Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya same mu"

Cikin dauriya Maimun ta sosa mazaunanta da ke ƙaiƙayi tana mai faɗin "Gaba ɗaya jiya na yi tilisss da giya, bansan lokacin da suka shigo ba, amma bata sami Alhaji ba ko?"

"Kowa ta samu a ciki har ni ma ta ganni"

Tun kafin Maimun ta ce wani abu suka fara jin warin ƙonewar abu, kamar wasa hayaƙi ya turnuƙe ɗakin, abin da Maimun bata saniba shine sigarin da take sha ne ya ya faɗa kan bed har yasa wuta ta kama, nan fa suka fara neman hanyar fita amma babu hali.

Dama duk mazan da ke aiki gidan sun koma gidan sarauta, Kuyangi ne kawai suma ƴan part ɗin Afnan ne, cikin ƙaramin lokaci gaba ɗaya gidan ya kama da wuta, da ƙyar su Maimun suka ceci rayuwarsu, masu aikin mata kuwa tun wutar bata iso part ɗin Afnan ba suka bar gidan da gudu dan sun cewa baza su iya kashewa ba, mutanen unguwa kuwa sai ihu ake da neman ceto, amma kafin a kashe wutar gaba ɗaya komi na gidan ya ƙone babu abin da ya yi saura, idanun Maimun sun zazzaro dan tsananin tsoro Hajara ce ta ce "Yau mun shiga uku me kuma ya kawo wannan wutar?"

Maimun da ke tattaro numfashinta da ƙyar ne ta ce "Ina zan sani kuwa ai tare mike da ke a ciki"

Amsar da Maimun ta bawa Hajara ya ɓata mata ra sosai, cikin fushi ta ce "Mtssss! ƙarya ki ke yi wallahi, ke ce silar wutar da ta kunnu, ko kin mance sigari na hannunki lokacin da na shigo"

Waro ido Maimun ta yi a tsorace "Lallai kuwa hakane, amma ya aka yi ta bar hannuna"

"Ina zan sani bayan haukarki ce ta sa shi faɗuwa daga hannunki"

Duka Maimun ta kaiwa Hajara a zafafe, ai kuwa suka fara dukan juna kamar maƙiya, sosai faɗa ya kaure tsakaninsu, mutanen da ke gefe sun gaji raba su amma ina sai ma abin da ya ƙaru, Hajara ta ce "Shegiya jaka wadda bata san darajar aure ba"

Ran Maimun ya gama ɓaci ta ƙara chakumo Hajara tana faɗin "Ke kuma karuwa me bin maza ko?"

"Ai babu karuwa kamar ki, ke an faɗa miki ina son auren da ki ka yi ne? tun lokacin da na samu labarin aurenki da Yarima nake neman hanyar da zan raba ku, kuma duk ƙawancen da nake nuna miki be kai zuciyata ba, na tabbata cewar Yarima zai samu labarin mugun halinki ya kora ki waje"

Wani wawan mari Maimun ta ɗauke Hajara da shi "Ashe dama ke makira ce? duk rufa miki asirin da nayi na shayar da ke na suturtaki"

Da ƙarfi Hajara ta ƙwace jikinta tana matsawa gefe ta ce "Ko maganin da Boka ya bamu a kan ki mallake Yarima ni ce na ɗauke shi, na canza miki da ƙasa a matsayin magani, ni ce na haɗa ki da Alhaji dan ya shawo kanki, sai kuma aka yi sa'a ya sameki a ƴar'iskarki ga son kuɗin tsiya kamar mayya, kina ganin kuɗi ki ka manne masa, ni ce na bashi wani magani da zai saka a gabansa a duk lokacin da zai kusance ki, saboda ki ji babu namijin da ki ke son ya kusanceki kamar shi" Bushewa da dariya Hajara ta yi kafin ta cigaba da faɗin "Idan ba ki mance ba, a lokacin kin nemi na samo miki maganin hips da mazaunai dan ki shawo kan Yarima ya fara sonki, to maganin da na kawo miki ba me kyau ba ne, magani ne wanda zai lalata miki mazaunai, ina mai tabbatar miki cewa nan gaba baza ki iya zama ba saboda yanda mazaunanki zasu lalace kamar ruwan da aka zuba a leda, kina tsammanin ni masoyiyarki ce? to banada wata maƙiyiya kamar ki, ke ɗinnan Maimun na tsaneki bana son ganin kina numfashi, tun kafin Alhaji ya fara kusantarki ni ce ta farko da ya fara kwana da ita, kuma ya laƙa min cutar HIV shiyasa kema na kawo miki shi dan ki samu rabonki....."

Wata irin kururwa Maimun ta yi tana mai shaƙo Hajara, amma sai ta yi saurin dafe mazaunanta dan jin wani irin ƙaiƙayi da ya shigeta, nan fa tafara sosawa kamar wata mahaukaciya, duk mutanen da ke gurin suka watse cike da mamakin hali irin na Maimun da ƙawarta, Hajara ma barin gurin ta yi tana mai cigaba da dariya.

Kamar wata zararra haka Maimun ta nufi hanyar gida tana zuba ihu.


ƘASAR SENEGAL
...............................
Husna kuwa da ke kwance har ta gama sadaƙarwa, kamar daga sama suka ji kukan motocin sojoji, ai da gudun tsiya matasan suka saki bindigoginsu tare da barin gurin, motocine na sojoji kusan guda goma, hamdala su Fulani suka yi suna mai godewa Allah, da sauri Halima ta fito daga motar ta nufi gurin da suke, cikin tausayawa ta ce "Hajiya ina fatar basu yi muku komi ba ko?"

Ɗaga kai Hajiya ta yi cikin jin daɗi ta ce "Allah ya yi miki albarka ƴarnan"

Da Ameen suka amsa, kafin Halima ta ɗaga Husna, sojojin kuwa tattara bindigogin suka yi, Halima ce ta kalli Fulani tana faɗin "Idan babu damuwa me zai hana ku tafi ƙasar Chad kafin komi ya lafa, duk abin da ke faruwa na sani, ɗazu bayan wucewarku na zo gidan, ina shiga ɗakin Mama na ji tana waya da ƴan daba, shiyasa na yi saurin kiran sojoji kuma Allah ya sa babu abin da ya faru, bayan haka ga waɗannan takaddun, ki aje gurinku takaddune na duk wata kadara da Baffa ya mallaka na san cewa Mama zata sa ya saka sunanta shiyasa na sace su"


Murmushi ta yi tana mai cewa "Zan koma gida yanzu dan be san na fito ba, duk waɗannan sojojin zasu yi muku rakiya har airport, na riga da na tanada muku jirgin masarauta, Aunty Muslimat Allah ya biya ku da gidan Aljannah"

Cikin farinciki kowa ya amsa da Ameen, kafin su Fulani suka shiga motar sojojin, su Easha kuwa tasu motar suka shiga tare da barin gurin cike da tausayinsu Hajiya.

Hanyar airport aka nufa da su, cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Chad, ba tare da Mama ta samu labarin abin da ke faruwa ba.



............................
A ɓangarensu Muby kuwa sati ɗaya suka kwashe a haka, shi kansa ya rame ba kamar lokacin baya ba, sai kuma hasken da fatarsa ta ƙara, dan har ya fara sabawa da ƙauyen yau tun safe Malan ya same shi a ɗakinsa zaune kan sallaya yana karanta alqur'an, sai da Muby ya kai aya sannan ya aje yana mai kallon Malan cikin murmushi.

Shima murmushin ya yi kafin ya ce "Masha Allah dama kai nake jira ko zamu shiga gurin matar taka" Tun kafin Malan ya rufe baki Muby ya miƙe yana mai cewa "Okay mu tafi"

Gaba Malan ya yi Muby bin bayansa har bakin ƙofar ɗakin, sallamar Mandula ce ta tsayar da su, hannunta ɗauke da kwanonin abinci, sai da ta gaidasu kafin ta aje abincin tana mai tambayar me jiki, Malan ne ya amsa da "Jiki Alhamdulillah" Sannan ya karanto wasu addu'oi kafin ya shiga da sallama, shima Muby bisimillah a bakinsa ya shiga.

Da mugun razana ya ja baya ganin yanda Afnan ta koma, duk jikinta blue ne har idanuwanta bakinta na fitar da wata irin kunfa me ɗauke da wasu layu, Malan ne ya matsa kusa da ita tare da cire layun daga bakinta, "Ka fito da ita tsakar gida, ke kuma Mandula ki shimfiɗa mama shimfiɗa"

Bada ɓata lokaci ba suka fitar da ita wajen gida, duk ƙurajen da ke jikinta sun ɓace babu alamun su ko kaɗan, tamkar bata taɓa yinsu ba, wasu ruwan addu'a ya miƙa masa yana faɗin "Ka bata ruwannan" A hankali Muby ya ɗauka yana mai tallofa kan Afnan ya ɗora saman cinyarsa, sai da ya yi bisimlillah sannan ya buɗe bakinta tare da zuba mata ruwan, ba laifi ruwan ya shiga da ɗan yawa, tun kafin ya sauke hannu Afnan ta ja doguwar ajiyar zuciya wadda ta sa Muby tsorata, idauwanta kuwa suka ƙyafta so ɗaya sai kuma ta sauke numfashi tana mai kallon duk waɗan da ke gurin.




*Sai haƙuri yau typing ɗin ba yawa, kuma na yi busy sosai amma duk da haka ga wannan ku sarara*


*Daga Asmeey ta Hydar Sayyada ta Sayyadi*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*







P. 22


Ai Muby bai san lokacin da ya ƙanƙameta a jikinsa ba har ya mance su Malan na gurin, Afnan kam sai yarfe ido take tana kallonsa, Malan ne ya ce "Alhamdulillah lallai sauƙi na Allah ne, kuma muna sa ran nasara"

Wani ruwan addu'ar ya miƙa masa kafin ya cigaba da faɗin "Wannan ruwan shafa mata za ka rinƙa yi a duk lokacin da zata kwanta bacci, zai kai tsawon sati ɗaya insha Allah muna sa ran zata dawo kamar yanda take"

Godiya Muby ya yi masa cikin tsananin farinciki ya ce "Za'a iya yi mata wanka yanzu kuwa?"

"Eh sosai ka samu ka yi mata wankan ko jikinta zai yi haske"

Mandula kuwa sai murmushi take ganin Uwar ɗakinta ta fara samun sauƙi.

Ruwan wanka Muby ya hana kafin ya shiga da Afnan bayin, tun da ya fara cire mata kayan jikinta ta zuba masa ido daga ya kalleta zata kawar da kai gefe, har yanzu bata iya tashi amma duk abin da zaka yi mata tana ji kuma tana kallo, amma magana bata fita a bakinta.

Shi kuwa Muby daga ta kawar da kai sai ya saki murmushi yana lumshe haɗaɗɗun idanunsa, a haka har ya gama yi mata wanka.

Duk wannan blue ɗin da ke jikinta ya fita tassss, fatar jikinta ta koma sumul tamkar babu abin da ya taɓa samunta, sai dai fa har yanzu bata iya motsa jikin nata, gashin kanta kuwa sosai ya wanke mata shi sannan ya ɗaura ɗan ƙaramin tawul a kai, brush ɗin da ke gefe ya ɗauka ya rasa ta yanda zai fara yi mata brush ɗin, a haka dai ya samu damar buɗe mata baki ya wanke shi tasssss, haƙoranta masu kyau da haske suka bayya, kan wata kujera da ke cikin bayin ya zaunar da ita tare da jinginawa, shima kayan jikin nasa ya fara cirewa dan ya yi wanka, Afnan na ganin haka ta gimtse idanuwanta, shi ko Muby mamaki ma take basa ganin yanda ta wani shan jinin jikinta, wankansa ya yi cikin natsuwa kafin ya ɗaukota suka koma ɗaki, sai da ya gama shiryawa cikin jallabiya ruwan toka itama ya shiryata cikin wata ƙaramar riga ruwan madara me kyau da laushi, daidai cinyarta rigar ta tsaya a gaban rigar akwai zanen flowers kalar sararin samaniya, muryar Bosho ya fara ji daga harabar gida yana zubawa Malan ashar, da sauri ya kwantar da Afnan kan katifar ya fito waje, Bosho na ganinsa ya galla masa harara "Yooo kai kuma lafiya da fitowa? an zo gulma kenan to Ubana ne babu wanda ya isa ya hanani yi masa abin da na ga dama" Muby da ransa ya gama ɓaci ne ya ce "Allah ya shiryeka amma ka sani cewa kaima za ka haifa, idan har ƴaƴanka suka yi maka haka za ka ji daɗi?"

"Ƴaƴana ai ba naka ba ne, idan sun yi min ba damuwarka ba ce"

Malan ne ya ce "Kaga Yarima dan Allah ka barshi kawai, koma daga ciki marar lafiya na buƙatar ka a kusa da ita"

Tun da Bosho ya ji an ce Yarima jikinsa ya fara rawa idanuwansa suka zazzaro, be taɓa sanin cewa Muby ɗan sarki ba ne sai yau, faɗuwa ya yi ƙasa yana birgima kamar ƙaramin yaro "Na tuba ka yafe ni, wallahi ba zan ƙara ko kallonsa ba idan ka yarda"

Dariya ce ta kusa ƙwacewa Muby amma sai ya cije yana mai cewa "Shikenan amma wannan ya zama na ƙarshe, kuma ka ba Mahaifinka haƙuri da shaida masa baza ka ƙara shan komi ba, and baza ka ƙara ko hararsa ba balle ɗaga masa murya"

"Na yi alƙawari daga yau na daina shan komi, Baba ka yafe min duk abin da nayi maka"

Cewar Bosho yana ƙaƙalo hawaye, Malan ne ya ce "Na yafe maka amma sai ka canza halinka, kuma sai ka fara sallah"

"Wallahi zan fara daga yau kuma jam'i ba zai wuce ni ba"

Muby ne ya ce "Ka daina halayyarka dan Allah, kuma ka fara sallah dan Allah ba dan tsoron abin da wani zai yi maka ba".

Girgiza kai Bosho ya yi kamar ƙadangare, sosai Malan ya ji daɗin yansa Bosho ya yi nadama kuma yana fatar Allah ya sa ya shiryu.


Sai da suka yi sati ɗaya cur yana shafa mata ruwan addu'ar da Malan ya bashi, a kullum sai Mandula ta kawo mata kunun gyaɗa me ɗan karen daɗi, Afnan kuwa ta lamushe dan jiki ya yi sauƙi, amma har yanzu bata iya tashi kuma bata magana, wannan abin na ɗagawa Muby hakali sai dai kawai ya cigaba da addu'a dan babu yanda ya iya, Bosho kuwa sallar jam'i bata wuce shi ƴar sana'a ya samu a ƙauyen yana taya wani mutum tsaron shagon kayansa, shiyasa ɗan kuɗin kashewa baya gagararsa, daga ya samu zai sayo ma su Malan abubuwan buƙata kama daga sabulu da kayan abinci, shaye-shaye kuwa ya daina dan ko sigari baya sha.

Sosai mutanen ƙauyen ke yabonsa da kuma jin daɗin yanda yake kula da Mahaifinsa, ga kyautatawa duk wanda be fi ƙarfinsa ba.


Yau sati uku da kwana huɗu kenan da zuwansu Muby ƙauyennan, kuma yau Muby ya samu magana da su Mommy ta waya dan network ya dawo, har da me martaba sun gaisa, daga ƙarshe ma video call ya kira suka rinƙa fira, sannan ya nuna musu Afnan da ke kwance tana kallonsu ba halin magana, addu'a su Mommy suka ƙara yi mata, kafin ta faɗawa Muby cewar Munirat ta zo har ta koma, sannan ta kuma ƙara sanar da shi zancen wutar da ta kama a gidansa, da Muby ya tambayi Mommy batun Maimun sai ta shaida masa cewar ta koma can gidansu, jinjina kai ya yi cikin mamaki kafin ya ce "Amma meyesa bata zo nan gida ba? ai ya kamata ta sauka a gida ba wai gidansu ba"

Mommy ce ta ce "Aa ka barta kawai idan ka dawo sai ka tafi ku dawo tare"

"Okay ba damuwa ku gaida su Ameer"

Da toh Mommy ta amsa kafin suka yi sallama, ba zato ba tsammani Muby ya ji Afnan ta ce "Hmmmmm..." Da sauri ya kalleta sai kuma yaga tana kallon wani gefen, matsawa kusa da ita ya yi tare da kama hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Allah ya ba ki lafiya Babyna, na ƙagu ki warke ko zan nuna miki tsananin ƙaunar da nake miki, ke ɗin rayuwata ce tabbas babu amfanin rayuwata idan babu ke" Numfashi ya sauke yana mai shafa gefen fuskarta, "Zamu tafi sallah idan na dawo zan ƙarasa faɗa miki yanda nake ƙaunarki".

Kiss ya manna mata a lips tare da ficewa daga ɗakin.

Yana fita Afnan ta miƙe zaune tana toshe dariyarta, a hankali ta leƙa tsakar gidan amma babu kowa, tsalle ta daka cikin murna ta ce "Hmmm ai kuwa bazan warke yanzu ba har sai kalamanka sun ƙare, sauƙin ka ɗaya ka kula da ni lokacin da nake neman me kula da ni"

Fitowa ta yi tsakar gidan ta ɗauro alwala, cikin natsuwa ta zura hijab ɗinta tare da kabbarta sallah, lokacin da ta gama ta jima tana addu'oi kafin ta yi saurin naɗe sallayar da hijab tana mai koma ta kwanta.

Shigowar su Muby kenan suka zauna tsakar gida, duk Malan ya lura da yanda Muby ya kasa natsuwa, murmushi ya yi kafin ya ce masa "Ka shiga ka duba marar lafiya mana" Ai tun kafin Malan ya rufe baki Muby ya miƙe yana ɗan sosa kai, "Tom bari na dubata"

Malan dai kallonsa yake har ya shige ɗakin, a kwance ya sameta kamar yanda ya barta, kunun gyaɗa ya zuba cikin Cup tare da zama gefenta, sai da ya ƙare mata kallo kafin ya tallafota kan ƙirjinsa, Afnan kam ƙara lafewa ta yi har ya fara bata kunun, sai wani yamutsa fuska take shi ko yana aikin tarairaya har ta sha ba laifi.

Aje Cup ɗin ya yi a ƙasa, yana kallon kunun da ya zuba gefen bakinta, be tsaya wata-wata ba ya kai bakinsa kan nata ya lashe kunun, zaro ido Afnan ta yi tana ƙare masa kallo, ganin yanda ta yi masa da ido ne ya bashi dariya ai kuwa ya haɗe bakinsu guri ɗaya, sosai yake lashe lips ɗinta kamar wanda ya samu sweet, Afnan kam kasa motsi ta yi dan lamarin ya fi ƙarfinta, ya daɗe yana lashe mata baki kafin ya rungumota a jikinsa tare da sauke numfashi, itama numfashin ta rinƙa saukewa dan har zuciyarta bata so ya daina kissing ɗinta ba,


Yana ganin yanda ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya matsar da bakinsa gefen kunneta ya ce "Ko na ƙara yin wani ne?" Wani irin zirrrrrrrr, Afnan ta ji duk tsikar jikinta ya tashi, kyawawan idanunta ta buɗe tare da saukewa kan haɗaɗɗar fuskarsa, ɗage mata gira ɗaya ya yi yana dariya ƙasa-ƙasa.


ƘASAR CHAD
.........................
A ɓangarensu Fulani kuwa yau satinsu biyu a Chad, sosai suka samu kwanciyar hankali amma gaba ɗayansu suna tunanin wanne hali sarki Shuraihu ke ciki, su Alhassan kuwa an dage da addu'oi gurin wani babban Malami ko za'a dace, ba laifi sun daina jin zafin da idanuwansu ke yi amma har yanzu basa iya ganin komi, sai jiya suke samun labarin abin da ke faruwa da Gimbiya gurin Ameer, dan ya gaji kiran layin Husna baya samu sai ya kira Fulani, hankalinsu ya mugun tashi jin cewar Afnan ba lafiya, amma da suka ji cewar Muby na tare da ita ne abun ya zo musu da sauƙi, a kullum Fulani sai dai ta shiga ɗaki ta rinƙa rusar kuka, dan ko ta kira layin mijin nata baya ɗagawa daga ƙarshe ma ya daina shiga.


Yau kam ba laifi dan su Alhassan sun fara samun sauƙi sosai har za su iya ganin mutum kaɗan-kaɗan, zaune suke a parlourn ana fira cikin nishaɗi wayar Husna ta ɗauki ƙara, Fulani da ke gefenta ne ta duba wayar ganin sunan Beey ne ya sa Fulani ta san cewa Ameer ne, miƙa ma Husna ta yi tana faɗin "Ga Ameer na kira"

Cike da kunya ta tashi tana ƙoƙarin barin gurin, da sauri wata Kuyanga ta riƙeta suna mai hawa sama, har ɗakin Hajjo ta kaita kafin ta fice daga ɗakin, Husna da ke waya da Ameer ne ta ce "Beey wai yaushe su Yarima za su dawo ne?"

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke kafin ya ce "Ni kaina bansan yaushe za ku dawo ba, amma sun yi waya da su Mommy ina ganin sun kusa dawowa"

"Allah ya bata lafiya ya kuma dawo da su lafiya"

"Ameen matata" Ameer ya faɗa.

Kamar Ameer a gabanta ya yi maganar ta wani rufe ido da tafukan hannunta, jin ta yi shuru ne yasa Ameer cewa "Kunya ki ke ji ne? amma idan Yaya Ashwan ne baza ki ji kunyarsa ba"

"Yaya Ashwan kuma, meye haɗina da shi?"

"Kina nufin ba soyayya ku ke yi ba?"

Mamaki ne ya kama Husna har ta kasa cewa komi, "Kina ji ina magana kin shareni, ki amsa min ba soyayya ku ke yi ba?"

"Haba Beey yanzu kuma zargina ka ke? sanin kanka ne bana da wani wanda nake so sama da kai, ni babu abin da ke tsakanina da Yaya Ashwan, asalima maganar soyayya bata taɓa shiga tsakanina da shi ba sai mutunci kawai"

"Shikenan na yarda amma ki kiyaye, bana son na rasaki wallahi"

"Hmm Beey kenan, dama kishi ke ɗawainiya da kai"

"Eh naji ɗin ai soyayyarki ce ta sanya"

Cewar Ameer yana dariya, sosai suka yi fira kafin daga ƙarshe suka yi sallama.


ƘASAR SENEGAL
..............................
Mama kuwa tun ranar da ta saka ƴan daba aiki har yau babu labari, layinsu ma baya shiga duk a tunaninta sun kashe su Fulani, so uku tana turawa a bincika idan suna gidansu Easha ko Muslimat amma bincike na nuna cewar basa gidan, kullum sai ta tasa Me martaba a gaba kan maganar takaddun amma magana ɗaya yake faɗa mata cewa be gani ba, tsawon lokacin da ya ɗauka ya rame sosai ga tunani kullum, Mama da ƴaƴanta kuwa sun mallake gida babu wanda ke samun sauƙi ko nan da nan, duk masu aikin gidan sun dawo tamkar bayi.

Yau Me martaba ya tashi da tsananin ciyon da ake ganin kamar ba zai rayu ba, tun safe yake aman wani baƙin ruwa, sosai hankalin Halima ya tashi dan ita ce ke kula da shi, tun da su Fulani suka yi tafiya bata sanarwa kowa abin da ake ciki ba, kuka take sosai tausayin Baffan nata ne kwance a zuciyarta, a hankali ta ce "Baffa Allah ya ba ka lafiya"

Cikin dauriya da ƙarfin hali ya sakar mata murmushi wanda ya fi kuka ciyo "Ameen na gode sosai amma ciyon da nake ba na tashi ba ne, ina matuƙar buƙatar ganin su Hajiya dan Allah a kira min su kafin na bar duniya" Saurin rufe masa baki Halima ta yi "Baffa baza ka mutu yanzu ba insha Allah, amma zancen su Hajiya ai ka kore su a gidan yanzu haka ba wanda ya san inda suke"

Tarin da ya fara ne ya sa shi kasa magana, sosai yake tari kafin ya samu tarin ya lafa "Na san cewa na aikata babban kuskure, amma ba yin kaina ba ne"

"Baffa na san cewa ba yin kanka ba ne, laifin Mama ne duk ita ce silar tashin hankalin da ke faruwa a gidannan, yanzu masu aiki ma so biyu kawai ake basu abinci, Bayi kuwa so ɗaya, Allah duk sun rame"

"Too munafukar banza me baƙin hali, wadda bata yo gadona ba, tashi ki fita daga nan tun kafin na makeki" Cikin sanyin jiki Halima ta fita tana mai rufo ƙofa.

Mama kuwa gefen be ɗin ta zauna sai wani yamutsa fuska take "Hmmm ai tun da ka nuna min taurin kai game da dukiyarka wallahi ni ce zan zama ajalinka, wannan kaɗan kenan daga cikin makircina, na ji ɗazu kana maganar su Fulani ko?" Bushewa da dariya ta yi kafin ta ce "Na aikasu lahira tun ranar da ka koresu na saka a kashe min su, saboda na tsane su kaima lokaci nake jira da za ka je inda suka tafi"

Tashin hankalin Me martaba ya ƙaru gabansa sai faɗuwa yake, hannu ya kai da ƙyar ya shaƙeta da iya ƙarfinsa, "Ƙarya ki ke Allah ya fi ki, idan har wani abin ya sami family na sai na hukuntaki" Duk idanuwan Mama sun zazzaro sai ƙoƙarin ƙwacewa take amma ta kasa, jifa da ita ya yi gefe ya koma ya kwanta, Mama na ganin an saketa ta runtuma da gudu waje tana ihu, gaba ɗaya masa kula da part ɗin Me martaba ne suka taru ana tambayar me ya faru, sai da ta daidaita natsuwarta kafin ta ce "Dan Ubanku yau duk wanda ya ba Sarki abinci sai ransa ya ɓace, bana buƙatar ganin wanda ya shiga ɗakinsa"

Cikin biyayya suka amsa da toh, wasu daga cikinsu na jin tausayin abubuwan da takewa mijin nata, Mama kuwa barin gurin ta yi tana zuba surutai.

Sarki Shuraihu da ke kwance ne hawayen takaici ya zubo kan kuncinsa, yana mamakin yanda aka yi duk waɗannan abubuwan suka faru, da ƙyar ya iya tashi ya ɗauki wayarsa da ke gefe, wata number ya danna yana mai dafe kansa, bugu biyu aka ɗaya bayan sun gama gaisawa Me martaba ya ce "Ina son ka bincika min duk inda su Hajiya suke na ba ka nan da zuwa gobe" Ba tare da ya tsaya jin komi ba ya yanke wayar, yana mai komawa ya kwanta cikin fargabar abin da Mama ta faɗa masa, fatansa dai kar Allah ya sa zancenta gaskiya ne.

.........................
Su Muby kuwa haka suka kasance har wata ɗaya ciffff, a lokacin Malan Abdulsallam ya tsorata da ganin har

Please Login or Register in order to submit comment