Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi mata ya tabbata dan kuwa gashi nan ta fara ganin alamu, Taufiƙa sai dai hakuri fa dan daga dukkan alama dai Abdallah ya rufe ƙofa,

A can falon Hajja kuwa bayan da ya tabbatar da Taufiƙa ta bar wajen,sai ya ɗan kuma gyara zaman shi cikin nutsuwa yace"Hajjah dama nazo ne akan maganar Dadyna!'yadda ta zuba masa ido da yanayin ruɗewa shine yaso bashi ƴar dariya,sai dai kuma yayi ƙoƙarin maida ta tunda dama ba al aldarshi bace,cikin ɗan ruɗewar da ta farayi tace"Abubakar ke nan?yace"wanda kika tafi dashi jiya!'ya faɗa idanun sa akan Bintu wadda ita kuma ta zubawa Hajja nata idon dan har yanzu al'amarin mamaki yake bata, bata taɓa yiwa Hajja kallon muguwaba amma sai gashi ya tabbata cewa itace makirar cikin zuri'ar Alhaji Baba,Hajja kuwa da kyar ta iya aro jarumta wanda duk da haka tsoran ta da rashin gaskiyar ta bai kasa bayyanuwa ba,cikin kasa haɗa ido da ɗayansu tace"Abdallah an samu akasi fa ban san ta inda abun ya juya ba saboda wannan mutumin ba Abubakar bane,kuma ina tunanin duk daga sharrin Habibu ne!'ta juya maganar dan san tabbatar da zargin ko sun gano makircinta,cikin dabi ar sa ta rashin gano ainahin abinda yake zuciyarsa,yace"Hajja yanzu kina nufin mun kuma rasa Dady?cike da mamaki take kallon sa,kana tace"amma ai na ɗauka duk ku kuka shirya hakan?ya akai kika san haka?ya kuma jefo mata wata tambayar,cikin ruɗewa da san kama kanta tace"ai shi ya faɗa da bakin sa!'a wannan karon Bintu ce ta jefo mata tata tambayar da cewa to Hajja ya akayi ya faɗa miki bayan wannan abun sirrine tsakanin su su uku?cike da tashin hankali take duban Bintu ta kasa bata amsar tambayar ta,Bintu bata saurari abinda zata ce ba ta cigaba da cewa,kinga hakan yana nufin an so yi masa wani abune da zai iya cutar dashi shi kuma yaga kawai gara ya bayyana cewa bashi ne Dady ba!'wani irin kallon tashin hankali tabi Bintu dashi kana tace"yanzu me kike nufi?nice zanyi ƙoƙarin cutar dashi?da sauri Bintu ta girgiza kanta tare da cewa abun ne akwai mamaki da ɗaure kai Hajja saboda mu ba irin bayanan ki Dady jafar yayi mana ba, hasali ma munzo ne dan sanar dake abin da ke faruwa,sai kuma muka ji saɓanin abin da ya kawo mu daga bakin ki,bayan kuma kince an ɗauke Dadyn!'Bintu ta ƙarasa maganarta da tsare Hajja da idanuwan ta irin na Abdallah,wata irin zufa ce ta shiga ketowa Hajja tana kuma mamakin yadda yara ƙananu suke son mozanta ta a fakaice,gashi sunƙi bata damar gano manufar su,ganin halin da tashiga ne yasa Abdallah miƙewa tare da cewa,shike nan Hajja yanzu ina shi wan can da muka saka a madadin Dady?da sauri tace"ai yana nan zan sa akawoshi!'Bintu tace"meyasa da kikaga ba Dady bane baki barshi yay tafiyarsa ba?a yanzu kam anzo gaɓar da take neman fito da kanta, kasa bawa Bintu amsa tayi saboda bata da amsar,dan haka shuru tayi tana rarraba ido, Abdallah ya kama hanyar fita daga falon ba tare da ya kuma tankawa ba.

Suna fita taji kamar an zareta daga cikin masifa,kai yaran nan sun iya tambayoyin da zasu saka mutum ya kama kansa sai kace wasu lauyoyi ko ƴan jarida,karma yarinyar nan taji labari,hatsabibiyar yarinya kawai,gaba ɗaya dai a wannan rana nutsuwar Hajja ta ƙare ta rasama ta kaimaiman tunanin da zatayi akan wannan al'amari,bata taɓa tunanin cewa akwai ranar da zata kwaɓe mata ba,bata taɓa tsammanin asirin ta zai iya neman tonuwa ba,kuma ko a yanzun ma bata tunanin haka a ranta dole zata san mafitawa rayuwarta,


Ɗan tsayawa yayi Bintu ta ƙaraso,kallon juna sukayi Sai kawai suka saka dariya,abinda ban taɓa gani ba a fuskar Abdallah,lallai yau farin ciki yay farin ciki,A hankali Bintu ta shiga gwada yadda Hajja tayi tun shigar su falon, Abdallah kuwa Binta kawai yake da wani kasalallan kallo yana murmushin gefan baki,da dai yaga ba da katawa zatayi ba kawai sai ya ja hannun ta suka cigaba da tafiya har zuwa sashen Hajiya Babba,

Kallo take binsu dashi wanda yake nuni da tsananin ƙaunar da take musu kuma har ta kasa ɓoyuwa cikin idanun ta,rungume Bintu tayi tana shafa kanta,ita kuma kamar wata mage tayi wani luf sai faman lum-lumshe idanuwa takeyi,sun ɗan daɗe a ɓangaren Hajiya Babba daga nan sukayi mata sallama suka koma sashen inno,sai da yaje yayi Sallah ya dawo kana ya samu Abincin inno najiran shi,ita Bintu tuni ma har taci nata saboda yunwar da take ji,shima zama yayi yaci, kana ya miƙe tare da ɗan kallon inda Bintu take zaune,so yake ya ɗan fita yaje gidan da yakai su Ummi,ƙarasowa yayi inda take zaune ta ƙurawa tv Ido kamar tanaso ta ciro mutanen dake ciki,zama yayi a kusa da ita tare da ɗan taɓa ta zabura tayi cikin tura baki tace"nikam ka bani tsoro ma!'yace"fita zanyi amma bazan jima ba!'da sauri tace"ba tare zamu tafiba?girgiza mata kai yayi tare dayi mata alama da girarsa, karyar da kai tayi kamar wata sabuwar marainiya,kana tace"ayya Yah Abdallah kasan fa ko ina tare muke zuwa meyasa yanzun bazaka dani ba? kai tsaye ya bata amsa da cewa nan ba gurin zuwan matan aure bane!'zaro idanu tayi tare da cewa to ai kai ma mijin aurene nikam tsoro nakeji bazan iya zama ba!'tashi ki tafi wajen inno!'ya faɗa yana miƙewa,tashi tayi jiki a sanyaye sai murza idanu da takeyi alamun dai tana son yin kuka,tsayawa yayi tare da zuba mata ido,shifa sam bashi da wata zarra akan abinda ya shafi BINTU,shi yasa yake kokarin ganin yayi abinda zai faranta mata,itace sanadin farin cikin sa da duk wata walwala da ya tsinci kansa aciki,kamo hannun ta yayi a hankali yayi mata masauƙi cikin faffaɗan ƙirjinsa,wani abu yake ji game da ita yana daɗa tsikarar zuciyarsa,mutsu mutsun da take ne yasa shi ɗago kanta sai yaga hawaye shaɓe shaɓe kan kyakkyawar fuskar ta,bakinsa ya kai kan fuskarta ya shiga share mata hawayen da harshensa, wanda ɗumin harshen nasa ya saukar mata da wata irin kasala da mutuwar jiki, cikin wata irin murya yake cewa ke Bint kin san zafin wannan kuwa kin san raɗadin zubar wayenki kuwa?bata fahimci mai yake nufi ba dan haka sai ta shiga girgiza masa kai,ɗan ware idanun sa yayi akan ta,daga nan kuma ya samu kansa da zura harshen sa cikin bakinta,take jikin ta ya shiga karkarwa,ganin ƙafafunta na san kasa ɗaukar ta yasa ta kuma rikoshi da kyau daga nan salon ya kuma sauyawa da wani irin mayataccen sumba mai ruɗa zuciya da gangar jiki,ba ga ogan ba,baga yarinyar ogan ba,wani irin mahaukacin salo yakewa Bint din tasa wanda shi kansa baibsan daga ina ya iyasaba,nema yake ya kasa control ɗin kansa akan Bintu,duk wani ƙarfin shi ƙare wa yake a duk lokacin da ya kasance da ita,suna cikin wannan halin basu ankara ba saijin kiran sallar magriba sukayi a tsakar kansu,wanda dole ta sa su rabuwa da juna,kawar da kanta tayi saboda kunyar abin da tayi,leƙa fuskarta yayi tare da cewa my ukty, na fasa fitar bazan barki ke ɗaya ba,da sauri ta juyo da fuskarta gareshi sai caraf ta kuma tsinkayar bakinsa cikin nata,amma ba sha yake ba tsayawa yayi yana kallon cikin idanun ta da ta kasa kallon sa,a hankali ya miƙe da ita ajikin sa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa,sai da ya shiga kana ya sake ta tare da shigewa toilet,yana fitowa yace"kiyi alwala masallaci zanje yanzu zan dawo!'kai ta ɗaga mishi kamar wata ƙadangaruwa dan bakinta da jikin ta duka amace suke da irin zazzafan kulawar Abdallah agareta.


Duk da cewa zuciyar ta ba anutse take ba hakan bai hanata son aiwatar da niyar ta ba,shirinta takeyi ta haɗa duk wani abu da zai iya zame mata arziki dan wucewa dashi,jira takeyi kawai gari ya waye ta fece,tana cikin wannan shirin kuma katsaham ta samu waya daga Alhaji Baba cewa yana buƙatar ta gobe da misalin goma a falonsa,(kasancewar Abdallah ya dawo da taron da safiya saboda wani tunani da yayi)jikin ta asanyaye ta amsa tare da ajiye wayar,ta gumi ta zabga tana tunanin abinda yasa ake hada taro rana tsaka,wata zuciyar tace mata ko dai mutuwar Umar ce ta samesu shi yasa ake son sanar da ita cikin nutsuwa, wannan tunanin da tayi ne yasa ta kwashewa da wata shegiyar dariya,wadda ita agurin ta ta cin nasara ce,yanzu hankalin ta ya kwanta sai kuma tsimayin abinda zai faru gobe.


Yana cikin filin jirgin sama na malam Aminu Kano ya samu wayar mahaifin sa,nasan kasancewar sa a gobe ƙarfe goma na safe cikin falon sa,cikin ladabi ya sanar da Alhaji Baba ai yana Kano saukar sa ke nan dan haka insha Allahu zai halarci taron,daga nan jirgin da zai kaishi Abuja ya wuce,yana sauka bai wuce ko ina ba sai gidan dasu Hajja suke,cikin girmamawa ya sanar da Hajjo cewa su shirya zai zo ya ɗauke su gobe dan zuwa estate zai gabatar dasu a wajen Alhaji Baba,


Duk wanda ya kamata yasan da wannan gagarumin taron ya sani har ma waɗan da Abdallah baicewa Alhaji Baba ya sanar dasuba, duk saida yasanar dasu ƴaƴan Hajja waɗan da suke nesa da yawa ne kawai bai ce lallai sai sunzo ba,Hajja kuwa ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba,babu yadda batayi da Alhaji Baba ya sanar da ita ko taron na meye,amma yaƙi cewa da ita komai, hasalima sai ya ɓoye mata cewa Abdallah ne ya haddasa taron,ganin yaki sanar da ita dalilin kawai sai ta rabu dashi dan bata son ta tsaurara bincike har ya ɗora mata ayar tambaya,waɗan da basu razana da kiran Alhaji Baba sune masu zuciziyar zinare, zuciyar da babu komai acikin ta sai Alkhairi,to Allah dai ya jiyar da mu Alkhairi a wannan zama na falon Alhaji Baba cewar da yawa daga cikin ahalin wannan estate ke nan.

A wannan rana da yawa daga cikin alhalin Alhaji Baba baccin su ragaggene daga na cikin gidan har na wajen irin su Baba nura kenan dasu Alhaji Hashir waɗan da kowa yasan da wannan taron dan duk da cewa suna garƙame amma saƙon ya tarar dasu,dan Abdallah bai bari Alhaji Baba yasan cewa ƴan uwan sa da ƴaƴan sa basa cikin gidan ba shi yayi uwa yayi makarbiya yace"zai sanar dasu,dan haka gaba ɗayansu hankalin su atashe yake, dukkanin su suna cikin halin nadama domin babu wanda ya tsammaci zuwan wannan rana agaresu, Alhaji Hashir kuka yake da idanun sa yana kaicon rayuwarsa da tsufan sa da gemun sa amma yabi ruɗin zuciya da kiɗan shaiɗan,yana matuƙar tsoro da jin kunyar haɗa ido da ɗan uwan sa,ji yake yi inama Allah zai ɗauki rayuwar sa kafin wannan rana ta jin kunya da mozanta ta waye,

Shi kuwa Dady Habib, bai san komai da yake faruwa ba, Abdallah bai bi takan sa ba,dan yasan shu'uman cin sa zai iya neman hanyar kufcewa daga garesu,tunda har yanzu baiga alamun nadama atare da shi ba,shi yasa ya rabu dashi sai agoben zaisa arufe masa idanu a shiga dashi har cikin falon Alhaji Baba,


Misalin ƙarfe takwas na safe Abdallah ya fito cikin shirin sa tsaf,sai zabga ƙamshi yake kamar wanda yayi ɓarin turare ajikin sa,Bintu dake ta sharar baccinta hankali kwance sai buɗe idanu tayi taga yana shirin fita,ai kuwa wata irin wuntsilowa tayi daga kan gadon tare da fara murza idanun ta,dan ba sai yayi mata bayani ba tasan cewa fita zaiyi ya barta,bai san ta farka ba sai takunta da yaji abayansa,tsayawa yayi tare da juyowa,kallanta ya shiga yi tun daga sama har ƙasa sanye take cikin wata ƴar figigiyar riga iya gwiwa gashinta kuwa duk yabi ya baje a kaɗarta,kana ganinta kaga wadda ta tashi daga bacci,da gira yayi mata nuni da jikinta,sai tashiga bin jikin nata da kallo amma dai ita bata ga komai ba,dan haka ta ɗago ta kalleshi da alamar tambaya,ɗan lanƙwashe kansa yayi a kafaɗarsa kana cikin taushin muryarsa yace"ba bina zakiyi ba?da sauri ta ɗaga mashi kai,yace"A hakan zaki bini me yasa yanzu bakya son zama a gida?tura ɗan bakinta tayi tare da cewa aiya nikam tsoro nakeji!'matsowa yayi gab da ita kana yace"Dady zanje na ɗauko kafin ki shirya ko kin manta da taron da muke dashi anjima?girgiza kai tayi tare da cewa to amma ka tsaya nayi wanka sai mu fita tare Ni sai na zauna wajen inno kafin ka dawo!'jan hannun ta yayi har zuwa cikin toilet ɗin kana ya shiga zare mata rigar jikin ta,duk da ƙoƙarin hanashi da tayi amma hakan ya gagara a wannan rana kuma a wannan lokaci sai da Abdallah yagane mata sirrin jikin ta, dan kuwa wanka yayi mata mai sunan wanka,tare da nan naɗota a tawul ya fito da ita,kana ya shirya ta kamar wata ƴar baby, ko da yake shi baby ce awajen sa, Bintu dai ta kasa haɗa ido da Abdallah har sa ilin da ya kaita ɗakin inno shi kuma ya juya ya bar gidan,dan zuwa ɗauko Dady Abubakar.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 58 ```


A FALON ALHAJI BABA.


Damisalin ƙarfe goma daidai falon Alhaji Baba ya ɗauki haramar al'ummar da suke zaune a ƙarƙashin sa,ciki kuwa har da Dady Habib wanda yayi tsumu-tsumu,dan shi sam bai taɓa tsammanin zai fuskanci wannan rana ba,tunda asirin sa ya tonu bai taɓa jin wani abu mai kama da jin kunya da nadama ba sai yanzu, wannan dalilin ne yasa ya kasa haɗa ido da kowa dake zaune cikin falon,a ta ɓangaren su Alhaji Hashir da Alhaji Nasir ma kusan hakane a gurin su,da sauran ƴan tawagar su ma baki ɗaya,Bintu dake kallon su ɗaya ɗaya,duk ta fahimci abinda ke zukatansu,abinda ya so bata dariya kenan wai kunyar duniya sukeji,bata lahiraba,kunyar Alhaji Baba sukeji ba ta ubangijin su ba,kaico da irin wannan rayuwar,da babu tsoran Allah acikin ta,kallonta ta maida kan Anty Nafisa wanda tana kallonta ta fuskanci tana farin ciki acan cikin ƙasan zuciyar ta,yayin da kuma azahirinta fuskar ke ɗauke da alhinin abinda take tsumayin ji cikin kunnuwanta, rashin ganin Umar shi ya kuma tabbatar mata da abinda take fata ne yake son tabbata,falon yayi tsit baka jin ƙarar komai sai ta na'urar sanyaya ɗaki da kuma fankokin dake kaɗawa,sai fitar numfashin waɗan da suke da nutsuwar yin sa.


Gyaran muryar da Alhaji Baba yayi yana tafe ne da bugawar zuciyar wasu da kuma samun nutsuwar wasu,A hankali ya fara gabatar da addu'a cikin tsananin nutsuwar sa da kamalarsa,bayan shafa addu'oin ne ya kuma gyara zaman sa tare da maida hankalinsa kan Abdallah kana yace"to Alhamdulillah Abdallah na cika maka alƙawarin ka kamar yadda nayi maka gashi nan na tara maka duk al'ummar dake cikin ESTATE ɗin nan,dan haka yanzu zaka iya fara gabatar da dalilin da yasa kasa aka tarasu!'rufe bakin Alhaji Baba dai dai yake da ƙara ƙarfin bugun zuciyoyi,sai kuma nutsatstsiyar Muryar Abdallah ta ƙara sa ruguza ɗan ragowar ƙarfin halinsu,yace"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin halittu,sai kuma ya ɗan yi shuru yana tunanin ta inda zai fara,idanunsa ne suka sauka akan Dady Habib dan haka ya cigaba da cewa'Alhaji Baba ina fata zakayi min afuwa game da abubuwa masu yawa da suka faru ba tare da saninka ba,san nan ina fata ka zama jarumi mai ƙarfin hali da yadda da duk wata ƙaddara da ta zo maka mai kyau ko akasin haka!'wani ɗan murmushi Alhaji Baba yayi kana yace"Abdallah baka da damuwa dani akan haka ai duk Musulmin ƙwarai dole ya kasance mai yadda da ƙaddara dan haka ka faɗi duk abinda yake tafe da kai insha Allahu zan kasance mai haƙurin ɗauka!'ya faɗa yana maida kallon sa kan matansa dan ya tabbatar da cewa suma haka take agaresu, Hajjah ce ta saki murmushin ƙarfin hali duk da bata da tabbacin zaman ya shafe ta ko bai shafeta ba,amma ya zama dole ta cigaba da yin pritendin dan tsira da ragowar mutuncinta,Anty Nafisa kuwa ji tayi zaman ya fara gundurar ta tunda yanzu ta fara hasaso wani abu daban,tunaninta ya fara bata cewa lallai wannan taron bai dangance ta ba kuma bai shafeta ba,tunda taga alamun duk mutanen cikin falon basu da wata masaniya akan abinda za a tattauna a wannan taron gaggawar, muryar Abdallah ce ta dawo da ita cikin hayyacinta inda ya cigaba da cewa,a kwai abubuwan mamaki wanda zan fara gabatar maka dasu yanzu,amma sai dai kuma banga Abba Umar ba ko bai ƙarasoba?wata mummunan faɗuwar gaba ce ta samu Anty Nafisa sai dai tayi saurin shiryawa abinda zata faɗa game da mutuwar Umar ɗin idan har saƙon bai tarar dasu ba,sai dai kuma Muryar da taji daga bakin ƙofar falon ALHAJI BABA ita taso zautar da tunaninta,Abba Umar ne yake shigowa cikin ɗan gaggawa tare da cewa afuwan ku gafarceni na makara ne saboda wani dalili mai ƙarfi!'mutanen da suka biyo bayan shi su kaja hankulan mutanen dake cikin falon har da Bintu wadda tayi saurin miƙewa cike da farin ciki ta rungume Hajjo da Anty Asma'u,take kuma kallo ya koma sama hatta da shi kansa Abba Umar ɗin da mamakin inda Bintu tasan su Hajja yake kallonsu, Abdallah kuwa wani irin murmushi ne ke fitowa daga bakinsa zuwa saman leɓansa,Alhaji Baba ne yace"Batula kin san sune?da sauri tace"Baba wannan kakata ce,da yayar ummina!'wata irin zabura Anty Nafisa tayi tare da cewa ƙarya kike wannan abun ba zai taɓa tabbata ba,bazaki taɓa zama ƴar Umar ba,kamar yadda ban taɓa haifa masa ɗa ba!'Abba Umar kamar wani dolo haka ya tsaya yana bin Bintu da su hajjo da Nafisa da kallo,gaba ɗaya ya rasa tunanin da zaiyi komai nashi ya tsaya,

Murya yaji daga bayanshi Muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba Muryar da ko a mafarki yajita sai ya ganeta,Muryar da yake kwana yake tashi da begen sake jinta,itace take cewa ƙarya kike yi Nafisa ba'a taɓa canja Ƙudurar Allah,kuma baza a taɓa sakewa tuwo sunaba,kin yi sake domin kuwa Bintu ta zama zakanyar dake juya akalar rayuwarki, Bintu Umar Balarabe kenan ƴar da kika so salwantar da rayuwarta,itace ta dawo gareki domin tona asirin ki na mugun nufi akan bawan Allah!'cewar fafi kenan da ya ɗora maganarsa daga inda Ammi Laila ta tsaya,tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Hajja dai bata san sanda jikin ta ya jiƙe da fitsari ba saboda tsabar tashin hankali dan tasan zuwan Dije taron nan tare kuma da su Laila ba Alkhairi bane a gareta,wato dama Dije ce ta gudu da su Laila ke nan?daɓas haka Nafisa ta koma ta zauna yayin da zufa ke ta zubo mata tamkar wadda ake ruwan sama akanta,yayin da fafi ya rugume Bintu tare da mahaigiyarshi da matar shi ciki kewa da shaukin ganin juna,shi kuwa Abba Umar sunkuyawa yayi tare da yin sujjadar shukurr,yana ɗagowa ya tarar da Bintu tsakiyar su shi da Laila ta rasa wajen wanda zata fara nufa,sai wasu irin hawaye da take fitarwa wanda ta tabbata na tsananin farinciki ne,yau gata ga iyayenta duka biyu babu hijabi tsakaninta dasu,ba ta ankaraba taji sun lulluɓeta duka su biyun sun rungume ta atsakiyar su,baka jin komai sai koke koken dake fita ƙasa ƙasa, wasu kuma da yawa mamaki ya hanasu kataɓus wasu kuma har yanzu basu fuskanci kan lamarin ba,Alhaji Baba kuwa yana zaune yana kallon ikon Allah, sai kuma ya jiyo da kallon sa kan Abdallah tare da cewa, Abdallah me nake gani haka mai ke faruwane?ya kamata ku FAHIMTAR dani, na shiga ɗimuwa da ruɗani na kasancewar ganin Umar ɗina da ɗiya har da mata idan banyi kuskuren fahimta ba!'Abdallah yace"Alhaji Baba ka kwantar da hankalin kazaka fahimci komai dan kuwa yanzu za a warware maka zare da abawa kuma abinda ka fahimta ba kayi kuskure ba,Bintu jikarka ce ta cikin jinin ka ɗiyar ɗan ka Abba Umar!'kabbara akasa tare da tu ajjubin wannan al'amari,inno da Hajiya Babba kuwa kukan farinciki suka saka,ko wacce na san ƙarajin Bintu ajikin ta A matasayinta na cikakkiyar jikar su,shima Alhaji Baba ɗagowa yayi ya kalli iyaye da ɗiyar tasu da suke cikin wani irin shauƙi na kasancewa da junan su,yace"Umar ku zauna kayi min bayanin abinda ka lulluɓemin!'zama sukayi gaba ɗayansu sai dai Abba Umar ya kasa haɗa ido da mahaifin nasa domin yasan shi ɗin mai laifine a gareshi.

Acan gefe kuma Hajiya zulaihat ce rabe babu abinda take sai kukan tunawa dana ta iyalan kuma gudan jinin ta,tausayin Bintu da ƙaunarta take ji har cikin zuciyar ta,yayin da Abdallah yakeji kamar ya tashi yaje ya rugumeta ya lallasheta yace"yi haƙuri Ammina kema naki farincikin yana kusa dake,amma ya fisan gabatar da komai daki daki idan ba haka ba abun zai cuɗe da yawa har a rasa abinda za 'aji dashi,amma dai ai sannu bata hana zuwa,mai da idanunsa kan Bintu yayi wanda yaji ajikinshi cewa itama idanun ta na kansa,ai kuwa suna haɗa ido yaga tayi masa wani irin kallo mai haɗe da wani irin shauƙi da kewa da bege gami da jinjina,lumshe idanun yayi tare da aika mata da sakon da ya kusa shiɗar da ita, Muryar Abba Umar ce ta karaɗe falon da fara bawa mahaifinsa hakura da neman gafarar sa dana mahaifiyar sa,kana ya ɗora da basu ainahin cikakken labarin haɗuwar sa da Laila da aurensu,kamar dai yadda Fafi ya sanar da Bintu,yana rufe bakin sa,Anty Nafisa ta zunduma wani irin ihu tamkar wata zararriya, Abdallah ne yayi mata tsawar da tasaka ta nutsuwa ba tare da ta shiryawa hakan ba,kana ya ɗora mata da cewa,muna jiran jin ta bakin ki ki sanar damu yadda akayi kika sa aje a kashe Bintu da mahaifiyar ta harma da Fafi?shuru tayi tamkar wadda ake magana da kurma,daga ƙarshe ma tace"ita sam sharri za ayi mata bata san komai akan wannan batu ba,kallon Bintu yayi tare da yi mata wata alama,cikin ƙan ƙanin lokaci kuwa akaji sautin Muryar Anty Nafisa ta cikin waya tamkar alokacin take magana,tsit falon yayi masu al'ajabi nayi masu fargaba nayi dan Hajjah ƙiris ya rage ta fara zawo bayan fitarin da ta lantaya,ta riga ta saddakar da cewa yaufa babu mafita kuma ranar tonon sililice,ranar jin kunya ranar nadama wadda bata taɓa tunanin cewa zata risketa ba,haka abin yake a ɓangaren Dady Habib da sauran makiran estate.


Wani irin kuka Nafisa takeyi kukan kaico da nadama,babu abun da ya kuma haukatata da wani irin fitinan nan kuka sai labarin da taji ya ɗora musu akan yadda yayi da saban aikin da ta bayar na kashe su shida su Hajjo da Bintu,da yadda ya kuɓutar da rayuwar su dake Allah yayi da sauran rayuwar su agaba sai ya bashi dabara da tunani da nasara akan mutanen har yayi nasarar juyar da hankalin su.

Tsit falon ya yayi baka jin komai sai fitar numfashi, wasu mai daɗi wasu na fargaba wasu kuma na tunanin makoma,kamar dai Anty Nafisa da tata ta riga ta ƙare acikin ESTATE ɗin Alhaji Baba,gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa zo nan ƴata Laila nasa Miki Albarka!'a hankali Laila ta ja jikinta ta matsa kusa da Alhaji Baba Wanda ya ɗan dafa hannun sa akanta ya shiga yi mata addu'oi da fatan Alkhairi arayuwarta baki ɗaya,haka abin ya kasance a wajen Hajiya Babba da inno,sai dai Hajjo ta kasa kataɓus bare ta samu damar sawa Lailan albarka kamar yadda sauran ƴan uwanta ko tace kishiyoyin ta sukayi,itama Lailan bataji zata iya kar ɓar Albarkar bakin Hajjah ba dan haka sai ta koma mazaunin ta ba tare da ta ƙarasa gaban Hajjan ba,masu ƙarfin halin magana ne suke iya tofa albarkacin bakinsu,Alhaji Baba yayi gyaran murya tare da ɗan gyara zaman sa kana yace"Abdallah ka gama gabatar da abinda kake son GABATAR wa ko da sauran bayanai a tare da kai?jinjina kansa yayi cikin ɗan motsa bakin sa yace"Alhaji Baba a kwai abubuwa masu tarin yawa da kuma mamaki acikin wannan zaman namu ƘUDURAR ALLAH CE take kan bayyana har yanzu da sauran mu,sai dai yanzu na miƙa ragamar bayanin Hannun Baffa Hashir ko Alhaji Nasir ga kuma Alhaji Kabir duk wanda yayi magana acikin su ya wadatar tunda bakin duk ɗaya ne!'yayi

Please Login or Register in order to submit comment