Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cuci tarbiyar da muka ɗauraki a kai, Allah ya isa tsakanina da ke"

"Ka yefe min Daddy ba laifi na ba ne, Hajara ce ta zugani a lokacin son duniya da mance cewar akwai lokacin nadama be zo min ba, na mance Allah baya bacci, na mance cewar akwai ranar da zan yi kuka da hawayena"

Tsawa Daddynta ya daka mata yana mai faɗin "Ba surutu nake so ba, duk lokacin da ki ka ɗauka meyesa ba ki yiwa kanki faɗa ba? kuma ki same shi a waje tun kafin na dawo na tarar da ke".



Ficewa ya yi yana mai cigaba da zuba mata faɗa.

Da dabara Maimun ta miƙe tana mai ɗaukar hijab ɗinta ta saka, tafiya ma sai ta cije lips take iya yi, har ta fita ƙofar gidan.


Wani Matashi ne ta samu kan babur yana shan arake, shekarunsa zai kai talatin da bakwai, daga nesa ya fara washe mata baki har ta ƙaraso inda ya ke, cikin muryarsa me kama da mashayi ya ce "Amarya amarya"


Wani mugun kallo Maimun ta watsa masa kafin ta ce "Uwarka ce amaryar? dan Uban babanka wallahi idan ka sake zuwa ƙofar gidammu sai na sa an yi maka dukan tsiya"

Cike da ɓacin rai mutumin ya sauko daga kan babur ɗinsa ya zabga mata lafiyayyen mari sai da Maimun ta kusa faɗuwa "Ke har kin isa ki zageni, imma ba dan ina ganin mutuncin Babanki ba, me zai haɗani da mace kamarki, kalleki wata jaka da ke, babu abin da ya yi saura sai wani ikon Allah, idan ki ka yi wasa sai ma na fasa aurenki, kuma ki sani matana uku ke ce ta huɗu, yarana kuwa su goma sha biyar ne, kowace mace tana da yara biyar dan haka kema za ki haifo mun naki"

"Sai dai idan Uwarka ce zata haifa maka, shegen banza, wallahi ba zai taɓa yuwa ba idan ba ka fasa aurena ba kai ba ɗan halak ba ne"

Zage-zage Maimun ta fara tana mai tsine masa, matashin me suna Bashiru kuwa biye mata ya yi suna zagin juna daga ƙarshe ya ja akwalarsa ya bar ƙofar gidan.


Yana wucewa ta zube ƙasa tare da rushewa da kuka "Wayyo ni Allah, me na aikatawa kaina haka? tabbas na cuci kaina da kaina Hajara Allah ya isa tsakanina da ke, ba zan taɓa yafe miki ba" Sai da ta ci kukanta me isarta kafin ta ja jiki ta koma ciki.



Sati ɗaya tsakani aka ɗaura aurenta da Bashiru, Mahaifiyarta ta yi kukan da bata taɓa yi ba a rayuwarta, Maimun kam hawayenta har daina zubowa suka yi dan duk abin da ake yi kallon mutane kawai take, washe garin ranar ne aka kaita ɗakinta, sauran matayen sai zagi da habaici suke har masu kai amarya suka watse, kowaccensu ɗaki ɗaya take da har da Maimun ɗakinta ɗaya babu parlour, kujerunta ma da sauran kayan ɗakin komawa da su aka yi.

Duk cikin matan Bashiru babu wadda ta yi karatun boko balle arabic, hakan ya sa basa ganin darajar mijinsu har ma da mutanen unguwa.

Tun ranar da aka kawo Maimun gidan mijinta be shiga ɗakin nata ba, duk yaran gidan ma Uwayensu sun hana su shiga wai kar ta laƙa musu cutar da ke jikinta, sauƙinta ɗaya shine Daddynta ya sama mata Doctor da ke kula da ita, kuma ya ɗorata kan magani, duk binciken da aka yi ya nuna cewa bata samu cutar HIV ba, amma mazaunanta sun lalace sai an yi aiki sosai a gurin.

Abinci so ɗaya take samu, shima sai idan yara sun rage sai ta haɗa sauran ta ci, rayuwa ta yiwa Maimun zafin da ta tsani duniyar gaba ɗaya, daga Daddynta har Mommynta babu wanda ya taɓa zuwa gidan balle ya ga halin da take ciki, kuma umarnin Mahaifinta ne cewar duk Mommynta ta tafi a bakin aurenta, a kullum idan Bashiru ya shigo gida sai ya yiwa Maimun ɗan banzan duka kafin ya bar ɗakin, hakan ya sa fuskarta lalacewa, duk shayun duka ne jikinta, ko maƙiyinta ya ganta a halin da take ciki sai ya tausaya mata.


.........................
Yau ta kama Friday kuma a yau ne aka zo neman auren Nabeelah, wani matashi ne ɗan ƙasar Mali, yaron abokin Mahaifinta ne me suna Nabeel, tun lokacin da suka zo kan lamarinsu Fadila ne ya ji ya kamu da son Nabeelah a ransa, sosai Me martaba ya ji daɗin wannan zancen, a babban parlour aka sauke su tare da zube musu kayan marmari da na more rayuwa, Nabeelah kam ta kasa samun natsuwa tun da ta ji maganar zuwa neman aurenta, Mom na ganin haka ta sameta a ɗaki dan ta san dole zata shiga damuwa.

Zaune take kan table ɗin da ke gaban mirrow kamar yanda ta barta a ɗazu "Nabeelah har yanzu ba ki gama shirin ba ne? mutane na jiranki amma kin zauna sai tunanin wanda be san kina yi ba"


Cikin sanyin jiki Nabeelah ta sunkuyar da kai "I'm so sorry Mom, but na kasa cire Yarima a raina, amma ki taya ni da addu'a"

"Shikenan Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi, amma kar ki watsawa Mahaifinki ƙasa a ido, Nabeel yaron abokinsa ne tun suna yara, na san halinsa yanada kirki sosai ga ibadah, tabbas zai riƙeki amana"

"Insha Allah zan ɗauki ƙaddara kamar yanda ta zo mun, ku iyayena ne kuna da right ɗin da za ku zaɓa mun wanda ku ke ra'ayi, na san cewa baza ku min zaɓin da be dace da ni ba"

Sosai Mom ta ji tausayinta, "Allah ya yi miki albarka, yanzu ki shirya sai ki same su a parlour"

"Tom insha Allah, yanzu zan shirya"

Fita daga ɗakin Mom ta yi, Nabeelah kuwa ta fara shirinta cikin haɗaɗɗar doguwar riga mai kyau, a can ta same su har Dad ɗinta.

Bayan sun gaisa ne aka barsu su kaɗai domin tattaunawa.

Nabeel ba laifi ya haɗu, kuma akwai natsuwa sosai, ga surutu kamar aku, cikin ƙanƙanin lokaci ya shawo kan Nabeelah, har suka yi fira ba laifi kuma ta amince masa tamkar ba wanda ke ranta. Sai yamma suka bar gidan bayan an saka ranar auren wata ɗaya.



.......................
A gefensu Muby kuwa tun ranar da wannan abin ya faru be sake ganin Afnan ba, daga zaran ya shiga part ɗin Mommy zai tarar bata ciki, haka kuma part ɗin Ameera, gaba ɗaya ya rame sai ido da kuma hasken da ya ƙara, sosai Ameer ke jin daɗin yanda Afnan ke gara Muby sai ma abin ya rinƙa basa dariya, cikin kwanakinnan Afnan ta saye waya ƙirar 15promax, sannan ta saka sabon layi.


Duk ƴan gidansu sai da ta yi waya da su, wanda rabon da su yi magana tun farawar rashin lafiyarta, Husna sai zuba surutu take tana faɗawa Afnan abin da ya faru bayan tafiyarta, ba ƙaramin haushi Afnan ta ji ba, saboda ta tsani abin da zai taɓa lafiyar Family ɗinta, daga ƙarshe suka yi sallama bayan ta ce Husna ta tura mata number su Esha.


Sai da ta samu natsuwa kafin ta kira Esha da Muslimat ta video call suka sha fira, Esha ce ta fara cewa "Wai meye sirrin ne matar Yarima? na ji labari gurin Husna wai an saki Maimun".

"An saki Maimun kuma? amma mun gama waya da Husna bata sanar da ni ba" Cewar Afnan tana waro ido, "Gaskiya banada labari amma anjima zan tambayi Ameer"

Muslimat ce ta ce "Ai kuwa shi mijin naki me zai hana ki tambayesa? wai anya ba ciki ne da ke ba, sai wani haske da kyau ki ka ƙara"

Dogon tsaki Afnan ta ja kafin ta ce "Ni babu abin da nake da, daga yin abu so ɗaya shine ciki" Dariya suka kwashe da ita Easha ta ce "Wai kina nufin duk zaman da ku ka yi a can ƙauyen so ɗaya Yarima ya aikata, gaskiya be cika jarumi ba, ya kamata ya yi ajiya kafin ki warke"

"Ai sai ki aje masa idan shi be samu ba"

"Daina wahalar da bakinki itama aurenta ya kusa" Cewar Muslima tana dariya.

Afnan ce ta ce "Aure fa? ai kuwa sai na zo dan baza a barni a baya ba, waye mijin ma?"

Muslima ce ta kuma cewa "Wani ɗan Senegel ne, hmmm guy ɗin ya haɗu fa sai ma kin gansa"

Easha dai shuru ta yi sai sauraronsu take, sun jima suna fira kafin daga baya suka yi sallama.


Misalin tara na dare Afnan na kwance ɗakin Mommy, dan yanzu ba anan Mommy ke kwana ba, Ameer ne ya yi sallama yana mai shigowa fuskarsa ɗauke da murmushi, waya na kunnensa suna magana da Husna, sai da Afnan ta yi musu jan ido kafin ya katse wayar, "Yawwa Ameer wai Maimun fa?"

Dariya Ameer ya yi yana faɗin "Auny Afnan wai dama ba ki san Brother ya yi waje da ita ba ne?"

"Idan na sani zan tambayeka, please ka faɗa min bana son yawan magana".

Duk abin da ya faru Ameer ya kwashe ya zayyanawa Afnan, sannan ya ƙara da cewa "Na ji labarin auren da Babanta ya yi mata da wani mutum me mata uku ita ce ta huɗu, yanzu haka tana da cutar mazaunai"

Cikin tausayi Afnan ta ce "Subhanallahi haƙiƙa rayuwa abin tsoro ce, yanzu abin da ya sameta kenan, rayuwar duniyar ma wanda be zo ba jiransa take yi, Allah ya sa mu dace"

Da ameen Ameer ya amsa yana mai miƙewa tsaye "Auny zan tafi sai da safe"

"Okay bari na rufe ƙofar" Hijab ɗin da ke jikinta ta ƙara gyarawa sannan ta bi bayansa, yana fita ta tura ƙofar, karaffffff ta ji an riƙe ƙofa tare da shigowa ciki.

A tsorace ta matsa baya ganin Muby tsaye yana watsa mata idanuwansa, duk ya zama wani iri, Office ma ba kullum yake zuwa ba saboda tunaninta, sanye yake cikin jallabiya fara, hannunsa ɗauke da laptop ɗinsa sai wayoyinsa uku, ɓata fuska Afnan ta yi tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa da niyar ficewa.

"Idan ki ka tafi za ki iya rasa ni" Cakkk ta tsaya zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.

A hankali ya koma gabanta yana mai rufe ƙofar, kusan mintuna biyu ya ƙura mata haɗaɗɗun idanunsa masu kyau da sheƙi "Mu koma ciki magana zamu yi"

"Ni ba zan koma gidanka ba fa"

Cewar Afnan tana gantsaro baki a gaba, hannunta ya kama suka koma kan bed, Afnan kam sai turo baki take ita ala dole ana bibiyarta, kayan da ke hannunsa ya aje kafin ya rusuna da gwuiwoyinsa ƙasa yana mai kallonta, ba zato ta ji ya ce "Kina sona?"

Yanayin yanda ya yi maganar kawai ya isa ya bawa me kallonsa tausayi, Afnan kuwa jikinta ya yi sanyi ta rasa wace amsa zata bashi, "Ki kalli cikin idona ki faɗa mun, na yi miki alƙawarin idan har ki ka ce bakya sona zan barki, amma ki sani cewar duk abin da ya sameni ke ce sila"

"Nima ai ba ka sona, kuma kai ne ka fara tsanata a kullum idan ka zo gidammu sai ka dakeni" Ta ƙarasa maganar cike da shagwaɓa, bakinta ya ƙurawa ido ganin yanda take turo shi gaba, "No ba haka ba ne, ke ce kin faye ɗagawa sosai"

"Kaima kana da ɗagawa"

"Tom shikenan na yarda amma ki yafe mun, dan na samu damar da zan nuna miki soyayyar da babu wani ɗa namijin da ya taɓa nuna miki"

"Uhmm ni bacci nake ji"

"Sai kin fara faɗa mun idan kina sona"

"Lallai ma so ka ke Fadila ta yi mun duka"

"Wace Fadila kuma, bana son kina mun maganar wata dan har abada ba zan yi miki kishiya ba insha Allah, ke ce ta farko a yanzu kuma ta ƙarshe my Princess" Rufe fuska Afnan ta yi cikin jin kunya, sosai ta ji daɗin abin da ya ce saboda macece ita me masifar kishi, musamman da ta gane cewar da gaske fa ta kamu da son Muby, tana ji a ranta baza ta iya rayuwa babu shi ba.

Haurawa kan bed ɗin ya yi tare da rungomata a jikinsa, kamar jira take ta ƙara shigewa jikinsa tana wani shagwaɓe fuska, laƙace mata hanci ya yi "Dama ana so ana kai kasuwa ko My Princess?"

"Eh dama kai ne burin zuciyata" Ta faɗa tana rufe fuska cikin ƙirjinsa.

"Tom a bani haƙƙina a matse nake sosai"
A tsorace ta fara barin jikinsa har hawaye ya fara taruwa cikin idanuwanta.

"Babyna meye na kuka kuma? daga kawai zan mori kayana, Allah duk waɗannan lokacin a wahalce nake kwana, na saba da ke sosai, kaɗan zan yi kin ji Baby kuma baza ki ji zafi ba"

"Aa akwai zafi mutuwa ka ke son nayi ne?"

Dariya Muby ya yi yana faɗin "Baza ki mutu ba, yau a hankali zan yi"

"Idan kuma Mommy ta same mu fa?"

"Aa tana ɗakin mijinta itama, dan haka ki bari mu kwashi soyayyarmu kawai".






*Mu haɗe a next page yau page ɗin babu yawa, lokacin baya na ce zamu yi kyautar 1Gb ga wadda ta fi sharing book ɗinmu, to sai kuma aka kasa samun wadda ma ke sharing, ina ganin masu tura book ɗina wasu groups ƴan Ƙungiyarmu ne kawai, amma bayan nan babu wadda ke sharing*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 26









Ɗan ɓata fuska ta kuma yi kamar zata yi kuka ta ce "Amma har yanzu ban warke ba, Mommy ta haɗa mun wani ruwa ina shiga, ka san menene?"

"Aa bansaniba sai kin faɗa Baby"

Marairaicewa ta yi tana faɗin "Ina jin zafi sosai idan na shiga ruwan, amma ta ce kar na daina shiga"

Langaɓe wuya Muby ya yi kamar yanda ta yi ya ce "Eyyeh sorry duk laifi na ne, zo mu gani idan gurin ya warke" Afnan na jin haka ta haura ƙarshen bed tana dariya "Ni baza ka gani ba, haka kawai ka kalle mun jiki"

"Jikinki ba nawa ba ne? Baby dan Allah ki bari na gani, ina son na san tsawon lokacin da zan kai ina haƙuri kafin ki warke"

"Sai nan da wata biyar zan dawo daidai"

Waro ido Muby ya yi yana mai haurawa kusa da ita, "Ai kuwa ba zai taɓa yuwa ba, ki fara nuna mun na gani"
Ya faɗa yana kiciniyar cire hijab ɗin da ke jikinta, Afnan na ganin haka ta fara zille-zille, duk ta ƙara tayar masa da feelings ɗinsa, ba ƙaramin laushi da kyau fatar jikinta ta ƙara ba, kamar yana taɓa auduga haka yake jin jikin nata, bugun ƙofar da ake ne yasa su biyun tsayawa cikin alamun rashin gaskiya, daga can waje Mommy ta ce "Yarima kanada hankali kuwa? a ɗakin nawa zaka biyo ta, ka buɗe ƙofar nan kafin ranka ya ɓace" Afnan kam kunya ce ta kamata, da sauri ta shige blanket tare da rufe jikinta, Muby kam babu kunya ya miƙe yana gyara jallabiyar da ke jikinsa duk ta jakushe, ƙofar ya buɗe yana lumshe ido, wani kallo Mommy ta watsa masa ganin duk rashin natsuwa ta bayyana kan fuskarsa "Lallai yarannan wallahi gobe zaku bar gidannan, ai sai ku koma ɗayan gidanka tun da abin da ku ke so kenan" Ɗan sosa kai Muby ya yi yana faɗin "Godiya nake Mommy Allah ya biya"

Harara ta galla masa tana mai kallon inda Afnan ke kwance "Ai sai ki buɗe fuskar ko, na daɗe da sanin kina son komawa ɗakinki kawai jan aji ki ke masa"

Afnan kam dariya ƙasa-ƙasa take yi, dan kunya duk ta rufeta.

Hannun Muby Mommy ta ja suka fice, dan ta san idan har ba haka ta yi ba tabbas sai ya kwana a ɗakinnan, ko kuma ya yi mata wayo su koma part ɗinsa.


Suna fita Afnan ta miƙe tare da sakawa ƙofar key.


Washe gari da misalin goma na safe su Alhaji suka kira Muby da Afnan, Me martaba dai murmushi kawai yake dan ya san cewa duk suna buƙatar junansu kawai shirme ne irin nasu, Alhaji ne ya ce "Toh Mahaifiyarku ta kawo ƙararku kan cewa ku bar mata gida"
Dariya da kuma kunya ce ta kama Afnan jin abin da Alhaji Babba ya ce, Muby ne ya tari numfashinsa da faɗin "Yawwa ko kai fa, ni dama babu abin da zan zauna na yi a gidannan, kawai ku bani matata na tafi da ita gidanmu"



"Sarkin marassa kunya ai shiyasa na faɗa musu abin da ka tashi aikatawa jiya, dan Allah Alhaji ku bashi matarsa ya tafi"
Murmushin manya Alhaji ya yi kafin ya ce "Ai ita Gimbiya ta ce a raba auren, shiyasa ma na kira Yarima ya bata takaddarta" A firgice Afnan ta ɗago tana kallon Muby kamar zata yi kuka, shima marairaicewa ya yi yana kallonta.
"Ko ya ki ka ce Gimbiya?" Alhaji ya faɗa yana kallonta, girgiza kai Afnan ta shiga yi alamun Aa, sai kuma ta miƙe da gudu ta fice daga ɗakin, Me martaba ne ya ce "Hmmm ikon Allah yara manyan gobe, kalli yanda ta fita kamar wadda za'a raba ta da rayuwarta"

"Amma Abba ni matsayin rayuwa ne a gurinta"

Cewar Muby idanunsa a ƙasa, Me martaba ne ya ce "Tashi ka bani guri anjima ku tattara ku tafi, akwai kayan lefen da aka haɗa jiya sai ku tafi da shi, na san cewa yanzu tana can cikin damuwa je ka rarrasheta Allah ya yi muku albarka ya kuma tabbatar da Alkhairi"

Da ameen suka amsa Muby ya miƙe cikin tsananin farinciki ya bar ɗakin, a room ɗin Mommy ya sameta kwance ta yi rufff da ciki, sai rusar kuka take tana sambatu, da sauri ya matsa kan bed ɗin ya rungumota "Baby sorry duk wannan kukan na meye ne?" Shigewa jikinsa ta yi tare da ƙara sautin kukan nata "Mijina dan Allah kar ka bari su Alhaji su raba mu, bana son na rasa ka" Tausayinta ne ya kama sa ganin da gaske kuka take ga numfashin da take saukewa akai-akai, "Daina kuka baza a raba mu ba, Abba ya ce anjima mu tafi gidammu" Ƴar dariya ta yi tana mai gyara kwaciya kan ƙirjinsa, "Da gaske love?"

"Yes kuma na fiki jin daɗin hakan saboda a can na san baza a hana min kayan marmarina ba".

Dukan wasa ta kai masa a ƙirji tana jan sajen da ke fuskarta.

"Yanzu tashi mu tafi part ɗina ina son na rage zafi ko kaɗan ne, Allah ba zan yi komi ba"

"Ni sai ka goya ni to"

"Wannan me sauƙi ne zo ki hau" Saukowa ya yi daga kan bed ɗin ya duƙa, ai kuwa ta ɗane kamar wata mage, tun da suka fara tafiya babu kowa a hanyoyin har suka kusa shiga part ɗinsa, Ameera da ke saukowa daga upstairs ne ta bushe da dariya tana faɗin "Brother yau kai ne a haka" Ɗaure fuska Muby ya yi dan kar ta raina sa "Ina wasa da ke ne? zan kama ki ne sai na ɓaɓɓallaki daga ke har Ameer zan yi maganinku" Shuru Ameera ta yi tare da komawa sama dan ta san halinsa sarai.


........................
A ɓangaren su Mama kuwa tun da aka tafi da su ake gana musu azaba, waɗan da ta saka aiki kuma an yanke musu hukuncin kisa saboda sun aikata kisan kai ba adadi, Mama satin ta ɗaya aka sakota, tun da ta koma gidansu ta kwanta rashin lafiya kullum cikin surutu take tana neman yafiya, yaranta kuwa Halima ce kaɗai ke zuwa dan ta duba ta, amma daga Bilkisu har Hauwa'u sun ɗauke ƙafa.

Yau ta kama weekend, su Alhassan na zaune a parlour Bilkisu ta shigo a hargitse jikinta duk tabon duka ne, babu wanda ya ko kalli inda take cikin kuka ta faɗi ƙasa tana mai rusa ihu kamar zata tashi gidan gaba ɗaya, Fulani da saukowarta kenan ta nufi gurinta da sauri tana tambayar abin da ya faru, Muhseen ne ya sha gaban Mahaifiyar tasa "Fulani dan Allah ki barta, bayan duk abubuwan da suka yi miki a gidannan"

"Aa Muhseen ai shi yaro na kowa ne, haƙƙine a gareni na san abin da ke faruwa, Bilkisu tashi ki zauna me yake faruwa ne?" Duk da cewar tana cikin damuwa amma hakan be hanata faɗin magana son ranta ba "Ina ruwanki da abin da ke faruwa? magulmaciya kawai yo mijina ne ya sakeni dan na sha maganin hana ɗaukar ciki sai kuma me ki ke son sani? mtssssss" Ta ja dogon tsaki tana mai nufar ɗakin da suke kwana idan sun zo gidan, salati Fulani ta yi jin an saki Bilkisu, ita ba maganganun da ta faɗa mata ba ne ya ɓata mata rai ba, sakin ne ya tashi hankalinta.


Suna cikin haka Hauwa'u ta shigo kamar zata tashi sama, tana ganin Fulani ta faɗa jikinta tare da fashewa da kuka "Fulani wallahi Mama ta cuce mu, Allah ya isar mana" Rufe mata baki Fulani ta yi, "Zauna anan Husna kawo mata ruwa ta sha"

Kan kujera me zaman mutum uku suka zauna, Husna kuwa ta miƙe dan ta kawo ruwa, su Muhseen kamar su yi mata shegen duka dan tun ranar da suka zagi Hajiya suke mugun jin haushinta. Ruwa Husna ta kawo cikin Cup me sanyi, cike da kunya Hauwa'u ta karɓa dan wata irin kunyarsu ma take ji, idan ta tuna cin mutuncin da suka rinƙa yi musu, sai da ta samu natsuwa kafin Fulani ta ce "Me ya faru kuma? har ki ke faɗawa Mahaifiyarki waɗannan lafuzzan, kar ki mance ita ce wadda ta haifeki, duk laifin da ta yi miki be dace ki haɗata da Allah ba" Ajiyar zuciya Hauwa'u ta sauke kafin ta kama hannun Fulani "Dole ne na haɗa Mahaifiyata da Allah, a yau ne na tabbata cewar ke ce Uwa ta gari, tun muna ƙanana Mama ta koya mana tsanarku ta nuna mana cewa ku abokan gaba ne, tun muna yara take sanar da mu ku ba mutanen zama ba ne, idan ba ki saniba yau zan sanar da ke cewar duk yaranki da suke mutuwa Mahaifiyarmu ce ke kashe su, ita ce ke zuwa gurin boka a saka miki magani cikin abinci, ko kuma a kashe yaron tun daga ciki ita ce silar ƙiyayyar da ke tsakaninku da su Sarki Ahmad, tun ranar da aka yi aurenmu ta kawo mana maganin hana ɗaukar ciki wai dan kar mu tsufa da sauri, wallahi nayi nadamar halayena dan Allah ku yafe mana gashi mijina ya ce na koma gida sai ya neme ni" Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

Sai da Fulani ta rarrasheta kafin ta raketa har ɗakin da Bilkisu ta shiga, tun a bakin ƙofa Bilkisu ke zuba ma Fulani ashar, tare da mugayan kalamai, kan cewa ita ce silar kashe musu aure, Fulani bata ce komi ba ta bar ɗakin cike da tausayinsu.

Satinsu ɗaya a gida kullum Bilkisu sai ta tashi hankalin kowa a gidan, daga ƙarshe Me martaba ya ce ta bar masa gidansa tun da bata son zaman lafiya, Alhassan ne ma ya roƙesa kan ya barta ta zauna, shiyasa Me martaba ya amince masa, amma ya ce duk ranar da ta ƙara yin abin da be dace ba sai ta bar masa gida, wannan dalilin ne ya sa Bilkisu shiga hankalinta, Hauwa'u kuwa ta dawo gefen su Fulani, dan ko shawara take nema gurinta take zuwa, zaman lafiya suke tamkar ciki ɗaya suka fito.



ƘASAR SUDAN
............................
A ɗakinsa ya sauke ta kan bed yana yi mata chakulkuli, Afnan kuwa sai dariya take har da ƙwarewa "Mijina dan Allah ka daina, yanzu idan ciyona ya tashi fa?"

"Baby wanne ciyon kuma? ai na san wasa ki ke yi, tsoro ne kawai irin naki ya kamata a ce kin warke yanzu"

"Aa ni ban warke ba, har yanzu akwai ɗinkin fa"

Kwanciya Muby ya yi a gefenta yana mai janyota jikinsa "Har yanzu fa Babe? nuna min na gani"

Zaro ido Afnan ta yi tana mai dukan ƙirjinsa da wasa "Lallai ma ni baza ka kallemin jikina ba"

"Amma nima jikina ne, Babe ki nuna mun

Please Login or Register in order to submit comment