Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin da zai ce, "Ameer a matsayina na ƴar'uwa a gareka ina son sanin damuwarka, tun ɗazu nake ganin yanda ka kasa samun natsuwa, idan har baza ka iya faɗawa Mommy ba, ni ka faɗa min zai iya kasancewa inada mafita"

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke, cike da gamsuwa da maganarta, ya san cewa ita ƙawar Maimun ce zai iya yuwa ta san abin da take aikatawa, ƙara tambayarsa Munirat ta yi a karo na uku, ba dan ya so ba ya kwashe duk abin da ya gani ya sanar mata, sannan ya miƙa mata wayarsa da ya ɗauki hotunan Maimun ɗin da abokan harkarta, a kiɗime Munirat ta miƙe cikin mugun razana ta ce "Subhanallahi, innalillahi wa inna ilaihir raji'un, sai da na hana Maimun, sai da na ce kar ta aikata, tun kafin na yi aure take neman hanyar da zata kawar da budurcinta, amma na hana ta saboda na san cewa idan har ta auri Brother dole zai sameta ba budurwa ba, son da take masa ya sa ta daure da duk sh'awarta, amma duk da haka tana romance da samarinta"

Komawa Munirat ta yi ta zauna tare da dafe kanta, "Yanzu abin da zata saka mana kenan, ta rasa wanda zata yaudara sai Brother tabbas sai kowa ya san da lamarinnan"

A fusace ta miƙe da niyar nufar Fada, Ameer ne ya yi saurin shan gabanta yana bata haƙuri, wani wawan mari ta zuba masa ranta a mugun ɓace, tun da Ameer yake da Yayar tasa bata taɓa yi masa ko tsawa ba, amma yau har da mari tabbas ya san ranta ya ɓaci, idanunta sun ciko da ƙwalla ta nuna sa da yatsa ta ce "Babu wani mahaluƙin da zai hanani nunawa Abba da Alhaji wannan baɗalar da Maimun ke aikatawa a gidan aurenta, idan ka sake shiga gabana sai na ɗauke ka da wani marin"

Ba tare da ta tsaya jin abin da Ameer ɗin zai faɗa ba ta nufi hanyar Fada.



ƘASAR SENEGAL
..............................
A ɓangaren su Fulani kuwa suna zaune da yaranta Me martaba da Mama suka shigo kamar an koro su, wannan karon daga Fulani sai su Alhassan Hajiya ta koma part ɗinta, kallo ɗaya Fulani ta yi tare da ɗauke kai gefe dan ta san cewa ba Alkhairi ba ne zuwan nasu.

Wata kujere me kyau Mama ta zauna tana mai harɗe ƙafa, Sarki Shuraihu kam kasa magana ya yi dan idanunsa na ƙasa, cikin rashin imani Mama ta kalli su Alhassan da ke kwance ta ce "Ku kuma makafin wofi ku fita zamu yi magana da Uwarku"

Ameer ne ya ce "Duk abin da za ki faɗa ki faɗa dan babu inda zamu tafi, rashin ganinmu ba shine zai sa mu bari a wulaƙanta Mahaifiyarmu ba"

"Kai Yarima Alhassan ka shiga hankalinka bana son rashin kunya, ko ni da nake Ubanka ban isa tana magana ina magana ba"

Jin abin da Me martaba ya ce ne yasa Alhassan shuru cike da mamaki, amma ya san cewa aikin Mama ya wuce nan, Fulani ce ta ce "Ku faɗi abin da ke tafe da ku"

Dogon tsaki Mama ta ja tana faɗin "Yawwa dama yau nake son ku tattara kayanku ku bar gidannan, bana buƙatar ku ƙara kwana ɗaya a nan"

Tsoro mamaki fargaba da kuma tashin hankali ne ƙarara kan fuskar Fulani, bata taɓa zaton lamarin ya kai haka ba, Alhassan kuwa jikinsa har rawa yake tsabagen ɓacin rai, Muhseen da Husna da ke gefe sai lalabe suke suna ƙoƙarin miƙewa tsaye, cikin tsawa Mama ta ce "Kana gani fa na yi mata magana amma kamar bada ita nake ba, ko kuma ni na bar muku gidan ne?"

Me martaba ne ya yi saurin cewa "Aa ba sai ta kai haka ba, Alhassan ku tashi ku shirya kayanku tun kafin na ɓata muku rai"

Ba tare da Fulani ta sake cewa komi ba ta miƙe tsaye tana kama yaran nata, a haka har suka sauko parlour, part ɗin Hajiya suka nufa wanda a lokacin ciyon kanta ya yi tsanani, sosai take jin jiki saboda maganganun da ɗan nata ya rinƙa faɗa mata, tana cikin haka Fulani ta kawo mata zancen korar da me martaba ya yi musu, cike da dauriya Hajiya ta ce "Babu inda za ku tafi ina Shuraihun ne?"

"Ai ba sai kin neme ni ba har kema gidan za ki bari"

Cewar Me martaba da shigowarsa kenan, Mama da su Bilkisu na bayansa, a fusace Hajiya ta ce "Kai Shuraihu ka bi duniya a sannu, ko babu komi ni ce na haifeka yanzu abin da zaka saka min kenan? saboda waɗannan tsinannun zaka kori iyalinka a gida"

Bilkisu ce ta ce "Ke ce tsinanna ba mu ba"

Wani irin mahaukacin mari Fulani ta ɗauke Bilkisu da shi tun kafin ta gama rufe baki, idan ran Fulani ya yi duba ya ɓaci, ihu Mama ta kurma tana mi yin cikin Fulani da niyar dukanta, Alhassan da yana jin takun Mama kamar zata iso gurin Mahaifiyarsa ne ya yi saurin tara mata ƙafarsa, ai kuwa Mama ta zube ƙasa rissss kamar an zube kayan wanki, Bulkisu da Hauwa'u kuwa ba kunya suka tuntsire da dariya, da ƙyar Mama ta miƙe tana mai shaƙo Alhassan ta ɗauke shi da mari, dafe kuncensa ya yi dan marin ya shige sa, har ta ɗaga hannu zata ƙara masa ta ji an riƙe hannun ta baya, gaba ɗayansu kallo suka mayar kan Easha da Muslimat ƙawayen Afnan, cikin ɓacin rai Easha ta yi wurgi da hannun Mama a gefe, sannan ta kama su Alhassan suka miƙe daga zaunen da suke.


Me martaba kuwa ya kasa cewa komi, a zuciyarsa baya son tafiyarsu amma idan ya ce zai hana, sai ya rinƙa jin tsoron Mama ya rasa menene dalili.

Muslimat ce ta ce "Duk abin da ke faruwa na sani kuma na samu labari, zamu tafi da su Fulani kamar yanda ku ke buƙata, amma fa ki sani cewar ke da ƴaƴanku akwai ranar nadama, na san cewa ba laifin Baffa ba ne ke ce silar duk abin da ke faruwa a gidannan"

Muslimat ta ƙarasa maganar tana nuna Mama cikin fushi.

Zage-zage su Bilkisu suka fara kamar ƴaƴan maguzawa, ba tare da su Easha sun amsa musu ba suka kama hannun Hajiya babba suna mai barin ɗakin, part ɗin Fulani suka koma dan haɗa kayansu, cikin ƙanƙanin lokaci suka gama shiri tare da barin gidan.

Mama na ganin su Hajiya sun bar gidan ta nufi part ɗin Me martaba, dan yanzu zama Fada ma ba kowanne lokaci yake yi ba, zaune ta same shi kan ƙayataccen gadonsa na alfarma, bed ne wanda ya amsa sunansa bed duk an yi masa ado da gold, ɗakin ya tsaru fiye da tunanin me tunani, sanyin Ac kuwa sai ratsa ko'ina yake.

Babu sallama ta faɗa ciki tana mai faɗin "Shuraihu wai ina takaddun da na yi maka magana ne?"

Me martaba da ya shiga duniyar tunani tun da su Fulani suka bar gidan gabansa ke faɗuwa, ɗago idanunsa ya yi yana mai faɗin "Wallahi na duba duk inda na san takaddun suna aje amma banganiba, kuma Alhassan kawai ya san inda na zuba su"

Dafe ƙirji Mama ta yi tana mai cewa "Kutumar Uba ƙarya ne baza ta sabu ba, dole ka san abin yi, idan ba haka ba ran kowa zai ɓace a gidannan"

Haƙuri ya shiga bata yana mai cewa zai nemo su duk inda suke.

Sai da ta gaji da masifa kafin ta fice daga ɗakin.

Me martaba kuwa dafe kansa ya yi yana mamakin abin da ke shirin faruwa da shi.

Mama na shiga ɗaki ta zauna kan sofa cike da rashin imani ta danna wata number a wayarta, bugu biyu aka ɗaga.

Daga can ɓangaren ba ka jin abin da ake faɗa, sai da ta gama sauraren abin da ake cewa kafin ta ce "Wani aiki nake so yanzunnan, zan tura maka hotunan wasu mutane ina buƙatar a kashe min su har lahira, bana son ka kirani zan kira da kaina, ba a jima da suka bar gidannan ba"

Shuru ta kuma yi alamun ana magana, sannan ta ce "Okay zan tura maka address na unguwa biyu yanzunnan, ina da tabbacin baza su wuce nan ba" Tana gama faɗin haka ta kashe wayar.

WhatsApp ta shiga tare da tura masa hotunan su Fulani da kuma address ɗin gidansu Easha da Muslimat, tana mai sakin murmushin mugunta a fili ta ce "Yanzu aka fara wasar, idan har ni ban haifi ɗa namiji a gidannan ba wallahi babu wanda ɗansa namiji zai yi rayuwa a ciki"

Su Esha kuwa suna barin gidan hanyar gidansu Muslima suka nufa, tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce uffan, kamar daga sama suka ji motarsu ta tsaya cakkk, Esha da ita ke driving ne ta fito dan ganin abin da ke faruwa, dariya suka ji an bushe da ita ana fata hannu, a ruɗe Easha ta maida dubanta kan wasu matasa kusan su biyar hannunsu ɗauke da bindigogi, su Fulani kuwa gaba ɗaya hankalinsu ƙara tashi ya yi, nan take matasan suka fiffito da su daga cikin motar, ɗaya daga cikinsu ne ya kalli Hajiya ya ce "Ranki ya daɗe mu umarni mike bi, kuma idan har da kuɗi babu abin da baza mu iya ba, a tsarinmu idan aka sa mu kashe mutum to sai mun fara faɗa masa wanda ya saka mu, da farko ni ne shugaban wannan dawagar kuma ba shakka kashe ku zamu yi kamar yanda muka faɗa, wadda ta saka mu kuwa ita ce wannan"

Hoton Mama ya nuna musu yana bushewa da dariya, duk cikinsu babu wanda ya yi mamaki dan sun san aikinta ya wuce hakan, har sun auna bindiga da niyar fasa musu kai sai Ogan su ya yi saurin dakatar da su yana cewa "Ku tsaya ai baza ayi haka ba, sai na fara ɗana kowacce daga cikinsu kafin su bar duniya, har ke tsohuwa ba zan raga miki ba, dan naga ku danginku dangin kyawawa ne"

Ya ƙarasa maganar yana lashe baki, umarni ya bada cewar a tattare shi dan ya fara da Husna da tun ɗazu jikinta ke rawa, sauran matasan ne suka tattare Ogan nasu aka saka Husna tsakiya, Fulani da su Hajiya Babba kuwa rushewa da kuka suka yi cikin tsananin takaici, ga hanyar ba mutane balle wani ya taimaka musu, su Alhassan kuwa tuni zufa ya gama wanke musu jiki, cikin ƙaraji Fulani ta ce "Ya ku waɗannan la'anannu kafin ku fara lalata min ƴa ina buƙatar ku kasheni dan ba zan iya ganin wannan tozarcin ba"

Dariya suka kwashe da ita cikin mugunta Babbansu ya ce "Ai bakin alƙalami ya bushe bayan na gama da ƴarki kema zan dawo kanki" Ya faɗa yana jifa da Husna ƙasa.



..........................
A gefensu Muby kuwa wani irin duka ya kaiwa ƙofar da ƙafa ai kuwa ta ɓalle, a tsaye ya samu Bosho na ƙoƙarin cire kayan jikinsa, tuni idanun Muby sun ƙanƙance be san lokacin da ya zubawa Bosho razanannen naushi ba, wanda ya sa shi faɗuwa ƙasa a sume, Malan na bakin ƙofa yana kallo dan kunya ta hana shi shiga daga ciki, duk da cewar Bosho ya suma amma Muby be ƙyalesa ba ya shiga dukansa hannu da ƙafa, sai da ya masa shegen dukan da ya canza masa kamanni kafin ya tuna cewar Malan na bakin ƙofar, da hannu ɗaya ya ɗaga Bosho yana mai jifa da shi waje.

Gurin Afnan ya koma tare da rungumeta a ƙirjinsa, sai a lokacin kukan da yake riƙewa ya kwace masa, sosai Muby ke zabga kuka tamkar ƙaramin yaro, hakan ya sa Malan shigowa cikin ɗakin be ko kalli halin da ɗan nasa ke ciki ba, rarrashin sa ya shiga yi amma ina ran maza ya ɓaci, tun da Allah ya haliicesa be taɓa shiga ɓacin rai kamar na yau ba, jijiyoyin kansa sun tashi ruɗu-ruɗu.

Malan ne ya ce "Allah ya ba ka nasara dan Allah ka daina wannan kukan, mu ƙara godewa Allah da ya sa be riga ya yi mata wani abun ba" Cikin tsawa Muby ya ce "Da kuwa sai na kashe shi da hannuna, saboda ita ɗin matata ce kuma ina ƙaunarta fiye da yanda nake son raina, zan iya rabuwa da kowa da komi saboda ita"

Ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji kamar namijin zaki, gaba ɗaya ya mance cewar Malan ne a gabansa, Mandula kuwa na bakin ƙofa tana jin yanda Muby ke zuba magana, Malan ne ya kuma cewa "Ka daidaita natsuwarka zuwa anjima zamu yi magana"

Ya faɗa yana mai barin ɗakin, a nan waje ya sami Bosho rashe-rashe, cikin takaici ya ja shi zuwa ɗakinsa, Mandula kuwa ta fice daga gidan dan dama ta zo ƙara duba Afnan ne.


A daren ranar kasa matsawa ko nan da nan Muby ya yi, Afnan kuwa idanunta a buɗe ta zuba masa su amma ko ƙyaftawa bata yi, ganin ba zai iya kwana ba wanka ba ne ya sa shi fitowa ya haɗa musu ruwa tare da komawa ɗakin ya ɗauko Afnan suka shiga wankan tare, da ƙyar ya iya yi musu wanka dan gaba ɗaya ƙyanƙyamin bayin yake, duk da cewar ba wata ƙazanta a ciki, amma a rayuwarsa be taɓa ganin bayi irin wannan ba, sai da ya kammala shiryasu cikin haɗaɗɗun kayan bacci kafin ya feshe su da turarukka masu daɗin ƙamshi, ƙurajen da ke jikinta kuwa sai yaga sun ƙara zubowa, kwantar da ita ya yi kafin ya rufeta da wani zanin gadon da ke gafe, duk abin da yake tana binsa da ido har ya zauna gefenta, wayarsa ya duba ko zai ga idan network ya dawo amma shuru har yanzu, a lokacin ƙarfe sha ɗayan dare, ga bacci ya ƙauracewa idanunsa, kuma abin da ke ɗaure masa kai shine rashin baccin Afnan, ganin katifar na da ɗan faɗi ne yasa shi kwanciya gefenta ya ƙara matsota jikinsa kamar wanda za'a ƙwace masa ita, a hankali ya fara jin wani sauyi na bin jikinsa, mararsa kuwa ta fara hautsinawa, cikin ƙarfin hali ya dafe gefen marar yana lumshe kyawawan idanunsa, tun abin na yi kaɗan har ya fara fin ƙarfinsa, musamman haɗa jikin da ya yi da Afnan sai wani zugi yake ji kamar ana datsa shi, kusan ƙarfe ɗaya bacci ya ƙaurace masa, kuma duk zai duba sai yaga idanun Afnan a buɗe, a lokacin zufa ta gama wanke masa jiki, gaba ɗaya karkarwa yake kamar me jin sanyi, idanuwansa kuwa sun ƙanƙance, ai be san lokacin da ya fara romancing ɗinta ba, cikin hikima ya haɗe bakinsu guri ɗaya yana masa wani irin tsotsa.






*Daga Asmeey ta Hydar, Sayyada ta Sayyadi*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 21




Gaba ɗaya ya fice a hayyacinsa, sosai yake mirzata ya mance da rashin lafiyarta, duk abin da yake idanuwan Afnan a tsaye tana kallonsa amma babu halin ɗaga koda yatsarta, ya daɗe a haka har ya samu sauƙin feelings ɗin nasa, a hankali ya koma gefe yana sauke numfashi, a ransa yake faɗin ita wannan komi nata daɗi ne da shi, be san lokacin da ya saki murmushi ba, sai da ya ƙara yin wani wankan kafin ya samu bacci.

Bosho kuwa tun da Mahaifinsa ya maida shi ɗaki be farka ba sai can dare, bakinsa ɗauke da ihu amma ihun baya fitowa sosai, duk jikinsa ya yi laushi, haka ya koma baccin wahala ba tare da wanke jiki ba.

Ƙarfe tara na safe zaune suke tsakar gida, bayan sun gama tattaunawa kan yanda lamarin zai kasance ne Muby ya ƙara watsa ruwan addu'ar, amma wannan karon be ɗaga daga bakin ƙofar ba, Bosho kuwa sai a lokacin ya fito daga ɗakinsa yana dafe jikinsa da ke tsami, ba tare da ya gaishe da kowa ba ya kalli Mahaifinsa yana faɗin "Baba ina karin kumallo na?"

Kallo ɗaya Malan ya yi masa yana mai ɗauke kai, sai Muby ne ya amsa masa da cewa "Ka duba ɗakin Malan akwai sauran kunun gyaɗa ka ɗauka"

Wani irin mugun tsaki Bosho ya ja yana faɗin "To kai ina ruwanka, idan har ba mafarki nayi ba jiya kaine ka min ɗan iskan duka, to wallahi ka jawa kanka dan sai na lalata shegiyar yarinyar da ka dakeni saboda ita"

A fusace Muby ya miƙe tare da chakumo Bosho yana ɗaukesa da mahaukacin mari, idanunsa sun rine zuwa ja ya ce "Wannan ya zama na ƙarshe, idan har ka sake gangancin kallon matata sai dai wani ba kai ba".

Jifa da shi ya yi gefe yana mai komawa ya zauna, Malan dai be tanka ba, Bosho kuwa kwalar rigarsa ya gyara yana mai shigewa ɗaki.


Har lokacin sallar azahar ta yi Muby na zaune a gurin shi da Malan suna fira, amma Bosho ya daɗe da fita gidan tun da ya ci abincin safe, da ƙyar Malan ya samu kan Muby suka tafi masallaci shima ba wata addu'a da ya tsaya ya dawo gida.


ƘASAR SUDAN
...........................
A ɓangarensu Munirat kuwa muryar Mommy ta ji tana faɗin "Dakata Munirat" Cakkk ta tsaya idanunta sun kaɗa, inda suke tsaye Mommy ta ƙaraso tana mai jan hannunta suka zauna, Ameer da ke tsaye ne ya sunkuyar da kai ƙasa dan be san ko Mommy ta ji abin da ke faruwa ba, shuru gurin ya ɗauka na ɗan wani lokaci kafin Mommy ta ce "Bana buƙatar Abbanku ya ji labarin abin da ke faruwa, kuma ina sane da duk maganar da ku ka yi"

Daga Ameer har Munirat kallon Mommy suke cikin mamaki, ɗaga musu kai ta yi alamun eh, kafin ta cigaba da faɗin "Duk maganar da ku ka yi na ji, dan haka ku bar komi a gurinku har sai Yarima ya dawo, yanzu idan ki ka nunawa Abbanki wannan abin ai be dace ba, tun tsiraicin matar ɗansa ne"

Munirat ce ta ce "Allah ya sawwaƙewa Brother wallahi, ya fi ƙarfin fasiƙa kamarta"

Kafaɗarta Mommy ta dafa cikin sanyin jiki ta ce "Na sani amma ku bar zancen kamar yanda na ce" Ɗaga kai suka yi alamun sun ji kafin suka koma cikin gidan.

Kwana biyu da zuwan Munirat gidan amma ta kasa zuwa gidan Muby dan ta duba Maimun, yau ta kama weekend haka kawai take son zuwa gidan, Ameera ta sanarwa ta shirya zasu tafi gidansu Maimun, cikin zumuɗi Ameera ta nufi ɗakinta dan shiryawa.

Shigar alfarma suka yi kaya iri ɗaya ne jikinsu amma kowa da kalar na shi, less ne me masifar kyau ruwan madara ya ji aikin stones a gaban rigar ruwan gold, ba ƙaramin sheƙi suke ba, a parlourn suka haɗe inda suka sami Mommy da Ameer suna fira, Ameer ne ya ce "Aunty Munirat ina zuwa haka?"

Yamutsa fuska Munirat ta yi kafin ta ce "Gidansu Brother"

"Amma kin san cewa Brother baya nan me za ki tafi ki yi a gidan kuma?"

"Wai Ameer ka bani ajiya ne? ko Mommy da na faɗa mata bata hanani ba sai kai, bana son hauka ka shiga hankalin ka da ni"

"Allah ya ba ki haƙuri, daga jiya zuwa yau Aunty kin canza sai faɗa ki ke yi"

"Kaine ka canza ni ai"

Dariya Ameera ta kwashe da shi tana tafa hannu, harara Ameer ya galla mata cikin jin haushi ya ce "Ni sa'anki ne?"

Shuru Ameera ta masa tana danne dariyarta.

Mommy da ke zaune tana sauraronsu ne ta ce "Kunga dan Allah ku tafi surutunnan ya isheni haka"

Zumbur Ameer ya miƙe "Nima zan tafi"

Ba tare da Munirat ta hana sa ba suka fice daga parlour, a harabar gida suka samu motoci goma da Munirat ta ce a shirya musu, Kuyangi mata su biyar ne suke take musu baya sai Dogarai kusan su goma, ba tare da ɓata lokaci ba motocin suka keta unguwar cikin ban sha'awa.


Dan gudun kar a san da fitarsu ne ma yasa Munirat ta hana a busa algaita, a ƙanƙanin lokaci suka sauka gidan, dirrect part ɗin Maimun suka nufa, sautin waƙoƙine kawai ke tashi har suka shiga parlourn, Munirat,Ameer,Ameera, kasa motsawa suka yi ganin taron maza da mata cike kamar gidan biki, a gefe ɗaya Maimun ce cikin shigar ƙananan kaya, kwalaben shaye-shaye kuwa a zube, toshe hanci suka yi dan warin giyar da ke tashi, sai a lokacin Hajara da ke duƙe ta yiwa wani saurayi botso ta ɗago tana kallonsu, a rikice ta miƙe tana mai gyara zaman bra ɗinta, ƙarasa shigowa su Ameer suka yi har gaban Maimun da hankalinta ma baya kanta, duk ta bugu sai surutai take yi.


Cike da ɓacin rai Munirat ta dakawa mutanen da ke ɗakin tsawa "Uwar me ku ke jira? kowa ya fice tun kafin ranku ya ɓaci, kai kuma tsohon banza ka sani cewar duk abin da ka yiwa ƴar wani sai an yi ma naka ƴaƴan, duniyar yanzu ma ba ka yiwa ƴaƴan wasu ba anyiwa naka balle ka yi" Ta ƙarasa maganar tana kallon Dajjijon da ke kusa da Maimun.

Miƙewa Maimun ɗin ta yi tana bushewa da dariya ta ce "Babu wanda zai fita, ke gidan Ubanki ne da za ki korar min mutane, wai tsaya ma ke wacece?"

Ameer ne ya ce "Uwarki ce shegiya ballagaza, wallahi duk sai Yarima ya kulleku idan ya dawo" Ai tun kafin ya rufe baki duk mutanen da ke ɗakin sun runtuma da gudu har Hajara ƙawar Maimun, Ameera ce ta ce "Lallai Aunty Maimun ko kuma na ce Maimun, ashe dama haka halinki ya ke? wallahi na tsaneki banza kawai Allah ya isa tsakaninmu da ke".

Dariya Maimun ta saki tana matsowa kusa da Ameera da niyar riƙota, cikin sauri Ameera ta matsa tana watsa mata harara, Munirat kuwa kasa magana ta yi tsabagen ɓacin rai, a fusace ta cewa su Ameer "Ku fito mu tafi dama abin da nake son tabbatarwa ne, kuma yanzu na ƙara gamsuwa"

"Me ki ke son tabbatarwa ne?" Cewar Maimun tana zubewa ƙasa, dan jiri ke ɗibarta.

Banza Munirat ta yi mata tana mai barin parlourn, Ameera ma ta bi bayanta, Ameer kam sai da ya ƙara ɗaukar wasu hotuna da kuma kayan shaye-shayen da ke gurin kafin ya bi bayansu.

Maimun da ke kwance rashe-rashe ne ta tashi da ƙyar tare da haurawa sama, tun daga bakin ƙofar ɗakinta take zuba amai har ta shiga ciki, sai kuma ta fara sosa mazaunanta, yau kwana biyu kenan suna yi mata ƙaiƙayi, sosai take sosawa har da samun wani ɗan ƙaramin kara ta cigaba da sosa gurin.

Su Munirat kuwa suna isa gida ta wuce part ɗin Mommy, kuka ta fashe da shi cikin takaici dan ta rasa me zata fara cewa.

Sai da ta yi me isarta kafin Mommy ta tambayeta abin da ke faruwa, duk abin da ya faru Munirat ta zayyanewa Mommy kafin ta ƙara da cewa "A gaskiya mun yi sake sosai, tun farko ba wani son aurennan nake ba, tabbas Maimun bata dace da Brother ba, Mommy ina tsoron abin da zai faru idan ya san halinta"

Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana mai cewa "Ni kaina ina tsoron abin da zai faru, yau kwana biyu kenan da tafiyarsu amma Numbersa baya shiga na san network ne, fatanmu Allah ya ba Gimbiya lafiya"

Da Ameen Munirat ta amsa tana mai ɗaukar wayarta da ke ƙara, ganin sunan Lovely ne yasa ta ɗaga tare da ficewa daga ɗakin.



Tun da Hajara ta bar gidansu Maimun bata dawo ba sai washe gari, a ɗaki ta sami Maimun zaune tana busa sigari hankali kwance, duka Hajara da kai mata tana faɗin "Amma ke banza ce wallahi, har kin samu damar sakin jiki haka bayan kin san abin da ya faru jiya"

Gyara zama Maimun ta yi kafin ta ce "Me ya faru jiya kuma?"

"Mtsssss! kina nufin ba ki san Munirat da ƙannenta sun same mu a halin maye ba"

Wani irin sarƙewa numfashin Maimun ya yi har ta fara tari, sigarin da ke hannunta kuwa ya faɗa kan bed bata saniba, Hajara ce ta ce "Ai gara ki sarƙe kam, tashin hankali

Please Login or Register in order to submit comment