Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka taho da matarka" Alhaji ya ƙarasa maganar yana dafe saitin zuciyarsa, da sauri me mertaba ya matsa kusa da shi yana faɗin "Sannu Alhaji" Ɗaga shi me martaba yayi tare da kallon Muby ya ce "Ka tabba cewa ka tafi ƙasar Senegal gobe, idan har ba fushina kake son gani ba" Hannun Alhaji ya kama suka bar ɗakin, tun da suka fita yake dafe da kansa wanda ke sara masa, ko sunan ƙasar aka kira wani zafi zuciyarsa ke yi balle ace matarsa.

Cike da dauriya ya miƙe dan sakarwa kansa ruwa.

Daga jiyan zuwa yau Mommy ta canza gaba ɗaya ta daina sakarwa Me martaba fuska, Alhaji Babba ma gaisuwa ce kawai ke haɗasu, misalin ƙarfe sha biyu na rana ya fito cikin shirinsa na manyan kaya wani ɗanyen yadi ne blue ya masifar ɗaukar jikinsa, gashin fuskarsa da na girarsa kuwa an gyara su tsaff, sai wani ƙyalli fuskar tasa ke yi.

A kansa hula ce kalar Alkyabbar jikinsa me kyau, hannunsa kuwa agogo ne wanda ya haɗe sosai da shigar jikinsa, fuskar nan tashi tamau babu alamar dariya, rabonsa da ganin Ashwan da Yusuf tun bayan da aka rufesa, a harabar gidan ya samesu cikin shigar manyan kaya, tun daga nesa suke yi masa dariya ƙasa-ƙasa musamman Ashwan da har wani noke kai yake, ko kallon inda suke be yi ba ya shige wata arniyar mota ƙirar Loxes me masifar kyau tana ɗauke da tambarin YARIMA GIDAN MULKI, motoci ashirin ne waɗan da zasu yi masa rakiya zuwa airport, Ashwan da Yusuf ma tasu motar suka shiga nan take motocin suka bar gidan, duk ta inda suka ratsa sai dai kaga ana kallonsu tare da basu hanya, har suka isa babban airport na garin, bada ɓata lokaci ba jirginsu me ɗauke da sunan YARIMA MULKI, ya tashi domin nufar ƙasar Senegal.



.........
A gefen Afnan kuwa tun da ta tashi take jin haushin kowa a gidan, musamman idan ta tuna cewa Muby zai shigo ƙasar a yau, Hajiya Babba kuwa Jakadiya ta saka a haɗawa Yarima abinci me rai da lafiya, gaba ɗaya gidan an ƙara gyara shi sosai, ta ko'ina masu aiki ne babu inda zaka duba ka samu tsinke, Mama kuwa yau kamar ta ɗora hannu a kai saboda mugun labarin da ya sameta, shiyasa ma ta tattaro yaranta suka zo gidan, Halima ce kawai bata zo ba.

Tun da aka ce su Yarima na harabar gidan ne Afnan ta shige ɗakinta tare da danna masa key, Sarki Shuraihu na fada yana karɓar ƙorafi na mutane ya ji labarin zuwansu, nan take ya ɓata rai kamar wanda aka yiwa mutuwa.

Rabon Muby da gidan tun lokacin da aka zaɓa masa Afnan sai kuma yau da Allah ya nufi zuwansa, gabansa sai duka yake tsabagen zafi, babu abin da ke ƙara masa ƙarfin gwuiwa face auren Fadila da zai yi, part ɗin Hajiya Babba aka sauke su tare da baje musu kayan motsa baki, abinci da aka zube musu kamar wani taron biki ake tsabagen yawa da haɗuwarsa, gaba ɗaya parlourn ya ɗume da ƙamshin abincin, Hajiya Babba sai tsokanarshi take wai ya zo biko, Muby kuwa a ransa kamar ya kurma ihu, amma a fili sai murmshin yaƙe yake, da sallama Mommy da Husna sai Bilkisu da ta biyo dan gulma suka shigo, har ƙasa Muby suka duƙa tare da gaishe da Fulani sannan Husna ta gaishe su, Bilkisu kuwa baza ka ce matar aure ba ce, dan shigar wasu ƙananan kaya tayi masu nuna tsiraici, ga wani uban rashin shape da take fama da shi, babu wani gaisuwa illa zubawa Ashwan ido da tayi kamar zata haɗiye shi, sai wani fari da ido take shi ko Ashwan be ma san tana yi ba dan Husna yake kallo ƙanwar Afnan, haka kawai ya ji yarinyar ta burge shi, kuma da yanda ta gaida su cikin ladabi da kamun kai.

Cike da fara'a Mommy ta samu guri kusa da Hajiya ta zauna tana faɗin "Mutanen Sudan ya ku ka iso?" Ashwan da Yusuf ne kawai suka amsa amma gogan sai wani sunne kai yake alamun kunya, kallonta ta mayar kan Husna da ke chat da Ameer ta ce "Tashi ki kira Gimbiya mana"

Miƙewa Husna ta yi cikin biyayya, daidai kusa da Bilkisu ne ƙafarta ta ɗan taka yatsar Bilkisu a rashin sani, wani irin ashar ta ja tare da miƙewa ba kunya ta sharararawa Husna mari tana faɗin "Uban me ki ke kallo? da har za ki taka ni, an faɗa miki ƙaramin gyara nayiwa jikina da har za ki taka ni" Bilkisu ta ƙarasa zancen nata tana wani jujjuya mazaunai ita ala dole Ashwan ya gani, duk da cewar ran Ashwan ya ɓaci amma dariya ce ke cinsa ganin yanda Bilkisu ke yi kamar wata mahaukaciya.

Hajiya Babba ce ta ce "Husna je ki inda aka aikeki" Kamar Husna zata yi kuka haka ta fice daga part ɗin.

Wani kallon tsana Muby ya jefa mata wanda yasa tayi muƙus guri ɗaya, tare da samun guri ta zauna.


Kusan mintuna talatin ana zaman jiranta, har so uku ana aikawa kiranta amma babu Afnan babu alamunta, Husna kuwa har ta gaji da zuwa da komowa, daga ƙarshe dai Fulani ce ta miƙe da kanta da niyar kiranta amma sai Hajiya ta ce "A a zauna abinki Husna tashi ki yiwa Yarima rakiya ɗakin matar tasa"

Innalillahi wa innailaihir raji'un, kawai yake nanatawa a ransa dan baya ƙaunar ganinta, kuma ga wannan rainin hankalin da tayi masa, ana jiran mutum tun ɗazu amma har yanzu shuru, Husna ce ta ƙatse masa zancen zucin da faɗin "Brother mu tafi"

Murmushi ya saki na dole sannan ya miƙe tare da bin bayanta.


Kusan bugu goma amma ta share shi, Husna ma ta gaji buga ƙofar har ta tafi abinta, sosai ya fara dukan ƙofar yana kiran sunanta amma Afnan kamar bada ita yake yi ba, har ya juya ze bar gurin sai kuma ya fasa tunawar da yayi cewa Alhaji ya ce idan har be dawo da Afnan ba, ba zai auri Fadila ba, lumshe idunuwansa yayi da ƙarfi, tare da shafa gashin kansa a hankali ya rage murya kamar wanda ke raɗa ya ce "Afnan........." Jin yanda ya kira sunanta ne kuma ya marairaice murya ya bata mamaki, musamman ainihin sunanta da ya kira be taɓa kiran sunanta ba, sai dai ya ce Gimbiya.

Kwance take kan bed ta yi rufff da ciki sanye cikin wasu ƙananan kaya, wani wando me laushi ne da kaɗan ya wuce mazaunanta pink, sai Top iyakar ƙirjinta wanda yake kamar bra kalar wandon jikinta, rigar tana da ta wajenta wadda ta ɗan sauko kaɗan, gashin kanta kuwa ta baje shi kan bed ɗin, idanuwanta a lumshe, jin ya sake magana ne yasa ta ɗan ja ƙaramin tsaki tana mai gyara kwanciyarta, "Please Gimbiya ki buɗe ƙofar nan, na roƙe ƙi da Allah wallahi idan har baki buɗe ba baza su aura min Fadila ba" Zumbur ta miƙe zaune har tana buge hannunta da gefen bed, a fusace ta nufi ƙofar cikin tsiwa ta buɗe, kwalar rigarsa ta chakuma da ƙarfi kamar wata zararra idanuwanta sun gama rinewa, wani irin kallo take masa wanda be taɓa gani ba, a hankali kuma ta sake masa rigar tana mai komawa cikin ɗakin tare da tafa hannayenta, "Wow Mubarak wow, gaskiya ne ashe duk wannan haƙurin na neman auren Fadila ne? sosai nake jin daɗin wannan shirin" Kan kujerar da ke tsakiyar ɗakin ta zauna tana me ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta cigaba da faɗin "A ranar da ka sakeni da umarninta ka sakeni, gashi kuma aurenta da umarnina za'a yi shi"

Ta ƙarasa maganar cikin ɗaga murya, saurin ƙarasowa yayi kamar ƙaramin yaro ya riƙe hannunta har jikinsa na rawa gurin faɗin "I'm so sorry kar ki mun haka, Fadila rayuwata ce"

"Ni kuma ƙasƙantacciya ce a gurina" Afnan ta ƙatse masa zancen a zafafe.

Hannunta ta ƙwace tana mai ƙoƙarin shigewa toilet, cikin zafin nama ya cakumo ƙugunta tare da juyota suna fuskantar juna, lumshe kyawawan idanunsa ya yi jin wata irin tsanarta na ratsa ko'ina na jikinsa, sai kuma ya janye jikin nasa a hankali "Na mayar da ke ɗakinki, but please ki zo mu koma gida ba zan iya rayuwa idan babu Fadila ba"

Murmushin takaici ta saki tana mai haɗe fuska da yatsa ta nuna shi rai ɓace ta ce "Na gaji da magana ka fitar min daga ɗaki" Wani ɗan ƙaramin ƙarfe da take rataya hijab ɗinda tayi sallah ta nufa, hijab ta ɗauka tare da sakawa da niyar bar masa ɗakin, muryar me martaba suka ji a baƙin ƙofa "Yarima zo ku tafi tun kafin raina yayi mummunan ɓaci, mayar da Gimbiya da kayi ba shine zai sa ta koma ɗakinka ba, duk lokacin da ka gama shawara ka kawo mana takaddar sakinta gaba ɗaya"

Ƙara rufe ido Muby yayi jin zafin da zuciyarsa ke masa, ba tare da ya ce komi ba ya fice daga ɗakin.

Hawayen da ke maƙale kan fiskar Afnan ne ta share tana mai hugin ɗin Baffan nata, bayanta yake bubbugawa a hankali "Daina wannan kukan babu wanda zai mayar da ke, faɗa min ƙasar da ki ke son zuwa domin ki cigaba da karatunki" Cikin jin daɗi ta ɗago tana mai riƙe hannun Mahaifin nata ta ce "Thanks Baffa nima nayi tunanin hakan, ina son zuwa ƙasar Chad" Laƙace mata hanci yayi "Wato kina son zuwa gurin su Hajjo ko? Fulani zata ji daɗi sosai dama ta ce bakwa son zuwa gurin iyayenta, kinga sai ki zauna a can kina karatunki babu wanda zai takura miki, ki shirya gobe kibi jirgin safiya"

"Na gode sosai Baffa na shiyasa nake sonka".



"Babu inda zata tafi idan har ina raye" Suka jiyo muryar Hajiya, Afnan na ganin Hajiya ta haɗe fuska tare da ƙarasawa gurinta sannu a hankali yanda Me martaba ba zai ji ta ce "Idan har kika hanani zuwa zan kashe Yarima na kashe Fadila sannan na kashe kaina, in har kina ganin ba zan iya ba ku hanani zuwa ƙasar Chad" Afnan na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin cikin taku irin na ƴaƴan sarauta.


Muby kuwa haka suka bar ƙasar ransa ya masifar ɓaci, musamman idan ya tuna haƙurin da ya rinƙa ba Afnan, da ƙyar ya iya kai kansa gida, suna isa ya shige part ɗinsa tare da rufewa.

Ashwan kam tunanin Husna ne ke neman hana shi shan iska, daga zaran ya rufe idanunsa ita yake gani.



ƘASAR CAMAROUN
...........
A ɓangaren Afnan tana zuba ido ganin an fara shirye-shiryen aure amma shuru ka ke ji.

Tana zaune a harabar gidan gefen wani lambu sanye cikin wasu kayan sarauta, a gefenta masu kula da ita ne kusan su goma, hannu ta miƙawa ɗaya daga cikinsu, wayarta ƙirar iphone aka ɗora mata a hannu, a hankali ta lalubo numbern Muby bugu ɗaya ya ɗaga jiki na rawa ya ce "Masoyiya kamar kinsan ke nake muradi a yanzu please ki zo ƙasarmu, dan ko na ce wa me martaba zan shigo ba zai bar ni ba"

Jin ta yi shuru ne yasa shima yin shurun dan baya son yana magana ana sherasa abin na ƙona masa rai "Ka yi shuru Masoyi" Ta faɗa a taƙaice, nan ma shuru taji yayi mata, daga ƙarshe ma ya kashe wayar tasa ganin zata raina masa hankali.

Tana ganin ya yanke call ta kalli wayar cike da jin haushi ta ce "Ba zai taɓa canja halinsa ba, har ni ɗin ma sai yayiwa ƙasaita" A fusace ta nufi part ɗin Mahaifinta, bakin ƙofar haɗaɗɗen parlourn suka haɗu da shi, tana ganinsa ta fashe da kuka tare da hugin ɗinsa "Sorry Shalele waye ya taɓa min ke? faɗamin ko ɗan gidan uban waye yau ba zai kwana a gidansu ba" Share hawayen ta yi kamar wata Baby ta ce "Yarima ne Dad"

"Yarima me yayi miki kuma?"

Jikinta ta janye kafin ta ce "Dad aurensa nake son yi a satinnan idan ba haka ba kashe kaina zan yi"

Da sauri ya rufe mata baki "No Shalelena ki daina faɗin haka, mu shiga daga ciki akwai maganar da nake son mu yi"

Hannnunta ya kama suka shige cikin parlourn da ya gama haɗuwa, kusa da shi ta zauna tare da zuba masa ido, sosai ya jinjinawa lamarin dan be san yanda zata ɗauka ba, cike da juriya ya ce "Aurenki da Yarima ba zai taɓa yuwa ba har sai Gimbiya ta koma ɗakinta" Zazzaro ido waje Fadila tayi jin abin da Mahaifin nata ya faɗa "Bangane ba Dad meye haɗin bazawara da mijin da zan aura?"

"Matarsa ce a halin yanzu, saboda ya mayar da ita kuma ya tafi har ƙasar Senegel roƙon Gimbiya ta dawo amma ta ce baza ta dawo ba, Alhaji Babba ya ce idan har Gimbiya bata dawo ba aurenku ba zai taɓa yuwa ba".

Wani mugun baƙin ciki ne ya tokare mata zuciya.

"Dad......" Ta kira sunansa.

"Ina jinki Shalelena"

Miƙewa tsaye ta yi cike da rashin tarbiya ta nuna shi da yatsa tana faɗin "Tun da baza ka aura min Yarima a wannan satin ba tabbas gawata zaku samu" Da guda ta fice daga parlourn, ai kuwa yabi bayanta tare da kiran sunanta amma ina Fadila ko ta kansa bata bi ba.

Ihu ya fara ji da kururuwa ta ɓangaren wakeken swimming pool ɗinda ke harabar gidan, a ruɗe ya ƙarasa gurin.

Fadila ya gani ta faɗa ciki, kuma ta bada umarnin kar wanda ya shiga domin cetonta.

Sama da ƙasa numfashinta ke yi, a tsawace Me martaba ya kalli masu aikin gidan maza da ke tsaye suna kallonta "Idan har ƴata da mutu gaba ɗayanku sai kun mutu, uban me ku ke jira? ku taimaketa kafin na rasata" Ganin yanda ran me martaba ya ɓaci ne yasa matasan da ke gurin faɗawa ciki, duk da haka sai da suka yi da ƙyar kafin suka iya cetonta lokacin har numfashinta ya fara ɗaukewa.

Parlourn aka nufa da ita, kamar wani jani talau haka Dad ke binsu a baya, hankalinsa ya gama tashi lallai ba zai rasa ƴarsa tilo saboda wani can ba, wanda be fi su a komi ba.

Ba ƙaramin ƙoƙari Doctorn da ke kula da su yayi ba gurin ganin ya ceto rayuwarta, a lokacin tashin hankalin Dad ya ƙara yawa fiye da ɗazu.

Ruwa aka ɗaura mata tare da allurori kafin kowa ya bar ɗakin ko zata samu hutu.


ƘASAR SENEGAL
.................
Tun ƙarfe shida na safe ta gama shirinta, cikin shigar abaya black sai wani ɗan ƙaramin mayafi red, ta masifar kyau musamman da ta ɗora wani glass ya haɗe sosai da kayan jikin nata, ɓangaren Fulani ta nufa Mubina na bayanta ɗauke da troly anan ta sami Hajiya da me martaba na ƙoƙarin zuwa fada, a bakin ƙofa Mubina ta tsaya zaman jiranta.


Fuskar Afnan ɗauke da murmushi abin da suna mance ranar da suka gani, ƙarasowa tayi tare da faɗin "Baffa ka tashi lafiya"

"Lafiya ƙalau Gimbiya kin gama shirin ne?"

"Yes Baffa, tsohuwa yane ko za ki hanani tafiyar ne?" Afnan ta faɗa tana mai kashe mata ido, shuru Hajiya ta yi ba tare da ta kula ta ba, itama Afnan ɗin gaban Fulani ta duƙa tana mai kama hannayenta ta ce "Barka da safiya" Ƙwace hannunta Fulani ta yi tare da ɗauke kai, murmushin gefen baki AFnan ta saki tana mai miƙewa tsaye jiki a sanyaye "Fulani yau shekaru da dama ban tafi ƙasar Chad ba, amma baza ki mun murna zan tafi karatu a can ba? kuma fa su Hajjo na can" Gaban Fulani ne ya faɗi tunawa da Alhassan da Muhseen da tayi, yanzu ya zaman zai kasance idan har Afnan ta gane su ƴan uku ne.

Me martaba ne ya girgiza mata kai alamun karta damu.

Murmushin ƙarfin hali Fulani ta ƙago tana faɗin "Uhmm Allah ya kai lafiya amma ki sani cewa akwai auren wani a kanki, kuma kinsan cewa aure ba abin wasa ba ne" Wani ƙololon baƙin ciki ne ya dirar mata a ƙahon zuci, ba tare da ta tanka ba ta fice daga ɗakin, me martaba ma bayanta ya bi.

Hajiya ce ta maida kallonta kan Fulani cikin rarrashi ta ce "Na san kina tunanin yanda Afnan zata gane cewa su ƴan uku ne, ina son ki gane ya kamata ta san da wannan abin da ake ɓoya mata, su kansu yaran basu san cewa ƴaƴan sarauta ba ne kun ɓoye musu, da sunan kuna kasuwanci a ƙasar nan, yanzu idan suka gane gaskiya me ku ke tsammanin zai faru?" Hajiya ta ƙarasa maganar cikin damuwa.

Ajiyar zuciya Fulani ta sauke kafin ta ce "Hakane gaskiya insha Allah komai zai zo da sauƙi, ni kaina ina son su dawo gidan Mahaifinsu"

"Allah yasa hakan" Cewar Hajiya Babba.

Har aiport me martaba da muƙarabbansa suka yi mata rakiya se masu kula da ita su biyar gamida Mubina su shida.

Sai da jirginsu me sunan GIMBIYA MULKI, ya tashi kafin Sarki Shuraihu suka bar gurin.

Tun da su Hajjo suka ji labarin zuwan Gimbiya aka fara shirye-shiryen tarbarta, gaba ɗaya an ƙara gyara gidan, duk da cewa gidan ba ƙaramin haɗaɗɗe ba ne, abinci kuwa kala-kala kamar wani shugaban ƙasa ne zai zo.

Gaba ɗaya mutanen gidan sun hallara a aiport ɗin Chad ana jiran isowar Gimbiya, cikin mutanen kuwa har da Alhassan da Muhseen.


*Ayi min afwa naga ƙorafanku sosai har da masu kuka, 😂 to a ƙara haƙuri yau dai nayi typing*



*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P.11



................................................................
Tun da ta fara taka matattakalar jirgin mutanen da ke gurin suka zuba mata ido, ganin cewa duk zamansu a ƙasar Chad basu taɓa ganin mace me kyau kamar Afnan ba, wasu matasa guda biyu masu kyau sosai fuskarsu ɗaya da Afnan babu abin da ya banbanta su, illa ita macece su kuma maza sai kuma tsayi da girman jikin da suka fita, sosai suka ƙura mata ido har basa son ɗauke kai, Afnan kuwa cike da taku irin na manyan ƴaƴan sarakuna ta ƙaraso wurin, su Mubina kuwa na take mata baya.

Hajjo da ke gefe tana sakin murmushi ne Afnan ta nufa tare da rungumeta cikin muryarta me ɗan karen zaƙi ta ce "Miss you Hajjo yau ga masoyiyarki tazo gurinki" Afnan ta ƙarasa maganar tana laƙace mata kumatu, ƴar dariya Hajjo ta yi kafin ta ce "Yooo ashe kina zuwa ziyara nayi tsammanin Mulkin naki ba zai bari ba"

Bubbuga ƙafa Afnan tayi kamar ƙaramar yarinya sai a lokacin ta lura da mutanen da ke gurin gami da masu kula da Hajjo, a can baya kuwa wasu matasa ne su biyu amma sun bata baya kamar magana suke yi shiyasa ma bata samu damar ganin fiskarsu ba, "Hajjo mu tafi please kin san cewa bana son tsayuwa" Afnan ta faɗa tana yin gaba, wata haɗaɗɗiyar mota ta shige tana mai rufe ƙofar, haka su Hajjo ma kowa ya shige tasa motar nan take motocin guda hamsin masu masifar kyau da tsada suka bar aiport ɗin.

Alhassan da Muhseen kuwa gaba ɗaya sun kasa samun natsuwa, tun lokacin da suka ga Afnan hankalinsu ya kasa kwanciya.

Sosai suke fira a haɗaɗɗen parloun gidan wanda babu inda zaka duba baka ga tulin dukiya ba, ginar gidan ma kawai abin kallo ne musamman yanda masu aikin gidan ke tsara komi.

Sai a lokacin su Alhassan suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, Afnan kuwa ko amsa sallamar bata yi ba balle ta kalli inda suke, Hajjo ce ta kalleta da mamaki sai kuma ta maida dubanta kan su Muhseen ta ce "Ku ƙaraso daga ciki mana" Sai a lokacin ta ɗago kyawawan idanunta ta sauke kansu, wata irin bugawa zuciyarta tayi ganin wani masifar kamanni da take yi da yaran, musamman Alhassan, bakinta na rawa ta ce "Hajjo su kuma waɗannan fa?" Ido Hajjo ta zuba mata ba tare da ta ce komi ba, dan babu wata amsa da zata iya bata, kusa da suka zauna Muhseen ne ya ce "Hajjo wannan wacece? kinga irin kamannin da mu ke yi kamar an tsaga kara"

"Allah ya sawwaƙa min, kaga nayi kama da wadda zata yi fuska iri ɗaya da ku?" Cewar Afnan tana watsa masa harara, Alhassan ne ya daka mata tsawa dan ya tsani a wulaƙanta ƙaninsa a gaban idanunsa, baya dariya ko kaɗan mugun miskili ne na ƙarshe, yana da wahala kaga yayi magana "Ki iya bakinki kina jina ko? naga alamar ke ƙaramar marar kunya ce zan ci ubanki wallahi" Ya ƙarasa maganar a zafafe idanunsa sun gama yin ja, muƙussss Afnan tayi cike da mamakin ɓacin ransa, sai taga yayi kamar da Baffanta, shima haka yake idan har yana fushi, dafa ƙafaɗarsa Muhseen yayi cikin rarrashi ya ce "Sorry Yaya dan Allah ka rage wannan fushin naka, ni ban ɗauki maganar da tayi da wata manufar ba"

Miƙewa Afnan tayi cike da fushi zata haura sama ta ƙara tsinkayo muryar Alhassan na faɗin "Dawo ki zauna" Cakkk ta tsaya tana mai cije lips, har wani tafiyar ƙasaita yake yi kamar wani sarki ya ƙaraso gabanta "Ki koma inda kika tashi, bana son rashin tarbiya idan har a gidannan zaki zauna a kullum sai nayi miki dukan tsiya" Yana gama faɗin hakan ya haura sama cike da gadara, haushi da takaici ne ya haɗe mata a guri ɗaya, Hajjo kuwa daɗi ya gama kamata dan tana son Afnan ta rage wannan izzar da take yi, yanzu kuwa dama ta samu Yayanta zai koya mata hankali, amma a zahiri sai ta haɗe fuska alamun bata ji daɗin abin da Alhassan yayi mata ba "Gimbiya zo ki zauna daina fushin, haka halinsa yake baya son rashin kunya ko kaɗan kuma baya son raini" Hajjo ta faɗa tana ƙara narke fuska. A ƙufule Afnan ta koma tare da zama fuska babu walwala, Muhseen ma kusa da ita ya koma dan shi haka kawai yake jin sonta be san dalili ba, "Sister kiyi haƙuri da abin da Yaya ya yi miki, insha Allah ba zai ƙara ba amma kema sai kin daina wannan halin naki, Hajjo ta faɗa mana ke ƴar sarkin Senegel ce, nasan dole zaki yi gadara amma ki aje gadararki a gefe idan har kina gaban Alhassan dan wallahi zai miki shegen duka" Bushewa da dariya Hajjo tayi jin abin da Muhseen ke faɗi, sosai maganar ta taɓa zuciyar Afnan ga kuma dariyar da Hajjo ke yi, a fusace ta miƙe tana duban abincin da ke kan makeken table ɗin da ke parlourn, ba tare da ɓata lokaci ba ta yi watsi da duka abincin da ke gurin, idanunta sun yi jajir ta ce "What ever he is i don't care, bana tsoronsa ina fatar ka gane" Da gudu ta haura sama cike da ɓacin rai. Hajjo ce ta ce "Muhseen zo nan" Kusa da ita ya zauna cikin damuwa ya share hawayen da suka zubo masa "Kukan me kake yi? kai kam ka cika saurin kuka"

"Hajjo kina ganin abin da wannan yarinyar ke yi? meyesa bata da tarbiya ne? haka halin gidansu yake, ina ganin iyayenta sun sangartata shiyasa take wulaƙanta kowa yanda take so" Hannun Hajjo ya kama yana mai cigaba da faɗin "Saboda iyayemmu basa da komi, yau inda Mahaifina wani ne nasan cewa baza mu ga wannan wulaƙancin ba, tabbas Hajjo ku iyaye ne na gari tun da har ƴarku ta fito gidan sarauta amma ku ka aurawa ɗan kasuwa" Tausayin Muhseen ne ya kama Hajjo, sannu a hankali ta ce "Hakane amma a kullum ina faɗa maka cewa shi arziƙi na Allah ne, Gimbiya tana da tarbiya sosai sai idan baka zauna

Please Login or Register in order to submit comment