Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon nata yayi, a hankali ta ce "Brother barka da wannan lokacin"

"Wa ya baki izinin zuwa da tarin motoci school? nan fa ba ƙasarku ba ce bana son hauka"

Jin tayi masa banza ne yasa ya ɗago manyan idanunsa yana watsa mata harara "Magana nake kin yi min banza"

"Brother dan Allah ka barta yau azumi take" Cewar Muhseen da isowarsa gurin kenan.

Afnan na ganin haka ta bar gurin cike da jin haushinsa.

Kallonsa Alhassan ya mayar kan Muhseen, yana sakin murmushi, tafawa suka yi cikin so da ƙaunar juna, a babban parlourn suka sami Afnan da Hajjo suna fira, amma duk firar Hajjo ce dan Afnan ba kome take amsawa ba, tana ganin sun shigo ta miƙe tare da haurawa sama.

Da kallo su duka suka bita har ta ɓacewa ganinsu, sosai Hajjo abin ya taɓa mata zuciya "Alhassan ku ƙaraso ina son magana da ku" Hajjo ta faɗa cikin kawar da damuwar da ke kan fuskarta.

Kusa da ita suka zauna suna mai jiran abin da zata ce, shuru ta yi na ɗan wani lokaci kafin hawayen da take riƙewa suka zubo kan fuskarta, har rige-rige goge mata suke yi cikin tashin hankali dan basu taɓa ganin kukanta ba, hannunsa ta kama tana sakin murmushi cike da fargaba ta ce "Gimbiya ƴar'uwarku ce ta jini, ina son ku cire duk wata tsangwama da ku ke mata saboda baza ku canza abin da Allah ya tsara ba......" Gummmm...., suka yi cike da ruɗu gami da mamaki, har haɗa baki suke gurin faɗin "Ƴar'uwarmu?" Ɗaga musu kai Hajjo ta yi tana murmushin yaƙe, kafin ta cigaba da faɗin "Tabbas abin da nake faɗa muku gaskiya ne, ku ƴan'uwa ne amma ina son ku ɓoye wannan sirrin ba tare da wani ya sani ba har ita Gimbiya, saboda abin da zai je ya dawo"

"Menene za'a ɓoye min?" Suka tsinkayo muryar Afnan da ke saukowa kan steps cike da gadara ta ƙaraso tana mai zama kujerar da ke gefensu.

Wani banzan kallo Ahassan ya watsa mata wanda yasa ta ɓata fuska tare da kawar da kai, sannan ya ce "Hajjo kiyi haƙuri amma wannan ba zancen a bar maganar, dan Allah ki fitar da mu duhu" "Eh Hajjo please muna son sanin yanda Sister ta zama Ƴar'uwarmu" Muhseen ya faɗa.

Wani irin mugun kallo Afnan ta watsa musu gaba ɗayansu cike da mugun jin haushi ta ce "Ƴan'uwana kuma how, wai meyesa baza ku barni na huta ba ne? a kullum kuna ƙoƙari laƙamin waɗannan talakawan, gaskiya na fara gaji dole zan bar ƙasar nan haba dan Allah" Wani irin haushinsu ne ke ƙara shiga zuciyarta.

Har Alhassan zai yi magana sai kuma ya fasa ganin Hajjo ta girgiza masa kai, "Gimbiya a matsayinki na mace kuma wadda har ta kai minzalin aure be dace kina nuna tsanar mutane a fili ba, tun da muke da Mahaifiyarki bata taɓa nuna tsana ko ƙyama ga bayin gidannan ba, a kwano ɗaya ma cin abinci take yi da su, dan Allah ina son ki daina wannan halin naki, kar ki mance fa yanzu a ƙarƙashin wani ki ke, kina da aure fa ina son a kullum ki kasance me haƙuri kuma da nuna ƙauna ga na ƙasa da ke" Cikin sanyin murya Hajjo ta ƙarasa maganar, shuru Afnan ta yi tare da sunkuyar da kai, kallonsu Muhseen Hajjo ta yi "Ku tashi ku tafi insha Allah zan yi magana da Mahaifinku dan ina son mu tafi ƙasar Senegal domin wannan maganar bata iya nan ba ne"

"Meyesa har sai mun tafi ƙasar Senegal kuma?" Cewar Muhseen.

Murmushi Hajjo ta saki kafin ta ce "Saboda maganar ba ƙarama ba ce amma ina son ku ƙara haƙuri, kuma ku ɗauki Gimbiya tamkar ciki ɗaya ku ka fito kafin lokacin da za su samu huta a makaranta mu tafi ƙasar gaba ɗaya"

"Insa Allah zamu kasance masu bin umarninki Hajjo" Alhassan ya faɗa yana barin gurin cike da tafiyar ƙasaita, shima Munseen ɗin bayansa ya bi.


Washe garin ranar misalin ƙarfe shida na yamma, gate man ya nufo babban parlourn masarautar, anan su ka ci karo da Jakadiya ɗauke da Basket ɗin abinci a hannu, gaisawa suka yi sannan ya shaida mata ta faɗawa Gimbiya Afnan ana yi mata sallama a waje, waro ido Jakadiya ta yi cike da tsoro ta ce "Rufa min asiri idan ba so ka ke a kulleni a yau ba, wannan me taƙamar tsiya r zan kira?"

"Haba Jakadiya dan Allah ki daure ki kira ta mutumin yana waje yana jira" Cewar gate man yana barin gurin.

Sai da ta kai abincin sannan ta nufi room ɗin Afnan, a bakin ƙofa ta samu kuyanginta har da Mubina a tsaye suna fira, cikin girmamawa suka gaisa kafin Jakadiya ta bawa Mubina saƙon da gate man ya bata, shuru na ɗan wani lokaci Mubina ta yi "Waye wannan ke neman Gimbiya, ko Yarima ne? okay bari na kira ta" Ɗakin Mubina ta yi nocking kusan mintuna uku kafin aka bata izinin shiga, sallama ɗauke a bakinta ta shiga har ƙasa ta rusuna "Allah ya ba ki nasara ana nenamanki a waje"

Kwanciyarta ta gyara na minti ɗaya cike da miskilanci ta ce "Waye da ba zai iya shigowa ba?"

"Allah ya ba ki nasara nima saƙon daga Jakadiya ne itama gate man ne ya faɗa mata cewar ana nemanki"

"Ko waye ma a ce masa bazan zo ba" Ficewa daga ɗakin Mubina tayi cikin girmamawa, mintuna biyar tsakani, Alhassan ya nufo ɗakin a bakin ƙofa Mubina ta hana shi shiga, wani mugun kallo ya watsa mata wanda yasa ta jaye gefe bata san lokaci ba, a fusace ya tura ƙofar, kwance take kamar yanda Mubina ta barta, ganin Alhassan saman kanta ne yasa ta tashi a firgice, "Ke ba ki ga saƙon ana nemanki ba ne?" Cije lips ta yi da ƙarfi ba tare da ta amsa masa ba.

"Ba magana nake miki ba?" Ya daka mata tsawa, "Na gani" Ta bashi amsa a ƙufule.

"Ki tashi ki same shi a gadin, Hajjo ta ce maybe Yarima ne, minti ɗaya na ba ki idan ba haka ba wallahi baza ki ji da daɗi ba" Ficewa yayi daga ɗakin yana mai rufo ƙofar.

Haushi da takaici ne ya gama mamaye zuciyarta, hijab ɗin da ke kan sallaya ta zura tare da feshe jikinta da mayataccen turarenta me ratsa zuciya, ita mamakin wanda ke nemanta take dan ta san Yarima dai ba zai zo Chad ba, tun da ta fara saukowa kan steps ɗin Hajjo ke murmushi har fa ƙaraso, cikin tura baki ta nufi hanyar fita daga parlourn ba tade da ta ce musu uffan ba, itama Hajjo ido ta zuba mata dan ta san halin Afnan sarai.

Ganin haka yasa Mubina bin bayanta tare sa sauran Kuyangin.

Daga can nesa take hangensa, sanye cikin ƙananan kaya gashin kansa ya kwanta gwanin sha'awa, yanayinsa ya nuna ba Yarima ba ne saboda shi wannan ba fari ba ne, chocolate colour ne kuma ba wani jiki ne da shi ba, sai dai ba'a iya ganin fuskarsa dan ya juya baya.

Har zata koma sai kuma ta fasa dan tana son ganin ko waye haka har ya san gidan da take.

Cike da gadara ta ƙaraso gurin, ba ƙaramin kyau da haɗuwa wurin yayi ba, ta ko'ina flowers ne masu kyau red colour, fararen kujeru na baje a gurin kowanne kujera da ɗan ƙaramin table ɗinsa na gold, sai kukan fsuntsayen da ke cikin wani babban keji me kyau da tsari, ta gefe ɗaya ko wani ɗan ƙaramin keji ne wanda Aku me magana ke ciki, ita da mijinta.

Shi ko Guy ɗin yana zaune ne saman ɗaya daga cikin kujerun da ke gurin an zube masa kayan motsa baki amma ko taɓawa be yi ba, ƙamshin turarenta ne yasa shi saurin ɗago haɗaɗɗun idanunsa masu masifar kyau ya sauke kanta.


ƘASAR SUDAN
....................

Tun da labari ya sami Alhaji kan tafiyar Afnan Chad ne ransa ya ɓaci, sosai ya kira Sarki Shuraihu ta waya tare da yi masa faɗa kan yardar da yayi Afnan ta bar ƙasar Senegal da aure a kanta, shi ko Sarki Shuraihu haƙuri ya rinƙa bashi sannan ya shaida masa zata dawo insha Allah, haka dai su ka yi sallama ran kowa babu daɗi.

Mommy kam ta dage kan Afnan baza ta dawo gidan yaronta ba, a palourn Alhaji ta same shi zaune kan kilishi yana kallon labaran duniya kan mamaken Tv da ke manne a bangon, da sallama ta shigo tare da samun guri ta zauna, murmushi Alhaji ya saki yana faɗin "Yau kuma ziyara aka kawo min har part ɗina" Itama Mommy murmushin ta yi "Allah ya ja zamaninka barka da wannan lokacin?"

"Barka ya ki ke ya zaman kaɗaici" Haɗe fuska Mommy ta yi jin abin da Alhaji ya ce dan ta san rashin Afnan yake nufi.

Murmushi ya saki yi a karo na biyu "To ina jinki na san cewa akwai magana dan baza ki zo kai tsaye ba" Tattara natsuwarta tayi gami da ɓoye ɓacin ranta ta ce "Allah ya ba ka nasara dama maganar Gimbiya ne"

"Ina sauraronki"

"Dama cewa nayi me zai hana a raba aurennan dan gaskiya zama haka ba zai yi ba, yanzu wannan yarinyar har zata bar ƙasar iyayenta da sunan makaranta kuma da aure a kanta, nikam ba zan lamunce ba" Mommy ta ƙarasa maganar kanta a ƙasa.

Gyara zama Alhaji ya yi cike da nazari ya ce "Hakane ɗazu ma nayi waya da shi Mahaifin nata kuma da yardar Allah zata dawo, ni da kaina ma zan dawo da ita ɗakin mijinta" Ɗago kai Mommy ta yi a ruɗe, "Allah ya ja zamaninka na yi tsammanin raba auren zaka yi amma kuma kana faɗin dawowa da ita"

"Yanzu a tunaninki raba auren shine zai kawo zaman lafiya? babu wani abin da zai haddasa face tashin hankali, ki tashi ki tafi zamu yi magana da Ahmad anjima" Miƙewa Mommy tayi ba dan tana so ba "Shikenan Allah ya ƙara nisan kwana"

Ficewa daga ɗakin ta yi cike da jin haushi.



A ɓangaren Maimun kuwa tana ganin Muby ya faɗo ɗakin ta tashi daga kwancen da take a ruɗe, wata ƙara ta saki jin wani zugi ya shigeta, harara ya galla mata cike da takaici ya ce "Yau kuma tsoro na ki ke ji? ai haƙƙinki zan ƙara ba ki wanda ki ke roƙona a kullum" Ya ƙarasa maganar yana dannawa ƙofar key.

Jin abin da ya ce ne yasa Maimun fashewa da kuka tare da durƙusawa ƙasa "Dan yarasulillahi ka yi haƙuri, wallahi ba zan ƙara ko kallonka ba idan ka yarda, please kar ka kasheni gidammu ma zan tafi" Ta faɗa a ruɗe.

Be bi ta kanta ba ya matso tare da tallofa, ganin da gaske yake ne yasa Maimun ƙara rushewa da wani kukan tana dukansa, ba ƙaramar wahala ya bata ba wannan karon, dan har numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa, sai wajen sha ɗaya ya saurara mata lokacin ko yatsarta bata iya ɗagawa, idanunta sun gama rinewa, ya jima sosai a kwancen kafin ya fice daga ɗakin, anan kwance ya barta tana haɗa gumi, da ƙyar ta iya taka ƙafarta, ƙofor ta sakawa key tare da barin key ɗin a jikin ƙofar sannan ta shige banɗaki.


Muby kam wani daɗi ne ke ratsa shi, wanka ya shige kusan mintuna talatin ya fito, haɗaɗɗen gashin kansa yake gogewa yana mai zama kan table ɗin da ke gaban mirrow, ya jima sosai yana shiri dan yana son zuwa Cameroun yau, wata arniyar shadda ya saka kalar sararin samaniya me laushi, ƙamshi ta ko'ina sai tashi yake ga wani kyau da ya ƙara, daga ƙasa yake jiyo hayaniya kamar faɗa ake, alkyabbarsa ya kafa saman kayan tare da ɗora hula, cike da mulki yake taka ƙasa, a parlourn ya sami Fadila tare da Kuyanginta, zaune take kan kujera me zaman mutum ɗaya, waya ce kan kunnenta da alama da Mahaifinta take waya, ƙamshin turernsa ne yasa ta ɗago da sauri tana mai ƙatse wayar.

A hankali ta tashi tana mai sakin murmushi "Hi Dear this surprised is for u, na yi kewarka sosai" Wani farinciki ne ya mamaye zuciyarsa amma sai ya haɗe fuska tunawarda yayi a ranar yana ta magana ta sheresa, Kunyanginta kuwa gaidashi su ka yi tare da ficewa, kan kujera ya zauna yana ƙare mata kallo ganin yanda ta haɗe cikin doguwar riga me adon duwatsuna masu kyau, kwalliyar da aka yi mata ta ƙarama adon nata fitowa, kan cinyarsa ta zauna tana mai saƙala hannayenta ta wuyansa.

"Please Dear ka yi magana"

"Me ki ke so na ce" Muby ya tambaya yana ƙara haɗe fuska, kwanciya tayi kan ƙirjinsa a hankali ta ce "Sorry na ce bazan ƙara ba" Hannunta ya kama tare da sakin murmushi "Dan kin ga ina sonki ne? ki ke mun haka yanzu na daina sonki" "Shhhhhhh....." Ta rufe masa baki da yatsarta "No kar ka ce haka, ba zan ƙara ba ka ji"

Jin saukowar mutum ne yasa Fadila ɗago kanta, Maimun ce sanye cikin wata ƙatuwar riga tafiya ma a wawware take yi, da ƙyar take taka ƙasa, tsabagen wahala ma bata lura da waɗan da ke parlourn ba ta nufi kichen ɗin, a table ta sami abincinta an gama haɗawa, ba ƙaramar yunwa dama take ji ba, nan ƙasa ta baje ta fara ɗibar girki sai da taji ta yi dammm, ta saki wata irin gyasa, a nan ta bar kwanonin ta fito, sai a lokacin take ganin abin da ke faruwa, Fadila kan cinyar mijinta shi ko be damu ba sai wani shafa masa saje take.

"Baby......" Maimun ta ƙwala masa kira, a fusace Fadila ta ɗago tana watsa mata harara, "Are you okay? ba ki ganin ina fira da shi ne da har za ki kawo mana ƙazamin jikinki a nan" Muƙusss Maimun ta yi tana zare ido, Fadila kuwa maida kallonta kan Muby tayi "Dear wai me nake shirin gani ne? kamar tafiyar wannan makirar ya canza"

Maimun na jin haka ta ƙara narke fuska tana ɗan duƙar da jiki ita ala dole an kashe arna, lumshe idanunsa yayi kafin ya ɗaga ta daga jikinsa "Is not what you think, kawai bata jin daɗi ne mu shiga daga ciki na san kin gaji sosai" Da mugun kallo Maimun ta bi bayansu har suka haura sama, wani ƙololon baƙin ciki ne ya ƙara dirar mata, yanzu wannan cin zarafin da me yayi kama, bayansu ta bi da sauri tana kiran sunansa, babu ko sallama ta faɗa ɗakin kwance ta same shi yana danna wayarsa sai Fadila da ta yi matashi da bayansa itama wayar take latsawa, "Baby wannan rashin dacewa ne, ni da nake matarka ma ban samu wannan kulawar ba, kawai kayi abin da zaka yi dani ka watsar" Zaro ido Fadila ta yi cike da mamaki ta kalli Muby "Kana nufin ka kwana da ita?" Shuru ya yi mata ba tare daya kallesu ba, rai ɓace ta miƙe daga kwacen da take ta fice daga ɗakin, da sauri yabi bayanta Maimun kam kamar ta rusa ihu ganin yanda suka maidata mahaukaciya.


A harabar gidan ya sameta tana ƙoƙarin barin gidan, "Fadila wait please, kinsan bana son taurin kai ko" Cakkk ta tsaya dan ta san halinsa, "Mu shiga motana ina son mu tafi masarauta ne" Ba dan ranta na so ba haka ta nufi motar da taga ya shiga.

A fadar gidan suka hallara har da Alhaji, Ameer kam sai hararar Fadila yake, tun da Alhaji ya fara magana kowa ke sauraronsa, kallonsa ya mayar kan Muby fuskarsa babu alamar wasa ya ce "Anjima da yamma ka shirya zamu tafi ƙasar Chad a tare, bana son jin wani ƙorafi idan har kana son auren Fadila to sai Gimbiya ta amince ta dawo ɗakinka"

Ɗago kai Muby yayi a hankali ya ce "Allah ya kaimu anjima" Ganin kallon da Mommy ta yi masa ne yasa shi sunkuyar da kai ƙasa.

"A gaskiya ba zan iya zama da kishiya ba dole zai sake su gaba ɗaya, idan ba haka ba sai dai na bar musu shi" Fadila ta faɗa cike da rashin tarbiya, a tsawace Me martaba ya ce "Kina da hankali kuwa? Mahaifin nawa ki ke faɗawa haka to ba zan yarda yarona ya auri mace kamarki ba wadda bata da tarbiya, ko Gimbiya da take taƙama da kanta ba ta taɓa sa'insa da Mahaifina ba balle ke dan haka tashi ki bani guri" Babu kunya ta tashi tana watsawa Alhaji harara tare da barin fadar, sunkuyar da kai Muby yayi cike da biyayya ya ce "Allah ya ba ka nasara ayi mana afwa zata gyara insha Allah, amma kar ka hanani auren Fadila wallahi ina ƙaunarta"

"Tashi ka fita daga nan tun kafin na ɓata maka rai" Me martaba ya faɗa rai ɓace.

Ficewa daga fadar Muby yayi jiki a sanyaye.

Mommy kuwa sai haɗe fuska take dan tun da suka fara magana take sauraronsu har suka gama bata ce uffan ba.


A palour ya sami Fadila tana fushi ta wani haɗe ƙafa, tana ganinsa ta tashi tare da hugin ɗinsa "Dear kana jin abin da Abbanka ke faɗa, wai ba zan aureka ba"

"No zamu yi aure kin ji, in Allah ya yarda Abba zai bari"

"Amma ni ba zan zauna da kishiya ba kuma baza ka tafi ƙasar Chad ba" Tureta yayi daga jikinsa cikin ɓacin rai ya ce "Bana son hauka, wannan halin naki ke sa muna samun matsala ki koma gida zamu yi waya"

"Dear abin da zaka ce min kenan? dan kawai zaka mayar da matarka wadda ko ƙaunarka bata yi"

"Saboda ke zan dawo da ita ai"

"Shikenan Dear amma please bayan aurenmu ka sake su gaba ɗaya har munafukar Maimun ɗin dan ba zan iya zama da wata ba, bayan haka Dear kar ka kwana da kowa har sai mun yi aure kai nawa ne ni ɗaya" Murmushin da ke ƙarama fuskarsa kyau sa saki yana faɗin "Shikenan duk yanda ki ke so hakan za'a yi, ki tafi waje an haɗa komi na tafiyarki, ko za ki kwana ne?"

Hannunsa ta kama a hankali ta ce "A a Dad ya ce na dawo a yau all the best Dear Allah yasa ta yarda da kai, ni ce na bada umarnin a saketa gashi nima sai da yardarta zan aureka"

"Sai dai idan Brother baya jin maganar Abba, amma ida har yana ji ba zai taɓa aurenki ba"

Cewar Ameer yana ɓata fuska.

"Kai ni ka ke faɗawa haka? dan uwarka"

"Uwarki de shegiya me bin maza, marar tarbiya" Ameer ya bata amsa, a fusace Muby ya ce "Wai me yake damunku ne? Fadila wannan rashin dacewa ne, Mahaifiyata ki ke zagi? kai kuma wa ya ba ka izinin shiga maganarmu?"

"Amma Brother kana ganin dacewar auren wanna ballagazar? duk iskancin Aunty Maimun da Gimbiya basa taka maganar Alhaji" "Ɓace min da gani tun kafin na haɗa kanka da tils" Barin gurin Ameer yayi yana Allah ya wadaran halin Fadila.


Da yamma jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Chad, sosai Husna da Ameer suka ji daɗin abin da ya faru, dan basa son ganin auren ya watse, itama Fadila gida ta koma cike da takaicin abin da Ameer ya yi mata.


ƘASAR SENEGAL
...............................
Tun da farar safiya Mama ta nufi gurin bokanta dan ganin duk aikin da ta saka a yi a kan me martaba babu abin da ke yin gaba, tare da malamin suka shigo masarautar, da Hajiya Babba ta tambayeta waye wannan sai ta ce mata ai me gyaran bed ɗin ɗakinta ne ya samu karaya, har bedroom ɗinta ya shige ba tare da wani tsoron Allah ba.

Gaba ɗaya ɗakin ya gama haɗe shi da hayaƙin magungunansa, ta ko'ina hayaƙi ne sai ka duba da kyau ka ke iya ganin abin da ke ɗakin.


Sai da ya gama surutansa sanna ya ciro wani garin magani ya miƙa mata, "Wannan ki zuba cikin abinci mijin naki, wannan kuma ki saka cikin abincin Yarima, ina mai tabbata miki cewa tashin hankali da rashin jituwa sai abin da ya ƙaru"

Jikinta na rawa ta karɓa.

Halima da shigowarta ɗakin kenan ta saki handbag ɗin da ke hannunta, tana zare ido cike da ruɗani ta ce "Mama....., me nake shirin gani haka?"

"Ke shigo daga ciki dan ubanki yaushe ki ka zo gidannan?"

Girgiza kai ta yi alamun baza ta ƙarasa ba, a ruɗe bokan ya kwashe tarkacensa ya bar ɗakin, kusan faɗuwa Halima ta yi da ya wuce ta gefenta dan ko ba'a faɗa mata ba ta gane waye shi.

Hannunta Mama ta kama tare da zaunar da ita kan sofa, "Mama me hakan ke nufi? ina fatar ba wani abun za ki yiwa Fulani ba"

Bakinta Mama ta buge cike da jin haushin ƴar tata ta ce "Koma menene be shafeki ba yaushe ki ka zo?"

"A tare muka zo amma shi ya tafi anjima zai zo mu koma, ya ce yana gaida ki amma dan Allah Mama ki faɗa min gaskiyar abin da ke faruwa"


"Wai gaskiyar me ki ke son sani? babu abin da ke faruwa Aljanu ne aka korar min"

Shuru Halima ta yi ba tare da ta yarda ba.


Miƙewa daga zaunen da take ta yi cike da zargin Mama ta ce "Zan shiga part ɗin Hajiya da Fulani"

"Sai dai part ɗin Hajiya ban yarje miki zuwa wani part ba"

Mama ta faɗa ranta a haɗe.

Rusunawa Halima ta yi cikin biyayya ta ce "Dan Allah Mama ki daina wannan kishin naki, kar ki mance fa Fulani ce ya kamata ta yi kishinki ba ke ba, da farko ita ce uwargida kuma Fulani a masarautar nan, ban taɓa ganin ta nuna kishinki ko da na rana ɗaya ba, duk da cewar tana kishin naki amma bata nunawa saboda haƙurinta da kawaici"

"Wai ni za ki nunawa halin ƙwarai Halima? tashi ki bani guri tun kafin na ɓata miki rai"

Ficewa daga ɗakin Halima ta yi tana mamakin hali irin na Mahaifiyarta, tun tasowarta ta san ƙulle-ƙullen da take yi amma bata taɓa tunanin abin ya kai har gun wani boka ba.

Da sallama ta shiga part ɗin Fulani, kwance ta sami Husna kan bed tana waya da Ameer, fizge wayar Halima ta yi tana dariya "Da waye ki ke waya? sai dariya ki ke"

Ɓata fuska Husna ta yi kamar zata yi kuka ta ce "Aunty Halima please ki bani wayar nan bana son yayi fushi" Taɓe baki Halima tayi tana mai miƙa mata wayar "Ai sai kiyi fa, nikam ina Fulani ne?"

Shigowar Fulani ne yasa Halima ƙarasawa ta yi hugin ɗinta, "Fulani nayi kewarki sosai, barka da wannan lokacin"

Itama Fulani murmushi tayi cike da farincikin ganin Halimar ta ce "Barka dai amarya ya mijin naki" Rufe fuska Halima ta yi alamun kunya, Husna da tana ganin Fulani ta shigo ne ta kashe wayar tare da matsowa ta ce "Nima nayi kewarki Aunty Halima ashe ke ki ka shigo"

Dariya suka saki gaba ɗaya kafin Halima ta ce "Ina za ki sani bayan kina shan firarki" Da gudu Husna ta fice daga ɗakin tana rufe fuska.

Kai Fulani ta girgiza tana faɗin "Ai Husna sai addu'a yarinya tana ƙarama ta fara soyayya, kuma ni abin da ke ɗaga min hankali da Ameer take soyayya yanzu idan iyayensu suka fargo ya lamarin zai kasance, ko Gimbiya ana fama da nata matsalar balle su da suka kunno kai yanzu".

Zama Halima tayi kan bed tana mai nazarin maganar "Nima ina tsoron abin da zai biyo baya, dan wallahi masarautunnan baza su taɓa laumuncewa ba kowa na ji da kansa, Allah dai ya sa mu dace"

Da ameen Fulani ta amsa kafin suka cigaba da fira, Halima ta ɗan jima kafin ta nufi part ɗin Hajiya.


ƘASAR CHAD
.....................
A ɓangaren Afnan kuwa wani irin faɗuwar gaba ne ta ji ganin fuskar da bata saniba da sunan ya zo gurinta, wani mugun kallo take binsa da shi cike da tsana ta ce "Can i know who you are?"

Haɗaɗɗen matashin da zai kai shekaru talatin da ɗaya ne ya faɗaɗa murmushinsa me kyau cikin muryarsa me zaƙi ya ce "Gimbiya Afnan kenan, ko zan iya magana da ke alone please"

Ƙara haɗe fuska ta yi cike da gajiya ta ce "Ba ka da labarin cewa na wuce sanin maza kamarka"

Ɗagowa yayi da mamakin abin da yaji ta faɗa "Ai ita soyayya bata san wannan ba, kuma ina ji a jikina ke mallaki na ce......" Wani mugun kallo ta yi masa me kama da banganeba.

Hannu ta ɗagama su Mubina alamun su basu guri,

Please Login or Register in order to submit comment