Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta,wata irin zufa ce take karyo masa ta ko ina,yayin da zuciyar sa babu abinda take sai bugu, wanda kuma tsabar fargaba ce tasa hakan,da ƙyar ya tattara miyan da ya daskare cikin bakin sa ya haɗiye shi tare da cewa,shugaba zamu gwada wannan ɗin amma daga baya zan iya haɗawa da yaudara!'wata shegiyar dariya shugaba ya sheƙe da ita har da riƙe ciki kana ya ɗan saurara tare da cewa shegen kaya nanu ai dama in dai yaudara ce ka iya ta,tunda ka yaudari mahaifinka waye bazaka iya yaudara ba,amma dai yanzu na gamsu da wannan tsarin tunda naga yanayi,abinda ka faɗa ɗin shi za'ayi amma kasan wannan yarinyar baza mu hada ta da tsafi ba tunda tun farko dama ta gagaremu ballan tana kuma yanzu!'sai yanzu nanu yaji dan dama tunda shugaba ya bashi dama da kuma goyan baya.


Sun ɗanyi nisa da fara tafiyar ya dube ta cikin dawowa yanayin sa na kullum yace"bani nombar inno a wayar ki mu kirata dan kar hankalin ta ya tashi!'miƙa masa tayi bayan ta duba sunan innon,ɗauka yayi awayar dake hannun sa ya kirata,ringin ɗin farko kuwa ta ɗaga,lokacin suna tare da Dady Habib,a hankali Abdallah yace"inno Barka da safiya!'cikin sauri inno ta amsa tana ɗorawa da cewa wai Abdallah ina kuka shiga kaida Bintu yau tun safe nake cikiyarku a cikin gidan nan?inno karki damu wani aikine ya taso mun cikin dare kuma tace bazata iya zama ba tana jin tsoro shine na tafi da ita!'jinjina kai inno tayi tana mamakin wai Abdallah ne da jero wannan dogon zan can duk saboda Bintu,cikin kulawa tace"aiyo ai hakan yayi kai da matar ka Allah dai ya baku nasara,saikun dawo,daga wannan sukayi sallama,juyowa tayi tana kallon Dady Habib da yayi shuru yana sauraren ta,tace"dama ai duk wanda ya samu mace kamar Bintu tabbas sai rayuwar sa ta canja tare da godewa Allah!'Dady Habib yayi murmushi tare da cewa jikokin naki ne?dariya tayi cikin farin ciki tace"sune kaga har sun hada kan su tamkar ba haɗa su akayi ba shi yasa nake cewa ita ma Taufiƙa zata haƙura duk ranar da taga bata da kowa A gefanta sai Sayyid, Allah dai ya baiyana mana shi cikin ƙoshin Lafiya!'da sauri Dady Habib ya amsa da Amin kana yace"to kuma ai baki tmbayesu inda sukaje ba!'inno tace rabu dasu mata da miji ne,kasan dai miji ba zai sace matar sa ba ko? murmushi kawai yayi b tare da yace"komai ba.


A ɓangaren Anty Nafisa kuwa tuni ta bada aikin gamawa da Abba Umar amma tace aɗan saurara zata faɗa musu ranar da take so aikin ya kasance,ba dan komai ne yasa ta jinkirta ba sai dan tana son ta fara bibiyar sa dan ta tabbatar da ko su Laila suna raye suma ta aikasu tare gaba ɗaya, ko hankalinta ya gama kwanciya tasa mu tayi rayuwar ta cikin farin ciki ba tare da fargaba ba,wan nan shine tunanin Nafisa,

A can kuma ɓangaren su Abdallah lokacin da suka gama waya da inno kallon Bintu yayi cikin haɗe gira dan karma ta kawo masa wasa cikin tambayar da yake son yi mata,ganin haka kuwa yasa ta nutsu tare da maida kanta daya ɓangaren,kamar daga sama taji maganarsa yana cewa Bint ke dawa kuke magana a cikin ɗakin nan kuma waya sanar miki da cewa Dady yana cikin dakin?kuma me yasa baki gayan ba tun asali kafin faruwar Al'amarin?cikin san tabbatar masa da gaskiyar abinda zata faɗa tace"wallahi ban santa ba kuma nima da farko ban sani ba saida ta sanar dani kuma yau baifi kwana uku da fara mafarkin da ita ba,tun ranar dai da mukaje wajen Malam ta fara zuwa kuma ita tace kar na gaya maka har sai mun shiga ɗakin munfito,kuma ita take min magana acikin ɗakin,Rimi Rimi ta faɗa masa maganganun da sukayi acikin ɗakin,cikin sheshsheƙar kukan da yake cinta tace"amma bata gayamin inda ummi na da fafina suke ba,inaso bagan su,amma bata gaya min ba,hannun sa har rawa yake gurin ƙoƙarin janyo Bintu jikin shi,ƙara shigewa tayi tana goga fukarta akan ƙirjin sa kamar yadda ta saba,rufe idanun sa yayi yana jin wani irin matsanancin tausayin bintu tare da wani abu mai girma da yake ratsa duk wata zuciya da gangar jikin shi,yana mamaye duk wata kafa mai muhimmanci dake cikin rukunin numfashin sa,hannu yasa ya ture ɗan mayafin dake kanta ya shiga shafa lallausar sumar kanta mai matukar santsi da ƙamshi,rufe idanun ta tayi wanda take anan bacci yayi awan gaba da ita,cikin mintunan da basu fi biyu da yin baccin Bintu ba suka ƙara so ƙofar gidan Hajjo.


Hajjah ta zubawa Habib ido dan san gano halin da yake ciki, amma hakan ya gagara,cikin ƙaunar ɗan nata da ya zamar mata ɗaya tamkar da dubu tace"Habibu mai yake damunka ne naga duk kayi wani sukuku da kai kamar bakajin dadi,ɗan murmushi yayi tare da cewa Hajjah kin san dai yanzu bani da wani abu wanda yake saka Ni damuwa face maganar Mansur shi kaɗai ne damuwa ta,ina jin abin har cikin raina, wannan halin nasa ina fata ALLAH ya canja masa shi.


Alhaji Baba ya kalli Alhaji Hashir cikin tsananin damuwar da ta taso masa a cikin wannan rana da tunawa da haziƙin ɗansa,wanda ya manta dashi tun bayan da akarasa shi, duk da cewa damuwar rasa shin yana tare da zukatan su,amma babu damar furtawa da baka,sai yau da yaji tamkar antashe shi daga bacci,ya tashi da azabar kewa da raɗaɗin rashin Abubakar ji yake tamkar yanzu aka neme shi aka rasa,so da yawa yakan kwana ya tashi da jin zafin abin amma ya rasa ta yaya akai ya kasa koda fita waje dan neman inda ɗan nasa ya shiga,abinda matuƙar mamaki ga kuma jikan sa da ya ɗauki soyayya ya ɗora masa shima ya rasa shi bayan rasa mahaifin sa,yanzu abin ne yake dawo masa tare da kaicon abin da ya hana shi yunƙurin neman ɗan sa da jikan sa,ɓatan Sayyid shi ya kuma saka zuciyar sa cikin wasu wasi da saka ayar tambaya akan lamarin gidan nasa,me yasa ake ɗauke masa zuriya?taɓa shi ɗan uwan sa Alhaji Hashir yayi tare da cewa ya dai Balarabe ka kiramu dan yin magana mai muhimmanci amma ka barmu kasa mana ido kai kuma ka tafi duniyar nazari,shin meke faruwa duk da nasan maganar bazata wuce akan ɗakin nan da aka tashi da gobarar sa ba!'ya faɗa yana duban dan uwan sa Alhaji Sa'ad da shima ya zubawa Alhaji Baba Ido dan son jin maƙasudin kiran da yasa akayi musu,Dady Mansur da Dady Habib da Abba Umar sai Baba nura da Ahmad da dai sauran ƴaƴan sa da ƴaƴan ƴan uwansa da suke tare aguri ɗaya cikin estate,yayin da kowa da abinda yake son ji daga bakin Alhaji Baba,wadan da suka san sirrin dimon suna fata ace abin da zai sanar dasu ke nan,wasu kuma saɓanin haka ne aran su.


Hajjah ce tace"ya kamata ku bar Alhaji ya nutsu tunda ya kiramu kun san zaiyi magana mai muhimmanci ne,kuma duk lokacin da mutum zai furta wata magana anaso ya tattaro tunanin sa da nutsuwa da kuma nazari akan abinda zai furta,saboda tuntuɓen harshe,dan haka Dan Allah karku rikitashi!'wani mugun kallo Baffa Hashir ya wurga mata tare da cewa to ƴar iya,dama nasan ko kowa baiyi magana ba ke saikin yi!'murmushi Hajjah tayi dan tasan dama can kanwarsu bata juƙuwa da Baffa Hashir,


Gyaran muryar da Alhaji Baba yayi ita ta sakawa kowa nutsuwa,tare da maida duk hankulan su kansa,cikin nutsuwar da bata hana damuwar sa baiyana ba,yace"duk hasashen ku bai zama daidai ba,domin nasan abinda zan fada muku bashi kuke tunanin zan faɗa ba,saboda nima yau tunanin ya fito daga zuciya ta zuwa kan harshena,ɗan shuru yayi,yayin da zuciyoyi suka ƙagauta da jin wannan batu,duk iya tunanin su akan dimon ne saboda su waɗan da suke abun sun san cewa Alhaji Baba bai san maganar dimon ɗin ta fita ba,balle yasan muguwar rigima da cutar data haifar a cikin zuri'arsa,Alhaji Baba yaci gaba da cewa,shi yasa zan sanar daku dan mu haɗu muyiwa kanmu da zuriar mu maganin abinda yake damunta,dan fitar da iska yayi ta bakin sa tare da sauke numfashin damuwar dake cunkushe a zuciyar sa,kana yaci gaba da cewa maganar Abubakar ce,,,wata irin zabura Dady Mansur yayi yayin da sauran mutanen ɗakin sukayi ɗif kamar babu wata halitta a falon,kowa da irin bugun da zuciyar sa keyi masa, Hajjah kuwa wasu hawaye ne suka sauko mata tana cewa Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah wanda yayi zuciya,kawai sai ta fashe da kukan farinciki nanatawa take Allah kasa lokacine yayi da gaskiya zata bayyana!'kowa ka kalla afalon nan da akwai abinda ke damun sa na matukar ruɗani da firgicin jin maganar Abubakar ta taso lokaci ɗaya, Dady Mansur kuwa kuka ya saka sosai wanda kana ji kasan kukane da yake fita tun daga ƙarƙashin zuciyar sa,ya kasa cewa komai sai sautin kukan sa dake fita gwanin tausayi,Dady Habib ne ya ɗan goge fuskarsa kana cikin nutsuwa yace"haba yaya bai kamata ba da girman ka kadinga abin yara!'wani Irin mahaukacin kallo me cike da fassarori da ma'anoni masu yawa Dady Mansur ya jefawa ɗan uwan nasa,ba tare kuma da ya iya ce masa komai ba,karon farko ke nan da yayiwa Mansur irin haka batare da ya tanka masa ba,ɗauke kansa yayi cike da mamakin wannan kallon da Mansur yake masa,ko me yake nufi da haka?


Alhaji Baba yayi wani ɗan murmushi na takaici kana ya cigaba da cewa,a yau kuma a yanzu nasa afara rokon ALLAH ba dare ba rana idan Abubakar yana lafiya Allah ya baiyana mana shi idan baya cikin haicinsa kuma Allah ya bashi lafiya ya dawo min dashi cikin gidan nan,idan kuma ya mutu,,,,,kukan Hajiya Babba ne ya dakatar da shi daga barin abinda zai faɗa,cikin kuka da matsanancin tashin hankali tace"dan Allah Alhaji karka ƙarasa,inason ganin jagora araye (dake sunan da take gaya masa mafi lokata acikin mutane saboda karar ɗan fari)taci gaba da cewa Wallahi inaso yazo gidan nan araye inaso naga waɗanda suka gurgunta min rayuwar sa akan abin ɗun,,,,bata ƙarasa ba inno ta rufe mata baki tare da girgiza mata kai,alamun kar ta faɗi abinda ke cikin zuciyar ta,tunda shi Alhaji Baba baƙo ne akan sanin hakan,zai iya zurfafa bincike akan al'amarin,shurun kuwa tayi bata sake cewa komai ba,sai dai kukan da taci gaba dayi ƙasa ƙasa,yayin da Hajjah ta zuba musu idanun ayar tambaya da wannan sabon Al'amarin, wai meke shirin faruwa a gidan nan ne haka? Alhaji Baba yace"dama abinda nake son sanar daku kenan kowa zai iya tafiya!'daga haka ya miƙe ya shige can cikin ƙuryar ɗakin sa,jiki asan yaye suka dinga ficewa daga falon kowa ya kasa magana dan sun rasa abin cewa,wasu farin cikine ya hana su magantuwa wasu kuma bakin ciki,kowa ya fita daga falon sai Abba Umar da Aliyu,da kuma Dady Habib,sai su inno,Abba Umar yace"Hajiya Babba ku daina kuka komai ya kusa wucewa insha Allah tun da har muka samu Alhaji Baba da kansa yayi maganar yaya,kuma daga nan nima gurin wani malami na zan wuce Musa aƙara tsanan ta rokon Allah!'Dady Habib yace"tabbas maganar Umar haka take nima ina da malaman da zan saka cikin lamarin, san nan a ganina ya kamata a hada da cigiya gidajen rediyo ko za a dace!'Hajjah tace"hakan yayi Allah yayi muku albarka!'shi Abba Aliyu ma atake nan ya fara kiran malaman sa kasan cewar shi malamin addinni ne ya fara shela yana sanar dasu asaka almajirai sauka,yanzu zai taho da kayan sadaka,inno tace"masha Allah Ubangiji Allah ya baiyana mana shi cikin farin ciki da cikakken lafiya!'gaba ɗaya suka amsa da Amin summa Amin.


Tunda ya fito yaji wani irin jiri na san kayar dashi,amma duk da haka sai da ya nufi ɓangaren ƙonannen dakin,zubewa yayi agurin yana cigaba da wani irin kuka mai matuƙar ciwo da saka mutum zazzafan zazzaɓi,Dady Mansur fa ya haukace da wannan al'amarin,shin ina Abubakar yake?ina kuma aka kaishi yanzu?kukan ya cigaba da yi,ya kuma kasa koda motsawa daga wajen,ji yayi an tsaya akan sa,da sauri ya juyo ganin Dije yasa shi saurin tashi tsaye yana kade jikin sa, ƙoƙarin barin gurin yake ta dakatar dashi da maganar ta data kusan saka shi fitsari a wando,shin yallaɓai Mansur wai meye haɗin ka da dakin nan ne?can kwanaki kai ne ka fara hanani zuwa gurin nan dan cika umarnin uwar dakina kuma har kayi min gargaɗin sake ganina agurin,san nan ina yawan ganin ka a gurin shin me ka ɓoye acikin ɗakin da yanzu rasashi yasa ka irin wannan kukan da tunda nake ban taɓa ganin magidan ci kamar ka nayin irinsa ba?Dady Mansur kallon Dije kawai yake amma bai bata amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyin ta ba,saima kaucewa da ya kuma yi dan barin wajen,cikin sauri Dije ta kuma cewa,Mansur kaji tsoran Allah ka bayyanawa mutane abinda kake aikatawa!'ko da bai bayyana ba ai yanzu mun gane shi kuma ko baka faɗa ba Mansur a kwai mugun abinda kake aikatawa!'cewar Dady Habib ke nan da isowar sa gurin kenan,Dady Mansur sakato yayi yana buɗe Habib da wani shegen kallo,tsawan sakanni shuru ya gifta ratsa tawajen,daga baya kuma Dady Mansur ya ɗauke kan sa daga kallon Dady Habib,tare da cigaba da tafiya ba tare da ya tanka musu ba,yanaji Dady Habib yana cewa tabbas anfara yin walƙiya acikin estate ɗin ALHAJI BALARABE kuma da sannu zamu ci gaba da binciko irin ku!'ya faɗa yana mai juyawa dan barin gurin.


Cikin sauri Dije ta koma ɗakin ta,ba abun da take sai kaiwa da kawowa, tabbas itama lokacin da tayiwa uwar ɗakin ta alƙawari yayi,so sai take son ganin ta dan sanar mata da abinda ta daɗe tana nema,yayin da ita kuma nata burin ita da Bintu zai cika na tona mata asiri dan sun riga sun shirya mata gadar zaren da baza ta iya fidda kanta ba,tun tuni wannan ranar take jira dan tabbas tasan idan ta kaiwa uwar ɗakinta wannan labarin ita kuma zata cika mata alƙawarin ta na bayyana mata fuskarta da kuma sakar mata yaran ta,ita kuma tuni ta shirya yadda wasan zai kasan ce,dan tasan yanzu matar ta sakan kan ce akanta dan kwantar da kanta tayi ta nuna mata tabbatas tana tare da ita ɗari bisa ɗari,dan haka tona asirin ta ba wani abun wahala bane agurin ta,wayar ta takalla tare da cizon yatsa dole sai dai ta jira kiranta,amma tasan dole zata kirata a cikin tsukin nan dan haka tana nan tana addu'a tare da jiran kiran ta ako da yaushe.

A hankali ya ke tashin ta har ta buɗe idanun ta dasu ka kunbura saboda kuka da damuwar da take ciki, tashi tayi tana ɗan duban wajen da suke ,amma dai batace masa komai ba,ganin damuwar dake cikin fuskarta ne yasa duk yaji jikin sa ya mutu,haɗa goshin sa yayi da nata sai ya zamana dogon hancin sa na gogar tsinin nata hancin,cikin sanyin murya yace", Bint ba son damuwar Nan,na daukar miki alƙawarin kamar yadda kika zama sanadin farinciki na nima sai na zama sanadin farin cikin ki,bazan bari kiyi kuka ba zan toshe duk wata hanyar damuwar ki,zan kawar da duk wani abun cutuwa A gareki,Bint zan samo miki fafinki da ummin ki aduk inda suke a faɗin duniyar nan!'.....

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 51 ```



Ko yanzu ma na tanadar miki da abinda zai iya rage miki damuwa!'ya faɗa yana goga siririn hancin sa kan tsinin hancin ta,rufe idanun ta tayi tana ƙoƙarin maida hawayen da suke san zubo mata,A hankali yasa hannu yana goge mata fuskar tare da ɗan gyara mata ita,ɗage mata gira yayi tare da cewa har kin ɗan yi kyau,bana so su ganki cikin damuwa da yawa!'zata yi magana yayi mata alamar tayi shiru,haka ta haƙura da tambayar da take bakin ta,fita sukayi sai faman kallan anguwar take yi saboda har yanzu bata fahimci inda suke ba.

Duban ta yayi tare da cewa ki shiga sai kiyi min iso!:ɗan jim tayi kamar tana tunanin wani abu,sai kuma ta gyada masa kai tare da saka kanta cikin madaidai cin gidan na bulo,sallama tayi cikin sassanyar Muryar ta,HAJJO dake zaune jikin bishiyar mango dake girke a faffaɗan tsakar gidan tayi wata irin zabura har zanin ta na ƙoƙarin kuncewa,cewa take yi, wa nake ji kamar Lailata Allah Ubangiji ka amsa addu'a ta na ganin Laila araye,idan mafarki ne kuma ka barni a haka karka farkar dani!'ta faɗa tana ƙarasawa bakin ƙofar da Bintu ta cokare agurin,zaro ido Hajjo tayi tare da dafe kirji bakinta har rawa yake gurin kiran Asma'u, Asma'u dake cikin daki tana haɗa wanki ta fito da gudu tana cewa lafiya Hajjo me yasa mek,,,,maganar ce ta maƙale mata sakamakon tozali da tayi da Bintu.


Cikin kiɗima ta matso kusa da Bintu, ta taɓata tare da cewa Laila kece da gaske? Bintu dai ido tasa musu saboda ita bata fahimci abinda hakan ke nufi ba ta daiji suna ambatar sunan mahaifiyar ta, Asma'u ta jawo hannun Bintu tare da cewa Hajjo wannan ba Laila bece"sai dai idan yarinyar Lailace!'Hajjo ta kamo Bintu cikin wani irin kuka mai tsanani da ban tausai,ta rungume ta,tana cewa tabbas wannan jinina ce,ko aduhu na laluba naji wannan halittar sai nagane jinina ce saboda tsarin halitta da komai babu inda ta baro Laila,ta wani bangaren kuma sak Umaru!'Bintu jin an ambaci mahaifinta yasa taji wani kuka ya ƙwace mata, Allah sarki ko a wane hali yake yanzu,tunda ta san Nafisa tana nan tana shirin kashe shi,jin hon daga waje yasa Asma'u tace"kai Hajjo ko dai tare suke da yaya Umar ne?bari na da naje na gani tunda har yanzu baya iya shigowa gidan nan kai tsaye!'ta faɗa tana figar mayafi akan igiya,ta fita cikin sauri,Hajjo kuwa kama hannun Bintu tayi ta kaita har kan tabarmar datake zaune,tare da saka ta gaba tana kallo bata fata ace mata Bintu ba jikarta bace,


Sallamar Abdallah yasa Hajjo ta dawo da hankalin ta kan bakin ƙofar tare da amsa sallamar,zubawa Abdallah ido tayi saboda hango kamannin Umar atare da shi,wani tabarmar Asma'u ta shimfiɗa masa ya zauna,idanun sa kan Bintu da yake son gano halin da take ciki, ji yake kamar bashi da lafiya saboda rashin walwalar Bintu, yarinyar da bata da batabarin damuwa tayi tasirin da zata hanata farinciki da walwala amma yanzu gaba ɗaya duk ta sauya,babu kunya Bintu ta matsa kusa dashi tare da langaɓe wuyanta a kafaɗar sa,tana ci gaba da yiwa su inno kallon rashin sani, cikin girmamawa Abdallah ya gaishe da Hajjo kana suka kuma gaisawa da Asma'u,Hajjo tace"bawan Allah daga ina duk da cewa ina maka kallon sani amma ina so kayi min bayani,amma dan Allah kar kace min wannan yarinyar ba ɗiyar Laila bace!'ta ƙarasa maganar cikin matso hawayen da suke kwarin idanunta, Asma'u ma shuru tayi ta zubawa Abdallah ido da kuma fatan jin kyakykyawan labari daga bakin sa,ɗan ajiyar numfashi Abdallah yaja tare da fesar da iskar da yacika bakin sa da ita,kana cikin nutsuwar sa da kuma salon maganarsa mai ratsa zuciya ya fara bawa Hajjo labari tun daga farkon zuwan Bintu ESTATE da irin gwagwarmayar da tasha da na nasa labarin da irin abubuwan da suka fuskan ta har kawo wannan rana da suka samu kuɓutar da Dady Abubakar daga cikin wannan ɗakin.

Wani Irin mamaki da al'ajabi da kuma tsoron duniya shi ne abinda ya riski Hajjo da Asma'u ko magana sun kasayi sai taraddadi da kuma hawayen tausayin ƴaƴan ta dakuma jikokin ta,cikin zubar hawaye tace"zo nan Batula naji ɗumin ki , ki maye min gurbin kewar mahaifanki Sulaiman da Laila!'da gudu Bintu ta waɗa jikin ta saboda yanzu ta fuskanci komai,wato wajen kakarta mahaifiyar ummin ta da fafinta Yah Abdallah ya kawota,kwanciya tayi ajikin matar da takeji kamar ta kwanta A jikin ummin ta ne,wasu hawaye masu dumi suke ta sararowa bisa kyakykyawar fuskarta,goge fuskarta Hajjo tayi kana ta gyara zaman ta cikin nuna jinjina tace"Abdallah kayi ƙoƙari kunyi ƙoƙari kuma zamu cigaba da addu'a da sadaka domin Allah ya kuma ɗora mu akan maƙiya insha Allah nasarar na garemu kamar yadda kuka kuɓutar da Abubakar da taimakon Ubangiji suma su Laila zaku kuɓutar da su da izinin Ubangiji,Ni ai yanzu hankalina yafi kwanciya kan da, saboda yanzu ina ji ajikina kamar yadda Allah ya baiyana min Bintu to zai baiyana min Sulaiman da Laila!'Asma'u ta ɗora da cewa insha Allahu rabbi ya nuna mana wannan rana!'gaba ɗaya suka amsa da Amin,Hajjo tace"yanzu mai zamu baku irin naku na ƴan gayu? ta faɗa tana kallon Abdallah da murmushi akan fuskarta,shima dan murmushin yayi tare da cewa ai Hajjo sai dai ko Bint Amma yanzu nake son juyawa ina da aiyukan da zan gabatar dasu yanzu!'Hajjo ta riƙe baki kai ɗan nan da wuri haka? amma dai ko furar garin mu ka bari na dama maka zata rage maka wani abu inyaso ko tafiya sai kayi da ita!'shuru yayi bai ce komai ba sai murmushi da ya ɗan yi,yana duban Bintu da tayi zuru tana binsu da ido,kafin Hajjo tayi magana ma tuni Asma'u ta tafi dama furar dan haka sai ta kuma dawo da duban ta kan Abdallah tana cewa, amma dai anan zaka barmin kishiyata mudan kwana biyu ko?jin jina kai yayi tare da cewa gobe zanzo mu tafi idan Allah ya kaimu!'to goben nan to babu damuwa Allah ya nuna mana ai ganin ku yafi min komai!'ganin kamar Hajjon bataji daɗi ba yasa shi cewa Hajjo karki damu indai Bint ce har sai kun gaji da ganin ta, insha Allah baza mu dawo muku nan ba sai da fafi da Ummi Laila,Kinga yanzu zaman bint bazai yuwu ba saboda akwai abubuwan dake gaban mu!'cikin gamsuwa da bayanin Abdallah Hajjo tace"karka damu na gamsu da maganarka, Allah ya baku nasara akan aiyukan ku na alheri ya kuma baiyana mana su cikin aminci shi kuma Abubakar Allah ya tashi kaɗunsa ya bashi lafiya!'amsawa sukayi da Amin cikin rangwamen damuwar da tayi kaka gida A zukatansu.


Lokacin da sukayi sallama har zai fita sai kuma ya ɗan yi jim da alamu dai akwai abinda yake son faɗa, inno tace" da akwai wani abu ne Abdullahi?cikin kwantar da murya yace"alfarma ce nake so kiyi min!'Hajjo tace"faɗi matsalar ka tsakanina da kai babu alfarma!'cikin ƙara tausasa murya yace"dan Allah Hajjo karki faɗawa Abba Umar komai kiyi shiru da bakin ki saboda ayanzu sanin sa zai iya haifar da wata babbar matsalar wan nan yazama sirrin mu har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana ƙarshen komai!'Hajjo ta ɗan yi jim kana kuma tace" idan kana ganin hakan zaifi to babu damuwa game da hakan kuma wannan tunani ne mai kyau, insha Allah bazai san komai ba!'yauwa Hajjo na gode da fahimta!'daga haka sukayi sallama ya fita,Hajjo tace"kije kuyi sallama mana Batula!'cikin sanyin jiki Bintu tabi Abdallah wanda har ya shiga mota.


A cikin motar ta same shi shi kaɗai,sai ta tsaya daga bakin ƙofar tana kallon sa idanuwan ta har sun cicciko da ƙwalla,miƙa mata hannun sa yayi alamar ta taho a hankali ta taka ta saka hannunta cikin nasa,janyo ta yayi cikin motar,yasa hannu ya rufe kana ya juyo da fuskarta gareshi,hmm gayamin wannan kuma na meye?ya faɗa yana lakato hawayen da suka zubo mata,fadawa jikin shi tayi tana ɗan sakin wata ƴar sheshsheƙa tare da ajiyar zuciya,shafa bayan ta ya shiga yi cikin ƙoƙarin samar mata da nutsuwa yace" ko bazaki iya zama ba mutafi?ɗan tura ƙaramin bakinta tayi tana ɗan bugun saitin zuciyar sa tace"kaima ka zauna mana sai goben mu tafi tare!'zaro idanuwan sa yayi tare da cewa kai Bint ya za ayi gan sameme dani na kwanar musu agida sai kace wanda mukazo wani garin!'shuru tayi batace komai ba,ɗago fuskarta yayi tare da ɗora bakinshi kan nata,A Hankali ya shiga tsotsa kamar mayunwacin da ya kwana baici ba,sun ɗau tsawon mintuna biyu kafin ya saketa,cikin muryar sa da ta sauya yace"maza shiga gida ina kallon ki!'cikin sanyin jiki kamar bata so, haka ta fita

Please Login or Register in order to submit comment