Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya zulaihat ba,ɗan shuru Rahima tayi tana kallon yadda Ammin ta haɗe mata girar sama da ta ƙasa,ta san ba dan komai takeyin hakan ba sai dan tayi garkuwa daga manyan tambayoyin da tasan zata yi mata,ƙara matsawa tayi kusa da ita kamar zata koma Cikin ta,abin da ya fusata Ammin ke nan,cikin hasala tace"waike kam Rahima meke damunki haka? gotai-gotai dake kin zo kina neman komawa ciki!'ta ƙara sa maganar amatuƙar fusace,dan so take ta kaucewa tambayar da Rahiman take son yi mata a duk lokacin da ta risketa cikin wannan yanayin,cikin marairaice fuska Rahima tace"kai Ammi ke ko irin kewan nan nawa bakyayi,tunda kika korani gurin Hajiya Babba baki taɓa cewa Rahima na ina kewarki yau kizo min mana ko kwana biyu kiyi min sai ki koma ,Ni kuma na gaji da kewarki da rashin ki nazo amma nazo kina korata da hantara!'ta faɗa tana mai goge hawayen da suka zubo mata akan fuska, Allah sarki uwa,sai kuma duk Ammi taji rashin daɗin abinda tayiwa autar ta ta,cikin sanyin murya tace"haba auta ya za ai nace bana kewarki,kema kin san faɗa ma ɓata bakine kawai dai inayin nesa dake ne dan bana son damuwata ta shafeki har ta sakaki cikin wani hali!'ta karasa maganar tare da jin tasowar wani ɗaci mai haɗe da zafi dake ƙunshe cikin zuciyar ta,kama hannun ta Rahima tayi tare da cewa,Ammi idan damuwarki bata saka min damuwa ba to rashin ki zai sa tabbas nima A rasani,domin tabbas kikaci gaba da ɓoye abinda yake ranki tare da baiyana damuwar ki to wataran sai dai nazo na tarar da babuke,yawan damuwarki ya kai mizanin da komai zai iya faruwa dake, Ammi Ni ban ce sai kin faɗa min damuwar ki ba,dan tunda na san bakya son faɗa min na haƙura, amma dai ina so ki rage yawan damuwar ko da ba duka bane nasan lafiyarki zata iya inganta!'murmushi Ammi tayi mai matukar ciwo kana cikin tausayin kanta da ɗiyar tata,tace"wallahi Rahima na rage damuwa tuni na fauwalawa Allah dukkan lamurana,dan da ace ban daina ba da bazan kai yanzu ba,to amma na riga nayi tawassali da tsarkakan sunayen Ubangiji na kuma san cewa ƙaddara jarabawar rayuwace,ta wani tafi ta wani ta wani bata kai ta wani ba, haka kuma ta wani kyakykyawa ta wani kishiyar hakan,dan haka ki daina damuwa,nima na daina damuwa tunda nasan Allah baya bacci yana ji yana kuma gani,kuma na roƙe shi cikin bacci na roƙe shi cikin ido biyu na roƙe shi da rana da dare da safe,haka kuma na roƙe shi cikin sakanni da mintuna da awowi,dan haka ina nan ina jiran Ranar da ƙudurar sa zata haɗu da irada,ranar da zaice ta kasan ce ita kuma ta kasan ce,domin nayi yaƙini tuni addu'a ta ta riga ta amsu sai jiran lokacin da zata baiyana!'Alhamdulillahi alakullin halin,da yayini a musulma na tashi cikin musulun ci kuma ya tsarkake zuciyata daga bin wanin sa ya bani kyakykyawar zuciyar da na kaɗaita shi shi ɗaya na kuma dogara da shi,cikin ma bayyanin farin ciki da samun nutsuwar zuciya Rahima tace"Allah ne abin godiya A ko da yau she!'daga nan Ammi ta zarce da yiwa Rahima nasiha tare da tunatarwa wanda suke shiga jinin jikin ta da ƙwaƙwalwar ta suna zagawa tare da samun wajen zama.


Hajjah ta zubawa Taufiƙa ido A yayin da ta gama ratta ba mata jawabin ta, cikin kuka da wani irin baƙin ciki dake tasowa tun daga ƙarƙashin zuciyar ta,wani ɗan murmushi Hajjah tayi kana tace"yaro dai yarone,to yanzu Ni me kike so nayi miki da kika kwaso uban kaya kika dawo nan,ko so kike na kira shi Abdallah n nace masa gaki ya aure ki? Taufiƙa ta kalli Hajjah da jajayen idanun ta da suka rune saboda kuka,tace"Hajjah dan Allah ku taimakamin wallahi zai iya yadda idan kuka gaya masa saboda kema kin san Yah Abdallah yana da biyayya,tunda itama waccen ƴar matsiyatan bashi ita akayi kuma yakarɓa,nima idan kuka ce masa ya aureni wallahi Hajjah zai yadda, na yadda zan zauna da Bintu Ni dai kawai kusa shi ya aure Ni dan Allah Hajjah!'ta faɗa tana mai saukowa ƙasa ta riƙe ƙafar Hajjah tana wani irin kuka kamar ankashe mata duka dangin ta,kafin Hajjah tayi magana Dady Habib dake shigowa falon yace"Hajjah ya kamata a duba lamarin yarinyar nan kar taje ta shiga wani hali akan abinda zamu iya bata!'shuru Hajja tayi cike da yin dogon nazari akan maganar Dady Habib,can taja numfashi tare da cewa.....


Fatimah y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 42```



Kai yanzu Habibu kana ganin wannan shine adalci?sunkuyar da kansa yayi kana cikin ladabi yace"Hajjah gani nayi kamar idan akai hakan shine hankalin ta zai kwanta, tunda kinga itama waccen yarinyar bashi ita akayi ina ga itama Taufiƙan idan aka bashi zai karɓa yayi biyayya!'wata irin harara Hajjah take zuba masa tun kafin ya ida maganar tasa,yana direwa kuwa ta ɗauka cikin faɗa tace"amma kai kam Habibu wallahi baka da kirki, wannan sankan har ina,saboda su bare ne a cikin mu shine zamu ƙuntatawa zuciyar su,wato tunda yayi biyayya a wan can to wan nan ma sai abashi koda ran sa baya so,ita kuma ƴarku a faran ta mata saboda itace ƴar dangi,to ba dani za ayi wannan sakarcin ba,kuje can kai da ita da wanda zai biye mata ku ƙaraci shirman ku amma banda Hajjah a ciki!'ta faɗa tana ƙoƙarin tashi dan barin falon gaba ɗaya,har ta bar falon bata bar mita ba, Taufiƙa kuwa gaban Dady Habib ɗin ta rarrafa tare da sakar masa wani ɗan kukan yaudara koda zai taimaka mata tunda taga alamun haka atare dashi,ɗago kansa yayi,kana ya dafa kanta cikin san kwantar mata da hankali yace"haba Taufi meye abin daga hankali? bayan ga ɗan uwanki nan Alhaji Baba ya baki,meye aibun Sayyid?cikin kukan da ya kuma ƙwace mata tace"Dady wallahi Ni bana son Sayyid a tunda can amatsayin abokai muke dan haka yanzu bazan iya zaman Aure dashi ba,dan Allah ka taimakamin ka sanar da Alhaji Baba halin da nake ciki,saboda kai ka ɗaine yake sauraran maganar ka, kuma kana gani Sayyid ɗin shima ya gudu saboda baya sona!'kul kar na kuma jin wannan maganar A bakin ki, wa yace miki Sayyid guduwa yayi? Sayyid ɓata yayi kuma insha Allah muna saran ganin sa anan kurkusa kar ki ƙara wannan maganar kinji,ki yi haƙuri maza tashi ki tafi ɗakin Hajjah tunda bakya son wajen innon ki kwantar da hankalin ki ki dai na yawan koke koken nan!'tashi tayi tana layi kamar wadda tasha wani abun,ta dai jine kawai amma ba dan ta yadda ba,itafa bata jin zata haƙura da soyayyar Yah Abdallah,saboda sonsa acikin jininta yake,da kallo Dady Habib ya bita cike da tausayi,dan tabbas da yana da damar da zai aura mata Abdallah da ya aura matashi ko dan samun nutsuwar ta


Har ya gama shirin sa bata tashi daga baccin da takeyi na bayan asuba ba,ɗan tsayawa yayi akan ta tare da zuba mata ido,tunanika ne suke ta kai kawo cikin ƙwaƙwalwar sa,a yanzu babu abinda yafi buƙata kamar yagano wanene wannan mutumin sai kuma iyayen Bintu wanda yake ganin kamar duk hanya ɗaya ce zata kai su ga cimma wannan nasarar,kallonta yake tamkar wanda ke son samo amsoshin sa a kan fuskar ta,a hankali ta shiga buɗe idanunta saboda A can cikin jikinta taji kamar ana kallonta,tana buɗe idanun nata kuwa suka shige cikin na Abdallah,da sauri ta ɗauke kanta saboda yadda taji gaɓoɓinta na amsawa da wannan sihirtaccen kallon da Abdallah yake mata,a hankali ta ɗan motsa bakin ta tare da cewa"Barka da safiya!'sai A lokacin ya ɗauke kansa daga tsumamman kallon da yake mata,tare da amsawa asaman laɓɓan sa kamar wanda akayi wa dolen amsawa,tashi tayi tsaye tana ƙoƙarin fita daga ɗakin,cikin miskilar muryar sa yace,"baki sanar dani dawowar Dije ba!'juyowa tayi batare da ta kalli cikin idanun sa ba, tace"to ya akayi kasani!'bai bata amsar tambayar ta ba sai ɗora mata da yayi da cewa,ki tabbatar kin samu keɓewa da ita yau,ina son sanin abinda ke tare da ita duk da cewa ina zatan Alkhairi,ki kula da kanki!'binsa kawai tayi da idanu tasan dai mutumin nan ba zai daina kasheta da mamakin sa ba gara kawai ta haƙura da ɗorawa kanta nazarin al'amarin sa,sauri tayi tabi bayan sa lokacin da taga ya sa kai ya fita daga ɗakin.


Yau kam har lokacin hira ta samu da inno,a cikin hakane ta samu damar gaya mata tana son zuwa gaida su Hajiya Babba da Hajjah,cikin kulawa inno tace"amma dai kin tabbatar kin sanar da mijinki ko?kai inno wai mijina!'cikin dariyar yarintar Bintun inno tace"au da meye idan ba mijinki ba?tura ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da zura dogon jijabin ta,bata cewa innon komai ba saboda ita har ga Allah haushi takeji idan inno ta ambaci Oga Abdallah da mijin ta, wannan mai shegen nunƙufurcin,itafa tana ji bata taɓa ganin dariyar sa ba,gara dai suyi su kashe gobarar da take gaban su kafin daga baya su san yadda zasuyi da Auren da aka ƙaƙaba musu basa so daga shi har ita,da wannan tunanin ta nufi ɓangaren Hajjah, wannan karon bata ko kalli sashen da ɗakin yake ba balle taji son zuwa gurin.

A hankali tayi sallama bayan ambata umarnin shiga,Hajjah ce zaune hakimce akan luntsumemiyar kujerar ta sai Dady Mansur da Dady Habib,wanda kallo ɗaya zakayi musu kasan cewa rayukan su duka aɓace yake,jikinta ne yayi sanyi da ganin su A cikin wannan yanayin sai kuma wani irin kallo da ta kasa gane ko na mene,da Dady Mansur yake mata,Hajjah ce tace"a'a Bintu ƙaraso mana kuma kin tsaya sai kace wata baƙuwa!'ta faɗa tana nunawa Bintu gurin zama kusa da ita,takowa tayi A hankali har ta zauna a inda Hajjah take nuna mata sai dai amai makon kan kujerar sai ta zauna ƙasan kujerar,cikin rawar murya ta fara gaida Hajjah kana ta gaida Dady Mansur da Dady Habib,shuru tayi yayin da zuciyar ta tashiga wani irin bugu wanda ta rasa na mene ne, Hajjah ce ta dubi Dady Mansur tace"na dai gaya maka karna kuma ji kaje wajen wani daga cikin ƴan uwan mahaifinka kayi musu rashin ɗa'a kaje kawai ka cigaba da addu'a Allah ya baiyana mana shi a duk inda yake,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka ya shirya mana ku baki ɗaya,amsawa sukayi atare wanda hakan yasa Bintu ta ɗago kanta dake sunkuye da wani irin sauri tare da bugun zuciyar da zai iya yi mata illah,sai dai kafin tayi tunanin wani abu har sun fita daga falon,bayan su tabi da wani irin kallo mai cike da razani da tsoro da kuma san gano wani abu da ya ƙulle mata kai.


Zubawa ƙeyar Bintu ido Hajjah tayi cike da tunanika bar katai,ita kuma wannan kome yake damunta? ta faɗa cikin zuciyar ta ganin yadda alokaci ɗaya duk ta firgice kamar wadda taga wani abin tsoro,ɗan dafa kafaɗar Bintun tayi dan san dawo da ita cikin hayyacin ta,a tsorace ta waigo ganin Hajjah ce yasa ta sakin wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyar da takasa ɓoyeta, Hajjah cikin nuna tsananin damuwa da halin da taga Bintun tashiga tace"Bintu lafiyarki kuwa koda wani abun da yake damunki?ta faɗa cikin nuna kulawar ta,da sauri Bintun ta girgiza kanta tare da cewa,dama gaidaki nazo nayi bari na wuce ɓangaren Hajiya Babba!'ta faɗa tana miƙewa tsaye, Hajjah tace"to da sauri haka ko ɗan hira bazaki tsaya kimin ba tunda ita waccen kasan da tayo muku ƙaura bacci bazai barta tayi hira ba!'batare da Bintu ta nuna san sanin wa take nufi ba,tace"ai zan kuma dawowa!'Hajjah tace"to shike nan ki gaida Innon da kuma mai gidan naki da kika fishi kirki!'kafin Hajjah ta kai ƙarshen zan canta tuni ta nemi Bintu A falon ta rasa,riƙe baki tayi cike da nazarin Abin da Bintu ta gani afalonta ya razana ta haka.


Tafe take dan zuwa sashen da Dije tayi mata kwatance,dan zuwa wajen Dijen,sai dai yanzu kwata kwata ba a nutse take kamar farkon fitowar ta ba,kafinta ta shiga ɓangaren Hajjah kenan,wai me yake faruwa da ita ne?ko dai zarar da ita ake son yi?me yasa yanzu take jin kamar mutumin nan yana kusa da ita?me yasa Muryar sa keyi mata gizo?wai wannan wane irin shu'umi kuma azzamin mutum ne,me yasa yake son cutar da ita ta hanyar son juyar mata da tunani? da wannan rikitaccen tunanin ta ƙarasa sashen da Dije take aiki,tayi sa a kuwa Dijen ce ta buɗe mata ƙofa,baƙaramin farin ciki Dije tayi da ganin Bintu ba,duk da cewa tana cikin ɗan yanayi na tsoron kar wani ya gansu,kama hannun Bintu tayi tana ƙoƙarin kaita cikin ɗakinta, Dady Mansur dake kallon su,cikin ɗaga murya
yace"ina zaki kai min wannan annobar? cikin sauri suka juyo yayin da Bintu jikin ta ya shiga rawa haka kuma hankalin ta ya kuma tashi da jin muryar da taji yanzu ta kuma sake jinta,wai waye wannan ɗin ne?muryar Dije ce ta katse mata dogon tunanin da ta waɗa akan wannan al'amarin dake son zarar mata da tunani,Dije tace"a'a yallaɓai dama inno ce ta aikota zan bata saƙon goro da na kawo mata tsara ba!'bai ce mata komai ba sai wani kallo da yayi musu su duka kana yayi ƙwafa tare da fita daga falon,kallon juna sukayi kafin Dijen ta kuma jan hannun Bintu da sauri suka faɗa ɗakin ta.


Cikin taka tsan tsan Dije ta gayawa Bintu duk yadda sukayi da uwar ɗakinta,sai dai ta ƙara mata da alwashin da taci da kuma alƙawarin da tayiwa Bintun duk suna nan sai ma abinda ya ƙaru,tace"Bintu dole ne mu tashi tsaye mu bada himma dan bankaɗawa waɗan nan mugayen mutane asiri,dole kuma musake yin ɗamara akan wadda mukayi da dan cimma nasara, Bintu da akwai mugaye da yawa acikin gidan nan don bazaki taɓa gane fuskar kowa ba,amma yanzu dole mu gane mu sakawa kowa ido,kar kiji cewa kin yadda da wane saboda haka bazaki bibiyi al Al'amarin sa ba, Bintu idan da hali Hatta inno da Hajiya Babba da Hajjah mu saka musu ido da duk wani motsin su,ba kuma wai na faɗi haka dan ina zarginsu bane a'a sai dai kin san Hausawa sunce idan allurar ka ta ɓata duba ta har cikin teku,nima zanyi nawa yin duk wata hanya zanyi bi dan ganin na samu abinda zan iya shaida wannan muguwar matar dashi!'Bintu tace"yauwa Mama Dije abinda zakiyi ƙoƙarin gano wa kenan ina ga sai mun fi saurin gano ko wacece A cikin gidan nan!'dije tace"Bintu ke dai kiyi abin da nace kiyi,saboda wannan aikin agurina yana da wahala kuma akwai hatsari,dan zata iya fuskantar cewa har yanzu ina nan akan bakana na yaudarar ta, kinsan wan can ma ganowa tayi da kanta,kuma da kike wannan batu ma Bintu idan kuma ba acikin estate ɗin nan take zaune ba fa,abin fa ba ƙarami bane saboda Ni har yanzu bata bani wata ƙofa da zan gane komai akanta ba, wannan matar ta iya takunta yadda bakya tunani shi yasa na gaya miki kar ki bar kowa da kuke tare hatta wannan nafisar ma ki kuma banƙaɗa cikin ta baza muka sa samun wani ɓoyayyan abu daga gareta ba!' Bintu tace"har Ammin Rahima?wani irin murmushi Dije tayi tare da cewa Bintu ke yarinya ce bazaki fahimci komai da nake son ganar dake yanzu ba,amma dan Allah kiyi abinda nace dake,na fiki daɗewa acikin gidan nan kuma tunani na da naki ba ɗaya bane,ko har yanzu baki yadda dani bane?cikin sauri Bintu ta girgiza kanta tare da cewa"kiyi haƙuri mama Dije ba haka nake nufi ba amma insha Allah zanyi abinda kikace fiye da yadda kike tunani!'dafa ta Dije tayi tare da cewa yauwa yariyar kirki, sannan ki dinga yi mana addu'a kinji domin komai baya tafiya dai dai sai da taimakon Ubangiji!'jikin Bintu ne yayi sanyi sai taji kamar ta faɗawa Dijen halin da take ciki a kwanakin nan sai dai kuma babu halin haka tunda har yanzu Dijen bata san komai akanta ba bata san ita wacece a cikin wannan gurɓatattun mutanen da suke son kawo ƙarshen suba,dan dole ta ƙirƙiro ƙaryar da ta sharawa Dijen tace"insha Allah inayi kema ki dingayi min addu'a mama Dije!'Dije amsa mata tayi cike da son ƙara mata ƙwarin gwiwa, duk da cewa ta fahimci cewa akwai abinda Bintun take ɓoye mata,amma dai ta ƙyaleta har zuwa ranar da zataji ta gamsu da ita A zuciyarta,sai da ta rakata har can waje kana sukayi sallama bintun ta nufi sashen Hajiya Babba cike da nazarin maganun Dijen.


Tun Bintu ba ta ɗaɗe da fita ba Anty Nafisa ta shigo ɓangaren innon,tunda ta tabbatar Bintun bata nan shike nan ta ɗorawa hanya idanun ta,tana son ganin shigowar Bintu, sai dai har ta shafe awa ɗaya babu Bintu babu alamar ta,to amma tayiwa kanta alƙawarin bazata bar sashen ba sai da mafitar damuwar ta,gashi ta kasa tambayar inno inda Bintun ta tafi,har innon sai da taso fahimtar kamar ba anutse Nafisan take ba,sai ta ɗan shiga yi mata nasiha kamar yadda ta saba yi mata alokuta da dama,a tunanin inno har yanzu wannan damuwar ce aranta ta rashin haihuwa,duk da ta ga abin yayi sauƙi yanzu sosai bakamar lokutan baya ba,da take yawan riskar Nafisan cikin wani irin yanayi na matukar damuwa,to da taga inno tana son ranfota ne yasa ta ɗan nutsu,sallamar Bintu yayi dai-dai da wata ɓoyayyar ajiyar zuciya da Anty Nafisa tayi,gaishe da ita Bintu tayi,daga nan tayi shigewar ta ɗaki ba tare da ta kuma kallon inda Nafisan take ba.

To ga dai biki kuma babu zanin ɗaurawa, Bintu ta dawo amma ta rasa hanyar magana da ita,tunda tasan cewa magar da zasuyi da Bintu ba ta mintuna bace,kuma maganar sirrice wadda ta shafi wani ɓangare na rayuwarta,to kuwa ta yaya zata iya yin wannan sirri inno tana cikin falon nan A zaune?tunanin tane ya tsinke lokacin da taji wayar inno na ringin,dawo da hankalin ta kan inno da ta ɗaga wayar tayi tana cewa to Alhaji gani nan zuwa!'runtse idanunta Nafisa tayi tare da yin hamdala ga Ubangiji abinda take daɗewa batayi ba sai idan takama,(sai dai kuma ba tasani ba wannan taimakon da ta samu daga Ubangiji ba na kowa bane sai na Bintu saboda Allah yana tare da ita akan niyar ta ta Alkhairi,da san taimakon bayin Allah)


Inno tace"to Nafisa zan je Alhaji na kirana kuma gashi Bintu ta shige ƙurya bare ki samu ɗan taya hira!'da sauri Anty Nafisa tace"kije kawai inno bari na bita ɗakin, na rasa me yasa har yanzu Bintu bata sake dani ba,ko dan bamu cika zama guri ɗaya bane oho mata,ta faɗa tana miƙewa dan ƙara sawa ɗakin Bintun,inno ma dake ƙoƙarin shiga sashen Alhaji Babba ta ƙofar dake cikin falon ta tace"to ina ga dai haka din ne yanzu sai kije ki rutsata dan kiji dalili!'cike da farin ciki Nafisa ta faɗa ɗakin Bintu wanda ko sallama bata samu damar yi mata ba, Bintu na tsaye jikin windon ɗakin nata,har yanzu tunanin ta yana akan muryar nan datake tai mata kai kawo a cikin kunnuwa, ta kuma ci alwashin sai ta nemo shi kowaye indai yana cikin estate ɗin nan,ga kuma babban aikin da Dije ta bata, ko tayata zata fara bincikar inno da Hajiya Babba da kuma Hajjah?ita dai tasan bata zargin ko ɗaya daga cikin su,to amma idan tayi la,akari da maganar fafi ɗinta sai taga cewa wannan fa ita ce shawara mai kyau kuma abar bi,tabbas Dije tayi dogon tsinkaye,shigowar Nafisan ce ta dakatar da ita daga tunanin ta,juyawa tayi tana kallon Nafisan cike da jin tsanar ta acikin zuciyar ta tare yin tur da mugun halinta,zama tayi tare da cewa Bintun zo ki zauna saboda maganar mu bata buƙatar tsayuwa!'

"A hankali ta ƙarasa kusa da Anty Nafisan ta zauna,shiru sukayi na wasu sakanni kana Anty Nafisa tace"Bintu kefa nake jira tun ɗazu kuma yanzu nazo kinyi min shiru!'to me zance dake yanzu?ta tambaye ta batare da wani shakka ba,me kike nufi ne Bintu?ɗan gyara zamanta Bintu tayi tare da ƙara yin ƙasa da murya tace"Anty Nafisa kin san yanzu duk shawarar da na baki ba zatayi kyau kamar ace nasan mafarin lamarin ba,amma duk da haka yanzun ma ba zan kasa ko mai a kan haka ba!'yauwa Bintu na san bazaki kasa yin kyakykyawan tunani akan matsala ta ba,kuma na gaya miki babu komai dana rufe miki da dawani abun kin san bazan ɓoye miki ba!'ta faɗa cikin san Bintu ta gasgata maganar ta,wani ɗan murmushi Bintu tayi wanda kana ganin sa kasan na yaƙe ne,kana tace"hanya ɗaya ce zaki bi dan mijin ki ya gaya miki abinda yake sirrin sa,hannu tasa ta ɗan shafa fuskarta kana taci gaba da cewa,in dai har kin san ya yadda dake ya kuma yadda bazaki taɓa cutar dashi ba,kuma da akwai amana da gaskiya a tsakanin ku to kawai ki tunkare shi kai tsaye ki tambaye shi,ina mai tabbatar miki da cewa indai yayi miki waɗan nan abubuwan dana lissafa to wallahi zai gaya miki batare da ya ɓoye miki komai ba!'shuru tayi ganin yadda Nafisan take mata wani irin kallo wanda kamar ma bata san tanayi mata shiba,can dai da ƙyar tace"Bintu kina da hankali kuwa ta yaya zan san duka waɗan nan abubu wan alhalin ban shiga zuciyar sa na gani ba,ban san meye a zuciyar sa game dani ba, ban kuma san wani irin kallo yake min ba, ban san wane irin zargi yake min ba? gaskiya Bintu ki sake tunani!'tsura mata ido Bintu tayi kana tace"Anty Nafisa ya akayi KIKASAN yana zarginki?bayan kuma kin ce baki san ta yadda za ayi kisan wane irin kallo yake miki a cikin idanuwan sa ba?tuni Anty Nafisa ta diririce gaba ɗaya Bintu yariyar cikin ta ta saka ta a kwana tamkar wadda take tuhumar ta da laifin kisa,ganin irin rikicewar da tayi ne yasa Bintu ta kuma tabbatar da zarginta tabbas a kwai Babban abinda Nafisa take ɓoyewa wanda kuma zai iya taimaka musu sosai cikin tafiyar su,kuma tayi alƙawarin sai ta faɗa mata kome taƙe ɓoyewa,yanzu zata bar ta da wannan sai kuma zama na biyu,miƙewa tayi tare da cewa,Anty Nafisa Ni zanje kiching ke kuma kije kiyi tunani akan shawarar da nabaki idan ta karɓu sai ki aikata ta,idan baki gamsu da ita ba,sai mu canja wata Kinga Nima sai na samu damar ƙara yin nazari,kinga dole sai kin yi haƙuri akan wannan aikin saboda ya ban banta da sauran ayyuka,su waɗan can na san komai shi kuma wannan sai dai nayi lalube,daga haka ta fita daga ɗakin batare da ta jira abinda Nafisan zata iya faɗa ba,ita ma tashi tayi jiki a saluɓe ta koma ɓangaren ta cike da tunanika iri-iri.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 43 ```


Tana shiga kiching ɗin ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ogan nata sanwa, sai dai gaba ɗayan ta bata jin ta dai dai saboda tunanin da ya cika mata ƙwaƙwalwalwa, ƙoƙarin ta kawai a yanzu gano me wannan muryar,duk da cewa yanzu duk wanda yayi magana ji take kamar waccan Muryar to amma da izinin Allah hakan ba zai sa ta kasa gano me ai nahin Muryar ba.


Wata tsawa shugaba azukyi ya dakawa Nanu, me kake yi haka ne?kasan wannan hanyar da ka biyo ba hanya bace me ɓullewa,me yasa baka tsaya akan wan can shirin namu ba, tabbas kayi gangan cin fallasa Muryar ka ga yarinyar nan,domin tabbas yanzu da abinda zata samu dama akanka ke nan!'ya ajiye maganar cikin wani irin huci na tsananin ɓaci rai da abin da nanun yayi,wanda aka kira da nanu yayi ƙasa da kan sa tare da cewa afuwa nake nema shugaba yanzu meye abinyi?babu wani abin yi nanu saboda ka nuna mana bamu da wani amfani a cikin wannan

Please Login or Register in order to submit comment