Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mulkin naki yake da gadara" Muby ya faɗa yana tallafota tare da maidata kan bed ɗin, hannunta ta saka gaba ɗaya ta janyosa ya faɗa kanta, waro kyawawan idanunsa ya yi yana ƙoƙarin janye jikinsa amma duk ta harɗe shi, sai wani ƙara shige masa take kamar wata mage, hijab ɗin da ke jikinta kuwa tuni ya yi nasa gefen, har wani duhu-duhu yake gani, dan tun ranar da ya fara kwana da Maimun baya iya yini ɗaya Feelings ɗinsa be motsa ba, ba ƙaramin riƙo Afnan ta yi masa ba, dan har wani aza masa ƙafa ta yi kan cinyarsa, a hankali ya fara ƙoƙarin zare ƙafar nata amma ta manne masa, sun jima a haka har jikinsa ya fara rawa kamar mazari, be san lokacin da ya haɗe bakinsu guri ɗaya ba dan already fuskarsu a kusa da juna take, gaba ɗaya ya ya fice a hayyacinsa ba ƙaramin daɗin kissing ɗinta yake ba a kowanne lokaci idan zai yi, tamkar su tabbata a haka, duk ya gama zaucewa, cike da ƙarfin hali ya haura kan bed ɗin tare da gyara kwaciyarsa kanta, duk da cewar bacci Afnan take amma tana jin yanda sassan jikinta ke amsawa saƙonninsa, ba ƙaramin daɗin hakan take ji ba, sai wani turo bakin nata take tana zura harshenta, Muby na ganin haka ya cafke harshen yana mai yi masa wani irin haɗiya kamar wanda ya samu sweet.






*SAI FA HAƘURI YAU PAGE ƊIN BA YAWA*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 16




Tun yana iya haƙurin yanayinsa har ya kasa jurewa, cikin basira ya cire mata kayan jikinta yana wani ƙara shige mata, Afnan kam baccin ne ya ƙara daɗi bata ma san wacce duniyar take ba, ƙarar wayarsa ce ta fargo da shi daga duniyar da ya shiga, mugun zafi mararsa ke masa ga kiran wayar na shigowa akai-akai, da ƙyar ya matsa inda wayar take ganin sunan Me martaba ne yasa shi saurin ɗagawa cike da girmamawa, ya jima yana wayar kafin ya ƙatse, toilet ya nufa a gaggauce ya ƙara yin wani wankan, cikin shigar manyan kaya shadda milk colour ya fito, ya haɗu kamar ka sace, har a lokacin Afnan bacci take kayan jikinta ya maida mata yana mai ɗaukar wayoyinsa ya fice daga ɗakin.

Sosai yake sura guda kan hanya har ya isa gidan, tun a harabar gidan kake jiyo yanda Dad ɗin Fadila ke zuba masifa, ba ƙaramin tashi hankalin Muby yayi ba ganin tarin mutanen da ke gurin, Fadila kuwa na gefe sai zare ido take kamar tsohuwar mayya, tana ganin Muby ta yi saurin ƙaraso inda yake cike da lanƙwasa ta kama hannunsa, murmushin yaƙe ya sakar mata yana mai faɗin "Me yake faruwa ne haka?"

Fari ta yi da ido tana wani gyara zaman Alkyabbar da ke jikinta ta ce "Neman aurenka mu ka zo, amma Abbanka ya ce ba zai bayar ba"

"What, aurena kuma?"

"Eh Dear wani abun ne dan na zo neman aurenka da kaina? tun yaushe nake son ka turo ayi maganar aure amma har yau ka kasa shiyasa na ce Dad ya zo neman auren ko na kashe kaina"

Hannunsa ya janye daga riƙon da ta yi masa yana mai nazarin maganarta "Amma kinsan ina son mace me aji ko?"

"Dear na sani amma duk abin da na yi ai soyayyarka ce ta ja mun"

"To duk wannan faɗan da Dad ɗinki yake yi na meye ne?"

"This's nothing Dear, Dad ɗina ne fa"

Cewar Fadila tana ɗaure fuska, shima haɗe fuska ya yi tare da ƙarasawa inda su Me martaba ke tsaye, cikin gimamawa ya rusuna har ƙasa ya gaishe su, da kallon banza Dad ɗin Fadila ya bi shi, "Gara da ka iso dan ayi komi ya ƙare" Cewar Dad ɗin Fadila.

Ɗagowa daga duƙen da yake Muby yayi "Allah ya ba ka nasara me yake faruwa ne?"

Sarki Ahmad ne ya maida kallonsa can inda Fadila ke tsaye ya ce "Dama maganar Gimbiya Fadila ne, a matsayina na Mahaifinka na katse alaƙar da ke tsakaninku, idan har ka sake ɗaga wayarta ban yafe maka ba" Wata irin razananniyar ƙara Fadila da ta ƙaraso gurin ta yi, ihu take kamar me sabon hauka Muby kam ya kasa ɗaga ƙafafunsa daga inda yake saboda baya ganin mutanen da ke gurin da kyau, Dad ɗin Fadila kuwa riƙeta yayi ganin tana neman zubawa da gudu, sai ƙoƙarin cafko Muby take amma Sarki Ahmad ya tare, cikin tsawa Me martaba ya ce ayi waje da su Fadila da Dad ɗin nata, tun abun na ƙarami har ya dawo babba dan Muby faɗuwa a gurin ya yi, nan take aka shige da shi Clinic ɗin da ke gidan, Fadila kuwa Dad ɗinta ne ya ja ta har zuwa inda aka baje motocinsu, ba ƙaramin rikicewa Fadila ta yi ba sai zage-zage take, har Dad ɗin nata bata bari ba.


Sai kusan yamma Muby ya farfaɗo amma baya iya taɓuka komi, a gefensa su Mommy ne da Ameera, suna yi masa sannu da jiki.

"Ina Fadila Mommy? please kar ku rabani da ita wallahi ina ƙaunarta"

Cike da tausayawa Mommy ta ce "Ka kwantar da hankalinka baza ka rasata ba, zan yi magana da Abbanka, Ameera haɗa masa tea ko jikinsa zai ƙara sakewa"

Tashi Ameera ta yi tare da fara haɗa masa, shi ko Muby kasa magana yayi dan jikinsa ya gama yin sanyi zuciyarsa sai bugawa take, gaba ɗaya ya mance da batun Afnan, shi muryar Fadila ce kawai yake buƙatar ji a halin yanzu, shigowar Alhaji Babba ne yasa Mommy tashi tare da faɗin "Allah ya taimakeka sannu da ƙarasowa"

"Yawwa sannu ya me jikin?"

"Jiki yayi sauƙi amma sunan Fadila ne ke bakinsa har yanzu" Mommy ta faɗa tana marairaice fuska.

Kusa da shi Alhaji ya zauna yana yi masa sannu, kawar da kai Muby yayi cike da gadara.

Alhaji ne ya ce "Ɗan nema kai, magana nake ma ka juya fuska"

"Idan har ba maganar Fadila ba, meye amfanin saurara" Cikin fushi Mommy ta ce "Yarima ka san da wanda ka ke magana, Alhaji ne a gabanka"

Tashi yayi da ƙyar sai a yanzu ya tuna da Afnan da kuma halin da take ciki, daidai lokacin da Ameera ta kawo masa tea, wani kallon banza ya watsa mata yana ficewa daga ɗakin, murmushi Alhaji ya yi tare da faɗin "Barshi kawai na san yanzu baya cikin hayyacinsa, Ameera ki faɗawa Driver ya sauke shi a gida kar ya yi Driving da kansa"

Da to Ameera ta amsa tana bin bayansa.

Lokacin da ta isa ma har Muby ya bar gidan, dan haka ta koma ciki.

Cike da dauriya ya nufi part ɗin nata, tun kafin ya gama ƙutsa kai ya ji saukar pilo a kansa, dafe kan nasa ya yi jin zafin da yake masa, gaba ɗaya Afnan ta watse parlourn da tarkace, ƴan aikinta kuwa suna gefe babu halin su magana, ganin Muby ya shigo yasa kowaccensu shigewa ɗaki, Afnan kuwa da gudu ta ƙaraso tare da ɗane masa jiki tana dariya, zubewa suka yi kan sofa su duka dama shi ba wani ƙarfin jikinsa yake ji ba, dukan ƙirjinsa ta fara tana matso ƙwalla, kamar zai maketa ya ɗaure fuska yana mai nufar sama, ai ko ta ƙara manno sa tare da faɗin "Yunwa nake ji Momma" Waro ido Muby ya yi jin abin da ta faɗa, "Yunwa ba ki ci abinci ba ne?" Girgiza masa kai ta yi tana tsalle sama, wani yarrr Muby ya ji ganin yanda dukiyar fulaninta da duk wata siffar jikinta sun motsa, cike da dauriya ya nufi kan daining da ita, lafiyayyar shinkafa ce joluf wadda ta sha karas da kayan ciki, sai ƙamshin girkin ke tashi, a gefe kuwa lemun kankana ne me sanyi wanda aka haɗa da Apple, sosai ta ci abincin duk ta ɓata gurin kamar ƙaramar yarinya, shima ya ci kaɗan ba laifi sannan ya haura sama cikin dabara dan ya samu ya watsa ruwa tare da rama sallar da ake binsa.

Lokacin da Afnan ta gama cin abincin ta nemi shi ta rasa, kuka ta fara har da hawaye, ƙofar parlourn ta fita dama doguwar riga ce a jikinta ruwan toka me kyau, a gaban rigar akwai tambarin sarauta, hular kanta ma a bakin ƙofar ta jefar, ba tare da sanin inda ta nufa ba ta fito harabar gidan, daidai lokacin da Maimun ke dawowa daga fitar da ta yi, ganin Afnan na tsalle-tsalle ne kuma ba takalma a ƙafarta ga gashin kanta ya wani baje ne yasa Maimun bushewa da dariya, Afnan na ganinta ta nufi gurin sai dariya take.

"Aunty alawa ki ka sayo mun ne?" Maimun da ke kallota cike da mamaki ta ce "Gimbiya lafiyarki kuwa?"

Dariya Afnan ta yi har tana ƙoƙarin karɓe jakar da ke hannun Maimun "Ina Gimbiya ta bani alawar, ko ke ce Gimbiyar?" Afnan ta faɗa.

Ganin haka yasa Maimun fara matsawa tana neman hanyar gudu dan taga alamar taɓin hankali ne ya sameta, ai kuwa suka tasa tsere tsakanin Afnan da Maimun, cikin mugun gudu Maimun ta faɗa part ɗinta tana mai rufe ƙofar, Afnan kuwa ta saka kuka har da birgima a ƙasa, sai da ta gaji dan kanta ta nufi gate ɗin gidan, tun daga nesa Gate Man ke kallon ikon Allah babu halin ya yi magana ta fara yi masa masifa, gaba ɗaya hankalinsa be kai ga tunanin hauka ke damunta ba, duk Dogaran da ke hanyar kusan su hamsin kowa da aikinsa, har ƙasa suka rusuna suna kwasar gaisuwa, ba tare da Afnan ta san abin da suke ba ta buɗe ƙofar tana mai ficewa daga gidan gaba ɗaya.


Sai da ta yi tafiya me nisan gaske har bata iya ganin gidan da ta fito, duk abin da ta gani a hanya sai ta ɗauka tana faɗin zata ajewa Momma, cikin rashin sa'a wasu ƴan iskan unguwar suka biyo ta hanyar cikin mota su uku, ɗaya daga cikinsu me tuƙin ne ya ce "Oga ga wata kaya can fa"

Wanda aka kira da Oga ne ya ce "Wace iri ce tamu ce ko tasu"

"Tamu ce Oga dan wannan ta wuce zinari ma"

Jin haka yasa Ogan nasu ɗagowa da sauri tare da bada umarnin a tsayar da mota, Afnan kam sai tsinto leda take, ba zato ba tsammani ta ji an ɗageta sama, ihu ta fara tana dukan bayansa amma ina ko a jikinsa, a motar suka sakata cikin tsananin gudu suka bar unguwar da ita.



ƘASAR SENEGAL
............................
Salati ɗauke a bakinta ta farka daga baccin ranar da ya ɗauketa, duk zufa ya wanke mata jiki gabanta na dukan uku-uku ga wani tsoro da ya mamaye mata zuciya, Husna da shigowarta ɗakin kenan ta ƙaraso gurin da Mahaifiyar tata ke kishingiɗe cike da damuwa ta ce "Fulani lafiya kuwa?"

Ajiyar zuciya Fulani ta sauke karo na ba adadi ta ce "Wani mummunan mafarki na yi, ina fatar Gimbiya na cikin ƙoshin lafiya hankalina ya matuƙar tashi, Husna bani ruwa na sha ban taɓa irin wannan mafarkin ba sai yau" Damuwa kwance kan fuskar Husna ta matsa kusa da Fridge ɗin da ke gefe ta ɗauko mata Faro tare da zubawa cikin Cup ɗin Gold, miƙa mata ruwan ta yi "Amma Fulani me hakan ke nufi?"

"Bana da tabbaci Husna kawai na san cewa akwai abin da ke shirin faruwa da ƴata, Allah ka tsare min ita a duk inda take"

"Ameen ya Allah Fulani" Su Alhassan suka amsa waɗan da shigowarsu kenan.

Kusa da Mahaifiyar tasu suka zauna, Muhseen ne ya ce "Fulani wai nikam meye matsalar matar can ne? gaba ɗaya ta tsanemu ko gaisuwarmu bata amsawa"

Daga jin haka Fulani ta san Mama yake nufi, murmushin yaƙe ta yi tana faɗin "Ina ganin dan rashin sabo ne, amma zata amsa wata rana"

Alhassan ne ya ce "Ni ban taɓa gaidata ba, asalima na tsaneta"

"Subhanallahi Alhassan bana son na sake jin haka daga bakinka, kar ka mance itama uwa ce a gareka"

"Shikenan Fulani insha Allah ba za a ƙara ba"

Husna ce ta ce "Yarima Alhassan yaushe zamu tafi gidansu Gimbiya, Allah na ƙagu na tafi"

Sunan da ake kiran su Alhassan kenan, murmushi ya sakar mata yana mai buɗe mata hannu alamar ta taho garesa, kan cinyarsa ta zauna tare da turo baki "Yaushe zamu tafi?"

Ta sake tambayarsa, Muhseen da ke gefen Fulani a kwance yana latsa waya ne ya ce "Ko dai Ameer ki ke son gani?"

Zumbur ta miƙe cikin alamun kunya ta ce "Allah Yarima Muhseen ba haka ba ne, kawai Gimbiya nake son gani"

"Hmm kin maidani marar ido ko? tun ranar da muka zo gidannan na gane kuna soyayya da Ameer, dan har a gaban wayarki hotonsa ne"

"Nima na sani, dan shima a gaban wayarsa hotonta ne ya saka, a ranar da muka tafi Sudan" Cewar Alhassan yana dariya.

Shuru Husna ta yi tare da rakuɓewa gefen Fulani da ke kallonsu cikin murmushi.

Kamar daga sama suka ji an duko ƙofar, Mama ce tsaye kamar wadda aka yiwa dole, daga Ahassan har su Husna ɗauke kai suka yi ga barin kallonta, haushi ne ya ƙara kamata cikin masifa ta ce "Yarasulillahi, yanzu tarbiyar da ki ka bawa ƴaƴan naki kenan? na shigo ɗaki amma ko gaisuwa ban samu ba"

Fulani ce ta ce "Allah ya ba ki haƙuri ki ƙaraso daga ciki mana"

"Ba zama ya kawoni ba, kai Alhassan ina takaddun gidajen da Mahaifinka ya ba ka a daren jiya, ina buƙar guda uku daga ciki" Shuru Alhassan ya yi kamar bada shi take ba, tsawa Fulani ta daka masa cikin ɓacin rai ta ce "Yarima ba magana ake maka ba?"

Cike da izzah ya ce "Fulani ki barta kawai, shi Baffa da ya bani takaddun be ce na bayar ga wani ba"

"To ba ka isaba wallahi ko Uban naka be isaba" Cewar Mama cikin masifa.

A fusace Alhassan ya miƙe ransa ya masifar ɓaci har wani kaɗawa idanunsa suka yi tsananin ɓacin rai "Ya isheki Malama ina ganin girmanki, takaddu kuma baza'a bada ba" Ficewa daga ɗakin ya yi cike da ɓacin rai, shima Muhseen ya bi bayansa ba tare da ya kalli inda take tsaye ba.

Ran Mama ya ɓaci sosai ga haushin shariyar da kowa ya yi mata, "Gaba ɗayanku sai kun yi nadama, musamman waɗannan shegun ƴaƴan naki, duk sai kun bar gidannan lokaci ne kawai nake jira mtsssss"

Mama ta faɗa tana ƙoƙarin barin ɗakin, cikin dauriya Fulani ta ce "Allah ya fiki insha Allah babu abin da za ki iya"

Dariya Mama ta bushe da shi tana wani fari da ido, "Ki maida hankali da kyau, kin san wacece ni kuma kin san abin da zan aikata, har kun isa ku ɓoye min haihuwar ƴaƴanki maza, to baza su yi dogon numfashi ba a duniya har ke ba zan lamunta miki ba" Jin abin da ta ce ne yasa Fulani shuru, dan bata son dogon zance, Mama ko masifa ta cigaba da yi tana zage-zage daga ƙarshe ta fice daga ɗakin, Husna da ke gefe ne ranta na zafi ta ce "Fulani wai meyesa Mama bata tsoron Allah ne?"

"Shhhhhhh...." Fulani ta ɗora yatsarta kan bakin Husna, "Ki daina cewa mutum baya tsoron Allah be dace ba, ta haifeki har ma wanda ya fiki"

Gigirza kai Husna ta yi alamun ta ji.


Mama na fita daga ɗakin ta nufi part ɗinsu Alhassan dan ta san yanzu haka sun nufi Fada, sai da ta gama zuba garin magani iri-iri kafin ta fara neman takaddun gidajen, babu inda bata duba ba amma komi bata samu ba, dan dole ta bar part ɗin cike da takaici, a ranta ta ƙudurta ɗauke dakaddun ta wacce hanya, bata jima da fita ba Alhassan ya shigo, daga can kan bed ya haura tare da ciro CC.Camera da ya saka a ɗakin, duk abin da ya faru sai da ya gani haka kuma duk inda ta saka maganin sai da ya cire, ba tare da ya faɗawa kowa ba ya je can bayan lambun da ke gidan ya zuba a ƙasar da ke gurin sannan ya kwarawa maganin ruwa.


Ɗakin me martaba ya nufa dan ya bincika abin da ke faruwa, nan ma CC.Camera ya cire wanda ya saka.

Duk wani layun da Mama ta saka da maganin da ta barbaɗa sai da Alhassan ya cire su, a can bayan gidan ya tafi ya ƙona su, ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin wata laya ɗaure da sunan Sarki Ahmad da kuma Sarki Shuraihu, tattarasu Alhassan ya yi tare da ƙonawa, tabbas ya san cewa be gama aikin da ke gabansa ba, dan ba iyakar ƙulle-ƙullen da Mama ke aikata a gidan ba kenan.

Sannan ya ƙudurta a ransa sauran ɗakunan da be saka CC.Camara ba anjima yake da niyar sakawa har ɗakin Mama ɗin.



ƘASAR SUDAN
............................
Muby kuwa bayan ya gama ne ya sauko ƙasa sanye cikin yadi me laushi da tsada na ƴaƴan sarakuna, ba ƙaramin kyau kayan jikin nasa suka yi ba musamman gashin kansa da ya sha gyara ga wani haske da fuskarsa ta ƙara, hular kansa na ɗauke da tambarin sarauta sai agogon Gold ɗin da ke hanunsa, ƙamshin turarensa ya gama baje parlourn, lokacin da ya sauko har su Mandula sun gama gyara haɗaɗɗen parlourn, ta ko'ina ƙamshin turaren huta ne ke tashi.

Afnan ya fara dubawa amma babu alamunta, Mandula da ke ƙoƙarin shiga ɗakinsu ne Muby ya kalla tare da faɗin "Ina Gimbiya?"

Sai da ta rusuna sannan ta gaishe shi, a fusace ya daka mata tsawa "Ina tambayarki kina gaishe ni, are you okay, na ce miki ina Gimbiya?"

Bakinta na rawa ta ce "Allah ya ba ka nasara wallahi bansan inda ta tafi ba"

"Ba ki san inda ta tafi ba, waye ya buɗe mata ƙofa, tafi ki kira mun su" Da sauri ta shige ɗakin, basu jima ba suka fito su duka tare da rusunawa ƙasa "Ina Gimbiya?" Abin da suka ji ya faɗa kenan, ransa a ɓace.

A tsorace suka ce basu ganta ba, kamar Muby zai yi musu dukan tsiya haka ya fice daga parlourn, tun daga bakin ƙofar part ɗin Maimun yake jiyo sautin waƙa na tashi, a parlour ya sameta daga ita sai pant da bra tana rawa hannunta ɗauke da Cup na Jus sai wani karairaya take, cikin fushi ya kashe waƙar sai a lokacin ta san da shigowarsa, jikinta na kyarma ta ce "Baby lafiya kuwa?"

Ba tare da ya amsa mata ba ya ce "Ina Gimbiya?"

"Gimbiya kuma? haba Baby nifa tun da ka ce na koma ciki ban fito ba, ina ganin ta tafi gurin kwartonta ne ba tare da ta faɗa maka ba"

"Idan ki ka sake alaƙanta matata da wani wallahi sai na fasa miki baki, ko babu komi tana da aurena a kanta ba za lamunce haɗata da wani banza ba"

"Calm down Baby ga wannan lemun ka sha, ni bansan inda ta tafi ba, tun a lokacin da na ganta da safe har yanzu ban sake ganin ko inuwarta ba"

Cewar Maimun tana matso shi tare da miƙa masa Cup ɗin da ke hannunta, sai wani shafa ƙirji take.

Wani banzan kallo ya watsa mata yana barin parlour, taɓe baki ta yi tana mai sakin waƙarta ta cigaba da taka rawa, sai wani shafa jikinta take.


Babu inda Muby be duba a gidan ba amma babu alamun Afnan, gaba ɗaya masu tsaron gidan ya tattara tare da tambayar ko da wanda ya ganta, amma maganar ɗaya ce suke faɗa, sun ganeta a harabar gida daga nan basu sake ganinta ba, gate man ne ke faɗa masa ɗazu ta fita amma be san inda ta tafi ba, wani mahaukacin mari Muby ya ɗaukesa da shi wanda ya sa Gate man ɗin ɗauke wuta na ɗan lokaci, a harzuƙe Muby ya ce "Ina buƙatar motoci hamsin a yanzunnan, idan har wani abun ya sameta babu wanda zan ragawa a cikinku"

Da sauri ya koma part ɗin nata, ba wani jimawa ya yi ba ya fito cikin shigar ƴaƴan sarakuna sosai Alkyabbar jikinsa ta yi masa kyau, yau har da rawani ya saka, idanunsa kawai ake gani, takalman ƙafarsa kawai za su kai dubu ɗari, balle agogon hannunsa da zai kai kimanin million ɗaya, fuskarsa tamau idanunsa kuwa sun gama rinewa, gashin idanun nasa har kwanciya suka yi tare da nannaɗewa daga sama, a harabar gidan ya samu motocin da ya saka a tanada masa guda hamsin kowacce mota ɗauke da tambarin YARIMA GIDAN MULKI, nan take aka wangame haɗaɗɗen gate ɗin gidan motocin suka fara ficewa.

Maimun da ke laɓe bakin ƙofa ne ta koma ciki da sauri ta ɗauko wayarta, numbern Hajara ta danna bugu biyu ta ɗaga a tare suka saki shewa har da wata irin dariya, Maimun ta ce "Bugun zuciya ai yau farinciki fal a raina"

Cike da son jin gulma Hajara ta ce "Sanar dani abin arziƙin da ya faru"

"An nemi Gimbiya an rasa" Bushewa da dariya suka ƙara yi cikin tsantsar mugunta Hajara ta ce "Shegiyar banza baza mu bari ta dawo gidannan ba, Allah yasa ƴan yankar kai ne suka hantama da ita"

"Ni kaina ina fatar haka saboda ta tasani a gaba cikin gidannan, jiya ma kwananta na karɓe amma ko a jikinta"

"Wai Maimun me ki ke yi da Yarima ne har yanzu? please lokaci ya yi da za ki ja naki rabon mu ƙara gaba"

"Ki kwantar da hankalinki ina jiran wani abu ne kafin komi ya haɗu, yanzu dai bari na shiga wanka kafin a dawo neman munafukar, Allah ya sa gawarta zasu tsinta a hanya"

Cikin dariya Hajara ta ce "Ke muguwa ce wallahi"

"Ai a tare mike muguntar bye zamu yi waya anjima"

Sallama suka yi kowa da abin da ke ransa.


Su Muby kuwa a hankali suke bin unguwar lungu da saƙo, amma babu alamun Afnan har kusan magrib, Muby ne ya bada umarnin a dakatar da motocin, haka ko aka yi gaba ɗaya motocin tsayawa suka guri ɗaya, kusan mintuna uku yana bincike a Laptop ɗinsa da ke kan cinyarsa, wayarsa da ke gaban rigarsa ya ciro tare da danna numbern Ashwan buga ɗaya ya ɗaga, ƙasa-ƙasa yake magana ba ka iya jiyo abin da suke faɗa, daga ƙarshe ya yanke call ɗin yana mai fitowa daga mota, a lokacin wani yaro ya gifta riƙe da leda zai kai kimanin shekaru sha biyar, ɗaga masa hannu Muby ya yi alamun ya ƙaraso, cikin girmawama yaron ya iso yana rusunawa tare da kwasar gaisuwa, "Dan Allah tambaya mike kai ɗan wannan unguwar ne?"

Washe baki yaron ya yi kamar wanda aka yiwa kyauta ya ce "Eh anan nake?"

"Yawwa muna cigiyar wata matashiya wadda baza ta wuce shekaru ashirin ba"

Sai da yaron ya ɗan yi shuru kafin ya ce "Idan har anan take gaskiya su Badaru sun sace ta, dan basa ganin mata su ƙyale, duk mancen da ta fito unguwar za su kamata su tafi da ita wani jeji inda suka gina gida, kuma Allah ya ba ka nasara fyaɗe suke yiwa mata, dan ko ɗazu sun ɗauki wata mahaukaciya a can gefen" Yaron ya faɗa yana nunawa Muby wata hanya da ke gefe.

A rikice ya ce "Za ka iya gane yanda yarinyar take?"

"Eh zan iya fara ce kuma me kyau daga gani ma sabuwar hauka ce"

Saurin damƙe hannunsa Muby ya yi yana faɗin "Ka san inda suka gina gidajen?"

"Eh na sani" Yaron ya bashi amsa.

Ɗaya daga cikin Dogaran Muby ya kira, da sauri ga ƙaraso yana faɗin "Allah ya ja zamaninka"

"Wannan yaron ku saka shi a motar gaba zai kai mu wani gurin"


Bada ɓata lokaci ba motocin suka bar unguwar cikin mahaukacin gudu.



*MASU ƘORAFIN RASHIN TYPING KULLUM NA FAƊA MUKU CEWA GAJEREN LABARI NE, KUMA LABARIN

Please Login or Register in order to submit comment