Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan har wasa ne yau sai na kakkaryaki a gidannan saboda matayena ba mazinata ba ne, idan kuwa da gaske ne sai na ɗauki mummunan mataki" Wannan karon Afnan da kanta ta tsorata da ganin yanda yanayinsa ya canza, jikin Ameera na kyarma ta ce "Wallahi Brother da gaske ne, har Ameer ma ya ɗauketa hoto"

"Ya subhanallahi....." Muby ya faɗa yana dafe bangon ɗakin, ai Afnan bata san lokacin da ta miƙe tare da kama shi ba, "Sorry ka bi a sannu kar ka faɗi" A tsawace Muby ya ce "Dallah malama sake min hannu, ai duk ke ce silar halin da na shiga" A fusace ya fice daga ɗakin, Afnan kuwa jiki a sanyaye ta koma ta zauna, tabbas ta san cewa bata kyauta ba, dan maganar saki ba wasa ba ce kuma har Alhaji ya ji maganar.


*Mu haɗe a next page, kasancewar gajeren labari ne shiyasa ban cika typing sosai, amsar masu ƙorafin cewa ana typing kaɗan*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


*TOPE. 10*



*PAGE. 24*



Tun da Muby ya bar gidan be dawo ba sai dare, part ɗin Maifinsa ya tafi inda ya samu Alhaji da Ameer suna fira, gaisuwa kawai ya yi be sake cewa uffan ba, haka kowa da ke ɗakin be kula shi ba, abun da Muby be saniba shine Alhaji ya sanarwa Me martaba zancen sakin da Afnan ta ce ya yi mata.

Cike da ɓacin rai Muby ya ce "Ameer meyesa ba ka sanar da su Abba zancen Maimun ba?"

Da mamaki Ameer ya ce "Zancen Maimun kuma?"

"Ka san cewa bana son ina tambaya ana tambayata ko? wallahi ranka zai ɓace"

Sunkuyar da kai Ameer ya yi yana faɗin "Ban sanar da su ba?"

"To meyesa"

"Brother dama Mommy ce ta ce na bari har ka dawo" Wata irin razananniyar tsawa Muby ya dakawa Ameer, har sai da su Alhaji suka ɗago jin yanda ran Muby ya ɓaci, kansa na sarawa ya miƙe, "Idan kaga dama ka faɗa musu dan a halin yanzu gidansu na fito kuma na bata saki uku masu rai da lafiya"

Marin da Abbansa ya ɗaukesa da shi ne ya shi dafe kuncensa yana kallonsa "Ashe ba ka da hankali Yarima, yanzu matayen naka ne ka saka gaba ɗayansu? ita kuma Maimun ɗin me ta yi maka?"

Cikin muryar da Muby be san yanada ba ya ce "Wai meyesa zan saki Afnan ne? babu wani sakin da ke tsakanina da ita, tun da na yi na farko ban sake ba, shima ƙaddara ce kuma tana kan kowa"

Hawayen da ya zubo masa ya share kafin ya kuma cewa "Bana buƙatar waninku ya yarda da abin da nake faɗa, amma ni ban saki Gimbiya ba kuma ba zan taɓa sakinta ba"

Cike da taƙama ya fice daga ɗakin, jikinsu Alhaji ya yi sanyi da jin yanda Muby ya yi magana, dan sai a yanzu suke ganin tsantsanr gaskiya a idanunsa, "Ameer me yake faruwa ne?"

Cewar Alhaji yana kallon Ameer da ke zaune cike da tausayin Yayan nasa, sunkuyar da kai ƙasa Ameer ya yi cike da kunya ya sanarwa su Sarki Ahmad abin da ke faruwa, ba ƙaramin girgiza suka yi ba jin abin da Maimun ta aikata musamman me martaba, sosai suka tattauna kan maganar tare da ajewa gobe zasu san abin yi.

Muby na shiga part ɗinsa toilet ya nufa, ya jima yana sakarwa kansa ruwa kafin ya fito, gaba ɗaya yau abincin ma gagararsa ya yi, a haka ya gama shirinsa cikin jallabiya ya kwanta, amma baccin ya kasa zuwa dan tunanin Afnan ne kwance a ransa, daga zaran ya juya sai ya ganta a kusa da shi, sai a yanzu ne ya gane cewa ya masifar shaƙuwa da ita tsawon lokacin da suka zauna tare, baccin ma kasa ɗaukarsa ya yi dan ji yake idan ba a jikinta ba ba zai iya samun bacci ba.


A ɓangaren Afnan ma haka, tun da Muby ya fita ta nemi natsuwarta ta rasa, duk tausayinsa ya kamata ganin yanda ya bar ɗakin, da daren ma sai juye-juye take.

Misalin ƙarfe goma na dare ne Muby ya nufi part ɗin Ameera, dan ya san a can zai sami Afnan, ai kuwa ya ci sa'a ƙofar a buɗe take, Ameera kuwa ta jima da yin bacci, tun da ya shiga ɗakin Afnan ta fara jin ƙamshin turarensa amma sai ta yi tsammanin tunani ne kawai take yi, kamar daga sama ta ji mutum kusa da ita, har ta buɗe baki da niyar ihu ya yi saurin toshe bakin nata, a hankali ya ce "Shhhhhhh...., mijinki ne fa"

Waro ido Afnan ta yi duk da cewar da ɗan duhu amma Muby ya ga hasken idanuwanta, "Ki tashi mu tafi bacci nake ji"

Hannun da ya rufe mata baki ta janye itama ta faɗa a hankali "No ba zan je ba"

"Shikenan zamu kwana anan kuwa"

"Aa dan Allah ka tafi, Ameera na ganin girmana bana son ta farka ta yi arba da mu"

"Ai abin da nake so kenan"

Muby ya faɗa yana mai shafa saman na shanunta, wani numfashi Afnan ta ja wanda ya sa Ameera motsawa, ai da sauri ta shige jikin Muby dan kar Ameera ta gansu, Muby na ganin haka ya tallafota tare da ficewa da ita daga ɗakin.

Be direta ko'ina ba sai kan be ɗinsa, ƙofar ya koma ya rufe yana mai kallon yanda ta ɗaure fuska, "Zo mu yi alwala sai mu kwanta bacci nake ji sosai" Afnan kam dama abin da take so kenan, dan ita kanta ta saba da bacci a jikinsa, gaba ɗaya tunaninta be kai ga wani abin ba har suka gama alwala, hijab ɗinta har ƙasa ne sai wando da riga na bacci red colour, me taushi da kyau, wandon dogo ne har ƙasa amma ana ganin jikinta, sai da suka gama sallah raƙa'a biyu sannan ya yi musu addu'oi, tare da yi mata tambayoyi, babu amsar da ta gagareta hakan ya masa daɗi sosai dan dama ya san a gidansu ba'a wasa da addini, to amma Afnan kam yanzu ta fara jin tsoro sosai, miƙewa ta yi ta koma kan bed ɗin ta raɓe a can ƙarshe, sai da Muby ya jima yana addu'a kafin ya kashe hasken ɗakin ya haura shima, a lokacin Afnan ta fara bacci abinta, kawai ji ta yi am fara lalubeta kamar mage, a firgice ta miƙe tana ƙoƙarin dirowa daga kan bed ɗin, ai kuwa Muby ya damƙota da ƙarfi "Babu inda za ki tafi Malama, bayan kin gama yi mun sharri, bari ma na ƙara tuna miki wani abun, ranar da ki ka ce na yi miki fyaɗe, wancan Game ne aka buga yanzu ne na asalin"

Jin yanda yake murzata ne yasa ta fashe da kuka, dan wannan karon ya sha banban da sauran ba ƙaramin zafin yanda yake matse mata na shanu take ba.

Cikin basira ya raba su da kayan jikinsu, a lokacin Afnan ta fara sarewa dan wani irin wasanni Muby ke zuba mata wanda ya sa ta ƙara gigicewa, tun da Afnan take bata taɓa shiga irin wannan yanayin ba, tana cikin haka ta ji yana karanto addu'ar saduwa, ai kuwa ji take kawai garammmmmm, gammmmm, Muby ya faɗa ciki, wata irin razananniyar ƙara ta saki wadda ta sa gaba ɗaya gidan amsawa, ihu take tana neman ɗauki amma Muby be san tana yi ba, sai ma ƙara masa ƙarfin gwuiwa kukan nata ke yi, tun tana iya kuka har muryarta ta gagara fitowa jikinta ya tsaya cakkkkk, sai nishi sama-sama kamar wadda ake fizgar ranta,shi ko be saurara mata ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar asuba, a lokacin Afnan ta daɗe da sumewa dan Muby ba ƙaramin jarumi ba ne, dama duk tsawon lokacinnan yana tara gajiyarsa ne, shi kansa sai da ya rinƙa kuka da sambatu kamar zai haukace dan wani daɗi na musamman Afnan ke da shi, ajikinta ya kwanta yana mai sauke numfashi, duk ya ƙanƙameta kamar zai ɓalle jikin nata, ya kai kusan mintuna biyar a haka kafin natsuwarsa ta dawo, sai a lokacin ya ga halin da take ciki, ga jini duk ya ɓace a zanin gadon, Afnan kuwa kamar gawa haka ta baje, a kiɗime Muby ya tallafota tare da mannata kan ƙirjinsa, duk a tunaninsa Afnan ba cikakkiyar budurwa ba ce shiyasa ya shigeta da ƙarfi, gaba ɗaya jikinta ya ɗauki zafi, cikin hanzari ya nufi toilet da ita, sai da ya ɗaura tawul kafun ya koma ciki, ruwan zafi ya haɗa mata wanda ya san zai gasata sosai.

Yana sakata ciki ta ja wani dogon numfashi tare da ƙanƙameshi a jiki, zafin ruwan na ratsata sai kuma kukan da take amma kukan baya fita sosai saboda muryarta ta dashe, duk tausayinta ya gama kama shi.

Sosai ya gasa ta kafin ya yi mata wankan tsarki, zanin gadon ya canza sannan ya ɗora wani, Afnan kam kasa haɗa ido da shi ta yi sai ma wani tsoronsa da ta fara ji, kan bed ya shimfiɗe ta tare da rufeta ta blanket ya koma toilet.

Shima wanka ya yi sannan ya haɗa da na tsarki tare da alwala, yanda ya barta haka ya sameta, hasken ɗakin ya kunna ai kuwa Afnan ta rufe ido dan wata irin kunyarsa take ji musamman yanda ta rinƙa jin sambatun da ya yi ta yi mata jiya da kuka, murmushi ya saki yana mai nufar mirrow, cikin natsuwa ya fara shafa mai me laushi, Afnan kam sai satar kallonsa take daga ya juyo ta rufe ido kamar me bacci, har ya gama shiryawa cikin jallabiya ruwan toka me tambarin sarauta, sallaya ya shimfiɗa tare da tada sallah, Afnan na ganin haka ta miƙe da niyar ficewa daga ɗakin, ƙara ta saki jin wani zugin da ya shigeta kamar ƙasanta zai tsage ai kuwa ta fashe da kuka har da birgima a kan bed kamar ƙaramar yarinya, Muby na gama sallah ko addu'a be yi ba ya hauro kan bed ɗin yana tambayar abin da ya faru, runtse ido ta yi dan bata son haɗa idanuwa da shi, murmushi ya sakar mata yana mai janyota jikinsa "Meya faru? abar ƙaunata i'm so sorry da zafi ko?"

Turo baki ta yi cikin muryarta da bata fita ta ce "Ni ka barni na tafi kai mugu ne"

"Mugu kuma? Babyna daɗinki ne ya yi yawa kuma ban yi tsammanin zan sameki a budurwa ba" Wani irin mugun kallo ta watsa mishi me kama da kama raina min hankali.

"Kana nufin na taɓa aikata zina kenan?"

"No ba abin da nake nufi ba ne, akwai abin da ya faru lokacin rashin lafiyarki shiyasa na faɗi hakan"

"Wannan kuma damuwarka ce, ni sai ka sakeni na koma gidammu kuma Allah ya isarmin tun da ka sanni ƴa mace azzalumi kawai........" Saurin haɗe bakinsu ya yi yana mai yi mata wani irin tsotsa Afnan kam ta ƙara tsorata dan ganin ya fara ƙoƙarin janye tawul ɗin da ke jikinta, hawayen da ya zubo mata ya fara sharewa sannan ya janye bakinsa a hankali "Matsoraciya ni babu abin da zan yi miki"

Ƙara lafewa ta yi a jikinsa jin wani zazzaɓi na shigarta, ganin haka ya sa shi kwantar da ita yana mai cewa "Ina zuwa bari na ɗauko miki magani" Ficewa daga ɗakin ya yi ya nufi wani room ɗin, be jima ba ya dawo ɗauke da magunguna, hannunsa ɗaya kuwa tea ne me zafi wanda ya sha kayan haɗi, kan table ɗin da ke gurin ya ɗora yana mai faɗin "Sai kin fara shan tea sai na ba ki maganin"

Ita dai kallonsa kawai take ganin yanda yake wani rawar ƙafa, da ƙyar ya samu ta sha tea ɗin gaba ɗaya jikinta ya hau ɓari, sai kawai ganin ya yi ta ƙara sumewa a jikinsa, kamar zararre haka ya fara kiran sunanta yana jijjigata, amma Afnan kam ko jinsa bata yi, a hankali ya kwatar da ita tare da buɗe ƙafafunta, ba ƙaramin tsorata da ganin ƙasanta ya yi ba, sosai ya tausaya mata dan ya ga ƙoƙarinta da har ta iya jurewa haka.

Ganin cewa sai an yi mata ɗinki ne ya sa shi ɗaukar wayarsa ya danna wata number, har sai da ta kusa katsewa kafin aka ɗaga, da sauri Muby ya ce "Idan a masarauta ki ka kwana ki sameni a room ɗina Gimbiya bata da lafiya ki zo da kayan ɗinki" Daga can ɓangaren Nurse Hafsat ta ce "Okay Sir"


Ba wani ɓata lokaci ta shigo part ɗin amma a parlour ta tsaya, Muby kuwa parlourn ya sameta cikin hanzari ya ce "Ki shiga tana ciki ba zan iya komi ba ne shiyasa na kira ki, amma ki bita a sannu please" Sosai Nurse Hafsat ta sha mamakin ganin yanda Muby ke rawar ƙafa kan Afnan, cikin room ɗin ta shiga tana murmushi.

Tun da ta shiga Muby ke zarya a parlour jikinsa duk ya yi sanyi, kusan awa ɗaya aka ɗauka kafin Nurse ɗin ta fito, "Allah ya ba ka nasara na gama, sai dai yanzu haka bacci take yi, kuma zata iya farkawa a kowanne lokaci, idan ta tashi sai ka sama mata abin da zata ci me nauyi.

Godiya ya yi mata kafin ta fice shi kuma ya sakawa ƙofar key.

Room ɗin ya koma dan baya son barinta ita ɗaya, hankali kwance take bacci amma tana sauke ajiyar zuciya me nauyi.


A gefenta ya zauna tare da ƙura mata kyawawan idanunsa masu kyau da haske, ya jima a hakan yana ƙarewa fuskarta da ta kumbura kallo, sai kusan ƙarfe tara ta farka bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, tana ganin Muby zaune a kusa da ita ta fashe da kuka dan ta yi zaton ya sake yi mata wani abun ne, "Baby sorry ban yi miki komi ba fa, kar ki lalata ɗinkin da aka yi miki" Marairaice fuska ta yi cike da tsoro ta ce "Ɗinki fa? na shiga uku Allah ya saka min shikenan ka lalata min rayuwa"

"Babyna dan Allah ki daina"


"Baza a daina ba ɗin"

Jin abin da ta ce ne yasa shi faɗin "Tom bari na sake yin wani" Yunƙurawa ta yi da niyar miƙewa amma ta kasa, ga wani zafin da take ji a ƙasanta sai dai zafin ya rage ba kamar ɗazun ba, jikinta kuwa ya yi sanyi.

"Ni ka kaini part ɗin Alhaji"

"No ba yanzu ba sai kin fara cin abinci, ki jirani ina zuwa"

Be jira abin da zata ce ba ya fice daga ɗakin,
yana fita ta tashi da ƙyar ta ja jiki zuwa toilet, sai da ta ƙara wani wankan kafin ta haɗo da alwala.

A lokacin da ya shigo Afnan ta gama sallah, hannunsa ɗauke da basket da flacks, a gefenta ya aje sannan ya fara zuba perpesun naman rago wanda ya sha kayan haɗi, sai kuma julof ɗin indomie da karas, Afnan da gama addu'arta kenan idanuwanta suka sauka kan kunun gyaɗan da ke cikin Cup, yawu ta haɗiye tana kallonsa yana ganin haka ya sakar mata murmushi, sannan ya miƙa mata, ai kuwa har jikinta na rawa gurin karɓa, sosai ta sha kunun dan abincin ma kaɗan ta ci, sai da ya nuna mata ɓacin ransa, magani ya bata shima ya sha rarrashi kafin ya samu ta sha, sai shagwaɓa take zuba masa har da wani kwantawa kan ƙirjinsa.

A haka wani baccin ya sace ta, kan bed ya maidata yana mai canza shigar jikinsa ya nufi fada, a can ya sami Alhaji na jiransa, da sallama ya shiga tare da gaidasu, fuskarsu ɗauke da murmushi suka amsa, zama ya yi yana mai sunkuyar da kai ƙasa, Alhaji ne ya ce "Ina Gimbiya?"

Ɗan sosa kai Muby ya yi kafin ya ce "Tana part ɗina"

Ɗaure fuska Me marta ya yi yana mai faɗin "Bayan ka sake ta me take a part ɗinka? na san cewa kai ne ka yi mata dole"

"Allah ya ba ka nasara wallahi ban saki matata ba, kawai sharri take mun, na san cewa a baya na nuna mata tsana sosai amma a yanzu ina masifar sonta"

Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke kafin ya ce anjima ku samemu a part ɗina akwai zaman da zamu yi misalin biyar na yamma, amma kafin nan ka mayar da Gimbiya part ɗin Mahaifiyarka, idan kuma ba haka ba wallahi sai ka haɗu da fushina, tashi ka bamu guri"

Ba tare da Muby ya ce uffan ba ya fice daga fada, dirrect nasa ɓangaren ya nufa.

Kamar yanda ya barta haka ya sameta, a hankali ya tallafota zuwa jikinsa, dama ba wani nauyin take da ba.


Har part ɗin Mommy ya tafi da ita a haka, duk inda ya gifta sai dai kaga Dogarai na zubewa ana kwasar gaisuwa, ɗaki ya samu Mommy zaune Ameera na gefenta, da sallama ya shiga tare da kwantar da Afnan kan bed ɗin Mahaifiyar tasa, da kallo duk su biyun suke binsa har ya zauna kusa da Afnan yana shafa gefen fuskarta, cikin kunya Ameera ta ce "Brother good morning, ashe Aunty Afnan a part ɗinka ta kwana, sai nemanta nake da asuba"

"Aa a cikin tasha ta kwana, sarkin sa ido kawai fice min daga nan" Saɗaf-saɗaf Ameera ta fice tana mai danne dariyarta.

Sai da suka gaisa da Mommy kafin ya miƙe da niyar fita "Me yake damunta ne?"

Lumshe ido Muby ya yi dan ya kasa bawa Mommy amsar tambayarta, "Amm dama bata jin daɗi ne"

"Tom Allah ya bata lafiya ta ci abinci kuwa?"

"Eh ta ci amma idan ta farka zan dawo na bata abinci"

Da mamaki Mommy ke kallonsa ganin yanda yake wani mazari kan Afnan, cikin alamun kunya ya fice daga ɗakin.

Duk da cewar Mommy na ɗakin amma Muby ya shigo duba Afnan fiye da so goma, har abin ya fara bawa Mommy haushi daga ƙarshe ma rufe ɗakin nata ta yi, da ƙyar ya iya ganin ƙarfe biyar ta buga, a part ɗin Alhaji ya samu su Afnan da me martaba har da Mommy.

Kana ganin idanuwan Afnan ka san babu gaskiya a ciki, sai wani sunkuyar da kai take.

Ba tare da ya kalli kowa ba ya nufi gurinta yana mai kama hannayenta ya ce "Babyna ya jikin naki, babu inda yake yi miki ciyo yanzu ko?"

Shuru Afnan ta yi tana mai ƙwace hannunta, Mommy ce ta ce "Yarima ka maida hankalinka, ko rashin kunyar zaka nuna mana"

Sai a lokacin ya ɗan sosa haɗaɗɗen gashin kansa yana mai gyara zamansa amma be saki hannun nata ba, "Ka sake mata hannu yanzu ba matarka ba ce tun da ka sawwaƙe mata" Cewar Alhaji yana haɗe fuska babu alamun wasa.

Marairaicewa Muby ya yi kafin ya ce "Dan Allah ki faɗa musu gaskiya, ki faɗa musu cewar ban sakeki ba zuciyata zata iya bugawa please Baby"

Afnan kam kasa magana ta yi sai raba idon da take, Alhaji ne ya kuma cewa "Gimbiya ke muke sauraro ki faɗa mana gaskiya aure ba abin wasa ba ne, kuma saki ya wuce a yi wasa da shi"

Sai da ta share ɗan guntun hawayen da ya zubo mata kafin ta ce "Ni be sakeni ba, amma bana son sa auren nake son a raba"

Gaba ɗaya ɗakin shuru ya ɗauka jin abin da ta ce, har shi kansa Muby jikinsa ya yi sanyi.

Me martaba ne ya ce "Shikenan kai Yarima ka ji abin da ta ce, wannan shine zama na ƙarshe da zamu yi a kan aurennan, dan haka ka sawwaƙe mata" Jikinsa ne ya fara ɓari idanuwansa sun rine jajir kamar garwashin wuta, kallo ɗaya Afnan ta yi masa sai kuma ta ji tsauyinsa ya kama ta, Mommy kam ta gama gane cewar suna masifar son junansu, kuma ta gane cewa Afnan tana jan aji ne kawai dan ita macece me mugun taƙama da gadara.

Mommy ce ta ce "Amma Allah ya ba ka nasara kar mu yi saurin raba aurennan, me zai hana Afnan ta cigaba da zama a part ɗina har lokacin da zata yanke hukuncin zama da shi ko kuma akasin haka, idan har ta ce baza ta iya ba na yarda a raba auren"

"Eh nima na yarda Mommy dan Allah kar ki bari a raba mu"

Me martaba ne ya ce "Shikenan Gimbiya ki zauna part ɗinta har mu san abin da zamu yi"

Wani irin sanyi Afnan ta ji a zuciyarta amma bata nuna alamun komi ba, sai ma ƙara ɓata fuskar da ta yi kamar bata so.

A haka Mommy ta kama hannunta suka fice daga ɗakin, zumbur Muby ya miƙe shima zai bi bayansu Alhaji ya ce "Dawo ka zauna idan ba haka ba ranka zai ɓace" Zuciyarsa ba daɗi ya koma inda ya tashi sai satar kallon Afnan yake har suka fice daga ɗakin.


ƘASAR SENEGAL
.............................
Su Sarki Shuraihu kuwa zaune yake fada yana tafiyar da mulkinsa, ba laifi jikinsa ya yi sauƙi sosai, kuma duk wani binciken da ya saka an gama yi, Mama kuwa kullum sai ta zagesa tassss kamar yaronta, Me martaba kam sai dai ya kalleta ya yi murmushi.


Suna cikin haka babban hadiminsa ya yi sallama tare da rusunawa ƙasa ya ce "Allah ya ja zamaninka mun gama komi mutanen na jiranka a babban parlour.

Murmushi Sarki Shuraihu ya yi kafin ya ce

"Yawwa zaka iya tafiya"

Sai da ya gama sallamar mutanen da ke fadar kafin ya nufi inda baƙinsa suke.

Mama da ke saukowa daga ƙasan steps ne a gefenta aminiyarta ce suna dariya har da tafawa, gaba ɗayansu kasa motsawa suka yi ganin su Fulani zaune suna fira cikin nishaɗi.

Bakin Mama na rawa ta ce "Kutumar Uba, dama kuna raye? ƙarya ne wallahi ai na daɗe da sakawa a kashe min ku, lallai mafarki nake yi ba gaskiya ba ne"

Alhassan da ke gefen Husna ne ya miƙe tsaye idanuwansu sun warke Alhamdulillah ya ce "Tabbas ba mafarki ba ne, gaskiya ne cewar muna raye kuma sai kin bar gidannan"

"Ihuuuuu....., kai ina baza ta saɓu ba, babu wanda ya isa ya fitar da ni a gidannan"

"Har da wanda ya gina gidan?"

Suka ji muryar Me martaba yana mai shigowa daga cikin parlourn.

Da gudu su Husna suka nufi Baffan nasu suna mai rungume shi, cikin tausayi da farincikin ganin ƴaƴan nasa ya ce "Allah ya yi muku albarka"

Da ameen suka amsa suna mai janyewa gefe, ƙawar Mama kuwa cikin dabara ta fice daga parlourn.

Wasu mutane kusan su biyar da sojoji goma ne suka shigo, Mama na ganin samarin da ta sa su kashe su Fulani ta fara ja da baya da niyar haurawa sama, da gudu sojojin suka taro ta tare da taso ƙeyarta a gaba, Me martaba ne ya ce "Haƙiƙa kin ci amanata, kuma Allah ya isa tsakanina da ke, dan haka na sakeki saki Uku babu ke babu gidana, kuma yanzu za ki je inda za ki girbi abin da ki ka shuka"

Ihu da kururuwa Mama ta fara tana roƙon yafiya, ko kallonta su Hajiya basu yi ba sai ma barin parlourn da suka yi.





*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 24



Tun da Muby ya bar gidan be dawo ba sai dare, part ɗin Maifinsa ya tafi inda ya samu Alhaji da Ameer suna fira,

Please Login or Register in order to submit comment