Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da su hukuncin da aka yanke, na auren Yarima da Maimun, wata faɗuwar gaba Gimbiya taji nan take hankalinta ya tashi, a ranta take faɗin wai ni za'a yiwa kishiya, kishiyar ma da ƴar talakawa kuma baiwa a gareni, "Kin yi shuru ke muke sauraro" Me martaba ya faɗa yana kallon Afnan, ɗan kau da kai tayi tana mai ɗaure fuska cike da gadara ta ce "Baffa ni ba zan iya zama da kishiya ba"

"Ai kuwa sai kin zauna, tun da uwar taki ma tana da kishiyar" Hajiya Babba ta faɗa tana gyara zama.

Murmushin takaici Afnan tayi, wanda take jin inda ita ke da damar raba aurenta da Muby da sai ta raba shi, cikin salon da ta saba ta motsa soft lips ɗinta tana faɗin "Da wata kishiyar gara zama babu aure"

A fusace Mama ta ce "Wannan wane irin furuci ne, kuma a gaban manya kike faɗin haka"

"Kinsan cewa ƙiyayya koya ake yi, daga an nuna mana ba'a son mu a lokacin muke fara buga wasar" Afnan ta bata amsa tana yamusta fuska, me martaba ne ya ce "Gimbiya bana son rashin kunya karna sake jin bakinki anan, hukunci ne sun gama yankewa ni kaina bana da damar da zan raba wannan auren"

"Aure kam ba zai rabu ba, tun da yana da damar auren mata har huɗu" Cewar Fulani.

Hajiya Babba kuwa dariya ta yi kafin ta kalli Gimbiya da ke faman cin magani ta ce "Ko Yarima ya fara samun shiga ne? wannan kishin haka gaskiya zan faɗa masa ya gyara sosai tun da har ya iya sace wannan zuciyar taki" Kamar Afnan zata yi kuka ta kalli me martaba da shima murmushin yake ta ce "Baffa kana jin Hajiya ko? gaskiya ta daina ni me zanyi da talaka kuma mummuna"

Taɓe baki Fulani tayi kafin ta ce "Ke Gimbiya ina rabaki da wannan kalaman amma kamar ƙara zugaki ake yi, wallahi ki daina saboda shi arziƙi da talauci duk na Allah ne, imma ba dan kina da son kai ba, ai ba za a kira Yarima talaka ba, mutum da aikinsa kuma Mahaifinsa nada dukiya da mulki" Fulani ta ƙarasa zancen tana girgiza kai, haɗe fuska Afnan tayi kafin ta miƙe tsaye cikin taƙama ta kalli mahaifin nata tana faɗin "Baffa zan iya tafiya"

"Eh a sauka lafiya" Me martaba ya faɗa yana kallon Mama da haushi ya gama rufeta, amma ta ɗayan ɓangaren daɗi ne fal a ranta jin za'a yiwa Gimbiya kishiya.

"Ko kina da magana ne" Cewar me martaba, "Allah ya baka nasara sai dai na ce Allah ya sanya alkhairi ya kuma basu zaman lafiya"

Mama ta faɗa tana sunkuyar da kai kamar wata ta Allah, "Ameen ya Allah bayan haka ki faɗawa Halima ta fito da wanda take so, na bata daga yau zuwa gobe ina son a haɗa auren gaba ɗaya" "Amma me martaba kamar lokaci yayi sauri"

Mama ta faɗa dan bata so haka ba, ta so ace kowa ya watse a barta daga ita sai ƴaƴan nata, tun da ita Gimbiya ba anan zata zauna ba.

"Wannan ai ba shawara ba ce umarni ne"

Cewar me martaba yana miƙewa tsaye cike da ɓacin rai, sosai abin da Mama ke yi masa a gidan ke damunsa, babu damar ya faɗi magana ba tare da ta tanka ba.



.............
Shirye-shirye ya kankama masarautu biyu sun tarwatse da shagali kamar gaba ɗaya duniya ake bikin, musamman masarautar Senegal ta ko'ina ka duba taron mutane ne, biki saura kwana biyu, tarewar Gimbiya Afnan da Yarima Muby ma haka, sosai ake tsuma ta.

Ta masifar yin haske da kyau, har wani ƙyalli take yi, haka ma Halima wadda zata auri wani matashi me suna Muhammad ɗan ƙasar ne suna son junansu, Mahaifinsa na da kuɗi ba laifi, kuma Muhammad akwai kyau ba ko kaɗan ba, yana son Halima shiyasa ana maganar auren iyayensa suka amince aka saka rana, Bilkisu da Hauwa'u kuwa tun biki na saura kwana huɗu suka tare a gidan, gulmace gulmace kam sai dai kar a ƙara, burinsu ɗaya su tarwatse auren Gimbiya da Yarima, ta wani ɓangaren kuma suna nuna cewa sun fi kowa farinciki da hakan, tun da tarewar Gimbiya Afnan ya kusa ta daina fita koda nan da parlour ne, kullum tana ɗakinta cikin tunani kala-kala, ta ɗan rame sai mugun miskilancin da ya ƙaru, magana ma sai kayi mata goma amma amsa ɗaya zaka samu, Eashat da Muslimah kawai ke ganin haƙoranta ko su ma sai ta kama, idan kaga fatar jikinta kamar wata zinariya tsananin kyau da laushi ya gama bayyana, musamman da take samun bacci.

Yau ma kamar kullum suna zaune a ɗakin Gimbiya, Muslima da Eashat na gefe ana chat, sai me gyaran jiki da ke faman haɗa wata dilka, tun da Afnan ta fara jin ƙamshin dilkar take toshe hanci wai wari take, da sallama Mubina ta shigo cike da girmamawa ta gaishesu kafin ta miƙawa Afnan wani flacks da gorar magani, "Meye kuma wannan?" Afnan ta tambaya, da murmushi Mubina ta ce "Fulani ce ta ce na kawo miki, kuma ta ce ki ci duka" Yamutsa fuska ta yi dan gaba ɗaya ciye-ciyennan ya fara isarta, kullum abu ɗaya.

Ɗaga mata hannu tayi alamar ta fice, sannan ta buɗe flacks ɗin, saurin kawar da kai gefe tayi kamar wadda ta ga abun ƙyame, bushewa da dariya Eshat tayi tana faɗin "Malama ki ci wannan haɗin fa, wallahi bama son Maimun ta kwace mana Yarima, kinsan dai yanda take son shi" Dogon tsaki Afnan ta ja har tana rufe ido, a hankali ta ce "Ita namiji ya dama amma ni ko a jikina, su tabbata a ɗaki ɗaya har abada"


Haɗe fuska Muslimah tayi kafin ta ce "Matsala ta da ke kenan baki san arziƙi ba, mijinki ne fa, kuma ko ya kake ƙinsa akwai kishi"

"Dallah Malamai ya isheku can ta matse muku da kishin, baiwar Allah ke nake jira ki fara shafa mun ko zan ci wannan masifar" Ta faɗa tana kallon me gyaran jiki, kafin ta maida kallonta kan kazar da ke cikin flacks wadda ta sha haɗi har wani turiri ke tashi, gyaran jiki aka fara yi mata irin na cikakkun ƴan sarauta, hatta dilkar da ake shafa mata daga ƙasar Indian aka zo da shi, musamman aka aika da saƙon kayan gyaran jiki domin cancaɗe Gimbiya, duk a zaton Fulani da gaske ne Yarima ya kwana da Afnan shiyasa ta zage damtse gurin gyara mata ƙasanta da ko'ina na jikinta, Afnan kuwa haushin wannan gyaran take yi gaba ɗaya an takura mata, idan ma ta so ɓoyewa to sai Fulani ta saka an nemota, babu yanda ta iya dole take zama ayi mata gyaran, duk abin da ake kawo mata ba wani daɗinsa take ji ba, amma fa daga ta gama ci zata fara jin wani sauyi a jikinta har wani zufa take yi, wani lokacin mararta ke ƙullewa ta rinƙa zafi tana hartsinawa, haka zata yini a ɗaki cike da feelings abin na damunta sosai, idan ma ta rasa abin da zata yi baccin dole ne ke ɗaukarta, baza ta tashi ba sai tayi mafarkin da ita kanta mamaki take yi".



............
Su Maimun manya tun ranar da me martaba ya yanke hukunci take cikin gyaran jiki, tsimi iri-iri take sha kamar zata haukata kanta, wani lokacin kamar ta yiwa namiji fyaɗe haka take ji tsabagen jaraba, musamman idan tana kallon hoton Muby nan fa zata fara shafe-shafe a jikinta tana ayyana yanda daren farkonsu zai kasance, gaba ɗaya ta mance cewar kishiya zata shiga, kuma kishiyar ma da Gimbiya, me taƙama da dukiya, kyau, izza, uwa uba muki, amma duk da haka Maimun bata shakkun abin da zai biyo baya, tun da dama ba son juna su ke ba, shiyasa ma take ganin Muby ya riga ya zama mallakinta.



Wani garin maganin matsi ta ɗauka a gefen mirrow, tare da zuba shi cikin wani kaskon wuta, rumfa ta yiwa kanta da shi yanda matsin zai shigeta sosai, ta jima a haka kafin ta miƙe tana wani irin miƙa kamar zata afkawa babu, ƙarar wayarta yasa ta matsa da sauri tana dubawa, Sister in-law ya bayyana kan fuskar wayar, da sauri ta ɗaga tana faɗin "Shegiya amaryar zamani" Daga can ɓangaren Munirat ta karɓe zancen da faɗin "Ai wallahi nayi fushi da ke, ashe Brother za ki aura bana da labari?" Dariya Maimun ta fashe da shi cikin tsananin farinciki ta ce "Baza ki gane ba, wannan labari ne me tsayi, kuma auren ya zo a ƙaddara, amma na san za ki shigo aurena ko?" Tsaki Munirat ta ja tana faɗin "Bakida hankali aure ko wata ban yi ba zan dawo gida, kawai ina yi muku fatan alkhairi, amma kina da aiki wallahi dan Gimbiya ba kanwar lasa ba ce, ya kamata ki sha maganin kyau saboda kinsan mijin sarauniyar kyau ta duniya za ki aura"

Cewar Munirat tana dariya.

Haushi ne ya kama Maimun nan take gabanta ya faɗi, ita kam kyawun Gimbiya na ɗaga mata hankali, cike da haushin maganar Maimun ta ce "Koma dai menene ai basa son junansu, na tabbata kwanaki kaɗan zan raba aurennan"

"Babu ruwana bada ni ba a wannan zancen"
Munirat ta ƙarasa maganar tana kashe waya, jifa da wayar Maimun ta yi tare da faɗawa kan bed, a rayuwarta babu abin da ke ɗaga mata hankali irin tsananin kyawun da Gimbiya Afnan take da, musamman idan ta yi wankan abaya, kamar wata aljana haka take fitowa tsabagen kyau.

Ganin hakan ba zai fishsheta ba ne yasa ta ɗaukar waya da sauri ta danna wata number, bugu ɗaya aka ɗaga, cikin damuwa Maimun ta ce "Hajara kina gida yanzu haka?" Wadda aka kira da Hajara ce ta ce "Amaryar Yarima me taƙama da mulki" A ƙufule Maimun ta ce "Dan Allah ki amsa min ina son na sameki a gidan ne"

"Yes ina gida, kin ci sa'a yanzun na dawo"

"Okay ki jirani ina kan hanya" Bata jira amsar da zata bata ba ta yanke waya, cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya tare da fitowa babban parlourn gidan, anan ta sami Mahaifiyarta zaune ita da wani ƙaramin yaro ɗan shekara sha biyar, daga gani ƙanin Mainun ɗin ne "Ina zuwa haka?" Mahaifiyarta ta tambaya, fuska a haɗe dan ta san halin Maimun da mugun baƙin yawo.

Kame-kame ta fara kafin ta ce "Gidansu Hajara, ba zan jima ba zan dawo"

"Ki yiwa kanki faɗa Maimun, wallahi aure za ki yi kuma kinsan gidan da za ki shiga, Allah ya kai lafiya saura idan kin tafi karki dawo"

"Kina ganin idanunta haka na san ba'a can kaɗai zata tsaya ba" Cewar yaron me suna Faruk.

Maimun da a halin yanzu bata buƙatar abin da zai hanata fita ne yasa ta, cije yatsa tana watsa masa harara "Zan dawo na sameka sai ka san da ni kake yi" Ta faɗa tana ficewa daga gidan.



Tun da ta isa gidansu Hajara ko zama basu yi ba, haka aka garzaya gurin wani Malamin Maimun wanda duk saurayin da ta gani kuma ta ji tana so nan take ake asirce shi, haka suka rinƙa ƙutsa daji kala-kala har suka shiga wani babban dajin da babu komi a ciki sai duhuwa da mugayen kukan tsuntsaye, har suka kawo gurin wata bukka me tarin kayan tarkace, tun daga nesa aka daka musu tsawa har sai da suka fara neman hanyar gudu "Ba,a shiga da takalma ku yaye mayafinku" Cikin murya me ban tsoro wani tsoho ke magana, kana ganinsa ka san ya tsufa sosai ga tarin gemu da ya cika da furfura, jikinsu na rawa suka cire takalma da mayafi, "Ta gefe-gefe zaku shigo" Tsohon ya ƙara daka musu tsawa, haka suka ƙaraso gurin jikinsu na karkarwa.

Zaunawa suka yi a can nesa da inda Bokon ke zaune, har Maimun ta buɗe baki da niyar magana ya ɗaga mata hannu.


Sai da ya gama bincikensa kafin ya ɗago jajayen idanunsa masu ban tsoro ya ce "Na san abin da ke tafe da ku, aurenki saura kwana biyu kacal, kina buƙatar a raba auren Gimbiya da Yarima saboda ya zamo mallakinki ke ɗaya ko ba haka ba?"

Bakin Maimun na rawa ta amsa da "Eh hakane"

Wata iriyar dariya ya kwashe da ida kafin ya ce "Auren Yarima da Gimbiya ba zai taɓa rabuwa ba, amma zamu iya dasa ƙiyayya tsakaninsu har ƙarshen rayuwarsu, idan kin amince ki aje mana tukyuici mu kuma mu fara aiki"


"Eh na amince dama bana buƙatar ganinsu a tare, idan son samu ne a raba musu ƙasa baki ɗaya"

Cike da mugunta Maimun ta ƙarasa zancen.

A tsawace Bokon ya kallate yana faɗin "Na faɗa miki cewa baza a iya raba su ba, ita ce ƙaddararsa ƙiyayya kawai ce marabarsu, dan haka ki aje mana abin buƙata sannan ku ɓace mana da gani, babu wani aikin da za ki yi, wannan aikin namu ne........."

Ya faɗa yana fashewa da dariya.

Da sauri ta buɗe jakar tare da ciro kuɗaɗe masu yawa ta aje, yana mai ci gaba da dariya ye ce "Ku tashi ku tafi aiki ya kammalu"

Kamar jira suke su ka miƙe tare da barin jejin, sai da suka yi tafiya me nisa kafin suka iso inda suka bar mota.


Suna cikin tafiya ne Hajara ta ce "Yanzu kina ganin wannan shine mafita?"

"Ƙwarai ma kuwa sauran aikin ya rage nawa, ba zan taɓa haƙuri ba har sai na raba wannan auren" Dariya suka fashe da ita har suna tafawa.



...................
A yau ta kama ranar ɗaurin aure, babu inda zaka juya ba tare da kaga jama'a ba ta kowanne saƙo, bayan an sauko juma'a aka ɗaura auren Yarima da matarsa Maimun, a ɓangaren Gimbiya kuwa auren Halima da mijinta Muhammad, kamar yau ne aka ɗaura auren Gimbiya tun da taji labarin anjima za'a tafi da ita ta shige ɗaki tare da rufe kanta, kukan ma kasa zuwa yayi.

Ƙafarta da hannu ta sha lalle ja da baƙi yayi masifar kyau, musamman da take farar mace, gashin kanta kuwa sai walwali yake, ta ko'ina jikinta ƙamshin turare ke tashi, idan zata gifta ta hawa na farko ba shakka sai ka ji ƙamshin turarenta a hawa na huɗu, kayan jikinta kuwa Allah yasa wankewa aka yi so uku ƙamshin na nan ba zai fita ba, Husna da ke ɗakin Fulani tana matsar kwalla saboda kewar ƴar'uwar tata ne ta kalli Halima da ke gefe itama ta sha lalle hannu da ƙafa kusan iri ɗaya da Gimbiya, "Aunty Halima yanzu shikenan zaku bar ni, wallahi har na fara kewarku musamman Gimbiya" Taɓe baki Halima tayi kafin ta ce "Ki bari idan kin ƙara girma Ameer ya turo mu sha biki" Rufe fuska Husna tayi alamun kunya, "Nifa ba soyayya nake da Ameer ba"

"Mun ji amma bamu yarda ba" Cewar Fulani lokacin da ta shigo ɗakin.


Kallon Halima tayi cikin sanyin jiki ta cigaba da faɗin "Za'a wuce da Gimbiya yanzu, kema masu tafiya da ke sun ƙaraso" Kamar jira Husna take Fulani ta gama magana ta fashe da kuka tare da ficewa daga ɗakin, dan tabbas sai a yanzu ta san zata yi kewar su.


Gaba ɗaya gidan ya hartsine da hayaniya, tun da aka fito da Gimbiya mutane ke basu hanya dan za'a shiga da ita part ɗin Sarki Shuraihu, wata irin arniyar atamfa ta saka doguwar riga ta bi jikinta sosai, ga uban hips ɗinta da ya gama bajewa, alkyabbar jikinta har ƙasa me adon duwatsu, fuskarnan babu kwalliya dan ta hana ayi mata, sai lokacin da aka fara yi mata nasiha ta samu damar yin hawaye, a ranta ta ƙudurta irin zaman da zata yi da Muby, tun da har yayi sanadiyar rabota da iyayenta.



Fulani kam kasa magana tayi, hawayen ma sai bayan an wuce da Afnan ta samu ya zubo mata, Husna kam tun da ta shige ɗaki take rusar kuka, gashi me martaba ya ce baza ta bi su ba, tare da Mubina kaɗai aka tafi saboda ta rinƙa kula da Afnan, dama tun a gida ita ce me kula da ita, Hajiya Babba ce ta hana kowa ya tafi, ta ce su bari daga baya idan ma ganin gidan zasu tafi sai su je.

Ƙarfe biyar na yamma tayi musu a Sudan, motocin gidansu Muby ne suka zo airport ɗin ɗaukarta guda ɗari, saboda daga nan za'a wuce sabon gidan da ya gina, wannan hukuncin daga Alhaji ne, shiyasa ma aka fara wucewa da Maimun, tun daga bakin gate mutane ke yabon gidan har suka shiga daga ciki, hawa huɗu ne me ji da lafiya, harabar gidan kawai ya isheka kallo balle kuma ka shiga ainihin taskar gidan, ta ko'ina tambarin sarauta ne tare da flowers, gida ne wanda ya amsa sunansa gida, pearking space kuwa motoci sun fi ɗari, ga kuma waɗanda ke waje, girman gidan ya wuce a kira shi da babbar unguwa ɗaya, dan faɗin gidan ya wuce misali, babu wada ya zo gidan ba tare da yayi maganar kyawunsa ba, hawa biyu a gefe ɗaya, hawa biyu a ɗayan gefen, na gafen hagun ne aka aje Maimun sai ɗayan wanda yake farkon shiga aka nufa da Afnan, tun daga farkon shiga haɗaɗɗen parlourn aka shimfiɗa red carpert, cikin tafiyar ƙasaita take takawa tare da yiwa gidan kallon banza, har suka ƙusa kai cikin rikitaccen parlourn da ya gama haɗuwa, Mubina da ke gefe ne ta matso kusa da Afnan a hankali ta ce "Gimbiya duk wannan kayan ɗakin me martaba ne yayi su, jiya da na tafi kai masa kunun aya naji yana bada umarnin a shigo da kayan anan ƙasar wai baya son ko cokali daga gefen ango" Murmushin yaƙe Afnan tayi wanda ya fi kuka ciyo kafin ta ce "Na sani dama Baffa ba zai taɓa bari naji kunya ba" Babban parlourn take ƙarewa kallo wanda ke ɗauke da set ɗin kujeru biyu masu masifar kyau, sai makeken Tv wanda ya baje kan bangon ɗakin, akwai ɗakuna biyu a parlourn wanda anyi su ne dan zuwan baƙi, a gefe kuwa Show glass ne cike da turarukkan ɗaki iri-iri, ta ɗayan ɓangaren an jibge haɗaɗɗen Fridge me girma, sai table a tsakiyar ɗakin kan sofa na gold, yana ɗauke ta kayan itatuwa kamar su tufa, lemu, da sauransu.

"Wow gaskiya na yaba da kayannan" Mubina ta faɗa tana kallon wani kilishi irin na ƴaƴan sarauta ya masifar yin kyau, a gefensa dianing ne irin na cikakkun sarakuna masu ji da mulki, kallon hoton Gimbiya da ke gefe ta yi wanda take sanye cikin alkyabba fuskarta ɗauke da murmushi, hawayen da ya zuba mata ta share tana mai ƙarasawa kusa da hoton tare da shafawa a hankali ta ce "Ranar da muka tafi wasar doki a ƙasar Chad" Murmushi Mubina tayi tana mai cewa "Ai ranar kowa yayi farinciki da gasar saboda kin baza baiwa, yanzu ki shiga daga ciki ko za ki huta"

Ɗaga kai Afnan tayi ba tare da ta ce komai ba, sannu a hankali ta fara taka steps ɗin wanda ya sha kyawawan flowers masu ƙamshi har ta isa sama, room uku ne a saman masu muminan kyau, ba tare da sanin nata ɗakin ba ta shiga na farkon, cakkk ta tsaya ganin yanda ɗakin ya tafi da imaninta, sosai taji daɗin ganin haɗuwar da ɗakin yayi, bed ɗaya ne me girman gaske, a ɗayan ɓangare kuwa wadrop ne wanda ke manne a bangon ɗakin, zaka yi tsammin gina shi aka yi, jikinsa duk mirrow ne sai gurin da ake aje takalma wanda shima a jikin bangon yake, kujera ɗaya ce me kama da bed me zaman mutun uku, irin ta sarauta, gefen bed ɗin ta zauna wanda ya sha zanin gado me tambarin sarauta fari tassss, gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, kar dai ace wannan al'adar zasu dawo da ita, idan hakane kuwa akwai matsala, ta faɗa aranta.


Dama a tsarin masarautar duk aka yi aure sai an kawo zanin gadon da aka kwanta, saboda ganin wacce irin mace aka auro.

Tashi tayi a hankali ta isa gaban wakeken mirrown da ke manne gefen bed, sannu a hankali ta fara cire kayan jikinta, ya rage daga ita sai pant da bra, wadrop ɗin da ke gefe ta buɗe, ai kuwa taga kayanta a ciki hamdala ta yi tana mai janyo wani farin tawul me laushi ta ɗaura, sannu a hankali ta cire bra tare da lunke kayan ta saka cikin wani ɗan ƙaramin basket me kyau, jin ana norcking ƙofar ne yasa ta tashi da sauri ta nemi ƙoton hijab ta saka, sai da ta daidaita natsuwarwa kafin ta haɗe fuska cikin taƙama ta ce "Shigo daga ciki" Mubina ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, "Gimbiya ƙawayen Aunty Maimun ne ke buƙatar ganinki wai za su tafi"

A tsawace Afnan ta ce "Ni uwarsu ce? da har idan basu ganni ba zasu lalace, ki ce musu banada lokaci"

Cikin girmamawa Mubina ta amsa tana fita daga ɗakin, a down steps ta same su kowaccen cikin shigar da take ganin ta burge, su uku ne duk jikinsu ya lalace da shafa mai, sai kallon parlourn su ke dan ko kaɗan Maimun baza ta haɗa kyawun nata parlourn da wannan ba, hoton Gimbiya Afnan suka zubawa ido ganin masifar kyawunta dama basu taɓa ganinta, cikin ƙawayen harda Hajara wadda ta raka Maimun gurin boka, murmushi Mubina tayi kafin ta ce "Gimbiya ta ce baza ku samu ganinta ba" Waro ido suka yi jin zancen da ake yi musu, taɓe baki Hajara ta yi kafin ta ce "Kamar wata zinariya, me zai hanata fitowa"

Cikin tsoro Mubina ta ce "Please bana son tashin hankali tun da ta ce baza ta samu fitowa ba sai ku ƙara gaba, idan ba hukunci kuke son samu ba" Ba dan suna so ba haka su ka bar gidan, cike da takaicin cin fuskar da Afnan tayi musu.


Misalin ƙarfe tara na dare kuwa Mommy da Alhaji gami da Ameera ne suka zo gidan, part ɗin Gimbiya suka sauka, sannan Alhaji yasa aka kira Maimun wadda taci uwar kwalliya kamar me shirin zuwa party, sai wani karairaya take kamar wata ƴar hau, bata jima da shigowa ba Muby ya shigo gidan, dama Mommy ta sanar da shi sun iso, sanye yake cikin shadda fara bugagga tare da babbar riga, ƙamshin turarensa ya gama haɗe harabar gidan, hular kansa ɗauke take da tambarin sarauta, sai wani baƙin glass da ya kafa, fuskarsa ɗaure kamar wanda aka yiwa mutuwa, haka kawai ya tsinci kansa cikin mugun ɓacin rai.



A bayansa Ashwan da Yusuf ne sai tsiya suke yi masa, kallonsu yayi cikin haɗe fuska ya ce "Bana son rakiyar kawai ku tafi"

"Calm down me yayi zafi kuma?" Cewar Ashwan yana murmushi, "No kawai ku koma tun da su Alhaji na ciki"

"Shikenan dama dare yayi ai, mu kwana lafiya amma please a bi mana Gimbiya a hankali" Yusuf ya faɗa yana barin gurin dan ya san abin da zai biyo baya, shima Ashwan ɗin bayansa ya bi yana dariya.


Suna fita gate Man ya rufe ƙofar, shi kuma Muby ya ƙusa kai ciki.


A zaune ya same su ana jiran Gimbiya tun ɗazu, da sallama ya shiga yana mai zama kusa da Alhaji cikin raha ya ce "Tsoho me abin mamaki"

Duka Alhaji ya kai masa yana faɗin "Kaji ɗan nema, tashi ka kira mana Gimbiyarka tun ɗazu ita ake jira" Wani ƙololon baƙinciki ne ya dirar masa a ƙahon zuci, wai Gimbiyarsa Maimun kuwa kawar da kai tayi tana jan tsaki a zuciya.


Sai a lokacin Muby ya lura da Maimun ɗin da sai wani fari take masa da ido, jin takun saukowa ne yasa kowa maida hankalinsa kan steps ɗin, wani ƙamshi ne ya fara bazuwa har ya gama haɗe parlourn, kishi ne ya kama Maimun dan sosai ƙamshin yayi daɗi, tana sanye cikin hijab har ƙasa sai wayarta da ke kunne alamun kira take amsawa, wani irin faɗuwa gaban Muby da Maimu yayi gani wani irin muminin kyau da Afnan ɗin tayi har wani sheƙi fuskarta ke yi.



A hankali ta samu ɗaya daga cikin kujerun ta zauna me zaman mutum ɗaya tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta jima sosai tana waya da Husna kafin suka yi sallama, cikin taƙama da gadara ta kalli su Mommy tana gaishe su, cike da fara'a su ka amsa musamman Mommy wadda take jin Gimbiya a ranta sosai, ganin

Please Login or Register in order to submit comment