Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda ake nan nan da ita ne yasa Maimun haɗe fuska cikin mugun tsanar Gimbiya.



Sosai aka yi musu nasiha tare da damƙa amanar su duka biyun hannunsa, Alhaji ne ya kalli Muby yana faɗin "Ina fatar ka san yanda kwanan zai kasance, dole masarauta na buƙatar shaida daga yau zuwa jibi, kasancewar Gimbiya ce uwargida yau zai zama ranar kwananta" Kunya ce ta kama Muby amma sai ya ɗaga kai alamun ya gane.


Gyara zama Afnan tayi cike da gadara gami da isa ta ce "Na yafewa ƙanwata Mainun ya kwana a ɗakinta" Daɗi ne ya mamaye zuciyar Maimun har ta kasa ɓoye farincikinta, duk da cewar ta girmewa Afnan ɗin amma dole zata yi haƙuri kasancewar ita ce uwar gida, "To ai shikenan Allah ya bada zaman lafiya mu zamu tafi" Mommy ta faɗa tana kallon Ameera da ke hararen Gimbiya ƙasa-ƙasa "Ai sai ki tashi mu tafi sarkin chatting" Dariya Ameera tayi tana miƙewa tsaye tare da kallon Maimun ta ce "Matar Brother Allah ya bada zaman lafiya"

"Ita kuma Gimbiya fa?" Cewar Alhaji.

Murmushin yaƙe Afnan tayi kafin ta ce "No need for that"

Daga faɗar haka ta nufi upsters, da kallo suka bita ganin yanda take wani taku cikin iya tafiya da gogewa, a lokacin Mubina na saukowa kan steps ɗin ɗauke da basket ɗinda Gimbiya ta ci abinci "Idan sun fita ki rufe min part ɗina" Ta faɗa tana mai cigaba da tafiya.


Bayan su Mommy sun bar gidan ne Muby ya bawa gate Man umarnin duk wanda zai zo kar a bari ya shiga.


Part ɗin Maimun ya nufa wanda ya tsaru sosai ba laifi sai dai shi kujerun parlourn set biyu ne, dirrect ɗakinsa ya nufa tare da shigewa toilet dan ya masifar gajiya, Maimun na ganin haka ta nufi nata ɗakin dan ta shirya.


Ya jima sosai yana wanka kafin ya fito ɗaure da tawul yana tsane jikinsa, Maimun da ke zaune cikin wata haɗaɗɗar shiga ta kayan bacci gaba ɗaya jikinta a bayyane, dama kuwa tana da diri sosai, nan take yanayin Muby ya fara sauyawa dan shi namiji ne me buƙata sosai, haɗe fuska yayi kamar be ganta ba, ita kuwa sai lashe lips take tana girgiza dukiyar fulaninta, gaban mirrown ya nufa tare da zama kan ƙaramar kujerar da ke nan, sannu a hankali ya fara shafa mai ɗinsa me laushi da tsada, kamar daga sama yaji hannun mutum a bayansa sai wani lailaya shi take.



*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P.7




Da ƙarfi ya lumshe kyawawan idanunsa jin yanda take shafa shi, cike da dauriya ya riƙe hannun nata tare da shafa gashin kansa, "Meye haka? kamar me jiran a kawota"

Fari tayi da ido tana mai ɗora ƙafarta kan cinyarsa, a hankali take masa tafiyar tsutsa cikin iya barikanci ta ce "Yarima kai fa mijina ne a yanzu, ina ganin ba laifi ba ne dan na nuna maka soyayya"

Tashi yayi a fusace ransa na ƙuna, a rayuwarsa ya tsani ballagazar mace wadda bata da kamun kai, cikin cool voice ɗinsa me daɗi ya ce "Ai sai ki bari mu yi sallah ko?"

"No nayi sallah tun ɗazu kawai kai nake muradi a yanzu" Mamaki ne ya hana shi magana, wace irin mace ce haka, ya tambayi kansa a zuciya.

"Idan har ke baza ki yi ba sai ki jirani na gama, bana son damuwa wallahi" Cikin tsawa ya faɗa yana mai buɗe wadrop, wata jallabiya irinta larabawa me masifar kyau fara ya saka tare da feshe jikinsa da turarukka masu ƙamshi, har wani matse ƙafa Maimun ke yi dan ta matsu ya hau kan bed ɗin, sallah yayi raka'a biyu ya jima yana addu'a a lokacin har Maimun ta fara zufa tsabagen jaraba, tana ganin ya tashi ta miƙe da sauri da niyar hugin ɗinsa, hannu ya ɗaga mata cike da takaicin banzan halin da take nuna masa "Wai ke mayya ce? yunwa nake ji a bari na ci abinci mana"

A fusace ya fice daga ɗakin, yana ayyana muguntar da zai yi mata tun da ta nuna masa ita ƴar layi ce, haɗaɗɗen kitchen ɗin ya shiga wanda ya gama tsaruwa, ruwan tea ya ɗora sannan ya zuba kayan ƙamshi, tea me kauri ya haɗa ya dawo parlour, zaunawa yayi kan sofa yana mai kurɓa tean sannu-sannu, lokacin da ya gama har sha biyu na dare ta kusa bugawa, gaba ɗaya bacci ya gama rufe masa ido, koda ya shiga tana nan kwance ido buɗe kamar wata aljana, be bi ta kanta ba ya shige toilet tare da yin brush, Maimun kuwa gaba ɗaya ta janye kayan jikinta wanda dama da shi da babu duk ɗaya, ɗan ƙaramin flacks da ke gefen mirrown ya ɗauka yana mai zuba ruwan kanunfari a wani ƙaramin cup, bayan ya gama sha ya rufe tare da kwanciya kan bed ɗin nesa kaɗan da ita, bed side lamp ɗin ya kashe yana mai janyo blanket ya rufa, kamar Maimun zata kurma ihu ta ce "Haba Yarima wannan rashin adalci ne, ina matarka ai ka san dole zan buƙace a yau" Jin abin da take faɗa ne yaso ya bashi dariya amma da yake ya iya takunsa sai ya shareta, kamar be ji abin da take faɗa ba, mirganawa tayi kan jikinsa tana shafa masa baya kamar wata mage, a zuciye ya damƙota tare da dannata kan bed ɗin, tana ganin haka ta ƙara banƙaro masa ƙirjin nata, sosai yake sarrafata kamar kwallo, Maimun kuwa sai nishi take tun ba'a je ko'ina ba, kusan mintuna talatin yana wasa da ita, ita kam ta gama sarewa babu abin da take buƙata face shi ɗin dai, duk wannan wasar ba zata yi mata ba, kayan jikinta wa watsar yana mai ƙoƙarin juyata yaji danshin abu kamar ruwa, cakkk ya tsaye numfashinsa sam-sama, gaba ɗaya ya ƙagu ya ji ya fara aiki, har wani jiri ke ɗibarsa, da ƙyar ya kai hannunsa kan bed side lamp ɗin, wani wawan tsaki ya ja yana mai tureta gefe ɗaya cikin masifa ya ce "Ashe baki da hankali, dama kinsan kina haila za ki zo ɗakina?"

Kamar Maimun zata fashe da kuka ta tashi zaune tana duba ƙasanta da ya lalace da jini, "Na shiga uku ni Maimun wallahi a yanzu ya zo mun, dan Allah kayi a haka kawai idan baka yi ba mutuwa zan yi"

"Idan kin fasa mutuwa baki yima Allah"

Muby ya faɗa ransa a ɓace, hanyar fita ya nuna mata yana mai dafe mararsa da ke barazanar barin jikinsa "Fice min da wannan ƙazantar"

"Karka mun haka....."

Tun kafin ta ƙarasa ya cafki hannunta tare da nufar ƙofa, yana isa ya jefata waje ya rufo ɗakin.

Zanin gadon ya cire yayi jifa da shi, sai da ya sake yin wani wankan da ruwa me ɗumi, sannan ya fito dafe da cikinsa wanda ke cizga, "Washhhh...." Ya furta a hankali yana lumshe ido.

Da ƙyar ya iya saka kayan bacci riga da wando masu kyau da laushi, a lokacin har yana ƙoƙarin faɗuwa, wani irin juyawa mararsa tayi wadda ta saka shi sakin ƴar ƙaramar ƙara, zubewa yayi gaban mirrown tare da dafe marar tasa yana jin wani irin zugi da take masa, haka kawai Gimbiya ta faɗo masa a rai, gajeren tsaki yaja dan ba zai iya zubarwa kansa da girma ba, idan mutuwa zai yi sai dai ya mutu, sannu a hankali ya tashi yana jan jiki, Fridge ɗin da ke ɗakin ya buɗe, lemu guda uku manya ya fidda cike da dauriya ya matse a cup, ruwan ɗumun da ke Flacks ya zuba, kafin ka ce me ya shanye yana yamutsa fuska.


Duk da ya shanye wannan lemun amma kamar ƙara masa ciyon ake duk ya hargitse, ya ɗauki tsawon lokaci kafin bacci ya ɗaukesa.


Maimun kuwa tana ganin Muby ya jefata waje ne yasa ta nufi ɗakinta jiki na rawa, gaba ɗaya ta fita a hayyacinta, duk wani kwaɗayinsa ya ƙara bazuwa a ranta, babu abin da take muradi face Muby, ko wanka bata yi ba haka ta saka pad tare da bajewa kan bed.




A ɓangeren Afnan tun lokacin da ta shige ɗaki take chat da Eashat, sai tsiya take yi mata wai ta sauka online Yarima zai zo kashe arna, ita ko haushin maganar ma take wai arna, suna cikin chat ɗin ne bacci ɓarawo ya sace ta, misalin ƙarfe uku ta farka tare da shiga banɗaki, alwala ta ɗauro kamar yanda ta saba kowanne dare idan har tana da tsarki, ta daɗe tana nafila kafin ta ɗauko Alqu'an cikin muryarta me zaƙin gaske take karantawa har aka kira sallar asubu, bayan tayi sallah ne ta koma baccin dan har wani rufewa da buɗewa idanunta ke yi, sai misalin tara na safe ta farka ko shima bugun ƙofar da Mubina ke yi mata ne yasa ta tashi da ƙyar ta buɗe, rusunawa Mubina tayi tana faɗin "Gimbiya an tashi lafiya?"

Juyawa Afnan tayi tare da cire hijab ɗinda ke jikinta, a hankali ta ce "Lafiya, me kike buƙata ne?"

"Allah ya baki nasara dama naga har wannan lokacin baki tashi ba ne, shine dalilin da yasa na ce bari na duba ko lafiya"

"Amma kinsan idan ina bacci ba'a tada ni ko?"

Sunkuyar da kai ƙasa Mubina ta yi kafin ta ce "Afwan insha Allah hakan baza ta kuma faruwa ba"

"Fice min daga ɗaki" Afnan ta faɗa tana mai shigewa toilet.

Da sauri Mubina ta fita tare da janyo ƙofa.


Ta jima cikin toilet ɗin kafin ta fito ɗaure da tawul ɗan ƙarami iya cinyarta, sai wani pink da ke hannunta tana tsane gashin kanta, kan Mirrow ta zauna sai wani yamutsu fuska take, ta ɓata lokaci sosai gurin tsara kwalliya kafin ta miƙe cikin ƙasaita ta buɗe wadrop ɗinta me cike da kaya, wata doguwar riga less me taushi blue ta ɗauka, sannu a hankali ta zura tana mai komawa gaban Mirrown, haka kawai taji yau tana ra'ayin ɗaura ɗankwali, dan dama ita da wahala kaga ta ɗaura shi sai dai fa ta aza Alkyabba a saman kanta, sosai ɗaurin yayi mata kyau kamar ba ita ba, sai ta ƙara wani irin hatsabibin kyau, turarenta me tsananin ƙamshi ta fesa tana mai ɗaukar wayarta ta fito daga ɗakin.


Koda ta sauko parlourn har Mubina ta gama haɗa breakfast dan haka daining ta nufa saboda yunwar da fara ji, perpesun kan shanu ne da dankalin turawa, sai tea da kuma kunun gyaɗa wanda ya sha madara sosai, a ɗayan gefen ƙwai ne soyayye wanda aka haɗa da nama, ɗayan cup ɗin kuwa juice ne wanda ya sha kwkwa da madara, da sauri Mubina ta ja mata kujera ta zauna, sai da aka zuba mata kowanne a pleate sannan tayi bismillah tare da fara ci a hankali.


Ta ɗauki tsawon lokaci tana ci kafin ta ji cikinta ya ɗauka, dama ba wani cin abinci take ba.

Norcking ƙofa ne yasa Mubina fitowa daga ɗakinta ta buɗe.

Maimun ce tsaye cikin wasu kafuran ƙananan kaya, ta wani haɗe fuska sai ka ce anyi mata dole, bangaje Mubina tayi tare da faɗawa parlourn ko sallama babu, har kan daining ta sami Afnan wadda tun da ake buga ƙofar ko kallon ɓangaren bata yi ba, duk da cewa Maimun na jin shakkun yi mata magana amma hakan be hanata ɗaukar cup ɗin juice ta kai baki ba, zama tayi kan ɗaya daga cikin kujerun kafin ta ce "Barka da wannan lokacin Uwargida?" Shuru Afnan tayi tana mai cigaba da latsa wayarta har yanzu kanta a ƙasa.

Ɗaga kafaɗa Maimun tayi alamun ko in kula, sanna ta cigaba da faɗin "Baby ya ce na zo na karɓi abincin da aka yi mana anan, kinsan duk wadda aka farma a daren farkonta da wahala ta iya girka wani abun".

Gaban Afnan ne yayi mummunan faɗuwa jin abin da Maimun ta ce, kar dai ace Yarima ya yi mata wani abun.


Kawar da zancen tayi tare da tashi cikin iya taku ta fara sauka kan daining ɗin, da sauri Maimun ta sha gabanta cike da rashin kunya ta shafa lips ɗinta tana faɗin "Bana son na yi dogon magana saboda jiya kamar Baby zai cire mun lips, sai wani lashe su yake kamar ya samu sweet".

Har Afnan ta buɗe baki da niyar magana sai ta fasa tana mai raɓa gefenta ta haura sama, dariya Maimun ta kwashe da ita tana faɗin "Yanzu aka fara, wallahi sai kin bar gidannan da ƙafafunki, ke gaki Gimbiya"

Shewa tayi tare da komawa daining ta kwashi kulolin abinci ta fice.


Cikin salonsa da ke ƙara masa kyau ya fara takowa har down steps, sanye yake cikin jallabiya fara hannunsa ɗauke da Cup, wanda lemun tsami ke a ciki, ƙamshin turarensa ne ya sanar da isowarsa, gashin kansa yake shafawa a hankali wanda ya gama haɗuwa, Maimun da ke kan sofa tayi rashe-rashe tana kwasar girki ne ta tashi da sauri har wani gyara dukiyar fulaninta take dan ta janyo hankalinsa, shi ko Muby bai ma san da zamanta a gun ba, sai kawai ganin mutum yayi a gabansa, "Lafiya kika tsare min hanya?"

Ya tambaya yana mai haɗe fuska, shigewa jikinsa tayi tana wani shafa masa saje, "Baby yanzu idan ban zo gurinka ba, gurin wa kake son na tafi?"

Cike da makirci ta yi maganar har tana rufe ido.

Janye ta yayi da ƙarfi, yana watsa mata harara cikin fushi da gajiya da halinta ya ce "Bana son hauka"

Barin gurin yayi cike da jin haushin yanda take wani shige masa, bayansa tabi tana kiran sunansa kamar wata ƴar hau, "Wai menen haka? Baby wannan fa ba daidai ba ne"

Banza yayi mata tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun, remote ya ɗauka dan ya tsani kallon tashar hausa, NTA ya saka dan jin labaran duniya, kasancewar yau Saturday ba aiki, ganin ya shareta ne ya sa ta kwaso kulolin abincin ta zube masa a gaba, har wani rawa jikinta ke yi gurin zuba masa, sai da ya bari ta gama zubawa ya kalleta cikin mamaki amma sai ya kasa furta komi dan yanda bakinsa ke yi masa nauyin magana.

"Baby ga abinci na zuba maka"

Yi yayi kamar bada shi take ba har sai da ta maimaita so uku, kafin ya lumshe ido a hankali cike da miskilanci ya ce "Baza a ci ba"

"Please kar ka mun haka, saboda kai na tashi na dafa duka waɗannan abincin fa"

Kafin ya ce wani abun su ka ji an banko ƙofar da ƙarfin tsiya, Afnan ce fuskarta haɗe babu alamar wasa, cikin taƙama ta ƙaraso gurin da kulolin abincin su ke, tana watsawa Maimun harara, Muby da ke zaune kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai dan ji yake kamar ya shaƙeta ta bar duniya, sai yaji ma tsanarta na ƙara darsuwa a ransa, kamar yanda itama Afnan ɗin daurewa kawai take amma ko ganinsa bata ra'ayin yi.


Bata bi ta kansu ba ta kwashe gaba ɗaya abincinta ta fice cike da gadara, da kallo Maimun ta bita cikin kunya, ta kalli Muby da idanunsa ke lumshe ta ce "Baby kaga abin da matarka ta mun ko? ita baza ta girka ba sai nawa zata ɗauka"

"Ko kuma nata kika ɗauko ba" Cewar Muby yana mai kwanciya tare da rufe ido dan bacci ma yake ji, cikin jin haushi Maimun ta ce "Kamar ya? meyesa zan tafi part ɗinta na ɗauko abinci bayan na iya dafawa"

"Karki raina mun hankali, tun kafin na aureki na san babu abin da kika iya ɓangaren abinci, ko ita ƴar gadarar bata iya komi ba, akwai me dafa mata, idan kika sake magana nan gurin sai kin tafi gidanku, an faɗa miki na mance da ƙazafin da ki ka mun ne?" Muƙussss Maimun ta lafe guri ɗaya, jin abin da ya faɗa, ta san cewa ƙaramin aikinsa ne ya turata gida, duk da cewar a masarautarsu ba'a saki.


Misalin ƙarfe biyu su Ashwan suka zo gidan, amma Afnan ta rufe part ɗinta tare da ba Mubina umarnin ko Muby ne ya zo kar ta buɗe ƙofa, a ɓangaren Maimun suka sauka sai wani salo take musu tare da canza tafiya kamar wani abu ya faru, ganin babu abin da Maimun ɗin ta dafa ne yasa Muby ya kwashe su suka nufi wani resturant, wanda sai manyan masu kuɗin garin ke shiga, motoci goma ne ka take musu baya, lokacin da suka isa duk waɗan da ke ciki fitar da su aka yi, daga can waje wasu mata na jiran Yarima ya fito ko zasu ɗauki hoto da shi, sai wuraren ƙarfe huɗu suka bar gurin direct masallaci suka nufa, bayan sun gama sallah suka nufi gidan sarautar.


Tun daga harabar gidan masu tsaro ke kwasar gaisuwa har ya shiga babban parlour, Ashwan ne ya kallesa yana faɗin "Wai ina zaka kaimu ne haka? ka san dai baza mu shiga fada ba ko?"

Taɓe baki Muby yayi kafin ya ce "Zan gaida Mommy na fito mu shiga tare mana"

"A a kam, a dawo lafiya ka same mu a mota" Cewar Yusuf yana kama hannun Ashwan suka fita.

Muby kuwa ɗakin Mommy ya nufa, Ameer kawai ya samu kwance kan bed ɗin Mommy yana waya da Husna, da sauri Ameer ya kashe wayar dan ya san halin gogan, "Brother sannu da zuwa"

Sai da ya zauna kan kilishin da ke kan sofa a hankali ya ce "Sannu kaima, da wa kake waya?"


Waro ido Ameer yayi yana mai noke kai, ya rasa ma abin da zai faɗa, ga kuma kiran Husna na shigowa dan taga an yanke waya.


"Bani wayar nan" Muby ya daka masa tsawa.

Daidai lokacin da Mommy ta shigo ɗakin, Ameer na ganin haka ya sauke ajiyar zaciya yana mai fita daga ɗakin, cikin girmamawa Muby ya gaishe ta yana sunne kai ƙasa "Sannu sarkin masifa ihun me kake masa haka?"

Sosa kai Muby yayi tare da lumshe ido a hankali ya ce "Da wata mace yake waya fa"

"Au hana shi soyayya zaka yi? bayan kai kayi aurenka"

"Amma Mommy ai Ameer yaro ne"

Muby ya faɗa yana ɓata fuska, murmushi Mommy tayi kafin ta ce "Ya ka baro yarannan?" Sai da ya ɗan haɗe fuska cikin takaici ya ce "Suna lafiya"

"Masha Allah abin da yasa ban aika musu abinci ba dan na san Mubina zata dafa musu, sannan anjima Kuyangi goma zasu tafi gidan, kaga suma zasu huta da wani aikin musamman Mubina zata samu masu rage mata wani abun"

"Hakane gaskiya Allah ya biya"

Da Ameen Mommy ta amsa tana ƙara yi masa nasiha, ya ɗan jima kafin ya shiga fada gurin me martaba, a can ya sami Alhaji, ba wani jimawa yayi ba ya fito.


Tun daga nesa su Ashwan ke masifa da jinini akan ya shanyasu, ɗan murmushi yayi wanda ya ƙarawa fuskarsa kyau "Ai rashin aure ne ke ɗawainiya da ku"

Bushewa da dariya Ashwan da Yusuf suka yi kafin Yusuf ya ce "Meye marabar? mun jima da sanin cewa babu abin da ya faru a daren jiya"

Wani irin tsaki Muby ya ja yana mai shigewa mota tare da ba Driver umarnin ya kai shi gida, da sauri su Ashwan suka shiga tasu motar suna dariya, nan take motocin suka bar gidan, tun a hanya suka rabu motocin Yarima kuwa gidanshi suka nufa, a bakin gate ya fara jin hayaniya kamar taron biki ake, ganin dawowarsa ne yasa Maimun da ƙawayenta shan jinin jikinsu, gaba ɗaya harabar gidan kayan party ne sai duma ke tashi, duk ƙawayen an sha ƙananan kaya kamar ba musulmai ba, be jira driver ya gama peraking ba ya fito a fusace ransa ya masifar ɓaci.

Maimun kuwa nufosa tayi dan gudun kar ya wulaƙantata gaban ƙawayenta, dan ta gama yi musu ƙaryar yana masifar sonta.

A sukwane ta kama hannunsa tana kashe masa ido "Baby sannu da zuwa" Wani mugun kallo ya watsa mata wanda yasa ta sake masa hannu ba shiri, sarai ta san halinsa baya ɗaukar hauka.

Cikin tsawa ya fara magana kamar zai yi musu dukan tsiya, "Bana buƙar na sake fitowa na sameku anan, wallahi idan na kuma ganin wata kilaki a gidana sai na kulleku...."

Ai tun kafin ya kai numfashi sun tattara takalmansu sun yi waje da gudu, Maimun kuwa sai magana take masa yayi mata banza, a can gefen swimming pool ya hangi mutum zaune amma bayanta kawai ake gani, Mubina na gefe riƙe da farantin kayan marmari da kuma lemu cikin Cup, sai a lokacin Maimun ta lura da ita, ganin shigar da ke jikinta ne yasa Muby saurin kawar da fuska, dama daga gefen babu ma'aikata maza, dan yayi musu iyaka da ɓangarorin matansa, part ɗin Maimun ya shige yana mai shan ƙamshi, har wani kyau tafiyar ta ƙara masa.


Afnan kuwa tana sanye ne cikin wando iya cinya, da ƴar ƙamar riga marar hannu, ko cibiyarta bata rufe ba, gashin kanta ta baza shi a bayanta yayi kwance, Laptop ne gabanta tana dannawa sai wani gyaɗa kai take alamun yanayin yayi mata daɗi, kamar daga sama suka ji muryar Maimun na faɗin "Sannunku da hutawa"

Mubina ce kawai ta gaisheta amma Afnan kanta na kan aikin da take yi, sosai ran Maimun ya ɓaci ta rasa meyesa duk lokacin da zata yi mata magana bata amsa mata.

Kusa da Afnan ta zauna cikin salon jan faɗa ta dafa kafaɗarta, tana faɗin "Magana nake miki" A fusace Afnan ta miƙe ranta ya gama ƙuna, ganin yanda Maimun ta dafa ta, da yatsa ta nunata bakinta na rawa ta ce "Da wanne hannun kika taɓa ni? yau sai kin ci ubanki"

Da ƙarfin tsiya ta damƙi wuyan Maimun tare da jefata cikin ruwan da ke gurin, Maimun kuwa bata iya ruwa ba nan take ta fara neman ceto, cike da gadara Afnan ta ce "Wannan shine hukuncinki, idan kin mutu sai a jafar da gawarki, dabba kawai wadda bata san abin da take ba, an faɗa miki kin kai matsayin da za ki taɓa jikina ki zauna lafiya" Ta ƙarasa maganar tana kallon Mubina, " Ki shigar min da kayana"

Cike da ladabi Mubina ta amsa tana kwashe Laptop ɗin da waya, Muby da fitowarsa kenan ya ga abin da ke faruwa, ga kuma Maimun har tana neman kasa numfashi da sauri ya ƙarasa gurin tare da faɗawa, da ƙyar ya samu damar cetota, a bakin ruwan ya kwantar da ita, idanunsa sun yi jajir, kallon Afnan yayi kamar wanda aka saka dole ya ce "Ya aka yi ta faɗa ciki?" Wani kallon tsana Afnan ta jefa masa kamar ta yi masa magana sai kuma ta fasa gami da barin gurin cikin kaɗa jikinta me masifar kyau, har wani juyawa west ɗinta ke yi wanda idan ka gani zaka zata ita ce ke juya su, mamaki ne ya kama shi ganin rainin hankalin da tayi masa, saurin kawar da kai yayi tare da tallafa Maimun ya shiga da ita part ɗinsu, yana isa ya jafeta kan sofa sannan ya haura sama dan canza kaya.

Maimun kuwa sai dare ta farka, duk ta galabaita a lokacin har Mommy ta aiko da Kuyangi masu kula da gidan, a sukwane tashi tsaye tana kallon inda take, sai yanzu take tuna abin da ya faru da ita, wani mugun ƙololon baƙin ciki ne ya rufeta, kamar ta kurma ihu haka take ji.

Jin saukowar mutum ne yasa ta maida kallonta kansa, ya wani haɗe fuska kamar wanda be taɓa dariya ba, hancinsa ya toshe tare da matsawa can gefe "Wai har yanzu kina nan? dallah malama je ki wanke ƙazantar da ke jikinki".

"Baby hanci fa kake toshe mun?"

Maimun ta faɗa tana ƙoƙarin taɓa sa, ai bai san lokacin da ya ruga da gudu waje ba, sai kakarin amai yake.

Haushi ne ya kamata ganin mugun wulaƙancin da yayi mata, ƙofa tayi tana mai sawa ranta sai ta rama abin da Afnan tayi mata koda kuwa zata yi yawo tsirara.


Kwanaki biyu currrr su ka shuɗe ana fama da Muby da Maimun, ita ala dole sai ya yi a haka ko tana Haila, lamarin nata ya fara bashi tsoro, Afnan kuwa tun a ranar da ta kaɗa Maimun cikin ruwa har yau basu sake haɗuwa ba, kullum

Please Login or Register in order to submit comment