Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jaki da nisa ba a takai ce dai dalilin aurena da Umar inno ce dan Hajiyata ce ta fara kawo mata maganar a matsayin ta na ƙawarta, to dake Allah ya ƙaddara nice matar Umar dole haka ya aureni ba dan yana sona ba!'Bintu ina da matukar kishi na hauka san nan ina son Umar da arziƙin gidansu,shi yasa nake matuƙar kishinsa,a haka muka ja shekaru ba haihuwa bare ɓari,Ni kuma alokacin sai na fara jin tsoro kar Umar ya fara tunanin ƙara aure ko Hajiya Babba ta saka shi yayi aure tunda dama kamar bata karɓeni amatsayin suruka ba,wan nan dalili ne yasa nayi matuƙar sawa Umar ido fiye da yadda kike zato,a kwai wani aminin sa Sulaiman tunda mukayi aure da Umar da shi kaɗai nasan shi kuma nasan yana zuwa Yola wajen sa dan haka sai da nasa aka yimin bincike ko yana da ƙanne dan ina tsoron kar shima yace zai bashi ƙanwar sa ya aura tunda yanzu kowa neman inda zaiji daɗi yake, A lokacin sai akabani tabbacin cewa yana da ƙanwa guda ɗaya amma anyi mata aure,hakan ne yasa hankali na ya ɗan kwanta kaɗan amma kullum ina cikin fargabar kar Umar yaje ya gano ƴar kyakykyawar bafulata na ya auro min,dan haka kawai sai na ɗauki wani salo na sakawa Umar tsoron yin aure da fargaba azuciyar sa sai na dinga yawan mugayen kalamai da alwashi kala-kala akan kishiya,har agaban Sulaiman nasha rantsuwa duk ranar da Umar yayi min kishiya sai na kasheta sai dai nima akasheni, Bintu duk wan nan abinda nakeyi ashe a banza nakeyi,dan katsaham na fahimci yanayin zuwan Umar Yola ya canja yana zuwa duk weak end a maimakon duk sati biyu ko wata, san nan Sulaiman shima zuwan sa ya ragu ba kamar da ba, anan ne nayi hanzarin tashi tsaye da bincike.

"Hawayen da suka zubo mata tasa hannu ta share saboda tuno abin sai take ji tamkar yanzu yake faruwa,ta cigaba da cewa, bincike na ya tabbatar min da cewa,Umar aure yayi kuma ya ajiye matar a Yola,abinda ya kuma tayar min da hankali shine wai har ma matar tasa na ɗauke da ciki wanda zata iya aifuwar sa yau ko gobe,hankalina yayi matuƙar tashi saboda nayi mamakin yadda Umar ya shammace Ni har yayi aure yana shirin samun ɗa ko ƴa amma ban sani ba,sawa nayi a binciko min matar tasa ƴar wace mutane ce dan nasan irin matakin da zan ɗauka,amma amsar da aka dawo min da ita,ita ta kuma saka Ni cikin ruɗani wai ƙanwar Sulaiman ce,Ni da A kace min Sulaiman bashi da wata ƙanwa sai mai aure, to ina yasamo wata ƙanwar?ko dai sakota akayi ne?ƙarshe dai har da kaina saida nayi tattaki naje har cikin gidan Laila batare da tasan koni wacece ba, na kuma ganowa kaina tashin hankalin da ya hana Ni bacci ya hana zuciya ta sukuni ya hanani walwala cin abinci ya zama wahala agurina,saboda ganin turtsetsen cikin ta,tana rayuwa cikin ɗaula da jin daɗi, tunanin da ya fara faɗomin shine kawai nasa akashe Laila da ɗan uwanta harma da shegen cikin dake jikinta,tunanin hakan da nayi sai nayi ƙoƙarin kawar da abinda ke fuskata na barshi acan ƙasan raina yana cina,ban nunawa Umar ko mai ba,kamar yadda ya ɓoye min ban nuna masa na sani ba,sai dai kuma can gefe na koma nayi hayar haya killer waɗan da dama tun can mun daɗe dasu mutanen Hajiyata ne,su natura domin su kashe Laila da Sulaiman domin na tabbatar zaman sa a duniya bazaiyi min amfani ba,cikin daren suka bugo min waya cewa ai sun same ta da jaririya banyi wani tunani ba na basu umarnin sukashe su duka su ukun har jaririyar kar su bar kowa a raye,Bintu a cikin daren suka kuma kirana suka sanar dani sun kashe su duka dan haka na kwantar da hankalina,duk abinda nake yi inayin sa cikin taku dan alokacin ma ko ɗakin Umar banje ba ina ɗakina dan nasan da abinda na shirya.

Bintu tun daga wannan rana na samu salama a zuciyata da kwanciyar hankali, amma sai dai kash mijina shi ya fansheni da ninkin baninkin damuwar da nashiga, wallahi Bintu halin da Umar ya shiga alokacin har saida na fara dana sanin abinda na aikata saboda idan nace miki bana son Umar tabbas nayi ƙarya,tun daga lokacin yake ciwo a tsaitsaye damuwa ta rafkar dashi ta wannan sanadin ya haɗu da ciwuka kusan kala uku,

"A haka ne muka kwashi shekaru rabon dana ce miki Umar yayi dariya har na manta sai dai ban sani ba ko idan ya fita cikin ƴan uwan sa da iyayen sa,damuwar da yake ciki ita ta sani yawan damuwa akan abinda na aikata har inno da wasu da yawa suke tunanin ko damuwar rashin haihuwa ce na saka a raina,sai kawai na bari a hakan amma Ni a raina na san ba haka bane,ganin halin da nake cikine yasa Hajiyata tadamu ta tasani a gaba da cewa lallai sai na faɗa mata damuwata,banyi niya ko sha'awar gayawa wani sirrina ba,shi yasa kawai na canja labarin da ce mata,likitoci sun tabbatar min da cewa bazan taɓa haihuwa ba, Ni kuma shine nasa akayi masa asirin da bazai taɓa yin aure ba ko da yayi ma bazai taɓa haihuwa ba,kuma gashi hakan ya tabbata shi yasa nake nadama A yanzu ina ganin kamar zanje nasa a warware sihirin da nasa akayi masa!'alokacin Hajiya sai ta nuna min abinda nayi nayi daidai dan haka kar na sake na aikata abinda nake son aikatawa,idan dai har ba so nake asirina ya tonu ba,tayi min faɗan dan me ban gaya mata tuntuni mun san madafa ba, wallahi Bintu alokacin babu wan nan tunanin da burin a raina amma lokaci ɗaya Hajiyata ta ɗorani a hanya idanuna suka rufe ya zamana babu abinda nake nema sai dukiyar Umar ita kaɗai nake buƙata,dan kuwa tabbas huɗu bar mahaifiyata tayi tasiri a zuciyata fiye da yadda ita take zato,har ma sai burina yake son fin nata yawa,sai kuma gashi katsaham Allah ya kawoki,dan haka sai nayi amfani da wannan damar nayi duk abinda nayi ko nake kanyi,har zuwa yau dana baki labarin abinda Umar ya faɗa min wanda ban taɓa tunani ko zaton cewa Umar zai kawoni cikin zargin sa ba,dan ina da tabbacin cewa ban bar masa wata alama da zai iya gano abinda na aikata masa ba.


Ba zan iya kwatan ta muku takaici da tsanar da Bintu ta ƙara ninkawa Nafisa ba,wai yanzu wannan matar dake gabanta ita ce tayi sanadin rabuwar ta da iyayenta,itace tayi sanadin da mahaifiyar ta take can cikin halin da bata sani ba,ke nan Nafisa bata san inda mahaifiyar ta take ba?to idan hakane waye ya kuma kawo musu farmaki na biyu?kuma shi meye nasa dalilin?kuma taya akayi suka san Lailan?da kanta ta shiga ta shiga hasaso komai dake faruwa, tabbatas tana zargin mutum ɗaya ne yake aikata duk wan nan,a yanzu ta gano me wayar nan shine ya ɗauke mahaifin Abdallah kuma shine ya ɗauke nata mahaifan,kuma shine masarrafin wan can ɗakin,to amma me yasa yace,bai san inda mahaifiyar ta take ba,domin ta tabbatar shine ya kira wayar ta wan can ranar,to meye yake ɓoyewa ko yake aikatawa a wan can ɗakin? tabbas dole lokaci yayi da zata farmaki wan can ɗakin ko ta wane hali kawai dai fatan nasara take gurin Ubangiji.


Anty Nafisa bata katse mata tunanin taba har sai da taga dai Bintun dai bata da niyar dawowa cikin hankalinta,kana tayi magana a hankali tace"Bintu ya dai bakice ko mai ba!'sai alokacin Bintu ta kalli Anty Nafisa tare da ƙirƙiro murmushi tace"to ai ke nake jira ban ji ƙarshen ba tunda har yanzu ban san manufar kiba,shin kinyi na dama ne ko zaki ɗora daga inda kika tsaya!'tayi shuru tana jiran amsar da Anty Nafisa zata bata,cikin jan dogon numfashi tace"gaskiya Bintu da naso na haƙura ki nema min fafitar da zan samu na cigaba da rayuwata a gidan nan,sai kuma naga hakan ba zai taɓa yiwuwa ba,saboda duk daren daɗewa wata rana asirina zai tonu balle yanzu da Umar ya tabbatar min da cewa, sai ya nemo farin cikin sa a duk inda suke,dan haka shawarar da nayan ke kawai zansa akashe shi bakuma na buƙatar hannun ki a wannan karon,Ni da kaina zan sa su babe su kashe shi idan kuma zasuyi min kamar yadda sukayi min a baya to sai na kashe shi da kaina,ta faɗa tana miƙewa tsaye,Binta da wani irin kallo Bintu tayi,kana tace"kina ganin hakan shine dai-dai?kai tsaye ta bata amsa tare da ficewa daga ɗakin bata ƙara koda waiwayenta ba,


"A wannan karon dai Bintu ta aro jarumtar mijinta,dan kuwa sam bata shiga tashin hankali akan furucin Nafisa na kashe mata mahaifi ba,zuciyar ta ta tsaida guri ɗaya da kuma naiman taimakon Allah,ta ɗaga wayar ta da tun shigowar ta ɗakin ta saka recording ta naɗe duk maganganun Anty Nafisa,wanda take fata su zame mata hujja ko anan gaba,yanzu babu abinda idanunta ke tun kara da hasasowa sai ɗakin nan zuciyar ta nan kawai take hanƙoro ta ƙagu da son ganin abinda ake aikatawa a cikin wannan ɗakin,da wan nan ƙwarin gwiwar ta tashi ta fara abinda ya kamata dan ida kyakykyawan nufin ta a yau.


Tofa yau ake yin ta,muje nest page muji shin ko Bintu zatayi nasara a wan nan karon,shin daniyal zai ganowa ogah Abdallah gidan da su Hajjon suke,shin zargin Bintu zai tabbata akan inno kuwa,ina labarin Abigirl? Duk ku biyo NI domin dai anzo gun....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 47 ```



Abdallah yana fita daga gidan officce suka wuce shida Yahya,bai daɗe da shiga officce ɗin ba sai ga Dady jafar, murmushi Abdallah yayi yace"Dady kafi Ni busy yanzu naga alama, tunda gashi har ina yin kwana biyu ban ganka ba!'wani irin murmushi Dady jafar yayi wanda yake nuni da tsan tsan farin cikin da yake ciki,farin cikin da yake ciki baya rasa nasaba da yadda yaga rayuwar Abdallah ta fara sauyawa kuma ga alamu sun fara nunawa suna samun nasara akan abinda suka saka gaba,cikin murmushin da yakasa gushewa akan kamilalliyar fuskar sa,yace"to ai naga ƴata Bintu ta fansheni tana kula min dakai yadda ya kamata,godiya mara adadi da yarinyar kirki!'ga mamakin sa sai yaga wani ɗan matashin murmushi ya baiyana akan fuskar Abdallah,a hankali ya lumshe idanun sa tare da jinginar da kansa a bayan kujerar,haka nan ya dinga jin maganar Sayyid na dawo masa daki daki,(taƙi bani dama saboda tana da matukar kamun kai da nutsuwa hakan ne yasa ko fuskar da zan yi mata wasan banza ban samu ba)kalaman da suka burgeshi sukayi masa daɗin sauraro ke nan daga bakin Sayyid, Dady jafar ne ya katse masa tunanin sa da cewa,to Malam Abdallah ina sauraron ka kayi min bayanin nasarar da muka samu tare da cigaban da aka kuma samu,ka kuma bani labarin da kace zai matuƙar bani mamaki!'ya ƙarasa maganar cikin ƙara dai daita zaman sa tare da taro nutsuwar sa kan Abdallah,

"Cikin nutsuwa Abdallah ya gaya masa ko wacece bintu,cike da matsanancin mamaki haɗe da farin ciki,Dady ya taso ya rungume Abdallah tare da cewa,ikon Allah kaga ƘUDURAR ALLAH ko Abdallah, wato duk abinda Allah yaso tabbas sai ya faru, wannan abin akwai al ajabi amma ikon Allah ya wuce ga haka,!'Dady ya daɗe yana jin jina wannan ƙudura ta ubangi,yayin da soyayyar musulunci ta kuma kafuwa cikin ransa da zuciyar sa,ya kuma gasgata Allah da Manzon sa,ya kuma godewa Allah da ya kawo masa Abdallah cikin rayuwar sa da har ya zama silar zamowar sa cikin musulunci,hawaye ne ya shiga zubo masa saboda tsabar imani da tsoran Allah yace"Alhamdulillah alakulli halin, Allah na gode maka da wannan baiwa da rahama da kayi min Allah kashirya waɗanda suka ɓata, Allah ka ƙarawa Annabi daraja, Allah ka tsare zuciyoyin mu daga ruɗin duniya da ƙyaleƙyalenta ka kare mu daga faɗawa cin haram ka karemu daga cutar ƴan uwan mu,ka tsare idanuwan mu daga kallon abun da ba namu ba, Allah ya Ubangiji ka tonawa azzalumai asiri kasa suji kunya a duniya ka kuma sa su gane gaskiya ka shirya su idan masu shiryuwa ne!'amin Abdallah ya faɗa nima nace Amin Ya Allah,daga nan suka tattauna sauran maganganun da ya kamata Dady jafar ya sani,daga nan suka gangaro kan maganar Abigirl inda suka tsaida magana akan cewa zai sa aje ataho da ita,yayi wa ma aikacin su na can wanda yake kula da shige da ficen Abigirl waya ya sanar dashi zai sa azo ataho da ita,daga nan suka fara jiran zuwan sakamakon Samira.


Kamma lallan guri ne me cike da nutsuwa, sam babu yawaitar jama a agurin saboda gurine na manyan mutane waɗan da suke buƙatar sirri dan hakane ba kowa ake bari ya shiga ba sai isu-isu manyan,Samira da Alhaji Sama'ila suna daga cikin mutanen dake zaune cikin gurin a kuma keɓantaccen guri,ga yanayin damuna da muke ciki wanda shine ya kuma ƙawata gurin da ƙamshin ƙasa dana furanni,zaune suke a kan ƙawatattun kujerun da suka zagaye gurin gaban su ɗan tebur ne wanda yake ɗauke da kayan sanyi kala-kala, Alhaji Sama'ila ya dubi Samira wadda ta nutsu ta kasa taɓa komai saboda ƙagauta da tayi taji abinda ta fi buƙatar ji a yanzu, murmushi yayi tare da cewa'haba My dear ki ɗan sha wani abu mana duk kinbi kin sawa kanki takura,ɗan murmushi tayi tare da ɗaukan drink ɗin da ya zuba mata,bata son ya fahimci wani abu atare da ita, shi yasa tayi saurin kawar da ɗokin dake kan fuskarta da yanayin ta,bata kuma ce masa komai akan abinda ya kawo su ba, sai da yagama jan ranta kana ya ɗan gyara zaman sa, tare da cewa,


Samira zan fara da baki labarin asalin dangantakar dake tsakanin mutane huɗu,dan ki fahimci yadda abin yake tun farko, Alhaji Balarabe da Alhaji Nasir da kuma Alhaji Shamsi sai Alhaji Kabiru,asalin su aminai ne waɗan da suka haɗu ayawon fatauci,wato neman kudi,daga baya ne bayan kowa ya samu abinyi sai duk suka watse,amma abin Allah shine A lokaci ɗaya suka kuma haɗuwa da junan su,acikin garin Abuja ke nan,daga nan ne suka ɗora da amintar su wadda har tafi yadda suke a baya, dukkanin su babu wanda bai tara dukiya ba,sai dai amma arziƙin Alhaji Balarabe na daban ne acikin su,lokacin da suka fara ankara cewa Alhaji Balarabe yayi musu zarra,shine lokacin gina ESTATE, estate shine mafarin komai shi ya haddasa komai,tun daga lokacin ya zamana abokan nasa sun fara gane abinda yake zuciyar su na tsananin hassada da ɓakin ciki,abin yayi matuƙar tasiri a zuciyar su,amma basu taɓa nunawa Alhaji Balarabe ko mai ba hasalima nunawa suke sun fishi farin ciki da duk wani ci gaba da zai samu,tun daga lokacin suka fara haɗuwa su biyu suna mitin ɗin yadda zasu dinga cutar Alhaji Balarabe ta wajen kasuwan cin su,to amma dake shi zuciyar sa cike take da aminci da kuma kyautatawa talakawa,sai hakan bai girgiza komai a cikin dukiyar sa ba,duk kuwa da irin yadda mahaifina suke yagar dukiyar Alhaji Baba tamkar babu gobe,sai daga baya suka kuma samun karuwa saboda sun gano manufar su ɗaya da ɗan uwan Alhaji Baba wato Alhaji Hashir,dan haka sai abu ya kuma cin uban na baya ha inci suke masa batare da arziƙin sa na raguwa ba saima karuwa da yake samu Ako da yaushe,mutum ɗaya ne yasan abinda suke aikatawa shine Alhaji shamsi saboda shi babu hannun sa acikin duk wani abu da suke aikatawa Alhaji Baba,A lokacin yaso faɗawa Alhaji Baba abinda ke faruwa sai kuma yayi tunanin idan yayi hakan tabbas zasu iya cutar da shi da kuma Alhaji Baba,tunda ya fahimci cewa sunyi nisa acikin san duniyar su,idanun su ya rufe,tabbas idan yayi ƙoƙarin dakatar dasu ko ya sanar wa da Alhaji Baba zasu iya yin komai A yadda ya fahimcesu,sai kawai ya ƙyalesu tunda har yanzu babu abinda ya ragu ko ya samu tawaye daga dukiyar Alhaji Baba sai ma arziƙin nasa da yake kara haɓaka.


A haka lokaci yaja suna kan wannan ƙadamin har zuwa yanzu da salon tafiyar ya sauya,


Abin ya samune ta sanadin wani da ɗaɗɗen waje da Alhaji Baba ya saya domin ayi masa kamfanin robobi wajen kuma gini yake buƙata mai ƙarko,shi yasa kullum ta Allah sai Alhaji Baba yaje wajen, har aka gama ginin ma aikatar nan akazo kan hakar rijiyar da zata dinga bada ruwan amfani a cikin ma aikatar to anan ne ko mai ya faru a lokacin daga shi sai ɗan sa ABUBAKAR saboda yawanci tare suke zuwa irin wannan guraren,dama ance komai da sanadin sa sai kiga idan Allah yace da rabon ka to sai kiga sanadi ko mai ƙankantar sa ya kawo maka rabonka to hakan ce ta faru da Alhaji Baba ɗan abu ƙarami kuma mara tushe da dalili shine ya kawo masa wan nan rabon, indai ba rabo ba to haka kawai babban mutum zai zauna yana tona taɓo? haƙar rijiyar da aka fara batayi nisa ba wan nan ne dalilin da yasa Alhaji Baba tsugunawa yana taɓa ƙasar wajen yana ɗan tottonawa ramin badan wani abu ba sai dan nishaɗi,taɓo abin yayi a hannunsa hakan ne yasa ya ƙara tura hannun dan san ganin ko meye aaboda santsin da yaji abun ke dashi,abu kamar wasa sai gashi yana ta zaro abu wanda shi dai bai fahimci ko menene ba, Abubakar yace"Alhaji Baba me kake cirowa ne haka sai kajiwa kanka ciwo!'ya faɗa yana tsugunawa shima gaban ramin da bashi da zurfi, Alhaji Baba yace"ina tunanin dai wani babban dutsene kaga idan na ciro ai narage musu aiki ko? Abubakar ya kuma cewa'haba Alhaji duba kaga fa kana ciro abu da wahala kace zaka ragewa waɗanda zasu ciro shi da masarrafi aiki!' Alhaji Baba dai bai ce masa komai ba yaci gaba da tagagarin ciro mulmulen dutsen da ya kasa zaroshi saboda santsin sa,Abubakar babu yadda ya iya haka ya naɗe hannun rigar sa ya shiga taya dattijon nasa aikin da ya rikitowa kansa,kamar wasa Abubakar ya janyo wani ƙarfe dake can gefe irin na masu aikin haƙa,yace"Baba bari mu tona da wannan muragewa kanmu aikin da ka ɗauko mana!'Alhaji Baba yace"Abubakar bazaka gane ba jinake kamar wannan abun ba dutse bane saboda yana da santsi idan kayi la'kari da yadda yake saɓulewa daga hannun mu!'to bari na haƙo da wannan sai muga wane alherin ne yake kiranmu!'ya faɗa yana cusa abun dan zaƙulo abun daga cikin ƙasa,cikin sakanni saiga abun mai girma kamar ma dai dai ciyar boll,sai wani irin ƙyalli da sheƙi yake yana haske musu idanu,cikin ma daukakin mamaki Abubakar yace"Baba wan nan ai dimon ne,abu mafi ƙololuwar daraja!'sunkuyawa yayi da sauri ya ɗauke shi a hannun sa tare da nufar wajen da suka ajiye mota,cikin wani irin zafin nama yake takawa har ya isa motar ya buɗe ya saka dimon ɗin kana yace"Baba shigo mutafi da sauri!'shiga Alhaji Baba yayi tare da yiwa Abubakar ɗin wani irin kallo kana yace"bangane abinda kake nufi da wannan rawar jikin ba?sai da Abubakar ya tada motar ya ɗauki hanyar barin kamfanin kana ya ja ajiyar zuciya tare da cewa Alhaji Baba baka San akan wannan al'amarin yanzun nan sai a harbe mu ba? Ai yanzu ganin dimon ɗin nan tashin hankali ne a wajen mu dan duk wanda ya san dashi to wallahi sai an biyomu ankashe mu!'jijina kai Alhaji Baba yayi tare da cewa maganarka haka take kuma nima nasan da haka,da farko nayi tunanin farin cikin samuwar dimon ɗin agaremu ne ya hanaka nutsuwa, murmushi Abubakar yayi tare da cewa haba Baba kamar kamanta waye habunka kuma duk arziƙin da muke dashi sai na hangi wani,Alhaji Baba cikin tunanin yadda zasuyi da wannan dimon ɗin yace"ban mantaka ba habu,amma bana son samuwar wan nan abu ya sauyaka daga kan kyawawan halayyar ka dana riga na sanka da ita saboda shi wannan ɗin samuwar ƙololuwar arziƙine darajar sa ta wuce tunanin ka saboda wan nan dimon ɗin babban ne kuma kasan yanzu me shi a kullum shike neman daɗi!'baba ya akayi kayi saurin gane darajar dimon ɗin? Alhaji Baba yace"haba habu karfa kamanta kasuwan ci nane fa a baya kuma ido ba mudu ba ai yasan kima!ɗan murmushi yayi batare da ya iya cewa mahaifin nasa ko mai ba,sai can bayan sun kusa shiga estate Alhaji Baba ya dubi ɗan nasa yace"Habu bai kamata mu shiga estate batare da mun yanke shawarar yadda zamuyi da dimon ɗin nan ba!'Abubakar yace"nima abinda nake tunani ke nan amma ina ga ɓoyeshi zamuyi kar mu bari kowa yasan da shi idan ba haka ba kuwa tabbas duniya taji za a iya zuwa har gida a farmaki rayuwar mu akan sa!'Alhaji Babba ya jinjina kai tare da cewa amma kasan sai na gayawa ƴar Agadez ko!'naji Baba Amma kasan ta yadda zaka faɗa mata ba tare da ka bari wani yaji ba dan wan nan abun sirrin junan mune bayan zune lokacin bayyana shi ba,daga nan sukayiwa junan su raɗar inda zasu ɓoye dimon ɗin,babu wanda yasan inda suka ajiye shi sai su biyun nan bayan Allah da ya haccesu baki daya.

Samira taja wani gauran numfashi tare da cewa to ku kuma ya akayi ku kasan da dimon ɗin? Alhaji Sama'ila yayi dariya tare da cewa,to ai wan nan ba Abune na mamaki ko wahala ba,yadda akayi mukasani kuwa shine ɗaya daga cikin mune yaji wato Nura ɗan Alhaji Hashir,alakacin da Alhaji ke faɗawa Hajiya Babba to shine yaji ya faɗa mana,amma ko ita Hajiya Babba bata san inda wan nan dimon yake ba,sai dai abinda ya ɗaure mana kai yadda akayi kwana kaɗan da faruwar al'amarin aka nemi Abubakar aka rasa tare da ɗan sa na biyu mai suna abdulraman,kuma tunda Aka ɗauke su har rana irin ta yau babu wanda yayi kukan rashin su ko cikiyar su,sai dai Alhaji Baba da ya fara cuta wadda har ta kaishi ga kwanciyar wasu watanni a asibiti!kinji abinda ya faru kuma yake kan faruwa kuma kinji akan abinda ake ta gumurzu akan sa!'


Baƙaramar dauriya Samaira tayi ba gurin ƙoƙarin hana kukan dake idanun ta kufce mata ba,wani irin azababban tausayi ne ya cika mata ƙirji Allah sarki Alhaji Baba yana tare da maƙiyan sa bai sani ba,kalaman Alhaji Abubakar sun fi taɓa mata zuciya,wato abinda ya faɗa kuma ya guje musu tun A lokacin shine ya faru akan sa,cikin dabara ta goge hawayen da ya ɗan fara zubowa daga idanuwan ta,kana tace"gaskiya wannan al'amarin da ɗaure kai yake to waye ya ɓoye Abubakar?shi kuma ɗan nasa yana ina yanzu? Alhaji Sama'ila yace"ɗan sa dai babu labarin inda yake, shi kuma abubakar tunda muka rasa shi hankalin kowa a cikin mu ya tashi, ko da yaushe cikin nema da binciken inda yake muke ba tare da kowa ya sani ba,kuma har yau ba musamu damar sanin inda yake ba!'miƙewa tsaye yayi tare da cewa to Samira lokaci yayi bari na wuce kar suzo suna jirana!'tace"shike nan Alhaji sai munyi waya zanyi tunanin abin da ya dace!'yauwa sai mun haɗu daga haka ya fita daga gurin yana fita itama Samira ta wuce, officce ɗin Abdallah inda suke dakon jiranta..


Wannan karon Abdallah ya kasa daure abinda yake ji acikin zuciyar sa,dan haka kana kallon ƙwayar idanun sa zaka gane yanayin da yake ciki na azabar raɗaɗin zuciya,yana kuma tausayawa waɗanda suka aikata wannan mummunan kuskure ga mahaifinsa,miƙewa yayi ba tare da ya iya cewa dasu komai ba,ya tattara kayayyakin sa ya bar officce ɗin,Samira ta kalli Dady jafar tare da cewa, Dady anya kuwa babu wata matsala atare da Oga Abdallah naga yana yawan shiga tashin hankali akan wan nan aikin namu?shima kallonta yayi yace"baki san komai bane Samira,amma yau zan gaya miki abinda baki sani ba saboda amanarki da gaskiya da yadda kika tsaya mana akan aikin nan cikin nuna hazaƙarki da ƙwarewarki ta aiki,bai saurara da maganar da yake ba har sai da ya tabbatar wa da

Please Login or Register in order to submit comment