Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayiwa yarinyar wanka ta gasa mata cibiya,akabamu abinci mukaci muka koshi,cikin kankanin lokaci muka dawo haiyacinmu, sai da muka nutsu sannan na bawa baffa jauro labarin abinda ya koromu daga gida, ya jinjina al'amarin tare kuma da tunanin suwaye wadan nan mutanen?zuwan kansune ko kuma turosu akai?mun kasa tsayar da tunanin mu akan kowa dan haka muka tattara al'amuran muka barwa Allah.

Baffa jauro yace"amma yanzu ku dan dakata zuwa wani lokaci kafin ku koma!'nace"hakane baffa yanzu komawar mu gida bazai yuwu ba saboda bamusan masu neman rayuwar mu ba koda yaushe zasu iya kara farmakar rayukan mu!' ranar da kika cika kwana bakwai na rada miki sunan hajjonmu wato fadima amminki tana kiranki da hajjo ni kuma ina kiranki da bintu dan nace" bazan boye miki suna ba ko dan tunawa da mahaifiyarmu wadda bamusan halin da suke ciki ba haryau.

Bintu nida mahaifiyarki muka baki ilmi na boko da na addini ko wanda yake zuwa makaranta bazai nuna miki ilmi ba,saboda kina da basira da kwakwalwa me.saurin daukar abu duk wani littafi da ake koyawa amakaranta mun koya mikishi haka ta bangaren addini duk wani littafi da aka koya manashi saida muka koya miki kama daga hadisi fiqhu akbari sira umdatul ahkam bulugu zaduzzau jaini da dai sauransu kuma alhamdulillah baki bamu kunya ba.

Haka muka cigaba da rayuwa arugar baffa jauro bamu da wata matsala sai na tunanin gida da halin da su hajjo suke ciki, kina da shekara biyar muka fara shirin komawa gida sai dai kuma wani babban tashin hankalin ya kuma da katar damu,Laila ta gayamun tana wasu irin mafarkai mara dadi tana yawan mafarki da wasu mutane wadan da sam ita bata sansuba arayuwarta suna yawan zuwar mata awani irin suffa marakyan gani mun kasa gane inda mafarkin ya dosa,cikin wannan yanayin da amminki ta fada yau dadi gobe sai Allah baffa jauro baya zaune baya tsaye da nemar mata magani, ahaka muka kuma share wasu shekaru biyar din har me faruwa ta faru.


Tunda Allah yasa muka shiga rugar baffa jauro Allah ya dora masa kaunarki, bintu dan haka baffa jauro yayi miki gata ya tsaya tsayin daka ya kula dake ya dafaki da kayan tsari kullum ta Allah da irin kalar rubutun da zaiyi miki ko tofi wanka kuwa ba dai ayi miki shi da ruwa normal ba sai anzuba masa abubuwa na tsari sauka kuwa kinshata bansan iya adadi ba, bintu kedin kudurar Allah ce kuma da sannu zaki zamewa wasu takalmin kaya!' babu wani abu da zaiyi tasiri akanki ke din kin riga kin gagara, anyi miki kuma ankoyar dake shiyasa bana shakka akanki domin duk wanda yanemi kariya da taimakon Allah to tabbas ubangiji yana tare dashi.


Mafarkan da mamanki takeyi har nema suke su zautar da ita, dan har azahiri take ganin mutanen dasuke neman rayuwarta suna razanata, kalmar da suke yawan nanata mata shine, ta haifo abinda yake shirin rusa rayuwarsu sun kasa taba bintu ko inda take basa iya kalla, dan haka zasu dauke ta zasu rabata da ke so suke suyi maganin matsalarsu tun kan abin ya gagaresu, baffa jauro yayi iyayinsa amma dake kaddara tariga fata babu tsumi ba dabara dole abinda Allah ya nufa sai ya faru. kuma abincikensa yace"wadannan mutane ba jinnu bane sai dai kuma mushirukaine ma'ana manyan matsafane dasu kayi kaurin suna a har karsu ta shirka, haka muka dukufa da addu'a babu dare babu rana, sai dai kuma babu yadda zamuyi kaddarar amminki ahaka Allah ya shiryota.

Awata safiyar juma'a ne muka tashi da gagarumin tashin hankali dan mun nemi Laila sama ko kasa mun rasata,na shiga tsananin rudani da tashin hankali kuka ya gagareni sai hadiyar zuciya kema da bawani wayo ne dake sosai ba saida kika tashi hankalinki kullum sai kinyi mana kuka akan mukaiki gurin amminki alokacin shekarunki basu fi tara zuwa gama ba, har yau har gobe ban dena kukan rashin yar uwata tilo danake matukar kauna ba.

Sai da akayi shekara hudu da bacewar laila nima na fara fuskantar tawa matsalar,ni dakaina nayi tunanin mubar rugar baffa jauro, ko muna kusa dasune bamu sani ba, baffa shine yabani kudin da nazo na sai wannan dan gidan da muke zaune ya kuma bani kudi yace nayi wata yar sana ar kuma nasakaki amakaranta shi yabani shawara da muyi nisa da yola ko zamu samu nutsuwa, haka kuwa akayi baffa yasa nayi shigar da zan badda kama saboda samun akasi yakuma samo mana babur wanda zai kaimu har babbar tasha,munyi kuka sosai na rabuwa karma ke kiji labari dan har numfashin kine yake daukewa, dan alokacin shekarunki goma sha uku dan haka baki taba mantawa da baffa jauro ba kusan kullum sai kince na kaiki gurinsa da kyar nasamu kika daina yi min zancansa amma nasan badan kin manta dashi bane


Bauchi shine garin da muka kuma Allah yasa na hadu da mutum me amana me suna gali, shiya kaimu gidansa har yasamo mana wannan gidan ya kuma bani shawarar abinda zanyi da dan jarin da baffa jauro ya bani yace na siyo kayan gwari kamar su mango data goba duk dai abinda yake lokaci, haka kuwa akayi, lokacin gobane da data dan haka su nake sai dawa, na kuma sami makaranta mai kyau nasakaki lokacin kina da shekara goma sha uku kasan cewar mun riga munyi miki kyakykyawan paundation kai tsaye aka kaiki aji uku na secondary nan dinma kawai an barkine dan ilminki yafi karfin aji uku.

Ahaka muka dinga gungura rayuwar mu har kikayi candy wato ssce, ta bangarena wadannan mutanen suna ta bibiyata sai dai bantaba gaya miki ba saboda banasan damuwarki,
alokaci daya kuma rayuwar ta tsaya mana cak dan jarin da nake tattalawa ya kare sai yawan rashin lafiya da nake Wanda duk baya rasa nasaba da irin ukubar da nakesha agun wadan can azzaluman kuma Nima sun sha alwashin sai sun rabani dake tunda na zame Miki katanga bayan su so suke su ga rayuwarki ta lalace shi yasa duk wanda take baki kariya sai sun ga bayansa dansu abatan basirarsu da duhun kansu indai babu wani garkuwa atare dake to hakkun zasu ci galaba akanki anasu karatun kenan anamu kuma basu san cewa Allah shine garkuwar bawansa kuma majibancin al'amuran sa lokacin da nake ta tunanin zuwansa bintu Ina ganin yakusa zuwa na dade da rubuta wannan sakon naki bintu dan nasan watakil alokacin da nakeso na sanar miki hakan bazai samu ba.

Abu na biyu shine bintu Ina yawan sanar dake akwai wanda zai zamar miki jagora to tabbas naji ajikina zaku hadu kince na sanar miki waye? akuma ina yake? to ni kam duk bansan wannan ba!' hasali ma bantaba ganin fuskarsa ba andai nuna min shi amafarki na kuma inasa ran haduwarku insha Allah danshima yana bukatarki dan hada karfi da karfe ku tai maki junanku!'

Abu na uku shine inda zaki nufa, to daga nan, ki wuce abuja duk yanda zaki ki samu koda aikine a estate din Alhji balarabe, Ina da tabbacin cewa duk wani abu yana cikin gidan nasan da wannan ki nutsu bintu karki sake ki nunawa wani ke din ahlin gidance, duk yanda zaki shaku da mutum karki yarda ki bashi yaddarki duk wanda kika gani ko shiga gidan yayi saka masa ido harsai kintabbatar da gaskiyarsa sannan ki barshi kuma kiyi hakuri da duk abinda zaki gani kibi ko mai asannu harki tadda gaci,akwai rudadden al'amari awannan ahlin dan haka kiyi taka tsantsan dan sai kin nutsu kinbi hanyo masu bullewa kafin ki fahimci komai mutanen gidan suna da ruda mutum, kuma ina da tabbacin mafarautanmu suna hade da alhlin gidannan.

Bintu tana kawowa karshen bayanin fafi ta saki wata sassanyar ajiyar zuciya,tare da wani kuka me cike da shauki bege da kuma kewa data mamayeta, wani irin kewar fafi da mamanta ne suka hadu suka da baibaye zuciya da ruhinta, tanaji dolene ta shiga koma inane dan nemo fafinta da mamanta, kowane hadarine zata iya fuskantar sa indai akan wadannan mutanen guda biyune, ashe fafi bashi ya haifeta ba amma ya sadaukar da rayuwarsa ya bar iyalansa da mahaifiyarsa da dukiyarsa da abokansa yan'uwansa da komai nasa, kawai dan ya tserar da rayuwarsu ita da mamanta, shiko fafi wane irin mutumne haka da irin wannan babbar sadaukarwa?me zatayi arayuwarta dan saka masa da dinbin alkhairin da yaiwa rayuwarta? wani shashen na zuciyarta yace"fatima baki da abinda zaki iya sakawa fafi dashi arayuwarki sai dai ki bishi da addu'a da kuma binciko inda aka kaisu aka boyesu, da kuma rusa magautanku kamar yadda ya gaya miki, hannu tasa tashare hawayen da suka ki daina zuba daga cikin idanunta, kana ahankali ta bude wani page, dan taga kamar da wani sauran rubutu, aiko hasashenta ya zama gaskiya, ga abinda yace mata, bintu ki duba cikin kayana zaki ga kudi dubu biyarne na dade ina tarasu domin irin wannan ranar ki dauka kiyi kudin mota duk da nasan da.wuya zai isheki Amma dai nasan zai kaiki Abuja kuma kisamu ki danci abinci, Allah yabaki sa'a ya kuma kareki daga duk wani sharri ya kuma hadaki da mai taimakonki cikin sauki, Allah ya yiwa rayuwar ki albarka.

Fatima ta kuma rushewa da wani rikitaccen kuka mai taba zuciya,duk wanda yaga halin da bintu take ciki awannan lokacin indai yana da imani da tausaiyi dole ya zubda mata da hawaye,tayi kuka tayi kuka har ta gaji sai wani irin masifaffan ciwo da kanta keyi mata tamkar zai tsage gida biyu,ahaka ta hakura ta lallashi kanta da mika dukkan lamuranta ga sarki Allah buwayi mai iko da komai,tare da fara kokarin shirin fuskantar gagarumin yakin dake gabanta.


......Abuja......

Kwanaki uku yayi cir yana istihara dan neman zabin Allah akan akan yakin da yake kokarin fuskanta,kuma alhdulillah yaji hankalinsa ya kwanta tare da samun kwarin gwiwa na shiga cikin ahlin Alhaji balarabe.

Acikon kwana ukunne yagama shirinsa tsaf dan komawa estate din, dama dady ya kaimasa duk kayansa da kuma duk wani abu nasa mai muhimmanci tun kafin yau din tazo,dan haka yana tashi daga aiki ya nufi gida dan yiwa mom sallamar da taci albarkacin dady, da farko baiyi niyar yi mata sallamar ba, amma da yayi wani tunani saiya ga bai kyautatawa dady ba amatsayinsa na wanda yake ta kokarin dai-dai ta rayuwarshi da tarin kyautatawa da neman mafitawa rayuwarshi.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 10 ```




Koda ya shiga falon mom din zama kawai yayi batare da ya iya cewa da ita komaiba,sam shi baisaba da yin magana anyhow ba, shiyasa take matukar yi masa wahala har ga Allah sautari rasa abin cewane yake hanashi magana, kamar misali dady awasu lokutan yanaso yayi mishi magana kodan nuna masa irin jin dadin da yake shiga duk lokacin da yaga yana kokarin kawar da damuwar dake dankare azuciyarsa, sai dai kuma yana rasa tayaya zai iya hakan.


Zuba masa ido tayi tana mamakin hali irin nasa, wai ace mutum da ransa da lafiyar sa amma sai yay awa biyu cur batare da ya bude baki yay magana ba, idan ma zaiyi bata wuce kalma biyu zuwa uku anya kuwa fatash zai iya rayuwa da mace?shin wace irin macece zata iya zama da fatash da wadannan halaye nasa?to shi tayaya ma zai iya wata soyayya?ita tana ganin ma bazai taba yin aure arayuwarsa ba tunda babu wanda ya ke shakka ko tsoro da zai tursasashi yayi auren, sai dai yay tazama ahaka tunda ya riga ya auri aiki, mom ita kadai da zuciyarta take mitar nan tare da cin alwashin bazata tanka masaba ko zasu kwana ahaka har sai taga iya gudun ruwansa.

Banza tabawa ajiyarsa kamar yadda ta kudurta aranta,sai dai kuma abun neman fin karfinta yake, dan bata ga alamun yana da niyar tanka mataba, saima kokari yake ya bar falon saboda yasan dady ayanzu shi yake jira, saurin dakatar dashi tayi da cewa"haba fatash sai kace wadanda suke zaman gaba me yay zafi haka!' kake tsaurara tsanarka agareni?kai kana ganin ya kamata ka tafi wani guri zama na tsawon wani lokaci batare da munyi sallama wa juna ba?ya kamata ka sassauta min nasan ni mai tarin kuskurece agareka amma ai na nemi yafiyarka kuma kace kaimun afuwa!' to meye kuma acikin ranka game dani haka fatash?
ta fada tana mai sakin wani dan marayan kuka gwanin tausayi.

Ahankali ya koma ya zauna yana mai hada hannayensa biyu tare da lan kwasasu cikin kwarewa da sabo, suka bada wani sauti kakasss!' kana ya dubeta cikin dauriya yace" mom sorry and please forgive me, ni zan wuce Allah kaddara saduwarmu!'daga haka bai iya kara koda harafi daya ba yasa kai ya fice batare ya waigo ba.

Sake da baki da Ido ta bishi, to meye amfanin neman yafiyarta ta?batare da ya saurari abinda zatace ba yai ficewarsa, ga tarin tambayoyin da tayi masa duk ya hada ya share tamkar ma batayi masa suba, ita dai tanaso taga ranar da za aiwa fatash tambaya ya amsa kai tsaye,wani lokacin idan kanasan amsar tambayarka agunshi sai dai kakula da aiyukanshi' a kanka ta nan ne kawai zaka gane amsarka amma ga wanda yasan hali.


Acikin mota ya sami dady shi kadai, dan basa bukatar driver awannan gabar,yana shiga dady ya tayar da motar yaja me gadi ya wangale musu wawakekiyar kofar get din suka fita.

Bayan shiru na dan wasu mintoci da fara tafiyarsu dady ya dan numfasa kana yace" abdallah ina mai baka shawara da kayi hakuri da duk abinda zaka gani ko katarar acikin gidan nan kasan shi gidane na jama'a da hada-hadarsu dan haka dole kajure hayaniya domin samun nasara akan kyakykyawan kudurinmu, anbaka bangare guda asashen kakarku hajiya zainab (inno) saboda itace babu kowa agabanta amma duk da haka kusan rabin yan mata da samarin gidan anan suke tarewa domin kamar nanne majalisarsu baccine kawai ke maidasu sashensu, to ni dai bansan meyasa aka baka masauki abangarenta ba,amma ni hakan yayi mun kasancewar kowa da kowa yana shiga bangarenta ma ana kowa nata ne tana kuma mu'amala da dukkan surukan gidan, kaga kenan a hasashena hakan wata babbar damace agareka da zaka samu kusanci da kowa na gidan zaka kuma kula da takun kowa, nasan kai mai basirane abdallah da kuma dogon hange bana jin ko dar akanka nasan insha Allah kaine da nasara akan makiyanku dan haka ka kula da ta kun kowa ko kallo mutum yayi agidan nan da ma'anarsa,ina maka fatan alkhari da nasara akan dukkanin rayuwar ka,san nan kayi min magana akan cewa kar gane wani abu akanka saboda kamannin ka da gidan da kuma mahaifinka, to wannan bako mai bane dan dukkanin su kansu ajuye yake anriga anmantar da dasu, sum manta wanene abubakar da wani gudan jininsa dan haka babu wanda zai ganeka sai wanda yay abun da kuma magoya bayansa dan haka inaso kasa ido sosai dan nasan su zasu iya ganoka amma bazasu taba nuna wata alama ba, suna da shiri akanka abdallah ka kiye!'

Adai-dai lokacin kuma suka karaso dan kareran get din da zai shiga da kai cikin ainahin estate din manyan masu gadi sojoji kusan biyarne akofar, kasancewar babu wanda baisan dady jafar ba yasa suka barsu suka shige kai tsaye zuwa get na biyu wanda daga shine kuma zakai ta ganin get-get na bangare bangare, batare da wani dogon bincikeba kai tsaye akabarsu suka shige bangaren Alhaji baba.

Alokaci daya abdallah yaji kansa yay wani irin mummunan sarawa da karfi tamkar ana buga masa guduma har sai da ya kai hannunsa ya dafe goshinsa, fahimtar hakanda dady yayi take yashiga karanto masa addu'a shima ahankali yake karanta innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un tare da allahumma ajirni fil musibati wa'aklifini khairan minha da la'ilaha'illa'anta subhanaka inni kuntu minazzalumin.kana ahankali sukayi sallama adai-dai lokacin da kofar ta zuge suka saka kai, yayin da sukaji wata kamilalliyar murya tana amsa musu,

Guri suka samu gaba dayansu akasa suka zube, saboda tsananin girmamawa ga tsohon dattijo mai tsananin mutumci da kamala.


Bayan sun gama gaisawa da dady ne, abdallah ya karayin kasa da kanshi kana ya gaishe da Alhaji baba, amsawa yayi cikin farin ciki da wani irin shauki na kauna da bege da lokaci daya ta saukarwa Alhaji baba.

Hannu ya mikawa abdallah yana cewa"zomana jikana abin alfaharina matso kaji dumin jikin kakanka!'abdallah bai kasance ragon namiji mai raunin zuciyaba amma ayau akuma gaban dattidon nan jiyake tamkar zai zubda hawayen tsananin tausayinsa da kuma kewarsa tare da zunzurutun kaunarsa hakanan yaji yana fargabar ranar da zai san cewa ya haifi bara gurbi acikin yayansa ya kuma hada iri da gubatacciyar zuria yana tsoron kar saboda bakin ciki ya hadiyi zuciya arasashi kowa ya huta.


Jin maganar Alhaji babane ya katseshi daga
dogon tunanin da ya fada yace" abdallah jikana kasaki jikinka kadauka cewa kana cikin gidanku kuma cikin ahlinkane, duk abinda zakayi kayishi kai tsaye amatsayinka na dan gidannan na kuma baka umarni duk wanda yay ba dai-dai ba acikin kannenka ka hukuntashi amatsayinka na babban yaya tunda yanzu babu wani babba saurayi da yay saura agaban mu duk suna da iyali!'ya karasa fada yana mai shafa kan abdallah.

Abdallah jinjina kai kawai yayi tare da kwantar da kanshi akafadar kakan nasa yana mai jin wata yar sangarta na shigarsa nakasan cewarsa tare da kakan nasa.


Cikin lokaci kankani babban holl dinsu da suke taruwa dan taro muhimmi ya cika makil, saboda sanarwar Alhaji baba na cewar duk wanda yake nan kusa har yan kaduna yana bukatar ganinsu cikin gaggawa,wadanda sukai nisa kamar na kano ko wata kasa haka akayi connecting dan suma su sami damar jin abinda ya hada taron.


Kowa ya nutsu yana sauraron bayanin Alhaji baba ta macrophon,kowa ya gamsu da abinda yasanar dasu har wasu suna cewa ai da ko awaya yasar musu ma ya wadatar.

Alhaji baba yayi gyaran murya kana yace"dalilina na cewa lallai sai kowa yazo shine inaso ku dauki abun da muhimmanci kuma kowa yasan cewa abdallah shima jika naneeee
(Waiyo ni fadima sauri nayi na zubawa mutanen dake dankare a holl din Ido ko zan samu nasarar riga su abdallah gano bara gurbin cikin zuriar Alhaji balarabe sai dai kash babu wanda ya nuna wani abu afuskarsa da zai sa na diga masa ayar tambaya,kai wadannan mutane ko suwaye akwai shu'umai)

Abdallah ya zubawa fuskoki da yawa ido ko shima zai fahimci wani sauyi daga wata fuska saboda jin furucin Alhaji baba, sai dai shi din ma babu abinda ya fuskanta.

Ahlin Alhaji balarabe sun karbi abdallah da hannu bibiyu, anan ya dinga ganin wata kauna akan fuskokinsu kansa ya daure matuka dan yakasa fuskantar gaskiyar kauna da akasinta, duk abu daya yake gani dauke a fuskokinsu, dady ane, ma da dady jafar yasan bai gamsu da zuwan abdallah ba, bai fahimci komai afuskarsa ba.


Ahaka taron ya watse kowa na kokarin ganin ya nunawa abdallah shi mai kaunarsa ne baka da zuci, Alhaji baba da kansa ya rakashi har bangaren inno ya sadashi da hadadden dakinsa kana yace" yayi wanka ga abinci nan ya dade da rigashi zuwa sannan ya kwanta ya huta.

Godiya abdallah yayi wa Alhaji baba,shi kuma ya juya ya fita yana mai tunasar dashi karya sake yi mai godiya. wadawa yayi bisa lumtsumeman gadon da yasamu wata iriyar shimfida ta alfarma da wani hadadden bedsheet,kansane yaji yana neman barewa gida biyu saboda yawan hayaniyar da yashaka yau shi tunda yake bai taba shiga hayaniya irin wannan ba dole dady yay ta bashi hakuri da tausarsa akan ya jure ashe yasan komai akan yawan hayaniyar gidan anya kuwa zai jura?

Tashi yay yana layi ya nufi bayi jikinsa duk babu kwari hutu kawai yake bukata yanzu dan wannan hayaniyar tasa duk san aikinsa yaji ba zai iya fita aiki gobe ba.


Tunda aka sauke ta atashar bulayi kawai take acikinta batasan ko Ina ba batasan kowa ba, batasan inda zata nufa ba, can kusa da wata mai abinci ta samu ta rabe sai baza manyan idanunta take taga ta inda Allah zai kawo mai agazamata, da dai taga zaman take ga yunwa na nukurkusarta kawai sai taciro naira dari biyu ta kara matsawa kusa da mai abincin tare da yi mata sallama!' alokaci daya kuma tana mika mata gudar dari biyu tace"abani abinci!matar mai abinci ta bi bintu da wani irin kallon yau naga India mai jin hausa,girgiza kanta matar tayi tana mai cewa' yi hakuri 'yan mata bamu da irin abincin ku anan sai dai kije restaurant' a canne suke yin kowane irin abinci!'ta karasa maganar da juyawa tana kallon mutanen da suka taru arumfar abincin nata, kallon bintu suke cike da farinciki yayin da wasu suke musun cewa ai amisha ce wasu kuwa suce ai pretty ce,

Bintu ta rasa inda zatasa kanta kawai sai tafashe da kuka!' saboda ita bata saba shiga cikin jama'a ba, balle wadannan da suke tai mata surutu aka, ganin haka yasa wani babban dan union ya sa wasu samari suka kori mutanen,

Matar nan mai abinci ta dubi bintu tace" yan mata Ina zakijene na ga kamar kin dade acikin tashar nan ko kin manta hanyane?da sauri bintu ta daga kanta!' matar tace"ayya to bari nasa yarinyata ta nuna miki hanya,juyawa tayi ta kalli budurwar dake tsaye agefanta tana saurarensu, tace" basira maza jeki ki nuna mata hanya ki saka ta a keke napep, ta fada masa sunan anguwar da zai kaita dan naga alama bakuwace batasan ko'inaba!'ta mikawa basira wata leda tana cewa" ga wannan sai ki bata idan zata iya cin abincin mu!'bintu cikin shagwababbiyar muryarta da ta riga ta sangarce agun baffa da fafi tace"na gode mama Allah ya saka miki da alkhari!' mai abinci cikin jin dadi tace"babu damuwa ki gaida gida Allah ya kiyaye!'ta amsa da amin tare da jin dadin karamcin da mama mai abinci tayi mata.


Tun kan ma su fita daga cikin tashar suka samu mai napep,basira ta dubi bintu tace" wace anguwa za'akaiki? bintu shiru tayi tana son ta tuna sunan anguwar da fafi ya gaya mata amma ikon Allah shaf ta manta,mai keke yace"Ina gafa wannan hausarce tayi mata nauyi bari na lissafo mata sunan anguwanni ko zataji ta fada!'kafun ma basira ta tanka masa ya shiga lissafo manyan anguwannin masu kudi da fada aji, bintu tanajinsa har yanzu bai fadi makamanciyar sunan anguwar da zataje ba .gajiyar da tayine yasa yana cewa'mai tama sule tace"muje nan zani!'me napep yace au wai dama kinajin hausa kan uba alkur an ban zaci ta'iya hausaba kudurar Allah kenan!'basira tace da Allah mazarkwaila sarkin zaki wuce kuje ka kaita ka'ishi mutane da surutu kamar ba gobe!'dariya yayi kawai dan yasan gaskiya ta fada, mikawa bintu ledar take away tayi gami dayiwa junansu sallama,mai napep yaja suka wuce.



Hajiya anzo mai tama a'ina zaki sauka?ahankali bintu take bin anguwar da kallo,tare da manya-nanyan gidajen da sukayi mata kawanya,tunani take idan ta sauka to Ina zata nufa?wa tasani acikin wannan haddadiyar anguwa ?amma abin da tasanine dole ta sauka tunda itane ta zabi akawota nan din, dan haka tace da mai napep ya sauketa,burki yaja akofar wani haddaden gida yana mai cewa" hajiya kudinki naira dari uku!' batare da tace"komai ba ta mika masa dari biyun dazu da mai abinci bata karba ba,yana amsa ya figi napep dinsa ya kara gaba.



Tsuru tayi agefan gidan da ya ajiyeta tare da zabga uban tagumi,ji tayi cikinta yana wani kuuu sai alokacin ta tuna da yunwar dake dankare acikinta, gabas ta kalla kudu da arewa bata ga kowa ba dan haka a nutse ta juya baya taci abincinta, duk da bata wani ci mai yawaba cikinta ya riga ya cushe.zama ta cigaba dayi awajen ga tsoro da ya cika ta, fanfo ta hango daga dan nesa da ita da sauri ta karasa gun ta bude fanfon aiko ruwa ya zubo shaaa, cikin azama ta kafa kai tasha tayi nak, kana ta daura alwala ta dawo inda take, ta shimfida dan kwalin kanta tayi sallolin da ake binta kana ta dora da na filfilu, tana nan dai azaune har aka kira sallar magriba sai alokacin ta fara ganin mutane suna fitowa masallaci, wasu kuma sun dawo daga aiki, sai kuma taji hankalinta ya

Please Login or Register in order to submit comment