Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

umarni, be jima ba su ka shigo tare da wasu mata su goma, kowaccensu sanye cikin kaya ruwan toka, har ƙasa su ka rusuna tare da gaisheta, ko kallon inda su ke bata yi ba ta ɗaga musu hannu, alamun su miƙe, matashin ta duba wanda ke jiran abin da zata ce, "Zaka iya tafiya, ka yi ma driver magana ya sauke ka".

Bata jira abin da zai ce ba ta kalli matan da ke gurin ta yi musu alama da su biyo ta, da sauri su ka bi bayanta kamar ana turasu, ɗan tsayawa ta yi da tafiyar tare da juyowa a ƙufule ta ce "Meye haka? ku ja baya please bana son ina tafiya ana shige min, jikinku tsami yake yi, idan na nuna ma kowa aikinsa ku tabbata kun yi wanka"

Kallonta su ke cikin mamakin abin da ta ce, dan sun san cewa dai ba bu wadda bata yi wanka ba a cikinsu ba.



Bayan ta gama nunawa kowa nasa aikin ne ta nufi wani ɗaki wanda ya gaji da haɗuwa, manya-manyan bed ne guda biyu a ciki sai kujera me zaman mutum uku, ta can ɓangaren kuwa wadrop ne me girma ya mamaye babban ɗakin, gefensa akwai gurin saka takalma, a gafe ɗaya kuma mirrow ne ɗauke da kayan rayuwa kamar shago, kan mamaken bed ɗin ta zauna tare da kunna wayarta da ɗazun ta kashe, sim ɗinta ta zube kan bed sannan ta saka wasu, murmushin gefen baki ta yi me kama da wata manufar, cikin takun ta me jan hankali ta shige toilet ɗin da ke ɗakin wanda ya gama tsaruwa bakinta ɗauke da addu'a, ta jima a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul, ɗaya a hannunta tana tsane gashin kanta da ya kwanta ta baya, ƙarar da wayarya ya yi ne yasa ta matsawa gurin ta ɗaga, shuru ta yi alamun daga can ɓangaren magana ake, kusan mintuna biyu ana magana, kafin ta ce "Good hakan ya yi ina buƙatar a kawo mun ita a nan gidan, ba tare da wani ya ganku ba"

Kashe wayar ta yi tana mai ƙarasawa gurin mirrow ta zauna, mintuna ashirin ta gama shirinta cikin wasu baƙaƙen kaya, wando da riga, sai wani takalma sawu ciki da black glass, ɗan ƙaramin mayafi ta yafa a fuska babu abin da ka ke gani face idanunta, amma daga gashin kanta har ƙasan fuskarta a rufe su ke da mayafi.


Sannu a hankali ta sauko down steps ƙamshin turarenta na bazuwa a gaba ɗaya inda ta ratsa har ta fito harabar gidan, tun da ta fara tafiya mutanen da ke tsaronta su ka duƙar da kai ƙasa ba tare da sun kalleta ba har ta nufi wani ɗan ƙaramin guri kamar ɗaki amma ba ɗaki ba, saboda babu rufi a saman ɗakin.


Tana shiga wasu maza guda biyu su ka rusuna cikin girmamawa, hannu ta ɗaga musu tana kallon matashiyar da ke zaune a kujera an ɗaɗɗaureta da wata igiya me kwauri, idanunta ɗaure da baƙin yadi.

Kujerar da ke gefe Afnan ta zauna fuska babu walwala ta ce "Za ku iya kwanceta" Da sauri ɗaya daga cikinsu ya kwanceta, sannan su ka bar ɗakin.

Maimun da tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta ne ta kalli Afnan jiki na rawa ta ce "Baiwar Allah me nayi miki? kika sa a kamani, idan har kuɗi ki ke buƙata ko nawa ne zan sa Mahaifina ya baki amma dan Allah kar ki kasheni" Tsawa Afnan ta daka mata wanda yasa Maimun tsurewa guri ɗaya tana mai share hawaye, mahayafin da ke fuskarta ta fara cirewa tare da glass ɗin, cikin gadara da nuna isa ta saki wani smile tana mai cewa "Kin yi mamaki ko? wannan kaɗan kenan daga cikin aiki na" Maimun da mamaki ya gama rufeta ta ce "Gimbiya...., bayan Munirat ta ce mun a yau za ku koma"

"Ba surutu nake so ba, dan haka ki kama bakinki" Afnan ta faɗa a masifance, shuru Maimun ta yi tana jiran abin da zai biyo baya.

Tafa hannu Afnan ta yi a karo na farko, wata kunyanga ta shigo ɗauke da ruwa a cikin wani farin roba, ɗaya robar kuma gishiri ne fari sol.

A jiye kayan kuyangar ta yi tare da ficewa.

Bakin Maimun na rawa ta ce "Me za ki yi da wannan.....?"

"Idan har ki ka sake magana sai dai Mahaifinki ya haifi wata amma ba ke ba" Cewar Afnan tana miƙewa tsaye, wani murgugujen ƙato ne ya shigo ɗakin, fuskarsa tamke gwanin tsoro, kana ganinsa ka san ba bu imani a tattare da shi, hannunsa ɗauke da wata zabgegiyar bulala ta sha maiƙo sai sheƙi take, ihu Maimun ta rafka ganin abin da ke shirin faruwa, sosai take kuka tana ba Afnan haƙuri amma ko kallonta bata yi ba ta fice daga ɗakin cikin taƙama.

Wannan murgujejen ƙaton ko be yi wata-wata ba ya fara dukan Maimun ta ko'ina, duk inda ya daka sai ya gurje nan take kuma jini zai fito, sai da ya yi mata shegen duka har bata wani numfashi, tun tana ihu har bakinta ya daina furta komi, cikin rashin imani ya kwara mata ruwan sanyin da ke cikin roba tare da watsa gishiri a kai, wata razananniyar ƙara Maimun ta ƙwala tana mai zubewa ƙasa a sume.



.................
Tun da Sarki Ahmad ya sanarwa Muby ɓacewar Afnan zuciyarsa ta yi fari fat, gaba ɗaya damuwarsa ta gushe, a ransa kuwa yana fatar ta tabbata a hannun waɗan da su ka sace ta har ƙarshen rayuwarta.

Kallonsa ya mayar kan Mahaifin nasa cikin gimamawa ya ce "Abbu dama akwai maganar da nake son muyi amma bansan yanda Alhaji zai ɗauki zancen ba" Kallonsa me martaba ya yi kafin ya ce "Ina fatar ba maganar Gimbiya zaka mun ba ko? dan naga alamar baka da wani sauran aji a gurinta" Sosai maganar ta yiwa Muby ɗaci amma sai ya ƙara sunkuyar da kai cikin girmamawa ya ce "Allah ya ja zamaninka ba maganar ta ba ce"

"Okay ina saurarenka" Me martaba ya faɗa yana maida hankalinsa kan ɗan nasa, tun kafin Muby ya ce wani abun suka ji sallamar Mommy, tana sanye cikin wata abaya me aikin duwatsu a gaban rigar akwai tambarin sarauta, sosai take zuba ƙamshi abin ka da farar fata sai ta haske gurin, a bayanta wata kunyanga ce ɗauke da farantin tufa, har ƙasa kuyangar ta durƙusa ta kwashi gaisuwa kafin ta fice daga ɗakin, "Mommy barka da wannan lokacin" Harara ta watsa masa cike da ɓacin rai ta zauna gami da faɗin "Ka kyauta Yarima, yau ka tabbatar min cewa ka isa da kanka, yanzu a ce matarka ta ɓata amma babu wani abin da ka tsinana, har ka samu damar da zaka yi fira" Ta ƙarashe maganar tana kallon me martaba, duk da ta san shima ba wani abun zai yi a kai ba.

"Mommy a mun afwa dan Allah amma ba zan iya zuwa nemanta ba" Muby ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa, da sauri ta ce "Koma ka zauna bana son shashashanci, ko na gama maganar da nake yi ne?" Komawa ya yi ya zauna yana lumshe ido, dan ransa ya fara ɓaci, gyaran murya me martaba ya yi kafin ya ce "Ba bu inda zai tafi, menene haɗinsa da ita, bayan kinga rashin mutuncin da iyayenta su ka yi mana, abinci ma babu wanda ya ci ko ɗaya, daga su har ƴaƴan nasu, gara ma Fulani ta ci wani abun amma Husna ma da ita ce ƙarama a cikinsu sai da ta nuna mana gadara, balle uwar gayya Gimbiya ina lura da ita ko gefen abincin bata kalla ba"


"Amma me martaba hakan baya nufin ya zuba ido, ba tare da ya binciko inda take ba"

"Kinga dan Allah ki bar yaro ya huta, Yarima tashi ka tafi sai na nemeka" Me martaba ya faɗa yana kallon Muby da kansa ke ƙasa tun lokacin da Mommy ta fara magana.

Ficewa ya yi cikin taku irin na cikakkun maza masu ji da mulki uwa uba kyau da ƙwarjini.



A parlourn ya sami Ashwan zaune da alama akwai abin da ke damunsa, cike da taƙama Muby ya zauna ba tare da ya ce ma Ashwan uffan ba, shi ko Ashwan be tsaya biyewa mulkin nasa ba ya kallesa cikin damuwa ya ce "Yarima ka ji abin da ke faruwa kuwa?"

Shuru Muby ya yi masa yana latsa waya kamar bada shi yake ba, "Wannan halin naka baza ka canza ba, magana nake yi maka amma ka share ni" Sai da ya ƙara ɗaukar wasu mintuna uku kafin ya lumshe kyawawan idanunsa masu masifar haske kafin ya ce "Bana buƙatar sani"

A ƙufule Ashwan ya ce "Ya kamata ka tsaya ka ji abin da ke faruwa mana"

"Wai ana dole ne?" Muby ya tambaya.

"Eh mana wannan ya zama dole saboda abin ya faru ne hanyar kai Munirat Abuja"

Ashwan ya faɗa cikin fushi, abin ya faru ne gurin kai Munirat kuma, Muby ya faɗa a ransa, gashin kansa ya shafa wanda ya sha gyara sai sheƙi ya ke cike da ƙosawa da magana ya ce "Me ya faru a hanyar?"

"A a ba zan faɗa ba tun da ka nuna baka ra'ayi"

"Okay fine" Muby ya faɗa yana ƙoƙarin tashi, da sauri Ashwan ya ce "Matsala ta da kai kenan, saurin ɗaukar zafi to an nemi Maimun an rasa babu irin duban da ba'a yi mata ba amma ba labari, ita kanta Munirat ta ce bata san inda take ba"

Murmushin gefen baki Muby ya yi yana mai lumshe idanu, a hankali kuma ya buɗe tare da faɗin "Na san wadda ta saka aka ɗauketa"

"Ka sani, to idan ka sani wacece?" Cewar Ashwan cikin mamaki, kallonsa Muby ya yi sai kuma ya tashi daga zaunen da yake tare da nufar hanyar ɗakinsa ba tare da ya ce masa komi ba.


Ya ɗauki kusan awa ɗaya a ɗaki kafin ya fito cikin shirinsa na kayan sarauta masu masifar kyau kana ganinsa kaga cikakken Yarima mai ji da kuɗi gami da taƙama, gashin kansa ya ƙara wani kyau kamar ya je gurin gyara, ƙamshin turarensa ya gama baje katafaren parlourn, a gaban rigar wasu kyawawan duwatsu ne ruwan madara, cike da izza yake takawa har ya iso inda ya bar Ashwan, sai dai wannan karon Ashwan na kwance kan kujera me zaman mutum uku, "Idan kaga dama ka biyo ni mu tafi"

Muby ya faɗa yana mai ficewa daga palourn.

Tun daga upstairs wasu dogarawa ke busa algaita tare da yi masa kirari, gaba ɗaya gidan sarautar ya ruɗe da sanarwar Yarima Muby zai shiga cikin gari, wohoho kar ka so ganin yanda dagorawa ke bajewa ƙasa suna kwasar gaisuwa har ya isa gurin jerin motocin da aka yi masa guda ashirin, wata mashahuriyar mota ya shiga ƙirar Lexus baƙa siɗik daga gani sabuwa ce dal, shima Ashwan ya rufa masa baya, nan take aka wangame musu makeken gate ɗin wanda shi kansa na gold ne, ba tare da ɓata lokaci ba su ka doshi cikin garin Sudan.


Laptop ɗinsa ya ɗauka tare da connecting a wayarsa, a hankali yake latse latsensa, wani katafaren guri su ka tsaya wanda ya gaji da haɗuwa, kana gani ka san gurin wasar dokuna ne, doki kala-kala masu kyau da tsafta, a can ɗaya gefen wasu haɗaɗɗun dokuna ne kusan su goma an yi musu kwalliya duk jikinsu kayan ado ne.

Da sauri drivern ya buɗe musu mota, cike da ƙasaita ya ƙara gurin da kyawawan dokunan su ke tare da hawan wani fari wanda duk a ciki yafi kyau kuma ya fi ado, Ashwan ya hau ɗaya black shima ya haɗu, wasu dogarai guda taƙwas masu kula da Yarima ne su ka hau guda taƙwas ɗin da su ka rage, sauran mutanen kuwa motoci su ka shiga, ba da ɓata lokaci ba su ka ɗauki hanya, duk inda su ka ratsa kallonsu ake saboda wani kyau da tsarin da abin ya bayar.


Ashwan da ke gefen Muby ne ya kalle shi cikin mamaki ya ce "Wai ina zamu tafi ne?"

"Gidan da Gimbiya Afnan ta saya, kuma ta sa aka yi kidnapping ɗin Mainun"
Muby ya bashi amsa yana mai ɓata fuska.

Cike da son jin abin da ke faruwa Ashwan ya ce "Gimbiya kuma, yaza ayi ta sace Mainun? bayan itama an yi kidnapping ɗinta, haba Yarima meyesa ka tsani wannan yarinyar ne? be kamata dan kuna faɗa a tsakaninku yasa ka zargeta da ɗauke Maimun ba"

"Ya isheka haka idan baka yarda ba ka zuba ido har mu ƙarasa idanunka zasu gane maka".

Daga haka Muby be sake cewa komi ba, shima Ashwan ɗin shuru ya yi cike da mamakin abin da Yarima ya faɗa, amma duk da haka har yanzu be yarda ba, sai sun tafi ya gani da idanunsa.




..................
Gaba ɗaya rabin mutanen ƙasar Senegal sun hallara a bbban airport da ke birnin ana jiran saukar gwarzo kuma Sarki me taƙama da mulki, kama daga babba har yaro babu wanda be samu labarin cewa Gimbiya Afnan ta ɓata a airport ɗin Sudan ba, mutane sai rububin zuwa ganin Sarki Shuraihu ake, da ƙyar aka samu damar shigewa da su motoci tare da nufar babbar masaurar garin.


Hankalin Fulani da Sarki Shuraihu har yanzu a tashe yake, musamman Sarki Shuraihu ya rasa abin da ke yi masa daɗi.


Wata unguwa su ka shiga wadda faɗin haɗuwarta ma ɓata lokaci ne, a bakin wani tamfatstsen gate me hoton zaki su ka tsaya, horn su ka yi nan take gate ɗin ya ɗage sama motocin su ka shige, tun daga farkon shiga gidan har pearking space red carpet ne kwance me masifar kyau, gidan ya lunka nasu Yarima Muby so biyu girma da kyau, babu abin da zaka rasa a gidan, hawa biyar ne masu masifar girma da haɗuwa gami da tsari, gaba ɗaya gidan na zagaye da tambarin sarauta, daga farkon hawa har ƙarshensa kana ganin masu tsaro ta ko'ina, kyawawan flowers ne baje ta gefen kowanne swimming pool, har guda huɗu, motocin da ke jere a gurin basa ƙirguwa saboda yawan da su ke da, pearking space kuwa har guda shida kowanne cike da motoci iri-iri masu masifar tsada da kyau.


Buɗe musu ƙofar aka yi cikin izza da taƙama Sarki Shuraihu ya fito, haka ma su Fulani, nan take aka fara tarbarsu mutane ta kowanne gefe, tare da yi musu barka da zuwa, cikin masu yi musu sannu da zuwa akwai wata Dattijiuwa me kyau fara sanye cikin kayan alfarma, duk jikinta gold ne kana ganinta ka san hutu ya zauna a jikinta, a bayanta kuwa wata mata ce me matsakaicin haske, sai dai ita tana sanye ne cikin kayan sarauta ta yi kyau sosai sai wani ɓata fuska take kamar wadda aka saka dole.


Babban parlourn gidan su ka sauka, wanda kana ganinsa ka san cewa idan ba cikakkun masu dukiya ba babu me iya zama a ciki, haɗuwarsa ta wuce a misalta shi, yana zagaye da kujeru kala-kala har kala goma, kuma kowacce kujera da nata adon, a gefe wani wangamemen TV ne sai magana yake shi ɗaya, kasancewar babu kowa a cikin parlourn, babu gefen da zaka juya idan har akwai kujeru ba tare da kaga makeken TV ba, komai na parlourn ya tsaru, daga ɓangaren bango hoton family ne sun yi masifar kyau, duk a cikin hoton ba bu wanda be yi murmushi ba, amma ban da Gimbiya Afnan da ke saman wani royal kujera me tambarin sarauta sanye cikin wata alkyabba, fuskarta a ɗaure babu alamar murmushi ko dariya, amma duk da haka ta haɗu sosai kamar sarauniyar kyawawa ta duniya.


Zama su ka yi gaba ɗayansu suna mai ƙara gaisawa, Husna ce ta matsa kusa da wannan Dattijuwar cikin damuwa ta ce "Hajiya barka da wannan lokacin?"

"Yawwa ya ku ka baro Sudan da mutanen ciki?" Cewar Dattijuwar tana kallon Husna da duk damuwa ta bayyana a fuskarta, hawayen da Husna ke riƙewa ne ya sulalo mata, faɗawa jikin Dattijuwar ta yi cikin kuka ta cigaba da faɗin "Hajiya wai yanzu da gaske Gimbiya ta ɓata? wallahi na kasa natsuwa dan Allah ayi wani abu a kai" Ta faɗa tana sheshsheƙar kuka, matar da ke gefe wadda daga gani Mahaifiyar Halima ce ta matso gurin cikin murmushin mugunta ta ce "Kar ki damu Husna insha Allah Gimbiya baza ta ɓace ba, kuma me martaba zai yi iya bakin ƙoƙarinsa gurin gano inda take"

Harara Husna ta galla mata cikin jin haushin murmushin da take ta ce "Bama buƙatar ki shiga maganar mu, idan ma kinsan cewa da saka hannunki a ɓatar Gimbiya, wallahi sai hukunci ya tabbata a kanki"

"Husna ranki zai masifar ɓaci idan na sake jin wata kalma ta fito daga bakinki" Cewar Fulani ranta ya gama ɓaci, ta rasa meyesa daga Gimbiya har Husna ba bu me ƙaunar Mama, da gudu Husna ta tashi tare da haurawa sama tana mai cigaba da kukanta.

Wayar me martaba ne tayi ƙara, da sauri ya ɗauka ganin baƙuwar number, sallama ya yi yana faɗin "Da wa nake magana?"

Daga can ɓangaren kuwa aka amsa da "Allah ya ja zamin me martaba a yanzunnan naga Yarima Mubarak ya nufi wani keɓaɓɓen guri tare da muƙarabbansa, kuma ɗazu naga an shiga da Gimbiya ta wannan hanyar, shine na ce bari na sanar da kai, saboda naji labarin Gimbiya ta ɓata, ba shakka Yarima ne yasa a ɗauketa"

Tashi me martaba ya yi ransa a ɓace, duk idanunsa sun yi jajir, a tsawace ya ce "Lallai ka kawo labari me daɗi, kuma marar daɗi, amma ka tura min address ɗin gurin da ka ke, a yanzunnan zan haɗa tafiya komawa Sudan, tabbas Yarima ya aikata babban kuskuren da dole za'a hukunta shi" Ya ƙarashe maganar yana kashe wayar.

Hajiya ce ta ce "Lafiya kuwa?" Cike da fushi Sarki Shuraihu ke sanar musu abin da ke faruwa, sosai kowa ke mamakin abin da me martaba ya faɗa, amma Fulani ta kasa gazgata hakan dan ta san Yarima ba zai sace Gimbiya ba, ko dan tsananin girman kai irin nasa.


"A gaskiya Yarima ba zai iya wannan abun ba, ya kamata ka sake bincikawa" Cewar Fulani.

Mama ce ta kalleta tana faɗin "Zai iya aikata fiye ma da hakan". Shuru Fulani ta yi ba tare da ta tanka ba, me martaba kuwa a zafafe ya ƙwalawa ɗaya daga cikin dogaransa da ke tsaron bakin parlourn, shigowa ya yi tare da rusunawa ya kwashi gaisuwa "Ina buƙatar a tanadar min jirgin da zan koma ƙasar Sudan yanzunnan bana buƙatar a ɗauki dogon lokaci"

"An gama ranka ya daɗe". Ya faɗa yana mai fita da sauri dan cika umarni.

Kallonsa Hajiya ta yi kafin ta ce "Shuraihu ina zuwa haka? idan ya ɗauketa ba matarsa ba ce, bana son tashin hankali fa"

Cike da girmamawa Sarki Shuraihu ya ce "Amma Hajiya dan tana matarsa shine zai sace ta? ya kamata ya yi magana idan yana buƙatar matarsa"

"Shikenan amma bana son ka janyo wata rigamar"

"Insha Allah babu wata matsala gobe da safe ma zamu dawo tare da ita" Cewar Sarki Shuraihu yana fita daga parloun.







*Na gode sosai da sharhinku a kan book ɗina, kuma insha Allah zan cigaba da antayo muku haɗaɗɗen book ɗinnan me taken GIDAN MULKI, ku dai kawai ku bi ni sannu cikin labarin, sannan masu tambayar menene ya janyo rashin jituwa tsakanin masarautar guda biyu, kawai ku kasance dani a sannu zaku san menene dalilin faruwar hakan*



*GIDAN MULKI*

*By*


*Asmeetar Hydar*









P.4




A ɓangaren Afnan kuwa zaune take a harabar gidan gurin wani hutawa me daɗi da sanyi, waya ce a kunnenta amma baka jin abin da take faɗa, ta jima sosai tana wayar kafin ta kashe tare da miƙewa da sauri ta koma ciki.

Gaba ɗaya masu tsaron gidan sun ɓuya daga ciki kamar babu kowa a gidan, Maimun kaɗai ce ba'a canza mata guri ba, dan har yanzu a sume take.


Tana shiga ɗakinta ta buɗe wata loka tare da ciro wani abu kamar jini cikin kwalba, murmushin mugunta ta saki tana mai shigewa toilet, ta jima sosai kafin ta fito.

Kana ganinta sai ka tsorata saboda yanda ta ɓata jikinta da wani jan abu, zaka yi tsammanin jini ne, rigar jikinta kuwa a yayyage kamar wadda aka yiwa fyaɗe, duk wanda yaga yanda jikin Afnan ya koma babu abin da zai yi zargi face tsammin fyaɗe aka yi mata, gashin kanta duk a hargitse bakinta kuwa ta shafa masa wannan jan abun, idanunta sun yi jajir, har da wani ɗangesa ƙafarta take kamar me koyon tafiya har ta isa gaban morrown ɗakin, nan take kuma ta fashe da wata mahaukaciyar dariya, tana faɗin "Ba'a ja da ni a zauna lafiya, duk wanda ya shiga hurumina tabbas sai ya san ya taɓani". Ta ƙarashe maganar tana ƙara ɗaure fuska kamar ba ita ce wadda ta gama dariya yanzu ba, dama haka Afnan take yana da wahala kaga ta yi dariya me sauti, idan ma kaga murmushinta tabbata a gida ne, a gidan ma sai idan tanada ra'ayin hakan. Sannu a hankali take saukowa kan steps ɗin cike da taƙama haka take motsa jikinta wanda ba namiji ba ko mace taga tsarin jikin Gimbiya Afnan to sai ta burgeta dan kyawun halittar da Allah ya yi mata.

A ɗakin da Maimun ke kwance ta shiga cikin gadara ta zauna gami da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, Maimun kuwa na jin shigowar mutum kamar wadda aka tsikara ta miƙe zaune jiri na ɗibarta, dafe ƙafafunta ta yi cikin mawuyancin hali ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri wallahi sharrin shaiɗan ne, ni kaina bansan lokacin da na faɗi hakan ba, kishi ne ya jani da kuma......."

"Shiiiiiiiiii......." Afnan ta faɗa tana ɗora yatsarta a baki.

Gyara zama ta yi tana mai motsa lips ɗinta a hankali kamar me ciyon magana ta ce "An zo daidai gurin, yanzu kin gane laifin da kika aikata ko?"

"Eh na gane amma ƙarya nake yi ba zan iya kashe rai ba, ko ƙwaro ban taɓa kashewa ba balle ɗan adam". Ta faɗa jiki na rawa.

"Kina tsammanin duk abin da ki ke faɗa game da ni ba zai dawo kunnena ba ne? so duk maganganun da ki ka faɗa jiya ya dawo kunnena, kar ki manta Gimbiya ce a gabanki me taƙama da mulki gami da kuɗi uwa uba kyawu". Afnan ta ƙarashe maganar tana haɗe fuska.


Zufan da ya karyowa Maimun ne ta sharce tana faɗin "Yes i have already knew that, amma dan Allah ki barni na tafi gida na san yanzu labari ya bazu a kan ɓacewata"

"Ƙwarai ma kuwa, zaki koma gida amma ba yanzu ba har sai wani burina ya cika" Cewar Afnan tana tashi tsaye cike da taƙama ta bar ɗakin.




Gaba ɗaya harabar gidan shuru kamar ba bu kowa Allah kaɗai ya san abin da Afnan ke shiryawa, daga can wajen gate kuwa mutanen Yarima Muby ne a tsatstsaye suna ƙoƙarin shiga gidan amma gate ɗin a rufe, Ashwan da

Please Login or Register in order to submit comment