Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu bata warke ba, saboda duk waɗan da ake kawo masa basa wuce sati biyu suke warkewa.

Muby kam kullum sai ya kwashi daɗi jikin Afnan, ita kanta duk ranar da be yi romancing ɗinta ba har wani iri take ji, idan dare ya yi kuwa haka zata matsu su dawo sallah ko zai yi abin da ya saba, amma har yau bata nuna masa wata alamar samun sauƙi ba shima be ga alamar sauƙin ba, kalaman soyayya kuwa ba'a magana wani lokacin har mamaki Afnan take yanda Muby ke faɗin yana ƙaunarta.

Misalin ƙarfe biyar na yamma Muby da Malan ne zaune tsakar gida, Bosho kuwa be jima da fita ba, "Gaskiya al'amarin samun saƙinnan ya fara bani mamaki, amma kuma ba'a mamaki da ikon Allah" Cewar Malan yana jinjina kai.

Ajiyar zuciya Muby ya sauke yana mai faɗin "Muna fatar ta samu lafiya ko zamu koma gida, ayyuka da yawa suna jira na dan ma akwai masu kula da komi shiyasa abun ya zo da sauƙi"


"Hakane amma akwai wata addu'a da zan ba ka ajima sai ka jaraba mu gani, insha Allah za'a dace"

"To Allah ya sa"

Fira suka cigaba da yi har aka kira sallar magrib, lokacin Bosho ya dawo daga shago, tsarabar kayan marmari ya kawo musu har da gasashshen nama wanda ya sha kayan alatu, kowa da ledarsa.

Karɓa Muby ya yi yana faɗin "Ka jirani ina zuwa"

Komawa ɗaki ya yi Bosho kuwa ya fara alwala, hannun Muby ɗauke da kuɗi ya fito yana murmushi, sai da Bosho ya gama kafin ya miƙa masa "Ga wannan dubu ɗari biyu ne kaima ka buɗe naka shagon, abin da ya sa ban ba ka kuɗin tun tuni ba saboda ina son na ga ka canza gaba ɗaya"

Kuka Bosho ya fashe da shi yana mai rusunawa ƙasa sai zuba godiya yake, haka Malan ma ya ƙara yiwa Muby godiya, "Alright godiyar ta isa haka lokacin sallah ya yi mu ƙarasa masallaci"

A can suka tsaya har aka kira isha'i, sai kusan tara suka dawo, wanda a lokacin Afnan bata san cewa sun shigo gidan ba, tana zaune sai yagar naman da Bosho ya kawo take, a bakin ƙofa wani abokin Malan ya tare shi suna gaisawa shi ko Bosho ya nufi majalisar abokanansa a can gefen gida.

Gaba ɗaya Afnan ta mance da cewar kowanne lokaci Muby zai iya dawowa, kamar daga sama ta ga an turo ƙofa, wani irin miƙewa ta yi tana mai tsalle gefe ɗaya, Muby kam kasa magana ya yi sai kallonta yake da kuma naman da ke hannunta, ido ta shiga rabawa alamun rashin gaskiya, cikin basarwa ta jefa sauran naman da ke hannunta a baki, dariya ce ta kwacewa Muby har da riƙe ciki, haɗe fuska Afnan ta yi tana mai komawa ta kwanta har da tattaro zanin da Muby ya rufeta ɗazun ta ƙara rufe jikinta wai ita marar lafiya, sai da ya gama dariyar kafin ya zauna kusa da ita yana faɗin "Sai yau na gane me shanye mana kunun gyaɗa kullum, dama kin warke shine ki ke wahalar da mu haka? musamman ni"

Shuru Afnan ta masa tana mai kawar da kai gefe, yana ganin haka ya fara yi mata chakulkuli ai kuwa ta fara dariya tana ture shi har suka faɗo ƙasan katifar, "Ashhhhhhh, bayana" Da sauri Muby ya ɗagota yana faɗin "Sorry Baby please for give me" Yanda yake maganar cikin sanyin murya da tsantsar ƙauna ne ya sa ta ƙura masa ido, kwantar da ita ya yi kan ƙirjinsa yana shafa bayan nata a hankali ya ce "Meyesa ba ki faɗa min kin samu sauƙi ba? sai da na gani da idona"

"Saboda bana sonka" Afnan ta faɗa tana kwace jikinta, wani irin zafi zuciyarsa ke yi jin furucin da ta yi, amma sai ya danne yana mai marairaice murya "Baby what are you saying? you know i so much love you, dan Allah kar ki sake faɗin haka, ko ba ki sona ni zan koya miki sona"

"Bana buƙata Mubarak please live me alone"

"No i can't do that ke rayuwata ce, dan Allah kar ki horani da abun da ya faru a baya, na gane kuskurena ina neman afwa"

Matsawa Afnan ta yi tana mai cigaba da tura baki ba tare da ta amsa masa ba, kusa da ita ya koma ya kuma janyota jikinsa ya matse, "Wai meye haka ne ka sake min jikina"

"Jikinki nawa ne, dan haka baza ki hanani ba"

"Au yau kuma ƙasussan ake son taɓawa? bayan kanada Maimun me kayan daɗi"

Haɗe fuska Muby ya yi kafin ya ce "Koma menene ke matata ce kuma ina sonki, ni yanzu haƙƙina ma zan karɓa".

Waro ido Afnan ta yi a tsorace dan ta san halinsa, "Bana so ka daina, muna komawa gida za ka bani takaddar sakina"

Wata irin faɗuwar gaba Muby ya ji kamar an ɗora masa guduma a zuciya, "Okay na ji idan har ki ka yarda na yi abin da nake so muna komawa zan yi abin da ki ke so"

Washe baki ta yi kafin ta ce "Eh na yarda idan har ka mun alƙawari"

"Au har sai na yi miki alƙwari? to ki bar kayan daɗinki nima zan bar sakina"

"No na yarda amma dan Allah kar ka kare alƙwarinka"

Shuru Muby ya kuma yi yana jin wani irin ƙuna a ransa, wai dama haka Afnan ta tsaneni har tana tunanin zamu rabu.

Hannunsa da ta riƙe ne ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga "Ni ka yi abin da zaka yi ko zan kwanta bacci nake ji"

Dariya ta so bashi ganin yanda ta maida fuska, kyawunta ya ƙara bayyana tamkar zinariya.

A ransa ya ƙudurta yau sai ya lashi zumarta, ita ko Afnan a tunaninta romance ɗin da ya saba yi mata ne zai yi, bata san cewa zuciyar Muby ta karkata wani gefen ba.






*Mu haɗe a next page daga ta ku Asmeey ta Hydar Sayyada ta Sayyadi*



,,,,,,,,,,,





*GIDAN MULKI*

*By*


*Asmeetãr Hydar*









P. 23








A ɓangarensu Nabeelah kuwa a yau ne Me martaba ya sa aka fito da su Fadila daga kurkukun bayi, kuma yau ne yake son yanke musu hukunci daidai da abin da suka aikata, ciki kuwa har da Mahaifin Fadila ɗin.


Gaba ɗaya fadar cike take da mutane ana kallonsu, Fadila kam ko wanda ya santa ba zai wani ganeta ba, ta zama tamkar mahaukaciya duk jikinta tabon dukan da aka rinƙa yi musu ne, Mahaifiyarta kuwa ƙuraje ne suka fito mata a jiki masu warin gaske, kowa da ke gurin toshe hanci ya yi tsabagen wari, sai kuma taɓin hankalin da ya sameta, a yanzu ma ɗaureta aka yi dan kar ta gudu.

Me martaba ne ya kallesu cikin mugun tsana musamman Fadila ji yake tamkar ya yi mata dukan tsiya, "Da farko ina yiwa kowa fatan alkhairi, waɗannan bayin Allah kunsan abin da suka aikata kuma yau nake da niyar yanke musu hukunci daidai da abin da suka shuka, to amma ganin yanda suka koma ne ya sa na janye batun hukuncin nasu, wannan kaɗai ya ishe su ishara, ina buƙatar a fitar da su daga ƙasar nan gaba ɗaya, tun kafin cutar jikinta ta shafi wani"

Kuka Fadila ta fashe da shi tana mai cewa "Dad please kar ka mana haka, dan Allah ka yafe mana......."

A tsawace ya ce "Allah ya sawwaƙa min na zama Mahaifi a gareki, tabbas sai yau nake nadamar sangartaki da na yi, wannan ba soyayya ba ce na nuna miki, amma hakan ya isheki kuma shine izina a gareki, kin tashi salwantar da rayuwar ƴata saboda baƙin hali irin naku da baƙar zuciya, ku fitar min da su tun kafin fushina ya tabbata a kansu".

Da ƙarfin tsiya aka fitar da Fadila da Mahaifanta, sosai Nabeelah ta tausaya musu kasancewar mace ce me tausayi, gaba ɗaya ta kasa sakewa har aka fice da su.

Part ɗinta ta koma wanda sabon gini ne, sosai aka tsara gurin dukiya kuwa ba'a magana, ɗakuna biyar ne wanda kowanne ke ɗauke da parlour na gaban kwatance, tana shiga ta faɗa kan bed tare da dafe kanta da ke sarawa, ta kasa gane meyesa idan ta rufe fuska take ganin Muby na yawo a idanuwanta, komi nasa burgeta yake tana son mancewa da shi amma abin ya gagara, a haka har Mom ta shigo amma Nabeelah bata san lokaci ba.

Jin an taɓa ta ne ya sa ta miƙe a zabure, ganin Mom ne ya sa ta saki ajiyar zuciya da kuma murmushi, itama Mom ɗin murmushin ne ta yi kafin ta ce "Yarima ki ke tunani ko?"

Cike da mamaki Nabeelah ta ƙara sauke idanuwanta kan fuskar Mom "Ummm...ummm, Yarima kuma Mom?"

"Eh Yarima Mubarak shi ki ke tunani, tun ranar da muka tafi ƙasar Sudan na lura da yanda soyayyarsa ta kama ki, amma meyesa ba ki sanar masa ba?"

Cikin alamun kunya Nabeelah ta ce "Ba wai na kasa faɗa masa ba ne, kawai ina ganin zan lalata musu zaman aurensu ne"

Ajiyar zuciya Mom ta sauke tana cewa "Hakane amma idan har kinga za ki iya haƙuri da shi ai ba damuwa, kawai tunanin ne bana so"

"Kar ki damu Mom zan iya haƙuri da shi, amma na san cewa zuciyata zata kamu da matsanancin ciyo wanda babu maganinsa sai Allah"

Cikin tausayi Mom ta kuma cewa "Ba laifi ba ne idan mace ta bayyana soyayyarta ga namiji, amma sai wanda ya cika sharuɗɗan da ya dace, na yaba da halin Yarima sosai shi mutum ne me karanci da kuma sanin ya kamata, ki yi tunani a kai amma wannan damuwar bana so"

"Shikenan Mom zan yi nazari"

"Hakan ya yi Allah ya miki albarka"

Da ameen Nabeelah ta amsa tana mai kwanciya kan bed ɗin.



.............................
Muby kuwa ganin banza ta faɗi ne ya sa shi cewa "Matso ki zauna a nan"

Ya nuna mata saman cinyarsa, waro kyawawan idanunta ta yi sai kuma ta shagwaɓe fuska alamun ta yi fushi, shima shagwaɓe fuskar ya yi kamar ƙaramin yaro "Shikenan bari ma na fice abuna"

"Eh ɗin ka tafi sai me to?"

"Hakama za ki ce? tom na fasa rabuwa da ke ko mun tafi gida"

"Tom ni ina ruwana, ina komawa zan tattara kayana na koma gidanmu, dama ba sona ka ke ba nima bana sonka" A duk lokacin da Afnan ta furta cewar bata son shi wani irin zafi zuciyarsa ke masa, murmushi ya sakar mata kafin ya ce "Okay dama bakya sona ne? ki kalli cikin idona ki faɗa mun cewa bakya sona"

Afnan kam sunkuyar da kai ta yi ƙasa dan wani kwarjini ya yi mata, "Afnan........" Wani iri jikinta ya yi jin yanda ya kira sunanta, yana da wahala ya kira sunanta kai tsaye.

"Ni ka fice mun daga ɗaki bana son damuwa"

"Ba zan fita ba har sai kin faɗa mun cewa bakya sona"

Ɗan turo baki gaba ta yi kamar zata yi kuka ta ce "Bana sonka"

"Kalli cikin idona sai ki faɗa mun, idan har ba ki kalli idona ba wallahi kina sona"

"Ni me zan yi da kai ne? na wuce sanin....."
Sai kuma ta kasa ƙarasawa, a hankali ya matsa kusa da ita, Afnan kam sai ja baya take tana neman hanyar gudu, "Ƙara maimaitawa, kin wuce sanina ko? to bari na gwada na gani waye ya wuce sanin wani"

Ƙanƙame jikinta ta yi tana galla masa harara, "Kar ka taɓani da ƙazamin jikinka"

Dariya maganar ta ba shi, "Ai kuwa ƙarya ki ka yi, ko kin mance cewar kullum sa na latse ki, kuma kullum sai na lashe bakinki, ashe ma kin samu sauƙi kawai shan daɗinki ki ke yi, kalli yanzu yanda ki ka wani tsayawa dan kawai kina son in manne miki"

"Allah ya sutura, ni me zan yi da kai"

Sallamar Malan ne yasa Afnan ƙarasawa, cikin murna Muby ya fito tsakar gidan yana faɗawa Malan cewar Afnan ta samu lafiya, ai kuwa da fara'a suka shiga ɗakin, a lokacin Afnan na zaune kan katifa sanye cikin hijab ɗinta.

Da murmushi Afnan ta gaishe da Malan har tana sunkuyar da kai, "Lafiya ƙalau Gimbiya, Allah mun gode maka tabbas kar ka cire tsammani ga mahaliccinka, haƙiƙa kin ga rayuwa amma yanzu kamar ba komi ba"

Afnan ce ta ce "Hakane gaskiya na gode sosai da ƙoƙarinka gareni Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"

"Ba ni ya kamata ki godewa ba mijinki ne, tabbas ba kowanne miji ne zai kula da matarsa haka ba, kin yi dacen miji Allah ya bar ƙauna"

Muby ne kawai ya amsa da ameen, Afnan kam haɗe fuska ta yi tamkar ba ita ce me murmushi yanzu ba, sai da safe Malan ya yi musu yana mai ficewa daga ɗakin, yana fita Afnan ta miƙe ta nufi trolyn da ke gefe, wasu kaya ta ciro kafin ta fito daga waje, Muby kam duk inda ta saka ƙafa nan zai saka idanuwansa.

Wanka ta shiga dan baza ta iya bacci ba tare da ta yi wanka ba, dama Muby ne ke yi mata to yanzu ya gane lafiyarta ƙalau, bata wani jima ba ta shigo cikin ƙaton hijab ɗinta, wannan karon a kwance ta same shi sanye cikin kayan bacci masu masifar kyau, hijab ta zame sai ga tawul ya bayyana ɗan ƙarami daidai santala-santalar cinyoyinta, gashin kanta kuwa ta ɗaure shi daga baya, numfashin Muby ne ya kusa ɗaukewa ganin yanda duk wata siffa ta jikinta ta bayyana, ga wani kyau da ke fizgarta, saurin runtse ido ya yi yana mai dafe saitin mararsa, shi kaɗai ya san yanda yake ji game da Afnan, amma baya son nuna mata sha'awarta da yeke yi, tabbas ya san yana tsananin ƙaunarta shiyasa yake son danne duk wani feelings nata dan kar ta yi tsammanin jikinta yake so.

Afnan kam ko gefensa bata kalla ba ta fara shirinta cikin wata arniyar rigar bacci me ɗan karen laushi, ba ƙaramin kyau ta yi ba musamman da rigar ta tsaya mata daidai cinya, tana ɗauke da siririn hannu kamar bra, gashin kanta kuwa ta gyara shi tare da baje shi a bayanta ya sauko kan ƙugunta.


Turarukka ta feshe jikinta da shi kafin ta rufe ɗakin, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai.

Zanin gadon da ke kan katifar ne ta ɗauka da niyar kwanciya a ƙasa, tana ɗora hannunta kan zanin Muby ya cafkota ta faɗo ƙirjinsa, "Meye haka ne wai? ka barni ni bana so"

"Babu abin da zan yi miki bacci zamu yi"

"Yau bana son bacci da namiji kawai ka barni"

Be saurareta ba ya ƙara haɗata ta jikinsa, tun tana ƙwace jikinta har ta daina, ƙamshin turarensa na ƙara shigarta.



A haka har bacci ya ɗauketa, Muby ya jima be samu baccin ba, dan wani daɗi na musamman yake ji, yana ganin baccin ya yi nisa ya fara lashe mata lips daga zaran ta motsa sai ya janye bakinsa, da haka har baccin ya ɗauke shi.

Misalin ƙarfe tara na safe suka fito cikin shirin komawa gida, Mandula ma a nan ta same su, ba ƙaramin farincikin ganin Afnan ta samu sauƙi ta yi ba, wanda har Bosho ya bata haƙuri kan abin da ya faru a baya, Malan kuwa sabon da ya yi da Muby ne ya sa shi jin kewarsa sosai, ba ƙaramin alkhairi Muby ya yiwa su Malan ba, har gidansu Mandula suka tafi tare da gaishe su, nan ma Muby ya zuba musu kuɗi, gurin da motarsu su Muby ke ajiye Malan da Bosho suka rako su, sannan Muby ya shaidawa Malan cewa nan da kwana biyu zai turo a rushe gidansa a gina masa wani, Malan kam har da kuka dan murna, a haka suka bar ƙauyen, tun da suka fara tafiya Afnan ta haɗe fuska, Mandula da ke bayan mota kuwa bacci ne ya ɗauketa har suka shiga ƙasar Sudan, a gidan sarauta suka sauka tun daga gate ake ihun murna, gaba ɓaya gidan ya ɗauka da dawowarsu Muby, Afnan kuwa part ɗin Alhaji ta nufa ba tare da Muby ya sani ba, masu aikin ne suka shige da trolyn kayansu, duk inda ya gifta sai dai kaga Dogarai na zubewa ana kwasar gaisuwa har ya shiga fada, anan ya sami Me martana da mutanen gari, sosai Sarki Ahmad ya yi farinciki da ganin ɗan nasa, musamman da ya samu labarin samun sauƙin Afnan, bayan sun gama magana da Muby ne ya koma part ɗin Mommy inda ya samu su Ameer zaune suna fira, cikin farinciki suka rungume shi, haɗaɗɗen idanunsa ya lumshe kafin ya ce "Kyawawan ƙannena fatar kuna lafiya?"

Ba su Ameera ba har Mommy ta sha mamakin ganin yanda Muby ya canza, sai smiling yake ga wani kyau da ya ƙara, har rige-rigen amsawa suke da lafiya ƙakau Brother, gefen Mommy ya zauna tare da gaidata, da fa'ara ta ce "Ya me jikin ina kuma ka baro ta?" Sai a lokacin ya fara dube-dube, "Wai bata shigo nan ba ne?"

"Aa bata shigo ba" Su Ameer suka faɗa.

Zumbur Muby ya miƙe har yana neman faɗuwa ya fice daga ɗakin, dirrect ɗakin Alhaji ya nufa dan ya san baza ta wuce can ba, ai kuwa a nan ya sameta zaune tana cin perpesun kifi, sai fira suke da da Alhaji suna dariya, ajiyar zuciya Muby ya sauke tare da sallama, Alhaji na ganinsa ya ɗaure fuska kamar be san da shigowarsa ba, itama Afnan ɗin haɗe fuska ta yi tana mai cigaba da cin kifinta, har ƙasa Muby ya rusuna yana gaishe da Alhaji amma ko kallonsa Alhaji be yi ba, abin da ya bawa Muby mamaki kenan, ya san cewa tabbas wani abun Afnan ta faɗa masa, wanda ya sa shi yin fushi.

"Alhaji sai gaisuwa nake amma shuru"

A fusace Alhaji ya ce "Bana son shashashanci Mubarak, ka fita daga ɗakinnan tun kafin na ɓata maka rai"

Sosai mamaki ya kama Muby dan ya san Alhaji baya kiran sunansa, kuma yana da wahala ya yi fushi irin haka, "Allah ya ba ka nasara idan har wani laifin nayi amun afwa, amma na zo na tafi da matata ne"

"Wace matar kenan?" Cewar Alhaji yana ɗaure fuska.
Itama Afnan ƙara haɗe fuska ta yi, marairaicewa Muby ya kuma yi kafin ya ce "Gata nan kusa da kai"

"Ashe ba ka da hankali Yarima, bayan ka yi mata saki uku shine ta zamo matarka, lallai ban taɓa sanin kai mutumin banza ba ne sai yau, tashi ka fita tun kafin na hukuntaka"

A tsorace Muby ya ɗago suka haɗa ido da Afnan, kawai sai yaga ta kawar da kai gefe.

"Yaushe hakan ta faru Gimbiya? wallahi ban saketa ba Alhaji"

"Ka gani ko Alhaji Babba, dama na faɗa maka zai ce be sakeni ba, haka ya rinƙa cewa har muka iso, kuma ya ce idan na koma gidansa sai ya kashe ni"

Zaro ido Muby ya yi yana mai dafe kansa, "Please Baby ki daina wasa da saki, babu wani sakin da ya shiga tsakaninmu"

Alhaji ne ya ce "Kai marar kunya wacece Babyn? au rashin kunya zaka kawo mun kenan, wadda ka ke cewa ka tsana yau ita ce ta zama abin so? gaskiyar Gimbiya da ta ce mun kasheta ka ke son yi, to baza ta koma ba tun da ka ƙarasa sakin da ya rage tsakaninku, kuma a gabanka zan aurar da ita ga wanda ya san darajarta"



"Aa Alhaji dan Allah kar ka mun haka, wallahi ban saki matata ba, kuma ina ƙaunarta har raina kar ku rabani da ita a karo na biyu"

"Kai dan ubanka dama mune muka raba auren farkon? yau naga iyashege"

"Koma menene naji amma ka bani abar ƙaunata"

"Anya babu abin da ke damunka kuwa? tashi ka fice ko kuma mu tashi mu ba ka guri"

Kamar Muby zai yi kuka haka ya bar ɗakin yana dafe kansa da ke sarawa, sai a yau ya tabbatarwa kansa cewar ba ƙaramin so yake yiwa Afnan ba, sai a yau ya san cewa duk son da ya yiwa Fadila ba gaskiya ba ne, aikin asiri ne dan ita soyayyar gaskiya ta daban ce, part ɗin Mommy ya koma, a lokacin su Ameer basa nan, zaune take kan kilishi tana shan kankana, wata Jakadiya kuwa na gefen ƙafarta tana danna mata ƙafar, ganin Muby ya shigo hannunsa a kai ne ya sa Jakadiyar miƙewa ta gaishe shi tare da fita daga ɗakin, da sauri Mommy ta gyara zamanta tare da faɗin "Yarima lafiya kuwa"

Kusa da ƙafafunta ya zauna yana mai faɗin "Mommy ban saketa ba, ban saki matata ba dan Allah kar ki bar Alhaji ya rabani da ita"

Cikin mamaki Mommy ta ce "Ka natsu ka faɗa min abin da ka ke nufi, waye zai rabaka da matarka kuma"

Da ƙyar ya iya sanarwa Mommy abin da ke faruwa, yana gama maganar ta yi murmushi irin nasu na manya, ganin tana murmushi ne ya sa Muby faɗin "Mommy kamar ba ki ɗauki maganar da muhimmacin ba"

"To ai naga ka yanke sauran igiyoyin ne, amma ka ke faɗin wai matarka"

"Yanzu Mommy kina nufin kema kin yarda da abin da Gimbiya ta ce?"

"Ƙwarai kuwa na yarda, saboda ka tsaneta dama can ba sonta ka ke ba, tashi ka je abinka kawai"

Ba ƙaramin tashi hankalin Muby ya yi ba, wai har Mommy kenan ta yarda cewar ya saki matarsa.

Jikinsa a sanyaye ya nufi part ɗinsa, ko Maimun be nema ba.

Afnan kuwa sai ƙara zuga Alhaji take, shi ko Alhaji duk a tunaninsa da gaske Muby ya saketa, shiyasa ma ya goya mata baya kan cewa zata zauna a nan gidan shi da kansa zai zaɓa mata miji, har part ɗin Ameera suka nufa ita da Alhaji, a lokacin Ameera na waya da Yusuf dan soyayya suke ba wanda ya sani sai Mommy kaɗai, tana ganin su Alhaji ta yi saurin kashe wayar tana murmushi.

Afnan kam haɗe fuska ta yi dan bata son raini ko kaɗan, tun kafin Alhaji ya ce wani abun Afnan ta ce "Idan ba damuwa ka kaini wani ɗakin dan ba zan iya kwana da ita ba"

Ameera kam ta san halin Afnan, kuma ta san cewa ita ce ta fara nuna ƙiyayya shiyasa Afnan ta ɗauka, "Haba matar Brother meye laifi dan kin kwana anan? tsoho me ran ƙarfe ka barta kawai wannan ɗakin ya ishemu tun da bed guda biyu ne sai ta kwana a ɗayan"

Alhaji ne ya ce "Tom shikenan mu kwana lafiya, Gimbiya ki daure ki kwana a nan, gobe idan Allah ya kai mu sai ki canza wani ɗakin"

Ɗaga kai Afnan ta yi alamun ta amince, sannan Alhaji ya musu sallama ya fice.

Tana ganin ya fita ta juya da niyar fita, Ameera ta yi saurin shan gabanta cikin cool voice ta ce "Matar Brother please kar ki tafi, na san cewa kina fushi da ni akan yanda na rinƙa yi miki, amma dan Allah ki yafe min" Afnan macece me sauƙin kai idan ka gane, kuma bata da riƙo sosai, murmushi ta sakar mata kafin ta ce "Shikenan amma ni ba matar yayanki ba ce, Maimun ce ta hannun damar ki"

Wani irin haɗe fuska Ameera ta yi tana cewa "Allah ya tsare ni, me Brother zai yi da karuwa"

"Karuwa kuma?"

Afnan ta tambaya, "Eh mana mu zauna na ba ki labarin abin da ta yi"

A kan sofa suka zauna Ameera ta kwashe duk abin da ya faru ta zayyanawa Afnan, ba ƙaramin girgiza Afnan ta yi da jin labarin ba, a lokacin Muby ya fito daga part ɗinsa zai tafi masallaci kamar an ce ya shiga ɗakin Ameera kawai ya ji zancen da suke yi kan matarsa Maimun, da mugun fusace ya daki ƙofar ɗakin ya shigo idanuwansa sun ƙanƙance, jikinsa har ɓari yake "Ameera abin da ki ka faɗa gaskiya ne ko wasa ki ke yi?

Please Login or Register in order to submit comment