Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda ya isa ya maida ki" Murmushin yaƙe ta yi masa ba tare da ta ce uffan ba, Fulani ce ta ce "Gimbiya yau ke ce ki ke kuka? akwai wata matsala ne ki faɗa mana domin sanin abin da ya kamata mu yi" "Babu wata matsala Fulani" Afnan ta faɗa a taƙaice. Kukan da take riƙewa ne ta fashe da shi kamar wadda iyayenta suka mutu, sosai take kukan dan jin yanda zuciyarta ke ƙuna, ba ƙaramin tausayinta suka ji ba ganin yanda ta dage take zabga kuka, rarrashinta Alhassan ya shiga yi har ya samu ta tsagaita, cikin muryarta da bata fita sosai ta ce "Wallahi bana son komawa gidansa, kawai biyayya nayi amma baya sona shima, Brother ka san me? saboda wata banza ya sakeni fa dan kawai yana sonta shine zai wulaƙantani a gaban mutane" Sosai tausayinta ya kama Alhassan dan ganin tsantsanar soyayyar Yarima kan fuskarta amma ta kasa yarda da abin da take ji game da shi.

"Ki yi haƙuri please ki daina tuna abin da ya wuce insha Allah ba zai sake maimaita abin da yayi ba"

Kwantar da kanta ta yi kan kafaɗarsa tana sauke ajiyar zuciya, nasiha Fulani ta yi mata me ratsa zuciya sai abin ya zo mata kamar sabo ganin take idan ta koma gidansa ba za ta sake dawowa ba, murmushi ta yiwa Fulani tare da kama hannunta "Insha Allah Fulani zan kasance me biyayya ga duk wani abin da ya zama haƙƙi a kaina"

Itama murmushin ta yi tana faɗin "Allah ya bada iko" Da Ameen su Ahassan suka amsa.

Ƙarfe shida aka fito dan tafiya ƙasar Sudan, sanye take cikin wata abaya milk colour me shegen kyau, ga wasu irin flowers da ke gaban rigar ruwan gange kalar ɗan ƙaramin mayafinta, ba ƙaramin kyau ta yi ba musamman kwalliyar da ke fuskarta simple makeup ne amma ya amshi haɗaɗɗiyar fuskarta, har part ɗin me martaba aka nufa da ita wanda hakan umarnin Hajiya ne, sosai yayi mata nasiha me ratsa jiki, sai yau take jin kamar za'a rabata da kowa nata, Mama kam sai harare-harare take ganin yanda su Alhassan suka fito cikin wasu masifaffun kayan sarauta ba ƙaramin kyau kayan suka yi musu ba, cike da munafurci ta fara yiwa Afnan nasiha kamar zata sauke mata Alqur'ani, har mamakin yanda take zuba magana kowa da ke ɗakin yake.

Me martaba ne ya ce daga Alhassan sai Hajjo zasu yi mata rakiya, haka ko aka yi jirgin masaurautar ne suka bi zuwa ƙasar Sudan, ƙarfe bakwai ta yi musu ne a garin, dirrect masarautar suka nufa, kasacewar an san da zuwansu ne yasa aka baza musu babar tarba tare da karramawa, a part ɗin Muby a ka sauke Afnan, sai su Alhassan da Hajjo da suka sauka part ɗin Mommy, Ameer kam sai wani shigewa Alhassan yake dan ya ji labarin ɗan'uwan Gimbiya ne, duk da cewar Mommy na jin haushin dawowar Afnan amma hakan be hanata karrama su Hajjo ba, haka Sarki Ahmad ma ya sakar musu fuska tare da nuna farincikin ganin Alhassan dan labari ya same shi kan dawowar yaran.

A ranar Alhaji ya sa Jakadiya tura Kuyangi da a gyara gidansu Gimbiya dan gobe zata tare, masu gyaran gidan su goma ne aka tura da safe za su fara aikin kafin a kai Afnan.


Muby da ke bakin ƙofar part ɗinsa ne ya ji wayarsa na ƙara, ƙofar parlourn ya buɗe bakinsa ɗauke da sallama, ba kowa a ciki sai sanyin A C da kuma Tv da ke kunne, a hankali ya zauna kan sofa dan ya gaji sosai, wayarsa da ke ƙara ya ciro gaban aljihun rigarsa, missed calls uku ya gani na Fadila har zai kira kuma ya sake ganin wani kiran ya shigo, sai da ta kusa yankewa ya ɗaga tare da yin shuru, daga can ɓangeren itama shurun ta yi cike da jin haushi, kusan mintuna uku ba wanda ya yi magana dan dole ta sauke ajin nata muryarta a shagwaɓe ta ce "Dear baza ka yi magana ba ne?" Banza ya yi mata kamar bada shi take ba, cigaba ta yi da faɗin "Wai laifin me nayi haka? a daina fushin haka ya isa"

Kamar me jin bacci ya ce "Ke kuma ba ki iya sallama ba balle gaisuwa"

"Sorry Dear na sha'afa ne ya hanya?"

"Sallamar kuma fa?" Ya ƙara katseta yana ɓata fuska kamar tana ganinsa.

A gajiye ta ce "Assalamualaika" "Waalaikissalam"

"To yanzu ka daina fushin ko?"

"Zan shiga wanka idan na fito zamu yi magana" Be jira abin da zata ce ba ya katse wayar.

Tashi yayi daga zaune da yake ya nufi bedroom ɗinsa, da mamaki yake kallon ƙofar jinta a rufe, kaɗan-kaɗan yake jin maganar Afnan da alama waya take har da dariya kamar wadda aka yiwa albishir da Aljanna.

Cikin gajiya da magana ya ɗan ɗaga murya yanda zata ji shi ya ce "Malama ki zo ki buɗewa mutane ƙofa kamar wani gidanki" Sarai ta ji abin da yake faɗa amma ta sharesa, ya jima sosai yana magana amma kamar bada ita yake ba daga ƙarshe ma shuru ya ji alamun bacci ya ɗauketa, ga kiran Fadila da ke shigowa akai-akai, ba shiri ya kashe wayar gabaaya yana mai shiga ɗayan room ɗin a hasale.



*INA MAI BA KU HAƘURI DA RASHIN TYPING KWANA BIYU BANA SAMUN LOKACI NE*




*GIDAN MULKI*


*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 14




*WANNAN PAGE ƊIN NA TEAM ƊIN GIMBIYA AFNAN NE, KU YI YANDA KU KE SO DA SHI, IDAN KUN SO MA KU HANA KOWA KARANTAWA INA YINKU OVER*




................................................................
A ɓangaren Maimun kuwa Ameera ce ta sanar da ita Muby ya dawo da Afnan, tun da labari ya sameta ta kasa zaune ta kasa tsaye, gate ɗin gidan ma rufewa ta saka ayi dan ta yi tsammanin a nan gidan za a kawota a daren, amma sai ta ji shuru babu alamun zuwansu, ta jima sosai a parlourn jiran motsin masu kawo Afnan amma har bacci ya fara ɗaukarta, kusan ƙarfe goma na dare ta farka a gigice saɓanin mafarkin da ta yi na Fadila na ƙoƙarin caka mata wuƙa ita kuma tana gudu cikin ƙasurgumin daji, can sai ga Afnan ta ƙaraso da wani farin doki cikin shigar abaya fara me kyau, ba tare da ɓata lokacin ba ta kama hannun Maimun ta ɗagota saman dokin suka bar jejin.

Sosai Maimun ke zufa dan ta tsorata da mafarkinnan da ta yi, da sauri ta haura sama tana mai ɗaukar wayarta da ke kan mirrow ta danna kiran Hajara, har sai da wayar ta ɗauke amma ba alamun za'a ɗaga. nan ma ta shiga kiran layin Muby amma a kashe, cike da takaici ta aje wayar tana mai kwanciya kan bed a tsorace.

Ba wani bacci ta samu ba shiyasa ma tun asuba ta farka, dama ba sallar take ba wanka kawai ta shige a gaggauce, ta jima tana kwalliya har haske ya fito lokacin ƙarfe tara na safe, a parlourn ta sami masu aiki ana faman gyara ko'ina kamar zata tambayesu kuma sai ta fasa, daining ta nufa inda ƙayataccen abinci ke zube kamar ana wani bikin, cikin ɗaga murya ta ƙwalawa ɗaya daga cikin masu aikin kira "Kee uban waye ya dafa abinci haka da yawa kamar masu shirin gayyato mutanen unguwa"

"Afwan Aunty Maimun dama Jakadiya ce ta ce a shiryawa su Yarima abinci za su shigo da safe" Tun kafin ta ƙarasa maganar suka fara jiyo ƙarar motoci, "Je ki leƙa mun su waye, kuma wa ya bada umarnin a buɗe gate bayan na hana"

Fasa cin abincin ta yi ta fice tana kaɗa jiki kamar zata karye, motoci ne kusan hamsin a harabar gidan a can nesa ta hangi matashin yaro me kama da Afnan, a bayansa Yarima ne da su Ashwan suna dariya ai bata ƙara sarewa ba sai da ta ga su Mommy da Me martaba har ma da Alhaji Babba sun fito mota, Afnan na gefen Hajjo sanye cikin wani ɗanyen less me masifar kyau golding colour, ba ƙaramin haɗuwa ta yi ba fuskar ta a haɗe kamar kullum, cike da gadara take taka ƙasa kamar me tausayin ƙasar, daga nesa Maimun ta tsinkayo muryar Ameer na faɗin "Aunty Maimun ƙaraso mana ga Gimbiyar kyawawa ta duniya ta dawo gidan Yarima ai sai ki zo tarbar uwargida sarautar mata, ƴar gaban goshin Yarima me taƙama da mulki gami da sarauta" Ameer ya ƙarasa maganar cike da mugunta.

Kamar Maimun zata rusa ihu haka ta iso tana dariyar yaƙe, gaishe da su Me martaba ta yi tare da kama hannun Afnan, a fusace Afnan ta ƙwace hannunta cikin gadara ta ce "Are you okay? wannan ya zama na ƙarshe da za ki taɓani da ƙazamin hannun nan naki kina jina ko?" Afnan ta faɗa tana mai nufar part ɗinta cike da taƙama.


Mommy ce ta ce "Mu ƙarasa daga ciki mana" Gaba ɗayansu part ɗin Afnan suka shige aka bar Maimun tsaye fuskarta ta cike da ɓacin rai ganin wulaƙancin da Afnan ta yi mata kuma babu wanda ya tanka.

Ba tare da tunanin abin da zai faru ba ta bi bayansu har parloun, a nan ta same su zaune an baje musu kayan abinci wanda ya ninka nata kyau da haɗuwa, kasancewar Afnan na shigowa ta haura ɗakinta ne yasa Maimun bata ganta ba, gefen Muby ta zauna haɗe da makirci ta ce "Baby sannu da gajiyar hanya" Shuru yayi kamar bada shi take ba, ƙara matso shi ta yi tana faɗin "Magana nake ka yi shuru" A gajiya ya ce "Lafiya malama ki matsa daga nan ko bakya ganin su Alhaji ne?"

"Amma ai kai mijina ne?" "Dan ina mijinki shine za ki nuna rashin kunya gaban iyayena?"

"Haba Baby to ai ba laifi ba ne, kana ganin ko sanar da ni tafiyar nan da zaka yi ba ka yi ba amma har ka ke min faɗa dan na zauna kusa da kai"

Ajiyar zuciya ya sauke dan ya san be kyauta ba a matsayinsa na miji haƙƙine a kansa ya sanarwa matarsa batun tafiyarsa, "Shikenan na ji nayi laifi amma yanzu ki koma part ɗinki zan shigo anjima"

"Amma yau part ɗina za ka kwana ko?"

"Tun da ke ce kika fi kowa, tun yaushe Gimbiya ta bar gidannan kin riƙe miji shine yanzu ba kunya za ki ce part ɗinki zai kwana" Cewar Ameer da ke sauraronsu tun ɗazu kasancewar yana kusa da ita Maimun ɗina.

Muby ne ya ce "Kai wai wanne irin marar kunya ne? ka yi ma Fadila yanzu kuma ka dawo kan Maimun, kai idan har ba Gimbiya ba kowa ma ba ka so, tashi ka fice tun kafin ranka ya ɓaci" Ameer na tura baki ya koma gefen Alhaji ya yi zamansa, Maimun kam kamar zata yi kuka ta bar part ɗin.


Muby da ke zaune ne wayarsa ta fara ƙara, Yusuf ya yi saurin kai hannu ya ɗauka dan ya san me kiran, tun ɗazu ta dame su da kira kamar mayya, Fadila da duk hankalinta ya tashi tana jin an ɗaga wayar ta fara magana kamar zautatta "Dearna please me nayi maka ne? tun jiya fa ka kashe wayarka yau kuma na rinƙa kira tun asuba amma ba ka ɗaga ba" Carafff Yusuf ya karɓe zancen "Wai ke mayya ce Fadila? wannan bawan Allah ya dawo da matarsa ki bari ya huta mana, yanzu haka muna gidansa an kawo uwargida zuwa anjima kwa yi magana" Ɗiffff ya kashe wayar yana jan tsaki, Ashwan ne ya bushe da dariya "Lallai Yusuf ba ka da dama, yanzu Fadilar ce ka ke ma ihu haka? shi kansa Yarima baya yi mata faɗa balle kai"

Harara Muby ya gallawa Ashwan yana kawar da kai gefe.

Su Hajjo kam sai ƙarfe biyu suka fito da niyar tafiya gida dan daga can zasu koma Senegal, Afnan da ke rungume da Alhassan ne ta ɗago jajayen idanunta da duk sun rine da kuka, "Brother dan Allah ka yi mun kwana biyu before ka koma"

"Kwana biyu fa? kina amaryar a a gaskiya zan rinƙa zuwa ina duba ki amma ba zan kwana a gidanki ba" Turo baki ta yi tana dukansa a ƙirji, "Ni gaskiya gobe zan shigo naga su Fulani" Dariya Hajjo da ke gefe ta yi "Ƴan nema kai, waye zai barki ji dawo gida yanzu, ai sai kin haihu zamu zo wankan jego"

Hawaye Afnan ta share tana ɓata fuska dan ji take kamar ta bisu, da ƙyar Alhassan ya rarrasheta ta suka bar gidan a kan cewa za'a turo mata Mubina bayan kwana biyu. Da gudu ta koma part ɗinta, a parlour ta zube tana rusar kuka kamar wanda aka yiwa mutuwa, Muby da su Ashwan kuwa a lambu suka zauna domin tattaunawa kan maganar Fadila, sai bayan sun yi sallar ƙarfe huɗu ne suka bar gidan shi ko Muby ya nufi part ɗin Maimun. Babu inda be duba ba amma babu ita babu alamunta, kan kujera ya zauna tare da ciro wayarsa ya fara latsawa, kusan mintuna ashirin a haka sannan ya ji shigowar mutum, wani kallon tuhuma ya watsa mata yana mai cigaba da latsa wayar tasa, ganin be kulata ba ne yasa ta nufi room ɗinta, "Gidan wa ki ka fito?" Wani irin murɗawa cikinta ya yi kamar zata saki fitsari ta ce "Ammmm...ammmm Hajara ce ta shigo shine na raketa bakin gate"

"Bakin gate har mu ka yi sallah a masallaci mu ka dawo kina bakin gate?" Muby ya faɗa hankalinsa na kan wayarsa,

"A a dama mun shiga kasuwa ne ta siyo wani abu mamanta ta aiketa, already akwai abun da nake son na saya a kasuwar shiyasa ma na tafi"

Shuru yayi yana mai nazarin kalamanta tabbas babu gaskiya a ciki, kusan mintuna uku tana tsaye, shi be ce ta wuce ba kuma be ce ta tsaya ba, cike da gajiya ta nufi sama shima be dakatar da ita ba dan baya son surutu.



.......................
A ɓangaren Fadila kuwa jin abin da Yusuf ya ce mata ne yasa ta tashi da sauri ta nufi fada gurin Mahaifinta, ko jiran me isar da saƙo bata yi ba ta faɗa ciki tana mai fashewa da kuka, ganin haka yasa Me martaba umartar mutane da su basu guri zai yi magana da ƴarsa, bayan kowa ya fita ne ta zauna gefensa tana mai cigaba da kukanta "Shalele waye ya taɓa ki? kinsan bana son wannan kukan naki"

"Dad dan Allah ku je neman aurena a gidansu Yarima idan har ba so ku ke na kashe kaina ba" Saurin rufe mata baki yayi yana faɗin "Daina faɗin haka ina Mom ɗin naki take"

"Ai ka san cewa baza ta goyi bayana ba Dad shiyasa ma na zo gurinka ni yau nake so a saka mana rana"

Cikin sanyin murya ya ce "Ai abin da za ki duba shine maza ne ke zuwa neman aure Shalele, idan har yana sonki shine zai zo ya nemi aurenki da iyayensa" "Amma Dad Mahaifinsa ya ce ba zan auri ɗansa ba wai bana da tarbiya"

"In ji waye? dole sai kin auri Yarima ki kwantar da hankalinki tun da har yana sonki ke ce za ki sa ya shigo neman aurenki"

Kuka Fadila ta ƙara fashewa da shi tana bubbuga ƙafa "Dad kamar Dear ya daina sona a gabansa abokinsa ya zageni fa"

"Ki daina wannan kukan haka zan yi magana da Mahifin nasa ta waya"

Hawayen ta share tana mai cewa "Shikenan Dad nima zan ce ma Dear ina son a saka ranar auren"

"Yawwa Shalele Allah yayi miki Albarka" Ba tare da ta amsa ba ta fice daga fadar ranta duk ba daɗi.

A babban parlour ta sami Mahaifiyar tata zaune kan kilishi sanye cikin kayan alfarma,Jakadiya na yi mata tausa, ba ko sallama ta zauna tana mai faɗin "Ke fita ki bamu guri zan yi magana da uwata" Cike da girmamawa Jakadiya ta fice, ko kallon inda take Fulani bata yi ba ta cigaba da tauna tufar da ke hannunta, "Mom kamar ba ki ga shigowata ba"

Rai ɓace Mahaifiyar tata ta ce "Fadila bansan me yake damunki ba, ki sani cewa wannan halin da kike yi be dace ga macen kirki ba, a kullum ina faɗa miki sallama yana da kyau ko da ma a ce babu kowa a guri"

Cike da rashin tarbiya Fadila ta ce "Ni kuma sallamar a gareni ba dole ba ce"

"Allah ya shiryeki" Fulani ta faɗa tana mai ƙoƙarin tashi daga kishingiɗen da take.

"But Mom magana na zo mu yi amma kina ƙoƙarin tashi" "Saboda naga rashin tarbiyar da ki ke wa uban naki kina son kawo min nima"

"Shikenan na ji ki yi haƙuri, dama ni maganar Dear ne please Mom wallahi zan iya mutuwa idan ban same shi ba"

"Idan ki ka mutu sai me?" Fulani ta daka mata tsawa rai ɓace ta cigaba da faɗin "Ban taɓa nadamar haihuwarki ba sai yau Fadila, tun da ki ka fara wayo nake fama da rashin tarbiya da ƙunci da ki ke sani, wallahi tun kina da sauran lokaci ki zama macen kirki tashi ki fice min daga ɗaki"

A fusace ta miƙe tana harare-harare tare da ficewa.


Tun da ta rufe kanta ɗaki bata fito ba har yamma, ba ƙaramin tashi hankalin me martaba yayi ba da Jakadiya ta sanar da shi Fadila ta rufe ɗaki tun rana bata ci abinci ba kuma ta hana kowa shiga, a ruɗe ya nufi part ɗin tare da tura ɗakin amma a rufe, daga ciki yake jin yanda take faffasa kwalabe kamar wadda ta zare sai surutai take, "Shalele dan Allah ki buɗe room ɗinnan idan har kina son farinciki na"

"Dad bana son ganin kowa a halin yanzu just go please if not i'll kill my self"

Fulani da ta ƙaraso gurin cike da ɓacin rai ta ce "Idan har ba ki kashe kanki ba sunanki ba Fadila ba, a rayuwarki kin fi son ganin ran kowa ya ɓaci"

Marin da me martaba ya ɗauketa da shi ne yasa gaba ɗaya masu aikin gidan da ke gurin sunkuyar da kansu suna barin gurin cike da mamaki, a tsorace Fulani ta ɗago tana kallonsa "Ka mareni saboda ƴarka? dan kawai ina faɗa mata gaskiya"

A tsawace me martaba ya ce "Gaskiyar banza, ki tattara kayanki ki koma gidanku sai na nemeki, dan zan iya yin komi a kan ƴata"

Fulani da hannunta ke kan kuncinta ta sauke a hankali ta ce "Shikenan zan tafi amma ka sani cewa daga kai har ƴar taka sai kun yi kuka marar iyaka, idan har wannan ce tarbiyar da zata zauna a kai" Tana ƙarasa faɗar haka ta bar gurin ranta na masifar zafi.

Sai a lokacin Fadila ta fito tare da faɗawa jikin Mahaifinta, rarrashinta ya shiga yi amma ina sai surutai take kamar wadda aljanu suka shafa, gaba ɗaya ɗakin ta hargitsa shi kayanta duk ta baje su har ta yanki kanta a hannu.

Da sauri Me martaba ya sa aka nufi Clinic ɗin da ke masauratar da ita.


Waya ya ɗaga yana mai danna numbern Sarki Ahmad.

A lokacin sun dawo daga rakiyar su Alhassan airport, wayarsa da ke gaban aljihun Alkyabbar da ke jikinsa ne ta fara ƙara, sannu a hankali ya ɗaga tare da sallama, jin wanda ke magana ne yasa shi ɓata rai kamar yana ganinsa, sama-sama suka gaisa kowa da abin da ke ransa, Sarki Ahmad ne ya ce "Ina fatar lafiya dai wannan kira haka da yamma?" Dad ɗin Fadila ne ya ce "Ba lafiya ba tun da saboda ɗanka ƴata na ƙoƙarin kashe kanta"

Da sauri Sarki Ahmad ya ce "Subhanallahi garin yaya hakan ta faru?"

"Wannan kuma kai zan tambaya saboda kai ne ka ce baza ka aura mata Yarima ba, ina mai tabbatar maka cewa idan har wani abun ya sami Gimbiya wallahi sai ran kowa ya ɓaci" A fusace Sarki Ahmad ya ce "Wannan ai zacen banza ne, babu wani mahaluƙin da ya isa ya haɗa aurennan kuma idan kana musu mu zuba" Ba ƙaramin cacar baki suka yi ba, dan Dad ɗin Fadila yana iya yin komi a kan ƴar tasa tilo, daga ƙarshe kowa ya kashe wayar cike da ɓacin rai.


Sarki Ahmad kam ransa ɓace ya isa gida ɓangaren Alhaji ya nufa, a ɗakinsa ya same shi zaune yana karanta wata jaridar hausa kan abubuwan da ke faruwa a ƙasar, da sallama ya shiga tare da gaishe shi cikin sanyin jiki ya samu guri ya zauna, fuskar Alhaji ɗauke da murmushi ya ce "Sannu da dawowa Ahmad kun raka su lafiya"

"Allah ya ba ka nasara lafiya ƙalau, amma akwai maganar da nake son nayi maka idan ba damuwa"

"Ina jinka wace magana ce haka?"

Zama Sarki Ahmad ya gyara cike da ɓacin rai ya ce "Batun auren Yarima da Gimbiya Fadila ne, yau Mahaifinta ya kirani tare da faɗa min maganganu marassa daɗi dan haka zancen auren an fasa, babu wanda zai karya wannan dokar ko bayan raina ban amince Yarima ya aure ta ba"

Alhaji ne ya ce "Ni kaina lamarin yarinyar yana ɗaure min kai gaba ɗaya bata da tarbiya, hukuncin da ka yanke shine daidai idan Yarima ya shigo sai a sanar masa dan ya faɗa mata gaskiya"

Sosai suka tattauna kan maganar da kuma yanda za su ɓullowa lamarin.


A gefensu Muby kuwa yana zaune a parlourn har magrib, tun da Maimun ta shiga bata fito ba tsoron kar ya ƙara yi mata tambaya, masallacin da ke unguwar ya nufa sai bayan sallar isha ya shigo gidan, ɓangaren Maimun ya shiga dan yayi mata sallama, be samu kowa a parlourn ba ya haura sama, daga bakin ƙofar ɗakinta yake jiyo wani sauti wanda ya kasa gane na menene, har zai koma sai kuma ya fasa yana mai tura ƙofar, jin ƙofar a rufe ne yasa shi kiran sunanta da ƙarfi, "Kina ina ne? ki zo ki buɗewa mutane ƙofa, kin wani rufe kamar gidanku" Jin shuru ne yasa shi ƙara dukan ƙofar, daidai lokacin da Maimun ta buɗe ɗakin, wani irin ɗaukewa numfashinsa ya kusa yi ganinta ɗaure da tawul iya cinya ga jikinta duk ruwa alamun daga wanka ta fito, Maimun kuwa sarai ta san cewa sallama ya zo yi mata, saurin kawar da kai yayi yana ɓata fuska "Ni zan tafi sai da safe" Tun kafin ya gama rufe baki ta shige jikinsa tana mai ƙanƙame shi, "Baby please ba zan iya jurar ganinka da wata macen ba, dan Allah ka kwana a nan" Ƙoƙarin janye jikinsa yake amma ina ta shige masa ga wani mugun Feelings da ke taso masa, tawul ɗin jikinta ta saki tana kashe masa ido, gaba ɗaya natsuwarsa ce ta fice lokaci ɗaya, saurin damƙo ƙugunta yayi yana mai haɗe bakinsu guri ɗaya, wani gantsarewa ta yi kamar wadda ke shirin tashi sama, ba shiri ya ɗagata zuwa cikin ɗakin tare da rufe ƙofa da ƙafarsa, kamar wata mayya haka Maimun ta zamar masa, duk da cewar tana jin zafin amma haka ta rinƙa biye masa dan kar ya wuce part ɗin Afnan, kusan asuba ana abu ɗaya amma Maimun ta kasa barinsa shi ko Muby dama ba kanwar lasa ba ne, daga ƙarshe dai kuka ta fashe masa da shi tana mai neman hanyar gudu amma be saurara mata ba sai asuba, sallar asubar ma a gida yayi sannan ya shige ɗakinsa dan rama baccin da be samu ba.


Yana fita Maimun ta saki shewa tana mirginawa kan bed, a fili ta ce "Kaɗan ki ka fara gani, Gimbiya ne sunanki ko wacece, sai na mayar

Please Login or Register in order to submit comment