Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi masa iyaka da Gimbiya Fadila, cikin sanyin jiki Muby ya ɗago kyawawan idanunsa ya sauke kan Alhaji a hankali kuma ya ce "Ayi mun afwa amma ba zan iya rabuwa da Fadila ba, saboda ita ce zaɓina kuma na yanke shawarar aurenta....." A tsawace me martaba ya ce "Kulll na raba ka da wahala, tun da ka tashi a gidannan ka taɓa ganin Alhaji ya yanke hukunci wani ya karya? dole zaka bi umarninsa"

Lumshe ido Muby yayi yana mai jin yanda zuciyarsa ke yi masa zafi, hankalinsa na ƙoƙarin barin jikinsa, kujerar da ke gefe me masifar kyau ya jingina tare da ciro hankacif ɗinsa me ƙamshi ya goge zufan da ke karyo masa, ba tare da sanin yayi furucin ba ya ce "Wannan shine karo na farko da ba zan bi umarninsa ba, Allah ya ƙara maka nasara" Muby na gama faɗin haka ya miƙe tare da ficewa daga parlourn, da sauri me martaba ya bada umarnin manya-manyan dogaran da ke tsaron fada da su kama Yarima Mubarak a kulle shi, Jakadiya aka aika ta sanar masa da saƙon. Parlournsa ta same shi zaune kan sofa yana zuƙa sigari, har wani rawa jikinta ke yi, dan bata taɓa ganin Yarima a wannan halin ba, "Allah ya baka nasara me martaba ne yayi umarni da a tafi da kai gidan gyaran hali, ya ce ko ta ƙarfin tsiya ne" Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonta, kafin yayi wani yunƙuri wasu majiya ƙarfin masarautar sun shigo tare da kakkamasa, duk da cewa suna da yawa amma da ƙyar suka iya tafiya da shi, Sarki Ahmad ya bada umarnin abinci ma so biyu za'a bashi tare da tsaresa har ranar da yayi nadama.

Maimun kuwa tashin hankalinta ya ƙaru jin abin da ke faruwa, a ranar Afnan ta bar ƙasar dan ko gidansu Muby bata tafi ba, kafin su Alhaji su ƙarasa ta daɗe ta barin ƙasar, dole haka suka dawo jiran abin da zai biyo baya.


A ɓangaren Gimbiya Fadila hana kowa zaman lafiya tayi a masarautarsu, ita ala dole Yarima Muby zata aura, tun lokacin da labari ya isa gurinta a kan an rufe Yarima ne ta fara shirin dawowa ƙasar, dama jirgin yamma ta bi to gashi dare yayi, sai da Mahaifinta ya rarrasheta a kan ta bari gobe zasu shiga ƙasar Sudan sannan ta ɗan kwantar da hankalinta.



ƘASAR SENEGAL
..............................
Tun da Sarki Shuraihu ya samu labarin abin da ke faruwa hankalinsa ya tashi, kai ba me martaba kaɗai ba hatta Hajiya abin ya ɗaga mata hankali, Fulani kuwa ɗaki ta shiga tana rusar kuka dan ta san ƴarta ta zama bazawara a halin yanzu, Mama kuwa daɗi ne ya hanata magana burinta ya cika.

Tun da Afnan ta shiga ɗakinta ta kasa fitowa dan sai yanzu take jin zafin sakin wulaƙancin da Muby yayi mata, tabbas gori da habaici zai fara tun da maƙiyanta sun samu abin da suke so.


Haka kawai ta tsinci kanta da tunanin daren jiya yanda suka rinƙa zagaye gida ita da Muby, saurin kawar da tunanin tayi tare da ɗaukar wayarta da ke ruri ta kashe gaba ɗaya.


Daga ƙasan parlourn take jiyo guɗa da ruri kamar ana ɗaurin aure, can ta fara jiyo muryar Bilkisu da Hajiya, tabbas ta san abin da take gudu ne ya fara faruwa.

Ɗan ƙaramin mayafinta ta ɗauka sannan ta fito daga ɗakin, Bilkisu ta gani ta sa masu aikin gidan duk sun yi sahu tana raba musu kyauta, a gafe kuwa Hauwa'u ce ke surutai da habaici, mamaki be ƙara rufeta ba sai da taga Mama na shigowa tare da me kiɗan kalangu, nan fa aka fara baje haja, masu rawa nayi masu kaɗe-kaɗe nayi.


Hajiya Babba kam kasa magana tayi dan lamarin yafi ƙarfinta, ganin haka yasa Husna nufar ɗakin me martaba ta sanar masa, bada ɓata lokaci ba ya bada umarnin duk family a hallara domin tattaunawa.


Hajiya babba bata taɓa shiga damuwa irin wannan ba, dan ko ita kanta Afnan ɗin abin be tada mata hankali kamar yanda hankalin Hajiya ya tashi ba, sun gama yanke hukuncin gobe zasu shiga ƙasar Sudan, saboda Muby ba zai saki ƴarsu a banza ba bayan ya gama tozartata, amma Hajiya Babba ta hana saboda bata son tashin hankali.


Me martaba ne ya gyara zama cikin fushi ya kalli Mama da ƴaƴan nata ya ce "Tabbas kun bani kunya kuma banyi mamakin abin da ku ka aikata ba, dama soyayyar da ku ke nunawa a fili ne kawai ba har zuciya ba?"

Kallonsa ya aje kan Bilkisu da ke zaune kafin ya cigaba da faɗin "Ke ce babba amma baki san inda ke yi miki ciyo ba, da ke da Hauwa'u ku tashi ku bar min gida kowa ta koma gidan mijinta, duk ranar da ku ka shigo gidannan sai wani tashin hankalin ya faru"

Mama ce ta ƙatse masa zancen da faɗin "Haba me martaba yara da gidan Mahaifinsu amma ana korarsu"

Shuru me martaba yayi jin yanda Mama ta yarfa shi gaban mutane, sai kuma ya maida kallonsa kan su Bilkisu cikin tsawa ya ce "Me ku ke jira? maza ku ɓace min da gani" Da sauri suka fice jiki na rawa, dan sarai sun san halin Mahaifinsu.

Nan Sarki Shuraihu ya sallami kowa, Afnan kuwa a ranar kasa bacci tayi, wani baƙin ciki ne ke ƙara zama a ranta, ta yanke shawarar daga komi ya lafa zata bar ƙasar.


WACECE GIMBIYA AFNAN?.

Shuraihu Muhammad Mulki, shine asalin sunan Mahaifinta ƴan ƙasar Senegal ne kuma cikakkun Shuwa'arab, Muhammad Mulki Mahaifin Shuraihu, shine sarkin Senegal a lokacin baya matarsa ɗaya aurensu shekaru goma babu magaji, matarsa me suna Habiba bata taɓa samun haihuwa ba amma hakan be sa Muhammad Mulki rabuwa da ita ko kuma ƙara aure ba, aurensu ya cika shekaru sha ɗaya ta samu ciki murna gurin mutanen Senegel da shi kansa Sarki Muhammad ba'a magana, sosai masauratar ta ɗauka kowa murna, ranar suna yaro ya ci suna Shuraihu wanda daga shi Sarki Muhammad be ƙara samun haihuwa ba, har Shuraihu ya cika shekaru goma, sosai suke nuna masa soyayya da kuma tarairaya shi, kowa masarautar na tsoron taɓa Shuraihu saboda wata irin izza da yake da baya son masu aikin gidan ko kaɗan, wannan ya samo asaline daga yanda iyayensa suka rene shi, a ƙasar indian yayi makaranta, lokacin da ya dawo yana da shekaru talatin sosai mulki da taƙama suka ƙara bayyana ga Shuraihu a can ya haɗu da wata matashiya ƴar sarkin ƙasar Chad me suna Hafsat, kasancewar kyawawan hallayarta da kuma riƙo da addini ya sa Shuraihu ƙara sonta, dan haka babu wani jan lokaci aka tura neman aure tare da saka rana, ranar da zasu dawo ɗaurin auren ne Allah yayiwa Sarki Muhammad Mahaifin Shuraihu rasuwa, masarautar Senegal ta girgiza matuƙa saboda adalin Sarki ne, bayan rasuwarsa da sati ɗaya aka ɗora Shuraihu Sarkin Senegal, yana da wata ƴar uwa me suna Zuwaira wadda ta laƙe masa a kan sai ya aureta, ganin haka yasa Mahaifiyar Alhaji wato Habiba yarda da auren dan ganin rashin yarda da hakan zai iya kawo wani tashin hankali, tun lokacin da Zuwaira ta shigo gidan zaman lafiya ya ƙare, musamman da aka bawa Hafsat Fulani, kullum cikin haibaici take.

A lokacin da aka auro Zuwaira Hafsat na da ciki, bayan wata tara ta haifo ɗanta namiji a ranar kamar Zuwaira zata kashe kowa da ke masarautar, kwana biyu da haihuwar yaro ya koma, ba ƙaramin tashin hankali Sarki Shuraihu ya shiga ba, amma haka suka fawwalawa Allah, daga lokacin Hafsat bata sake samun ciki ba, amma alamun ciki ya bayyana kan Zuwaira, tun da taga haka ta fara yiwa Fulani Habaici, Fulani kuwa sai dai ta tashi ta bar gurin ko kuma ta shareta, lokacin haihuwa Zuwaira ta haifo ƴa mace, wanda ba haka ta so ba, Sarki Shuraihu ya ji daɗi sosai kan ƙaruwar da aka samu, ranar suna yarinya ta ci suna Bilkisu, tun tana ƙarama Mahaifiyarta ke koya mata mugun hali, a haka har ta sake haihuwa ta haifo mace aka saka mata suna Hauwa'u, kamar zata tashi masarautar dan tsananin ɓacin rai, wai akwai wanda yake yi mata asiri yana canza yaran cikinta, sarai Fulani ta san cewa da ita Zuwaira take, amma sai ta bar zancen kawai, haka ta duƙufa da addu'a kan Allah ya bata haihuwa, cikin ikon Allah ta samu ciki amma cikin nada wata biyar ya zube, wannan karon sosai Fulani ta ci kuka a ɗaki, gori kuwa babu wanda bata sha kan Mama ba, har ta sake samun ciki na uku shima mace ta haifo yarinya ta ci suna Halima, a lokacin Fulani ta cire rai ga samun haihuwa tare da riƙe ƴaƴan Mama tamkar nata, bata nuna wani banbanci saboda Fulani mace ce me son yara.

Halima ƴar Zuwaira nada shekara ɗaya Fulani ta samu ciki, dan haka ta tashi hankalin Sarki Shuraihu a kan zata koma gida ta haihu a can, babu yanda ya iya haka ya barta, Mama kuwa baƙin ciki ne ya cika ta, lokacin da cikin Fulani ya cika wata tara Sarki Shuraihu ya tafi ƙasar Chad domin ganin halin da matarsa ke ciki, a ranar da ya isa ne ta haihu wanda ta haifo yara uku rassss maza biyu mace ɗaya, Sarki Shuraihu har da kukansa dan farinciki, bayan an gama gyara yaran ne Fulani ta nemi keɓancewa da mijin nata, inda ta ce masa ya ɓoye haihuwar mazan da tayi har sai lokaci yayi, sannan ta nuna masa tana son a ce mace kawai ta haifa, da farko Sarki Shuraihu ya nuna rashin amincewarsa da ƙyar Fulani ta sha kansa, ranar suna yara suka ci suna Alhasan sai ɗayan kuma Muhseen, kasancewar macen ita ce da ƙarshe sai suka saka mata suna Afnan, ana kiranta da Gimbiya, bayan suna da wata goma ta bar ƴaƴan nata maza a gurin iyayenta, sannan suka koma da macen me suna Afnan, babu irin muguntar da ƴaƴan Mama basa yiwa Gimbiya sun tsaneta, idan kaga tana dariya tabbata suna tare da Halima, babu abin da ke ɗagawa Mama hankali irin ganin kyawun Gimbiya wanda kowa ke masifar sonta, ita kuwa yarinyar ta faye zama gurin Mahaifinta Sarki Shuraihu wanda gaba ɗaya ta kwashe halayyarsa, bata son magana sosai ga masifar gadara da mulki tun tana ƙarama, ko tafiya take haka zata rinƙa karairaya tare da haɗe fuska kamar yanda Me martaba ke yi, ba ƙaramin haushin yanda take yi su Bilkisu ke ji ba, dan su ko yaya suka yi abin baya yi musu kyau, lokaci-lokaci Mama na zuwa duba yaran nata haka Sarki Shuraihu da Hajiya kakarsu Afnan, wadda itama ta yarda da hukuncin da aka yanke, idan ka cire Mama da yaranta babu wanda be san cewa Sarki Shuraihu na da ƴaƴa maza ba, shekarun Afnan uku ne Fulani ta sake samun wani cikin, ai kuwa sun yi murna sosai banda Mama wadda sai dai ta nuna soyayya a zahiri, bayan wata tara Allah ya sauketa lafiya ta haifo ƴa mace, ranar suna aka sakawa yarinya suna Asma'u suna kiranta da Husna, lokacin da Afnan ta cika shekaru tara ne ta haddace alqur'an wanda a littafai ta san da dama, ko kaɗan bata wasa da addininta, duk da cewar tana zuwa school, gaba ɗaya makarantar da ke garin babu wanda ya kai kuɗin wadda aka saka Gimbiya, sosai Mama ke jin haushin yanda Sarki Shuraihu ke kula da Gimbiya, haka zaman gidan sarautar ya cigaba wanda Gimbiya da ƙanwarta Husna basa samun shan iska gaban Mama, wannan dalilin ne yasa Afnan fara tsanar su, duk da cewa Halima bata biyewa Mahaifiyarsu amma hakan be sa Afnan sonta ba, so da yawa Mama na ba Jakadiyar Fulani magani ta saka cikin abincin me martaba, sai dai ita Jakadiya bata sakawa Fulani take kaiwa, saboda ta san ba Alkhairi Mama ke shukawa ba, ba ƙaramin ilimi Afnan take da ba, wanda a school ɗinsu babu wanda be san Afnan Shuraihu Mulki ba, idan ta shiga school kowa bata hanya yake yi, saboda bata ɗaukar raini kuma bata ƙaunar talaka a rayuwarta, ita kawai ƴanu'wanta ta sani, ganin zaman lafiya na neman ƙauracewa masaurautar Senegal ne ya sa Kakarsu Afnan wadda su ke kira da Hajiya Babba, ta yanke hukuncin daga Bilkisu har Hauwa'u su fitar da mijin aure, saboda ita ke faɗa a ji, har Mahaifin nasu bata isa ta kafa doka ya taka ba, babu rin zagin da ba'a yi musu akan cewa sun kai shekarun aure ya kamata su yi amma kamar ƙara musu ake yi.

Hajiya Babba na da wani ɗanu'wanta, me suna Tukur wanda lokacin da iyayensu suka rasu shine ke kula da ita, duk da cewa ubansu ne ɗaya kowa da Mahaifiyarsa, amma haka Tukur ya ɗauki Hajiya Babba tamkar ciki ɗaya suka fito, yana da yara huɗu Sani, Jamilu, Abubakar da kuma Ahmad, wanda shine Sarkin Sudan, Mahaifinsu Tukur wanda su ke kira da Alhaji yana son zumunci sosai baya wasa da dangi, shiyasa ma a duk shekara haka zai tattara iyalansa su tafi ƙasar Senegel gidansu Sarki Shuraihu, sosai alaƙar su ke tafiya wanda Sarki Ahmad matarsa ɗaya me suna Hadiza, yana da yara huɗu Mubarak wanda shine na farko ana kiransa da Yarima Muby, yayi karatunsa a ƙasar larabawa inda ya karanci ɓangaren lafiya, larabci kuwa kamar daga bakinsa aka fara, babu abin da ke ƙara masa tsanar Afnan ganin yanda itama ta iya arabic kusan ma ta fishi iyawa, Yarima nada ƙanwa me suna Munirat ita ce ta biyu, sannan Ameer da Ameera ƴan biyu ne, yanzu haka suna matakin ƙarshe a jami'a, tsakanin Mubarak da Afnan kuwa duk lokacin da zasu zo ƙasar haka suke faɗa kamar ba ƴan'uwa ba, haka ma idan su Afnan ɗin suka je ƙasar Sudan, a kullum sai Mubarak yayi mata duka, musamman idan ya ga yanda take nuna Mulki da gadara, bata sakar masa fuska ko kaɗan, tun yana burgeta har ya fita ranta, saboda yanda yake takura mata baya barinta shaƙat, wannan rashin jituwar ne ya sa Alhaji da Hajiya yanke hukuncin haɗa aurensu, ba ƙaramin girgiza kowa maganar auren ta yi ba, tun daga lokacin zumunci ya fara baya-baya tsakanin Masarautun, kowa na ganin cewa yafi wani, Sarki shuraihu kuwa har gurin Hajiya ya tafi ya roƙeta a kan baya son auren, amma Hajiya ta ce be isa ba, tabbas idan Gimbiya ta ƙarasa makaranta sai an haɗa auren, haka Sarki Shuraihu ya haƙura ba dan yana so ba, ɓangaren Muby ma haka tun a ranar da aka yanke magana ya ce ba zai sake zuwa ƙasar ba, dan haka ya maida hankalinsa kan aikinsa dan ya gina babban asibiti a garin Sudan me sunan MUBARAK MULKI HOSPITAL, wanda ake taimakawa talakawa marassa ƙarfi, duk da cewa shima ba wani damunsa talaka yayi ba.

Hajiya Babba kuwa ta tasa su Bilkisu gaba a kan su fitar da waɗan da zasu aura, dan dole kowaccensu ta kawo nata zaɓin aka yi aure, babu abin da suka duba sai kuɗi, dan gaba ɗaya mazajen nasu masu masifar kuɗi ne shiyasa ma Mahaifiyarsu ta yarda, ba tare da saka wani binciken ba, da Sarki Shuraihu ya ce zai bincika sai ta ce masa ai ta saka kuma ta gane suna da halayyar ƙwarai, dan haka aka saka rana wata ɗaya lokaci na cikawa aka ɗaura aurensu a rana ɗaya, kuma a ranar suka tare.

Aurensu da shakera ɗaya ne aka ɗaura auren Mubarak Ahmad Mulki, da Afnan Shuraihu Mulki, ba ƙaramin ɓarin kuɗi aka yi ba kowacce masarautar na son ace tafi ɗaya, wannan taƙama da mulkin ne ya sa Sarki Shuraihu ƙin yarda a kai Afnan gidan mijinta, haka Sarki Ahmad ma ya ce babu wanda zai ce a kawo ta, Alhaji da Hajiya Babba kuwa abun ya ɗaure musu kai saboda ganin yanda suke ƙoƙarin kashe zumunci, Fulani babu irin magiyar da bata yi ba a kan a tafi da amarya amma Me martaba ya ce ba za a tafi da ita ba, har yau har gobe Afnan bata san cewa tana da ƴan'uwa maza ba, kuma bata taɓa kawo tunanin hakan ba, wannan shine taƙaitaccen labarin masarautar Sudan da kuma Senegal.




............
A washe garin ranar da Muby ya saki Afnan ne Gimbiya Fadila da Mahaifinta suka tafi ƙasar Sudan, da fari Sarki Ahmad ya so hana auren, ganin cewa suma ƴan Mulki ne kuma da dukiya ya sa shi amincewa, amma ya ce baza a saki Yarima ba har sai Alhaji Babba ya bada umarni.

A haka suka koma ba tare da Fadila ta samu ganin Muby ba, kwanansa uku a rufe ya rame yayi duhu kamar ba shi ba, duk aikin da bayi ke yi shima yana yi, wannan umarnin Alhaji ne.

Kullum cikin tunanin Gimbiya Fadila wadda yake matuƙar so, wannan shine karo na farko da ya taɓa faɗawa soyayya, duk da cewa Afnan ta fi ta kyau nesa ba kusa ba amma hakan be dame shi ba, kuma ya ƙudurta a ransa ba zai taɓa janye manufarsa ba.

Alhaji Babba kuwa a ranar ya shiga ƙasar Senegal domin tattaunawa shi da ƴar'uwar tasa, amma be samu ganin Sarki Shuraihu ba saboda fushin da yake yi.

A nan yake samun labarin saki ɗaya ne aka yi mata, sosai hankalin Alhaji ya ɗan kwanta sannan ya ce zata koma ɗakinta, tare da shaida musu cewar Yarima zai auri Gimbiya Fadila saboda ya nuna yana sonta, ya kamata ayi masa adalci wannan karon ya auri zaɓin ransa, tun da duka sauran zaɓa masa aka yi, Hajiya Babba ta yarda da shawarar amma ta ce sai Yarima ya zo ya bada haƙuri da kansa, sannan baza ta koma ba har sai an gama aurensa da Gimbiya Fadila, a haka aka aje maganar sannan Alhaji ya koma ƙasar Sudan.

Bayan tafiyarsu ne Hajiya ta saka a kira mata Gimbiya, dan taji daga bakinta.




*Muje zuwa fans ɗin gidan Mulki yanzu aja fara, yawan sharhi yawan typing ayi share saboda Allah*




*GIDAN MULKI*

*By*


*Asmeetar Hydar*







P.10




Tun da Hajiya Babba ta fara magana Afnan ta yi kamar bada ita take yi ba, ganin haka yasa Hajiya daka mata tsawa cikin ɓacin rai ta ce "Wai ba magana nake yi miki ba ne?"

Yamutsa fuska Afnan ta yi tana mai motsa lips ɗinta a hankali ta ce "No one should force me to return to his house, and if i am forced to go back, i will kill myself mark my words" Tana gama faɗin haka ta bar part ɗin cikin tafiyarta me jan hankali.

Sosai Hajiya Babba ta tausaya mata, saboda ta san cewa wannan sakin da aka yi mata na wulaƙanci ne, amma babu wata mafita face ta koma gidan mijinta.

Sarki Shuraihu kuwa wannan karon ya yi fushin da kowa a fadar tsoron tunkararsa yake yi, musamman maganar komawar Gimbiya, shiyasa ma Afnan ta ci gaba da harkokin gabanta kamar kowanne lokaci.


.........
A ɓangaren Muby kuwa yau satinsa ɗaya a rufe kuma yau aka fitar da shi daga ɓangaren bayi, zaune yake cikin shigar ƙananan kaya gashin fuskarsa duk ya ƙara yawa amma hakan be hana kyawun fuskar fitowa ba, idanuwansa kuwa saun ƙara wani haske amma ya rame sosai kamar wanda ya kwanta ciyo, Alhaji Babba da me martaba sai Mommy ne zaune a parlourn, cikin haɗe fuska Alhaji ya maida kallonsa kan Muby da ke zaune kansa a ƙasa ya ce "Mun yanke hukuncin aura maka Gimbiya Fadila tun da ita ce zaɓinka, amma idan har kana buƙatar aurenta sai ka mayarda matarka Gimbiya" Ɗago kansa yayi tare da sauke haɗaɗɗun idanunsa kan Alhaji, jin yanda zuciyarsa ke bugawa ga kuma tsanar Afnan da ta ƙara dira a zucuyarsa, ganin irin kallon da me martaba yayi masa ne yasa shi maida kansa ƙasa cikin girmamawa.

Alhaji kuwa cigaba yayi da faɗin "Dan haka ka mayar da ita a yanzu, idan har kana buƙatar aurenka, bayan ka maidata zaka tafi har ƙasarsu ka bata haƙuri kuma ku dawo tare".
Wani zufa ne ke karyo masa kamar wanda yayi tsere da kura, bakinsa na rawa ya furta na maida matata Afnan" Yana gama faɗin haka ya zube ƙasa a sume, ihu Mommy ta yi tare da nufarsa, amma Alhaji da me martaba kam ko kallon inda yake basu yi ba, ruwan da ke kan wani haɗaɗɗen ƙaramin table ne ta ɗauka tana yayyafa masa, ajiyar zuciya ya sauke da ƙarfi wanda yasa su Alhaji kallonsa cikin mamaki, ba tare da ya sake cewa uffan ba ya ƙara sumewa a karo na biyu, wannan karon ba Mommy ba hatta Alhaji Babba da me martaba hankalinsu ya tashi, nan take aka nufi Clinic ɗinda ke cikin masarautar da shi, tare da bashi agajin gaggawa, sosai ruɗu da damuwa suka haɗewa Mommy, a zuciyarta take faɗin idan har Afnan ce silar wannan rashin lafiyar na ɗanta, tabbas sai ta raba auren kuma ta koreta daga rayuwar ɗanta, lokaci ɗaya kuma ta ji tsanar yarinyar a ranta tare da jin mugun haushinta.

Muby be farka ba sai dare, Alhaji ne kawai a gefensa yana yi masa sannu, ɗaga kai Muby yayi alamun yawwa, sosai kansa ke sarawa har wani jiri yake gani, abubuwan da suka faru ne yake tariyowa kamar wanda aka tsikara ya tashi zaune daidai lokacin da me martaba ya shigo ɗakin, "Sannu Yarima ya jikin naka" Idanunsa ya lumshe a hankali ya furta "Alhamdulillah, ina Fadila?" Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Alhaji da me martaba jin abin da Muby ke faɗi, kafin Alhaji ya ɗaure fuska ya ce "Gobe in Allah ya kaimu zaka tafi ƙasar Senegal ka taho da matarka, duk da cewar Kakarta ta ce har sai anyi auren Fadila sannan zata tare, amma hakan ba zai hana ta zuwa ƙasar nan ba, idan yaso sai ta zauna a masaurata kafin komai ya kammala"

"Dan Allah ku bar yaro haka, wallahi idan har yarona ya mutu sanadiyar Gimbiya ba zan taɓa yafewa ba, tun da ya nuna baya sonta kuma aurensu ya mutu be dace a ce an saka shi dole ya mayar da ita ba" Cewar Mommy da shigowarta kenan fuskarta babu alamun wasa.

Da mamaki su duka su ke kallonta dan jin abin da take faɗa, kusa da Muby ta ƙaraso tare da kama hannunsa ta ce "Ka daina damuwa ka ji idan har baka sonta babu wanda zai dawo maka da ita" Cikin tsawa Me martaba ya ce "Fulani....., ke da kanki ki ke faɗin haka? sanin kanki ne bana son Mahaifina ya aje doka a gidannan wani ya taka" "Haka nima ba zan so a kashe min yaro ba, idan kuma hakane sai dai na koma gidammu dan ba zan zauna ba" Tana ƙarasa faɗar haka ta fice daga ɗakin, shuru dukkaninsu suka yi, shi kam Muby daɗi ne ya kama shi, saboda Mommy bata taɓa shiga maganarsa irin haka ba, ya tabbata cewa yanzu babu wanda zai sa ya dawo da Gimbiya, tana da aurensa a kai a halin yanzu ta je can ta rinƙa yawo yanda take so, ya faɗa a ransa yana cije lips a hankali.


A bazata ya tsinkayo muryar me martaba na faɗin "Kamar yanda na faɗa maka gobe zaka tafi gurin matarka, ka sani cewa ba sonka ne bama yi ba, kawai soyyarce haka Hajiya Babba ƙanwata ce kuma ina ji da ita, yanzu meye amfanin raba zumuncin da ka ke ƙoƙarin yi? dan Allah idan har ba so ku ke baƙinciki ya kashe ni ba, to ka je ƙasar Senegal

Please Login or Register in order to submit comment