Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hankali ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun cike da ƙasaita ta ce "What did you just said? maimaita mun please"

Shima zaman yayi yana mai fuskantarta "Da farko sunana Umar ni ɗan ƙasar nan ne kuma Malami ne a School ɗin da ki ka fara zuwa jiya, maganar gaskiya ina sonki kuma da aure na san cewa za ki ji maganar wani iri but ina son ki fahimceni"

Murmushin takaici ta yi wanda ya fi kuka ciyo, jin bata amsa shi ba ne yasa shi cigaba da faɗin "Ina fatar zan samu karɓuwa Gimbiya ko kuma na ce Gimbiyar zuciyata"

A fusace Afnan ta miƙe daga zaunen da take cike da haɗe fuska ta fara taka ƙasa, da sauri ya sha gabanta yana mai kama hannunta "Please Gimbiya wallahi ina ƙaunarki tun da na ganki a jiya na kamu da sonki musamman yau da ki ke a gabana....."

Wani mahaukacin mari ya ji an ɗauke shi wanda yasa shi sakin hannunta ba tare da ya sani ba, be ƙare jin zafin ba ya ji wani marin ta ɗayan ɓangaren, a hasale Muby ya chakumo kwalar rigarsa idanunsa sun gama rinewa har wani karkarwa jikinsa ke yi, bakinsa na rawa ya ce "Matar tawa ka ke so?"

Dukansa ya shiga yi hannu da ƙafa, Afnan kam da gudu ta shige dan kar ya dawo gurinta, sosai ya yiwa Umar shegen duka da ƙyar su Alhassan suka ƙwace shi ai kuwa da gudu ya bar gidan ko takalmansa be ɗauka ba.

A fusace Muby ya nufi parlourn gidan ba tare da lura da su Alhassan da ke gefe ba, a nan ya samu Alhaji da Hajjo suna gaisawa ransa ya gama ɓaci dubata ya fara amma be ganta ba "Ina wannan yarinyar?"

Ya tambaya yana mai kallon Mubina da ke tsaye, cikin girmamawa ta nuna masa upsters ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya haura sama, su Hajjo na kiransa amma be saurare su ba, da sauri suka bi bayansa har da su Alhassan da shigowarsu kenan.




*MUJE ZUWA YANZU AKA FARA, KU CIGABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN ASMEETAR HYDAR DOMIN JIN WANNAN HAƊAƊƊEN LABARIN ME ƊAUKE DA ABUBUWAN AL'AJABI......*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*









P.13







A bakin ƙofar ya sami su Mubina duk idanunta sun zazzaro alamun tsoro, a fusace ya daki ƙofar nan take ta buɗe, Afnan da ke kwance kan makeken bed ɗinta ne ta tashi da sauri da niyar faɗawa toilet, tsalle ɗaya ya cafko gashin kanta da ƙarfi ya matse, lips ɗinta ta cije jin tsananin zafin da ke ratsata.

Alhaji da shigowarsu kenan ya daka masa tsawa a fusace "Yarima kanada hankali kuwa? ka sake mata gashi wannan ba tarbiyar masarautarmu ba ce" Idanunsa da suka gama rinewa ya ɗago cikin ɓacin rai ya ce "Sai ta faɗa mun wanene banzan da yake zuwa fira gurinta"

"Wallahi ba banza ba ne" Afnan ta faɗa tana watsa masa harara, sakin gashin nata yayi tare da kama hannunta ya murɗe yana faɗin "Da auren nawa ki ke soyayya? babu abin da zai hanani yi miki shegen duka yau" Da ƙarfin tsiya ya jata zuwa parlour, Hajjo kam jikinta ya gama sanyi dan ta san ita ce silar fitar Afnan, amma ai bata san cewa ba Yarima ba ne.

Sunansa Alhaji ya shiga kira amma ina Muby ransa ya gama ɓaci, Alhassan da ke gefe ne ya kalli Muhseen ya ce "Maganinta kenan ta san cewa ba mijinta ba ne amma ta zauna"

"Ni ba wannan ba ma, babu abin da ya burgeni irin kyawun Yariman nan wallahi kamar shi yayi kansa yanzu Sister mijinta na da irin wannan kyau haka take ƙushe shi" Muhseen ya faɗa cike da mamaki.

Tsaki Alhassan ya ja yana mai ficewa daga ɗakin.

A parlourn suka same su, fuskar Muby a haɗe yake ce ma Afnan ta fara tsallen kwaɗo amma ta yi kamar ba da ita yake ba "Ina wasa da ke ne? ki fara abin da na saka ki tun kafin na ɓaɓɓalaki"

Wani mugun kallo ta watsa masa cike da gadara ta ce "Ba zan yi ba, kuma ka bani takaddar sakina dan ba zan koma gidanka ba"

"Wai kinada hankali kuwa mijin naki ki ke faɗawa haka?" Alhassan ya faɗa yana kallonta.

Juyawa ta yi a fusace zata koma sama Alhaji ya ce "Dawo ki zauna Gimbiya" Kamar zata yi kuka ta koma kusa da Hajjo ta harɗe kafafunta. Kusan mintuna uku suka ɗauka ba tare da kowa ya ce uffan ba, daga bisani Alhaji ya ce "Ina mai ƙara ba kowa haƙuri, mu ba raba auren ya kawo mu ba kuma ba takaddar saki a ka kawo ba, abin da ya kawo mu shine tafiya da Gimbiya, amma inhar ta amince zata koma, tabbas idan bata amince ba baza mu yi mata dole ba"

"Wannan haka yake amma nima ina da magana" Cewar Hajjo.


Alhaji ne ya ce "Muna sauraronki"

Ajiyar zuciya HAjjo ta sauke cike da fargaba ta ce "Ina son gaba ɗayammu mu tafi ƙasar Senegal domin akwai magana me muhimmaci da nake son mu yi"

Alhassan ne ya karɓe zancen da faɗin "Yawwa Hajjo har naji daɗi wallahi dan ni kaina ina son fita daga wasiwasin da nake ciki" Sosai suka tattauna a kan maganar, Alhaji ma ya nuna cewa ba damuwa gobe da safe zasu shiga ƙasar Senegal, cikin takaici Afnan ta bar parlourn, da kallo Muby ya bita har zai dakatar da ita sai kuma ya fasa dan baya son rainin da take masa a gaban jama'a.


Misalin ƙarfe tara na dare ne Muhseen ya nufi ɗakin Afnan a lokaci har bacci ya fara ɗaukarta, kwance take kan sallaya tun da ta yi sallar isha'i bacci ya sace ta a nan, fuskartar cike da bacci ta kalli Muhseen tana ɓata fuska "Lafiya Malam? ka shigowa mutane ɗaki"
"Lafiyarce ta kawo haka dama Hajjo ce ta ce na canza miki ɗaki saboda ɗazu su Jakadiya suka kashe wani ƙatoton ɓera a ƙarƙashin bed ɗinki..." Tun da Afnan ta ji an ambaci ɓera ta miƙe tsaye da gudu ta fice daga ɗakin tana rusa ihu, shima Muhseen bayanta ya bi yana dariya ƙasa-ƙasa, a bakin ƙofa ya sameta jikinta na rawa, haɗe fuska ya yi kamar gaske ya ce "Mu tafi ko?" Gaba ya wuce tana binsa a baya har suka haura hawa na uku, tun da ta zo gidan bata taɓa wuce hawa na farko ba sosai gurin ya tsaru, wani korido ne suka bi tare da tsayawa gaban wani room wanda ƙofarsa ma abun kallo ne, "Yawwa ga room ɗinnan sai ki kwanta kafin zuwa gobe" Muhseen ya faɗa yana barin gurin, cikin ɗari-ɗari ta kunna kai amma bata ganin komi sosai dan hasken bed side Lamp ne kawai, idanunta cike da bacci ta dannawa ƙofar key tare da nufar bed ɗin ba tare da lura da mutum da ke kwance ba, tun lokacin da ta shigo yake kallonta ta ɗan hasken da ke ɗakin, mamaki ne ya kamasa da kuma tunanin meya kawota room ɗinsa har da wani saka key, hijab ɗinda ke jikinta ta cire tana mai jifa da shi gefe, da sauri Muby ya gimtse idanunsa ganin wasu irin masifaffun kayan baccin da ke jikinta farare masu masifar kyau, ƴar ƙaramar riga ce da kaɗan ta rufe mazaunanta sai ta wajenta wadda shara-shara ce ba wani abun da ta ɓoye, ba tare da fargaba ba ta faɗa kan bed da bismillah ɗauke a bakinta, a tare suka ƙwalla ƙara jin abin da basu yi zato ba, shi idanunsa na rufe be san lokacin da ta faɗo masa ba, ita ko tsoro da tashin hankali ne ya shigeta jinta a ƙirjin namiji, jikinta na rawa ta ce "Waye......?"
Jin tambayar da ta yi masa ne yasa shi haɗe fuska dan yayi tsammanin ta san yana ciki ta shigo, bakinta ya murɗe da ƙarfi yana faɗin "Tambayata ki ke yi? bayan kin shigo neman haƙƙinki, na san cewa iskanci ne ya kawoki ɗakina amma imba haka ba, duk yawan ɗakunan da ke gidannan sai wannan za ki shigo" Sai a lokacin ta gane waye jin muryarsa da ta yi, cike da tsiwa ta ce "Na fi ƙarfinka wallahi, ni me zan yi da kai har ka ke maganar haƙƙi, ko an faɗa maka ni ƴar iska ce" Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin janye jikinta, hannayensa ya saka ta bayanta ya maidota kan ƙirjinsa, "To waye ɗan iskan?" Muby ya tambayeta yana sakin numfashi dan ƙamshin turarenta ya gama tafiya da imaninsa nan take feelings ɗinsa ya fara tasowa, jin yanayin da yayi maganar ne kuma yana wani shinshina ta yasa ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta, nan fa suka fara kokawa, ganin tana neman rainasa ne yasa shi saka dukkanin ƙarfinsa yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, a hankali ya sauko da bakinsa kan kunneta cikin raɗa ya ce "Idan har kina son na barki a gidanku sai kin yarda nayi abin da nake so, idan ba haka ba zan yi ta ƙarfi kuma dole sai kin koma gidana" Hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata ta yi saurin maidawa, "Ba zan amince ba kuma idan ka yi min wannan iskancin Allah ya isa" Ta faɗa tana tura baki.
Nauyin jikinsa ya sakar mata tsabagen mugunta har da danna jikin nasa yake, da ƙyar ta iya fito da maganarta "Please ka saukeni bana son wannan abin"

"Ni kuma ina so" Ya bata amsa cike da ƙarfin hali, wani irin murɗawa mararsa ta yi kamar zata bar jikinsa, west ɗinta ya chakumo yana matsawa jikinsa na rawa ya ce "Idan ma ba ki yarda ba ke halal ɗina ce"
Daga saman rigar har ƙasa ya sa hannu da ƙarfin tsiya ya yaga, hannayenta ta tattare kan ƙirjinta tana faɗin "Wallahi ba zan yarda ba sai an fitar min da haƙƙina" Be saurari abin da take faɗa ba ya fara wasa da gaba ɗayan jikinta, har wani nishaɗi na musamman yake ji dan ya kasa gane meyesa jikin Afnan ke daɗi gurin romance, ba ƙaramin wahalar da ita yayi ba shi kansa ya masifar wahala, da ƙyar ya iya cire kayan jikinsa, duk da cewar tana jin daɗin abin da yake yi mata amma hankalinta ya masifar tashi da taji babu kaya a jikinsa, bakinta na rawa ta ce "Ka sauka a kaina bana so kar ka ɓata min rayuwa" Duk maganar da take Muby baya jinta dan ba a hayyacinsa yake ba.

Ganin da gaske yake neman ƙwace mata budurci yasa ta kama gefen wuyansa ta gurin jijiyarsa ta murɗa da ƙarfi, kamar wanda aka saka ma kasala haka jikinsa ya sake guri ɗaya, gaba ɗaya ya kasa ɗaga ko hannunsa gashi duk ya manne mata, ta kasa raba jikinta da nasa dan dole ta gyara kwanciyarta kan ƙirjinsa jiran baccin da zai ɗauketa, idanunsa a buɗe yana kallonta amma babu halin yayi abin da yake so, ga wani zafin da mararsa ke masa kusan sha ɗayan dare suna a haka kafin bacci ya ɗauketa, gaba ɗaya ta wani shige masa hankali kwance take sauke numfashi, ba ƙaramin kyau bacci yake yi mata ba sosai ya zuba mata ido yana son ganin muninta amma ya kasa dan wani kyau ta ƙara masa, be jima ba shima baccin wahala yayi awon gaba da shi.

Kiran sallar farko ya farka wanda a lokacin duk rabin jikin Afnan a jikinsa ne, ta wani lanƙamo wuyansa da hannayenta, fuskarta ɗauke da murmushi gashin kanta ya baje kan bed ɗin, a hankali ya fara ƙoƙarin janye jikinsa amma ina sai ma ƙara rungumosa da ta yi, be ankaraba suka faɗa ƙasan sofa.

"Ashhhhhhh..."

Ta furta tana buɗe kyawawan idanunta, sai a lokacin ta lura ashe faɗowa suka yi, da sauri ta yunƙura da niyar tashi, sai kuma ta ƙara matse shi ganin babu komi a jikinta, "Malama sake min jikina" Muby ya faɗa yana haɗe fuska.

Itama haɗe fuskar ta yi tana tura baki "Baza a sake ka ba ɗin, ai kaine ka cire min kayana"

"To shikenan bari na maida miki kayan" Ƙara janyosa ta yi cike da shagwaɓa ta ce "Ni bana so ka rufe idanunka na saka hijab ɗina" Jin yanda take shagwaɓa ne yasa shi zuba mata ido, wai dama ta iya magana haka, ya tambayi kansa a zuciya, haka kawai ya tsinci kansa da rufe idanun nasa kamar yanda ta faɗa.

Miƙewa tayi daga kwancen da take ta fara laluben inda ta jafar da hijab ɗinta jiya, tana ganinsa ta zura tare da ficewa daga ɗakin da gudu, jin buɗewar ƙofar ne yasa shi gane ta fita, sannu a hankali ya tashi tare da mayarda jallabiyarsa yana mai shigewa toilet.



Ƙarfe tara na safe zaune suke kan daining gaba ɗaya ana karin kummalo, amma banda Afnan da tun da ta bar ɗakin Muby ba wanda ya sake ganinta, Hajjo da ke gefe ne ta maida kallonta kan Muby da ke sanye cikin ƙananan kaya ya masifar yin kyau ga wani farin glass me kyau da ya kafa, "Me gidana ina Gimbiya ne? ko wani abun ne ya hanata fitowa" Kallon Hajjo kowa da ke parlourn yayi da mamakin jin abin da ta ce musamman Muhseen da Muby da sun san cewa ba a ɗakinta ta kwana ba.

Murmushin yaƙe ya saki yana faɗin "Ina ganin bacci ne be isheta ba"

Gyaɗa kai Hajjo ta yi tana mamakin abin da ya hana Afnan fitowa har wannan lokacin. Bata gama tunanin ba suka fara jiyo takun tafiyarta, su Mubina na bayanta ɗauke da troly tana sanye cikin wando da riga red sai dai rigar ta ɗan sauko har kan cinyarta, wandon kuma me faɗi ne an yi masa adon duwatsu na gold a ƙasa, ta ɗora ƙaramin hijab black me taushi wanda ya tsaya mata kan kafaɗarta fuskarta kuwa a haɗe kamar wadda aka yiwa mutuwa ba ƙaramin kyau ta yi ba, ƙamshin turarenta sai zarya yake a parlour, cike da ƙasaita ta ƙaraso tana gaida mutanen da ke gurin, ko kallon inda Muby yake bata yi ba kamar yanda shima kallo ɗaya yayi mata tare da kawar da kai gefe.

Alhaji Babba ne ya ce "Amarya kin sha ƙamshi duk wannan kwalliyar ta jikana ne?" Wani mugun baƙin ciki ne ya cika mata zuciya musamman da ta tuna abun da Muby ya yi mata jiya, a hankali ta ce "Uhmm Alhaji kenan ni babu wata kwalliya da nayi"

"To shikenan na ji amma ai shi mijin naki na san yaga kwalliyar ko Yarima?" Alhaji ya faɗa yana kallon Muby.

"Eh Alhaji" Muby ya faɗa a taƙaice.

Fira suka cigaba da yi Afnan na cin abincinta, cike da nishaɗi dan ta san idan har ta koma gida babu wanda ya isa ya maidata gidan Yarima. Can Muby ya kalli Hajjo da fara'a ya ce "Nikam waɗannan kyawawan samarin masu kama da Gimbiya fa? tun jiya nake son yin magana amma na sha'afa" Saurin kawar da zancen Alhaji ya yi da faɗin "Kowa ya shirya ko zamu kama hanya" Ba tare da tunanin komi ba Muby ya miƙe yana mai haurawa sama.




ƘASAR SENEGAL
...............................
Sha biyu na rana ta yi musu ne a ƙasar Senegal, daga Alhaji,Hajjo,Afnan,Muby,Alhassan,Muhseen, da kuma su Mubina da dama komawa da su ya zama dole, ba ƙaramin tarba aka yi musu ba dan tun suna hanya me martaba da Fulani suka samu labari, hankalinsu ya masifar tashi da suka ji labarin har da su Alhassan ne, shiyasa ma daga me martaba har ita Fulani babu wanda ya hallara a parlourn har wajen ƙarfe huɗu, Mama kuwa haushi ne ya kamata ganin cewa babu wanda ya sanar mata zuwansu Hajjo, ga maganin da malaminta ya bata har yanzu tunanin yanda zata yi da shi take amma ta kasa samun mafita.

Bayan kowa ya samu natsuwa ne Alhaji ya nemi ganin Me martaba da Fulani, Husna kam tun da taga su Alhassan ta manne musu sai cewa take suna kama da Baffanta, sosai yarinyar ta shiga ransu ganin yanda bata nuna wata ƙyamarsu, yanzu haka ma kusa da Alhassan take tana bashi labarin yanda Afnan ke taurin kai, da kuma yanda Hajiya ke son ta koma ɗakin mijinta amma taƙi yarda, a lokacin Mama ta shigo parlourn da niyar zubawa Yarima maganin, ai kusan faɗuwa ƙasa ta kusa yi ganin Alhassan da Muhseen, ga masifar kamar da suke da Afnan, bakinta na rawa take faɗin "Waɗannan kuma su waye haka?" Fulani da ke bayanta tana ƙoƙarin shigowa daga ciki tare da me martaba ne ta ce "Ƴaƴana ne su ko akwai wata matsala ne?" Gaba ɗaya ɗakin kallon Fulani ake, Alhassan da Muhseen ko da sauri suka miƙe tsaye har haɗa baki suke gurin faɗin "Baffa.....Mami.."
Sunan da suke kiran iyayen nasu kenan.


Matsawa suka yi tare da rungume su cike da farinciki, ba Mama ba wannan karon har Afnan da Husna mamaki ne kwance kan fuskarsu, shin su waye waɗannan kuma a ina me martaba ya sansu har suke kiransa da Baffa, Afnan ce ke zancen zuci gaba ɗaya ta gama ruɗewa.

Bayan kowa ya samu guri ya zauna ne me martaba ya gaishe da su Alhaji da Hajjo kafin ya cigaba da faɗin "Ina buƙatar a tara min kowa a fada sannan a kira su Bilkisu da su zo gaba ɗayansu" Cike da girmamawa Husna ta ce "Baffa bari na kira su Aunty Bilkisu, yanzu" Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar wayarta ta fice daga parloun, Mama kam zaman dirshan ta yi tabbas abin da take zargi shine ke shirin faruwa, to idan har da gaske ne yaya aka yi hakan ta faru.

Su kansu Alhassan mamakin ganin iyayensu cikin wannan gida suka yi, ga kayan jikinsu ya nuna cewa sai masu haɗi da sarauta ke sakawa.


Ba da ɓata lokaci ba fada ta cika maƙil da mutane, a ciki kuwa har da su Mama can gefe da ƴaƴanta, Alhassan da Muhseen na gefen Mahaifinsu, tun kafin Sarki Shuraihu ya yi magana mutanen da ke gurin ke zargin cewa ƴaƴansa ne saboda tsananin kamar da suke da, shi kansa Muby be san da lamarin ba, amma Alhaji Babba suna da labarin komi.

Gyaran murya Me martaba ya yi cike da izzah ya ce "Na san cewa mutane da dama sun ga baƙuwar fuska anan gurin waɗan da ko ban faɗa ba kun ga kammanina kan fusar matasan yarannan da ke kusa da ni" Ya nuna su Alhassan da ke mamakin wai dama Mahaifinsu sarki ne, to meyesa ya barsu a can kuma a ka ɓoye musu, Sarki Shuraihu kuwa cigaba da faɗin yayi "Waɗannan da ku ke gani ƴaƴana ne na sunnah waɗan da mu ka haifa da matata ta farko wato Fulani, a lokaci ɗaya ta haifesu da Gimbiya AFnan, sai dai wani babban dalili ne yasa mu ka bar yaran a can ƙasar Chad mu ka zo da Gimbiya kawai, yanzunnan zan nuna muku shaida saboda kore zargin wasu daga cikinku" Nan take wasu dogarai suka shigo da wani wakeken Tv aka jona shi yanda kowa da ke fadar zai iya gani, Mama kam zufa ce ke karyo mata kamar wadda ta zubawa jikinta ruwa, ita da ƴaƴanta kana ganinsu ka san hankalinsu a tashe yake, ai basu ƙara ruɗewa ba sai da a ka nuno videon Alhassan Munseen Gimbiya suna jarirai su uku kwance gefen Fulani, a can gefen kuwa Hajjo ce na yi musu wasa suna dariya, kana ganinsu ka san ƴan uku ne kuma kammanninsu ɗaya, da murmushi me martaba ya kalli jama'ar da ke gurin ya cigaba da faɗin "Gimbiya su uku ne aka haifa, kasancewar wani dalilin ne yasa na bar ƴaƴana maza a can ƙasar Chad kuma na ɓoye musu asalin ko ni waye" Duk abin da ya faru me martaba ya kwashe ya sanar musu, nan fada ta ɗauki tafi da farinciki, labari ya gama mamaye gaba ɗaya masarautar, cike da baƙin ciki Mama ta bar gurin tana tunanin hanyar da zata raba su da duniya.

Afnan kam kasa motsawa ta yi daga inda take zaune, duk jikinta yayi sanyi kunyar ƴan'uwan nata ne ya hanata kallon inda suke lura da hakan yasa Muhseen matsawa kusa da ita yana murmushi "Sisterna meyesa bakya murna da kasancewarmu jini ɗaya" Faɗawa jikinsa ta yi tana fashewa da kuka sosai take nadamar abin da ta rinƙa yi musu, bubbuga bayanta ya shiga yi yana rarrashinta, kallonta ta mayar kan Alhassan sai kawai taga ya haɗe fuska kamar be santa ba, a hankali ta koma kusa da shi tare da kama hannunsa, ƙwace hannun nasa yayi yana galla mata harara, itama harar tasa ta yi tana tura baki ta ce a hankali yanda babu wanda zai ji "Bana tsoronka yanzu tun da a rana ɗaya a ka haifemu, kawai ina roƙonka da ka yafe min please i know that i hort you guys so much but try to for give me Alhassan" Ɗago kansa ya yi yana dariya ya ce "Ni ki ke kira da sunana ko? dan kawai rana ɗaya aka haifemu lallai yau me hana nayi miki duka sai Allah" Itama dariyar ta yi tana mintsilin shi a wuya.
Bayan ɗan wani lokaci Fada ta watse ya rage Family ne kawai kowa na zaune ana sauraron Alhaji da ke magana, bayan ya gama nuna alhininsa kan lamarin, "Masha Allah muna ƙara godewa Allah da ya nuna mana wannan rana musamman wannan babban sirri da ake ɓoyewa, yanzu kuma sai maganar komawar Gimbiya dan shine abin da ya kawo mu, amma fa sai idan ta yarda" Bilkisu da Hauwa'u da ke zaune can gefe ne suka taɓe baki cike da jin haushi, Halima kuwa gyaɗa kai tayi tana mamakin hali irin na ƴan'uwan nata. Me martaba ne ya ɓata fuska tare da kawar da kai, har Afnan zata yi magana Alhassan ya yi saurin riƙe mata hannu a hankali ya ce "Idan har kina son na haƙura kuma kina son mu shirya ki koma ɗakin mijinki, na san cewa kina son Yarima kawai ɓoyewa ki ke saboda tsabagen miskilanci" Turo baki ta yi cike da shagwaɓa ta ce "Ni bana sonsa"

"To shikenan na yarda bakya sonsa ki koma ɗakinki saboda Allah kuma saboda ni" Kamar zata yi kuka ta ce "Okay" Hajiya ce ta maida kallonta kan Afnan ta ce "Gimbiya ke ake jira fa, kin amince ko kuma a raba auren?" Ta kusan mintuna biyu kafin ta ɗago idanunta da suka ciko da hawaye ta ce "Na amince zan koma" Sosai Hajiya da Fulani suka yi murnar jin wannan zancen, Husna ko tuni ta fice dan ta sanarwa Ameer abin da ke faruwa ta waya.

Muby ko haɗe fuska yayi kamar wanda aka yiwa mutuwa.

Me martaba kam kasa magana yayi dan babu abin da zai iya cewa game da lamarin.


Tun da ta shige ɗakinta ta ke kwance kan bed hawaye duk ya gama wanke mata fuska, ta san cewa tabbas zamanta ya zama dole a gidan Yarima, zata koma ne kawai dan ɗan'uwanta Alhassan na buƙatar zamanta kuma dan goge laifin abubuwan da ta rinƙa yi musu, jin buɗewar ƙofar ne yasa ta ɗago dan ganin waye, Fulani ce tare da su Alhassan sai kuma Husna da ke bayansu, komawa ta yi daga kwancen da take dan a halin yanzu bata son magana ma.

Zama suka yi kusa da ita, Muhseen kam kwanciya yayi gefenta tare da faɗin "Kukan me ki ke Sisterna? idan har bakya son komawa ki faɗa mana babu

Please Login or Register in order to submit comment