Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daddaɗan labari, kamar yanda suka ji labarin cikin Munirat, farinciki ta kowanne ɓangare.

Kunun gyaɗa Mommy ta haɗawa Afnan, amma ko kallonsa bata yi ba, sai ma ƙoƙarin amai take yi, robar Fara kuwa ta ci kusan goma, su Esha sai dariya suke yi mata dama da yamma zasu koma ƙasar Senegal, Ameer kam a Lambun gidan suka tare shi da abar ƙaunarsa, su Ashwan ma sun zo ƙarfe biyu lokacin da Mommy zata koma, har gate Afnan ta rakasu.


Wayarta da ke hannunta ne ta fara ƙara, ganin baƙuwar number ya sa ta ɗaga amma bata ce uffan ba, daga can ɓangaren Halima ta ce "Gimbiya Halima ce ke magana ya ki ke?" Afnan na murmushi ta amsa da "Lafiya ƙalau Aunty Halima ya gida?"

"Alhamdulillah, jiya Husna ke faɗa mun sun shigo Sudan, gaskiya na so na zo nima amma cikin da nake da yana bani wahala sosai, but idan na haihu zan shigo insha Allah"

Cike da murna Afnan ta ce "Wow Aunty Halima ciki? na taya ki murna Allah ya raba lafiya"

"Ameen na gode kema ai Fulani ta sanar da ni ɗazu cewar kina da cikin sati biyu da kwanaki" Ɗiffff Afnan ta kashe wayar cikin kunya, dan tana masifar jin kunya a ce tana da ciki, shafa cikin nata ta yi a zahiri ta ce "Allah ya raya mun duk abin da ke cikinnan nawa, tare da rayuwa me albarka"

"Idan har ina numfashi ba zan taɓa bari ki haife shi ba, wallahi idan har ina raye sai na kasheki na kashe mijinki, da duk wanda ke ƙaunarki......"

A mugun tsorace Afnan ta juyo dan ganin wanda ke faɗar waɗannan mugayen kalaman.






*Sai mun haɗe a next page*





*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*










P. 29







..............................................................
A ɓangaren Maimun kuwa ba laifi jikinta ya fara samun sauƙi dan har tana iya fitowa tsakar gida, mutanen gidan kam halinsu sai abin da ya ƙaru, amma suna ɗan shige mata saboda sun samu labarin Mahaifinta me kuɗi ne, dama a rayuwarsu babu abin da suke so fiye da kuɗi, tun da mijinta ya ga ta fara samun sauƙi a kullum sai ya kusanceta, tun Maimun na kuka da kokawa har ta haƙura tare da fawwalawa Allah lamuranta, sosai take nadamar abubuwan da ta rinƙa aikatawa wanda sai a yanzu take ganin cewa ita mugunta tabbas bata ƙarƙo.

Fatanta ɗaya shine ta samu damar ganin Muby da Afnan ta roƙe su gafara, likitan da ke duba ta kuwa kullum sai ya zo ganin yanda jikinta yake.

So ɗaya ta taɓa zuwa gidansu kamar Mahaifinta zai kasheta da duka, hakan ya sa Maimun bata sake zuwa gidansu ba, amma Mahaifiyarta na tura mata saƙo.

Yau ma kamar kullum wani yaro ne ya shigo gidan yana neman Maimun, Uwargidan ce ta fito daga ɗakinta jiki na rawa ta ce "Wa ake nema ne?"

Maimun da fitowarta daga bayi ne ta karɓe zancen da cewa "Saƙo ya kawo mun, miƙo min nan na gode sosai" Wata leda da takadda Maimun ta karɓa hannun yaron, carafff Uwargidan ta buge ledar ta watse a ƙasa, sabulun wanki da taliya ɗaya ne ciki sai canjin da yaron ya kawo, ko kallon inda kayan ke zube Maimun bata yi ba ta shige ɗaki ɗauke da takaddar a hannu, ita farincikin samun address ɗin gidan da su Muby suka koma take yi, dama yau kwana uku tana neman gidan amma bata samu ba sai yau.

Duk da cewar Maimun bata kula Shatu Uwargidansu ba amma hakan be hanata shiga ɗakin Maimun tana habaici ba "Gidan uban wa ki ka samo abinci haka? har da su taliya, yoooo ashe shegiyar uwarki ta aiko miki da abinci shine har ki ke sayarwa mutane"

Ran Maimun a ɓace ta ce "Kinga Shatu dan Allah ki kama kanki da ni, bana son tashin hankali idan taliyar ce ki ke so, ki je ki ɗauka sai ku dafa, amma ku aje mun saura"

"Uhmmmmm tom muna godiya sosai, amma taliya ɗaya waye zai ci waye zai haƙura"

"Aa ni bansaniba kawai idan kun gama a rage mun nawa, idan kuma ku ka hana mun wallahi ba zan ƙara kawo abinci gidannan ba"

Shatu na washe ƙazamin bakinta ta ce "Ai baza a yi haka ba, bari na je na ɗora yanzu" Ta ƙarasa maganar tana barin ɗakin.

Maimun kuwa takaddar ta adana saboda a gobe take son zuwa gidan ba tare da kowa ya sani ba.


...................................
Duk masu aikin gidan sun zagaye Hajara ƙawar Maimun da duk jikinta ƙazanta ne, kamanninta sun canza fatar jikinta kuwa har tsagewa take, sai dai kaga tsutsa na faɗowa daga cikin sasssan jikinta, a tsorace Afnan ta ja baya tana mai karanta duk addu'ar da ta zo bakinta, surutun masu aikin gidan ne ya fito da su Muby, da sauri ya ƙarasa gaban Afnan yana mai mannata a ƙirjinsa, "Wacece wannan kuma?" Cewar Ashwan yana toshe hanci, duk waɗan da ke gurin toshe hanci suke tsabagen warin da Hajara ke fitarwa, babu kunya ta bushe da dariya har tana tafa hannu "Sannu masoya munafukan banza, sanadiyar ku na shiga wannan tashin hankali, amma zan iya cewa Maimun ce sila matarka, kuma wallahi sai na ɗauki mataki babu wanda zan raga ma"

"Sai dai Uwarki ce baza ki raga ma ba, shegiya me baƙin hali, ku fitar mana ita daga gida please tun kafin na kassarata" Cewar Easha tana nufar Hajara gadan-gadan, masu tsaron gidan kam sai ja baya suke dan basa son taɓa jikinta, sai a yanzu Muby ya gane wacece dan ya taɓa dawowa gida ya same su ita da Maimun, a fusace ya bar jikin Afnan fuskarsa ta gama rinewa, yana isa ya wanketa da mahaukatan maru guda biyu, shaƙota ya yi da ƙarfin tsiya kamar zai halakata ya ce "Ke dabba ƙazama me baƙin hali, babu abin da ya haɗamu da ke balle har ki samu damar shigowa har cikin gidana, sai yanzu na gane cewa ke ce ƙawar Maimun, kin aikata babban kuskure na shigowa gidana" Ganin yana ƙoƙarin kasheta ne ya sa su Ashwan ɓanɓare Hajara da ƙyar, ai kuwa ta runtuma da gudu, "Idan har ku ka yarda ta gudu sai na hukuntaku wallahi" Cewar Muby yana kallon masu tsaron gidan, suna jin haka suka bi bayan Hajara, wadda ke faman ƙyalla guda kan hanya har ta iso titin da ke unguwar, tsayawa ta yi dan ganin ko har yanzu mutane na biye da ita, ai kuwa ta hangi Dogarai kusan su ashirin sun yo kanta daidai lokacin da wata ƙatuwar mota ta miƙo titi, ba tare da Hajara ta lura ba ta faɗawa titin, cikin zafin nama motar ta ɗauketa sama, ji ka ke timmmmm....., duk naman jikinta ya yi ratsa-ratsa, Dogaran na ganin haka suka koma da baya, motar da ta kaɗe ta kuwa ko tsayawa bata yi ba.



Muby da sauran mutane na harabar gida ba wanda ya samu natsuwa tun bayan jin kalaman Hajara, Afnan kam ta maƙalewa Muby kamar zata shige jikinsa dan tsoron kar Hajara ta rabata da Babyn da ke cikinta, suna cikin haka Dogaran suka dawo tare da faɗin abin da ya sami Hajara, duk da cewar sun girgiza da jin abin da ya faru amma hakan be hana hankalinsu kwantawa ba.

Komawa daga ciki suka yi masu aikin gidan ma suka tafi harkokin gabansu.


Duk da hakan hankalin Afnan a tashe yake, kusa da Muby ta zauna har da wani ɗora hannunsa kan cikinta, Muslima da Easha ne suka fashe da dariya ganin abun da ya tsorata Afnan yau, "Lallai Gimbiya wai yau ke ce a tsorace haka? Easha please ku duba mun lamarinannan" Cewar Muslima tana mai cigaba da dariyarta.

Muby ne ya yi saurin cewa "No ku daina kar ku ƙara tsorata mun Babyna, ai jaruma ce bata tsoron komi ko Baby?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Afnan, ɗaga masa kai ta yi tana faɗin "Eh amma ba a wasa da rayuwa, ni gaskiya har yanzu hankali a tashe yake, anya Hajara baza ta fito mana fatalwa ba?"

Gaba ɗaya ɗakin bushewa da dariya suka yi ganin da gaske Afnan ke maganar har da ɗan matso ƙwalla, Cakkkkk Muby ya ɗagata sama yana mai nufar Upstairs "Ai sai ku ci kanku da dariyar, ni na tafi kwantarwa Baby da hankali"

Ashwan ne ya ce "Tom a sauka lafiya muma tafiya zamiyi, anjima zamu same ku a airport"

Kallonsa Muslima ta yi tana sunne kai, "Ƴammatana mu tafi ki raka mu ko?" Ya faɗa yana mai kashe mata ido.

Kunya ce ta kama Muslima dan ba laifi macece me kunya, har gurin motar ta yi musu rakiya kafin ta koma daga ciki.


Su Muby kuwa ɗakinsa ya nufa da Afnan, ɗan ɓata fuska ta yi kamar me shirin yin kuka, "Tom me ya faru kuma Baby?" "Uhmm..uhmmm ni room ɗina zamu tafi yau"

"Wai shine ake ɓata fuska haka? okay bari mu tafi can" A ɗakinta ya direta yana mai kwanciya gefenta tare da sauke ajiyar zuciya.

Shuru Afnan ta masa dan wani irin sauyin da jikinta ya yi, Muby ne ya ce "Baby bacci ne?"

Gangarowa jikinsa ta yi tana wani irin shagwaɓe fuska "Ni dama.....dama.....dama...."

"Dama me?" Muby ya tambaya yana ƴar dariya dan ya gane abin da take nufi.

"Uhmm...Allah ka gane me nake so kawai zolaya ce"

"Aa banganeba faɗa mun mana"

"Tom ba Babynka ba ne wai sai shi yana son ayi masa wasa" Dariya ce ta ƙwacewa Muby har da mirginawa, ai kuwa Afnan ta fashe da kuka hihihi har da hawaye, tsagaita dariyar ya yi yana rarrashinta dan be yi zaton abin ya kai haka ba, "Wai me ki ke so ne? faɗa mun Baby bana son wannan kukan fa"

Ƙwace jikinta ta yi tana mai cigaba da kukanta dan ta gane ya san abin da take nufi kawai yana son wasa da hankalinta ne, hugging ɗinta ya kuma yi ta baya yana mai kashe mata ido ɗaya "Tom zo na yi ma Baby wasa" Cike da murna Afnan ta ɗane kan cinyarsa tana dariya, maɓallin rigarsa ta fara cirewa tana wani kashe ido kamar wadda zata yi bacci, gaba ɗaya ta ruɗa shi da salonta tun kafin ta gama cire masa kayan Muby ya gigice, ai tuni salon ya canza suka fara farantawa juna, duk iya yin Muby amma Afnan ta ƙi yarda ya shiga daga ciki, so biyar suna wanka dan laƙe masa ta yi kamar kaska, abun ya ba Muby mamaki sosai ganin lokaci ɗaya Afnan ɗinsa ta canza kamar ba ita ba, idan ma ya daina romance ɗin sai ta fashe masa da kuka ta ce ai Baby ya ce acigaba da yi kar a daina, Muby ko dama abin da yake so kenan, sai da suka gama yagalgala juna kafin suka sake yin sabon wanka.


Ƙarfe biyar saura su Easha suka fito cikin shirinsu na komawa, har da Ameer ya zo rakiya sai dai Ameera bata samu zuwa ba dan exam ɗin da suke da, daga sama suka fara jin takun su Muby har suka fara hangensu cikin wata irin shiga tamkar zinarai, shadda ce bugagga kalar sararin samaniya, kayan jikinsu iri ɗaya kowannensu ya ɗora alkyabba saman kayan, Afnan kuwa ta saka takalma irin na sarauta gaba ɗaya ƙafarta a ciki, hannunta ɗauke da handbang, ɗayan hannun kuwa ta saƙalo shi a gefen Muby, ƙamshin turansu ne ke tashi har suka sauko ƙasa.

Kowa da ke parlourn sai yaba kwalliyar su ake dan ba ƙaramin haɗuwa suka yi ba, Easha ce ta ce "Ina zuwa da handbag kuma matar Yarima?"

Ɗan murmushi Afnan ta yi tana mai faɗin "Mijina ne ya ce mun yana son na yi masa lalle, idan muka kai ku airport zan sauka a gurin me lalle sai ta yi mun kafin mu dawo gida"


"Okay mu tafi ko" Muslima ta faɗa tana yin gaba.


Airport suka nufa wanda jirgin Masarautar Sudan za su bi, idanun Afnan ya ciko ta ƙwalla ganin da gaske fa komawa za su yi.

Ameer da Husna kam suna gefe sai ƙus-ƙus suke, million ɗaya Muby ya basu jirginsu na ɗagawa suka bar gurin, su Ashwan basu samu damar zuwa ba, tun daga hanya Ameer ya nufi gida su Muby kuwa suka nufi Shop ɗin wata hamshaƙiyar me zane, a wajen Shop ɗin ya sauketa, Afnan kam shagwaɓa ta fara zuba masa wai sai sun shiga tare, cikin mutunci matar ta karrama su, sai da aka fara lallen kafin ya tafi, matar kam sai kallonsu take cike da sha'awa ganin yanda Muby ke nan nan da ita.


Bayan sallar magrib ya zo ɗaukarta, dan sai da ya yi sallah kafin ya dawo, jan lalle ne me masifar kyau, musamman fatar jikin Afnan da ke fara sol, kuɗi masu yawa Muby ya biya ganin yanda lallen ya haɗu kamar ya lashe hannayenta.

A harabar gidan ya sauke su, ba tare da jin komi ba ya ɗagata zuwa cikin gidan, masu aikin kuwa duk sun sunkuyar da kai saboda ganin abin da basu saba ganin Yarimansu na yi ba.




Tun da ƙarfe tara ta buga Afnan ta fara rigima, tana son cin Fara.

Dole ta sa Muby fita dan ya sayo mata, wannan karon roba ashirin ya sayo ya zube kichen, sai da ta ci biyar a daren kafin hankakinta ya kwanta.


Misalin sha biyu na rana, Afnan na ɗakin Muby dan gyara masa, shi ko ya fita Office an yi masa kiran gaggawa, ita da ƴan aiki suka gama gyara gidan tasss, ƙamshi na tashi ta ko'ina, Kichen ta koma dan dafa abincin rana, dama ita ke abinci kowanne lokaci, dan bata ra'ayin masu aiki su yi mata, ɗakinta da na Mijinta ita ke gyarawa, tuwon shinkafa ta ɗora da miyar kuka wadda ta sha naman rago, sai da ta gama kafin ta fara pepper chicken wanda ya gaji da haɗuwa, sai Jus ɗin kwakwa ya sha madara da Flavour, a Fridge ta saka kafin ta koma sama dan ta shiga wanka.

Awa ɗaya ya ɗauketa har shiri, Abaya ce maroon colour me adon duwatsuna, sai ɗan ƙaramin mayafin Abayar wanda ta ɗaure gashin kanta da shi, haɗaɗɗun turarukka ta fara fesawa fuskarta ɗauke da murmushi, daga sama ta fara jiyo yanda security ke faman surutu, immediately ta sauko har tana haɗa steps, a bakin gate ta samu masu aikin gidan sun hana wata matashiya shigowa har suna ƙoƙarin dukanta, fuskar matar cikin niqab ta saka ƙaton hijab har ƙasa, "Let her come in please" Afnan ta faɗa tana gyara tsayuwa cike da taƙama, cikin sanyin jiki matar ta shigo har ƙasa ta rusuna sannan ta janye niqab ɗin da ke fuskarta, cike da mamaki Afnan ke kallon Maimun da idanuwanta sun gama cikowa da hawaye, a fusace Afnan ta ce "So are you the one, what are you doing in my husband house?"

Fashewa da kuka Maimun ta yi cikin nadamar abubuwan da ta aikata, "Dan Allah ki yafe mun Gimbiya, wallahi nayi nadamar abubuwan da na aikata miki, haƙiƙa na zalunceku daga ke har mijinki, ko da ace baza ki ƙara yarda da ni ba, ina mai neman alfarma da ki yafe mun" Sosai tausayinta ya kama Afnan, musamman yanda taga Maimun ta koma tamkar ba ita ba, har parlour suka shiga tare, wata ƙararrawa Afnan ta danna sai ga me aiki ta shigo cikin girmama ta rusuna tana mai gaida Maimun, Afnan ce ta ce "Ki kawo mata abun da zata sha"

Sai kallon ko'ina Maimun ke yi, dan ganin yanda gidan ya haɗu kamar baza'a mutu ba, tabbas ta san ta yiwa kanta, yanzu gashi wadda ta tsana a baya tana zama gidan da ko gidan shugaban ƙasar Sudan ba zai nuna masa kyau ba.

Duk abubuwan buƙata sai da aka zubewa Maimun, kamar zata haɗiye kulolin abincin haka ta rinƙa ci, ba ƙaramin tausayinta Afnan ta ji ba, suna cikin haka Motar Muby ta shigo gidan, motocine guda ashirin masu tsadar gaske, wata arniyar mota ce aka buɗe masa, cike da gadara ya fito gidan, ya matsu ya shiga dan ganin farincikin zuciyarsa, tun da ya fito Dogarai ke zubewa suna kwasar gaisuwa shi ko yana ɗaga musu hannu fuska ɗauke da murmushi har ya shige parlourn, Afnan da ke zaune tana latsa waya ne ta ji an ɗagata sama ana juyi da ita, ƙamshin turarensa ne ya tabbatar mata cewa mijinta ne, Muby da ke kallonta ma be lura da wadda ke zaune a gefe ba, a hankali ya sauke Afnan tare da hugging ɗinta kamar zai maidata jikinsa "Baby i miss u, yau aiki ya yi mana yawa shiyasa ban dawo da sauri ba" Ɗaga masa gira ɗaya ta yi tana mai shagwaɓe fuska "An yi maka afwan mijina sannu da zuwa ya aiki?"

"Aiki Alhamdulillah ya Babyna?" Ya faɗa yana shafa cikinta, rusunawa ya yi sannan ya ɗora kunnensa kan cikin nata "Baby kin ji motsin da Babynmu yake kuwa?" Dariya Afnan ta yi tana janye cikinta, gaba ɗaya ta mance cewar Maimun na gurin, "Baby mu tafi sama yau a matse nake wallahi" Alamu ta yi masa da ya kalli bayansa, shi ko be gane abin da take nufi ba sai da ta ce "Ga baƙuwa fa" Da sauri Muby ya juya yana kallon Maimun da ke zaune ta sunkuyar da kai ƙasa, sai da ya yi mata kallon tsafff kafin ya gane ta, "Uban wa ya kawo ki gidana? gads kuna ina? ku zo ku fitar mun da this idiot humman being a gidana"

"Mijina dan Allah ka barta ba wani abun zata yi mana ba, kawai ta zo ne neman yafiyar mu"

Share hawayen da ya zubo mata Maimun ta yi kafin ta ce "Yarima na san cewa babu wacce kafi tsana a halin yanzu sama da ni, amma da zaka tsaya na sanar da kai abin da ke tafe da ni da duk wani zarginka gareni zai yi sauƙi" Tsagaitawa Maimun ta yi da magana kafin ta kwashe duk abin da ya faru tun daga lokacin da suka fara zuwa gurin boka har auren da Mahaifinta ya yi mata, duk da cewar Muby na cike da tsanarta amma hakan be hana sa jin tausayinta ba.

"Na yafe miki duk abin da ki ka mana, haka ma Baby ta yafe miki muna fatar Allah ya kawo miki sauƙi a gidan aurenki" Kuɗi ya kawo masu yawa ya bata, Afnan kuwa ta yi mata kyautar less da atamfa sai turarukka masu tsadar gaske, sannan ta bata dubu ɗari biyu, cikin tsananin farinci Maimun ta rinƙa godiya har da kukanta, sai da ta ƙara cin abinci kafin ta bar gidan.


A ƙwana a tashi har tsawon wata ɗaya da sati biyu, kullum sai Muby ya sha fama da Afnan a kan ta hana shi haƙƙinsa amma sai ta ce masa har yanzu bata warke ba, cikinta kuwa ya ɗan fara tasawa ga wani kyau da ta ƙara shape ɗinta kuwa ya fito sosai, ba laifi tana zuwa gidansu Muby wani lokacin sai dare idan Muby ya dawo daga Office sai ya ɗaukota su dawo tare, satin da ya wuce ne su Ashwan suka tafi neman auren Muslima, inda aka saka rana wata ɗaya daidai, Easha kuwa next week Friday ne za'a ɗaura aurenta da muradin zuciyarta.

Soyayya kuwa tsakanin Yusuf da Ameera kowa gidan ya sani, Muby kam sai shan ƙamshi yake wai Yusuf zai ja masa raini, ya rasa wadda zai aura sai Ameera, Me martaba kuwa ya ce tana gama School za'a yi auren.

Yanzu Afnan ta daina cin fara kullum Flower take haɗawa ta tsantsara Gurasa wadda ta sha kayan haɗi, kuma sai ta cika attaruhu me yaji sosai, kullum sai Muby ya ɓoye yajin saboda yanda yake ganin ta kular masa.

Yau ma kamar kullum sanye take cikin wando da riga milk colour, wandon iyakar cinya sai ƴar ƙaramar riga daidai ƙugunta, gaba ɗaya ta hargitsa Kichen gurin neman yaji, ga Gurasa a parlour ta gama amma ta nemi yaji sama da ƙasa babu, ana cikin haka Muby ya shigo a gajiye dan tun safe ya bar gidan saboda aikin da ke gabansa, yau kwana uku kenan yana rabawa marayu kayan abinci, ga kuma masallacin da ake ginawa har guda uku cikin wasu ƙauyukan da ke gefensu, islamiyya kuwa har guda biyar aka yi.

Ƙarar da yake ji daga cikin Kichen ɗinne ya tabbatar masa cewar tana ciki, a hankali ya shigo daga yana mai rungumota ta baya "Hi Babe am back" Ɓata fuska Afnan ta yi tana mai matso ƙwalla duk ta gaji da zagaye "Ina yajin da nake cin gurasa na?"

Laƙace mata hanci ya yi yana dariya "Shine ake fushi da ni haka? gaskiya ba zan ba ki yaji ba, kina son Babynmu ya samu matsala ne?"

"Tom ai ni ba zan iya cin Gurasa babu yaji ba, kawai cokali uku zan zuba sai ka ɗauki sauran"
Waro kyawawan idanunsa ya yi yana mai lumshe su a hankali "Wai dama haka ki ke cin yajin ne?"

"Cokali biyar ne kawai nake sakawa, dan ma na ce yau zan saka uku"

"Tom ba zan bayar ba" Ya faɗa yana mai ficewa, bayansa ta bi tana roƙonsa ai kuwa ya haura sama da gudu, itama ta rufa masa baya tana dariya "Mijina dan Allah ka bani ko cokali uku ne"

Zagaye suka fara har Afnan ta gaji duk da cewar ba wani gudun take ba saboda cikin da ke jikinta, tana ganin Muby ya ƙi tsayawa ta koma da baya kamar zata faɗi har da sakin ƙara kamar gaske, tsalle ɗaya Muby ya daka tare da cafkota ta faɗo ƙirjinsa, ajiyar zuciya suka sauke lokaci ɗaya dan hankalinsa ya tashi "Baby are you okay? na ce miki ki rinƙa kula sosai amma ke bakya jin magana ban san meyesa ki ke wasa da cikinnan ba" A ɗan faɗace ya yi maganar, hawayen ƙarya ta ƙaƙalo tana mai bubbuga ƙafa "Dama na sani ka fi son Babyn ko? shikenan ba damuwa"

"Ba haka ba ne gaba ɗayanku ina sonku, amma yana da matuƙar muhimmanci mu kula da abin da ke cikin naki, ni duk ba wannan ba mu tafi daga ciki dan yau ba zan haƙura ba"

Ya faɗa yana ɗagata sama, witsil wutsil ta fara tana faɗin "Gurasa zan ci ni yunwa nake ji, ka mayar da ni parlour"

"Idan na gama ba ki asalin Gurasar sai ki koma parlour, amma yau ba zan haƙura ba gaskiya Babe".

Sai da suka yi wanka tare kafin ya naɗota cikin tawul, kafin su gama shafa mai Muby ya hargitse mata, dan ganin yanda duk wata siffa ta jikinta ta canza, na shanunta sun yi mulmulmul gwanin sha'awa, ai kasa haƙuri ya yi, itama Afnan a matse take magungun da Mommy ta bata duk sun kusa ƙarewa, a kullum sai ta sha kowanne kusan Cup ɗaya, haka zata rinƙa miƙa tamkar zata shiɗe.

Kan bed suka zube cike da kewar juna, wani irin kafurin kiss Afnan ke yi masa wanda ya kusan zauta shi, Muby kam ya daburce sai shagalgalata yake, duk inda ya kai hancinsa ƙamshi ke tashi me daɗin gaske.

Sun kai kusan mintuna talatin suna romancing juna kafin Muby ya yi bismillah cike da ƙwarewa ya shige hanyarsa.




*Mu haɗe a next page*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*

Please Login or Register in order to submit comment