Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki fara kuka ba tukunna, sai idan kin shigo gidana" Ta tsinkayo muryar Muby tsaye a bakin ƙofar ɗakin ya harɗe hannayensa idanunsa kamar garwashin wuta, cigaba ya yi da faɗin "Duk abin da kika shirya be yi tasiri ba, baƙincikina ɗaya ɓata min suna da kika yi cikin family, na tsaneki kamar yanda na tsani mutuwa ta"

"Haka kazalika nima na tsaneka fiye da yanda na tsani wutar jahannama, bana sonka bana muradin haɗa jini da kai"

Fasashshen kwalbar mirrow da ke ƙasa ta ɗauka tare da damƙe shi a hannunta da ƙarfin tsiya, nan take hannun ya tsatstsage cikin dauriya da taurin rai ta share hawayen da ya zubo mata kafin ta yamutsa lips ɗinta a hankali ta ce "Baka da dukiya, baka da mulki, baka da kyawu da nasabar da zaka mallaki mace kamata, na wuce saninka Yarima, ba zan taɓa iya rayuwa da talaka kamar ka ba" Da gudu ta shige toilet ta rufo ƙofar tare da zubewa ƙasa tana mai cigaba da rusar kukanta.


Murmushin gefen baki Muby ya yi kafin ya ce a fili "A yau ɗinnan zaki tare a gidana ba sai wani satin ba, saboda wannan furucin naki"

Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin cikin taƙama da nuna isa.



*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P.5








A ɓangaren su Hajiya Babba kuwa sosai suka tattauna kan maganar amma ran kowa be so ba, suna cikin magana ne Muby ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, wannan karon yana sanye ne cikin manyan kaya farin yadi me laushi da kyau, ƙamshin turarensa ya gama gauraye ko'ina, rusunawa ya yi tare da gaishe su dan har yanzu be gama sakin jiki ba.

Daga Hajiya Babba sai Alhaji ne kawai suka amsa masa, amma Sarki Shuraihu kamar ya kamasa ya yi mai dukan tsiya, "Allah ya ƙara maka nasara dama magana ce ke tafe da ni"

Cewar Muby yana mai ƙara sunkuyar da kai.

Kamar anyiwa Abbun nasa dole haka ya amsa cikin ɗaure fuska "Faɗi maganarka muna saurarenka"

Lumshe kyawawan idanun nasa ya yi masu ƙara ma face ɗinsa kyau ya ce "Dama idan ba damuwa me zai hana Gimbiya ta tare a yau akwai wani gidana da yake ta FGT ko a can ma zamu zauna"

Ya ƙarasa maganar yana shafa gashin kansa, wanda ya gama haɗuwa.

Kallonsa Mommy ta yi sai kuma ta miƙe tana faɗin "Ni zan shiga daga ciki"

Bata jira cewar ɗaya daga cikinsu ba ta fice daga fadar cike da takaicin abin da ɗan nata ya yi.


Hajiya Babba ce ta yi murmushi kafin ta ce "Yaran zamani kenan, to kaji fa abin da ya ce ka amince kuwa?" Ta faɗa tana kallon Alhaji.

Shima murmushin ya yi kafin ya ce "Ban amince da wannan maganar ba, kamar yanda aka ce sai wani satin dole zai haƙura tun da yau da gobe a gurin Allah ba wuya".

Ba dan Muby na so ba ya tashi yana godiya, cike da gadara ya bar gurin.


..................
Washe garin ranar Sarki Shuraihu da ahalinsa su ka bar ƙasar, sosai Gimbiya Afnan ke cikin damuwa ta rasa abin da ke yi mata daɗi.

Daga Mahaifinta har Hajiya Babba babu wanda ta yiwa magana, idan ma sun yi mata magana sai dai ta kallesu kawai ko kuma ta ɗaga musu kai, tun da suka shiga harabar gidan wanda gaba ɗaya an tsara shi komai ya haɗu tamkar wani shagalin ake, yau hatta masu aikin gidan sun yi wanka tare da saka sabbin kaya, dan sarai sun san halin Gimbiya bata ƙaunar ƙazanta ko kaɗan, shiyasa ma ko tsinke baza ka gani a tsakar gidan ba.

Da ƙarfin tsiya ta banke ƙofar tare da me ƙoƙarin buɗe mata, a fusace ta nufi baban parlourn gidan cike da taƙama duk inda ta gifta sai kaga dogarai da kuyangi sun zube ƙasa, amma ko arziƙin kallo ba sa samu, Mubina me kula da ita ne ta ƙaraso da sauri tana faɗin "Allah ya taimaki Gimbiya sannunku da zuwa" Wani irin wawan mari ta ɗauketa da shi wanda yasa Mubina faɗuwa kan gwuiwoyinta cike da ladabi ta ce "Tuba nake Gimbiya ayi min afwa......" Ai bata ƙarasa ba taji saukar wani marin da yasa ta dafe kuncenta, a zafafe Afnan ta nuna ta da yatsa cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Idan ina tafiya ba'a shiga gabana, kuma idan ina cikin fushi ba'a yi mun magana" Tana gama faɗin haka ta bar gurin cike da ƙasaita take taka steps ɗin, duk masu tsaron haɗaɗɗen parlourn sun san cewa ran Gimbiya a ɓace yake, shiyasa ma basa ko gaisuwa sai dai su rusuna ƙasa kawai, a sama suka ci karo da Mama na ƙoƙarin saukowa, kaɗan ya rage Afnan ta bugeta, ganin haka yasa Mama janyewa da sauri dan ta san halin Gimbiya sarai zata iya jefar da ita ƙasa.


Ɗakinta ta shige tare da banko ƙofar, Mama da ke tsaye baki sake ta ja gajeren tsaki tana taɓe baki, "Daɗin abin dai ba a namiji kika fito ba, da wannan gadarar taki ta kashe mu tun kafin lokacinmu ya zo" Ta ƙarashe maganar tana barin gurin.


Tun da ta shiga ɗakin take kwance kan makeken bed ɗinta wanda ya gama haɗuwa da tsaruwa, ɗakin na ɗauke da beds har kala uku masu masifar kyau, wadrop uku mirrown uku, kai komi na ɗakin nata set uku ne wanda kana ganinsu ka san sai wanda ya cika zai iya mallakarsu.


Duk abin da ke ɗakin kalar sararin samaniya ne, a gefen bango kuwa wani tamfatsetsen hoton Gimbiya ne wanda ta yi shi ita kaɗai, kusa da wani farin doki ya sha kwalliya, ita kuwa ta riƙe linzamin dokin tare da jingina masa, fuskarta a haɗe amma ta yi kyau sosai kyawawan idanunta su suka ƙara fito da hoton.


Bugun ƙofar ɗakin ta fara jiyowa tare da kiran sunanta, amma kamar bada ita ake ba ta ƙara gyara kwanciya tana janyo wayarta ta saka karatun Alqur'an ko zata samu sauƙi a ranta, suratul Al,Anfal ne dama tana jin daɗin surar, cikin zazzaƙar muryarta take bin karatun tana lumshe ido, nan take bacci ya ɗauketa.



Fulani da labari ya isota a kan cewa Gimbiya sun dawo ne hankalinta ya kwanta, duk da cewar a jiya Husna ta faɗa mata abin da ke faruwa, sosai zancen ya taɓata shiyasa ma ta aika Halima ta kira Gimbiya gashi kuma ta rufe ɗakin nata, a hankali ta miƙe tare da nufar down steps cikin shigar alfarma, ta yi kyau sosai sanye take cikin wata atamfa ruwan madara wadda aka baza mata adon duwatsu, a parlourn ta sami Mama zaune ita da wata ƙawarta me suna Hajiya Saratu, kana ganinsu ka san gulma ake yi, cikin fara'a Fulani ta ƙaraso su ka gaisa da matar, Mama da bakinta ke ƙaiƙayi ta kalli Fulani cikin salon mugunta ta ce "Ashe abin da ya faru da Gimbiya kenan? to Allah ya tsare gaba amma aikin gama ya riga ya gama, sai a sakata cikin ruwan zafi dan na san ba ƙaramin buɗewa tayi ba....." Hannu Fulani ta ɗaga mata fuskarta a haɗe ta ce "Ya isa haka, meyesa wani lokacin ba ki iya magana ba ne? koma menene ai sai ki bari idan muna a keɓance, ina ganin hakan kamar tonon asiri ne"

"Menene abun tonon asiri a ciki bayan gaba ɗaya masarauta ta ɗauka da zancen Yarima ya yiwa Gimbiya fyaɗe...."

Cewar Hajiya Saratu tana murushi.

Husna da dawowarta daga islamiya kenan taji abin da ke faruwa, sosai maganar ta tsaya mata a rai, a ƙufule ta ce "Ita kuma ƴarki da kowa ya san cewa karuwa ce fa? ki fara gyara matsalar gidanku kafin ki shiga lamarin gidannan, ina tsammanin ke baƙuwa ce baƙuwar ma ta kishiyar Uwa"

Ta ƙarasa maganar tana riƙe hannun Fulani da tun da suke faɗa mata magana ta kasa motsa koda ƙafafunta.

Jin saukowar mutun daga upsters ne yasa kowa shuru ana jiran ganin waye, wata matashiyar yarinya ce wadda zata kai shekaru ashirin da tara zuwa talatin, tana sanye cikin doguwar riga red, kanta babu ɗankwali sai wani cingom da kake ji ƙasss-ƙasss-ƙasss, cike da rashin tarbiya ta ƙaraso tana mai zama kusa da Mama, "Me yake faruwa naga uwar gayya tsaye? kamar wadda aka dasa, tare da me mara mata baya" Ta faɗa tana watsawa Fulani wani kallo wanda za'a kira shi da kallon rainin hankali, carafffff Husna ta karɓe zancen da faɗin "Idan kin lura zaki ga uwar guzuma zaune tare da me mara mata baya, ko kina nufin baki lura da buhun gishiri da na lemun tsami a kusa da ke ba?"

A harzuƙe matashiyar ta miƙe da niyar watsa mata mari "Bilkisu karki soma wannan ɗanyen aikin naji duk abin da ke faruwa, da girmanki amma kina abu kamar ƙaramar yarinya" Cewar Hajiya Babba tana saukowa a hankali, da sauri Husna ta tarota su ka sauko tare.

Mama da haushi ya kamata ne ta ce "Amma Hajiya kina jin abin da take faɗa mana ko?"

"Idan har ita Bilkisu bata fara ba babu abin da zai sa Husna ta amsa mata, me ma ya kawota nan gidan yau?" Hajiya Babba ta faɗa tana mai zama kan haɗaɗɗiyar kujerar da ke parlourn me zaman mutum ɗaya.

Da sauri Bilkisu ta ce "Haba Hajiya mutum da gidan Ubansa, shikenan dan nayi aure sai a hanani zuwa gida? ni gaskiya ba zan lamunta ba, shiyasa Hauwa'u ta daina zuwa dan ta san daga zaran ta zo, mayu zasu tasa ta gaba, ita da gidan Ubanta...."

"Ke ce mayya wallahi, kuma ni bana tsoronki"

Husna ta faɗa tana murguɗa baki, Fulani ce ta kalleta fuska a haɗe ta ce "Husna bana son rashin kunya, tashi mu tafi na san yanzu haka yunwa kike ji"

"Lallai kam gara a tafi dan babu yanda za'ayi da mu"

Cewar Mama tana juya baya, ko kallon inda take Fulani bata yi ba ta ja hannun Husna su ka haura sama.

Hajiya Babba kuwa harara ta gallawa Bilkisu kafin ta ce "Shikenan abin da ki ke buƙata ko? wallahi Bilkisu ke da Hauw'au na rasa halin wa ku ka kwaso, koda yake na mance ga Uwarku nan halinta ku ka ɗauka, ina fatar Allah ya shiryeku" Har Mama ta buɗe baki da niyar magana Hajiya ta daka matsa tsawa "Bana son yawan surutu" Shuru ka ke ji Mama ta tsuke baki, dan ta san halin Hajiya sarai a gidan.



Misalin ƙarfe biyar na yamma ta sauko down steps ɗin sanye cikin wani wando me faɗi, da riga iya ƙugunta, gashin kanta ta ɗaure shi yana rito a baya, sai wata hula me tambarin sarauta, takalman ƙafarta kuwa flat ne me taushi, tun da ta fara tafiya ƙamshin turarenta ke ratsa ko'ina a gidan, ba laifi ranta ya ɗanyi sanyi amma fa fuskarnan a haɗe, a bayanta kuwa kuyangarta Mubina ce ɗauke da wani abu a faranti kamar yadi, duk inda ta ratsa sai kaga mutane na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa har ta fito harabar gidan, sun yi tafiya me tsayi kafin suka isa wani guri a can bayan gidan wanda gaba ɗaya tsarin gurin ya haɗu, daga farkon shiga gurin har ƙarshensa carpet ne ruwan ganye me masifar laushi, gurin nada faɗi da girma, daga can ɓangaren wasu kyawawan dokuna ne a jere suna harbin iska, sai kuma wasu mata su biyu cikin irin shigar da Gimbiya tayi, amma ko kaɗan basu kai kyawun da tayi ba, kowaccensu saman doki suna zagayen gurin, daga nesa suka hangeta ta shigo, nan take suka nufo gurin fuskarsu ɗauke da murmushi, Easha da Muslimat kenan ƙawayen Gimbiya Afnan, tana ji da su sosai tun suna yara, iyayensu nada masifar kuɗi a garin, kana ganinsu ka san arziƙi ya zauna gami da kwanciyar hankali, duk da cewar Afnan ba wani shiga lamarinsu take ba amma hakan baya hana su zo gidan, tun da suka samu labarin ta shigo ƙasar suka zo amma sai yanzu suka ganta, dama idan tana bacci ba'a tashinta.


Suna ƙarasowa suka sauko kan dokunan tare da huggin ɗinta cikin murna da farincikin sake haɗuwa, yamutsa fuska Afnan ta yi kafin ta janye jikinta a hankali ta ce "Hi guys nayi kewarku"


Easha ce ta ce "Muma haka tun ɗazu muka iso amma an hanamu ganinki"

"Kema kinsan baza a bari mu ganta ba har sai ta tashi daga bacci" Cewar Muslimah tana ɗaukar farantin da ke hannun Mubina sannan tayi mata alamar ta tafi.


Nan take suka ɗaurawa Doki ɗaya jan ƙyalle tare da jera Dokuna uku guri ɗaya, bada ɓata lokaci ba kowa ya hau nasa, nan fa dokunan suka fara zagaye gurin suna gudu kamar zasu tashi sama, duk cikin tseren da ake Afnan ce a gaba dan ta fisu iya wasar doki, kamar tauraruwa me wutsiya haka take buga linzamin dokin har ta isa gurin da ɗayan Dokin me jan ƙyalle ke tsaye, sai da aka ƙara mintuna biyu kafin Easha da Muslimat suka iso, dariya sosai Muslimat ta yi kafin ta ce "Gaskiya mun yarda cewa kin kasa mu, amma na sha mamakin ganin yanda kika iya gudu haka bayan Yarima ya cika aiki"


Harara Afnan ta galla mata kafin ta ce "Kema kinsan duk shiri ne ba zan taɓa yarda wani abu ya shiga tsakaninmu ba"

"Ai ina ganin yanda kike tafiya na san cewa sharri ki ka yi masa" Cewar Easha tana fashewa da dariya, sun jima sosai suna wasar dokunan kafin suka koma can gefen wata rumfa me masifar kyau ga iska na kaɗawa kamar lokacin ruwan sama, gurin ya bada ma'ana ba bu abin da zaka rasa a ɓangaren kayan itatuwa.

Basu jima da zama ba Mubina ta shigo gurin da wani irin mahaukacin gudu har tana faɗuwa, ta ƙaraso gurin cikin girmamawa ta zube ƙasa baki na rawa take faɗin "Gimbiya wallahi za su kashe Husna" A ruɗe Afnan ta tashi tsaye cike da tsoro ta ce "Su waye?" "Gimbiya Bilkisu da ƴan ɗakinsu" Tun kafin Mubina ta gama bada amsa Afnan ta bar gurin cikin mugun ɓacin rai, yau za'a yita ta ƙare dama ina ɗaga musu ƙafa ne, amma daga yau sun kawo ƙarshe.




.............
Tun daga Compound Alhaji Mansir ke masifa kamar wanda aka kwashewa dukiya, a bayansa Maimun ce sai matsar kwallah take, jikinta kuwa sai ma ƙara kumburi yake.

Har cikin fadar Sarki Ahmad su ka shiga, kasancewar sananne a gidan shiyasa suka barshi ya shiga har ciki.


Me martaba na ganinsa ya san cewa zancen Maimun ne ya kawo sa dan ya san za'a yi haka.

Bayan sun samu guri sun zauna ne, tare da gaisuwa Alhaji Mansir ya ce "Allah ya ja zamaninka na kawo ƙara a matsayinka na sarki a wannan babbar ƙasa, kuma wanda ke kare haƙƙin ɗan adam, ina son a bi mun haƙƙina da kuma na ƴata" Ya ƙarasa maganar yana nuna Maimun da ke zaune.

Mutanen da ke gurin kuwa kowa ya yi shuru ana sauraron abin da me martaba zai ce, gyaran murya Sarki Ahmad ya yi cikin taƙama da mulki ya ce "Ina sauraronka me yake tafe da kai?"

"Allah ya baka nasara tun da har kana buƙatar jama'ar da ke gurinnan su san halin da ake ciki shikenan, abin da ke faruwa shine ɗanka Yarima ya yiwa ƴata mugun duka wanda ya sa gaba ɗaya jikinta ya lalace, a gaskiya babu namijin da zai yarda ya aureta a haka, wannan dalilin ne yasa na kawo ƙara da a ɗaukar mana mataki"

Shuru me martaba ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya ce "Hakane ba wai na mance da hukuncin da zan ɗauka ba ne, kawai lokaci nake jira"

Waziri ne ya ce "Allah ya ja zamaninka ya kuma kareka, kar a ce nayi kazagi amma me zai hana a haɗa auren Yarima da Maimun, tun da shine silar lalacewar jikinta"

Kallonsa Maimun tayi tare da kashe masa ido ɗaya dama ta gama haɗa baki da shi akan zata biya shi kuɗi me tsoka, me martaba ne ya ɗan yi shuru na wani lokacin kafin ya ce "Ka kawo magana me amfani Waziri, dan haka a kiramun Yarima yanzunnan"



"Allah ya ƙara maka nasara, ai Yarima ya fita shi da Yusuf tun ɗazu"

Waziri ya bashi amsa yana sunkuyar da kai ƙasa, kallon Alhaji Mansir me martaba ya yi yana faɗin "Shikenan a matsyina na adalin sarki kuma me kare haƙƙin mutanen ƙasata"

Gyara rawanin kansa ya yi yana mai kallon Maimun da ke jiran abin da zai ce, cigaba ya yi da faɗin "Na yanke hukuncin aure tsakanin Yarima Mubarak da Maimun a kan dalilin abin da ya aikata mata, insha Allah ranar da Gimbiya zata tare a ranar za'a kaisu tare, wannan hukuncin da na yanke babu wanda zai canza shi"

Sosai maganar tayiwa Maimun daɗi gaba ɗaya ta rasa inda zata saka kanta saboda farinciki, nan take Waziri ya fara yima me martaba kirari tare da koɗa shi.

Bayan an aje magana ne Alhaji Mansir ya yi sallama tare da barin gidan.


Misalin ƙarfe tara na dare Sarki Ahmad ya tara meeting na mutanen gida, kowa ya hallara harda Alhaji, Ameera da ke gefe ta haɗe fuska ne ta kalli Ameer a hankali ta ce "Na san be wuce maganar Gimbiya ba, na rasa meyesa baza a raba wannan auren ba"

"Kema kin faye surutu Ameera ai sai ki tsaya muji abin da ke faruwa" Ameer ya faɗa yana cigaba da danna wayarsa.

Sarki Ahmad kuwa ya rasa yanda zai fara maganar dan ya san halin Alhaji sarai, kuma yanzu idan yaji labarin auren da zai yiwa Yarima akwai tashin hankali.

Mommy ce ta ƙatse masa zancen ta faɗin "Me martaba kayi shuru Allah yasa dai lafiya"



Muby da tun lokacin da ya zauna yake jiran abin da Mahaifin nasa zai ce ne ya kalli Mommy cikin iya miskilanci ya ce "Ni har na fara jin bacci fa"



Murmushi Mommy tayi kafin ta ce "Ka ƙara haƙuri na san yana jin nauyin maganar da zai yi ne....." Tun kafin Mommy ka ƙarasa magana suka tsinkayo muryar me martaba na faɗin "Ɗazu Alhaji Mansir ya kawo ƙarar abin da Yarima ya yi ma Maimun, kuma na yanke hukuncin da nake ganin ya fi"



Gaban Muby ne ya faɗi jin abin da me martaba ya faɗa, gyara zama Alhaji ya yi kafin ya ce "Wanne hukunci aka yanke?"

"Aure tsakanin Yarima da Maimun a rana ɗaya za su tare da Gimbiya, kuma gaban mutane na yanke wannan hukuncin dan Allah Alhaji karka dakatar da wannan lamarin..."


A tsawace Alhaji ya ce "Menene hujjar ka na yanke hukunci me tsauri haka, yanzu da wanne ido zamu kalli Shuraihu da ƴar tasa?"

"Ayi min afwa Alhaji amma wannan shine hukuncin da ya dace" Har Alhaji zai kuma magana Mommy tayi saurin cewa "Allah ya ba ka haƙuri Alhaji, amma ina ganin laifin Yarima ne, kawai muyi musu fatan zaman lafiya"

Gaba ɗaya kasa samun wanda zai yi magana aka yi, Muby kam jira yake ya tashi saboda zuciyarsa da ke bugawa da ƙarfi, Ameera da ke gefe daɗi ya gama cika ta dan tana son Maimun ta auri Yarima.

Me martaba ne ya ce "Tashi ku tafi dama shine dalilin da ya sa na tara ku"

Kamar wanda ƙwai ya fashewa a jiki haka ya miƙe tare da barin ɗakin jikinsa na rawa, gaba ɗaya hankalinsa ya gushe, mata biyu a rana ɗaya kuma babu wacce yake so.





*Sai kun yi haƙuri yau typing ɗin ba yawa, bayan haka bana samun isashshen lokacin da zan rinƙa yin typing kullum*



👑👑 *GIDAN MULKI* 👑👑

*By*

*Asmeetar Hydar*







*𝐖𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐩𝐚𝐠𝐞 𝐝'𝐢𝐧 𝐧𝐚 𝐭𝐚𝐰𝐚𝐠𝐚𝐫 𝐆𝐢𝐦𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚 𝐭𝐚𝐲𝐚𝐭𝐚 𝐤𝐢𝐬𝐡𝐢, 𝐝𝐮𝐤 𝐝𝐚 𝐜𝐞𝐰𝐚𝐫 𝐤𝐮𝐧 𝐜𝐞 𝐌𝐮𝐥𝐤𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐭𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐲𝐚𝐰𝐚, 𝐚𝐦𝐦𝐚 𝐡𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐳𝐚𝐢 𝐡𝐚𝐧𝐚 𝐤𝐮 𝐭𝐚𝐲𝐚 𝐭𝐚 𝐤𝐢𝐬𝐡𝐢𝐧 𝐘𝐚𝐫𝐢𝐦𝐚 𝐛𝐚*



P.6





........A ɓangaren su Afnan kuwa da gudu ta faɗa parlourn, wani irin mugun burki ta ja ganin yanda Bilkisu ke jibgar Husna, Halima na gefe tana ƙoƙarin janye ƴar'uwar tata, ai Afnan bata tsaya wata-wata ba ta rarumi wani katako wanda flower ke ciki ta buga mata a kai, ihu Bilkisu ta kurma tana mai dafe inda jini ke zuba, cike da gadara Afnan ta nunata da yatsa kamar sa'arta ta ce "This is just a few of the things i have provided for you guys, na gaji da haukar ku wallahi"

Husna kuwa tashi tayi da ƙyar jikinta na rawa ta rungume Afnan, Mama da ta faɗo parlourn kamar an korota ne ta fara zuba masifa ba tare da jin ba'a si ba, ko kallonta Gimbiya bata yi ba ta ja hannun Husna su ka haura sama.


Bilkisu kuwa har ta fara ganin jiri saboda jinin da ya fara shiga fuskarta, da sauri Halima da Mama su ka kamata tare da ficewa da ita clinic ɗinda ke cikin masarautar.


Ɗakin Fulani Afnan ta nufa da Husna tana faɗin "Me ya haɗa ku da ita?"

"Wai cewa take an yi miki fyaɗe, ni kuma ba zan iya shuru ba dan be dace tana faɗar haka ba, shine fa ta fara dukana kamar ta samu jaka"

Husna ta faɗa tana matse kwalla dan Bilkisu me jiki ce, da sallama suka shiga ɗakin Fulani, wanda ya gama tsaruwa kamar Aljannar duniya, komai na ɗakin pink and blue ne, hatta pentin ɗakin pink ne kana ganinsa ka san kuɗi ya zauna, babu abin da be tsaru ba a ɗakin, Tv biyu ne a ciki sai bed ɗaya wanda ke da girman gaske, a gaban bed ɗin wata kujera ce me kama da bed me laushin tsiya, har wani lutsawa take yi, daga can ɓangaren rumfa ce tare da kayan marmari a kan wani ƙaramin faranti na gold, daga ganin ɗakin ka san sai matan sarakuna masu ji da mulki gami da dukiya zasu iya mallakarsa, a zaune kan wani kilishi suka sameta, sanye cikin hijab hannunta ɗaya riƙe da chazbaha tana tazbihi.


Ganin yanda Husna ke dafe jikinta ne yasa Fulani faɗin "Husna Lafiya kuwa?"

"Aunty Bilkisu ce ta dakeni?"

"Ina fatar baki yi wani abun ba ko?"

Cewar Fulani tana kallon Gimbiya dan ta san halinta sarai, ɗan yamutsa fuska Afnan tayi kafin ta zauna gefen bed ɗin a hankali ta ce "Mataki na ɗauka daidai da abin da tayi"

Cike da tsoro Fulani ta tashi tana mai kallon Afnan ta ce "Gimbiya me kika yi? kinsan bana son yawan matsala a gidannan ko?"

"Haba Fulani yanzu kina son na zuba ido wata banza ta daki ƙanwata ban ɗauki mataki ba?"

Fita Fulani tayi dan bata ma son jin komi, Afnan kuwa kwanciyarta ta yi tana mai ruff da ciki, sallamar Mubina ne yasa ta ɗan maida kallonta kan ƙofar, cikin girmamawa ta rusuna tare da faɗin "Gimbiya ƙawayenki na jira a waje, sun ce zasu tafi"

"Su tafi mana ba zan iya fita ba" Afnan ta bata amsa tana mai cigaba da kwanciyarta.

A hankali Mubina ta fice dan gudun fushi ya dawo kanta.


A ranar kuwa anga tashin hankali gurin Mama da ƴaƴanta, habaici kuwa kamar daga garesu aka fara, Afnan kam nata ido ne kawai, dan dama bata shiga harkarsu sai idan an taɓo ta, haka washe garin ranar Bilkisu ta koma cike da baƙin cikin abin da Afnan tayi mata, tare da mugun ƙudiri a ranta.


Zaune take kusa da Abbanta sai Hajiya Babba da Fulani da ke gefe, bada jimawa ba Mama ta shigo fuska a haɗe sai harare garki take yiwa ƴan ɗakin, bayan kowa ya natsu ne me martaba ya sanar

Please Login or Register in order to submit comment