Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanye cikin wani ɗanyen yadi me laushi kalar sararin samaniya, ya masifar yin kyau fuskar nan tashi sanye cikin baƙin glass, ƙamshin turarensa ne ya sanarwa dogaran da ke tsaron part ɗin fitowarsa, saman kayan ya ɗora wata baƙar alƙibba me kauri, gaba ɗaya gaban alƙibbar an yi masa wani aiki me masifar kyau da duwatsun gold, takalman ƙafarsa kuwa, me tambarin sarauta ne sawu ciki, agogon da ke ɗaure a hannunsa na gold me sheƙi ya kalla fuskarsa tamau kamar kullum, ƙarfe ɗaya da mintuna hamsin, ɗan ƙaramin tsaki ya ja yana mai kallon Mahaifin nasa da shima Mubyn ya ke kallo, cikin girmamawa ya ce "Abbu barka da rana"

Kallonsa Sarki Ahmad ya yi ganin kamar ba bu abin da ya faru, amma sai ya dafa ƙafaɗarsa yana faɗin "Me ya haɗaka da Gimbiya" Rassss..., gaban Muby ya faɗi jin abin da me martaba ya ce, ko dai Afnan ta faɗawa mutane abin da ya faru a tsakininsu ne, idan kuwa hakane wallahi yau zata tare ɗakina.


Muby ya faɗa cikin ransa, yana mai jin haushi da tsanar yarinyar a ransa.

Kamar wanda aka sa dole ya yi magana ya ɗan taɓe baki tare da faɗin "Abbu ba bu abin da ya faru, ko ta ce maka nayi mata wani abun ne?" "Ka san cewa bana son ina tambaya ana tambaya na ko? ka faɗa mun gaskiya tun kafin na yi bincike da kaina"

Lumshe ido Muby ya yi yana mai shafa gashin kansa a hankali gami da gajiya da magana ya ce "Ba bu abin da ya faru Abbu"

Kallonsa me martaba yake cikin ƙika wa ƙala, amma sai ya kama hannunsa su ka nufi waje inda ake shirin ɗaurin aure.



Sosai mutane su ka zo ɗaurin auren ƴar Sarki Ahmad me suna Munirat, ita ce ke bin Prince Muby daga ita sai shi, yarinyar tana da hankali sosai bata ɗauki sarauta kamar yanda ƴan gidansu ke taƙama ba, shiyasa ma ba ɗan gidan sarauta ta aura ba, wani matashi ne mazaunin garin Abuja, shugaban Navy na Nigeria, iyayensa na da kuɗi sosai shiyasa ma da aka zo neman auren ba'a ɓata lokaci ba, duk da cewar Sarki Ahmad yaso ace ɗan gidan sarauta zata aura, amma dole ya haƙura ya bada auren nata tun da ta nuna tana sonsa.



Munirat nada wata ƙawa me suna Maimun tana son Prince Muby kamar zata yi hauka, a kullum tana zuwa gidan saboda kawai ta ganshi, tun tana ɓoye masa soyayyarta har ta kai ga bayyana masa amma shi ko a jikinsa dan bata gabansa, Maimun na ɗaya daga cikin ƴaƴan masu kuɗin garin dan za'a iya saka Mahaifinta na uku a cikin masu dukiyar garin, sai dai ita ba fara ba ce chocolate colour ce kuma tana da kyau ba laifi, dan ba da wani abun Gimbiya Afnan zata nuna mata kyau ba, kuma Maimun akwai kayan marmari har tafi Afnan zubin halitta sosai, shiyasa take ganin cewa ko ba bu komi Muby zai amincewa soyayyarta, so da yawa tana kai masa tallar kanta amma sai ya nuna mata shi ba zai iya amincewa buƙatar ta ba, kuma ba zai iya aikata zina ba, duk da hakan bata wucewa sai ta gama shafe masa jiki da taɓe-taɓe.


Misalin ƙarfe biyu aka ɗaura auren Munirat Ahmad Mulki da mijinta General Khalil Muhammad a kan sadaki million ɗaya laƙadan ba ajalan ba, sosai ake busa algaita da kaɗe-kaɗe musamman da rundunar sojojin su ka ƙaraso cikin shigar kakinsu, motoci hamsin ne aka rako angon kuma duk cikin motar ba bu wadda baza ka yaba ba, Muby da ke gefe mutane sun cika shi da gaisuwa kowa na son ya taɓa hannunsa dan kawai su gaisa, da ƙyar ya ja jikinsa tare da kama hannun abokinsa Ashwan yana faɗin "Ina Yusuf ɗin ne? na ce masa bayan ɗaurin aure akwai inda zamu tafi, kuma sarai ya san bana son jira".

Ya faɗa suna shiga harabar gidan, Ashwan ne ya ce "No ba haka ba ne, akwai inda ya ce mun zai biya kafin ya iso ina ganin ya kusa ƙarasowa ma"

Cewar Ashwan yana murmushi, shima fa Ashwan akwai kyau sosai yana da aji gami da taƙama iya nasa, amma ko kaɗan be kai Prince Muby ba.


Tun daga nesa Maimun ta hangi Muby tsaye tare da Ashwan, ai kuwa ta nemi natsuwarta ta rasa dan tsananin kyawun da ya yi mata, har wani lashe lips take yi, kallon amarya Munirat da ke gefe ta yi tana faɗin "Ina zuwa ku ƙarasa daga ciki ga bugun numfashina can" Baki Munirat ta taɓe tana faɗin "A dai bi a hankali, kinsan yau uwargida ta shigo" Ba tare da Maimun ta gane abin da Munirat ke nufi ba ta bar gurin cike da rawar kai.


Kamar daga sama ya ji an yi hugin ɗinsa, tare da shafa ƙirjinsa cikin salon iya barikanci ta ce "Sweet barka da warhaka"
Ashwan da ke mamakin rashin kunya irin na Maimun ne ya ɓata fuska yana mai cewa "Malama ki ɗaga shi haka, ko ba bu komi ai mutane na kallonki, kar fa ki mance mijin wata ne....." "Ya isa haka Ashwan dama na daɗe da sanin ka tsaneni to amma abin da baka sani ba shine muddin ina numfashi a doron ƙasa ba bu wata macen da zata raɓi Prince imba ni ba"

Da ƙarfin tsiya ya janyota daga bayansa yana mai watsa mata harara "A matsayinki na wa za ki faɗi hakan"

"A matsayinta na karuwa kuma ballazaga marar aji" Gaba ɗayansu juyawa su ka yi dan ganin waye, Gimbiya Afnan ce tsaye fuska ba bu walwala ranta ya masifar ɓaci ganin hannun Muby riƙe da na Maimun.

Kayan jikinta yake kallo yana mamakin wai har ta koma ta canza kaya, sanye take cikin wata arniyar abaya kalar sararin samaniya, gashin kanta ya sauko ta goshinta kwance luff-luff, sai wani ɗan ƙaramin mayafin abayar da ta yafa daga bayan ƙugunta gashin kanta ne kwance sai rito yake, baƙi siɗik yana sheƙi, hannunta riƙe da wayarta ƙirar iphone 15promax, agogon da ke hannunta ta kalla wanda ya masifar ƙarɓarta, kana ganinsa ka san kuɗi ya yi kuka, lokaci ta duba har biyu ta gota sosai, hannu ta ɗagawa kunyanginta da ke bayanta, da sauri ɗaya daga cikinsu ta nufota tare da sanya mata alƙibba me kyau da sheƙi black colour, gaban Maimun ne ya yi masifar faɗuwa ganin wani irin kyau da ƙwarjini da Afnan ta yi mata, ga wani smile da take kamar wata zinariya, sannu a hankali take taka grass carpet ɗin da ke harabar gidan cike da gadara gami da ƙasaita ta iso gurin, kallonta ta mayar kan Maimun da ke tsaye jikinta na ɓari, ita ba tsoron Afnan take ba amma kyawunta ke firgitata, tun kafin ta ƙarasa tunanin zucin da take ta ji an ɗauketa da wani mahaukacin marin da yasa ta janye hannunta kan na Muby ba shiri, cikin mamaki Ashwan da Muby ke kallonta ganin abin da ta aikata, kamar daga sama su ka ji ta ce "Uwar wa ta baki izinin taɓa jikin mijina? idan har kin mance bari na tuna miki kina ƙoƙarin shiga hurumin da ba naki ba, kina neman faɗawa wutar da zata ƙonaki daga ke har danginki da ma duk magoya bayanki" Tsayuwa ta gyara cikin yarda da kai ta ce "Not even him" Ta ƙarashe maganar tana nuna Muby da yatsa duk tsoron Allah ya gama rufe sa, wai yau Afnan ke kiransa da mijinta, saurin kawar da zancen ya yi tare da kama hannunta ya murɗe da ƙarfi, amma taurin kai ya hanata yin ƙara, sai ma wani killer smile da ta saki tana mai fizge hannunta ta ce "Au na mance fa karuwarka na mara ko? idan har kana buƙatar cigaba da fasiƙancin da ka ke yi tilas ne ka sakeni.." A fusace ya ɗaga hannu da niyar aza mata mari, cikin sauri ta kama hannun kamar wadda zata iya dukansa ta ce "No, i can't take this from you, bana ɗaya daga cikin matan da mazajensu ke duka suna zuba ido basa ɗaukar mataki, kalleni da kyau ka gani kaga nayi kama da macen da za'a kira da sunan baiwa a gurin mijinta?".

Ta faɗa tana nuna jikinta da hannu, lumshe ido Muby ya yi da ƙarfi dan ya ji zafin maganar, Maimun kuwa tun lokacin da aka zabga mata mari take dafe da kuncenta, a ranta take faɗin lallai dole zata tashi tsaye baza ta zuba ido a rabata da wanda take so ba, a tsawace Afnan ta katse mata zancen da faɗin "Get lost please, tun kafin na hukunta ki".

Cikin tsatstsarfa Maimun ta bar gurin har tana ƙoƙarin karo da mutanen da ke shige da fice.

Afnan na ganin ta wuce ta ɗagawa kuyanginta hannu, nan take ta bar gurin cikin tafiyarta da ke jan hankalin me kallo, kamar wani marar rai haka Muby ya zuba mata ido har ta shige babban parlourn gidan

Yusuf da isowarsa kenan ya yi sallama yana faɗin "Lafiya ku ka tsaya haka kamar masu jiran tsammani" Caraffff Ashwan ya karɓe zancen da faɗin "Wannan yafi jiran tsammani"

"Gimbiya ce ko?" Yusuf ya tambaya yana kallon Muby da ke shafa gashin kansa, Ashwan ne ya ce "Ya aka yi ka sani?"

Murmushi Yusuf ya kuma yi yana mai dafa kafaɗar Muby ya ce "Na san cewa ita kaɗai ce ta isa saka damuwa a fuskar My guy, ko ba haka ba?" Ya faɗa yana murmushi dan Yusuf ba dai fara'a ba.

Shine baƙi a cikinsu amma yafi Ashwan kyau, ko kallon inda yake Muby be yi ba ya bar gurin fuskarsa a murtuƙe, gaba ɗaya ya rasa yanda zai yi da Afnan dole zai sawwaƙe mata kowa ya huta, idan ya so ya samu zaɓin ransa ya aura.


Da sauri su Ashwan su ka bi bayansa dan sun san idan ransa ya ɓace abin da ke faruwa, zaune su ka same shi yana busa sigari duk idanunsa sun yi jajir.

Yusuf ne ya zauna gefensa cikin tausasa murya ya ce "Dan Allah ka daina wannan abin da ka ke yi, zaka jawa kanka wata matsalar fa"

"Yusuf please live me alone, bana son surutu, ku fice mun daga part" Ya faɗa rai ɓace, be jira abin da zasu ce ba ya shige room ɗinsa tare da banko ƙofa.


Yana shiga ya ya cire rigar da ke jikinsa, yana mai duba bayansa da Afnan ta yanza ɗazu, gurin na ɗaure da bandeji, amma duk da hakan akwai shahun jini a kai.


Ƙofa ya yi yana mai shigewa toilet.



Maimun na shiga ɗakin da su Munirat ke ciki ta faɗa kan bed tare da sakin ihu me razanarwa tana dukan bed ɗin kamar ta samu mutum, kuyangin da ke tsaye a ɗakin Munirat ta yiwa alamun su fice, cikin girmamawa su ka rusuna tare da ficewa daga ɗakin.


A hankali ta dawo gefen ƙawar tata tana tambayar abin da ke faruwa amma shuru Maimun ta kasa bata amsa, "Okay fine tun da baza ki faɗa mun damuwarki ba" Ta faɗa tana mai shirin miƙewa, hannunta Maimun ta kama cikin sauke ajiyar zauciya ta ce "Sai yaushe zan auri yayanki ne, ko har sai matarsa ta mutu zan mallake sa? idan har sai Gimbiya ta mutu zan auri Yarima to wallahi ni ce zan zama ajalinta...." Da sauri Munirat ta rufe mata baki tana mai jin tsoron furucin da Maimun ta yi, dan ta san tabbas zata aikata fiye da hakan.

Tashi tsaye Maimun ta yi tana mai sakin murmushin mugunta cike da yadda da kai ta ce "You have already knew who i am, dole Gimbiya zata mutu saboda ba zan iya zaman kishi da ƴar taƙama da gadara ba, ni ba bu abin da ke ɗaga mun hankali irin kyawun da take da shegiya me fuskar aljanu, wallahi na tsaneta"

"Haba Maimun dan Allah ki daina faɗar haka, kar tsautsayi ya sa a ji wannan zancen"


A masifance Maimun ta ce "An so what? ai bana tsoronta kawai ina raga mata ne dan tana Gimbiya" "Ashe kuwa kinga tsoronta ki ke yi" Munirat ta bata amsa tana cigaba da gyara mayafinta dan an kusa zuwa ɗaukar amarya.



Misalin ƙarfe biyar na yamma Sarki Shuraihu su ka yi sallama dan da safe zasu koma ƙasar Senegal, amarya Munirat kuwa tun da ƙarfe huɗu aka nufi garin Abuja da ita.

...........
Tun da su Afnan su ka koma Hotel ɗin da su ka sauka take ɗaki kwance zuciyarta na saƙa mata abubuwa iri-iri, sai ta ji kamar kar ta koma ƙasar tasu, bugun ƙofar da aka yi ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga, sai da ta ƙara mintuna uku kafin ta ce "Come in" Tana rufe jikinta ta blenket, wata kunyangarta ce me suna Mubina ta shigo cike da ladabi ta rusuna tana faɗin "Barka da dare Gimbiya, me martaba na buƙatar ganinki, ya ce ki same shi a ɗakin da Fulani ta sauka"

Hannu Afnan ta ɗaga mata alamun ta fice, fita Mubina ta yi tana mai jan ƙofar.


A zaune ta same su suna fira cikin so da ƙaunar juna, Halima kuwa na gefe tana waya da Mahaifiyarta, da sallama Afnan ta shiga tana mai zama kusa da Fulani, "Barkanku da dare" Ta faɗa cikin ɗaure fuska, me martaba ne ya ce "Yau kuma ni ake yima mulki Gimbiya?" Ɗan murmushi ta yi wanda ya ƙasa mata kyau kafin ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya cike da taƙama ta ce "Uhmm Baffa ai ban isa nayi maka mulki ba, ko ka mance a gurinka na gada"

"Hakane kam ai mulki sai gurin Mahaifinki, dan nikam ba haka nake ba, duk da cewar Mahaifina ya yi sarauta amma ban yi kaɗan daga cikin isar da ki ke nunawa ba" Fulani ta faɗa tana mai kawar da kai gefe, Husna ce ta fashe da dariya tana faɗin "Fulani gaskiya ke ta daban ce, yanzu wai a lokacin baki nuna gadara ba?"

"Har abinci ina ci da masu kula da ni, amma na san yayarki baza ta iya ba" Fulani ta bata amsa.


"Allah ya sawaƙa, ni har akwai wata ƙasƙantacciyar me aiki da zan ci abinci tare da ita? na fi ƙarfin hakan ai"

Afnan ta faɗa tana mai ƙara tamke fuska.

Shuru Fulani ta yi tana mamakin hali irin na Gimbiya.


Me martaba ne ya saki murmushi cikin so da ƙaunar ƴar tasa, duk a cikin ƴaƴansa yafi son Gimbiya shiyasa baya son ganin ɓacin ranta, kallonta ya yi yana faɗin "Ke dai barsu kawai basa son gaskiya amma me zai kai ki cin abinci da bayinki, daina fushin haka dama na saka an kiraki ne dan mu yi fira, ina fatar kin shirya kayanki duka ko?" Yamutsa fuska ta yi kafin ta ce "No Baffa ba zan tafi da ko kala ɗaya ba zan barsu anan idan almajirai sun shigo bara masu kula da Hotel ɗin su basu"

"Okay hakan ma ya yi". Cewar me martaba.

Tun da ta zauna take gallawa Halima harara ita kuwa Halima sai dai ta kawar da kai gefe dan bata son tashin hankali, ta san cewa magana ɗaya zata faɗa yanzu zai janyo rigima.

Duk firar ma tsakanin me martaba da Gimbiya ne, amma Fulani shuru ta yi tare da zuba musu ido, har ƙarfe sha ɗaya na dare ta buga, sannan Afnan ta yi musu sallama ta fice.


..........
Washe gari misalin ƙarfe shida gaba ɗaya tawagar Sarki Shuraihu sun hallara a harabar Hotel ɗin, a can wajen gate kuwa Sarki Ahmad ne da nasa muƙarraban anzo rakiya, cikin kamala Sarki Shuraihu da iyalansa su ka fito har inda mitocinsu suke, Gimbiya Afnan an haɗe cikin shadda gizna me laushi da ƙamshi, sai ɗan ƙaramin mayafin da ta yafa, ƙamshin turarenta ya gama mamaye gaba ɗaya harabar gurin, agogon hannunta kuwa sai walwali yake yana ɗauke da tambarin sarauta, gaba ɗayansu shiga motocin su ka yi, nan take aka fara fita da motocin cikin busa algaita, ba tare da ɓata lokaci ba Sarki Ahmad ya shiga motarsa su ka rufa musu baya, idan kaga yawan motocin zaka yi tsammin gaba ɗaya shugabannin duniya ne ke shagalin biki, direct babban airport ɗin garin su ka nufa, mutane an cika ana kallon sarakuna masu ji da mulki gami da taƙama.


Bayan kowa ya gama fitowa ne Sarki Ahmad ya kalli surukin nasa yana faɗin "Ina ku ka baro Gimbiya?"

"Gimbiya kuma.....?" Cewar Fulani tana duba motar da Afnan ta shiga, mamaki ne ya kamata ganin ba bu kowa, cikin tsawar da Fulani bata taɓa yi ba ta kalli drivern tana faɗin "Ina Gimbiya ko bata shiga wannan motar ba ne?"

Cike da tsoro drivern ya ce "Allah ya ja zamaninki wallahi ta shiga amma bansan yanda aka yi ta ɓata ba".

Ya ƙarashe maganar yana durƙusawa kan gwuiwoyinsa, nan take aka bada umarnin rufe airport ɗin, tare da hana kowanne jirgi tafiya, sannan aka saka sanarwar ɓacewar Gimbiya Afnan.



*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*










P. 3





"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" me martaba ya faɗa yana ƙoƙarin faɗuwa saboda jirin da ke neman kada shi, da sauri Husna da Halima su ka riƙo sa tare da kai shi mota.

Ba bu inda ba'a bincika ba a cikin airport ɗin amma babu Gimbiya babu labarinta, sosai Fulani ta shiga tashin hankali, kawai tana dannewa ne amma abin ya taɓa ta, Sarki Ahmad ne ya koma gurin motar da aka kai Sarki Shuraihu, a jingine ya same shi yana mai dafe da kansa, cikin nuna alhini Sarki Ahmad ya ce "Ina ganin zan kira Yarima saboda ya sa bincike sosai a can cikin gari, zai iya kasancewa daga can ne muka rasa ta" Cike da fushi gami da nuna isa Sarki Shuraihu ya ce "Bama buƙatar wani taimako daga gareka saboda duk abin da ya faru kai ne silar hakan"

"Ni ne sila kuma?" Sarki Ahmad ya tambaya yana mai ɗaure fuska, fitowa daga motar Sarki Shuraihu ya yi cike da ƙasaita yana faɗin "Ƙwarai kuwa saboda sanadiyar auren ƴarka aka sace ƴata, amma ka sani cewa duk abin da ya sami Gimbiya wallahi ba zan lamunce maka ba, daga kai har yaron naka..."

Ƙarar da wayar Sarki Shuraihu ta yi ne yasa shi saurin ɗagawa yana mai karawa a kanne, abun da yaji daga ɗayan ɓangare ne yasa shi ja baya da sauri yana mai salati duk zufa ta wanke masa fuska, baki na rawa yake faɗin "Dan Allah kar ku kashe ta ko nawa ku ke so zan baku amma please kar ku taɓa lafiyarta"

Shuru ya kuma yi alamun ana magana a can ɓangaren, cikin firgici Sarki Shuraihu ya saki wayar da ke hannunsa yana mai jinginawa a mota, a rayuwarsa ba bu wadda ya fi so sama da Gimbiya.

Fulani ce ta ƙaraso gurin tana mai ɗaga shi tare da tambayar abin da ke faruwa, hannunta ya kama kafin ya kalli Sarki Ahmad yana faɗin "Wasu ne su ka yi kidnapping ɗin Gimbiya, kuma sun ce ko gaba ɗaya dukiyar da muka mallaka zamu basu baza su sake ta ba, wai basa buƙatar dukiyarmu ko mulki rayuwarta kawai su ke so kuma sun samu, babban abin da ya ɗaga mun hankali cewar da su ka yi idan har muka fasa barin ƙasar nan sai sun kashe ta a yau, abin da kawai zai ceci rayuwarta shine mu bar ƙasar nan ba tare da wani bincike ko tura matakan tsaro ba" Ya ƙarashe maganar yana mai dafe zuciyarsa da ke bugawa a kai a kai.

Fulani ce ta ja baya cikin tsananin tsorata gami da firgici ta ce "Subhanallahi wannan wacce irin masifa ce, Allah ka kawo mana ɗauki" Sarki Ahmad ne ya fara magana cikin ƙasaita ya ce "Dole zamu sanarwa matakan tsaro baza mu bi ra'ayinsu ba"

"Really? if anything happen to my Daughter" Tsayuwarsa ya kuma gyarawa kafin ya cigaba da faɗin "I'll never for give you, daga kai har iyalanka"


Ya ƙarasa maganar yana mai bada umarnin a buɗe hanyoyin da aka rufe, su Halima da Husna kuwa suna gefe hankalinsu a tashe dan Fulani ta sanar musu abin da ke faruwa.


Cikin abin da be fi awa ɗaya ba jirginsu ya tashi, Sarki Ahmad da masu take masa baya kuwa komawa su ka yi dan babu wani abin da zasu iya, tun da Sarki Shuraihu ya nuna baya buƙatar ayi bincike a kan ƴar tasa gudun kar a rasa rayuwarta, amma ya san dole Sarki Shuraihu zai dawo ƙasar bada daɗewa ba domin ceton rayuwar Gimbiya mafi soyuwa a garesa.




............
"Hahahahaha! gud job guys kun yi abin da ya dace dan haka dole na biyaku da kaso me tsoka" Cewar Gimbiya Afnan da ke zaune kan wata kujera me masifar kyau da tsada ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, wasu maza kusan su arba'in suna bayanta alamun ita ce shugabarsu, ɗaya daga cikinsu ne ya kalleta yana murmushi cikin girmamawa ya ce "Zamu iya yin fiye da hakan ma, idan har za ki biyamu abin da muke buƙata, saboda kinsan Mahaifinki zai iya yin komi saboda ke, ko yanzu bamu san shirinsa ba, domin tabbas zai dawo ƙasar nan, dan ya bincika abin da ke faruwa".

Fuska Afnan ta haɗe tare da miƙewa tsaye cikin taƙama gami da yadda da kai ta ce "Na san da haka, shiyasa ma na yi kidnapping kaina da kaina, abin da nake so da ku shine a sama min gida wanda zan iya zama a ciki na tsawon lokaci, amma fa bana son gidan haya kuma bana buƙatar madaidaici, a sama ma min wanda ya tsaru sosai, kuma ya gaji da haɗuwa". Ta faɗa tana mai zama kan kujerar da ta tashi.

Cikin biyayya su ka amsa da an gama Gimbiya, ɗaya daga cikinsu ne ya buga waya tare da bada umarnin a bincikawa Gimbiya Afnan gidan da zata zauna.


Mintuna ashirin tsakani su ka nufi wani babban gida me hawa biyu, ya masifar kyau kana ganinsa ka san kuɗi sun yi kuka, a filin gidan wani rsatsatstsen carpet ne ruwan ganye me laushin tsiya, ta can ɓangeren kuwa swimming pool ne har kala biyu tare da gurin buga wasanni iri-iri, pearking space kuwa motoci ne kala goma masu tsadar gaske, a ko'ina ka duba fitilu ne masu haske sun gama haske harabar gidan, ga flowers nan kala-kala masu kyau da ƙamshi, daga bakin gate ɗin har ƙofar shiga parlourn gidan masu tsaronta ne suna sanye cikin shuɗin kaya.

Sannu a hankali take taka grass carpet ɗin cikin iya tafiya da ƙasaita, har ta shige makeken parlourn me ɗauke da kayan more rayuwa gaba ɗaya tsarin parlourn ya haɗu, kama daga kujerun da ke ciki har sauran tarkacen, a can gefe TV ne mai girman gaske ya baje a bangon, ta ɗaya ɓangaren wani kilishi ne na manyan ƴaƴan sarauta masu ji da kuɗi, sai wani wangamemen table a tsakiya kan wani carpet me taushi, kalar kujerun da ke parlourn, ta ko'ina ƙamshi ke tashi kamar daga nan aka fara sarrafa turarukka, kallonta ta mayar kan wani tamfatsetsen fridge da ke gefe wanda ke cike da kayan marmari, sannan ta maida duban ta ga wani matashi da ke tsaye a gurin daga gani shine ya sayar mata da gidan, cike da gadara ta zauna kan luwa luwan kujerun da ke tsakiyar parlourn me zaman mutum ɗaya, tana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sannu a hankali take motsa lips ɗinta kamar dole ta ce "Ina ƴammatan da na ce ina buƙata"

Cikin girmamawa matashin ya ce "Suna daga waje umarninki su ke jira, ko zasu shigo daga ciki"

"They can come in" Ta bashi amsa tana mai kawar da kai gefe.

Fita ya yi dan cika

Please Login or Register in order to submit comment