Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ke ƴar aiki a gidannan, sai na mayar da ke tamkar karya me neman abincin da zata kai baki" Tana jan jiki ta shige ban ɗaki dan ta sakarwa kanta ruwa babu zancen addu'a haka ta faɗa ciki.


Afan kuwa dama bata yi tsammanin ganin Muby ba, shiyasa ma ƙarfe tara na bugawa ta rufe part ɗinta tare da kwanciya, kiran sallar farko ta farka, sai da ta fara yin wanka kafin ta haɗo da alwala.

Nafila ta fara kafin ta yi sallar asuba, ta jima kan sallaya tana karatu har bacci ya ɗauketa, misalin ƙarfe bakwai ƙarar wayarta ya tasheta, da ƙyar ta kai hannu kan sofa ta ɗauko wayar tana mai karawa a kunne, muryar Muslimat ne ya ƙatse mata baccin nata "Lallai kuwa amaryar Yarima dole ki yi bacci dan jiya Muby ya hana mana ke bacci" Dogon tsaki Afnan ta ja tana faɗin "Meye haka? ko an faɗa miki a nan part ɗin ya kwana, ya ma aka yi kika san na dawo?" Ƴar dariya Muslimat ta yi "Jiya na dawo daga Indian karɓo wani saƙon ta jirgin masauratarku na bi, shine na sauka a gidanku Husna ke faɗa min ai Yarima ya zo bikonki"

"Okay ina Eashat?"

"Tana gida kinsan exams suke yanzu, amma kina aikin me? Yarima be kwana part ɗinki ba a ina ya kwana kenan?" Cike da gajiyawa da zancen Afnan ta ce "Ba zai wuce part ɗin wancan talakar ba, amma ni be dameni ba"

"Ya kamata ya dame ki, kar ki mance cewa mijinki ne, kuma tun da har kin yarda za ki koma dole ki tashi tsaye domin karɓar mijinki ba zama za ki yi ba" Ajiyar zuciya Muslimat ta sauke tana mai cigaba da faɗin "Gimbiya sanin kanki ne babu abin da Yarima ya rasa a rayuwarsa, kama daga kyau dukiya nasaba mulki ilimi, idan har za ki farka daga baccin da ki ke yi ya kamata ki farka, kuma ina son ki sani cewa kina son Yarima kawai yarda da zuciyarki ne ki ka kasa yi"


"Wai meyesa ku ke faɗin ina son Yarima ne? ban taɓa jin ƙaunarsa a raina ba, a kullum tsanarsa ke ƙara darsuwa cikin zuciyata"

"Ban yarda ba Gimbiya" Muslimat ta ƙatseta.

"Ina son ki sani cewar idan har ki ka ƙara fita gidan Yarima wallahi kin bani kunya, ki zauna ki ƙara tunani kuma ki gyara gidanki ki koyawa kanki son mijinki tun da har kin ce ba son shi ki ke ba"

Jin sallama daga ƙasa ne yasa Afnan faɗin "Ina zuwa Babe zan kiraki anjima"

Kashe wayar ta yi tana mai saukowa ƙasa, Jakadiya ce ɗauke da basket ɗin abinci ta jere kan daining, masu aiki duk sun gyara ko'ina sai ƙamshin turaren ƙasar Sudan ke tashi, har ƙasa Jakadiya ta rusuna ta kwashi gaisuwa, ba laifi Afnan ta ɗan sakar mata fuska "Ya su Alhaji da Mommy?" Afnan ta tambaya, bakin Jakadiya har kunne ta ce "Lafiya ƙalau suna gaishe ki, ni zan koma yanzu dan akwai aiki da dama a gabana, dama abinci ne Fulani ta ce a kawo miki"

"To a sauka lafiya, ki cewa Mommy muna godiya da abincin"

"Za a sanar mata insha Allah"
Ficewa daga parlourn ta yi, Afnan kuma ta nufi daining dan yau da sauri take son cin abinci.

Perpesun naman rago ne da indomie wanda ya sha kayan haɗi, sai ɗayan flacks ɗin kunun gyaɗa wanda ya sha haɗuwa, ba ƙaramin daɗi Afnan ta ji ba ganin kunun gyaɗa, dama tana tunanin me zata ci da safennan.


Hankali kwance ta zuba abincin har ta fara ci sai ga wata Kuyangar da take kula da ɓangarenta, "Allah ya ba ki nasara a yi min afwa na zo na zuba miki abincin sai kuma naga har kin gama"

Ko kallonta Afnan bata yi ba ta cigaba da cin abincinta, dole ta sa yarinyar juyawa da niyar barin gurin, kamar daga sama ta ji Afnan ta ce "Meye sunanki?"

Da sauri ta ce "Mandula" Bushewa da dariya Afnan ta yi har da sakin cokalin da ke hannunta, ita kanta ta mance ranar da ta yi dariya irin haka, lokaci ɗaya kuma ta haɗe fuska tare da kallon Mandula ta ce "Sunan mutum ne haka? ko rainin hankali"

Cike da tsoro yarinyar ta ce "Cikakken sunana Shafa'atu amma iyayena suna kirana da Mandula saboda sunan kakarmu aka saka min"

"Okay ai sai ki tafi ko" Cewar Afnan.

Barin gurin Mandula ta yi cikin girmamawa.

Ba wani jimawa ta yi da gama cin abincin ba ta koma tsakar parlourn kan kujera me zaman mutum ɗaya ta kafe, Tv ta kunna dan haka kawai take ra'ayin kallo a halin yanzu, bakinsa ɗauke da sallama ya shigo sanye cikin jallabiya, fuskarsa ta ƙara kyau sosai ga gyaran da sajensa da gashin kansa suka sha, ƙamshin turarensa duk ya baje parlourn, hannunsa na dama na ɗauke da wani troly red, kallo ɗaya ta yi masa tare da ɗauke kai, ganinta cikin ƙaton hijab ne har ƙasa ya bashi mamaki, amma sai ya ƙara haɗe fuska yana mai dire mata troly, "Wannan kayan wanki na ne ina son ki wanke mun su gaba ɗaya kafin na dawo" Kamar yana magana da kurma haka ta yi banza da shi, a tsawace ya ce "Magana nake yi miki, idan har na dawo ba tare da kin wanke min kayana ba za ki sha mamakina" Barin parlourn yayi yana mai buga ƙofar rai ɓace.


Murmushin mugunta Afnan ta saki tana mai tashi ta haura sama da sauri, bata wani jima ba ta fito sanye cikin wando da riga, wandon iyakar cinya, ya wani ɗameta ga uban hips ɗinta da ya fito, sai ƴar ƙaramar rigar da ta tsaya daidai ƙugunta me gajeren hannu, ba ƙaramin kyau ta yi ba mussaman da ta ɗaure gashin kanta a tsakiyar kai, wayarta da ke hannunta ta kunna waƙar larabawa me ɗan karen daɗi, sannu a hankali take bin waƙar har ta sauko inda trolyn ke ajiye.


Ƙwalawa Mandula kira ta yi cike da gadara, da sauri ta fito tana washe baki, "Ranki ya daɗe ga ni"

Kallonta Afnan ta yi tana mai nufar ƙofar fita "Ki biyoni da trolynnan"

A harabar gidan suka tsaya, daidai lambun gidan inda masu aiki baza su iya ganinta ba.

Umarnin komawa ta ba Mandula, tana mai baje kayan a ƙasa, cike da mugunta ta ce "Zan nuna maka yanda ake magana cikin biyayya"

Bayan awa ɗaya, Muby ya fito daga part ɗin Maimun dan zuwa kiran da me martaba ke yi masa, tun daga nesa ya ke hangen kayansa an shanye kamar waɗan da aka ciro cikin caɓo, gabansa ne ya faɗi ganin fararen kayan likitocinsa da yake son sakawa anjima, "Subhanallahi" Ya faɗa yana ƙarasawa gurin, duk kayansa da ya ba Afnan ta wanke sun lalace da caɓo, musamman fararen jallabiyarsa, daga can nesa ya ke jiyo waƙa na tashi a hankali ta cikin lambun, a fusace ya nufi gurin ransa ya masifar ɓaci.


Cakkk ya tsaya ganin Afnan ce tsaye tana mai taka rawa a hankali, sosai rawar ta yi mata kyau musamman waƙar da ke tashi da larabci, ga yanda take bin waƙar kamar tare da ita aka tsara.

Ƙurawa hips ɗinta ido yayi ganin yanda ƙugun nata ke juyawa kamar ana wanashi, wani yawu ya haɗe yana kawar da kai gefe. Afnan kuwa jin kamar tsayuwar mutum a kanta ne ya sa ta juyo a tsorace, ido huɗu suka yi da shi, ya wani zuba mata eyes kamar zai haɗiyeta, murguɗa masa baki ta yi tana faɗin "Lafiya ka tsare ni da waɗannan idanuwan naka kamar me jin bacci" Ƙara waro idon yayi yana mamakin yanda ta yi masa maganar kamar bata yi wani lafin ba, "Bayan kin lalata min kaya da caɓo ne ki ke faɗa min haka?" Sai a lokacin ta tuna laifinta, cike da tsoro ta fara ja baya tana neman hanyar tserewa.




*Afwan Fans rashin typing kullum ayi mun uzuri, kasancewar gajeren labari ne shiyasa nake ɗan ɗaukar lokaci, har yanzu muna bibiyar masu sharing books ɗimmu domin cire wadda ta fi kowa sharing*



*GIDAN MULKI*

*By*


*Asmeetar Hydar*





P. 15



*NA SADAUKAR DA PAGE ƊINNAN GA TEAM ƊIN GIMBIYA AFNAN* 👏







Bakinta na rawa take faɗin "Kar ka matsoni bana son rashin kunya, ni ba sa'arka ba ce"

Ba tare da ya saurareta ba ya fara taku cike da ƙasaita, fuskarsa a haɗe yake watsa mata kyawawan idanunsa masu masifar kyau, "Idan har kika yarda na kamaki za ki sha matuƙar wahala, gara ki kawo kanki tun ban fusata ba"

"Ba zan kawo kaina ba sai ka fusata na gani"

Afnan ta faɗa tana mai tsalle da niyar shigewa ƙofar baya wadda zata sadata da part ɗinta, taku ɗaya ya damƙo ta, ta faɗo ƙirjinsa.

Numfashi suka sauke lokaci ɗaya, wani irin kallo ta watsa masa me kama da meye haka, shima kallon nata yeke ido cikin ido, "Ina rashin kunyar taki ne?" "Ka sake min jikina"

A hankali ya lumshe ido yana mai faɗin "Idan ba haka ba?"

"Ni babu abin da zan yi kawai ka sake min jikina"

Cikin fushi Muby ya ce "Wai ina jikin da ki ke magana ne? ni da nake da Maimun me zan yi da wannan ƙasussan wai jiki" Wani irin ɓacin rai Afnan ta ji, amma sai ta dake tare da sakin murmushin gefen baki "Ai sai ka koma can gurinta ba nan ba"

"Kina tsammanin wani abun zan yi miki? uban wa ya ce ki lalata min kaya da caɓo" Muby ya ƙarasa maganar yana murɗe mata kunne, cikin dauriya ta ɗago idanunta ta sauke kan fuskarsa "Amma ba Ubana ba dai ko?" Zaro ido Muby yayi da mamaki "Sai Uban waye to?" Da ƙarfin tsiya cike da jin zafin matseta da yayi ta ce "Duk yanda ka ɗauka haka nake nufi"

"Me nake shirin gani haka?" Suka ji Maimun na faɗa tana tsaye daga bakin ƙofar Lambun ta wani harɗe hannayenta, daga ita sai pant da bra, ta aza wata munafukar rigar wanka sama, duk jikinta a waje, tana ganin Muby ya juyo ta fara jijjiga jikin nata tana wani irin karairaya, dariya ma abin ya so ya ba Afnan amma sai ta haɗe fuska cikin taku irin na ƴaƴan sarauta ta ƙaraso daidai inda Maimun ɗin ke tsaye, "Wa ya ba ki izinin shigowa part ɗina?" Afnan ta faɗa a gadarance, fari da ido Maimun ta yi tana mai ƙara gyara zaman bra ɗinta ta ce "Gidan mijina ne babu inda za'a mun iyaka" Ɗaga mata hannu Afnan ta yi alamun ta dakata "Kin san da wa ki ke magana kuwa? kina magana ne da Gimbiya Afnan ƴar sarkin sarakai me taƙama da mulki, tun kafin na rufe idona na buɗe bana buƙatar ganin inuwarki a nan"

"Idan kuma ba haka ba.....?" Maimun ta ƙatseta, ai tun kafin ta ƙarasa Afna ta wanke ta da lafiyayyen mari, a haukace ta rarumi wani ƙarfen da ake rufe ƙofar lambun ta nufi Maimun cikin ɓacin rai, Maimun na ganin halaka fili ta runtuma da gudu tana faɗin Gimbiya ta haukace, Muby da ke kallonsu tun ɗazu ba tare da ya amsa ba ne yayi saurin ƙarasowa, ai kuwa Afnan ta buga masa ƙarfen a baya, da sauri ya ja da baya yana dafe gurinda ta dake sa, be gama mamaki ba ya ga ta fara ƙoƙarin cire kayan jikinta tana wasu surutai waɗan da baya fahimta, cikin zafin nama ya cafkota, yana faɗin "Lafiya ki ke kuwa?" Dariya ta fashe da shi tana shafa sajensa "Kamo shi nan, kamo shi nan" Ta rinƙa faɗa tana washe haƙora, ba ƙaramin tashi hankali Muby ya shiga ba, ya kasa gane me ke shirin faruwa shin haukace ko kuma Aljanu ne, ganin babu me bashi amsa ne yasa shi nufar part ɗinta rungume da ita a ƙirjinsa, a ɗakinta ya sauketa, ai kuwa fa fara baje kayan ɗakin tana ihu yeeeee kayan wasa yeeeee kayan wasa, sai a lokacin ya fahimci cewar haukacewa ta yi, innalillahi wa inna ilaihir raji'un kawai yake nanatawa a ransa.


Da gudu da nufosa tana jan hannunsa wai su yi wasa, ƙwace hannun nasa yayi da ƙarfi ya fice daga ɗakin, ai kuwa ta biyosa a baya saurin rufeta daga ciki yayi tare da saka ma ƙofar key, dukan ƙofar Afnan ta shiga yi tana faɗin "Momma ki buɗe mu yi wasa, Momma ina za ki tafi ki barni?" Haka dai ta rinƙa magana ita ɗaya tana wasa da filon da ke kan bed ɗin.



A parlour Yarima ya zauna kan kujera me zaman mutum ɗaya, dafe kansa yayi da ke zafi duk ya rasa abin da ke masa daɗi a halin yanzu, mamaki ne ya ishe shi da kuma al'ajabi, ya jima a haka kafin ya samu natsuwarsa ta ɗan dawo, cikin sanyin jiki ya ƙwalawa Mandula kira, da sauri ta fito tana mai rusunawa "Allah ya ba ka nasara barka da wannan lokacin?"


Fuskarsa a haɗe ya ce "Bana son kowa ya haura saman ɗakin Gimbiya har sai na dawo" Cike da ladabi Mandula ta ce "Insha Allahu za'a kiyaye" Ba tare da ya amsata ba ya fice daga parlourn.

Tun da ya fara driving hankalinsa ke kan Afnan, ya rasa meyesa yake jin gabansa na fuɗuwa, a harabar gidan nasu ya tsaya tare da jingina kansa a kujerar motar, jin ana bubbuga glass ɗin ne yasa shi maida fuskarsa gefen, Ameer ne tsaye da alama school zai tafi "Brother barka da zuwa?"

Marfin motar Ameer ya buɗe masa ya fito jiki a sanyeye, "Brother yau kai ɗaya ka fito, ina Drivern ne?" Nan ma shuru Muby yayi masa yana mai nufar fada, shima Ameer ɗin ya rufa masa baya dan ya san ba lafiya ba.

Tun daga nesa me isar da saƙo ya fara shaidawa Sarki Ahmad zuwan Yarima da Ameer, cike da girmamawa suka shiga bakinsu ɗauke da sallama, gefen Me martaba suka zauna suna kwasar gaisuwa, murmushi Sarki Ahmad yayi kafin ya ce "Yarima lafiya kuwa?"

Ameer ne ya ce "Allah ya ba ka nasara ni kaina ina ganin akwai abin da ke damunsa" Jiki a sanyaye Muby ya ce "Allah ya ba ka nasara akwai maganar da ke tafe da ni amma nafi son mu keɓance" Nan take me martaba ya bada umarnin kowa ya basu guri, sannan ya maida kallonsa kan Muby da shima Abban nasa yake kallo "Ina jinka Yarima me yake tafe da kai? bana son ka kawo min maganar wancan yarinyar dan baza ka aureta ba" Cike da ruɗu Muby ya ce "Allah ya taimakeka dan Allah ku rufa min asiri wallahi ina son Fadila, ku tausaya min da tashin hankalin da ke gabana a yanzu"

"Tashin hankali na me kuma?" Me martaba ya faɗa yana gyara zama.

Hular da ke kansa Muby ya cire yana goge zufan da ya karyo masa, gaba ɗaya ya rasa yanda zai faɗawa Abban nasa maganar.

"Ka yi shuru Yarima me yake faruwa ne?"

"Abba dama Gimbiya ce" Ameer ne ya yi saurin cewa "Me ya sameta Brother?" Wani mugun kallo Muby ya watsa masa yana faɗin "Wai ba na hakana saka baki idan ina magana ba? wannan ya zama na ƙarshe"

Me martaba ne ya ƙatse Muby da faɗin "Ina sauraronka me ya sameta"

"Abba taɓin hankali ne, wallahi lafiya ƙalau mu ke tare da ita da safennan, haka kawai ta hargitse lokaci guda"

"Taɓin hankali?" Me martaba da Ameer suka faɗa a lokaci ɗaya.

Shuru fada ta ɗauka, gaba ɗaya hankalin me martaba ya tashi, lallai wannan ba ƙaramar magana ba ce, tabbas idan ya ce zai faɗawa su Alhaji abin da kefaruwa ba shakka iyayen Gimbiya za su ji labari.

Ajiyar zuciya me martaba ya sauke "Ina son wannan ya zama sirri tsakaninmu, daga ni kai sai Ameer" Kallon Ameer me martaba yayi fuskarsa a haɗe ya ce "Idan har maganar nan ta fita tabbas sai ranka ya ɓace"

Cikin girmamawa Ameer ye ce "Ba zan faɗawa kowa ba Abba"

"Ina ita Gimbiyar ne?"

Sarki Ahmad ya tambaya.

"Abba tana gida na rufeta a ɗaki dan ina ganin kamar zata iya tafiya wani gurin"

Jinjina kai me martaba yayi tare da ɗaukar wayarsa ya danna wata number, babu ɓata lokaci wani Doctor ya shigo sanye cikin fararen kaya, cike da fara'a suka ƙara gaisawa sannan Me martaba ya kallesa cikin fahimta ya ce "Yawwa sannu da ƙarosowa, dama akwai wata da mu ke son ka duba mana, mata ce ga Yarima, dan haka za ku tafi gidansa yanzu domin matar tasa na gida".

"Allah ya ƙara nisan kwana yanzu kuwa insha Allah kuma za'a yi iya ƙoƙari" Tashi suka yi shi da Muby, da sauri Ameer ya miƙe da niyar tafiya tare da su, Sarki Ahmad ya ce "Dawo ka zauna bana son shashanci.

Dole ta sa Ameer zama ba dan yana so ba.

A tare Muby da likitan suka tafi can gidan, tun daga ƙasa suke jiyo ihu da maganganu, Muby ne ya kalli Doctorn yana faɗin "Ina zuwa bari na fara yi mata allurar bacci, ga guri ka zauna"


Haurawa sama Muby yayi, gaba ɗaya ta lalata ɗakin da tarkace babu inda zaka duba da ke tsaftace, tana ganinsa ta nufosa da gudu tare da faɗawa jikinsa "Momma kin dawo? Momma wasa zamu yi" Cike da jin haushi Yarima ya janyeta jikinsa yana mai komawa da ita kan bed, sai kallonsa take tana dariya duk gashin kanta ya hargitse, tana ganin ya ciro allura a gaban rigarsa ta fara matsawa baya tana ƙaƙalo hawaye "Momma zafi Momma bana so" Sai da ya gama haɗa allurar sannan ya aje gefe, murmusin ƙarfin hali ya sakar mata kafin ya ce "Zo ƴar Momma ba zan yi miki ba, zo mu yi wasarmu" Girgiza kai ta yi alamun baza ta zo ba, Muby na ganin haka ya damƙota da ƙarfi ya mannata ka bed, ihu ta rinƙa kurmawa tana ƙoƙarin ƙwace kanta amma ya danneta da dukkan ƙarfinsa, lokaci ɗaya jikinta ya sake, allurar ya yi mata tare da jinginta kan ƙirjinsa yana bubbuga bayanta, da ƙarfi ta jaye jikinta tare da faɗuwa ƙasa tana birgima kamar ƙaramar yarinya sai ihu take tana faɗin "Wayyyo Momma zafi Wayyyyooo Momma zafi" Mintuna biyar ta samu kafin baccin ya ɗauketa, toilet ya nufa da ita dan ganin jikinta duk ya ɓaci, kayan jikin nata ya fara cirewa, wani yarrrrr gaba ɗaya sassansa suka yi, dama ba kayan arziƙi ne a jikinta ba, da ƙyar ya samu damar yi mata wanka duk sai da ya taɓe mata jiki kaɗan ya rage ya afka mata amma sai ya danne duk wani Feelings tunawar da yayi Doctor na jiransa, shiryata yayi cikin wata doguwar riga tare da fesheta da turare, sannan ya saka mata ƙaton hijab ya nufi nasa ɗakin da ita.


Kan bed ɗinsa ya kwantar da ita sannan ya koma parlour suka taho da Doctor.

Dubata ya fara yi kafin ya yi mata wasu allurori, Muby ne ya ce "Me yake damunta?"

"Gaskiya duk iya duban da nayi banga wani abun da ke damunta ba, ina tsammanin Aljanu ne amma be shafi ƙwaƙwalwarta ba, insha Allah idan ta farka zata dawo daidai"
Godiya Muby ya yi sannan suka sauko ƙasa, umarni ya ba Driver da ya mayar da Doctor.

A hanyar komawa part ɗinta suka ci karo da Maimun zata fito cikin shigar ƙananan kaya da jaka rataye a kafaɗarta alamun fita zata yi.

"Gidan Uban wa za ki tafi da wannan shigar?"

A tsorace Maimun ta ce "Gida zan tafi Mom bata da lafiya"

"Koma ciki babu inda za ki tafi"

"Baby dan Allah......"

"Ki koma ciki bana son shirme"

Yana gama faɗin haka ya bar gurin, tana ganin ya shige part ɗin Afnan ta fice daga gidan.


...............
A ɓangaren Fadila kuwa ta kasa samun natsuwa duk lokacin da zata kira Muby baya ɗagawa, wani lokacin kuma wayar tasa a kashe, gaba ɗaya zaman gidan ya daina yi mata daɗi tun da Mahaifiyarta ta bar gidan, yau ma zaune take a lambu kan kilishi tana kurɓar Jus a hankali, daga nesa ta fara jiyo surutu, tun kafin ta tashi ta hangi ƙawarta Nabeela kamar wadda aka ciro daga gidan mahaukata ko gabanta bata kallo.

Da matuƙar mamaki Fadila ta miƙe daga zaunen da take "Nabeela.....dama kina raye?"

Dariyar takaici Nabeela ta yi kafin ta ce "Tabbas ina raye kin yi mamakin ganina ko?"

Cikin alamun rashin gaskiya ga duk zufa ta wanke mata jiki ta ce "No that's not posible, ƙarya ne Nabeela kin mutu kin riga da kin baƙunci lahira ta yaya wanda ya mutu zai dawo?"

Wata irin mahaukaciyar dariya Nabeela ta yi wadda ta sa Fadila faɗuwa ƙasa cikin tsananin tsoro, da yatsa Nabeela ta nunata idanunta duk a waje ta ce "Ki yi gaggawar sanar da kowa abin da kika aikata, ki faɗawa mutane sarƙaƙiyar da aka ƙulla idan ba haka ba ni ce zan zama ajalinki" Cikin tsawa Nabeela ta ƙarasa maganar tana bushewa da dariya, cike da tsoro Fadila ta rufe idanunta tare da toshe kunnuwanta, tashin hankalin da take ciki ya gama hargitsata a ruɗe ta ɗago amma bata ga kowa ba, dube-dube ta fara amma babu alamun Nabeela a gurin, ai da gudun tsiya Fadila ta koma cikin gidan, ba Mahaifinta ba hatta mutanen da ke masarautar hankalinsu ya tashi, Fadila kuwa ta kasa tsayawa guri ɗaya, daga mutane sun matsa za su kamata zata ƙara runtumawa da gudu tana faɗin "Wayyyyo kuna ganin zata kasheni, Dad please help me i don't want to die now" Da ƙyar a ka samu damar riƙeta tare da nufar ɗakin nata da ita, sai da Fadila ta samu natsuwa kafin aka barta daga ita sai Dad ɗin nata, shima duk ya jiƙe da gumi, a hankali ya ɗagota daga kwancen da ke duk idanunta sun zazzaro "Sannu Shalele ya ki ke jin jikin naki?"

"Dad please ka fice bana son damuwa"

Miƙewa yayi da sauri yana faɗin "Shikenan anjima idan kina son magana da ni sai ki aika a kira ni"

Ba tare da ta amsa masa ba ta kawar da kai gefe tana tura baki, ficewa daga ɗakin Dad ɗin nata yayi yana mai kallonta.

..................
A ɓangaren Muby kuwa yana shiga parlourn ya kira Mandula tare da bata umarnin gyara ɗakin Afnan, cikin biyayya ta nufi ɗakin domin cika umarni.

Kamar yanda ya barta haka ya sameta tana bacci, a gefen bed ɗin ya zauna dan baya jin zai iya zuwa Hospital ya barta a gida, ya ɗan jima sosai a zaunen kafin ya miƙe tare da shigewa toilet dan sakarwa kansa ruwa, kusan mintuna talatin ya fito ɗaure da pink tawul me laushi a ƙugunsa, sai ɗan ƙarami a hannunsa yana tsane gashin kansa, kan kujerar da ke gaban makeken mirrown ya zauna kafin ya fara shafa wani ƙayataccen mai me laushi, gashin kansa kuwa sosai ya gyara shi, tare da feshe jikinsa da turarukka masu daɗin ƙamshi, haɗaɗɗen wadrop ɗin glass ɗin da ke gefe ya buɗe, tsafff ya shirya cikin gajeren wando da T-shert, ya masifar yin kyau musamman da wandon ya tsaya masa daidadi gwuiwarsa, sai ƙafar tasa ta wani haɗewa kamar hasken tauraruwa, nishin Afnan ne ya sa shi maida kansa gefen, har ta iso ƙarshen bed ɗin tana ƙoƙarin faɗuwa, da sauri ya matsa gurin tare da jaye kilishin da ke ƙasan tsabagen mugunta, ai kuwa tana faɗawa da buga kanta a tiles, murmushin mugunta ya saki yana faɗin "Bana tsammanin rashin lafiyarki zai sa na tausaya miki"

Afnan kuwa duk da cewar tana cikin allurar bacci amma sai da zafin ya ratsa ta, daga cikin baccin ta ce "Washhhh......, Momma zafi"

"Washhhhhh.... Momma zafi, ai wannan ma kaɗan ki ka gani, duk ina

Please Login or Register in order to submit comment