Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefe suka shige, Easha kam ta gama lura cewa akwai matsala tsakanin Afnan da Muby, duk da ta san cewa dama ba jituwa a tsakaninsu.

"Mrs Mubarak wai me yake faruwa ne? nifa ban gane irin wannan zaman naku ba"

Mayafin da ke jikinta Afnan ta ɗora kan bed tana mai faɗin "Hmmm babu komi fa, kawai ɗan ƙaramin saɓani ne amma zan shawo kan lamarin"

"Kina nufin har yanzu babu zaman lafiya a tsakaninku?"

"Wallahi lafiya ƙalau muke, kawai kwana biyu ne sai a hankali"

Cewar Afnan tana latsa wayarta, duk yanda Easha ta yi dan ta san abin da ke faruwa amma Afnan ta gagara faɗa mata, saboda ba kowanne sirri take sanar da su ba, musamman kan lamarin aurenta.

Ƙofa Easha ta yi kafin ta ce "Idan ta yi wari zamu ji, amma fa ki bi a sannu dan yanda Yarima ke da kyau haka wata na iya ƙwace miki shi, dan kin ga izina daga Fadila ma"

Wata irin muguwar faɗuwar gaba ce ta kama Afnan, dan sosai take jin son mijin nata har ranta, tana cikin wannan tunanin ne Muby ya shigo waya a kunnesa, kana ganin fuskarsa ka san cewa da mace yake magana, kuma kamar soyayya suke yi.

Ai Afnan bata ƙara firgita ba sai da ta ji ya ce "Masoyiyata zan kira ki anjima ina kusa da Mommy ne"

Ba ka jin abin da ake faɗa daga can ɓangaren, shiyasa Afnan bata ji amsar da yarinyar ta bashi ba, ƙatse wayar Muby ya yi yana mai miƙawa Easha handbang ɗinta "Ki duba wayarki a ciki ina jin kira na shigowa kusan 2 missed calls" Karɓar handbag ɗin Easha ta yi tana godiya shi kuma ya fice ba tare da ya kalli inda Afnan ke zaune ba, zuciyarta har wani zafi take ranta ya gama ɓaci kamar ta kurma ihu, "Idan za ki tashi ki bi mijinki ki tashi dan wallahi yanzu ba'a wasa da mazaje, nikam bari na ɗaga waya Habibi na kira ɗan albarka" Easha ta ƙarasa maganar tana ɗaga waya tare da ficewa daga ɗakin, ai Afnan bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, duk fuskarta ta jiƙe da hawaye ganin take har yanzu yana can yana waya da wata.

Bayansa ta bi da sauri har tana ƙoƙarin zamewa.

Daga Ashwan sai Muslima ta samu a parlour, sai dariya suke kamar sun daɗe da sabawa, kamar zata yi kuka ta ce "Yaya Ashwan ina mijina?"

Dariya su Ashwan suka kuma yi ganin yanda ta ɓata fuska, Muslima ce ta ce "Ya tafi room ɗinsa ki same shi a can" Ai bata jira abin da Muslima zata ƙarasa faɗa ba ta bar parlourn. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga ɗakin nasa, yana kwance kan makeken bed ɗinsa, har yanzu waya ce a kunnensa sai faman dariya yake kamar wanda aka yiwa albishir da aljannah, gaba ɗaya kishi ya tsayawa Afnan a wuya, jira kawai take ta fashe.

Muby da ke kwance kuwa ya ji shigowarta sai ma ya ƙara sautin dariyar har yana faɗin "Allah Baby ke ta musamman ce, gaskiya ban taɓa haɗuwa da macen da ta iya soyayya kamar ki ba, ina faɗa miki ni matata bata kula da ni, shiyasa ma na ce bari na amince miki kawai ayi bikinnan kowa ya huta, zan faɗawa su Abba ko za su zo nema min aurenki" Kasancewar wayar na speeker ya sa Afnan ta ji yarinyar na faɗin "Godiya nake sosai rabin raina, ka san na daɗe ina jiran wannan ranar, kasancewar ba ƙaramin so nake yi maka ba, bana son na rasaka......" Ai bata ƙarasa ba Afnan ta yo kukan kura ta faɗo kan bed ɗin, wayar ta raruma tare da bugawa a ƙasa ji ka ke ƙasssss, ta yi kaca-kaca, kuka ta fashe da shi har da birgima a ƙasa, sosai take kukan kamar ranta zai fita, Muby kam be ce mata komi ba ya miƙe yana ƙoƙarin barin room ɗin fuskarsa a haɗe.




..............................
A ɓangaren su Nabeelah kuwa biki na ta ƙarasowa sai shirye-shirye ake babu kama hannun yaro, zancen Muby kam har tana mancewa da shi ma, abin da ta lura shine ba ƙaunar aurensa take ba, kawai kyawunsa ne ke ruɗarta, dan Nabeel ma ba laifi ya iya soyya tamkar zai haɗiye ta, kullum magana ɗaya Allah ka mallaka masa ita a matsayin abokiyar rayuwa, Nabeelah kam sai dai ta yi shuru tana sauraronsa dan yanzu tana jin son sa sosai a cikin ranta.

Ranar Friday suka shigo ƙasar Sudan sayayyar kayan aure a Shop ɗin Yarima Muby, wannan shawarar Fadila ce tana son ganin Muby ko so ɗaya kafin aurenta, "Nabeelah......Nabeelah...." Ta ji ana kiranta, a tsorace ta juyo dan ganin waye.







*Mu haɗe a next page please, ku yi share saboda Allah, waɗan da basa group na sharhi ku yi reacting hakan ma ya wadatar amma babu like kuma ba ki shiga group na sharhi ba gaskiya before na fara next book zan yi waje da ko wacece*




*GIDAN MULKI*


*By*

*Asmeetar Hydar*










P. 28







Fadila ce a tsaye tana rusa ihu, da sauri Nabeel ya ƙarasa gurin ganin Nabeelah har ta riga shi isa, da gudu suka iso bakin titin da Mahaifiyarta ke kwance cikin jini, Fadila na kuka tamkar zata yi hauka ta tallafo Asabe duk fuskarta ta yi kaca-kaca da jini, Nabeelah ce ta kama mata suka nufi mota da ita, Hospital ɗin da ke kusa suka kai ta, amma kafin a fara wani abun rai ya yi halinsa, ba ƙaramin girgiza mutuwar ta sa Nabeelah ba, Fadila kam zubewa ƙasa ta yi a sume dan a halin yanzu komi ya ƙare mata, dama Mahaifyarta ce kawai ta rage yanzu kuma Allah ya ɗauki ranta.

Sai da aka yi jana'izarta kafin Fadila ta farka, Nabeel da Nabeelah na gefenta a zaune, duk rashin imaninka idan ka kalli Fadila sai ka tausaya mata, kuɗi suka aje mata tare da biyan Doctor kuɗin magungunanta, Nabeel ne ya ce "Tom mu zamu tafi saboda a yau mike son komawa, Allah ya gafartawa Mahaifyarki tare da duk wani musulmi"

Muryar Fadila na rawa ta amsa da "Ameen na gode sosai, Nabeelah Allah ya biya ki kuma ina roƙon da ki yafe mun duk abubuwan da na yi miki"

"Na daɗe da yafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya"

Fadila na kallo suka bar ɗakin, zuciyarta na ƙuna tamkar zata fito daga ƙirjinta.

Washe garin ranar aka sallameta, ɗan kuɗin da suke bara da wanda Muby ya bata ne ta tattara ta kama gidan haya daidai da ita, ɗan ƙaramin ɗaki ɗaya me ɗauke da bayi, ƙaramar shimfiɗa ta saka da kuma kayan amfani daidai ƙarfinta, kwana uku da rasuwar Mahaifiyarta Fadila ta fara sana'ar Awara a bakin ƙofa, ba laifi tana samun mutane masu saya har ta kawar da wasu lalurorinta.



........................
Afnan kuwa tana ganin Muby zai fice ta ƙara sautin kukanta har tana bubbuga bed ɗin, dariyarsa ya ƙumshe tare da ƙarasowa gurin, daidai lokacin da wayar Afnan ta fara ƙara, ko kallon inda wayar take bata yi ba, hakan ya sa Muby ɗauka ganin sunan Munirat ne ya sa shi ɗagawa, tun kafin ya ce wani abun ya ji ta ce "Aunty Afnan congratulation na ji labarin kun tare a sabon gida, and ges what? ina da ciki wata biyu"

"Tom sannu marar kunya ba ita ba ce, mijinta ne" Cike da kunya Munirat ta ce "Brother..... so sorry amma ina ita Gimbiya ne?"

"Bansaniba malama ina tare da matata ki kashe wayarki, ba ita za ki faɗawa kina da ciki ba sai dai Alhaji Babba" Ɗifffff Muby ya ƙatse wayar, a lokacin Afnan ta zuba masa ido jin abin da yake cewa, ganin yanda take kallonsa ne ya sa shi aje wayar yana haɗe fuska.

"Kin gama kukan ne? ko har yanzu da saura"

Banza ta yi masa sai ma kawar da kai gefe, sannu a hankali ya zauna yana faɗin "Fushi ki ke har yanzu ko na tafi gurin rabin raina...." Wangale baki Afnan ta kuma yi kamar zata rusa ihu, caraffffff ya haɗe bakinsu guri ɗaya yana mai sakar mata kissing lafiyayye, sosai saƙonninsa ke shigarta, dan har wani shiɗewa take, dama abin da take so kenan ai kuwa ta fara mayar masa da martani, gaba ɗaya ta gigita shi da yanda take sarrafa harshenta a cikin bakinsa, ba ƙaramin mamaki ya sha ba ganin yanda Afnan ta mugun iya kiss kamar ta shiga makarantar koyon sumbata, kayan jikinsu ya fara rage musu ba musu ta taya shi, suka ƙara luluƙawa duniyar soyayya, yau kam ya gama sarewa da lamarin Afnan dan ita ce ta koma mijin ya dawo mata, duk wani sashe na jikinsa sai da ta murje, ita kanta bata san ta iya waɗannan abubuwan ba, duk yanda ya so ya yi sex amma ta hana masa, amma ta gamsar da shi sosai har ya samu natsuwa, ita kanta ta ji daɗin yanda ya saraffata tamkar zai maida ta jikinsa.

A gefe suka koma suna sauke numfashi, Afnan kuwa ta matsa tana mai shigewa jikinsa ta ƙanƙame shi, cikin zolaya ya ce "Ai na ji sai ihu ki ke min wai akwai daɗi kar na daina" Waro haɗaɗɗun idanunta ta yi cikin shagwaɓa ta ce "Amma kaima ka ce mun baza ka ƙara min kishiya ba, kuma har da cewa wai a saman sararin samaniya mike ko a ina" Dariya Muby ya yi yana kashe mata ido ɗaya "Ni bansan na faɗi hakan ba, ke ɗin ta musamman ce, amma please yaushe za ki bani wancan ɗin"

"No sai na warke, har yanzu akwai....."

Amai da ya zo mata ne ya sa ta kasa ƙarasa maganar da take son faɗa, gaba ɗaya ta lalata masa jiki duk idanuwanta sun yi jajir, sai da ta gama zuba aman kafin ya nufi toilet da ita, a lokacin an fara kiraye-kirayen sallar magrib, su Ashwan kam sai faman jiran fitowar sa suke amma shuru, dan haka suka nufi masallaci har da Ameer.


Kafin ka ce me Afnan ta zuba amai ya fi so uku, duk ta galabaita kamar wadda ta kwana ɗaya a kwance ba lafiya, Muby kam ya firgice sai sannu yake yi mata, tausayinta ya gama rufe sa ganin yanda take wahala, sai da ya gama gyara gurin da ta ɓata kafin ya ƙara yi musu wanka, sallah ma a gida ya yi, itama da ƙyar ta samu yin sallah dan jirin da ke ɗibarta, tun kafin ta gama addu'a wani aman ya ƙara taso mata, da gudu ta nufi bayi shima ya rufa mata baya har yana tuntuɓe, wannan karon zubewa ƙasa ta yi dan tsabagen wahala, wanka Muby ya sake yi mata tare da shiryata cikin wando da riga, kan bed ya kwantar da ita yana faɗin "Baby sannu, ya jikin ne?"

A wahalce Afnan ta ce "Wacece ka ke waya da ita ɗazu?" Mamaki ne ya kama Muby dan shi ya mance da yarinyar ma, dama ya yi ne dan ya shawo hankalinta, "Kawai ki bar wannan a gefe, bari na aunaki ko zan san maganin da ya dace ki sha" Be jira abin da zata ce ba, ya nufi wani ɗan ƙaramin ɗakin da ke manne gefen wadrop, kayan awo ya ɗauko tare da zama gefenta, ido Afnan ta zuba masa zuciyarta na bugawa, ita hankalinta ya kasa kwanciya kan lamarin wadda yake waya da ita, aunata ya fara yi cikin ƙwarewa, jininta ya ɗiba kaɗan yana fatar abin da yake gani kan fuskar matar tasa gaskiya ne.

Sai da ya gama duk wani gwaje-gwaje kafin ya maida kallonsa kan Afnan da har bacci ya ɗauketa, wani irin farinciki ke ziyartar zuciyar Muby ganin cewa tana ɗauke da ciki sati biyu da kwana huɗu, dan murna ma har ya kasa zaune balle tsaye, Afnan da baccin be yi nisa ba ne ta farka tana mai zuba masa ido ganin yanda yake kallonta tamkar zai haɗiyeta, "Wacece wadda ka ke waya da ita?" Afnan ta kuma faɗa tana ƙoƙarin yin kuka, da sauri ya ƙaraso yana mai rungumeta "Sorry Baby dan Allah kar ki saka damuwa a ranki, kin san na faɗa miki ba ke ba kishiya insha Allah, amma kar ki sa damuwa ta taɓa lafiyar Babyanmu" Ya ƙarasa maganar yana shafa cikin Afnan, ɓata fuska ta yi tana faɗin "Banganeba...." Da gudu ta sauko tana mai nufar toilet, sosai take kwara amai har jikinta ya yi sanyi, Muby kam ya rasa abin yi dan ganin lokaci ɗaya ta canza kamanni, sai da ya ƙara gyara mata jiki kafin suka koma ɗaki, magunguna ya haɗa mata da allurori, "Ina zuwa bari na haɗa miki tea ko cikin naki zai ɗan tashi"

Sai da ya yi da ƙyar kafin ya samu ta sha, ai kuwa duk ta wanke masa jiki da shi, dan dole ya shiryata zuwa hospital, a parlor ya sami su Yusuf suna ƙoƙarin wucewa, ganin Muby ɗauke da Afnan yana zuba sauri ya sa gaba ɗayansu miƙewa, ko kallonsu be yi ba ya fara saukowa ƙasa, suma bayansa suka bi har gurin da motoci ke aje, a tsawace ya ce "Ina Driver ka buɗe mota" A rikice Driver ya buɗe masa ƙofa Muby ya saka Afnan bayan motar, ko jiran Driver be yi ba ya shige tare da ficewa daga gidan cikin matsanincin gudu, su Ashwan ma motoci suka shiga suna mai bin bayansa.

Hospital ɗinsa ya nufa da ita, babu ɓata lokaci aka shiga da ita room ɗin da ke cikin Office ɗinsa, duk Muby ya firgice dan ganin yanda numfashinta ke sama da ƙasa.


Mintuna talatin Nurse Farida ta ɗauka kafin ta fito fuskarta ɗauke da murmushi "Ina taya ka murna Sir, matarka na ɗauke da juna biyu sati biyu da kwana huɗu"

"Thanks na sani amma ya jikin nata, yanzu aman ya tsaya?"

"Yes Sir mun tsayar da shi, amma ya kamata ta samu lafiyayyen abinci domin jikinta zai samu ƙwari" Su Yusuf da ke gefe sai washe baki suke, Ameer kuwa ya kalli Husna a hankali ya faɗa yanda babu wanda zai ji "Saura ke, daga zaran na ƙarasa School zamu yi aurenmu ko? nima ki haifa min Baby"

Rufe ido Husna ta yi tana matsawa gefen Muslima, gaba ɗayansu cikin room ɗin suka shiga Muby ne a gaba sai murmushi yake.

Afnan na kwance ɗaure da Drip, gefen bed ɗin ya zauna yana mai kama hannunta "Baby sannu duk ni ne na ja miki ko?"

Itama shi take kallo amma ta kasa cewa uffan, ya jiki kowa da ke ɗakin ya yi mata, sai dai ta ɗaga kai kawai dan jikinta ya mutu, Muby kuwa sai magana yake kamar zautacce.

A nan suka yi sallar isha, ƙarfe takwas da rabi ruwan ya ƙare, Yusuf da Ameera ne suka tafi nemo abincin da zata ci, gasassun kaji ne guda biyar da kayan sanyi, sai Friderice wanda ya gaji da haɗuwa, ba laifi ta ci abincin amma magana sama-sama dan har yanzu da sauran gajiya a jikinta, bayan ta yi sallah ne suka fito domin barin hospital ɗin.

Ashwan da Yusuf motarsu suka shiga suna mai yi musu sai da safe, Ameer da Ameera ma haka, fuskar Husna cike da damuwa ta kalli Afnan da ke kwance gefen Muby ta ce "Ni gidansu Beey zan kwana"

Ai Afnan bata san lokacin da ta fincike jikinta daga na Muby ba, kama hannun Husna ta yi fuska babu walhala "Baza ki kwana ba, marar kunyar yarinya har kin san daɗin soyayya ko? ba Beey ba Boo, Muslima please ku shiga mota tare da Husna yau zan ga rashin kunya irin nata" Duk waɗan da ke gurin dariyar Afnan suke, ganin ta warware kamar ba me ciyo ba.

Tare da su Muslima Husna ta shiga, sai Muby da Afnan da ke mota ɗaya, tun da suka isa Husna ke haɗe fuska ita an hanata kwana gidansu Ameer, ɗakin da zata kwana Afnan ta nuna mata sannan ta kai su Muslima ɗaki ɗaya, sun jima suna fira sai tsiya suke yi mata wai me ciki me ciki, goma saura ta yi musu sallama dan baccin da ke damunta, a ɗakinta ta fara zuwa dan watsa ruwa, sosai ta yi wanka kafin ta shirya cikin wasu kayan bacci me masifar kyau, ƴar ƙaramar riga ce iya ƙugunta, idan ma ta ɗaga hannu zaka iya ganin cibiyarta, wandon ko da kaɗan ya wuce mazaunanta, gashin kanta ta gyara tare da ɗaurewa guri ɗaya, turarukka kuwa sai da suka yi kuka a jikinta, gorar maganin da Mommy ta bata ne ta fitar wanda har ya kusan rabi, duk ta shanye saboda daɗin da maginin yake da, sai da ta zuba a Cup kafin ta saka zuma kaɗan ta shanye, garin kanin fari ta ɗebo a cokali ta watsa baki, ƙarar buɗe ƙofa ne ya sa ta juyo tana ƙare masa kallo, Muby ne tsaye cikin shigar kayan bacci people colour shima, dogon wando da riga me laushi, Afnan na ganinsa ta marairaice fuska kamar zata yi kuka "Uhmmm...uhmmm...."

Da sauri Muby ya ƙaraso yana faɗin "Baby lafiya?"

"Ba yunwa nake ji ba"

"Yunwa kuma? to mu tafi akwai sauran kajin da Yusuf ya sayo miki sai ki ci"

"Aa Fara nake so, idan ba fara ba ni ba zan ci komi ba sai dai na kwana da yunwa" Ta ƙarasa maganar tana shigewa jikinsa, "Tom sarkin rigima, mu tafi na sayo miki" Tsalle Afnan ta daka tana mai buɗe Wadrop ta ciro ƙaton hijab ta zura, sai kallonta Muby ke yi ganin yanda na shanunta suka ƙara cikowa, fuskarta kuwa ta ƙara kyau, "Dan Allah ki daina tsalle tsallennan kar ki ja mana matsala"

"Hmmm ai yanzu zaka fi son Babynka fiye da ni ko? dama na san ba sona ka ke ba ka fi son Babynka" Afnan ta faɗa tana matso hawayen ƙarya, "Kai waya faɗa miki? ke ɗin jinina ce"

Daɗi ne ya kamata har wani gyaɗa kai take "Tom Babyn kuma fa?"

"Baby kuma rayuwata ne" Bubbuga ƙafa Afnan ta fara tana faɗin "Wallahi ba zan yarda ba, shine jini"

Dariya ta bashi ganin yanda take yi, "Tom na ji shine jini ke ce rayuwa, mu tafi ko"

A ɗakinsa suka koma ya saka jallabiya sannan suka fito.

Kasancewar goma da wani abu na dare ne yasa har yanzu mutane na nan kamar yanzu ne safiya ta waye, leda uku ya yi me ɗauke da Snacks da kuma kayan sanyi, Afnan kuma fara ce har roba uku masu girma, a mota ya sameta kamar yanda ya barta, tun a hanya Afnan ta canye robar Fara biyu har ta fara cin na uku, Muby kam kallonta kawai yake jin yanda take tauna farar.

Suna isa gida ya miƙa mata ledodin "Ki kaiwa su Easha da Husna"

"Tom sun gode, ka tafi zan sameka a ɗaki"

"Allah ba zan yarda ba sai mun tafi tare"

Ƴar dariya Afnan ta yi tana mai nufar ɗakin Husna, kwance ta sameta tana waya da Ameer, ƙara haɗe fuska Afnan ta yi kafin ta ce "Kin san bana son wayar dare ko? wallahi zan ɓata miki rai"

Kashe wayar Husna ta yi tana bata haƙuri, ba tare da Afnan ta kula ta ba ta aje ledar da ke hannunta "Gashinan Yarima ya ce a kawo miki"

Ta faɗa tana barin ɗakin, dan Afnan bata son Husna ta shigewa soyayya sosai tun tana ƙarama, balle yanzu da karatu ne a gabanta ko Secondry bata ƙarasa ba.

Ɗakin su Muslima ta kai sauran ledodin tana fitowa ta ci karo da Muby tsaye yana sakar mata killer smile "Wai duk inda na tafi sai ka biyo ni"

"Eh ina son na rinƙa kula mana da Babynmu ne"

Wucewa gaba Afnan ta yi tana faɗin "That's why i said ka fi son Babyn a kaina, sai naga wanda zai ƙara kwanciya a jikinka"

Muby na dariya ya rungumota ta baya, sai ji ta yi an ɗageta sama, tsalle-tsalle ta fara tana dariya, a ɗakinsa ya sauketa kan bed yana faɗin "Hmmm ai kuwa zan ƙara aure"

"Hahhhhh..., ka je ka ƙara sai na zubar da cikin jikina tun da dama ba sona ka ke ba"

A mugun tsorace Muby ya ɗago har idanunsa sun kaɗa sun yi jajir "Cikina za ki zubar? sai a yau na san cewa duk soyayyar da ki ke faɗa mun ba gaskiya ba ne, tsanar da ki ke mun baza ta taɓa zama soyayya ba"
Miƙewa ya yi da niyar ficewa ta yi saurin riƙo hannunsa fuskarta ɗauke da hawaye "I'm sorry mijina ba zan ƙara faɗar hakan ba, fushinka zai kasance zunubi a gareki, dan Allah kar ka yi fushi" Tausayinta ne ya kama sa ganin yanda duk fuskarta ta jiƙe da hawaye, a hankali ya zauna yana mai mannata a ƙirjinsa a tare suka sauke ajiyar zuciya, "Baby kar ki ƙara mun haka kin ji? ki cire duk wata damuwa a ranki, ba zan yi miki kishiya ba insha Allah, a halin yanzu bana da ra'ayin auren mata biyu" Cikin so da ƙaunar mijin nata ta ce "Thanks so much mijina"

"Ni ba wani godiya kawai ki bari na yi abin da ya dace"

Murmushi ta saki tana miƙewa tsaye "Tom bari na yi brush ka san na ci Fara, bana son mijina ya ji wani abun da ba ƙamshi ba a jikina, a kowanne lokaci ina buƙatar ka rinƙa jin ƙamshi ta kowacce siffa a jikina, ka san cewa ƙazanta ma na kawo ƙiyayya" Afnan ta faɗa tana nufar toilet, Muby kam da mamaki ya ke binta da kallo har ta shige, sabon brush ta buɗe sannan ta wanke bakinta sosai, sai da ta ƙara watsa ruwa dan tana jin wani iri a jikinta, Muby na jin ƙarar ruwa kamar tana wanka ya shige daga ciki shima, a tare suka yi wankan, Afnan kam zaƙewa ta yi ta wanke shi tassss, shima Muby haka har da wasu kalar abubuwan da hankali ba zai ɗauka ba, tun a bayi ya sakar mata kasala.

Kwance a ƙirjinsa suka fito sai dariya suke, babu wani jira Muby ya fara hargitsa mata tunani, Afnan kam abin da take so kenan dan ta rasa dalili tun ranar da Muby ya fara kusantar ta take masifar son ta ji ya ƙara yi, amma rashin warkewarta ne ya hana, duk da cewar Muby be shiga daga ciki ba amma Afnan ta gamsar da shi da salonta me tsayawa a rai.

Sai kusan ƙarfe ɗayan dare kowannensu ya samu gamsuwa, wanka suka shiga a tare tamkar zasu canye juna a bayin.

Kamar ƴar Baby haka ya kwantar da ita kan bed, kayan baccinsu ya maida musu tare da janyota jikinsa, addu'ar bacci ya yi musu yana mai rufe su da blanket, kasancewar bacci na idon Afnan ya sa tana kwanciya ya ɗauketa, Muby kam yana ganin ta yi bacci ya yo alwala tare da yin sallah raƙa'a biyu, sosai ya yi addu'a da kuma godewa Allah da ya mallaka masa mace kamar Afnan kuma ya bashi kyautar abun da yake so sosai a rayuwarsa.


Washe garin ranar tun ƙarfe tara na safe su Mommy suka zo gidan, Afnan sai sunne kai take ganin yanda Mommy ke tarairaya ta, tun jiya su Ameer suka sanar da mutanen gida, Me martaba ma ya yi murna sosai jin wannan

Please Login or Register in order to submit comment