Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa ya samu labari"


Gyaɗe kai Muby ya yi cikin gamsuwa, ba tare da ya amsa ba ya fara taku cikin izza yana mai barin gurin.

A babban parlourn ya sami Ameera zaune kusa da Mommy, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, gaishe shi Ameera ta yi amma ya yi mata banza, yana mai zama kusa da Mommy ya ce "Barka da wannan lokacin Mommy"

Kallonsa ta yi cikin alamun tambaya "Yawwa Yarima ya iyalan?"

Sai da ya ɗan haɗe fuska kafin ya ce "Alhamdulillah"

Mommy ce ta kuma cewa "Yarima lafiya kuwa?"

Kasa amsawa ya yi sai dai lumshe kyawawan idanunsa masu haske, "Magana nake ka yi shuru"

Haɗaɗɗun idanuwansa ya ɗago tare da faɗin "Afwan na shiga ɗan wani tunanin ne, Mommy dama........dama......" Sai kuma ya kasa ƙarasawa, "Dama me?"

Mommy ta faɗa.

"Dama Gimbiya ce ba lafiya shine nake son sawwaƙe mata, dan gaskiya ba zan iya zama da ita ba"

Cike da ɓacin rai Mommy ta ce "Amma ba ka da hankali, yanzu dan matarka ba lafiya shine za ka rabu da ita, anya kanada imani kuwa Yarima"

"Dan Allah ku fahimceni, ba haka nake nufi ba"

Kallon Ameera ya yi yana ƙara murtuƙe fuska ya ce "Ki cewa Jakadiya a haɗa mun karin kumallo yanzunnan, a ɗakin Alhaji"

Da to Ameera ta amsa tana barin gurin.

Duk zacen da ya rinƙa zubawa Mommy kasa amsa masa ta yi, ta san cewa a baya bata son haɗin Gimbiya da Yarima amma yanzu ta rasa dalilin son haɗin, daga ƙarshe ma tashi Mommy ta yi da niyar barin gurin, miƙewa Muby ya yi yana ɓata fuska kamar zai kuka ya ce "Mommy please ki tsaya mu gama magana".

"Okay me ka ke son na ce kana so na raba auren ne? to hakan baza ta taɓa faruwa ba, duk da cewar ban san rashin lafiyar da ke damunta ba, haƙiƙa ba ƙarami ba ne, idan har baza ka iya jinyarta har ta warke ba ka kawo mun ita zan kula da ita har zuwa samun sauƙin ta"

Tana gama faɗin haka ta bar parlourn, shi ko Muby Fada ya nufa gurin me martaba jiki a sanyaye, sun jima suna tattaunawa kan lamarin kafin ya koma ɓangaren Alhaji, shima abinci kawai ya ci be wani jima ba ya bar gidan.



Motocin da ya gani masu masifar kyau da tsada ne ya bashi mamaki, ba tare da ya san abin da ke faruwa ba ya nufi part ɗin Maimun, kamar yanda ya barshi haka ya same shi, wannan karon ma har da tarin tarkace, zama kan kujera ya yi yana mai dafe kansa, kamar an tsikare shi kuma ya haura sama da sauri har yana haɗa steps, yana shiga room ɗinsa ya buɗe wata loka ya ɗauko sigarinsa da ya mance ranar da ya sha, a gefen bed ɗinsa ya zauna yana mai kunnawa, har wani bubbuga kai yake tsabar shigar da take masa, sai da ya sha guda uku kafin ya shige toilet, be wani jima ba ya fito duk gashin gansa ya jiƙe da ruwa, tawul ya sa yana gogewa maganganun da suka yi da Mommy ne ka yawo a ransa, nan take kuma ya tuna da Mandula me aikinsu ta ce akwai kawunta da zai iya maganin matsalarsu.

Fitowa ya yi daga part ɗin ya nufi ɓangaren Afnan, mutane ya samu zazzaune a parlourn, shi dai babu wadda ya sani a cikinsu, wata matashiya ce da kuma Dattijuwa, sai wasu Kuyangi kusan su goma sanye cikin kaya iri ɗaya a can baya kaɗan.

Murmushi matashiyar ta yi tare da faɗin "Mom kinga Yarima ya dawo"

Cikin mamaki Muby ya zauna tare da gaishe da wadda aka kira da Mom fuskarsa na nuna alamar tambayoyi.

Amsawa ta yi cike da fara'a ta ce "Na san kana tunanin inda ka sammu ko? da farko ni matar sarkin Cameroun ce, Mahaifiya ga yarinyar da ka tashi aure a lokacin baya wato Fadila, wannan kuma ƴata ce Nabeelah na san cewa ka samu labarin abin da ke faruwa, to ko yanzu ma magana ce ke tafe da mu idan ba damuwa zamu iya farawa"

Jinjina kai Muby ya yi cikin ɗan sakin fuska ya ce "Masha Allah ba damuwa sannunku da zuwa, bari na sa a kawo muku abun taɓawa"

Saurin dakatar da shi Mom ta yi da faɗin, "Aa da ka barshi, dan a halin yanzu a ƙoshe mike"


Kallonsa ya maida kan Nabeelah ya ce "Har da ke ma?"

Ƙara faɗaɗa murmushinta Nabeelah ta yi, dan tun ranar da ta fara ganinsa take jin son shi har ranta, amma tana samun labarin ya yi aure kuma Fadila na son shi, yasa ta janye jikinta, dan ta san ba sa'arta ba ne"

"Eh mun gode sosai, ka barshi kawai".
Sannan ta kalli Kuyangin da ke tsaye ta yi musu alamar su fice, cikin biyayya suka bar parlourn.

Shuru na ɗan wani lokaci kowa ya ɗauka, kafin Nabeealah ta sauke a jiyar zuciya ta ce "Da farko dai na san ka samu labarin abin da ya faru da Fadila, to akwai wani sirrin da ba ka saniba, wanda zai iya rusa dukkan farincikinka, na san cewa zaka yi mamakin wannan wanne irin sirri ne, to dalilin sirrin ne ya sa muka zo har ƙasarku domin na sauke nauyin da ke kaina" Nabeelah ta ƙarasa maganar tana buɗe handbag ɗin da ke genfenta me kyau ta ciro wani ɗan ƙaramin kasko, a ƙasa ta aje kaskon kafin ta buɗe marfinsa cikin ƙarfin hali, daga Mom ɗinta har Muby sun cika da mamakin abin da ke shirin faruwa, Nebeelah kuwa murmushi ta kuma yi kafin ta ce "Wannan shine asirin da Mahaifiyar Fadila ta yi maka saboda ka auri ƴarta, idan baza ka mance ba farkon haɗuwarku da Fadila, ta ce maka ɓarayi ne suka sace ta har suka kawota nan garin, to ba ɓarayi ba ne, gaskiyar lamari shine akwai wani taron biki da suka zo nan ƙasar, a lokacin ta fara ganinka kuma ta ji babu wani namijin da take so sai kai, daga nan ta yi bincike a kanka kuma ta samu labarin ka yi aure, lokutan baya da suka wuce an yi auren ƙanwarka Munirat wanda dalilin hakan ya sa matarka Gimbiya zuwa nan ƙasar ita da iyayenta, tun da Fadila ta samu labarin Gimbiya ta shigo ƙasar ne ta shirya cikin kaya irin na talakawa ta shigo, to kayan da ke jikinta Mahaifiyarta ce ta bata wanda suka ɗauko daga gurin boka, kuma bokan ya tabbatar musu cewar idan har ku ka yi ido huɗu da Fadila cikin shigar tabbas zaka fara ƙaunarta, a ranar da Gimbiya ta tafi shopping ne Fadila ma ta nufi gurin, saboda ta yi tsammanin a tare ku ka tafi, sai kuma bayan ta tafi ne taga saɓanin hakan, wanda har Gimbiya ta wulaƙantata tare da tozarci, bayan sun wuce ne Fadila ta nufi babban gurin Shopping ɗinka, sai kuwa aka yi sa'a ka shigo duba masu aikin gurin, a nan ne ka ganta cikin shigar talakawa kamar wata mahaukaciya, har take ce maka ɓarayi ne suka sace ta, daga lokacin ka ji duk duniya babu wadda ka ke so sai ita"

Tsagaitawa da labarin Nabeelah ta yi, kafin ta cigaba da faɗin "A halin yanzu rashin lafiyar Gimbiya Mahaifiyar Fadila ce ta tura mata shi, kai kuma yanzu haka akwai asirin da ke jikinka wanda zai sa ka ji Gimbiya ta fita ranka, zai sa ka rinƙa jin ƙyanƙyamin ciyon da ke jikinta daga ƙarshe ka saketa, wannan shine asirin da aka yi maka"

Nabeelah ta nuna kaskon da ke ajiye a ƙasa, har Muby ya kai hannu zai taɓa ta yi saurin ce masa "A a kar ka taɓa, idan har ka taɓa akwai matsala yanzunnan zan ƙona asirin"

Ashana ta fidda a jakarta ta kunna wuta ciki, kusan mintuna biyar kafin wani irin hayaƙi baƙiƙirin ya fito, lokaci ɗaya Muby ya dafe kansa, kamar wanda aka tsikara kuma ya miƙe tsaye cikin ɗimauta, Mom ce ta ce "Yarima koma ka zauna"

Cikin sanyin jiki ya koma inda ya tashi yana karanto addu'oi a zuciyarsa, cike da tausayawa Mom ta kuma ce "Haƙiƙa Asabe ta cutar da rayuwarku, amma Allah baya bacci, kuma zai bi muku haƙƙinku ko ba anan duniya ba"

"Kuma babban abin tashin hankalin shine na kasa gane inda suka aje asirin da aka yiwa Gimbiya" Cewar Nabeelah tana kallon Yarima.

Shima kallonta ya yi kafin ya ce "Na gode sosai da ƙoƙarinki, insha Allah gobe da safe zamu tafi da ita gurin wani malami, ina sa ran za'a dace"

Sosai Nabeelah ta ji daɗin yanda Yarima ya dawo hayyacinsa.

Mom ce ta miƙe tana faɗin "Mu zamu koma Allah ya ƙara sauƙi, lokacin da muka shigo Gimbiya na ciki dan bamu samu ganinta ba, muna fatar Allah ya ƙara tsarewa"

Da ameen Muby ya amsa yana ƙara godiya, har inda jerin motocinsu suke ya rakasu kafin ya dawo part ɗin nata, yana shiga ɗakinta ya haura cikin ɗokin son ganinta, a kwance ya sameta tana bacci kan sofa duk jikinta ya lalace da ƙurajen, da alama tana sosa su shiyasa suka ƙara ɓacewa, cikin tausayawa ya matsa yana mai tallofa kanta ya ɗora saman cinyarsa, wata irin ajiyar zuciya Afnan ta sauke tare da ƙara ruƙunƙume shi, ba zato ba tsammani ya ga kawai ya ɗora hannunsa kan fuskarta yana shafawa, sai kuma ya yi saurin ɗauke kai daga barin kallonta, daidai lokacin da ta ware idanunwanta kan fuskarsa, wannan karon kasa motsi ta yi, sai zuba masa ido kawai tana lumshe su a hankali.

"Sannu Baby insha Allah za ki samu lafiya"

Duk da cewar bata san me sunan Babyn da ya kirata ke nufi ba, amma hakan be hanata murmushi ba, sosai tausayinta ya ƙara shiga zuciyarsa, kan bed ya maidata yana mai gyara mata kwanciya, amma abin mamakin shine ta kasa cewa komi, kuma ta kasa magana balle ta miƙe da ƙafafunta, cikin tsoro da damuwa ya ɗagata tsaye dan ya ga ko zata iya tsayuwa, amma sai ganin ya yi ta ƙara langaɓewa kamar kayan wanki, gabansa ne ya cigaba da dukan uku-uku, kwanciya ya gyara mata yana mai fita ɗakin da sauri, be jima da fitar ba ya dawo tare da Mandula, cikin bada umarni ya ce "Ki haɗa mana kayanmu a troly, ki fita da shi waje zan fito da Gimbiya yanzu"

"Tom yallaɓai" Cewar Mandula tana nufar ƙayataccen Wadrop ɗin da ke gefe.


Cikin ƙanƙanin lokaci suka shirya, a bayan mota ya kwantar da ita ya nufi part ɗin Maimun dan yi mata sallama, amma babu kowa a ciki, duk inda ya san zai ganta ya duba amma be sameta ba, dan haka ya koma gurinsu Mandula da Afnan da ke mota suka bar gidan.


Tun a hanya ya sanarwa Me martaba da Mommy zancen tafiyarsu, amma be faɗawa Mommy abin da ke damun Afnan ba, dama daga Ameer sai Me martaba ne suka san da lamarin.


Sai da suka fita har ƙasar Sudan, ba ƙaramar tafiya suka sha ba, wani ƙauyen da ke can wajen garin me suna Kalfu suka sauka, Mandula kuwa ta yi musu jagora har gidan Kawun nata me suna Malam Abdulsallam, shahararren Malamin addini ne me zaman kansa, cikin fara'a ya tarye su tare da basu kyakykyawan masauki, Afnan kuwa wani ɗakin aka kaita me ƴar ƙaramar katifa sai shimfiɗa da ke tsakar ɗakin, babu laifi ɗakin akwai ɗan sanyi ga kuma tsafta, Malam Abdulsallam shi ɗaya ke zama a gidan kasancewar matarsa Bushira Allah ya yi mata rasuwa shekarun baya, sai yaronsa ɗaya me suna Bosho yanada shekaru ashirin da takwas, tun da su Muby suka isa gidan yake kallon tsarin ko'ina amma sai ya kasa sakewa, dan yana ganin ba zai iya doguwar rayuwa a nan ba, Mandula kuwa ɗakin da aka kwantar da Afnan ta koma dan ta basu wuri su tattauna.


Bayan Muby ya gama ba Malan labari ne, ya jinjinawa al'amarin, sannan ya ce "Insha Allah zan yi iya ƙoƙarina, zuwa ajima akwai ruwan addu'ar da za'a zuba cikin ɗakin da take, daga lokacin da ka watsa ruwan addu'ar babu wanda zai ƙara shiga ɗakin har ranar da zan kammala addu'oi"

Cikin gamsuwa da maganarsa Muby ya ce "Shikenan amma har tsawon wani lokaci ne za'a ɗauka?"

Murmushi Malan ya yi irin nasu na manya kafin ya ce "Haƙiƙa kana ƙaunar wannan matar taka, wanda har idanuwanka sun kasa ɓoyewa balle kuma bakinka, kar ka damu ba wani dogon lokaci ba ne, idan har Allah ya yarda, ka san shi sauƙi daga Allah ne"

"Hakane Allah ya bada sa'a" Cewar Muby yana sunne kai ƙasa, ya kasa gazgata zancen Malamin, a kan cewa wai yana son Gimbiya, shi be taɓa jin sonta a ransa ba.


Da yamma misalin ƙarfe biyar Malan ya nufi ƙofar ɗakin da Muby suke, sai da ya fara sallama kafin aka bashi umarnin shiga, Muby na zaune kusa da Afnan, kanta na saman ƙirjinsa yana bubbuga bayanta a hankali, robar furar da aka kawo musu Malan ya kalla sai yaga ba laifi sun sha furar, hamdala ya yiwa Allah yana mai miƙa masa ruwan addu'ar.

Karɓa Muby ya yi yana godiya, kafin ya ce "Yanzu ne zan zuba?"

"Eh yanzu zaka zuba, akwai wani ɗaki da ke kusa da wannan idan ka gama sai ka koma ciki, saboda aiki na sheɗanu za su iya komawa kan duk wanda ke kusa da su"

A hankali ya kwantar da ita, yana mai miƙewa tsaye, Malam Abdulsallam kuwa ya fice daga ɗakin, har Muby zai fara watsa ruwan addu'ar sai ya tsaya, dan ya san cewa daga yau be san ranar da zai sake ganinta ba, a hankali ya rusuna gabanta tare da sakar mata kiss a kumatu, Afnan kam bata san duniyar da take ba, sai hawayen da ya zubo gefen idonta, ganin cewa shima zai iya hawayen ne yasa shi tashi tsammmm ya fara aikin zuba ruwan addu'ar, tun kafin ya gama Afnan ta fara wani gurnani kamar macen zaki, sai fizge-fizge take amma ta kasa miƙewa daga inda take kwance, nan take hayaƙi ya fara baibaye ɗakin, da sauri Muby ya fice yana mai zaman dirshan a bakin ƙofar, idanunsa sun gama yin ja hankalinsa kuwa duk ya tashi.


Jin an taɓa shi daga baya ne yasa shi ɗago idonsa ya sauke kan Malan, cike da ƙarfin gwuiwa Malan ya ce "Yarima ka kwantar da hankalinka, wannan alamu ne na nasara, idan har ba zan iya da Aljanun da ke jikinta ba, da baza ka ga wannan baƙin hayaƙin ba"

Ajiyar zuciya Muby ya sauke kafin ya ce "Amma ta yaya zata iya rayuwa ba tare da abinci da kuma kawar da wata lalurar ba?"

"Kar ka damu da wannan, a halin yanzu ba ita ba ce, kuma ko zata yi shekara a haka babu abin da zai sameta dan bata ci abinci ba, shine dalilin wannan ruwan addu'ar da na baka"

Sai da Malan ya kwantar masa da hankali kafin ya shaida masa Mandula ta tafi gidan iyayenta har lokacin da za su tashi komawa, kasancewar a ƙauyen iyayen nata suke.


Suna cikin haka Bosho ya shigo gidan yana tangaɗi alamun a buge yake, sai surutai ke fita bakinsa, Mahaifinsa kuwa ya sha zagi, ran Muby ne ya matuƙar ɓaci jin yanda Bosho ke zagin Malan Abdulsallam, amma sai ya danne zuciyarsa gudun janyo abin da zai sa ran Malan ɗin ya ɓaci, sai da ya gaji da zage zagensa sannan ya faɗi a gurin yana sheƙa amai, Malan ne ya girgiza kai yana mai faɗin "Wannan shine ƙaddarata, Bashir ne yarona na farko amma be gaji halina ba, in taƙaice maka har rago ya siya ya canzawa kansa suna zuwa Bosho, wato sarkin tantirai na ƙauyennan, na rasa yanda zan yi da shi"

Muby ne ya ce "Gaskiya akwai rashin jin daɗi, amma insha Allah zai daina komi lokaci ne"

Daga haka suka cigaba da fira har aka kira sallar magrib, tare da Muby suka tafi masallacin da ke ƙofar gidan, sai bayan isha suka dawo, tun a zauren gidan suke jin ihun Mandula na kiran sunan Gimbiya kamar zata ƙarar da muryarta, Malan ne ya ce "Wannan kamar muryar Mandula, ko ta zo gidan ne?"

Saurin shiga daga ciki Muby ya yi yana faɗin "Ita ce ina ganin ta shigo bayan fitarmu"

A bakin ƙofar ɗakin da Afnan ke ciki, Mandula ce tsaye sai rusa kuka take hannu a kai, da sauri Muby ya ƙarasa yana tambayar abin da ke faruwa, cikin kuka Mandula ta nuna masa ƙofar ɗakin Afnan da ke rufe ta ce "Bosho ne ciki yana ƙoƙarin yiwa Gimbiya fyaɗe"


A mugun fusace Muby ya miƙe jikinsa har rawa yake idanunsa sun gama rinewa kamar garwashin wuta ya nufi ƙofar ɗakin.



ƘASAR SUDAN
...........................
Ameer kam ya shiga ruɗu da tashin hankali, dan yau kwana biyu kenan be yi waya da Husna ba, kuma a yau Ashwan ke faɗa masa ya taya shi neman Number Husna, sosai ya ƙara ruɗewa dan ya san idan ya ce zai yi aure a yanzu baza a bari ba, kuma yana tsoron Ashwan ya karɓe masa Husnarsa, abar ƙaunarsa dan ba ƙaramin so ne ke tsakaninsu ba.


Ba tare da sanin Muby ya yi tafiya ba Ameer ya ɗauki ɗaya daga cikin motocin gidan ya nufi gidan Brothern nasa, tun da ya fara Driving maganganun Ashwan ke dawo masa sabo a ransa, lallai dole zai faɗawa Muby abin da ke faruwa tsakaninsa da Husna dan ba zai zuba ido a raba shi da ita ba, a haɗaɗɗen harabar gidan ya yi pearking, ya jima zaune yana tsoron shiga daga ciki, dan be san yanda Muby zai ɗauki lamarin ba, ƙila ma ya ce ya barwa Ashwan kawai, jikinsa a sanyaye ya fito daga motar Dogaran da ke gidan kuwa na gaishe shi cikin girmamawa, fuskar Ameer a sake yake amsawa har ma yana tsokanarsu, dan Ameer akwai son wasa baya da girman kai ko kaɗan.


Part ɗin Afnan ya wuce kai tsaye, har parlourn amma Kuyangin da ke mata aiki ne kawai ya samu, ɗaya daga cikinsu ke shaida masa ai Yarima Muby ya yi tafiya shi da Gimbiya, cikin mamaki Ameer ya bar part ɗin dan be da labarin tafiyar ta su.

Har ya wuce ƙofar da zata sada shi da part ɗi Maimun sai kuma ya dawo da baya, kamar kar ya shiga amma sai wata zuciyar ta ce ka shiga mana ai gidan yayanka ne, lokacin da ya shigo parlour ba kowa a ciki, ya ɗan jima a zaune jiran ko zata fito amma shuru, hakan ya sa shi haurawa sama tun daga steps yake jin wani irin nishi kamar ana dafa mutum, sai kuma ƙarar dukan abu daga cikin ɗakin Maimun, already Ameer be san ɗakin waye ba, dan be taɓa shiga ɓangaren nata ba, hannun ƙofar ya kama yana mai buɗewa dan ganin abin da ke faruwa.




*A yi sharing saboda Allah, a baza sharhi fiye da yanda aka saba, ina ƙaunarku sosai godiya me yawa, duk wadda ta karanta shafinnan dan Allah ta yi min addu'ar Allah ya cika min burina na alkhairi da kuma al'umma baki ɗaya, ku kasance tare da alƙalamin Asmy ta Hydar uwargida gun Hydar ƴar guda ɗaya, Sayyada ta Sayyadi* 😊😊


*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 20




Wani irin bugawa ƙirjin Ameer ya yi wanda ya sa shi dafe handle ɗin ƙofar da ƙarfin tsiya, jikinsa na rawa idanuwansa kuwa sun zazzaro, Maimun ya gani kwance su uku kan bed ɗin aurenta na sunnah, ita da ƙawarta Hajara sai kuma wani tsoho wanda zai kai shekaru fiye da arba'in, amma kana gani ka san yana da mafisar kuɗi, dan jin daɗi da hutu ya bayyana a jikinsa.

Ba komi ya ƙara tadawa Ameer hankali ba sai ganin cewa gaba ɗayansu ba kaya a jikinsu, idan Alhajin ya gama amfani da Maimun sai ya komawa Hajara, idan kuma suka gama sai a ɗora tsakanin Maimun da Hajara, gaba ɗaya basa cikin hayyacinsu, har Ameer ya jima a tsaye gurin, daga ƙarshe ya ja ƙafarsa ya bar part ɗin jiri na ɗibarsa, tabbas idan aka ce masa Maimun mazinaciya ce ko aka ce masa ƴar lessbian ce ba zai taɓa yarda ba, amma yanzu gashi ya gani da idanunsa, kamar wanda aka tsikara kuma ya koma ciki da sauri, ya kai kusan mintuna biyar kafin ya fito, be wani tsaya komi ba ya fice daga gidan zuciyarsa na bugawa, tun da Ameer yake be taɓa ganin tashin hankali da masifa irin na yau ba, matar aure mazinaciya kuma ƴar lessbian, a ɗakin aurenta ta kawo garde wanda ba muharraminta ba, yana cikin Driving ne ya danna layin Muby amma sai ya ji a kashe, ajiye wayar ya yi yana mai komawa gefen titi ya pearker motar, wani irin gumi ne ke karyo masa alamun tsoro duk ya bayyana kan fuskarsa, kamar daga sama ya ji ana bubbuga glass ɗin motar, idanuwansa ya sauke kan Yusuf da ke tsaye yana murmushi, da sauri Ameer ya ƙaƙaro murmushin shima yana gaida Yusuf tare da sauke glass ɗin motar.


Yusuf ne ya ce "Ameer lafiya kuwa, ina zuwa haka?"

"Brother Yusuf dama na fito gidan Yarima ne, amma sai na samu baya nan wai sun yi tafiya da Gimbiya amma bansan ina suka tafi ba"

"Eyyeh ai wani ƙauye ne ta can bayan gari, ya kai Gimbiya gurin wani malamin addini, saboda rashin lafiyarta, ɗazu ya kirani yake sanar min zasu tafi"

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke kafin ya ce "Mu je na rage maka hanya ko da mota ka fito ne?"

Yusuf ne ya ce "Aa je abinka da su Mami muka fito, motarmu na a can gefen"

Sallama suka yi kafin Ameer ɗin ya ja mota yana barin gurin.


Tun da Ameer ya isa gida ya kasa zaune ko tsaye, tunaninsa ɗaya ne shin ya faɗawa su Mommy abin da ke faruwa ne ko ya bari sai Muby ya dawo, yana cikin tunanin ne wayarsa ta fara ƙara, ganin sunan Aunty Munirat ne ya sa shi ɗagawa yana faɗin "Mun yi fushi gaskiya"

Daga can ɓangaren ƴar dariya Munirat ta yi tana faɗin "Ka fito ina bakin gate, na yi muku zuwan bazata"

Dariya Ameer ya kwashe da ita kafin ya ce "Kin mance ranar ma haka ki ka mun, kawai kinsa na rinƙa yawon nemanku ashe wasa ki ke yi"

"Tom yau ba wasa nake ba ka fito ka gani"

"A a gaskiya ba zan fito ba, sai na fara ganin Dogarai sun shigo da kayanki" Tun kafin ya gama rufe baki yaga ana shigowa da troly da kuma kayayyaki iri-iri, sai Munirat da ke bayansu tana sakarwa Ameer murmusi, Ameer kam kasa motsawa ya yi dan kamar mafarki ya rinƙa ganin abin, Ameera da ke saukowa kan step ne ta sheƙo da gudu tana mai rungume Munirat cikin tsananin farinciki, dan rabonsu da juna tun ranar aurenta.

Sosai gidan ya ɗauka da zuwanta, har Fada ta tafi gurin Abban nata, sun daɗe suna fira kafin ta tafi ɗakin Alhaji, bata samu ganin Mommy ba sai yamma.

A ɗakin Mommy ta koma suka cigaba da fira, tun da suka fara firar Ameer ya kasa cewa komi, Munirat ce kawai ta gane yana cikin damuwa, ganin hakan ya sa ta miƙe cikin sakin fuska ta ce "Mommy ina zuwa please, Ameer zo ka rakani wani gurin"

Mommy ce ta ce "Ina zuwa kuma?"

"No a cikin gida ne ba waje zamu tafi ba"

Munirat ta faɗa tana kama hannun Ameer suka bar ɗakin.

A can gurin shaƙatawar da ke gefen Fada suka tafi, shi dai Ameer kallonta kawai yake be san dalilin kiran nasa ba, sai da suka samu gurin zama kafin ta maida kallonta kansa cikim haɗe fuska babu alamun wasa ta ce "Ameer ina son ka faɗa min abin da ke damunka, bana son ka ɓoye mun komi"

Cikin mamaki ya ɗago yana kallon Auntyn tasa, itama shi ɗin take kallo jiran

Please Login or Register in order to submit comment