Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

YA ƊAU GANGARA A HALIN YANZU*



*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*







P. 17




*NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE GA TEAM ƊIN GIMBIYA AFNAN, WANNAN SHINE CIKON ALƘAWARIN DA NA YI MUKU KUMA SHINE CIKON PAGE NA UKU DA NA MALLAKA MUKU, KU YI YANDA KU KE SO DA SHI*






Sosai motocin ke gudu kan babban titin da ke garin, sai da suka yi tafiya me nisan gaske kafin yaron ya nuna musu wata hanyar da zata fitar da su ta wajen garin, daga nesa kana hango wani tsararren gida shi ɗaya a jejin, nesa kaɗan da gurin suka tsaya kafin ɗaya daga cikin Dogaran ya buɗe masa mota.

Cike da ƙasaita ya fito tare da gyara zaman rawaninsa, gaba ɗaya mutanen da ke motar fitowa suka yi tare da mara masa baya, har ƙofar da zata sada su da gidan yaron ya nuna musu, ba ƙaramin tashin hankali Muby ya shiga ba ganin yanda gidan ke ɗauke da ƙofofi da yawa, a matsayinsa na Yarima me jiran gado be san da wannan taɓarar da ake aƙasarsa ba, duk inda suka shiga babu wani haske sosai har suka shigo harabar gidan, daga cikin wani ɗaki suke jiyo sautin waƙa na tashi da kuma surutun mutane, nan take Muby ya bada umarnin a zagaye gidan, ba tare da ɓata lokaci ba Dogarai kusan su talatin suka zageye ko'ina na gidan, da mugun ƙarfi Muby ya daki ƙofar ɗakin, gaba ɗaya mutanen da ke ɗakin samari su biyar ne a zazzaune kowannensu da gajeren wando, kana ganinsu ka san a buge suke tiliss, ga kayan shaye-shaye a zube, ɗaya daga cikinsu ne ya ce "Kai waye haka kamar Yarima"

Duk da cewa a buge suke amma sai da tsoro ya mamaye su, ƙafafunsu kuwa basa iya ɗagawa tsabagen buguwar da suka yi.

Sai a lokacin Muby ya lura da mataye da dama a ɗaɗɗaure, wasu sun suma wasu kuma an gama amfani da su suna kwance cikin mawuyacin hali, wasu ma kana ganinsu ka san sun saba da harkar, a can ɗaure ya ga Afnan duk ƙafa da hannayenta a ɗaure, ba ƙaramin tashi hankalinsa ya yi ba ganin kamar bata numfashi, cikin tsawa ya ce ma sauran Dogaran "Ku kama matsiyatan nan, babu wanda zan ragawa a cikinsu"

Cikin sauri aka cafke matasan tare da yin waje da su, matayen kuma kuncesu aka yi dan wasu ɗaurin da ke jikinsu har ya fara cin naman jikinsu.

Cike da tausaya Muby ya tallafo Afnan yana mai yin waje da ita.

Sai da aka fito da kowa da ke gidan sannan Muby ya bada umarnin a sakawa gidan wuta, haka ko aka yi, a bayan mota ya sakata shima ya shiga tare da ɗora kanta saman cinyarsa, hannunta ya shiga murzawa dan yana jin yanda jikinta ya ɗauki zafi, Dirrect Hospital ɗinsa suka nufa cikin gaggawa aka shiga da matayen har da Afnan wadda a halin yanzu babu abin da ke motsi a jikinta.

Office ɗinsa Muby ya nufa hankalinsa a tashe, kasa duba Afnan ɗin ya yi da kansa dan jikinsa ya fara rawa ransa ya gama ɓaci, toilet ɗin da ke cikin Office ɗin ya shiga, ya jima a ciki kafin ya fito.

Sallaya ya shimfiɗa tare da kabbarta sallah.

Bayan ya gama ya ɗora da karatun Alqur'an, be jima da karatun ba wata Nurse ta shigo ɗauke da takaddu a hannunta, sai da ya kai aya kafin ya rufe Alqur'an.

Cikin girmama ta ce "Sir mun gama bincike a kan ƴammatan da aka kawo, and result ya tabbatar cewa gaba ɗaya matan an yi musu fyaɗe dan har da masu ciki ma"

"What gaba ɗayansu?"

Muby ya faɗa yana miƙewa daga zaunen da yake.

Jikin Nurse ɗin na rawa ta ce "Yes Sir haka binciken ya nuna, zaka iya ƙara bincikawa idan ba ka gamsu ba"

Da ƙarfin tsiya ya kai naushi kan wani glass Cup da ke kan Fridge nan take ya fashe, idanunsa duk sun rine kamar garwashin wuta, tabbas ya san cewa binciken Nurse Faridah gaskiya ne dan bata wasa da aikinta, "You can go now"

Cewar Muby yana karɓar takaddun da ke hannunta.


A ranar kasa bacci ya yi kuma be iya zuwa duba Afnan ɗin ba, matasan da aka kama kuwa masarauta aka tafi da su, shi ko yaron da ya kai su jejin gidansu a ka maida shi tare da kyauta me yawa ga iyayensa, a Hospital ɗin nasa ya kwana, tun ƙarfe shida na safe Nurse Faridah ta nufo Office ɗin nasa, ta jima tana nucking har ta juya zata koma ta ji ya ce "Come in"

A sukwane ta faɗa tana mai faɗin "Morning Sir please marar lafiya ɗaya ta hargitsa gaba ɗaya ɗakin ina ganin ta samu matsalar taɓin hankali"

Muby na jin haka ya san cewa Afnan ce, ba tare da ya amsa mata ba ya ɗauki key ɗin motarsa yana mai ficewa daga Office ɗin.

Tun daga bakin ƙofa yake ganin yanda take buge-buge da jefe-jefe tana faɗin "A a zafi Mommah, A a zafi Mommah bana so" Allah ya sa ma sun ɗaure mata ƙafafunta shiyasa bata samu damar tashi ba, cikin kiɗima Muby ya matsa daga inda take tana ganinsa ta faɗa jikinsa tare da rushewa da kuka, sosai take kukan tana faɗin zafi Mommah, shima hugin ɗin nata ya yi a karo na farko da ya ji tsananin tausayinta ya gama kama shi, ba Nurse Faridah ba hatta mutanen da ke ɗakin sun masifar shan mamaki ganin Muby rungume da mace a jikinsa kuma wadda ke ciyon hauka, sai a lokacin Nurse Faridah ke tunanin ko ita ce Gimbiya Afnan da aka ce ya aura, to idan ita ce ya aka yi ta kamu da ciyon hauka, bata gama tunanin ba ta ji muryar Muby na faɗin "Zo ki kunceta, sauran matan da suka rage zan turo a maida kowacce gidansu"

Cikin biyayya ta ce "Okay Sir"

Ba tare da ɓata lokaci ba Nurse Faridah ta banye mata igiyar da aka ɗaureta, cakkk Muby ya ɗaga Afnan yana mai ficewa waje da ita, duk inda ka duba kallonsu ake da mamaki wasu da dama na cewa matarsa ce wasu kuwa na cewa ƙanwarsa ce, a gaban wata arniyar mota ya tsaya sannan ya sakata a baya tare da rufe motar gudun kar ta fito.

Ya jima yana waya kafin ya shiga yana mai barin harabar Hospital ɗin, ba ƙaramin arziƙi ya yi ba dan Afnan ta kasa zama cikin motar sai tsalle tsalle take tana kuka har suka isa gidan, nan take gate ɗin ya wangame.

Sosai gidan ya ƙara kyau dan masu aiki na kan aikinsu, sai da ya parker motar sannan ya buɗe mata amma ta kasa aje ƙafar a ƙasa, lumshe idanunsa ya yi yana mai cije lips ɗinsa da ƙarfi, wani irin zafi zuciyarsa ke masa kamar zata tsage, ɗaga ta sama ya yi yana mai nufar part ɗinsu, a toilet ya direta dan ba ƙaramin datti jikinta ya yi ba har wani tsami take, tana ganin ya fara cire mata kaya ta koma da baya tare da rushewa da kuka, shi dariya ma ta bashi ganin yanda take matse ido, sai da ya fara haɗa ruwan zafi sannan suka fara kokawar cire kayan jikinta, duk ta cukyuikuye masa kaya, dole ta sa shi cire nasa ya rage daga shi sai boxer, gashin ƙorjinsa ya kwanta lufff har wani sheƙi yake yi.

Da ƙyar ya samu damar cire kayan nata, ihu ta fara tana birgima a cikin kwamin wankan, zafin ruwan na shiga ta ƙasanta, duk ta riƙe masa wuya kamar zata ɓalla sa, yanda take jijjiga jikin nata yasa duk yanayinsa ya canza, sai da ya gama yi mata wankan kafin shima ya yi nasa, a lokacin Afnan na gefe tana kallon kanta cikin madubin da ke toilet ɗin sai dariya take, tawul ɗin da ya ɗaura mata ma jifa da shi ta yi, ya jima yana wankan kafin suka fito a tare, ba ƙaramar wahala ya sha ba kafin ya samu damar shiryata cikin wando da riga marar nauyi pink colour kayan sun masifar karɓarta, shi da kansa ya gyara mata gashin kanta, kafin ya gama shiryawa ta lalata ɗakin zanin gadon ma a ƙasa ya tsince shi, shima cikin wando da rigar ya shirya blue and black me kyau musamman rigar da ke ɗauke da tambarin Yarima a baya, da gudu Afnan ta ɗane masa tana dariya, har sai da turaren da ke hannunsa ya tashi faɗuwa.

A fusace ya ce "Malama wannan haukar taki ni ki ke ba wahala 'im tied wallahi"

"Hahahha..... Mommah menene wahala?"

Afnan ta faɗa tana yakuce masa hanci, "Washhhhhh, wannan masifar da me ya yi kama"

Turaren ya fesa musu yana mai ɗorawa kan mirrow, da dabara ya samu damar fita ya shaidawa Mandula ta ɗora musu abinci, be koma ɗakin ba ya nufi part ɗin Maimun dan ya duba ta, tun daga parlourn ya fara haɗuwa da kwalaben giya da kwalayen sigari, wata irin faɗuwar gaba ce ta zo masa, gaba ɗaya parlourn ya gama lalacewa da ƙazanta, duk ɗakunan da ke part ɗin ya duba amma babu Maimun babu alamunta, mamakin inda ta tafi yake amma sai ya basar yana mai saukowa cike da ƙasaita, a rayuwarsa ya tsani ƙazanta nan take zai fara jin yanayin jikinsa na canzawa, kwalaben kayan mayen da ke nan ya kalla da kyau yana girgiza kai, cikin mugun haushi ya koma part ɗin Afnan, a parlourn ya sameta tana wasanni kamar wata ƙaramar yarinya sai watsi take da pilows ɗin, kan kujera me zaman mutum ɗaya ya zauna, tare da danna kiran me martaba, sosai suka yi magana kan ciyon da ke damun Afnan, domin Muby ya tabbata masa cewar hauka ce ba Aljanu ba, bayan sun yi sallama ne Mandula ta ƙaraso tana faɗin "Allah ya ba ka nasara abincin na kan daining"

Hannu ya ɗaga mata alamun ta tafi.

Ganin ta tsaya ne yasa shi faɗin "Kina da magana ne?"

"Eh ranka ya daɗe dama maganar rashin lafiyar Gimbiya ne, idan zaka bani dama akwai wani kawuna da ke ƙauyemmu yana yiwa masu taɓin hankali addu'a sosai kuma ana samun dacewa" Shuru Muby ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya ce "Idan mun gama breakfast zan neme ki"

"Godiya nake" Cewar Mandula tana barin gurin.

Shi ko Muby ta can gefe ya hangi Afnan da ke faman wasa, tana ganin ya miƙe ta ƙaraso da gudu, da sauri ya matsa baya "Ke wai wannan haukar taki har duka ki ke yi ne?"

Washe baki ta yi ba tare da ta ce masa komi ba, hannunta ya riƙe har suka ƙarasa inda Mandula ta jere musu juluf ɗin taliya wanda ya sha naman kaza, sai coffee da ya sha kayan haɗi, yamutsu fuska Afnan ta yi kamar wadda ke neman wani abun, "Menene kuma haka?" Muby ya daka mata tsawa, kuka ta fashe da shi jin ihun da ya yi mata, gaba ɗaya ta ruɗe ganin haka ya sa shi toshe kunnensa dan ƙarar kukan nata ya cika masa kunne, rarrashinta ya shiga yi har ya samu ta yi shuru, cike da gajiya ya ce "Me ki ke so ne?"

Turo baki ta yi gaba kafin ta ce "Yunwa nake ji abinci zan ci"

"Alright zo nan ki zauna" Ya faɗa yana nuna mata cinyarsa, da sauri ta ɗane kan cinyar tasa tana mai tura masa bakinta.

Sai da ya fara bata abincin ta ci sannan shima ya ci nasa, kana ganin fiskarta ka san ba wani daɗin abincin take ji ba.

Kafin ya gama cin nasa abincin har ta yi bacci kan ƙirjinsa.

Sama ya haura da ita har ɗakinsa, kan bed ya kwantar da ita, daga cikin baccin ta riƙe masa hannu babu yanda be yi ba amma ta kama masa hannu ba halin ya tashi, dole ta sa shi kwanciya gefenta, baccin ma kasa zuwa ya yi dan jin yanda zuciyarsa ke zafi, musamman idan ya tuna cewar an lalata mata rayuwa, wai matarsa wasu gardawa suka yiwa fyaɗe, gimtse haɗaɗɗun idanunsa ya yi cike da ɓacin rai, a ransa ya ƙudurta dole zai shiga masaurata gobe domin a kai matasan kotu.


Ƙura mata ido ya yi ganin yanda take baccin hankali kwance, ya kasa gane meyesa yake jin tausayinta, nan take kuma tunanin Fadila ya faɗo masa a rai, wata irin faɗuwar gaba ne ya ji lokaci ɗaya, ko a wanne hali take yanzu gashi babu damar ya kirata, duk wannan damuwar ya kasa samun masalaha.

A haka har baccin safen ya ɗauke sa shima.


Maimun kuwa dama ba a gida ta kwana ba, sai tara na safe ta shigo gidan, ai da sauri ta saka masu aikinta gyara mata part ɗin nata, sannan ta shiga wanka, sai da ta gama penti-pentinta sannan ta sauko downstep waya kare a kunnenta, kan daining ta zauna dan cika ma cikinta abinci, da Hajara abokiyar cin mushe take waya, sun jima suna wayar kafin daga baya suka yi sallama.

Dama yau kwananta ne amma hakan be dameta ba, sai ma neman hanyar da zata kuɓucewa Muby take, ta san cewa tabbas sai ya zo neman haƙƙinsa.

Shiyasa ma ta shirya ƙaryar da zata yi masa dan bata son komi ya shiga tsakaninsu.

A harabar gidan ta fita har gurin masu aiki, cikin rashin kunya ta kalli wani tsoho da ke bawa Flowera ruwa zai kai shekaru arba'in ta ce "Kai ina Babyna ko ya fita aiki ne?"

Cikin biyayya tsohon ya ce "Allah ya taimakeki ai tun da suka dawo da Gimbiya da safe be ƙara fita ba"

"Gimbiya......, a ina ku ka ganeta?"

Cewar Maimun cike da mamaki.

Duk abin da ya faru tsohon ya kwashe tare da sanar mata, wata irin shewa ta saki gami da nufar part ɗin Afnan.

Sosai take kallon part ɗin komi a gyara ga wani irin ƙamshi na tashi me ɗan karen daɗi, ganin ba kowa a ƙasan ne yasa ta haurawa sama cike da masifa.

Ɗakin Afnan ta fara shiga amma bata ga kowa ba, tun da aka kawota gidan bata taɓa hawa saman ba, ba ƙaramin girgiza ta yi ba ganin mugun haɗuwar da ɗakin ya yi, musamman makeken bed ɗinta, wani irin bugawa zuciyar Maimun ta yi ganin wata kujerar da ke gefen bed ɗin ta Gold me masifar kyau ɗauke da tambarin sarauta, jiri na ɗibarta ta fice daga ɗakin tare da nufar ɗakin Muby, kamar yanda suke haka ta same su kwance, wannan karon Afnan ta shige masa gaba ɗaya a jiki, shi ko Muby ya zageye hannayensa ta bayanta, fuskarta kuwa na kan ƙirjinsa bacci suke cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Kururuwa Maimun ta yi cike da masifa ta haura kan bed ɗin, a firgice su biyun suka farka musamman Afnan da hankalinta ya ƙara gushewa kawai sai ta fashe da ku ka tana ƙara ƙanƙame Muby kamar za'a rabata da shi, shima rungumeta ya kuma yi yana bubbuga bayanta a hankali, hakan ba ƙaramin ƙara hargitsa Maimun ɗin ya yi ba, "Baby me nake shirin gani haka? wannan mahaukaciyar ka ke latsewa kamar ka samu kayan wanki"

Wani mugun kallo ya watsa mata wanda ya sa ta sha jinin jikinta, "Fita daga ɗakinnan Maimun"

"Hehehe, na fita fa? ai ba zai taɓa yuwa ba yau kwanan ɗakina ne, dan haka ka tashi mu tafi"

Banza ya yi mata a lokacin Afnan har ta koma baccin da take, sai numfashin da take saukewa a hankali.

Da ƙarfin tsiya Maimun ta janyota daga jikin Muby, cikin rashin sa'a kan Afnan ya daki gefen bed ɗin, wata ƙara ta saki me razanarwa dan ba ƙaramin dakuwa ta yi ba, nan take gurin ya tashi, a fusace Muby ya damƙi hannun Maimun tare da zabga mata lafiyayyun mari har guda biyu yana mai wurgi da ita ƙasa, da yatsa ya nunata ransa a ɓace ya ce "Idan har na sake ganinki part ɗinnan sai na wulaƙantaki dabba mahaukaciya wadda bata da imani"

Idanun Maimun sun gama fitowa waje tsabagen marin da aka auna mata, sosai marin ya shigeta idanunta kuwa sun gama cikowa da hawaye, "Wallahi ba zan fita ba sai ka tashi mun tafi, wannan rashin adalci ne ai ka gama kwananka da ita"

"Kwana ɗaya na yi gurinta, ranar da nake da kwananta ke ce ki ka amshe"

"Koma menene be dameni ba, kawai ka tashi mu tafi"

Jin kukan Afnan na ƙaruwa ne ga kuma damuwar da Maimun ke masa ya sa shi miƙewa da sauri ya cire belt ɗinsa yana mai nufarta cikin ɓacin rai, da gudun tsiya Maimun ta fice daga ɗakin tana faɗin "Allah ba zan yarda da cin amana ba"

Tana fita ya dannawa ƙofar key, Afnan kuwa gurinsa ta ƙaraso tare da faɗawa ƙirjinsa tana mai cigaba da kukanta, kan bed ɗin suka koma dan ya duba goshin nata.

Sai da aka sha fama kafin ya samu damar danna mata goshin kuka da ihu kam sai da ta sha shi, daga ƙarshe baccin wahala ya ɗauketa, jikinta ya taɓa ya ji da zafi ga kuma sheshsheƙar kukan da take, toilet ya shiga dan sakar ma kansa ruwa a lokacin sha biyun rana ta kusa bugawa, cikin shigar manyan kaya ya fito farare masu kyau, ƙamshin turarensa ya gama haɗe ɗakin, wayarsa da ke ƙara ya ɗauka ganin sunan Yusuf ya sa shi jan tsaki yana mai karawa a kunne, daga ɗayan ɓangaren ya ce "Yarima manya muna ƙofar gida ka fito, tun da yanzu ganinka ma sai da kati"

Ƴar dariya Muby ya yi yana faɗin "Kamar kun san ina son karɓowa Afnan magani, ku bani minti ɗaya"
Ya faɗa yana kashe wayar.

Sai da ya gama shiri tasss kafin ya sauka ƙasa, me gyaran parlourn ya samu tana aikinta, har ƙasa ta rusuna tana gaishe shi "Lafiya ƙalau a dafa mun tuwon shinkafa da miyar kifi bana son albasa ya yi yawa a ciki, kafin na dawo ku tabbata Gimbiya ta ci abinci, ku lura da ita da kyau idan har ta ƙara fita gaba ɗayanku sai kun sha mamakina"

"Allah ya ƙara maka nasara hakan baza ta faru ba insha Allah"

Ficewa daga parlourn Muby ya yi yana mai kallon kiran da Yusuf ke ƙara yi masa.

A bakin gate ya samu su Ashwan, daga nesa yake ganin yanda suke masa dariya ƙasa-ƙasa, ko kallonsu be yi ba ya shige motar, Ashwan ne ya ce "Wai nikam maganin me za'a karɓowa Gimbiyarmu"

Yusuf ne ya yi saurin karɓe zancen da faɗin "Ƙaruwa aka samu mana, ai kana ganin fiskarsa ka san an gama cika aiki"

Banza Muby ya yi musu har suka fara fita daga unguwar, sai tsiya suke masa shi ko a ransa dariya ma suke ba shi, dan ya san cewa babu wani abun da ya shiga tsakaninsu kuma babu abin da zai shiga tun da har wasu su ka riga shi sanin matarsa.


Tun da suka tafi Hospital ɗin yake zarya dan duba marassa lafiya, sai kusan magrib suka nufi hanyar gida, a masallacin unguwar Ashwan ya tsaya dan su yi sallah, sai da aka gama isha'i suka koma gidan, tun a harabar gidan ka ke jin muryar Maimun da masu aiki kamar zata yi musu dukan tsiya, tana ganin Muby ta ƙaraso da sauri cike da rashin kamun kai, kayan bacci ne wandon iya cinyarta sai ƴar rigar da ta tsaya kan ƙugunta, duk jikinta ana gani har shayun pant ɗin jikinta.

Wani irin mugun kallo Muby ya yi mata me kama da kina da hankali kuwa, Maimun kam ko a jikinta bata ma san yana yi ba, "Baby kana jin mahaukatan masu aikin nan, ina buƙatar a cire mun duk hakukuwan da ke part ɗina a darennan, wai shine za su ce sai gobe"

Ashwan da Yusuf kam part ɗin Afnan suka nufa dan kallo ɗaya suka yi mata tare da ɗauke kai.

"Maimun kin san abin da ki ke yi kuwa?"

Wani irin juyi ta yi tana ƙara gyara tsayuwa ta ce "Na sani Baby wannan wankan ya tafi da kai, dama kai nayi wa"

A tsawace ya ce "Ki koma ciki tun kafin raina ya gama ɓaci"

"Haba Baby wai meyesa ka ke min haka ne? meye laifin shigar jikina dan kawai na fito a hakan"

Ran Muby ne ya ƙara ɓaci jin yanda take ɗaga masa murya kamar ba shine sama da ita ba, "Ko Gimbiya da ta fiki wayewa bata irin wannan shigar a gaban masu aiki, dan haka ki koma ciki kafin na nuna miki halina"

Ganin idanunsa sun rine ga wani rawa da hannunsa ke yi yasa ta koma ciki da sauri.

A parlour ya sami Ashwan,Yusuf,Afan, ana faman gudu kamar yara tana binsu da Cup ɗin glass zata buga musu, tana ganin Muby ta saki Cup ɗin tare da ƙarasowa gurinsa da gudu ta faɗa jikinsa tana dariya, ɗagata sama ya yi yana juyi da ita kamar Baby, "Sarkin rigima yau kuma abokanan nawa za'a daka"

Dariya ta kwashe da shi tana wintsila ƙafa, ba ƙaramin tsoro su Ashwan suka yi ba, a kujera suka zauna suna sauke numfashi, sai a lokacin Muby ya samu damar yin dariyarsa, Yusuf ya ce "Wai me yake faruwa ne Yarima, anya ba Aljanu ke damun Gimbiya ba?"

"Kaga Malan zan yi muku bayani amma ba yanzu ba, mu koma dianing please"

A dianig suka baje tare da kwasar girki, Afnan na kan cinyar Muby sai wasanni take dan already ta ci nata abincin, su Yusuf kam mamaki hana su magana ya yi, sai wajen tara na dare ya raka su har gun motarsu tare da yi musu sallama.

Sai da ya sha fama kafin ta sha maganinta, bata jima ba bacci ɓarawo ya kwasheta, rufeta ya yi yana mai shafa mata addu'a ya nufi part ɗin Maimun.

Yana shiga ɗakinsa wanka ya fara yi dan yanda yake jin jikinsa, ya yi mamakin rashin ganin Maimun a ɗakin nasa, ga wani feelings da ke taso masa, a daddafe ya gama shiri cikin kayan bacci wando da riga kalar sararin samiya, sai da ya gyara haɗaɗɗen gashin kansa tare da fesa turarensa ya nufi ɗakin nata.


Maimun da ke waya ta ji buɗewar ƙofa da sauri ta kashe wayar tana mai kwanciya kamar me baccin gaske, ƙofar Muby ya rufe yana mai kashe hasken ɗakin ya nufi kan bed ɗin, bed side lamp ya kunna wanda ya ɗan ba ma ɗakin damar haske kaɗan.

Maimun kuwa kamar ta rusa ihu dan wani haushi take ji, a hankali ya matsa kusa da ita dan tun shigoworsa ya san ba bacci take ba, "Na san cewa ba bacci ki ke yi ba Maimun"

A zabure ta miƙe tana kallonsa cike da takaici ta ce "Eh ba bacci nake ba sai me ya faru? bana son abin da ka ke so yau ka barni na yi bacci na"

Cike da mamaki yake kallonta, sai ya ga ta ma raina masa wayo, har shi zai roƙeta a kan abin da ya san haƙƙi ne a kansa, da ƙarfi ya janyota jikinsa yana faɗin "Ba ra'ayinki nake so ba"

"Wallahi ba ka isaba, ai ba'a dole"

Cikin sa'a ta kwace jikinta tana mai komawa ƙarshen gadon, "Na faɗa maka bana so kuma bana ra'ayinka yanzu na daina ƙaunar jikinka ka gane ko?" Shuru Muby ya yi na ɗan wani lokaci yana nazarin kalamanta, ita ko Maimun ƙara matsewa ƙarshen bed ɗin ta yi tana jiran abin da zai yi.


ƘASAR CAMEROUN
..................................
A ɓangaren Fadila kuwa tun ranar da suka koma ƙasarsu ta hana kowa zaman kafiya, ga lamarin Nabeelah na ƙara hargitsa ta, a kullum sai ta ganta a gidan amma kafin ta fargo bata ganin kowa, ta fi tsammanin cewa fatalwa take gani ba Nabeelah ba.

Yau ma

Please Login or Register in order to submit comment