Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane ba kawai karabu dani sai na ɗauko shi koda bazan same shi a raye ba!'waye ne haka?bata bashi amsa ba saboda ganin wani waje daga can kusurwar ɗakin anyi shedar zanen ƙofa amma babu ƙofar,gurin ta tunkara gadan gadan tare da saka hannunta a tunanin ta bangone saboda babu wata alama da zata nuna maka ba bango ne gaba ɗaya ba,ashe ƙoface akayi mata kalar fentin san nan kuma ashafe take babu tudu, kamar yadda bangon yake haka take sak sai wannan shatin da Bintu ta gani, cikin sauri suka kalli juna da Abdallah,kana kuma atare sukayi Bismillah suka tura ƙofar saiga ƙofa ta buɗe.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 49 ```



Kamar an tsunkule shi haka ya tashi afirgice,zoban sa da yake ta faman wuta ya kalla abin baƙaramin ɗaure masa kai yayi ba,saboda tunda yake da zoban baitaba nuna masa wan nan alamar ba,da sauri ya tashi tsaye Saboda tunawar da yayi duk sanda zoben yayi wuta shike nuna masa cewar da akwai matsala,siddabarun sa yayi dan ya ɓullacikin ɗakin ba tare da yayi tafiya ba kamar yadda ya saba a duk sanda yaso,sai dai ga mamakin sa abin yaƙi yiwuwa hakan ne ya kuma tabbatar masa cewa da akwai babbar matsala,cikin sauri ya fita daga ɗakin nasa ya wuce falon sa ya fita duk cikin tashin hankali da fargaba,duk takun da zaiyi bugun zuciyar sa ƙaruwa yake.


Ihu Bintu ta saka tare da kanƙame Abdallah cikin wata irin kiɗima da rawar jiki,riƙeta yayi ajikin sa tare da zubawa daskarerren mutumin ido, lulluɓe yake cikin wani abu kamar yana, babu abinda ke motsi ajikin sa sai ƙirjin sa dake nuna alamun bugun zuciya,ƙirjin Abdallah shima babu abin da yakeyi sai bugu dan har yanzu bai fuskan ci waye a cikin wannan dabai bayin ba amma dai tabbas ganin mutumin ya tsunkar mai da zuciya,Bintu ce tayi saurin dawowa cikin hankalinta lokacin da kunnuwan ta suka fara jiyo mata alamun taku ta can wajen dakin saboda tagar da ke kusa da ita wadda take agarƙame, jijjiga Abdallah ta shiga yi cikin tashin hankali tace"wayyo Yahh Abdallah lokaci yayi yana nan tahowa mu ɗauke shi mu gudu!'yace"Bint sai dai mu mu nemi gurin tsira tunda kinga bashi kadai bane,kuma idan mun ɗauke shi bamu san inda zamu kaishi ba!'cikin tashin hankali da kukan da ya kufce mata tace"Yah Abdallah saboda shi nazo saboda na fita dashi nazo idan ban fita dashi daga gurin nan ba to babu amfanin da zuwa dakin nan yayi mana!'shi dai har yanzu Abdallah bai fahimci abinda Bint take nufi ba,amma dai zaiyi ƙoƙarin yin abinda take so,kallon ƙofar tayi cikin wani irin tashin hankali da ketowar wata zazzafar zufa tace"musan abin yi Yahh Abdallah da akwai matsala idan mutumin nan ya gan mu fa!'


Tun daga bakin ƙofar yasan cewa yau akwai babban tashin hankali,cikin matsanancin tsoron da ya fara fin ƙarfin zuciyar shi da gangar jikin sa ya faɗa cikin ɗakin, wayyo Ni kam Fatima saida na gwammace banzo wan nan tsurkun ba,tashin hankalin da nagani ya wuce abin misali,samu nayi na kuma raɓewa ajikin ƙofar ɗakin da su Bintu suke ciki kamar wata ƙadangaruwa,zuciyata kuwa tafi tasu bugawa dan Ni dai banga fitowar su daga ɗakin ba,wata irin gigitacciyar ƙara ce ta dawo dani hankalina,meye haka?waye yayi min wannan ɓannar?wani irin ƙara yake wadda take nuni da mugun tashin hankalin da yake ciki,hargitsa gurin yake yana wani irin juyi aɗakin,waye yake son ganin karshena?baku isa ba ko su waye kunyi kaɗan ku sabauta min burina na shekaru sama da talatin dole sai na cika burina,ɗakin ya nufa gadan gadan dan san tabbatar da ko ajiyar sa tana nan.


Numfashin Bintu kaɗan ne bai zuƙe gaba ɗaya ba dan dai Allah yayi da sauran shan ruwan ta agaba amma mugun tsoro da firgicin da tashiga tsaf zai iya sawa ta haɗiyi zuciya,shi kan sa Abdallah ya shiga cikin firgici amma fa shi ba dan Bintu ba tabbas sai ya ga fuskar wan nan baƙin azzzlumin, cikin rawar baki da jiki Bintu tace"ga..g..gashi nan zai shigo!'ta faɗa tana wani irin jan numfashi kamar ta shiɗe,kamar daga sama taji Muryar matar da take zuwan mata amafarki wadda a yanzu ta gane ba Aljana ce kuma ba mafarki take ba, gani kawai take kamar amafarkin, tana mata magana, kin kakkausar murya tace"Bintu ki kwantar da hankalin ki insha Allah nasara na garemu ki nutsu kiji abinda zan gaya miki!'cikin sauri ta gyada kai duk da cewa ita bata ganin matar,matar ko nace aljanar taci gaba da cewa zan riƙe shi a bakin ƙofar nan amma na wasu ƴan daƙiƙa ne,kuyi gaggawar fita da mutumin nan ku kai shi wani ke ɓan taccen guri!' cikin tashin hankali Bintu tace"kina zan cen fita ta yaya zamu fita bayan yana bakin ƙofar,aljanar tace"zan riƙe ƙofar ne ta yadda zai ja lokaci bai buɗe ta ba,kuma dama ayanzu sihirin sa ba zaiyi tasiri ba tunda kun riga kunga sirrin sa,ɗan abinda yake dashi kuma bazai masa amfani yanzu ba,Bintu ta kuma cewa har yanzu dai baki gaya min abinda nake son ji ba,shin ta ina zamu fita?shi dai Abdallah sake da baki da hanci yake kallon abin al'ajabi agurin matar tasa dan shi kawai gani yayi tana magana amma bai san da waye take yi ba,ci gaba yayi da zubawa sarautar Allah ido,gani yayi Bintu ta bi wani ɓangare daga can lokon ɗakin da kallo tana cewa naga wajen!'aljanar tace"yauwa to a wajen ki duba akwai ƙofar da zata fitar daku har farfajiyar da ake ajiye dukan motocin gidan!'cikin sauri Bintu taja hannun Abdallah har zuwa gaban wannan mutumin da bashi da maraba da ice ta wani bangaren, tana cewa muyi sauri mu fita bamu da ishashshen lokaci!' ba tare da ya tsaya yi mata wasu tambayoyi ba kawai yayi abinda ta umarce shi bai sha wahalar ɗauke mutumin ba saboda babu wani nauyi atare da shi,sai dai kuma wani tashin hankalin da suka kuma riska har yafi na baya,saboda wata irin wuta ce ta fara ci a cikin dakin kamar wadda take jira a taɓa mutumin,kuma da sauri da sauri take ci,cikin wani sabon tashin hankalin Bintu ta nufi ƙofar daniyar buɗewa amma abin ya gagara kuka ta farayi tana jijjiga ƙofar da ko motsi batayi,yayin da wutar take tunkaro su ga kuma Abdallah saɓe da mutumin a kafaɗar sa,wutar na daɗa tun karo su Bintu na ƙara azamar da ɗa buga ƙofar,ji tayi matar ta kuma cewa da ita Bintu kiyi sauri ga can karfen dake jikin bangon gabas shi zaki ɗauka da Bismillah San nan ki buga ƙofar dashi kina ambatan sunan Allah insha Allah ƙofar zata buɗe!'cikin zafin nama Bintu ta tunkari wajen da ƙarfen yake wanda kuma wutar tana gab da isa wajen ƙarfan, Abdallah ne yayi ƙarfin halin cewa Bintu kina da hankali kuwa kina ganin wuta na tunkarar wajen amma kina ƙoƙarin kai kanki!'ba tare da ta saurari abinda yake cewa ba ta isa gurin tana daukar karfen, wutar na kamawa awajen cikin sauri ta matsa daga gurin ta koma bakin ƙofar tare da yin Bismillah ta daki ƙofar da ƙarfi tana ambatar sunan Allah cikin ƙudura ta Ubangiji ƙofar ta buɗe, tamkar walƙiya haka suka bar wajen wanda kuma suna fita ƙofar ta koma yadda take tamkar ba ataɓa taɓa ta ba,hakan ke da wuya kuma baƙin azzzlumin ya antayo cikin ɗakin tare da fara zazzare idanun sa yana bin wutar dake daɗa ruruwa da kallo,wanda hakan yake tabbatar masa da cewa mai faruwa ta gama faruwa, zubewa yayi a ƙasan wajen daɓas baiƙi alokacin nan wutar ta haɗa dashi ta cinye ba, tashin hankalin da yake ciki ba zai misaltu ba a wan nan lokacin,ya kasa yin komai banda zubawa wajen da ya ajiye ABUBAKAR da yayi da idanu ko ƙiftawa ba yayi,maƙoshin sa kuwa ya kasa haɗiye koda miyau ne.


Wucin da ya rufe fatar jikin sa da wani irin zafi me shiga ɓargon jiki shine ya ankarar dashi halin da yake ciki,cikin sauri ya fita daga ɗakin zuciyar sa in banda balbala da wuta babu abinda take yi,yana fita daga gurin kuwa wata irin wuta ta mamaki ta mamaye dakin,wani abin al'ajabi kuma iya gurin ne kawai yake ci da wutar duk da cewa da akwai motoci ta bayan dakin, zubawa ɗakin ido yayi idanun sunyi wata irin kala tamkar garwashi,kamannin sa har sauyawa sukayi saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali, ƙoƙari yayi ya bar wajen tun kafin asirin sa ya ƙarasa tonuwa.


Wata irin ƙaƙƙar far ajiyar zuciya Bintu ta saki lokacin da taga sun fita daga cikin ESTATE din lafiya ba tare da sun hadu da wata tuhuma ba,shigewa tayi jikin sa tana fidda wani numfashi wanda kana jin sa kasan na wahala ne,runtse idanun ta tayi saboda zugin ƙonuwar da sai yanzu tasan tayi ta ta ratsa fatar ta,A hankali yasa hannun sa guda ya shafa kanta da duk ya hargitse saboda wahala,zuciyar sa kuwa cike take da tausayi da tarin tambayoyi,agame da wannan al'amarin da yafaru akan idanun sa,ɗan zamewa tayi daga jikin sa dan san bashi damar ci gaba da tuki cikin nutsuwa,sai dai duk sakan da sai ta duba bayan ta dan tabbatar da cewa yana nan,gani take kamar har yanzu basu tsira ba,kamar za a iya ƙara ɗauke shi ta hanyar tsafi,amma idan ta tuna da cewa Allah yana tare da su kuma nasarar tasuce sai hankalin ta ya ɗan kwanta,tafiya suka ɗanyi mai nisa kana taga sun ƙara so wani ɗan madaidaicin gida mai kyau mota ma batafi biyu ce zata iya shiga farfajiyar gidan ba,fita yayi ya buɗe get ɗin kana ya dawo yaja suka shiga,


Ga mamakin su sai kuma sukaji yanzu yayi nauyi bakamar da farko da Abdallah ya ɗauke shi ba,hakan yasa Abdallah ya ɗauke shi da nishi,a hankali suka shiga cikin madaidaicin falon da babu wasu kayan tarkace idan ka ɗauke tv da ec sai frige da kujeru, bai tsaya ba sai da ya dangana da can ƙuryar ɗakin dake cikin falon anan ya kwantar da mutumin da har yanzu bai san waye shi ba,tsayawa sukayi akan sa tare da zuba masa ido,tsuguna wa Bintu tayi agaban sa cikin fidda zafafan hawaye tasa hannun ta ta fara goge wan nan abun mai kamar yana ajikin sa da fuskar sa,cikin kukan da ya tsanan ta agareta tace"Allah sarki rayuwa ke nan yanzu ɗan uwanka ma sai ya zama abin farmaki agareka,ko kai ka farmake shi ko shi ya farmaki rayuwar ka,tabbas Dady kaga rayuwar da bantaɓa ji ko ganin irin ta a duniya ba,to amma hakan ba wani abune na mamaki ba duba da yadda duniyar ta koma duk abinda kake zaton ba zai yiwu ba yanzu shi yake yuwuwa, abubuwan al'ajabi da ɗaure kai su suke ta faruwa yanzu,sai dai muyi fatan Allah ya shiga tsakanin mu da shaidan ya kuma tsare zukatan mu da shiga mummunan rayuwa!'tana faɗa tana cigaba da yaye abin daga kan fuskar sa, Abdallah dama yaya lafiyar kura ai faruwar wannan lamari sai ya ƙara kurumtar dashi domin shi kansa so yake yaga yace wani abu amma hakan ya gagara,ga kuma tambayoyi fal aransa.


Zama ko makaman cin haka bai same shi ba,tabbas yasan babu waɗan da zasuyi masa irin wannan muguwar ɓar bar sai yaran nan,wai ma tun asali mai yasa shi kasa ɗaukar mataki akan su?me yasa baiyi ƙoƙarin ganin bayan su ba?bazan taɓa barin ku kutona min asiri acikin ESTATE ɗin nan ba,bazan baku wannan damar ba kunyi naku kun gama saura nawa wallahi babu wanda zan ƙyale acikin ku kaf sai na ƙarar daku,saboda tsabar baƙin ciki baisan sanda wani kuka ya kece masa ba mai tsananin karfi da fitar da wani amon sauti wanda yake cike da abubuwa na bakin ciki masu tarin yawa.



Cikin hawayen da suke ci gaba da wanke mata fuska ta ɗago da kanta tana kallon fuskar Abdallah da ya zuba idanun sa akan fuskar mutumin da yake jin wata iriyar faduwar gaba akan sa,kama hannun sa tayi ta jawo shi zama yayi gefan ta batare da yace kala ba,sai dai kawai yabi sawunta na jeruwa akasan gadon da mutumin yake kai,kamar saukar aradu haka yaji muryar Bintu nayi masa amsa kuwa yayin da take cewa Yahh Abdallah wannan shine Dadyn ka farin cikin ka burinka alfaharin ka wanda kake kwana dashi kake tashi kake kuma mararin san ganin sa da ganin bayan wanda ya sace maka shi ya hanaka jin daɗin mahaifanka!'ta ƙare maganar da zuba masa jiƙaƙƙun idanun ta,bakin ta kawai yake kalla sai ya koma ya kalli fuskar mutumin da Bintu kira da mahaifinsa,ya rasa da bakin da zaiyi magana,ya kuma kasa tan-tance halin da yake ciki tsakanin farin ciki da ɓakin ciki,to idan yace farinciki zaiyi ta yaya zaiyi farin cikin bayan ga mahaifin nasa a kwance bashi da maraba da gawa,idan kuma ɓakin ciki yace zaiyi ta yaya zaiyi shi bayan ga mahaifinsa agabansa wanda ya dauki shekaru yana faman neman inda yake,kawai sai ya kifa kansa ajikin Dady Abubakar yana fidda wani irin numfashi mai haɗe da wani irin zazzafan huci,yana kuma haɗiye wani abu mai girma da ya daɗe tokare amaƙoshinsa,shuru su kayi gaba dayan su,sai bayan wasu ƴan daƙiƙa ne Bintu ta samu kanta da ɗora hannun ta saman tattausar sumar sa tana shafawa cikin yanayin lallashi da tausayin kan su tace"yanzu me zamuyi agidan nan?ba tajira amsar saba ta ci gaba da cewa nayi tunanin muje mu kaishi gurin malam mu ajiyeshi,kaga za ayi masa magani sannan kuma ya samu tsaro, dan nasan tabbas sai yabi sahun mu,kuma ina ga mukai shi yanzu a cikin daren nan!'ta faɗa tana ɗan bin bangon ɗakin da idanu dan lalubo agogo,lokacin ta ga har ya tura ɗan yanzu baifi saura awa ɗaya akira assalatu ba,dawo da duban ta kan Abdallah tayi wanda har yanzu bai ɗago kan sa ba tun ƙifawar da yayi ajikin mahaifin sa,sai kuwa da yanzu maganar Bintu ta san yaya masa zuciyar sa tunanin sa kuma ya dawo kan hanya, kallon ta yayi idanun sa cike da wani ruwa wanda nake zaton ƙwalla ce ya hanata fitowa saboda tsananin bayaso yayi kuka agaban Bintu,yace"bari na kira su Safwan suzo su kaishi!'to me yasa mu baza mu kaishi ba?zuba mata ido yayi yana ganin yadda take cije bakinta har da wasu tarin ƙwallan da suka cika ƙwayar idanun nata,kamo hannun ta yayi babu zato ko tsammani saiji tayi ya kifa ta akan kafar sa da ya miƙeta, kafin ta gama tunanin abin da zaiyi mata kuma ta tsinci hannun sa kan gadon bayanta inda rigarta ta ƙone har ya shafi fatar jikinta,me yasa kike ɓoyewa?ya tamabeta cikin muryar sa da ta kuma yin ƙasa yana kuma zagaye yatsan sa agurin,cikin jin zafin ƙunar tace"na fiso mu gama da lafiyar Dady kafin tawa tunda ni mai sauƙi ne!'a gurin ki ko?ya faɗa yana zaro wayarta dake aljihun sa,cikin sakanni ya turawa su Safwan test saboda yana da tabbacin dai yanzu sun dawo Abuja,yana tura test ɗin ya tashi ya fara haɗa kayan wanke ciwo zuwa yayi ya wanke mata sai dai a wannan karon baƙaramjn dauriya tayi ba,ko dai dan taga ba allura bace,yana gamawa su Safwan suka bashi tabbacin sun ƙara so gidan cewa yayi su shigo,fita yayi dan buɗe musu ƙofa,yana bawa Bintu umarnin, ta shiga toilet zasu shigo su ɗauki Dadyn,daga haka ya fita daga ɗakin,jim kaɗan suka shigo gaba ɗayan su, yaji daɗi da bai samu Bint a ɗakin ba,kama Dady Abubakar su kayi tare da fita dashi,har cikin mota suka sakashi tare da gargaɗin Abdallah da kuma kiyayewar da yakeson suyi.


A zaune ya same ta ta haɗa kanta da gwiwar ta,yanzu sun gama da ɓangaren Dady sai kuma mahaifiyar ta da fafinta Allah yasa suna cikin lafiya,fatan ta ke nan a kullum,shigowar sa ce yasa ta ɗago kanta,dukbdavba kallon shi take yiba amma dai tana kallon saitin da yake,tahowa yayi gabanta tare da kamo hannun ta miƙar da ita tsaye yayi,kana yaja ta zuwa toilet,cikin matuƙar kula yace"zaki iya wanka?daga masa kai tayi idanunta nasan fitar da ruwa,girgiza mata kai yayi yana cewa a'a Ni fa ba kuka nace kiyi ba, Bint meyasa kuka baya yi miki wahala ne?ya faɗa cikin yanayin zolaya duk dan san yaga ta saki ranta,ɗan tura bakin kuwa tayi zatayi magana ke nan ya ɗora bakin sa kan nata,sanyin harshen sa tare da ƙamshin da ya zauna da'iman acikin sa,yasa ta lumshe idanun ta,bata kuma yi ƙoƙarin ƙwace kanta ba ta saki jikin ta suna tanɗe bakin juna,saida suka dau tsawon mintuna biyu a haka kana ya janye yana mai kashe mata ido tare da cewa, Bint kin kuma ko?kallon sa tayi da alamun tambaya,dan langaɓe kan sa yayi tare da turo mata jajayen lip ɗinsa yace"kin kuma cinye min baki bayan ban rama wan can ba!'ai tana jin haka ta juya masa baya tare da rufe fuskar ta da tafikan hannun ta.wani dan murmushi ne ya suɓuce masa ganin yasamu abin da yake so sai juya zai fita,juyowa tayi ta zubawa bayan sa idanu,karaf sai gashi ya juyo,da sauri ta kawar da kanta,yace"ya dai ko nazo nayi miki wankan?kukan shagwaɓa tasa masa tana buga ƙafar ta aƙasa,fita yayi tare da ja mata ƙofar.


Bayan fitowar ta shima shiga yayi yayo wankan,a bakin gadon ya same ta duk tabi ta kanannaɗe jikinta da bedsheet ɗin saboda babu abinda zata ɗaura towel kuwa tana ganin idan ta daura abinda ya faru ranar zai kuma maimaituwa,shi yasa taga kamar zama da bedsheet din yafi mata sauki,har ya gama abinda yakeyi yasaka kayan bacci bata motsa daga nan inda take ba,ɗan daga banta yayi kana yace"Bint kinji anfara Kiran sallah ina fata dai kin yi alwala? daga masa kai tayi,fita yayi daga ɗakin jim kaɗan ya shigo da sallaya da kuma doguwar jallabiyar sa wadda ta ɗan ɗage masa,miƙawa Bintu yayi tare da bata umarnin ta saka,tana daga zaune ta zura rigar san nan ta tashi tsaye,duk da cewa tayi masa kaɗan rigar amma saida tayi wa Bintu yawa,sabon tawul ya bata mai girma yace"maza rufe kanki muyi sallah!'karɓa tayi ta rufe jikin ta kana suka tayar da Sallah.


Duk da matsanancin rashin hankalin da yake ciki amma haka ya daure ya ɓoye bai nuna wata damuwa akan fuskar sa ba,yabi ayarin da suke shiga sallah shima ya shiga yayi kamar yadda suka saba shida sauran ƴan uwansa,yana fitowa ya bar gidan dan yasan tabbas za ayi maganar ƙonewar dakin kuma bayaso ya tsaya ganin takaici,kamar yadda yayi zato don kuwa haka ce ta kasan ce,duk inda ka gifta zancan ƙonewar dakin akeyi,wasu dayawa basu ɗakin ya ƙone batare da sun san abinda ke cikin saba shekara talatin da ɗoriya,Alhaji Baba da kansa sai da yayi tu ajjubin Al'amarin.


Bacci suke yi baccin da basu samu sunyi shi a daren jiya ba,idan kuga yadda Bintu da Abdallah suka cure guri ɗaya sai abin ya baka mamaki da da dariya ga kuma sha'awa, Bintun ce cikin jikin shi ya kanannaɗeta kamar wani zai ƙwace masa ita,wayar da ya karba a hannun Safwan ce ta fara ringin wanda shine dalilin farkawar sa daga baccin da yake yin sa ba tare da wani dadi ba,saboda mafarkan da suka da baibaye baccin marasa daɗi,da sauri ya dauki wayar dan kar ƙarar ta ta tashi Bintu,daniyal ne ya kira shi bayan sun gaisa daniyal yake cewa Oga nayi ta kiran wayoyin ka wasu suyi ringin wasu kuma akashe shine na sanar da Safwan ya bani wan nan layin!'Abdallah cikin yanayin bacci yace"haka ne Daniyal me ya faru? daniyal yace"Oga ka manta da tafiyar mu cikin suleja?cikin sauri Abdallah ya miƙe har saida Bintu ta farka a razane,yace"daniyal na sha'afa amma yanzu ka shirya kazo gidan nan na gari ka same Ni!'daniyal ya amsa cikin girmamawa kana suka ajiye wayar,Bintu da gaba ɗaya hankalin ta yana kansa cikin tsoro tace"me ya faru Allah yasa dai ba Dady bane!'ta faɗa cikin sanyin kuka,yace bashi bane amma dai yanzu mu shirya da akwai inda zamuje,bari nayi waya Safwan ya samo miki kaya ya bawa daniyal ya taho dasu,


Sorry no edittin
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 50 ```


Ba tace dashi komai ba amma dai gani take kamar wani abun yake ɓoye mata,ba'A fi mituna goma ba sai ga kiran daniyal,ba tare da ya ɗauki wayar ba ya tashi ya fita daga ɗakin,jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata leda,miƙawa Bintu yayi tare da cewa sauri ki saka zamu tafi!'tashi tayi tana ƙoƙarin shigewa toilet sai taga ya juya ya fita daga ɗakin hakan ne ya bata damar saka rigar tare da yana mayafin ta asaman kanta,fita tayi falon gidan wanda suka ci karo da Abdallah shima ya fito cikin shigar sa ta ƙananun kaya wadda sukayi masa matukar kyau suka kuma fito da zallar kyawun jikin sa,ɗan kallon sa tayi kana ta ɗauke kai,yayi mata kyau sosai amma ita yanzu tsoron kallon sa ma takeyi dan kar yayi mata wata fassarar,


Sarai ya gano ta amma bai magantu ba,fita sukayi tare, Daniyal yana ganin su yayi saurin buɗe motar suka shiga baya,ya rufe tare da komawa mazaunin drever,a hankali ya fara jan motar har suka fita daga gidan,fita yayi ya rufe get din kana ya dawo suka dauki hanyar zuwa gidan Hajjo.


Hankalin shugaba azukyi idan yayi dubu to duk sun tashi,wai mai yasa nanu yake son zama sanadin mutuwar kasuwancin su ne?anya kuwa ba cire shi daga harkar zaiyi ba dan karya jawo musu abinda zaizo ya tarwatsa jin dadin rayuwar su ba,nanu ne ya dawo da shugaba daga duniyar razanin da ya fara shiga akan mummunan karshen da yake son jawo musu,yace"shugaba kayi magana mana, wannan al'amari fa ba ƙaramin abu bane sun riga sun karya Ni sun rusani sun kai rayuwata ƙasa tunda suka riga suka ɗauke Abubakar suka sami Abigirl a hannun su,na tabbatar da cewa duk sanda Abigirl ko ABUBAKAR suka farfaɗo daga suman sihirin da mukayi musu ƙaryar mu ta ƙare daga Ni harku dan haka dole mu haɗu mu nemowa kanmu da rayuwar mu mafita!'shugaba yace"lallai nanu ka haukace da waɗan nan kalaman naka ai yanzu kai wan nan ta shafa bamu ba, tunda dakin nan ba ajiyar muce acikin sa ba,kuma Abubakar da tarkacen dake cikin ɗakin basune tasirin mu ba kowa tasirin tsafin sa daban,kamar yadda kowannen mu matsalarsa da ban,yanzu ka gaya min taimakon da kake so muyi maka dan ayanzu shi kaɗai ne abinda ya rage tsakanin mu da kai!'duk da cewa nanu baiji dadin maganar shugaba ba amma sai ya danne abinda ke taso masa ya kwantar da kai yace"yanzu so nake asato min yarinyar nan daga nan zan janyo shi mijin nata yazo inda muke,kaga kashe su duka bazaiyi min wuya ba!'Shugaba yace"nasan saboda rufin asirin ka kake son yin duk wan nan abun ko?kamar wani gaula haka nanu ya daga wa shugaba azukyi kai,dariya shugaba yayi tare da cewa shi kuma Abubakar ɗin ya zakayi dashi?kasan idan ka kashe su baka kashe Abubakar ba tamkar ka sare reshe baka kashe miciji baka sare kansa bane?yayi shuru tare da zubawa nanu idanu yana jiran amsarsa,wani wahalallan numfashi ya fesar kana yace"shima Abubakar ɗin kashe shi zanyi!'ka haƙura da dimon ɗin ke nan!'cewar shugaba,shuru nanu yakuma yi cike da zurfafa tunani,can ya ɗago kansa da idanun sa da sukayi jajur saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki,shuga rasa dimon ɗin nan tamkar rasa rayuwata ne bazan iya haƙura dashi ba,zan sace wannan shegiyar yarinyar da ita zanyi garkuwa Abdallah yakawo min kansa da mahaifin sa!'idan kuma bai aminta da haka ba fa? tambayoyin shugaba fa neman zauta ƙwaƙwalwal nanu sukeyi duk hanyar da ya samo sai shugaba ya kawo lalacewar

Please Login or Register in order to submit comment