Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shuru yana mai zubawa kyakykyawar fuskar Bintu idanu,sunkuyar da kanta tayi saboda yadda kallon nasa ke tasar mata da duk wata tsiga ta jiki da kasala,yayin da su Alhaji Nasir suka shiga share zufa wanda basu san ma ta inda take zubo musu ba,haka kuma gaba ɗaya falon su aka sawa idanu Baba Ahmad da dai sauran ahlin Baffa Hashir duk tsumayi suke suji abinda tosffin nasu su kuma suka aikata,dan kuwa ga alamun rashin gaskiya nan tsaf akan fuskokin su,shima dai Alhaji Baba ido ya sawa ɗan uwan nasa da kuma aminan sa guda biyu mafi kusanci agareshi,Dady Mansur ne yace"ku muke sauraro ku wakilta ɗaya daga cikin ku idan kuma bazaku iya fada ba muna da hanyar sanin komai ba tare da mun wahalaba!'Abdallah yace"Dady inaga kawai a kunna wayar!"Dady jafar ne ya miƙowa Dady Mansur wayar dake hannun sa,karɓa yayi tare da kunnata cikin sakanni sai ga muryar Alhaji Sama'ila na fitowa tun daga farkon fara aikin da Samira tayi na sirri har zuwa inda ya sanar da ita komai akan diamon,wayar tana tsayawa falon ya rude da surutai daga masu Allah wadai sai masu fatan shiriya iyalan su kuwa kuka suke sosai da irin wannan tozarcin da Baffa Hashir da Baba nura suka janyo musu,gaba ɗaya sai sukaji duk sun mozanta acikin mutane,da ƙyar Alhaji Baba ya tsawatar falon ya kuma ɗaukar shuru na wasu ƴan sakanni kana cikin wata irin murya wanda take nuni da tsananin halin baƙin ciki da takaicin da yake ciki yace"sannu Nasiru sannun ku Hashir!''' ɗan shuru yayi saboda wani abu mai ɗaci da ya tokare maƙogaran sa,daga bisani yaci gaba da cewa, abokai na da ƴan uwana sune suka zama masu ha intata muna fukaina masu san ganin bayana,hannu yasa ya ɗan goge ƙwallar dake son fallasa halin da zuciyar shi take ciki,kana ya cigaba da cewa nasan akan wannan dalilin ne na rasa gidan jinina ɗan da babu kamarsa sai dai kwatankwacin sa zan iya yafe komai amma banda wanda ya rabani da ɗan da kuma jikana,amma ku kuje babu komai rayuwace,na barku da Allah tunda yanzu ma ba dabarata ce ta fallasaku ba ƙarshen makircin kune yazo,dan Allah ba ya barin mai zalinci,na gode Allah da rahamar sa agareni na gode Allah da ya kawo min Abdallah cikin zuri'a ta!'ya faɗa yana sakin wani ɗan murmushi na samun sukuni da yayi azuciyar sa a sakamakon yawan ambatan Allah.


Baffa Hashir cikin tsananin jin kunya da nadama wadda take neman karya garkuwar jiki da ruhin sa, yace"ɗan uwa ina mai neman gafarar ka da kafemin cin amanar da nayi maka duk da cewa ban cutar da rayuwarka ko wani daga cikin ahlinka ba, amma naci dukiyar ka kuma naso aikata babban kuskure akan abinda ba nawa ba ba kuma na ɗana ba,a yanzu ina mai cikin tsananin nadamar abinda na aikata,tabbas na kasance maci amana mai saka Alkhairi da sharri,ka yafe min ɗan uwana ina cikin wani hali na na rashin samun yafiyar ka!'ya ƙarasa maganar da rushewa da wani matsanan cin kuka wanda har saida Alhaji Baba ya runtse idanun sa,daga nan suma suka samu damar neman gafara da yafiya magiya da kukan da suke shi ya tabbatar wa da jama ar gurin cewa sunyi taubatun nasuha,dan haka Alhaji Baba yayi gyaran murya tare da cewa haƙika kunyi kuskure a cikin tafiyar da al'amuran duniya da rayuwarku,kamar ba kuyi karatuba kai Hashir kamanta da hadisin da mahaifina yake yawan yi mana maimaicin sa,cewa Annabi Muhammad (s.w.a) yace"duk jikin da ta ginu da haramun ba zata shiga aljanna ba,haka kuma duk mai annami manci ba zai shiga aljanna ba,kai kuma gashi a wannan gaɓar duk sai gashi ka aikata waɗan nan laifukan,dan haka ina mai jan hankalin mu anan da mu gujewa cin haram komai ƙan ƙantar ta,mugujewa ha'inci,da cin amana,domin Allah baya yafe laifin da akayiwa bayinsa,daga ƙarshe ina mai tunatar daku muhimmancin gaskiya da rikon amana,na yafe muku Allah ya yafe mana baki ɗaya,amma ku sani duk wanda yake aikata wani mummunan laifi to ya dinga tunawa da mutuwa san nan kuma duk abinda yake yi Ubangijin sammai da ƙassai yana kallon sa,ko da ka mutu asirin ka bai tonuba to tabbas a lahira za a nuna maka dukan aiyukan ka,da kunyar lahira kuwa gara ta duniya,zanso idan ina aikata mugun aiki asirina ya tonu ko hakan zai iya zama sanadin shiriyata, Allah yasa mu dace ya kuma karemu daga ruɗin zuciya ya tsare imanin mu!'da Amin suka amsa yayin da jikkuna su kayi sanyi zuciyoyi suka mutu hankula suka fara dawowa jiki,kiran sallar da akayi shi ya dakatar dasu daga ci gaba da gabatar da al'amuran da suke faruwa,Alhaji Baba yace"ya kamata muje muyi sallah ina yaso sai mu dawo mu ɗora daga inda muka tsaya idan akwai wani abun kenan!'Abdallah ne ya fara miƙewa idanun sa suna shawagi akan Dady Habib da Hajjah gani yake kamar zasu iya guduwa dan haka kawai sai yace" da Dady Mansur da Dady jafar su tafi suyi Sallah da Dady Habib saboda yanayin jikinsa su sun fahimci abinda yake nufi,yayin da wasu sukayi tunanin ko Dady Habib ɗin bai da lafiya ne,a hankali aka shiga watsewa daga falon, Abdallah yana fitowa ya kira wayar Safwan yace"su ke waye gaba ɗaya estate din Nan kar su bari ko ƙwaro ya fita,har gefan Hajjah bai bari ba sai da ya tabbatar da tsaron wajen.

A bangaren Anty Nafisa kuwa tunda ta fita sai taji bata da kwarin gwiwar shiga ɓangaren ta,tunanin makomar ta a wajen Abba Umar shine abinda ya da baibaye ƙwaƙwalwarta,jikin ta asanyaye haka ta shiga falon tana mai jin tsananin faɗuwar gaba akan abinda zai biyo bayan tonuwar asirin ta,

Duk da cewa kowa ɗokance yake da ya keɓe da iyalan sa,tsakanin Abba Umar da Fafi,amma hakan suka hakura suka nufi masallaci bayan sunyi alwala da tunanin ai yanzu komai ya wuce babu abinda zai kuma rabasu da iyalansu idan ba mutuwaba,lokaci lokaci zaka ga murmushi kan fuskar Abba Umar wanda yake nuni da tsananin farincikin da yake ciki ga matar shi Laila ga gudan jininshi Bintu babu abunda zaice da Allah sai godiya Alhamdulillah masha Allah.


Su inno dai da Hajiya Babba su sukayi ma sauƙin baƙi,Hajiya Babba kamar yadda ta saba tayiwa inno kara da alkunya ita tabarwa ragamar karrama surukar tata tare da ririta ta tamkar basu taɓa yin suruka acikin ESTATE ba,Hajiya zulaihat ma tana manne da Laila,dan ko ɓangaren ta bata koma ba,Bintu kuwa gatan har nema yake yayi mata yawa sai dai duk da haka ta kasa sukunin rashin ganin Oganta Abdallah maganin kukanta,wata irin kewar sa takeji tare da tsananin bege,wanda har kawo yanzu ta kasa fassara hakan da cewa ƙauna ce mara algus,

Bayan idar da sallar ne mazan duk suka hallara a falon Alhaji Baba,yayin da ya bada umarnin akawo abinci a fara ci kafin ci gaba da tattaunawa,a lokacin ne kuma ya saka waya yayi kiran Alhajin Nafisa ya sanar dashi yana buƙatar ganin sa tare da Hajiya ladidi,kowa yana sabga cikin walwala amma banda Dady Habib wanda bugun da zuciyarsa take yi tafi ƙarfin a misalta,yanzu yafi kowa shiga tashin hankali tabbas da ya samu hanya sai ya gudu dan yana ganin guduwar ita ce kadai mafita
agareshi da kuma samun sauki a gareshi.


Hajja kam tun komawarta bangaren ta take zawo har sai da Nana karama tace"wai Hajja lafiyar ki kuwa naga sai sunturin banɗaki kike?bata iya bawa ƴar tata amsa ba sai komawa da tayi ban dakin dan ta ga alama zaman cikin sa sai yafi mata sauƙi,a kwai abinda take ɓoyewa wanda babu wanda yasan shi kuma tana ganin lallai lokacin tonuwar wannan sirri yayi shi yasa abun ya haɗe mata bata jin cewa duk sanyin zuciyar Alhaji Baba zai iya yafe mata wan nan al'amari,a yanzu kaico da nadama take,shin tayaya zata iya fuskantar Alhaji Baba da wannan sirrin wanda tasan cewa koda su Abdallah sun san wancan to tabbas basu san wannan ba,yaya duniya zata kalleta da sauran ƴaƴan ta idan sukaji abinda ta aikata,dole tasa ta ci gaba da zaman banɗakin domin tun yanzu ta fara jin kunyar haɗa idanu da iyalanta,

Oga Abdallah kuwa mai gaiya mai aiki duk yadda ya kai ka san yin juriyar hakura da ganin Bintu abun gagara yayi, cikin rashin sukuni ya nufi ɓangaren inno,yana shiga falon yaci karo da Dije zata shiga kiching inda suke hada hadar dafa abinci,tsayawa tayi tare da cewa,a'a yallaɓai ko kana buƙatar wani abunne? cikin ɗan basarwa da farincikin da yaji na samun dama yace"ki bawa Bintu ruwa ta kawo min!'daga haka yayi saurin faɗawa falon sa,wani ɗan murmushi tayi tare da shigewa ɗakin inno inda Bintun suke tare da su Laila da Hajjo,yafito Bintu tayi,suna fita ta miƙa mata ruwan da ta ɗauko,ba ta haɗa da komai ba,dan tasan ba wai ruwan yake buƙata ba,tace"maza jeki kaiwa mijinki yana cikin falonsa!'ai kafin ta kai ga rufe bakinta tuni ta tsinci Bintu abakin kofar falon Abdallah,riƙe baki tayi cike da dariyar yarintar Bintun.

Kamar an jehota haka ya ganta a gabansa kasan cewar tun shigarsa bai zaunaba,zuba mata idanunsa masu saukar mata gajiya yayi,haka nan ta dinga jin wani irin sanyi har cikin kashinta sunkuyar da kanta tayi tana jin wasu ƙwallan da bata san daga ina suke ba,ɗan ware idan sa ya kuma yi akanta,kana a hankali ya riƙota kamar wanda yake tsoran kar yaji mata ciwo,ɗagowa tayi ta shiga yi masa wani irin kallo daya fara sashi kokuwa da numfashinsa, cikin wani irin salo da shauƙi ya haɗe ta jikin sa,tare da ɗora fuskarshi saman kanta,zame ɗan kwalin kanta yayi ya shiga shinshina gashinta kamar wanda ya samu turare,Bintu cikin wata irin kasala ta kuma lafkewa cikin faffaɗan ƙirjinsa,can kasan maƙoshi ta tsinkayi Muryar sa yana cewa my Bint,sai kuma me kike bukata? Ummm faɗa min!"ya faɗa cikin cusa kanshi a wuyanta yana goga fuskarsa da ɗan gemun sa akan uyan nata, cikin wata iriyar kasala da yake saukar mata ta shiga goga fuskar ta a kan ƙirjin sa tare da cewa"Ni kam ka gama min komai bani da wata sauran damuwa,ka cika min burina ka dawo min da farin ciki na, wannan ma kaɗai ya isheni!'ɗan murmushin gefan baki yayi tare da cewa a'a faɗa min dai ina sauraren ki da akwai wani farin cikin da kike bukata!'girgiza kanta ta shiga yi jikin ta yana kuma mutuwa da salon da ogan nata yake mata,kamar daga sama taji bakin shi cikin nata wata doguwar sumba yayi mata tare da cewa hmm Bint ki duba mana bakya bukatar wan Nan?a ruɗe ta kuma girgiza masa kanta,ya kuma sumbatar idanunta yana cewa da wannan ma,ya sumbaci goshinta da wannan ma,daga nan ya zarce da yiwa bakinta wata irin tsotsa tamkar wanda ya samu sweet.....

Mu haɗu a falon Alhaji Baba zama na biyu

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 59 ```



"Kiran da yaji a wayar sa dake soke gaban rigar sa ita ta fara dawo dashi hankalin sa,amma duk da haka bai saki Bintu ba,a hankali ya zare bakin shi daga nata,tare da zuba mata ido,hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya,leƙa fuskar ya shigayi tare da cewa duk bakya buƙatar waɗan nan eye Bint?janye jikin ta tashiga yi a ƙoƙarin ta nasan guduwa,domin ita sam bata gane inda maganarsa ta dosa ba,riƙeta yayi ganin zata gudu yace"baki bani amsa ba,ko sai anjima zaki gaya min?da sauri ta daga kanta kamar zatayi kuka, murmushi yayi tare da sumbatar dogon hancinta,kana ya saketa,sai da taje bakin ƙofa kana ta ɗan dakata tare da juyowa tace"kayi sauri ka fito kazo falon Alhaji Baba saboda ina buƙatar ganin farincikin Ammi da Oga Abdallah!'tana gama faɗa tayi waje da gudu fuskarta dauke da murmushi,zubawa kofar idanu yayi hannuwan sa zube cikin aljihun shi,ɗan shafa cikinsa yayi dan shi sai yanzu ne ma yake jin yunwar gashi kuma su kaɗai ake bukata a falon Alhaji Baba,kafin ya samo mafita sai ga Bintu ta dawo hannun ta ɗauke da plat wanda yake shaƙe da jelof ɗin shinkafa da uban kifi wanda kusan rabin abincin kifine,sai ƙamshi take gwanin da ɗi da burgewa,har tazo gaban shi ta janyo dan Centre ɗin tsakiyar falon ta ajiye yana kallonta,sai da ta ɗago taga kallon da yake mata,sai kuma ta tura baki tare da cewa wai miye ne haka da kallo?bai bata amsa ba sai zama da yayi yana maida duban shi kan abincin,cikin kasalar da ganin ta ke saukar masa yace"abun burgewa mata tana son mijinta yaci abinci kamar kinsan yunwa nakeji!'kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita kan cinyar sa tare da cewa ke kinci abincin ne?girgiza kanta tayi,bai ce komai ba ya shiga miƙa mata abincin bayan ya ɗebo a spoon,Bata son yawan yi masa gardama hakan yasa ta buɗe bakinta ya shiga bata abincin,sai da ya tabbatar ta koshi kana shima yaci,yana gamawa ya ɗaga ta yana cewa muje Bint kar muga dakarun Alhaji Baba akanmu!' dariya tayi kana ta zagaya hannun ta ta saƙalo hannun shi,a haka suka fita dan zuwa falon Alhaji Baba.


Kamar yadda akayi a farko haka yanzu ma kowa ya hallara har da ƙari,saboda yanzu da akwai Alhjin Nafisa da kuma Hajiyar ta Ladidi,kowa ya nutsu,shigowar Abdallah da Bintu kawai ake jira,yayin da Hajjah take cikin wani irin hali duban farko zaka san cewa a kwai tsoro da tarin fargaba a tare da ita, Anty Nafisa ma tun da ta ga zuwan baban ta da kuma Hajiyar ta cikinta ya kuma durar ruwa,cike take da tashin hankalin abinda zai biyo bayan abinda ta shuka,


Hannun su rike dana juna sukayi sallama,wanda su sun manta a yanayin da suke,sai da Bintu taga kallon da Inno take watsa mata kana ta ankara,da sauri ta zare hannun ta daga nasa,can wajen Ummin ta ta nufa ta zauna tare da kwantar da kanta a kafadar ta,shi kuwa Abdallah daga nan gefan Dady Mansur da Dady jafar ya zauna,Alhaji Baba ne ya bawa Abdallah umarni da ya buɗe taro da addu'a,bayan sun shafa addu'ar ne Alhaji Baba ya dubi Abdallah tare da cewa,har yanzu kai muke bi Abdallah meye abu na gaba da zaka gabatar mana dashi?wayar Safwan ya kira yace"ku shigo dashi!'baiyi minti ɗaya da kashe wayar ba,akayi sallama a ƙofar falon tare da sako kai alokaci ɗaya.


Kaf mutanen falon sai gasu a tsaye,daga mai murza idanu sai mai zaro su dan san da ɗa tabbatar da abinda idan nasu yake gani,A hankali Alhaji Baba ya shiga takowa har zuwa inda Dady Abubakar yake tsaye cikin kyakkyawar shiga ta kamala kai baka ce shine wanda yayi tsawon shekaru ba tare da yasan inda kansa yake ba,kama hannun sa yayi cikin nasa jikin sa har rawa yake gwanin tausayi, zuba masa idanu yayi sai ga hawaye shar suna tsartuwa daga idanun Alhaji Baba jarumin namiji,sai ga Hajiya Babba ma tazo saboda ta kasa daurewa tsayawa daga nesa ga Ni take kamar zata iya yin saken da zata kuma rasa ɗan nata,ita kanta Hajiya zulaihat alkunya tayi amma idanun ta tamkar zasu faɗo ƙasa saboda kallon Abubakar kuka take yi mai tsanani wanda yake tafe da wani irin kewa da shauƙi,duk ƴan uwansa dake zaune a falon babu wanda yake son ko ƙifta idanun sa yayi dan kar ya buɗe yaga babu Dady Abubakar,Abba Umar ne yazo da sauri tare da cewa, Alhaji Baba yayane fa ko baku gane shiba?bai sauraren su ba ya tafi ya rungume ɗan uwan sa tare da sanbatun farin cikin sake kasancewar sa acikin su, cikin ƙanƙanun lokaci falon ya dau sautin kukan mutane,Hajiya Babba kuwa kama su tayi gaba ɗaya shida Umar ɗin ta rungume ta kasa cewa komai sai wani irin murmushi wanda yake haɗowa da wasu zafafan hawaye,shafa kawunan su takeyi kamar baza ta sakesu ba,A hankali Alhaji Baba ya zaresu daga jikin ta shima yayi musu kamar yadda tayi,duk kan su sun rasa bakin magana sai zubar hawaye ,cikin nutsuwa yajasu suka koma inda yake a zaune daga nan yabawa sauran ƴan uwan sa damar raɓar Abubakar ɗin dan nuna farin cikinsu na dawowar sa,cur cur haka zaka ga duk wanda suka rungumi juna ya koma yana hawaye kai abun dai gwanin tausayi,rarrafawa yayi har gaban inno matar da ta so shi ta nuna masa kauna tamkar ita ta haifeshi,ɗora kanshi yayi bisa ƙafafunta,hannun ta tadora a kansa tana mai cigaba da zubar hawaye,A hankali tace"Abubakarina Allah ya nufi ganawar mu,yau ƙudura ta hadu da irada,ƙudurar Allah ce take ta wanzuwa acikin wannan zuri'a tamu,dama inaji ajikina zuwan Bintu da Abdallah cikin ESTATE ɗin nan haskene da warwarewar duk kanin matsalolin mu,na daɗe inajiran wannan rana mai ɗumbin tarihi a garemu, Allah ya karemu ya kuma shiga tsakanin nagari da mugu!'ɗagowa yayi cikin san kwantar musu da hankali,yace"inno ku daina kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya nufemu da sake haɗuwa!'A hankali Bintu ta tashi taje har gaban Ammi ta kama hannun ta ta miƙar da ita,kowa sai ya maida kallonshi kanta,bata tsaya da Ammi ba sai a gaban Dady Abubakar,hannun shi ta kama ta haɗa dana Ammi idanun ta cike taf da hawaye tace"duba nan Dady kar kamanta da macen da ta ɗauki tsawon shekaru idanun ta na tsiyayar da hawayen rashin ka da na gudan jininta,Ammi kenan macen da tashaƙi ɓacin ran da ya kusa illata rayuwarta, duk saboda kai,Ammi ki kawar da fulako ki tarbi Dadyn mu,saboda abinda ke zuciyar ki ya wanku,abinda ya tsaya a ƙahon zuciyarki ya faɗa!'kuma takawa tayi taje ta kamo hannun Abdallah, tana zuwa ta haɗa dana Ammi da Dady Abubakar cikin hawayen tausayin su,tace"ya Abdallah inaso kayi farin ciki kamar yadda kasani, kaji irin abinda naji lokacin da ka haɗani da Ummina da Abbana,kaima yau gaka ga Dady ga kuma Ammi,ta ɗan kalli Ammi da ta zuba mata ido tana san fahimtar inda zancan BINTU ya dosa tace"Ammi ga nan Ya Abdallah shine ɗanki da suka ɓace lokaci ɗaya da Dady,wata irin zabura Ammi tayi sai kuma ta koma tare da riƙe hannun Abdallah kamar zata ɓallashi, Allahu Akbar tabbas naji ajikina kullum fatana kenan abinda nake tunani akan ka ya zama gaskiya, Alhamdulillah,yau haske ya baiyana duhu ya yaye,yau ranar farin ciki ce a cikin wannan ahlin,ta faɗa cikin zubar da wasu zafafan hawaye wanda zamu iya kiran su dana farinciki,


Dady Habib kuwa tamkar zararre haka ya koma yana zaune amma duba ɗaya zakayi masa kasan cewa baya hayyacin sa,cewa yake yi nayi sake nayi sake yau gashi ƘUDURAR ALLAH ta baiyana,Dady Mansur dake hankalce da shi da Dady jafar sune kawai suka fahimci halin da yake ciki ga kuma maganganun da yakeyi,wanda basu ji abinda yake cewa ba,amma dai tabbas alamu sun nuna Dady Habib yana cikin wani yanayi na tsaka mai wuya,kowa a cikin falon nan farinciki yake, amma banda waɗan da suka shuka suke jiran girbewa,idan ka duba zuciyoyin su tamkar ƙabari haka suke,su kuwa su Alhaji Hashir sun shige cikin masu taya ɗan uwan su murna da samun ɗan sa da jikokin sa,tunda su sun samu salamar yafiyar wanda suka yiwa kuma nasu ƙullin makircin bai kai na su Dady Habib ba, wannan dalilin ne yasa suka samu nutsuwar zuciya.

A hankali Abdallah ya rungume mahaifiyar sa ya haɗa da Dady,Rahima da ta ƙaraso itama ta rungume ɗan uwanta,ɗago idanunshi yayi ya ɗorasu kan rigimammiyar fuskarta kamar yadda yake faɗa,nuni yayi mata da ta share hawayen fuskarta, murmushi ne ya suɓucewa Ummi da sauran waɗan da suka kula da abinda Abdallah yayiwa Bintu,ita kuwa Bintu umarnin mijinta tabi tasa hannu ta goge hawayen da suka ɓata kyakykyawar fuskar ta,zama yayi ya zaunar da Ammi da Dady Abubakar,kana ya koma mazaunin sa,fuskar sa ɗauke da wani ɗan maƙalallan murmushi,shuru falon ya kuma ɗauka yayin da zuciyar Dady Habib ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, zufa kuwa tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan zafi.


Abdallah ya buɗe baki zaiyi magana kenan, sai Dady Habib ya riga shi cikin yanayin fita daga haiyaci da tashin hankali na birnin kunya, yace"me zakace? me kuma yayi saura?kai dai wan nan yaro bakaji da kyauba,na tabbata dama zaka zama annoba arayuwata shi yasa tun farko naso wan can shegiyar ta kashe min kai,amma sai ta munafunceni saboda wata manufa tata,to gashi nan dai itama bata tsira daga tarkonka ba, wallahi bazan ɓoye muku ba na tsaneka kai da mahaifinka da wannan tsinanniyar yarinyar me kwana ido biyu,duk kece kika jawo komai!'ya faɗa yana nuna Bintu da kamar zai je ya rufeta da duka,a tsorace kowa yake kallon Dady Habib,Alhaji Baba kuwa bakinsa buɗe da tsananin mamaki yake duban ɗan nasa,haka jama ar da basu san komai akan abinda ke faruwa ba, Abdallah kuwa waya ya yiwa Safwan tare da bashi umarnin a shigo da Abigirl,ci gaba yayi da kallon Dady Habib da ya kasa zama sai muzurai yakeyi yana kuma faɗar maganganun da tun ba a fahimta har mutane suka soma fuskantar inda tashin hankalin nasa ya dosa.


Safwan ne yayi sallama ya shigo tare da Abigirl wadda tayi firi firi da ita kana ganin ta kasan cewa alhaki na biye da ita,tsakiyar falon Alhaji Baba ya zaunar da ita,kana ya juya ya koma inda ya a fito,kowa sai hankalin sa ya dawo kan Abigirl ita kuma hankalinta yana kan Dady Habib da ya zuba mata ido kamar wanda yake son aikamata da wani saƙo na gargaɗi,kawar da kanta tayi ta maida kan Abdallah da ya farayi mata magana cikin nutsuwar sa ta ko da yaushe,yace"kamar yadda na gaya miki ranar ne bana so kiyi min gaddama ko kuskure acikin abinda nake son sani daga gareki,nasan kin san abinda zai iya biyowa baya akan rashin bani haɗin kai da zakiyi,dan haka inaso ki faɗi komai da komai da kika sani akan yadda kika sameni, da yadda kika raine Ni da kuma manufarki akaina!'daga haka yayi shuru tare da maida kallon sa can ɓangaren da Bintu take,yayin da kuma ɗaukacin mutanen dake falon suka maida hankalinsu kan Abigirl, wadda ta zubawa Dady Habib ido,shi kuma yana maida mata da kallon gargaɗi, harma ya manta abin da yagama faɗa yanzu cikin fita hayyaci,kawar da kanta tayi daga gareshi tare da share hawayen da suke ta rige rigen sauka kan fuskarta,Dady jafar ne yace"ke muke sauraro!'duban shi tayi cikin saddaƙarwa tace"zan faɗa,zan faɗi duk wani abu da nasani,amma dan Allah karkuyi min komai,kubarni na koma garin mu bazan kuma waiwayar garin nan ba, ko da me maƙwaftaka dashine!'Dady jafar yace"idan har kika faɗi gaskiya kuma waɗan da kika aikatawa laifi suka yafe miki,to babu abun da za ayi miki,dan haka muna sauraranki!'


SHEKARA TALATIN da suka gabata,

Sunana Abigirl Adebayo ina zaune acikin garin Abuja nida mijina pastor David,tun da mukayi aure bamu taɓa haihuwa ba,tun bamu damu ba har muka fara nuna damuwar mu afili, mutane suka fara fuskantar halin da muke ciki,wala agida ko choch kullum addu'oin mu shine Allah ya bamu haihuwa,sai dai abin yaci tura shuru kamar ba roƙo muke ba,har ta kai da cewa na fara bin manyan bokaye da matsafa,amma duk abin da nakeyi mijina David bai sani ba,dan Ni nafishi damuwa da rashin haihuwar mu,mahaifiya ta ita ta kuma ƙara iza mun wutar san haihuwa saboda huɗu bar da tayi min wanda a da sam ba tunanina kenan ba,tayi min nuni da yadda David yake da arziki,ta nuna mini cewa idan ban haihuba,bazan taɓa samun abinda nakeso daga David ba,tace"min ai yanzu dan ban aihu bane yasa baya sakimin kuɗaɗe masu yawa,amma duk randa na samu baby to zanyi arziƙi ta sanadin baby,huɗubar ta tayi tasiri gareni,hakan ne yasa na kuma tashi tsaye gurin neman aihuwa ba dare ba rana,a kuma cikin lokacin ne komai ya faru,a ranar da bazan manta da ita ba,naje gurin bokana yake sanar dani Lallai sai na samo ƙaramin yaro na raine shi tsawon shekara talatin sa an nan zan samu abinda nakeso wannan shine laƙanin da bokana ya bani,kuma shine dalilin da yasa na taho ina tunanin hanyar da zanbi dan samun

Please Login or Register in order to submit comment