasa cikin sangarta da salon shagwaɓarta dake matuƙar burge Abdallah da sakashi cikin wani yanayi, take cewa Allah Ni dai naƙi wayon me yasa baka faɗa ba kafin ka goyani?ban fa warke ba jikina yana ciwo!' cikin nutsatstsiyar dariyarshi yace"haba my Bint wan Nan karon babu zafi sai daɗi!'ya faɗa yana kashe mata ido daya,kuma tura kanta tayi cikin ƙirjinshi saboda kunyar daya bata,ɗaukar ta yayi cak suka nufi bedroom ɗinsu dan raya sunnar Manzo s,w,a.

Yau dai jirgin su Abdallah da sauran ƙannenshi ya tashi tare da rakiyar iyayensu da abokan arziƙi,tunda suka je Madina babu abinda suke sai bautar ubangiji,a cikin kwana goma sha biyar da sukayi a garin na Manzo s.w.a ba ƙaramin nutsuwar zuciya suka samu ba,gashi su Bintu kansu ya haɗe kula suke da junan su basa so ko kusa da a taɓa daya daga cikin su saboda tsananin zumuncin da suka riƙe,ga mazajensu da suke tattalinsu da kaffa kaffa dasu,dukaninsu suna cikin farin ciki da walwala,daga nan kuma kowa ya nufi ƙasar da ya zaɓa A matsayin cin amarci,shi Abdallah dake yana da wani bincike akan wani criminal da ya gudo daga can naija,ya dawo nan kasar Siriya,dan haka kawai sai suka wuce can da niyar Bintu zatayi karatun wucin gadi anan kafin su koma,hakan kuwa ba ƙaramin farinciki ya saka Bintu ba, dan haka ta nunawa Abdallah sha awarta na koyon nau ikan girkuna, saboda ko ta koma naija abinda zata karanta ke nan,yayi na am da buƙatar ta dan haka sukayi ban kwana da ƴan uwansu kowa ya nufi inda yafi wayo,


Rayuwar Abdallah da Bintu, rayuwa ce da kai tsaye zamu kirata da rayuwar farinciki da fahimtar juna,komai yayi farko haka yana da ƙarshe,Bintu bata taɓa tunanin zata kai irin wannan matsayin ba a rayuwarta, to amma dake abun ƙudurace ta Allah sai gata a inda batayi zato ko tsammani ba,ta fara karatunta na catering cikin nasara,shima Abdallah a gefe ɗaya yana gudanar da aiyukan sa wanda yake saka ran San n nasara insha Allah...

Bayan wata biyar,sai ga ciki ya baiyana a jikin Ummi Laila,waiyo zakuso kuga farincikin ABBA Umar,abin dai ba a cewa komai, Allah ya nufa Laila da Umar ɗan su yafi ɗaya a duniya,sai kuma wani abin al'ajabin, ko da yake kaɗan daga ƙudurar Allah ke nan,sai ga Anty Samira ma da cikin Dady jafar, Allahu Akbar bayan cire rai da samun wannan kyauta tsawon shekaru sai gashi Allah ya nuna masa ikonsa da buwayarsa,lallai bawa kar ya taba cire tsammani da rahamar Ubangiji, A hankali kuma sai ciki yay ta ɓullowa jikin jikokin Alhaji Baba,su Taufiƙa su Farida Hauwa'u, Rahima, kai abun dai masha Allah sai fatan duk Allah ya sauke su lafiya.



Lokacin da Bintu taji labarin cikin da ummin ta take dashi sai da tayi kuka tayi suddar shukurr,sai kuma na ƴan uwanta wanda hakan yasa ta farinciki da kuma jin kwadayin samun ciki, ,fafy ne yake faɗa mata lokacin da suke waya,ya kuma sanar da ita an saka ranar usainar sa,daɗi kan daɗi ke nan,ganin tana ƙoƙarin fasa masa dodon kunne kawai sai ya kashe wayar yana dariya,wato dan bata san shima ya kusa zama Baba akaro na biyu bane, da ji zatayi kamar tayi tsuntsuwa, kawai ta taho naija, Abdallah yana dawowa da zan cen da ta fara tararshi ke nan,sai da ta gama faɗa mashi kuma wai sai ta saka masa kuka itama sai yayi mata ciki tunda su Taufiƙa ma suna dashi, bayan kuma ta riga su yin aure amma suka zo suka rigata,a kullum wautar Bintu mamaki da dariya take bashi amma kuma da yayi wani tunani sai yaga ai shi gaba ta kaishi,dan haka sai ya matseta cikin jikinshi yana cewa yi shuru my ukty ciki kike so ba?ta daga kanta kamar wata ƙaramar yarinya,yace"to maza share hawayenki insha Allah yau zan miki ciki,bazan ƙyaleki ba har sai na tabbatar da cewa na dasa ƙwaina a nan!'ya faɗa yana shafa kan mararta,dariya tayi cike da farin ciki tana da ɗa rungumo shi jikita tace"yauwa my zauji!'

Allah mai ƙudura da irada gagara iko gagara misali,sai ga shi maganar Abdallah ta tabbata dan kuwa tsakanin ranar da yau da ta zagayo wata ɗaya cif, Abdallah ya tabbatar da cewa ya dasa ɗan sa ko ƴarsa a marar Bintu,shuru yayi dan yana so sai ya tabbatar da hakan,yau tunda ta dawo daga makaranta take kwance ta kasa tashi ko da abinci taci,dan ma gurinta tsaf yake kamar babu halittar dake motsi acikin gidan,saboda tsananin tsaftarshi da ƙamshin da yake tashi,a gurin,a haka ya shigo ya same ta kamar ruwa,cikin sauri ya ɗauke ta yana dubata kamar wanda akace masa wani abu ya sameta,yace"my Bint meke damunki?langaɓar da kanta tayi akafadarshi tana cusa kanta a wuyanshi,ba tare da ta bashi amsar tambayara shi ba, tace"wayyo my zauji, inason wan nan ƙamshin naka dan Allah kabarni in kwana ina shakarshi!'ba tare da yace"mata komai ba ya ɗaga ta suka nufi bedroom kana yace"anya my zaujaty babu ajiyata acikin nan naki? bari dai na bin cike ki sai hankalina yafi kwanciya!"zaro manyan idanunta tayi tace"amma dai ba allura zaka mun ba ko? yace"haba my jewel ya kamata ace kin daina tsoran allura tunda kinga fa kin kusa girma!'bata gane abinda yake nufi ba dan haka sai tayi rau-rau kamar zatayi kuka,cikin sauri yace"nifa bance zanyi miki allura ba,duba ki kawai zanyi!'hakan da yafaɗa sai ta hakura yayi mata duk wani binciken da yakamata,bata ankara ba sai ji tayi yana juyi da ita a tsakar dakin tare da bin ko inan ta da wani zazzafan kiss,wanda har sai da ya ruɗa ya sauya mata yanayinta abinka da dama wadda take kusa saboda cikin da ke jikinta yana ɗan sata jin bukatar mijinta,ai kuwa dai biye masa tayi suka jika junansu da ƙauna mai tsayawa a zuciya da ruhi,bayan sun sami nutsuwa ne ya mamayeta da dukkan jikinsa yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, kana cikin so da kulawa yace"my ukty sai ki shirya dan kin kusa zama

Please Login or Register in order to submit comment