Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba dai a warke ba,idan kina buƙatar sarana to ina so kibi ayari domin abin layin markaɗe ne bai zo kan ƙaramin kai irinki ba,idan na gama da manyan kawuna zan tsaya na saurare ki,kuma kisha kurumin ki ki daina haƙilo shi wanda kikeyi dan shi wallahi ko fuskarki ba zai tan-tance ta cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba balle yayi miki duba irin na zumunci balle kuma duban soyayya, Oga Abdallah yafi ƙarfin ki dan ba dan irinku Aka halicce shiba Allah ya halicci bawansa Abdallah don mata masu kyakykyawar zuciya da tsoron Allah da kuma taimakon bayin Allah, zuciyar Oga Abdallah ta zinare ce ke kuma ta gawayi,to gaya min tayaya wannan haɗin gambizar zai yuwu,dan haka ki sawa zuciyarki shidin ba abokin rayuwar ki bane dan insha Allah Allah ba zai yi masa wannan jarabtar ta Auren ki ba ko iri-irin ki ba,ina so ki cigaba da saka ido akan wannan wasan Ni kuma insha Allah zanyi miki addu'ar tsawan kwana domin kiga ƙarshen wasan wanda zai zama gaskiya Abdubint for ever,ya kika gani?Taufiƙa ki kiyayi ranar na dama ranar da nasani ranar da sirrin ɓoye zai fito ranar da fuskoki da yawa zasu baiyana suna masu kaico da rayuwar da suka shuka,ki kuma kiyayi ranar da ƘUDURAR ALLAH zata baiyana,dan haka ina mai baki shawara da ki tuba tun kafin ranar dan karki kasance,cikin masu danasani wadda zata zamar miki ƙeya,kuma zaki kasan ce cikin mutanen da saran da nayi musu shi kaɗai ya isheki ba sai na kai ga asarar zubar da dafina ba!'har zata wuce sai kuma ta ɗan juyo dai-dai saitin kunnen Taufiƙa wadda ta tafasa kamar wuta saboda zafi da mamakin kalaman Bintu wanda suka matuƙar sakata cikin ruɗani da shakku mai tsanani akan Bintun,tace"abinda na manta ban gaya miki ba shine dafina baya cin wanda ya tsaya ga Allah ya kuma kiyaye dokokinsa,dafina ya tsaya ne akan mugaye ɓaragurbi masu ɗoyin baki da ƙwaƙwalwa,daga haka tayi shigewar ta ɗakinta tare da banko mata ƙofar da ƙarfi saboda ƙara tura mata haushi.


Tabbas idan taufiƙa tace"maganganun Bintu basu taɓa ta ba tayi ƙarya,sosai kanta ya kulle tare kuma da san neman ƙarin haske ga kalaman Bintun wanda suke kama da magana mai harshen damo,a kwai manufa A cikin kalaman Bintun,cikin mutuwar jiki da zuciya taja jikinta ta shige ɗakin su.


BaTaufiƙa ka ɗai ce ta shiga halin rikicewa da kalaman Bintun ba,hatta da Abdallah da Hajiya Babba da ta kawo kai dan sanarwa inno kiran gaggawar da ya same su daga Alhaji Baba sai da ta shiga wani yanayi na matukar zurfafa tunani,kasa shiga falon tayi ta koma saboda bazataso wani yaganta cikin wannan hali na kiɗima ba.


Tun dawo war sa daga masallaci da ya wuce tiraning sai lokacin ya shigo, wanda shigar sa ke nan kunnuwansa suka fara jiyo masa kalaman Taufiƙa, tsaki yayi zai wuce saboda bai ga amfanin sauraren shashan cin Taufiƙan ba,amma kafin ya saka ƙafar sa cikin falon sa ya tsinkayo ɗaɗdaɗar muryar Bintu tana maida wa Taufiƙa Raddi cike da kar sashi da kuma san zuwan wata rana mai ɗinbin tarihi agareta,tabbas shima ya shiga halin rikicewa da wannan sabon Al'amarin, tabbas ya daɗe yana tunanin abinda Bintu takeyi bai ci ace wai dan taimakon musulunci kawai take ba, idan yayi duba da ranar da ta bashi tabbacin zata taimaka masa da dukkan rayuwar ta,tabbas ranar ya hangi yadda wutar fansa ke ci a tsakiyar idanunta,to ga kuma wannan kalaman nata masu shige da har shene damo,meye gaskiyar tarihin wannan yarinya meye gaskiyar,abinda ya kawota ahlin nan?kai akwai wani abun da Bintu ta ɓoye wanda ita kaɗai tasan shi sai Ubangijin ta,ta yaya zaiyi ya gano wannan gaskiya da ta ɓoye masa?anya kuwa Bintu bata da alaƙa da ahlin ALHAJI BALARABE?dafe kansa yayi A yayin da yake zama ƙasan carpet ɗin dake malale tsakiyar haɗadɗan falon nasa,tare da runtse idanun sa,wai meye yasa abin mamakin cikin gidan nan baya karewa?kafin ya gama da wani al amarin wani ya taso, tabbas al al'amari Bintu wani babban al amarine da dole sai ya nutsu dan gano shi,kuma shi kaɗai zaiyi wannan binciken batare da sa hannun kowa ba kuma zai bar shi a matsayin sirrin zuciyar shi,


Hajiya Babba tunda ta koma ɓangaren ta take kaiwa da kawowa itafa a rikice take da wannan al amari na Bintu, tabbas A kwai wani ɓoyayyen sirri da Bintu take ɓoyewa,to me yasa takejin wani irin sabon kusanci A cikin jikinta game da Bintun? kuma tanaji ajikinta komeye agame da Bintu to Alheri ne,(Hajiya Babba macece mai matuƙar dogon hange da baiwa mai tarin yawa to ba wani abin mamaki bane dan shaidar Bintu jikar tace ta baiyana acikin jikinta da zuciyar ta duk da ita bata taɓa kawo wannan tunanin ba) amma tabbas tanaji ajikin ta Bintu haske ce ga ahlin ta kuma madubi mai haska baya,

"Zama tayi tare da ɗaga hannuwan ta sama tana mai addu'a tunda ga ƙasan zuciyarta har zuwa kan bakinta,ya Allah ka zama gatanmu kajiɓanci lamuranmu Ni da dukkanin musulmi masu tsoronka,ya Allah ka sakawa waɗanda aka aka zalunta ya Allah ka war ware mana ƙullin da aka ƙulla mai wuyar kwancewa,ya Allah ka tsare mu daga sharrin kiɗan shaiɗan ka kiyaye zuciyoyin mu daga faɗa wa halaka katsare mu da aikata saɓonka, Allah kakiyaye mu da aikin na dama kasa kar mu tozarta a duniya da lahira, Amin Ya Allah.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 37 ```



Wayar tace tashiga neman ɗauki, cikin nutsuwa ta shafa addu'o'in ta, tare da janyo wayar ta kara a kunnen ta,cikin girmamawa tace"Alhaji wallahi wani ɗan saɓani aka samu amma yanzu zan kuma gwada wayar tata idan batayi ba sai na koma ɓangaren nata!'ta ɗaya ɓangaren Alhaji Baba yace"kizo ai na samu wayar tata tuni ke muke jira, Hajiya Babba tace"to madalla gani nan tafe!'bayan ta ajiye wayar tare da tafiya dan amsa kiran megidan nasu, suji abinda yake faruwa da sammakon nan kuma.


Tana dosar coridon da zai sada ta da falon Alhaji Baban ta fara jiyo tashin Muryar Dady Mansur, a ranta tace"sababbe kaci kanka wato ma shine sanadin tarasu da wannan safiyar,to Allah Ubangiji ya shirya,ta faɗa tare da yin sallama cikin falon,amsawa sukayi gaba ɗaya kana sukayi gaisuwa a tsakanin su,cikin nuna halin dayake ciki na tashin hankali ya gaida Hajiya Babba, Dady Habib ma dake zaune ƙasan ƙafar Alhaji Baba yana ja masa yatsu ya gaida ta cikin tsananin biyayya, Hajiya Babba ta amsa fuskarta cike da ƙauna da kuma alfahari da yaron nasu wanda ya ya ƙwace girman Mansur tunda ya zubda girman to su sun ɗauka sun bawa Habib.

"Ɗan gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa kai Mansur tun yaushe ne baka ga shi Sayyid ɗin ba?cikin ƙara san zafafa abun yace" Nabil yace"sam baiga ya shigo jiya ba, ma ana dai bai kwana gida ba,da farko ma yayi tunanin yana sashena sai da aka idar da Sallah kana nake ce masa ina Sayyid,to shine yake sanar dani,gashi tun alokacin nasa aduban duk inda akasan yana zuwa amma babu wani labari!'ya ƙara sa maganar cikin yanayin fargabar abinda zai faru da ɗan nasa, Alhaji Baba yayi gyaran murya kana yace"to Ni dai aganina Sayyid ba yaro bane da za ace ya ɓata,sai dai wani abu daban dan haka Ni aganina mu jira zuwa jimawa idan bai dawo ba sai mu ɗauki mataki!'inno tace"gaskiya Alhaji Ni dai ashawarata gara ayi saurin fara neman yaron nan tun da kasan duniyar yanzu ta zama abin tsoro,ba zai yiwu ace har sai wani lokaci mu fara ne man sa ba,kuma dai kaga yaran nan duk runtsi sai sun kwana a gida,barantana muce sun saba yin irin haka!'tana ajiye maganar ta Hajiya Babba,ta ɗauka ita ma dai shawarar da ta bayar ke nan kamar yadda inno tace" ita kuwa Hajjah tayi musu kara amatsayin ta na kakar Sayyid,dan haka batace komai ba baya ga fatan Allah ya baiyana shi da gaggawa,Dady Habib yace"yanzu yaya katashi muje mu bayar da cikiyar sa gida jen ƴan uwa da abokan nan sa,idan ba a ganshi ba zuwa gobe sai mu sanarwa ƴan sanda,tun da yanzu bamu da tabbacin ɓata yayi kaga bai kamata muyi saurin sanar da ƴan sanda ba!'Alhaji Baba yace"to madalla hakan yayi, Allah Ubangiji ya kareshi aduk inda yake ya dawo mana dashi cikin ƙoshin Lafiya,Amin suka amsa gaba ɗayan su,daga nan Dady Mansur da Dady Habib suka fita dan fara aiwatar da abin da ya dace,Hajjah da Inno ma tashi sukayi suka koma sashen su kasan cewar yau turakar ta uwar gida ce Hajiya Safiya buzuwar Agadez.


Me sace Sayyid yake nufi?anya kuwa ba wani abune da ya dan ganci bin sahun ta ba? tabbas dole ne ta dawo da Dije cikin gidan nan tunda tasan itama Dijen bata da wani garanti akan ta bata san ko ita wacece ba,amma Dijen ce lamarin ta akwai sa shakku wanda hakan ne yasa tasa akayi nesa da ita daga estate ɗin gaba ɗaya, dan taga kamar tana shirin munafun tar ta ita da shegiyar yariyar nan,ga shi kuma rashin Dijen na son ya dameta,dan rashin ta shi yake sawa duk wasu abubuwa suke faruwa batare da sanin ta ba,gashi Sayyid ɗin ma ga dukkan alamu dai yafaɗa tarko, yanzu ya za ayi tasan waɗan da suka kama Sayyid idan ƙama shin akayi?tabbas a kwai ƙura,wata zuciyar tace da ita toke meye na far gaba bayan kin tabbatar da cewa Sayyid bazai iya bada baya nai akanki ba,tunda bai sanki ba,nunfashi ta ja mai tafe da ajiyar zuciya tana mai ƙara gaskata abin da zuciyar ta ta sanar da ita akan lallai su Alhaji Nasir su suka ɗauke Sayyid saboda suna tunanin yana aiki tare da wani akan buƙatar su,wanda basu san waye ba,shine suke son su sani ta hanyar ƙwamushe shi Sayyid ɗin,kuma suna tunanin zasu samu hanyar sanin inda Abubakar yake,wani ɗan murmushi tayi wanda alamun tane kawai ya nuna hakan,fulawar dake gaban ta Koriya shar ta cikin lambun da take ciki tasa hannu ta ɗan tsinka,tare da cewa Alhaji Hashir Alhaji Nasir Alhaji Kabir da sauran tawagar ku tabbas kunyi ta banza, domin ina da tabbacin babu abinda zaku iya ganowa game dani,saboda ban bar wata sheda da zata sa mai nemana ya sameni ba,kwayi ku gama ku dawo musu da ɗan su,Ni kam na riga nayi nisan da babu mai kamoni,(hmmm Allah mai kowa mai komai shi yake da ikon kamaki koma zai kamaki cikin ƙudurar sa,tafi-tafi dai ita dama akewa ai ƙarshen ta ƙasane)cikin ƙwarin gwiwa ta bar lanbun.


Duk tabi ta birkita ɗakin duk wani waje da tasan yana ajiye muhimman abubuwan sa saida ta duba,ɗan dakatawa tayi tana mai cizan yatsan ta tare da bin ko ina na cikin tangameman ɗakin da ido,cikin sauri ta nufi wata ƴar jaka wadda baza ta wuce girman jakar mata ta rataya wa ba,buɗe jakar tayi tare da zazzage ta gaba ɗaya tana mai fatan samun abinda take nema,takardun da suka faɗo ta shiga dubawa da ɗaɗɗaya yayin da kuma bugun zuciyarta ke kuma tsananta,saboda tsananin tashin hankali da fargabar abinda ta gani rubuce cikin takaddun,goge idan ta ta kumayi saboda ta kuma tabbatar wa ba gizo yake mata ba,tabbas wannan sa hannu ne na mijinta akan ya mallaka wa ɗiyar sa gidan mansa dake cikin garin na Abuja,ta kuma buɗe wata itama ya sa hannu akan ya mallaka wa ɗiyar sa wani babban mension da bai daɗe da gama gina shi ba,sai ta ukun ita kuma kamfanin sa na auduga ya bata,hannu ta ɗora aka tare da zunduma wani ihu,da sauri ta rufe bakin tana mai fashewa da wani irin kuka mai tada hankali.


"Wayyo rayuwa me yasa zakiyi min haka? Ni Nafisa naga ta kaina ashe shukar dusa nakeyi ban sani ba,me yasa banyi irin tunanin da Bintu tayi ba tun kafin zuwan wannan rana,kuka takeyi sosai tana san batu tamkar wata zararriya,anya zata yadda duk wannan wahalar da tayi ta tashi abanza,waifa wannan ke nan data gani,bata san iya adadin waɗan da yasaka hannun ba,dole tayi wani abu tun kafin ta zama asararriya dan kuwa ta rasa wannan uwar dukiya ta Umar ba iya asara tayiba ita kanta ta zama asararriyar,kwashe su tayi gaba ɗaya tana mai aiyanawa dole ta sami Bintu dan ita ka ɗaice zata kawo mata mafita akan wannan al amari.

Ita ba sa hannun ne a yanzu ya dame taba,ƴar dayake iƙirarin ya bawa itace tafi damunta,to wai shin wace ƴar yake nufi?a i'na yasame ta a ina ya gano ta?idan ya gano ta yanzu tana ina?to ya akayi hakan ta farune dama matacce Yana dawowa?ko dai Umar tunani ya fara zautar shi?idan kuwa hakane ya zama dole agareta ta binciki Umar dan sanin inda ya dosa da kuma abinda yake nufi da mallaka wa gaibu dukiyar da ta jima tana farauta.


Hello Samira!'daga ɗaya ɓangaren Samira tace"ya naji muryarka kamar ba dai-dai ba?Samira akwai matsala amma ki ɗan yi haƙuri zan kiraki,yanzu ina kan hanyata ta zuwa guest house zamuyi miting, ko da yake anjima mu haɗu kawai sai muyi magana!'daga haka ya kashe wayar dai dai kuma lokacin ya ƙara so gidan su da suke haɗuwa dan zaman tattauna matsalar su.


Samira ta dubi oga Abdallah tayi masa alamun ko ya fahimci wani abu? dake wayar a amsa kuwa ta sakata,Safwan ne yace"kema dai kin san bazai wuce tashin hankalin an riga su ƙwamushe Sayyid ba,kuma zasuyi tunanin waɗanda suke tare dashi ne suka ɓoyeshi dan kar su sami damar samun bayanai daga Sayyid ɗin,samuyal yace"hakane sai dai ina ga tunanin su zai iya canjawa!'Abdallah ne cikin yanayin ƙasaitar sa ya ɗan motsa bakinsa kana yace"basu da wannan damar tunda muna tare dasu ta ko ina ko kun manta lawan ayanzu shine drivern Alhaji Nasir?mun mamayesu ta ko ina ga kuma Samira dan haka duk ta inda zasu ɓulla mu zasu gani!'Samira ta ɗora da cewa,kuma bana tunanin zasu iya canja hanyar da suke kai a yanzu domin mun riga munyi musu shigar sauri,mune muke juya tunanin su,koda sunyi tunanin hakan to tabbas Nice zan kuma ɗora su a hanya ta yadda zamu samu dukkanin abinda muke so!'Abdallah yace"mu saka ido akan motsin kowa domin ayanzu munzo gaɓar da zamu fara han kalta da motsin kowa ta hakane kuma zamu damar ɗora zargin mu akan duk wanda muka ga wata alama atare dashi,sace"Sayyid zaiyi matuƙar ɗagawa wanda suke sakashi aiki, kuma tanan zamuyi ƙoƙarin gano ko waye domin bibiyar sa.

Hmmm Abdallah da sauran rina A kaba fa, gano wannan shu'umai sai andage da addu'a dan sun san takan ɓadda kama cikin mutanen kirki, sai su saka ɓaƙar fuskar su cikin fararen fuskoki yadda fararen fuskokin zasu haska su a kasa gane ɓakin fuskar tasu to Allah dai ya baku nasara Abdubint.


A can kuma ɓangaren su Alhaji Hashir tare da Alhaji Kabir,sai Baba nura da Sama'ila da kuma,Salisu,yayin da Alhaji rufa'i ya kasance shine kaɗai babu acikinsu,kuma waɗan nan mutane sun kasan ce duk alhalin su ne suke musu wannan faɗi tashin, wato Alhaji Nasir da ɗan sa Sama'ila Sai Alhaji Hashir da ɗan sa Baba nura,sai kuma Alhaji Kabir shima da ɗan sa Salisu, dukkanin su sun yi zurfi cikin nazarin wannan lamari da ya taso musu,cikin dogon tunanin da Alhaji Nasir yayi yace"anya kuwa bamuyi gangan cin fita daga lamarin yaron nan Abdallah ba?nifa ina ganin kamar dasa hannun sa cikin wannan lamari!'Alhaji Sama'ila ne yayi saurin tarar sa da cewa haba Abba tayaya Abdallah yasan da wannan shirin namu balle har ya ɓullo mana ta haka? Ni ina ganin fa wannan fa bashine abinda Abdallah yake nema awajen mu ba dan haka ka daina sako shi cikin wannan sabgar!'Baffa Hashir yace"maganar Sama'ila akan hanya take Ni nafi tunanin mutanen nan sun ɗauke Sayyid ne kawai saboda suma sun gano muna bibiyar sahun su,dan haka sun ɗauke shi sun ɓoyeshi saboda kar mu samu wasu bayanai a tare da Sayyid ɗin!' wannan shine gaskiyar maganar cewar Alhaji Kabir kenan,kuma ina da tabbacin basu ka ɗai bane me amfani da Sayyid daban yake, kawai Ni aganina mu cigaba da bincike mubar maganar Sayyid, abu me mahimmanci agurin mu shine sanin inda Abubakar yake,dan haka mu cigaba da wannan binciken ta hakan zamu kuma gano waɗanda suke da irin manufar mu!tafi suka ɗauka gaba dayan su cikin nuna gamsuwa da batun na Alhaji Kabir,da wannan shawarar suka sami matsaya a tattaunawar su ta yau.


Kaf Alhaji Sama'ila ya zaiyanawa Samira tattaunawar da sukayi awanni biyu da suka wuce,tare da ƙara wa da faɗin to kinji shawarar da muka yanke akan wannan al'amari,Samira ta ɗan ja ajiyar zuciya tare da cewa shawararka tayi wannan ma Abune mai kyau da Yakamata musani, dan haka idan kuna da buƙatar taimako na hanya A buɗe take!'murmushi yayi tare da cewa ki kwantar da hankalin ki Samira lokacin buƙatarki yana nan zuwa!'itama murmushin tayi tana mai ɗaukar ice cream ɗin dake gaban ta, haka suka cigaba da ɗan tattaunawa cikin ƙara bugun cikin sa ba tare da ya gano hakan ba.


Alhaji Mansur fa yatashi hankalin sa,saboda har yanzu da rana take faɗuwa baiji wata alama da ke nuna masa cewa Sayyid zai dawo ba,ya tashi hankalin kowa dake cikin ESTATE da wan nan shegen kwakwazon nasa da rigima, to dama ya lafiyar kura, Hajjah ce tayi kiran sa ta zaunar dashi tare da yima sa nasiha yayi hakuri za aga Sayyid ɗin, amma tamkar tura shi takeyi,gajiya tayi ta sa masa ido dan fadan da yafi ƙarfin ka dole ka maida shi wasa,


Ta auna kiran Bintu yayi so goma amma wayar yaƙi shiga, gashi duk sakanni tashin hankalin ta da ɗa girmama yakeyi,idan ta zauna ji take kamar ko mai zai iya zuwa ya faru,neman taimakon Bintu take cikin gaggawa,so take ta samu mafita kafin dawowar Umar,so takeyi ta samu hanyar da zata ɓullo masa dan Sanin abinda take ƙwaɗayin sani,gashi bata son yawan zuwa ɓangaren innon dan gudun shiga cikin zargi,amma dole nan da zuwa safiya tasan abinyi.


Ta ɓangaren Abdallah kuwa yayi mugun saka ido akan al amuran da suke tafiya a cikin estate ɗin,amma abin da yake bashi mamaki har yanzu bai ga wata shaida da zai nuna masa wani yana da ɓoyayyiyar alaƙa da Sayyid ba,ɗan numfashi ya fesar yana mai cigaba da zame kayan dake jikin sa dan dawowar sake nan,ɗan ƙwanƙwasa ƙofar akayi batare da ɗaukar wani lokaci ba ya bada izinin shigowa, dan yasan babu mai shigowa ɗakin sa sai Bintu,sallama tayi cikin siririyar muryar ta tare da shigowa,kallon ta ya shigayi ƙasa ƙasa batare da yabari ta kula da hakan ba,tayi kyau cikin shigar riga da siket na atamfa wanda yayi ɗas ajikin ta, tamkar wata ɗawisu haka ya shiga kallon takun ta ga wani irin ƙayataccen ƙamshi da yagame ƙofofin hancin sa,samun kan sa yayi da ƙara buɗe hancin sa dan cigaba da shaƙar ƙamshin,yana wani lumshe idanun sa tamkar wanda yake jin bacci,Muryar tace ta dawo dashi hayyacin sa tare da saurin cigaba da abinda yakeyi,tace wai inno tace nazo kana kirana!'ko dai kike so kizo?ya faɗa batare da ya dubi inda take ba,cikin yanayin ta na sakalci tace"Ni kam Inno tace kana kirana!'yana ƙoƙarin shiga toilet ya ɗan dubeta kana yace"kawai kice kinzo gun mijinki ba sai kinyi wani kwana ba!'ya faɗa tare da shigewa toilet ɗin,kallo tabishi dashi kana tayi ƙwafa,wai miji Ni banga wani miji anan ba? Abdallah yana da matuƙar ƙarfin ji shiyasa bai sha wahalar jiyo abinda Bintu tace"ba,kaɗa kansa yayi tare da sakin wani murmushi yace"yarinya zakiga bakiga miji ba saikin gyara wannan kalamin naki.


Ita kuwa Bintu tafiyar ta tayi ɗakin ta, tana cewa yau komai za ayi bazanyi kwanan wahalaba,mutum duk abi aka nainaye shi ya rasa ko hanyar yin numfashi mai kyau.


Lokacin da ya fito bai ganta ba yayi tunanin tana falon sa,dan haka shiryawa yayi cikin kayan bacci masu kyau kana ya fesa turarukan sa masu sanyin ƙamshi,tare da fita zuwa falon,da idanu ya dinga karaɗe falon amma bai ga ko ƙyallin Bintu ba,ƙara sawa yayi dining yacika cikin sa da girkunan gargajiya irin wanda Bintu tayi matuƙar ƙwarewa akan su,sai kuma akayi dace Abdallah yana matuƙar san girkin gargajiya shi yasa bai taɓa gajiyawa da nau'ikan girkin da take shirya masa ba, dan har abincin Fulani yi masa takeyi,haka kuma kullum ji yake kamar ana ƙara wa hannun ta zaƙi,sai da ya gama ya koma falon ya zauna yana ɗan taɓa aiki a computer,tun yana tsammanin dawowar Bintu har dai ya fidda rai,saboda lokaci yaja yasan bazata taɓa fitowa a wannan lokacin ba,tashi yayi ya koma ɗakinsa ya kuma yin brosh kana ya kwanta, sai dai haka nan yake ji ya kasa bacci kamar da abin da yake buƙata akusa dashi,sai diramar Bintu dake dawo mashi wani yayi murmushi wani yayi tsaki da haka dai bacci ɓarawo ya sace shi.


"Washe gari tunda ya dawo daga masallaci bai kuma fita ba yana zaune ta shigo tana ganin sa ta fara rarraba idanu kamar wata mara gaskiya,da ƙyar ta ƙara sa kusa dashi ta gaida shi amsawa yayi batare da ya kalli inda take ba,zata miƙe kenan wayar ta da sai yanzu ta kunna ta ta fara babureshon,juyowa yayi tare da zubawa Bintu ido, wadda ita kuma ta zubawa lambar da ake kiran da ita idanu,saboda wata irin nomba ce batafi guda uku ba kuma da wani irin yare ba da normal lambobi ba,ganin hannun ta yana rawa yasa Abdallah ruƙo hannun nata tare da karɓar wayar,shima zubawa nombobin ido yayi yana mai karanta addu'oi a bakin sa kana cikin yadda da Ubangiji da ka ɗaitakar zatin sa ya danna ok tare da saka amsa kuwa.

"Wata mummunan dariya aka saki tare da cewa yarinya mai tunani to ya kike keda gwarzan angon naki?ko da yake ba sai na tambayeki ba tun da Ni masani ne akan duk wani motsin ku,bawani Abune yasa na kiraku ba sai dan nayi muku gar gaɗi akan ku kiyaye da shiga sabgata domin ban kaɗai wani sirrina da sanin ko Ni waye, domin duk abinda kuke nema baza ku same shiba a halin yanzu daku da duk wani me san shiga hurumi na,baku isa ganin bayana ba ƙananan kifaye,sai dai Ni naga bayan ku da duk wani mai burin ƙwatar burina,ku tsaya iya matsayin ku na neman iyayen ku wanda kuma ina tabbatar muku da cewa bazaku taɓa samun su ba,domin ku ɗin ma baku tsira daga tarkona ba, kune cika makon burina da ku zan yi amfani na samu cikar burina,daga nan kuma sai nayi mai yuwu daku da iyayen naku!'


Wata mahaukaciyar dariyar ya kuma sheƙewa da ita, yana mai cigaba da cewa,yarinya mai hikima na yaba miki matuƙar yabawa da irin gudun mawar da kike bawa mijin ki dan ganin ya lalubo inda mahaifin sa yake,to ke mai yasa baki sanar dashi ya tayaki nemo taki mahaifiyar ba?kai ba daban zan ɓata shirina ba da na gaya miki inda mahaifiyarki take da kuma hannun wadda take riƙe dasu,ita da yayanta, FATIMAH UMAR BALARABE,DA ABDALLAH ABUBAKAR BALARABE,haɗin yayi kyau ina muku fatan shan wahala,daga haƙa ƙit wayar ta yamke,


Tofa kar ku manta Abdallah bai san wacece Bintu ba Bintu ma batasan wanene Abdallah ba,kamar yadda yake mata kallon wadda zata taimaka dan ceto rayuwar wasu mutanen,haka ita ma take masa kallon wanda zai ceci ahlin sa daga wata babbar matsala,ko ya zasuji? ko wane hali zasu shiga bayan jin wannan murya? to mu antaya gaba ɗaya cikin fage na gaba dan jin yadda zata kaya........



Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 38 ```


Wani irin kakkauran miyau Bintu ta haɗiya wanda yake tafe da wani gishirin tashin hankali,to waye wannan mutumin?waye kuma Abdallah A

Please Login or Register in order to submit comment