Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

part ɗinta a rufe gashi kuma yau da dare ne za'a kai shaida gurin Alhaji, kuma yau ne kwanan Maimun ya ƙare, shiyasa ma Afnan ta rufe nata part dan ta ƙudurtawa ranta ba zai kwana a part ɗinta ba.

Muby kuwa tun da ya ga kiran Alhaji ya san me yake nufi, jiki a sanyaye ya ɗaga wayar yana mai sallama tare da gaishe shi.

Cikin faɗa Alhaji ya ce
"Ai ka san ba gaisuwarka nake nema ba, kai ake jira har yanzu baku fito ba ne?" Sai da Muby ya daidaita natsuwarsa kafin ya ce "Zuwa anjima kaɗan zamu fito"

"To yayi sai kun iso" Cewar Alhaji yana katse wayar.

Tun da Alhaji ya yanke wayar Muby ya kasa koda tashi daga kan bed ɗinda da yake, agogon da ke hannunsa na gold ne ya duba ƙarfe takwas da rabi na dare, zumbur ya miƙe yana mai buɗe wadrop ya ciro wasu haɗaɗɗun kaya, irin na sarakuna masu adon flowers red a gaba rigar, sai wata alkyabba da kayan ta fito da shi, cikin sauri ya saka dan lokaci na neman ƙurewa, shi kam be san yanda zata kaya ba, babu wadda ya kwana da ita duk cikinsu, daga ƙasa ya fara jiyo maganar Maimun kamar tana masifa, cikin hanzari ya feshe jikinsa da turare, tare da kafa wata arniyar hula me sheƙi, a parlourn ya sami Mubina da Maimun ana gardama, a tsawace ya ce "Lafiya haka? an cika mun kunne da surutu"

Rusunawa Mubina tayi cike da girmamawa ta ce "Saƙo ne daga Gimbiya, wai baza ta samu zuwa ba amma ta bani wannan na baka"

Mamaki da haushi ne ya dirsa a zuciyarsa amma sai ya cije yana faɗin "Meye a cikin ledar?"

"Nima ta ce na kawo ne kawai bata sanar da ni ba" Mubina ta faɗa kanta a ƙasa.

"Ajiye a nan ki tafi"

Cewar Muby da ke kallon Maimun, ta wani haɗe fuska tun ɗazu take son ganin abin da ke cikin ledar amma Mubina ta ce baza ta gani ba.

Mubina na fita Maimun ta rarumo ledar tare da yagawa, farin zanin gado ne ƙal me kyau sai ƙamshi ke tashi, sai kuma wani abu kamar jini cikin farar roba, zaro ido Muby yayi ganin abin da ke ciki, lallai yarinyar nan wato ita basirar ta kenan.


Maimun da bata san amfanin kayan ba sai ta fara ɓata fuska tana ƙunƙuni, "Bani nan ki je ki shirya zamu tafi gida"

"Gida kuma, me zamu yi a can?" Kayan da ke hannunta ya karɓa yana mai haurawa sama ba tare da ya amsa mata ba.

Ganin haka yasa gabanta fara dukan uku-uku duk a zatonta maidata gida zai yi.


Koda suka isa can gidan ma har Alhaji na ƙoƙarin tashi dan ya gaji da jira shuru, bayan sun gama gaisawa ne parlourn ya ɗauki shuru, dan wannan karon harda wasu Dattijai su biyar sai mata masu shekaru su huɗu, da kuma Mommy har da me martaba da Alhaji a gefe, cike da kunya Muby ya fito da zanin gadon ya aje a tsakiyar parlourn, Mommy kam kawar da kai tayi dan tsananin kunya, ɗaya daga cikin matan ne ta buɗe ledar tare da zube zanin gado guda biyu shane-shane da jini, wata irin algaita Dattijon da gefen Muby ya busa nan take gidan sarautar ya ɗauka, duk da cewar dare ne, amma kowa na jiran sakamako, idan har aka ji shuru yana nufin ba'a dace ba, idan kuma aka ji anyi busa yana nufin dacewa, kamar daga sama suka ji an ƙara wata busar, nan fa kowa ya shiga mamaki, dan sun san cewa Gimbiya dai Yarima ya riga da ya gama aiki, amma gashi anyi busa, sosai Alhaji babba yaji daɗin abin da ya faru, bayan kowa yayi shuru ne Me martaba ya ce "Masha Allah amma ina ita Gimbiya?"

Sunne kai Muby yayi kafin a hankali ya ce "Bata jin daɗin jikinta ne"

"To Allah yasa Alkhairi ne" Cewar me martaba, gaba ɗaya ɗakin aka amsa da Ameen.

Sai a lokacin Maimun ta fahimci abin da ke wakana, nan fa ta fara sunne kai har tana rufe fuska da mayafi.


Ƙarfe goma suka isa gida, dan haka ya nufi part ɗin Afnan dan yau kwananta zai fara, Maimun kuwa kamar zata yi hauka, haka ta shige part ɗinta tare da banko ƙofar, mintuna biyar yana buga ƙofa amma shuru, a lokacin Afnan ta jima da bacci, Mubina da itama daga baccin ta tashi ne ta fara jin buga ƙofa, da sauri ta fito, tana buɗe ƙofar taga mutum tsaye har yana ƙoƙarin komawa, a tsawace ya ce "Tun tuni ana buga ƙofa amma kin kasa tashi ki buɗe" Haƙuri ta fara bashi tana sunkuyar da kai, kota kanta be bi ba ya haura sama, a steps suka ci karo da Afnan tana ƙoƙarin sauko, wasu rikitattun kayan bacci ne ke jikinta pink masu masifar taushi, wandon da kaɗan ya wuce mazaunata, sai wata fingilar riga da ta ɗan tsaya mata a ƙugu me ƙaramin hannu, na shanunta sun wani tsaya cirko-cirko, gashin kanta ta kame ta baya sai rito yake, jikinta ya wani kyau har sheƙi yake, ƙamshin turarensu ne ya haɗe guri ɗaya nan take daɗin ƙamshin ya baje steps ɗin har ƙasa, dogon tsaki ta ja har tana rufe ido, a hankali ta fara motsa lips ɗinta cike da jin bacci ta ce "What the heck?"

Kyawawan idanunsa ya lumshe jin abin da ta ce, ya ma rasa wanne hukunci zai yi mata, "Are you talking to me?"

Ya tambayeta yana damƙe hannunta da ƙarfi, "Wasshhhhh...., yes i'm talking to you, sai kuma me ya faru? ka tashi mutane suna bacci, ni ba'a tada ni idan ina bacci" Ta faɗa cike da tsiwa tana ƙwace hannunta.






*GOBE IN ALLAH YA KAIMU AKWAI GASA TSAKANIN TEAM ƊIN YARIMA, DA TEAM ƊIN GIMBIYA, SO GASAR ZA'A YITA NE DOMIN TANTANCE MASOYAN YARIMA DA MASOYAN GIMBIYA, IDAN HAR AKA SAMU GEFEN DA AKA FI YAWA TO INSHA ALLAH A WANNAN GEFEN ZAMU ƘARA MUSU ƘARFIN GWUIWA, SANNAN AKWAI KYAUTAR FREE PAGES HAR UKU GA WAƊAN DA SUKA LASHE GASAR, LOKACI 8:00pm DAIDAI*



*GIDAN MULKI*

*By*


*Asmeetar Hydar*






P. 8




..........
Hannu ya sa zai janyota tana ganin haka ta haura sama da gudu, bayanta ya bi suka fara tsera sai zagaye ko'ina suke, duk ta gama gajiya har tana neman zamewa, shi ko Muby mamaki ne ya kama shi ganin ya kasa kama ta.

Da gudu ta sauko ƙasa ai kuwa ya mara mata baya, tana ganin haka ta fice daga parlourn, nan fa tsere ya fara kamar me wasan doki haka ta koma, gaba ɗaya sun gama hargitse wajen da ƙarar gudunsu, masu tsaron kam basu ma san ana yi ba.

Maimun da ta kasa bacci saboda tsabar kishi ne ta fara jiyo ƙarar takun mutane, da sauri ta fito, cikin tsoro-tsoro ta buɗe ƙofar tana leƙo kai waje, abin da ta gani ne yasa ta jin wani mugun baƙin ciki ya ƙara darsuwa a ranta, hankalinta be ƙara tashi ba sai da taga shigar da ke jikin Afnan, ga wani kyau da ya bayyana gareta, ita Muby ne ma ya bata mamaki fiye da Afnan ɗin, kamar zata yi ihu haka ta nufesa cikin ɓacin rai ta shige tsakinsu tare da raba hannayenta, Cakkkk suka dakata suna kallonta, haɗe fuska Muby yayi dan ganin yanda mata biyu na son raina masa hankali, tsalle ɗaya yayi ya damƙo Afnan yana mai tallafota sama duk ta shige masa a jiki, kusan sanƙarewa Maimun tayi da ganin abin da Muby ke yi, ko kallon inda take be yi ba ya nufi hanyar part ɗinsu, Afnan kuwa sai ƙara narke masa take tana wani shinshini gefen wuyansa, ɗan leƙo kanta tayi ta kalli Maimun, sai kuma ta kashe mata ido ɗaya, wani ƙololon baƙin ciki ne ya haɗe mata a zuci, wai dama suna son juna ne ko kuma tsabar jaraba ne, to imma jaraba ne ni meyesa be yi mun haka ba, ganin tunanin zucin ba zai ceceta ba ne yasa ta koma ciki da sauri.


Tana shiga ta danna kiran Hajara, har sai da wayar ta kusan yankewa kafin ta ɗaga, "Ina kika saka wayar ne? sai kira nake shuru" Cewar Maimun.

Tsaki Hajara ta ja me sauti kafin ta gyara kwanciya dan bacci take, cikin muryar bacci ta ce "Kamar ya? so ɗaya kika kira ni kuma be katse ba na ɗauka, ina bacci na me daɗi kin tasheni me yake faruwa ne, ina Yarima?"

"Yana gidanku" Maimun ta bata amsa.

"Okay faɗamun abin da ke faruwa" Hajara ta tambaya dan ta san dole da wata a ƙasa.

Duk abin da ya faru a ranar sai da Maimun ta kwashe ta sanar mata, har abin da ya faru a daren yau.


Cike da jin bacci Hajara ta ce gobe zata zo gidan su yi magana, a haka suka yi sallama.


Muby be dire Afnan ko'ina ba sai tsakiyar prlourn, yana sauketa ta wani haɗe fuska tana yamutsa lips "Ban yafe ba taɓa jikina da kayi"

Ta faɗa tana haurawa sama da gudu, da kallo ya bi jikinta, ganin yanda komai ke motsawa, saurin kawar da kai yayi yana mai kwanciya kan kujera me zaman mutum uku, Afnan na shiga ta dannawa ƙofar key tare da zubewa kan bed ta fara maida numfashi, sai yanzu take jin baushin kanta, da yanda ta biye masa.



Haka washe gari tun da ta farka sallah bata koma ba, ta jima a zaune tana lazimi kafin ta sauko ƙasa sanye cikin hijab ɗinta, dan ita macece me son hijab, bata yawaita sakin jikinta irin haka ba sai idan tana ra'ayi, Muby da dawowarsa daga masallaci kenan yaga mutum tsaye ta wani kafesa da ido, "Malama lafiya?"

Cikin iya taƙama da gadara ta fara tafiya kamar bada ita yake ba, "Ke wai me kika taka ne? a duk lokacin da nake yi miki magana sai ki yi kamar bakya ji, an faɗa miki ina son magana da ke ne?"

Dakatawa tayi da tafiyar tare da juyowa a hankali, "Idan har baka son magana da ni, sai ka sakeni dan na tsaneka"

Gimtse ido Muby yayi da ƙarfi dan ya ji zafin kalmar, amma kasancewar namiji ne marar son raini yasa bai nuna ba, "Idan ina da halin rabuwa da ke zan rabu da ke, dama umarni ne ya sa nake zama da ke, amma na kusa auro zaɓin raina"

Murmushin takaici Afnan ta yi kafin ta ce "Idan ka fasa ƙara aure sunanka be cika Mubarak ba" Hannunta ya damƙe da ƙarfi tare da murɗawa, ƙara ta saki tana cije lips dan zafin da ya ratsa ta, a rayuwarta bata son abin da ya taɓa lafiyarta, cikin alamun jin zafi ta ce "Sake min hannu"

"Idan ba haka ba? ki ƙwace mana ai kina taƙama da mulki, me zai hana ki jarraba"

Juya fuska ta yi tana mai cigaba da cije lips, sosai yake matse hannun kamar ya samu sa'ansa, ita ko Afnan ta kasa bashi haƙuri ga wani raɗaɗin da hannunta ke yi, Muby kuwa a ransa ya ƙudurta ba zai sake hannun ba har sai ta bashi haƙuri.

Kusan mintuna uku a haka idanunta sun cicciko da ƙwalla, dan yanzu ji take kamar hannun ba a jikinta yake ba, jin buɗewar ƙofa ne yasa su maida kallonsu kan Mubina da ke fitowa daga ɗakinta, da ƙarfi yayi jifa da Afnan ƙasa ya haura sama cike da taƙama, jin zafin kayen ne yasa ta sakin ƴar ƙaramar ƙara tana dafe west ɗinta da ke zugi, ƙarasowa Mubina ta yi tare da kama ta "Sannu Gimbiya" Mubina ta faɗa cikin tsoro-tsoro, hawayen da ya zubowa Afnan ne ta share tana mai faɗin "Bana son taimakonki, me ya fito da ke ma?"

"Allah ya baki nasara dama masu gyaran part ɗinki ne zan rabawa kowacce aikinta" Mubina ta faɗa a tsorace, ko kallonta Afnan bata yi ba ta shige kitchen tana dafe bayanta, ruwan ɗumi ta ɗora a ƙayataccen tukunyarta me kyau da tsada, sannan ta zauna kan haɗaɗɗiyar kujerar da ke gurin jiran ruwan yayi zafi, tun da ta zauna take tunanin gida da kuma hanyar da zata bi dan raba aurennan, a halin yanzu wata irin masifar tsanarsa ke ƙaruwa a ranta.

Lokacin da haske ya fara har ruwan yayi zafi, a Flacks ta juye tare da nufar sama, da sauri ɗaya daga cikin masu aikin wadda ita ce ke gyara parlourn ta ƙaraso tana ƙoƙarin ɗaukar Flacks ɗin da ke hannun Afnan, wata irin razananniyar tsawa ta daka mata wadda ta sa gaba ɗaya masu aikin hallara jikinsu na rawa, cike da ɓacin rai gami da nuna isa ta ce "Wannan ya zama na ƙarshe idan har ba aikin da aka saka mutum ba, bana buƙatar yana shiga wanda be shafe shi ba, daga yau kowa aikinsa zai yi ina fatar kun gane" Cikin girmamawa su ka amsa da eh, Mubina ce ta karɓi Flacks ɗin suka nufi sama, ɗaya daga cikin masu aikin ne ta taɓe baki kafin ta ce "Ikon Allah nifa wannan gadarar da take yi a haka Yarima ke zama da ita?"

"Koma yaya ne ai ba damuwarki ba ce, kawai aikin da ya kawo mu shi ya kamata mu yi ba gulma ba" Cewar ɗaya daga cikinsu tana barin gurin.



Misalin ƙarfe tara Mubina ta gama haɗa komai na girki, tare da jerewa kan dianing.

Lokacin Afnan har ta fito sanye cikin atampa riga da siket me ɗan banzan kyau, ta sha ɗaurin ɗankwali me steps tare da jan shi ta baya, gashin kanta kuwa ya kwanta kan goshinta, ƙamshin turensu ne ya haɗu guri ɗaya, sarai taji fitowarsa amma tsabage mulki ya hanata ko kallon inda yake, shima yana cikin shadda fara ƙal me kyau da laushi sai black hula me zanen sarauta, ya wani irin kyau kamar wanda ya kashe arna, sajen fuskarsa da gashin kansa kuwa sun ƙara masa kyau, amma fuskar nan a haɗe kamar yanda Afnan ta haɗe fuska.

Kan dianing su ka zauna lokaci ɗaya amma babu wanda ya kalli wani, cikin girmamawa masu aikin ke gaisuwa, daga Yarima har Gimbiya babu wanda ya amsa, ganin haka ne yasa suka bar gurin, ɗaya ce kawai me serving abinci ta tsaye tare da fara haɗa musu, indomie ce wadda ta sha kayan ciki sai ƙamshi ke tashi a can gefe kuwa kunun gyaɗa ne wanda ya sha madara, kasancewar Afnan na son kunun gyaɗa ya sa Mubina ke yawan yi mata shi.

Bayan ta gama zuba musu ne ta fara zuba coffee, cikin biyayya ta aje tare da barin parlourn, tun lokacin da suka fara cin abincin kowa ke ɓata fuska kamar waɗan da abincin be yiwa daɗi ba, duk da cewar ba ita ta dafa ba amma yaji daɗi tun da ranar kwananta ne, Muby baya cin abincin masu aiki amma yanzu dole zai fara saboda ba a gida yake ba, a gida ne Ameera ke yi masa ko kuma idan Mommy zata yiwa Me martaba sai ya ce ta yi har da shi.

Ba wani abinci ta ci ba ta tashi tare da barin gurin, da kallo ya bita sai yaga ta ƙara masa kyau, be jima ba shima ya fice daga parlourn.


A ɓangaren Maimun kuwa tana ganin Muby ya fita gidan ta shirya tare da ficewa itama, gurin bokanta suka koma ita da ƙawarta Hajara, zaune suke suna jiran fitowarsa daga ƴar ƙaramar bukkarsa, ta baya-baya ya fara fitowa har ya zauna, yana ƙyalle wata irin dariya, murya kamar ta gardawa ya ce "Inda ma baku wahalar da kanku gurin zuwa nan ba, saboda wadda ku ke yi dan ita a yau ne zata bar gidan Yarima, kuma a yau ne aurensu zai mutu" Bokon ya ƙarasa maganar cikin bushewa da dariya, kamar Maimun zata yi tsalle dan farinciki ta ce "Amma ka ce mana aurensu ba zai mutu ba"

Cikin tsawa bokon ya ce "Na faɗa miki ba'a mana tambaya anan, kawai naku saurare ne"

Haƙuri suka fara bashi, sai da ya gama buga ƙasa kafin ya ɗago cikin mummunar fuskarsa ya ce "Bincike na ya nuna min cewa, zuwan da Gimbiya ta yi ƙasar nan, ta wulaƙanta wata matashiya, to wannan matashiyar ce zata yi sanadiyar raba auren Yarima da Gimbiya, dan haka ku tashi ku tafi" Jikinsu Maimun na rawa suka bar jejin cike da farinciki marar misiltuwa, tun da ta dawo gida take zuba ido dan ganin zuwan matashiyar da aka ce amma shuru, har yamma ta yi babu labarin komi, kiran da tayiwa Hajara kuwa yafi hamsin daga ƙarshe ma kashe wayar Hajara tayi.


Biyar na yamma na bugawa Afnan ta fara jin wani masifaffen ciyon kai, haka kawai gabanta ya fara faɗuwa amma ta rasa dalili.

Gashi Muby shuru tun lokacin da ya fita, har faɗuwar gaban ya fara bata tsoro, dan sosai ƙirjinta ke sama da ƙasa, tashi tayi daga kan bed ɗin ta shige toilet dan sakar ma kanta ruwa, ta jima sosai kafin ta fito ɗaure da ɗan ƙaramin tawul, tun daga harabar gidan take jiyo hayaniya wanda idan ba kunnuwanta ba ne, muryar Muby ne da Ashwan amma abin da yafi bata mamaki shine, bata taɓa jin muryar Muby haka ba, duk masifarsa da izzarsa be taɓa ɗaga murya haka ba, komai nasa in cool voice yake yi, koda ma ace ihu zai yi, to cikin sanyin murya zaka ji kasancewar ba mutum ba ne me son hayaniya.


Share zancen tayi tana mai cigaba da shafa mai, har ta gama tare da saka wata doguwar riga wadda daga sama ta kame ƙasan rigar kuwa ta baje, sosai kayan suka yi mata kyau sky blue ne sai hula red ai kuwa shigar ta haɗeta, musamman da ta ɗaura wata red akyabba kai sai ta fito tamkar Sarauniya, amma fa har yanzu surutun take ji, dan haka harabar gidan ta nufa domin ganin abin da ke faruwa, tsoro ne da fargaba gami da tashin hankali ya bayyana kan kyakykyawar fuskarta.


Muby ne da Ashwan sai Maimun, duk sun rirriƙe shi kamar wani me aljanu, babu abin da yake furtawa sai "Wallahi ku sake ni yau sai ta bar gidannan, bana tsoron ɓacin ran kowa, da na zauna da ita gara na kashe kaina"

"Subhanallahi...." Shine abin da Afnan ke furtawa a fili, jin furucin kashe kai da Muby ke faɗa, lallai a yau ne ta tabbar ya tsaneta fiye da yanda bata zato, dan haka ta saka a ranta ko Hajiya Babba zata koreta a gida yau sai ta rabu da shi, cike da taƙama ta ƙaraso gurin, a hankali ta kalli Ashwan da ke ƙoƙarin tare gaban Muby ganin zai damƙo Afnan, "Ku barshi mana ai shi ba ƙaramin yaro ba ne"

Ta faɗa cikin salon iya magana.

Da ƙarfi ya ƙwace kansa yana mai watsa mata mugun kallo, Maimun kuwa ta rasa abin da ke yi mata daɗi, farinciki ya gama mamaye mata zuciya yau ƙarshen auren da take fama ya zo, tsayuwa Muby ya gyara yana mai ƙara tamke fuska cike da tsanarta ya ce "Idan baki mance ba na faɗa miki irin tsanar da nayi miki, dan haka zama da ke ya zo ƙarshe ba zan iya rayuwa da ke ba, tsanar da nake yi miki ta fi ƙarfin yanda kike tunani" Numfashi ya sauke da ƙarfi yana lumshe lue-lue eyes ɗinsa, sai kuma ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce "Shigo Masoyiyata abin ƙaunata, kuma muradin zuciyata"

Daga Maimun har Afnan kallon gate ɗin suke dan ganin wacece, Ashwan ne kawai be kalla ba saboda shi ya san duk abin da ke faruwa, wata matashiya ce cikin kayan sarauta a bayanta masu kula da ita ne kusan su ashirin, duk kayan jikinsu iri ɗaya suna take mata baya.


Fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso gabansu tare da kama hannun Muby tana wani fari da ido, mamaki ne ya gama rufe Afnan amma sai ta aje mamakin a gefe tana son tunano inda ta san wannan fuskar, Maimun kuwa kasa magana tayi ganin wata masifar ta kunno kai, kallon Afnan matashiyar tayi kafin ta ƙara sakin murmushi a karo na biyu tana faɗin "Na san yanzu haka mamakin inda kika sanni kike yi, tabbas kin sanni kuma har magana mun taɓa yi da ke, da farko sunana Gimbiya Fadila kuma ƴar sarkin Cameron, ni ce wadda kika watsa ma yawu ranar da kuka fita shopping da muƙarrabanki, ki sani cewa a duk faɗin duniya babu wanda Mahaifina ke so sama da ni, kuma ni kaɗai Allah ya mallaka masa, baya son ɓacin raina shiyasa ma na nuna masa mijinki a matsayin wanda nake so, tare da bada umarnin a sake ki dan ba zan zauna da ƴar mulki kamata ba, kuma a yanzunnan gaban idonki Yarima zai sake ki, sannan ki tattara gadararki da mulkin naki, ki bar mana gidanmu, idan kuma kika nuna min taurin kai wallahi sai na sa an kulleki" Da sauri Afnan ta ɗago jajayen idanunta ta sauke kan Fadila, murmushin gen baki ta yi tare da motsa lips ɗinta a hankali cikin gadara ta ce "A yanzu ne na tabbar cewa ko a cikin masu mulki ke ƙaramar ƴar tasha ce, menene amfanin zama da wanda baya sonka, ai ni taimakawa rayuwata kika yi, ba zan iya magana me tsayi ba saboda gajiya zan yi" Kallonta ta mayar kan Muby da tun lokacin da Fadila ke magana ya tsareta da ido, haka kawai yake jin son yarinyar tun sanda suka haɗu, Afnan ce ta ƙatse shi da faɗin "Me kake jira ai sai ka sake ni"


Ɗaga masa kai Fadila tayi alamun ya sake ta ɗin, jiki na rawa Ashwan ya matso yana bashi haƙuri dan ya san cewa idan har Muby yayi gangancin sakin Afnan ba ƙaramin tashin hankali masarautar Sudan da Senegal zasu yi ba, duk a cikin masarautun ba'a yarda da sakin aure ba, shiyasa ma Ashwan ɗin ya kasa samun natsuwa.

A fusace Muby ya janye jikinsa yana faɗin.



*AFWAN YAU TYPING ƊIN BA YAWA A SHAƘATA DA WANNAN, TEAM ƊIN GIMBIYA SAI A FARA ADDU'A KO* 😂




*GIDAN MULKI*

*By*


*Asmeetar Hydar*








P. 9





"Ba kai zaka tsara min wanda zan zauna da shi ba" Ya faɗa yana ciro takaddar da ke gaban aljihun rigarsa tare da miƙa mata, a hankali ta fara warwarewa, ba Ashwan ba hatta Afnan sai da jinta da ganinta ya ɗauke na wucen gadi, tabbas ta san ba ƙaramin tashin hankali wannan sakin zai janyo ba.

Jiki a sanyaye take taka ƙasa har ta shige part ɗinta, dan babu abin da zata tsaya yi a halin yanzu, kayanta ta haɗa a troly sannan ta sanarwa Mubina ta shirya zasu koma Senegal a yau. Ashwan kuwa haushi ne yasa shi barin gidan, a sanyaye Maimun ta koma nata part tana tsoron kar itama a ce a saketa, ta rasa wanne mataki zata ɗauka yanzu, dan haka ta yanke shawarar komawa gurin boka ko zai raba Yarima da Gimbiya Fadila.


Tun da Alhaji Babba ya fara zubawa Muby masifa kansa ke ƙasa, gaba ɗaya fada ta hartsine da labarin rabuwar Gimbiya da Yarima, abun da be taɓa faruwa ba kenan a masarautar, duk da cewa Sarki Ahmad baya son auren amma ransa ya masifar ɓaci, Mommy kam komawa part ɗinta tayi dan bata son ganin ɗan nata a halin yanzu, sosai Alhaji ya nuna ɓacin ransa, tare da

Please Login or Register in order to submit comment