Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankailinki jikinki, idan kuwa ba haka ba allura zata tono garma!' takarasa maganarta cikin nutsuwa da yanayin kamala, ta yadda idan ba kana gab da ita ba baza kataba cewa ga abinda take fadawa matar dan kishiyarta kuma 'yar aminiyarta hjy ladidi ba,

Aunty nafisa taja wata doguwar numfashi me cike da fargabar bullowar wani gagarumin tashin hankali da kuma kwantacciyar damuwar da take kokarin tasowa ,tace" inno bazaki taba ganewa ba, ni kadai nasan yawan tarin damuwar da nake ciki da kuma tsananin fargaba, inno na rasa gane manufar mutanen gidan nan' idan ka dasawa wannan ayar tambaya daga baya sai kafara kokwanto, idan zargina yasauka daga kan wannan sai yafada kan wancan inno al'amarin gidan nan akwai rikitarwa da saka mutum cikin rudani, baka taba gane me amana bare me gaskiya, baza kataba gane mugu ba, bare makiyi!' tana dire maganarta inno ta dauka dacewa" kamar yadda kikeyi, ki boye fuskarki haka suma sukeyi harma sun zartaki a'iya taku, yadda bakisan zuciyarsu ba, suma basu san taki ba , yadda bakisan shirinsu ba, kema basu san nakiba, koni kaina da ke zaune gabanki matsayin surukarki ban san me kike shiryawa azuciyarki da rayuwarki ba!' tarufe zancanta tare da zubawa nafisar ido danjin abinda zatace" cikin kidima da bayyah nan nan tsoro!' tace'" ni kuma inno ? toni me zan kullah ? inno nima baki yarda dani ba?
inno tayi wani dan murmushi !' kana tace" yo nafisa ai duk wanda ya kwana yatashi cikin gidan nan ba abin yarda bane, ko da bakone ya shigo ya fita saina dora masa ayar tambaya, bare kuma ke surukar gidan nan!' cikin tsananin mamaki aunty nafisa tace" to inno meyasa ? kuma saboda me? meyasa kowa yake zargin kowa aginnnan ?
kuma suwaye ? inno tayi murmushi tare da cewa" nafisa nima bansani ba, bansan kuma suwaye ba, ban san a'ina bane ,da yaushe ne, duk ban saniba, shiyasa nace' miki ke kanki abar zargice agidan nan,'yayan gidan ma ba abin yarda mane bare kuma ke nafisa,kawai dai Ina baki shawara karki bari ta bare dake, shawarace kawai!'zukudi aunty nafisa tayi cike da matukar al'ajabin lamarin!' na cikin wannan estate wannan shi ake cewa" kowa tasa tafishshe shi".



__________________


Wata hatsabiyar dariya shugaba azikwi ya buahe da'ita!' san nan cikin katuwar muryarsa, yace" nanuu kai kadai ne zaka shiga dakin nan dan cika ragowar bukatar dodo jack, bayan kai bama bukatar kowa yashiga, san nan Abu na biyu dolene mu nemo yarinyar nan domin itace ragowar cikar burin mu, rasata yana dai- dai da rushe rayuwarmu da farin cikin mu,haka kuma idan ba mubi 'ka'idoji ba shima kawota rayuwar mu, babban tashin hankali ne da rasa rayuka,dan haka bayan aiki da tsafi dole muyi aiki da tunani da lura da kuma tuggu!' yana rufe bakinsa wanda aka kira da nanuu yace" shugaba ina da yakini akan baza musaba umarni da san zuciyarmu ba, ita kuma yarinyar muna nan muna bibiyarta,datemakon jack bazamu kusre ba!'

To fa waiya abin yakene? duk inda kuke zatansa ya wuce ku dan kucigaba da bina asannu.


Comments........
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P


💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 6 ```



'Dakine guda acikin estate din ta can wani bangare na musamman wanda ba kowane yakebi ta hanyarba, babu wanda yasan meye' acikin dakin da kuma mamallakan dakin,sai dai kuma wani abun mamaki babu wanda aka taba gani ya bude dakin ko kuma yabi ta hanyar,da dakin yake,
dayawa-yawan zuciyoyi nakai komo da taraddadi akan dakin, haka kuma zuciya da gan- garjiki suna son kai kansu inda wannan dakin yake, amma kash,hakan ya kasa samuwa daga dukkanin bangarorin dake son sanin abunda aka 'kunshe acikin dakin da kuma amfanin zamansa anan, kai harma da mamallakan dakin.
Adai-dai kuma wannan lokacin ne dije me aikin hjy madina matar mansur, tafito da wani kullin abu ahannunta sai yan dube-debe take kai kana ganin yanayinta zaka hango rashin gaskiya aidanunta,cikin sanda ta nufi can baya inda wannan dakin yake, alhj mansur da tun fitowarta ya hangota a lokacin da yake fitowa daga bangaren alhj baba(alhj balarabe)cikin sauri da azama ya mara mata baya dan ganin abinda take kokarinyi,abinka da namiji kakkarfa nan da nan ya taddata,cikin wata iriyar gugitacciyar tsawa,yace"ke dijeeee karki sake ki kara wani taku daga nan inda kike!'dije cikin tashin hankali da rawar jiki ta tsaya tare da juyawa dan ganin wanda yake neman fasa mata 'ya'yan hanji da wannan' razananniyar tsawar ,ganin uban dakinta tsaye yana aika mata da wani' shakurarren kallo me cike da gargadi da barazana,yasa ta kara kidimewa,da sauri ta karaso inda yake tsaye tana mai cewa"yallabai agafarceni wlh sani akayi bada niyar kaina nazo gurin nan ba, cikin tsareta da ido alhj mansur yace" dije.wani irin gan-gancine yakaiki ga zuwa gurin nan? kinsan kuwa komu bama iya zuwa hanyar nan amma ke kike kokarin saida ranki akan kudi!' wayasaka ki wannan aikin? kuma mezakiyi anan din?san nan meye wannan ahannunki? yayinda dady babba(alhj mansur) yakewa dije wadan nan tambayoyi ita tuni ta dade da antayawa' zuzzurfan tunani na yaya zatayi ta tseratar da rayuwarsu ita da yarta,tabbas idan bata kai wannan ajiyar inda akasata takaiba tana cikin tsaka me wuya,sannan kuma shima kaiwar wani tashin hankalinne wanda shima ya hada da rayuwarta, san nan fadin wanda ya aikota shima yana dai-dai da rasa rayuwar danta, to yanzu meye mafita agareta?kai suwaye anan gurin? ta ji wata murya daga bayansu ayayin da me maganar take nufosu saida ya karaso san nan ta fahimci waye alhj habib ne wanda ake masa lakabi da Abba 1,cikin nutsuwa ya dubi dady babba wanda yake ta faman muzurai yana wani hade rai,yace dashi yaya meke faruwane anan?cikin hargagi dady babba yace"kawai kaje babu ruwanka bana san saka ido da munafurci,Abba ane yayi murmushi cikin sanyiwa dan uwan nasa biyayya yace"yaya kayi hakuri ba Ina nufin wani Abu bane mara kyau amma kayi hakuri,dije kuwa hamdala tayi ganin ta samu hanyar kubuta daga wadan nan razannun tambayoyi daga uban gidanta,cikin sanda ta fece daga gurin ba tare da sun ankaraba.
cikin fada-fada da yanayinsa na rashin hakuri yace"ai dama habibu dole ka bani hakuri tunda kasan baka kyauta mun,duk abinda zanyi idanka yana kaina ka daukeni tamkar wani mara gaskiya Ina amatsayin yayanka kuma babba acikin gidan nan idan ka dauke yaya nana da sakina da hafsa kaf gidan nan nine babba amma bani da damar da zan aiwatar da abu ya zauna acikin gidan nan, saika kai karata gurin alhj baba, to Ina mai tabbatar maka billahillazi idan baka fita harkata ba zaka ga abinda zai faru, babu ruwana da ciki dayan da muka fito dan wani lokacin rufin asirin da dan uba zaiyi maka dan ciki dayan bazai yi maka shi ba!' yana zuwa nan not azancen sa ya kada babbar rigarsa ya juya afusace ya bar Abba ane tsaye da tsananin mamaki da takaicin halin dan uwan nasa.

Cike da razana da bayyanannen tsoro take duban nafisar, san nan cikin dan daga sauti tace'" nafisa kina da hankali kuwa? kinsan abinda kike shirin aikata mana kuwa!'sai kuma ta dan sassauta, cikin kwantar da murya tace" haba nafisatu yaya kike son bata rawarki da tsalle kinsan kuwa babban tashin hankalin da zamu dauwama aciki in dai ki kai saken da wannan' sirrin ya tonu,to bari in fada miki abinda har yanzu baki sani ba, alhj balarabe estate ta wuce duk inda kike tunani, ta wuce zatan me zato, a'iya tuggu da makirci, kowa yana' iya takunsa baza ki taba gane abinda ke cikin zuciyoyinsu ba,dan haka ki sake sabuwar damara indai har abinda kike fada gaskiyane!'ahankali nafisa ta dago kanta dake sunkwiye, idanunta sun kumbura sunyi ja tamkar garwashin wuta,tace'" mama na kasa!' damuwata tayi girman da bazata iya boyuwaba, Ina cikin mummunan tashin hankali aduk sanda naga dare yayi gari zai waye, damuwata 'karuwa take duk sanda na tuna lokaci yana zuwa da zan iya rasa umar,tsorona karuwa yake' aduk sanda na tuna, bansan wane rana bane wane lokacine, da wane yanayine wan can rudadden al'marin zaizo me cike da sarkakiyar da warware shi sai wanda ya kullah shi,mama ayanzu inajin garamun mutuwata da zuwan wan nan rana bazan iya kallon idanun umar ba, dana sani mama da na hakura da saukar KUDURAR ALLAH da ban kasance ahalin da nake ciki ayanzu ba!' ta karasa maganar da sakin wani rikitaccen kuka me bayyana abinda yake can cikin kasan zuciya,ita kanta mama kukan take yi wanda yake cike da cunkushewar zuciya na rashin tunanin mafita.

Pastor David hause

Kallo take masa me cike da tsoro,takowa yake gabanta cikin wani kakkarfan taku wanda duk takunsa daya ji take yana tafiya da bugun zuciyarta,fuskarsa me tsananin kyau da haiba da kuma tsananin kwarjini, ahade staf babu alamun murmushi bare dariya da dama ba al'darsa bace,tsayawa yayi akanta batare da ya tanka mata ba,dama tasan za'a rina da yaya ma tasamu yazo din,kallansa tayi sai dai ta rasa ta inda zata fara magana,tamkar ba itace me kururuwa da fade- fade akwanakin ba,daga kafarsa da yayi daniyar Bari wurinne yasa tayi hanzarin dawowa hayyacinta,tare da saurin kama tattausan hannunsa, san nan cikin rawar murya tace"FATASH...cikin wata murya me tsananin dadi wanda ta hade da yanayin fushi da muskilanci sai ta hadu ta bada wani daddan sauti,yace"don't coll me FATASH I'm doctor ABDALLAH,daga haka ya maida bakinsa ya tsuke tamkar bashine yayi maganar ba,cikin tsananin rudani da tashin hankali take kallallonsa, ga tarin maganganu da tashirya yi masa amma ta gagara furta masa Koda kalma daya saboda tsananin kwarjini da tarin ilhamomi da allah yay masa cikin kudurorinsa,tana kallo ya wuce cikin nisatstsan takunsa me cike da wani salo me burgewa, har ya bacewa idanunta, anan ne kuma takece da wani irin kakkarfan kuka me cike da ta kaici da tarin da nasani.

FATASH. saurayine dan kimanin shekaru talatin zuwa talatin da daya, kyakykyawan gaskene fari amma ba tas ba, wata irin kalace dashi me wuyar samu, yana da saje wanda ya kara kawata kyakykyawar fuskar tashi,dogone me dogayen gabobi saidai kuma ba siriri bane acike yake babu rama ajikinshi,fatarshi cike take da gargasa me laushi yana da kyan tsari kwarai abangaren halitta,ta bangaren halayya kuwa zan iya cewa fatash murdaddan mutumne, tun yana karami iyayensa basu Isa su gane inda ya dosa ba, muskiline na karshe wanda baza kataba cewa ya ma taba magana ba ko dariya,yana da matukar zurfin ciki bai yadda da kowa ba sai kansa yana da tsentsami ta ko wane bangare,bai iya so ba baisan ya ake yi ba, shi dai kawai yaje asibitinsa ya yini aiki ya kwana aiki bayasan damuwa ta surutu, shiyasa baya shiga sabgar iyayen nasa musamman mamansa,tun yana yaro yake da muradin wani abu wanda ako da yaushe ake haska masa acikin mafarkinsa tun bay gane ba harya fahimta, kuma yasa aransa sai yabi wan nan hasken,tun yana shekara goma sha uku iyayensa suka kaishi can u.s dan yayi karatu dan kaucewa abinda suke zatawa yaron nasu, sai dai kash basu nan tuni Alllah ya saukar da KUDURAR sa akan fatash ba ya saukar da haskensa akansa,allah me kudura buwayi gagara misali, yayi cewa FATASH baze tashi cikin duhuba,zuwanshi u.s yasamar masa da nutsuwa ta yadda zai guda nar da rayuwarsa cikin haske, yashiga neman malaman addini manya-manya ya kuma dace,ashekarun da yayi a u.s ya haddace alkur'ani me girma ya haddace manya- manyan littattafan addini,ayanzu fatash yayi nisa kuma bazai taba jin kiran da mahaifan NASA suke masa ba.


Mom abigail ce zaune tsakiyar rog capet din dake malale akasan falon,tayi kuka har ta gaji dan kanta, hawaye duk sun bushe mata,kofar falonce ta sanar da ita akwai bako wanda kesan shigowa ta hanyar wani Jan futula da yake kawo haske ta cikin falon,ahan kali ta jawo rumot din kafar ta danna nan take glass door din ta zuge, matar dake bakin door din ta shigo afuja atan kana ganin ta kasan tayi yar doguwar tafiya amma saboda bala'i naa cinta ko zama bata iya ba ta hau sababi,tace' ke abigail Ina wannan tsinan nan yaron naki? da baya ganin kan mutane da furfura maza ki fito mun dashi tun kan naci miki mutunci!' da sauri abigail ta mike tare da Jan hannun mamanta ta, cikin yanayin roko da magiya tace" mama kiyi shiru zo muje sama muyi magana fatash son yana nan kin san kuma bayasan hayaniya bare kuma irin wannan!'cikin hangame baki na matukar mamaki maman abigail tace" woo na wawoo abigail kene kika koma haka kinajin tsoran yarinyanki!'kasancewar yanzu cikin gurbatacciyar hausarta take maganar, abigail tace'"naji mama ni dai kizo muje sama zamuyi shawara dole sai mun hada da dabara kinsan halinsa yanzu fatash bazai murduba yana nan da halinsa saima wanda ya karu
dakyar mama ta yadda da shawarar abigail,suka haura sama amma taki yadda tasa komai abakinta ,sai ta samu mafita, mama ta gyara zamanta tare da kara fuskantar yar tata,kana tace" abigail Ina mafitar?cikin yanayinta na damuwa race" mama aure zanyi masa Ina ganin shine kawai abunda zai canja shi daga wannan halayya,mama ta zuba mata ido kana ahankali ta furzar da wani zazzafan iska daga bakinta,tace'"kina ganin wannan itace' mafita agaremu? kuma kina ganin zai amince da wannan' din? cikin sauri abigail tace'"akwai hanyar da zanbi,Ina ganin niomy zan fara kawowa mu gwada akanta ko zamu dace, daganan sai mu fara addu'a akansa!' mama ta sauke tagumin da tayi,sannan tace' to allah yasa karyaa karya musu yarinya, dan haukan dankin nan kullum karuwa yake!'nan da nan mom abigail ta hada rai, tare da cewa" gaskiya mama kidaina cewa fatash mahaukaci,idan kika sake yajiki kuma wallahi babu ruwana!'ta fada ta na gunaguni.


...... BAUCHI.....


Adame take kallon bakin fafi wanda yake tayi mata nasihu tun tashinsu a safiyar yau, ta fuskance shi yau kwata-kwata baya cikin walwala, duk da yanayin rayuwar dasuke ciki hakan bai hanasu walwala da farinciki ba,fafi yakance mata bintu duk wanda ya kasance me yadda da kaddara da tawakkali da jarrabawar rayuwa baya taba Bari asan damuwarshi Kuma baya bada kofar da za asan ahalin dayake ciki,shiyasa zaki ga Ina yawan janki da wasa domin kikasance me boye damuwarki aduk inda kika kasance!'
rumtse idanunta tayi adai dai lokacin da taji fafi kana kiran sunanta,hakan ya nuna mata lallai tayi nisa atunaninta,fafi yace"da ita bintuna ban hanaki irin wannan zurfin tunanin ba kina karamarki dake ?cikin dan tura baki da kuma tarin kwallar da tacika fararan idanunta tace"fafi kaine,banaso,kadaina!'to bintu me kuma nayi? fafin ya tambayeta cikin sigar lallami, cikin gab da rushewa da kukan da ya tokare mata makoshi,tace"fafi wannan maganganun ne banaso jinake kamar wasiya kake ajiyemun!'shima cikin san rushewa da kukan yace " a'a bintu kar muyi haka dake ai ba yau na fara yi miki irin wannan zantukan ba!' cikin rushewa da kukan da ta kasa rikewa tace" fafi yau na musamman ne bantaba jin yadda nakejiba ayau,inajin wata kewa na mamaye dukkan sassan jiki da ruhina,fafi bazaka gayan abinda kake boyen ba har sai mun rabu, fafi kadaina boyen komai na girma fa,kar ka tafi kabarni baka gayan yadda zan fuskancesu ba,karka tafi baka gayan wadànda zan mamaya ba, kar ka tafi baka gayan inda zanje da abinda zanje dashi ba,fafi karka tafi baka bani tarin amsoshin tambayoyi na da suke kanka ba,kuka take sosai
tamkar zata shid'e,fafi ma kuka take, kukan kewa kukan tausayi kukan fargaba,kukan wayyo rayuwa, yana matukar tausayin bintu,to yanzu me zaice mata? tayaya zai fara gaya mata?abu daya yasan zai iya nuna mata, wanda zai haska mata hanya,ta katse masa tunani da cewa'fafi kai nake sauraro,ahankali ya kama hannunta yace"bintu ba'abinda zan iya fada miki,sai abu daya,shine kije ki nemoshi aduk inda yake,zaku haska hanyar junanku dukkanin ku kuna bukatar temakon juna!'wani guri taga ya zubawa ido yana kuma girgiza kansa,yayin da bakinsa ya sarkafe ya kasa karasa mata,cikin kidima tashiga girgizashi tana cewa"fafi menene?ka fadamun a'ina yake yaza ai na ganeshi? meye sunansa?wane gari zan nufa?amma, Ina fafi shiru da alama dai fafi....


Tofa tafi-tafi dai akwai'fa murda-murda duk inda kuke zaton al'amarin ya wuce haka,
soyayya zazzafa me cike da wani irin salo me ratsa,zuciya cin amana makirci, tausayi ga kuma curku dadden lamari.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 7 ```


...... ABUJA.....

Pastor david ya zubawa mom abigail Ido yana sauraren tatsuniyar datake rangada masa,wai zata kawowa fatash matar aure,abin da matukar wuya,waisu mata meyasa kullum tunaninsu baya yakeyi,duba sai kace bata san halinsa ba,amma sai bai saurin gwasaleta ba,yace"yanzu kina ganin wannan mafitarce zata bulle miki?kina ganin yaron nan zai iya kallon macen da zaki kawo amatsayin matar da kikeso ya aura? abigail ina jiye miki aikin danasani akan abinda bazai amfaneki ba!'ya dire zancen da zuba mata Ido dan jin abinda zatace",
cike da karfin gwiwa mom abigail tace"tabbas zanyi duk yanda zanyi dan ganin fatash awannan karon bai bani kunya ba,mace zan kawo mai wayo da kissa, wadda duk irin tsananin murdewa da kafiya da miskilancinsa sai ya sauko yabita, awannan karon bazanyi sakeba!'ta karasa maganarta cike da confidence,david yayi murmushi me dauke da ma anoni kana yace"shike nan amma kisani duk abinda ya biyo baya karki nemeni,sannan ina da sharadi bayan amin cewata!'da sauritace"meye sharadin?yace" nima akwai abinda nake shirin zartarwa akan fatash,yanzu na bar miki filin amma indai dabararki batayi ba zanyi abinda na shirya, kuma karki sake kice dan me? idan lokaci yayi kawai ki zuban Ido kamar yadda nayi miki karkiyi mun tashin hankali, karki daga mun hankali,Ina fatan kin amince!'batare da wani dogon tunani ba tace" ta amince.


....alhj balarabe estate....

Dijee ce agurfane gaban uwargijiyarta, babu abinda take sai kakkarwa da rawar baki,hankalinta amatukar tashe yake zuciyarta tana cike da alhini da danasanin shigowarta cikin wannan ahli,cikin wata irin gigitacciyar tsawa matar tace da'ita"amma dai ke dije ban taba sanin cewa bakyasan rayuwarki ba sai yanzu, kinsan kuwa abinda kika jamun?kinsan tashin hankalin da kika jefani?ko da ike dama naga take-takenki bakyasan wannan aikin da nasaki,to ki sani yadda aka fara dake to tabbas dake za'agama,kinriga kinsan sirrina ayanzu baki da fita dolene kisawa bakin ki linzami ko dan rayuwar yaranki, kuma dolene mu gyara wannan bar nar tare,dan haka yadda nake cikin tashin hankali dole kema ki dandana kiji ya'akeji!'daga nan tayi wani shu'umin murmushi tare da jefawa dijee wayar hannunta tana ci gaba da wata dariyar mugunta,da sauri dijee ta kawar da fuskarta daga kan allon wayar dan ganin yadda wasu katti zaratan maza majiya karfi kewa danta masduk wani irin duka nafitar haiyaci,jini suke fitar masa tako ina,ita kuwa kanwarsa azaba suke mata da ruwa me tsananin sanyi dasaka mutum tafiyar suman wucin gadi,cikin wani irin rikitaccen kuka me taba zuciyar me imani tace" dan allah rankishi dade ki taimakamun kisa arabu dasu, na daukar miki alkawari duk abinda kikasani zanyi batare da kuskure ba, kiji kaina, suka dai suka ragen aduniya, sune sanyin idaniyata!'ta fada tana rike da kafar hajiyar ,fuzge kafarta tayi taja baya gami da tamke fuska, kana tace"dije wannan alkawarin dakika dauka shi kadai zai taimaki yaranki daga fadawa tarkona,dan haka kije saina nemeki!

D.A.D special hospital.shine asibitin dr abdallah (fatash) cikin takunshi na zaratan maza karfafa masuji da da tsantsar kyau da kwarjini yanufi lifter hawa na biyar inda anan office dinsa yake, yana shiga sakatariar sa me suna nabiha tayi azamar mikewa tare da tattaro nutsuwarta,tace" good morning sir!'ko gefan da take bai samu alfarmar kallonsa ba, bare ita, yana shigewa ta saki wata kakkarfar ajiyar zuciya ta tsabagen tsoro da kuma azababbiyar soyayya me cin zuciya da ruhi.

Hadadden office ne wanda yake cike da duk wani nau'i na amfanin lafiyar dan' adam,zama yayi cikin kyakykyawar kujerarshi me kama da ta sarauta,kana cikin yanayinsa me cike da nutsuwa yasa hannu ya fara duba wasu muhimman fayal, cikakkun mintuna goma da shigarsa sannan nabiha ta yi kokarin fara gabatar da marasa lafiyar dasuke ta tsumayin jiransa,

Agajiye yake taka dogayen kafafunshi akan tattausan carpet din dake malale akasan tan gameman falon,idanushi alumshe suke dan bazaka taba tsammanin yana kallon gabanshi ba,

Mom dake zaune tun misalin bakwai na mangariba tana dakon shigowarshi, tayi saurin mikewa dan tarbanshi sai dai kuma wani kallo da ya bita dashi me cike da alamun gargadi shine ya dakatar da'ita daga niyarta na kama jakar dake a hannunsa,ganin yana kokarin shigewane yasa tayi azamar bin bayanshi dan tasan indai tabari ganinsa yanzu ya kufce mata ta tafka babbar asara dan kuma ganinsa zaiyi mata matukar wuya, yana jin takunta amma sam bai kula ba, danshi magana daya zuwa biyu ma gagararshi takeyi,zama tayi afalonshi kana cikin marairai tar murya tace fatash son dan allah zanjiraka anan ka gama bukatun ka inason zanyi magana da kai! ta fada tana mai hade hannayenta alamar roko dan Jim yayi sai kuma ahankali ya gyada kanshi gami da karasa shigewa,

Rawa tayi harda juyi dan tasan tunda ya riga ya amsa to tabbas zai fito ya saurareta, danshi indai yace zaiyi abu da wuya kaga ya sauya magana yau agareta farar ranace me wuyar zuwa.


Kukane irin kukan nan me wahala wanda haryi take tamkar zata shide tun tanayi da karfinta harya zamana karfinnata ya kare sai wani irin Jan ajiyar zuciya me tsananin karfi, ita dai tana ji tana gani tasan fafin nata bai mutu ba, to amma me? gaba daya jikinsa asake yake babu inda yake motsi ajikin nasa,sai'idanunsa daya kafesu awake daya kwayar idanne kawai take jujjuyawa sai kuma numfashi dayake fitarwa sasa-sama, amma bada ban wadannan alamu ba to dashi da gawa basu da maraba, hannunsa ta kuma rikewa tana jijjigawa cikin dasheshshiyar muryarta da bata fita , tace" fafi Ina rokaka da allah katashi karkamin haka bani da kowa sai kai ina zansaka kaina? ta inazan fara nemansa ?a'ina yake? wayeshi ? fafi duk bansani ba, bani da nutsumi bare da bara, ni ban san komai ba akan rayuwata,fafi bazan iya ba ,bansan ta ina zan fara fuskantar wadan nan cukurkudaddun al'amuran ba,wayyoni kam bansan ina zan nufa ba fafi kayi min magana mana kaji fafi kace wani abu bintun kace agefanka tanai maka magiya, kaji tausaina mana ko 'ka'kane kaji fafina!'maganganu take iri da kala da na hankali da na tsantsan yarinta,sai dai kuma duk abanza baisan ma tanayi ba, abinka da lungu ba wasu jama'ane dayawaba,ba kuma tayi tunanin neman taimako ba, dakyar ta iya tashi tayi sallar isha tare da nafilar wuturi,zazzabine mai zafi ya rufeta ga wani wahalallan ciwan kai dayake neman bara mata kan gida biyu.


..ABUJA..

Sai da tayi zaman kusan awa daya afalon tana jiranshi batare kuma da ta kosa ba, har saida ya gama yangarshi kana ya fito.sansanyan kamshin sa ne yasanar mata da zuwanshi,anutse yake takawa har zuwa inda luntsumemiyar kujerarshi ta zama take, zama yay tare da mike sambala-sambalan kafafunshi ya kwantar da kanshi saman kujerar yana mai lumshe manyan idanunshi,shiru falon yayi bakajin komai sai karar na'urar sanyaya waje, ahankali mom tadan muskuta cikin taka tsantsan,dan yanzu wani babban motsi zatai yace zai bar mata wajen ba kuma tare da ta fadi abinda ya zaunar da'ita tsawon awa daya ba,cikin kokarin kalato jarumta tace"son dan allah kasaurari abinda zan fada maka ka kuma fahimceni, tasan bazai tankata ba, dan haka taci gaba da cewa"kasan ni maman kace bazan taba son abinda zai cutar da kai ba ina neman alfarma awajenka inaso awannan karon kabani martabata ta mahaifiyarka ka mutuntani kayi min biyayya kasani farin ciki akaro na farko arayuwarka!' ahankali yake bude manyan idanunsa wanda suke cike da bacci da kuma gajiya,d'an tashi yayi zaune, yana d'an taune lip dinshi kana ya fara motsasu ahankali yace"mom please I'm very tried if you finish the talking I need

Please Login or Register in order to submit comment