Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar kullum kwance take a ɗakinta misalin ƙarfe takwas na dare, ta sha'afa da danna wayarta ta ji ƙarar buɗewar ƙofar ɗakin, a masifance ta ce "Uban waye haka? bana son ana shigo mun ɗaki ba tare da tambaya ba"

Jin shuru ne yasa ta maida kallonta kan ƙofar, ihu ta saki a razane ganin Nabeelah sanye cikin fararen kaya idanunta da bakinta na zubar da jini, dariya Nabeelah ta yi me tsoratarwa sannan ta ce "Wannan shine gargaɗin da zan yi miki na ƙarshe, ki faɗawa kowa abin da ke faruwa" Matsowa Nabeelah ta fara yi kamar zata taɓa Fadila, ai kuwa Fadila ta saki wata irin ƙara tare da zubewa ƙasa a sume, koda ta tashi ta ganta ɗakin Dad ɗinta, a tsorace ta ce "Wayyo Allah ki mun rai wallahi zan faɗa, zan faɗa musu abin da ke faruwa, zan faɗa musu abin da na yi miki" Ba ƙaramin tashi hankalin Dad ɗin nata ya yi ba jin abin da take faɗi, "Shalele calm down, me za ki faɗa ne?"

Kuka Fadila ta fashe da shi kafin ta ce "Mom ina Mom? ku fara kiramun ita wallahi zan faɗa muku abin da na yi"

Cikin rarrashi Dad ɗinta ya ce "Ina zuwa ki jirani yanzu zan tafi da kaina na kirata"

Da gudu ta miƙe daga kan bed ɗin "Mu tafi tare idan na zauna kasheni zata yi"

Dan dole Me martaba ya kamata suka fice daga ɗakin.






*Sai mun haɗe a next page, anan ne zamu san menene Gimbiya Fadila ta aikata, shin Yarima zai yiwa Maimun dole ko zai ja girmansa, menene dalilin da ya sa Maimun canzawa Yarima, duk amsar wannan zamu samu a next page, ku cigaba da bibiyar alƙalamin Asmeetar Hydar domin jin yanda zata kaya, 😛 na san kuna jin haushin rashin typing kullum, to am so sorry for that masoyan littafin gidan Mulki, ƙaunarku nake har raina, ayi sharing a duk group ɗin da ku ke ciki, ina buƙatar sharhi fiye da yanda ku ka saba yi min hakan zai bani damar zuba muku lafuzza masu daɗi*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*






P. 18




..........................................................
Har gidan iyayen Mom ɗin Fadila suka tafi, wanda da ƙyar aka samu ta shigo babban parlourn, a lokacin tashin hankalin Fadila ya ƙara yawaita, jikinta na rawa idanuwanta sun gama zazzarowa, ai bata ƙara shiga tashin hankali ba sai da taga Nabeelah da wata Dattijuwa wadda zata yi sa'ar Mom, cikin ruɗu Mom ɗin Fadila ta miƙe daga zaunen da take bakinta na rawa ta nuna Dattijuwar matar ta ce "Asabe......?"

Wadda aka kira da Asabe ce ta durƙushe ƙasa tare da rushewa da kuka, gaba ɗaya mutanen da ke ɗakin sun zuba ido suna kallon ikon Allah, Fadila kuwa ihu take tana faɗin "Dad please ka taikameni ga Nabeelah zata kashe ni"

Cikin tashin hankali Dad ɗin nata ya kamata, yana mai ruƙunƙumeta a jikinsa, duk jikinta ya saki numfashinta kuwa ya fara neman tsayawa, Asabe kam idanunta na ƙasa cikin alamun kunya.

Bayan kowa ya natsu ne Asabe ta ƙara share hawayenta cikin sanyin jiki ta fara bada labari kamar haka, "A lokacin da mike ƴammata shekaru da dama da suka wuce, ni ƙawar Fulani ce wadda kowa ke tsammanin Mahaifiyar Fadila ce, a kullum ina jin haushi da takaicin yanda maza ke neman aurenta musamman masu kuɗi, tun da na samu labarin cewa akwai wani ɗan sarauta da ke neman aurenta hankali ya tashi na ji duk duniya na ƙara tsanarta, daga nan na fara bin bokaye da malamai a kan a hana auren amma Allah be nufa ba, bayan aurenta da kwanaki na sa bokana ya kasheta, sai dai ya ce zai hanata haihuwa dan kisan kai ba zai yuba ba, haka dai na zauna ni ba aure kuma ba makaranta har wani saurayina ya yaudareni ya yi min ciki, a lokacin kuma nake samun labarin Mahaifiyar Fadilah tana da ciki, ba ƙaramin shiga damuwa na yi ba amma sai na ƙudurtawa zuciyata mugun nufi, cikin ikon Allah ranar da nake ciyon naƙuda a ranar ƙawata ke ciyon itama, asibiti ɗaya aka kai mu da ita, saurayina kuwa ya san duk abin da ke tsakanina da ƙawar tawa, shine ya haɗa kai da likitan aka canza ƴaƴanmu, Fadilah ita ce asalin ƴata kuma jinina"

Salati gaba ɗaya ɗakin ya ɗauka, Mommy kam kasa magana ta yi idanunta sun ciko da ƙwallah, Fadila sai zare ido take tsabagen rashin gaskiya, Asabe na kuka ta cigaba da faɗin "Bayan an canza yaran ne na ɗauki ƴarku Nabeelah na bar ƙasar nan, amma mijina yana bibiyar ƴarmu Fadilah har ta mallaki hankalin kanta, lokacin da ya faɗa mata abin da ke faruwa ta ƙaryata shi har ma ta zazzageshi, hakan ya sa mu ka tafi hospital aka yi awon jini da kuma nuna mata shaidar abin da ke faruwa, tun Fadilah na shekaru sha biyar ta san cewa ni ce mahaifiyarta, amma sai na umarceta da ta ɓoye sirrin saboda zai amfane mu gaba ɗaya, da haka kuma na haɗa su ƙawance da Nabeelah ƴarku, wata ranar juma'a ce Nabeelah ta ji maganar da nake da saurayina wanda take tsammanin shine Ubanta, a lokacin ta ɗauki aniyar tona asirin da mike ɓoyewa, daga nan Mahaifin Fadilah ya kamata tare da rufe ta a ɗaki, washe garin ranar na kira Fadilah nake faɗa mata cewar Nabeelah ta samu labarin abin da ke faruwa, tun asubar fari Fadilah ta zo gidammu cikin ɓacin rai, wanda ya yi sanadiyar da ta yiwa Nabeelah illah har muna zaton cewa ta bar duniya, sannan muka ɗauketa tare da zubar da ita cikin wani jeji, sai bayan wata ɗaya da hakan ne Nabeelah ta dawo ƙasar nan, sannan ta fara yi mana barazana da cewar mu tona asirin abin da ke faruwa tun kafin ita ta faɗawa duniya, da farko mun yi tsammanin fatalwa ce, sai daga baya ta nuna mana cewar tabbas ba fatalwa ba ce"

Tsagaita kukan da take ta yi kafin ta faɗi gaban Mom ta ce "Ina mai neman afwa da girman Allah ki yafe mana, da ke da mijinki da kuma Nabeelah, kuma ba iyakar nan na tsaya ba na samu labarin........" Tun kafin ta faɗi abin da take son faɗa

Me martaba ya yi wurgi da Fadilah da ke jikinsa yana watsa mata mugun kallo, fuskarsa ta rine jajir ya kalli Asabe da ke raba ido ya ce "Tabbas kin cika azzaluma kuma makira maciya amana, tun lokacin da na ganki tare da matata na ji na tsaneki, kuma sai na hukuntaki wallahi da ke da mijin naki har wannan shegiyar ƴar taku"

Ya ƙarasa maganar yana nuna Fadilah da ke can gefe jikinta na ɓari.

Cikin ƙarfin hali ta miƙe da sauri ta nufi Mom tare da kama ƙafafunta, "Please Mom ki yafe min dan Allah, insha Allah zan zame miki ƴar kirki, ba zan sake saɓa miki ba amma kar ki ce na bar gidanku"

"Sake min ƙafa Fadilah tun kafin na yi miki mugun baki, tun kina ƙarama ki ke ƙona min rai kin kasance yarinya marar imani da tausayi, Allah ya isa tsakanina da ku ba zan yafe muku ba" Mom ta faɗa tana fashewa da kuka, Nabeelah da ke can zaune idanunta na hawaye ne ta matsa kusa da Mom ɗin nata suka rungume juna.

Sosai suke kuka cikin tsananin tausayi.

Me martaba kuwa ficewa ya yi daga parlourn, ba a jima ba ya dawo tare da wasu Dogarai kusan su goma ya ce a fita da su Fadilah, sai da aka yi da gaske kafin suka samu damar fitar da ita tana rusa ihu kamar zata tashi gidan gaba ɗaya, Mom ce ta ce "Allah mun gode maka da ka bayyana mana gaskiya, sai yau na gane abin da nake ji game da Fadilah, wallahi wasu lokutan ina cewa ba ƴata ba ce, amma haka nake danne zuciyata na yi istigfari"

Me martaba kuwa kasa kallon Mom ya yi dan wata kunyarta yake ji, saboda abubuwan da ya rinƙa yi mata saboda Fadilah.

Sun daɗe a gidan suna tattauna kan maganar kafin Dad ya nemi Mom ta koma gidansa, amma ta ce baza ta koma ba, sai da Nabeelah ta saka baki kafin ta yarda zata koma.

Haka kuwa aka yi suka koma gida cikin tsananin farinciki da annashuwa, Nabeelah yarinya ce me kamun kai, duk da cewar Asabe ta so ta zama tantariyar ƴar iska, amma Allah be nufa ba, shiyasa ma zamanta gurin iyayenta be yi wahala ba dan akwai tarbiyya sosai a jikinta.

Misalin ƙarfe tara na dare ta sami Mom ɗinta a ɗaki, bakinta ɗauke da sallama ta shiga amma ta kasa haɗa ido da ita, Mom ce ta ce "Nabeelah ƴata kunya ce haka? ki saki jikinki ni Mahaifiyarki ce kin ji ko?"

Murmushi Nabeelah ta yi cikin alamun kunya ta ce "Insha Allah Hajiya"

"Hajiya kuma? bana son wannan sunan ke ƴata ce ki kira ni da Mom"

Ƙara sunkuyar da kai ta yi kafin ta ce "Shikenan Mom, dama akwai maganar da ke tafe da ni".

"To ina jinki".

"Dama a kan Yarima Mubarak ne wanda yake son auren Gimbiya Fadilah"

Haɗe fuska Mom ta yi tana mai faɗin "Sunanta Fadilah ba Gimbiya ba, wacce Masarautar take mulki?"

Ƴar dariya Nabeelah ta yi jin abin da Mom ta ce, "Alright afwan Mom, to dama ina son mu tafi ƙasar Sudan gobe idan Allah ya kaimu, kuma tare da ke nake son mu tafi, saboda akwai wata magana da nake son faɗawa Yarima"

Shuru Mom ta yi na ɗan wani lokacin tana mamakin abin da Nabeelah ke son faɗawa Yarima, amma sai ta kawar da zancen ta ce "To Allah ya kai mu lafiya insha Allah zan sanarwa Dad ɗinki anjima"

Godiya Nabeelah ta yi cikin farinciki ta yiwa Mom sallama tana mai barin ɗakin.


ƘASAR SENEGAL
...............................

A ɓangaren su Alhassan kuwa ya tasa Mama a gaba, a kullum cikin gasa mata magana yake tare da nuna mata cewar ya san shirin da take a gidan, wanda hakan ya sa ta bazama bin bokaye dan a kashe su, duk inda ta aje laya ko ta zuba magani, Alhassan na bibiyarta daga ƙarshe ya cire abin da ta saka.


Yau ma kamar kullum zaune take gaban wani gagarumin bokanta wanda ƙawarta ta kawota, wani tsoho ne me muguwar fuska, ga uban gashin da ya zube kan fuskarsa me tsananin ƙazanta, dariya bokan ya yi cikin muryarsa me ban tsoro ya ce "Na san abin da ke tafe da ku, kina son a kashe magajin sarki sannan a kori matarsa daga gidan ko ba haka ba?"

Jikin Mama na rawa ta ce "Ƙwarai kuwa boka wannan shine abin da ke tafe da ni, kuma ina son a watsar da yaran nata, duk su mance da juna, amma abin da ke bani mamaki shine duk lokacin da zan yi wani aiki baya yi kamar akwai wanda ke lura da ni"

Dariya bokan ya sake bushewa da ita a karo na biyu, sai da ya gama bincikensa kafin ya ɗago da jajayen idanunsa ya ce "Wannan gaskiya ne, duk wani aikin da ki ke akwai Yariman gidan na bibiyarki, dan haka baza ki yi aiki da kanki ba, zamu saka Aljanu su yi miki komi, sannan zancen a raba kan ƴaƴan hakan ba zai yuwu ba, a halin yanzu Gimbiyarku ta haukace, kuma haukace da babu maganinta har abada, bincike na ya nuna cewar macece ta yi wannan aikin, ki faɗi wata buƙatar amma wannan ba za ki samu ba" Bokan ya ƙarasa zacen yana dariya irin ta mugayen Bokaye.

Ba ƙaramin farinciki Mama ta shiga ba jin labarin da bokan ya faɗa, cikin azama ta ce "Bana buƙar komi a yanzu kawai burina a nunawa Alhasaan kuskurensa, saboda na san shine kaɗai ke bibiyata, ina son ya yi nadama marar iyaka, saboda ya gane sirrina, Mahaifiyarsu kuma a bari har wannan aikin ya kammalu, ni da kaina zan yi maganinta, ina buƙatar komi ya dawo hannuna, ya kasance ni ke bada umarni a gidan".

"Ku aje mana abin sadaka sannan ku tafi aiki ya kammalu"

Cewar Bokan a tsawace.

Cike da tsoro su Mama suka aje kuɗi me yawan gaske tare da barin jejin.


Tun da ta sauka harabar gidan take jiyo maganar su Hajiya Babba, ai kuwa ta ƙara sauri cikin parlourn, a kwance ta sami Alhassan Muhseen da Husnah, cikin mawuyacin hali, cike da makirci ta ƙaraso tana faɗin "Subhanallahi me yake faruwa ne haka?"

Hajiya Babba ce ta fashe da kuka cikin kiɗima ta ce "Allah ne ya jarabci su Yarima da ciyon makanta, wanda ɗazu haka lafiyarsu ƙalau amma a halin yanzu basa gani"

Wani irin salati Mama ta rafka tana tafa hannu, kallonta ta mayar kan Fulani da ke gefe hawaye na zuba kan idanunta, kana ganinta ka san tana cikin mugun tashin hankali, magana kuwa bata fita a bakinta.

"Ashe abin da ke faruwa kenan to Allah ya sawwaƙa" Cewar Mama tana nufar ɓangarenta.

Da kallo Fulani ta bita tana mai girgiza kai.

Husna da ke kwance kan cinyar Hajiya ta ce "Fulani bana ganin komi, dan Allah ku saka min magani ido zafi yake min"

Cikin tausayawa da ƙarfin hali Alhassan ya ce "Ƙanwata ki daina kuka kina jina ko? komai da ki ke gani nufi ne na Allah, kuma Allah S W T ya ce mu rinƙa karɓar ƙaddara me kyau ko akasin hakan"

Kuka ne ya kwacewa Fulani ta miƙe da sauri ta bar parlourn.


Lokacin da Me martaba ya shigo daga ciki, ko kallon inda yaran suke be yi ba, ya nufi ɗakin Mama, da mamaki Hajiya Babba ta ce "Shuraihu lafiya kuwa ko ba ka samu kabarin abin da ke faruwa da yarannan ba ne?"

Cikin ɗaga murya abin da be taɓa yiwa Mahaifiyar tasa ba ya ce "Sai me ya faru? ai ba ni na ɗora musu ciyon makantar ba, dan Allah kar wani ya dameni zan shiga daga ciki"

Ba tare da ya tsaya jin abin da Hajiya zata ce ba ya bar gurin.

Muhseen ne ya ce "Hajiya anya Baffa ne kuwa wannan?"

Alhassan ne ya yi saurin cewa "Kar ka ga laifin Baffa, saboda na san cewa ba yin kansa ba ne"

"Yin waye to? har ni Mahaifinku zai faɗawa haka kamar ba ni ce na haifesa ba"

Cikin tausayi Alhassan ya kuma cewa "Dan Allah Hajiya ki yi haƙuri wallahi ba yin Baffa ba ne, insha Allah komi zai zo da sauƙi"


"Ai sauƙi kam sai gurin Allah makafin banza makafin wofi, ashe ƙaddararku kenan to Allah ya kiyaye gaba" Cewar Bilkisu da ke shigowa parlourn, Hauwa'u na bayanta sai dariya suke.

A fusace Hajiya ta ce "Ku dan Ubanku waye ya ce ku zo gidannan?"

Cike da rashin tarbiyayya Bilkisu ta ce "Sai dai Ubanki ba namu ba Hajiya, wannan ai cin fuska ne"

Hauwa'u ce ta karɓe zacen da faɗin "Komi ya wakana yanzu sai barin gidannan munafukan Allah, har ke Hajiya sai kin bar gidannan tun da ba na mijinki ba ne, idan kuma kina son ki je inda mijin naki ya tafi ne ai shikenan"

Kuka Hajiya ta fashe da shi wanda ya sa su Mamah fitowa da Me martaba, Fulani kuwa duk hayaniyar da ake tana ji daga sama amma sai ta kasa motsa koda ƙafarta ne.

Me martaba ne ya ce "Hajiya meya faru kuma?"

Husna da itama kukan take ne ta ce "Baffa su Aunty Bilkisu ne suka zagi Hajiya kuma har da cewa zasu kasheta"

Mari Bilkisu ta kaiwa Husna a baki ko alamun tausayi babu ta ce "Makirar banza to sai aka ce me? dan an zageta"

Mama ce ta yi shewa har da wata irin guɗa me ƙara ta ce "Yawwa ƴaƴan Albarka, kai kuma zo mu koma daga ciki ko zaka ramawa Uwar taka ce?"

Da sauri me martaba ya ce "A a waneni ai ban isa na rama mata ba" Komawa daga ciki suka yi Mama na wata tafiya kamar zata kare.

Alhassan da Muhseen kam kasa magana suka yi, har su Bilkisu suka ƙarace zaginsu da rashin kunya suka bar parlourn.

Hajiya Babba ce ta ce "Yarima ku tashi mu haura sama gun Mahaifiyarku"

Jagora ta yi musu har ɗakin Fulani, wadda a lokacin sai dai ta kalli yaran da ido amma babu bakin magana, a gadon da ke ɗakin Hajiya ta kwantar da yaran kafin ta zauna gefen Fulani, sun jima a haka ba tare da kowa ya iya cewa uffan ba, sai dai sautin kukan Husna da tun ɗazu ta kasa daina kukan nata, cikin ƙarfin hali Hajiya ta ce "Ina ganin shurun nan naki ba zai yi ba, dole zamu dage da addu'a da kuma sadaka fiye da yanda mike yi a baya, tabbas na tsorata da ganin gidannan ya juya lokaci ɗaya, wai yau ni Shuraihu ke ɗagawa murya" Hajiya ta faɗa tana mai danne kukan da ke shirin zuwa mata, Mama kam har yanzu bakinta ne ya kasa motsawa, dan ta san idan har ta ce zata yi magana kuka ne zai zo mata, nasiha sosai Hajiya ta yi musu tare da ƙara musu ƙarfin gwuiwa, a lokacin shi kansa Alhassan kasa danne hawayen nasa ya yi, dan namiji ne me dauriya da kuma taurin rai, amma jin yanda Hajiya ke magana ya sa zuciyarsa zafi da kuma tausayinta.

Mama kuwa suna shiga ɗaki ta kalli Me martaba cike da bada umarni ta ce "Akwai abun da nake son na faɗa amma ba shawara nake nema a gurinka ba" Kamar wata Uwarsa ya ce "Ina jinki ranki ya daɗe koma menene yanzunnan za'a yi miki shi"

Mumurshin mugunta Mama ta yi kafin ta ce "Sunana nake son a saka ga duk wata ƙadarorinka, har da wannan gidan da mike ciki, bayan haka a yau nake son ka kori munafukar matar can taka har ma da Hajiya Babba"

Cikin faɗuwar gaba Me martaba ya ce "Hajiya kuma?"

"Eh Hajiya ko baza ka iya ba ne?"

"A a wane ni? yanzu za su bar gidan, a gaban idonki ma kuwa".

Dariya Mama ta saki irinta cikakkun ƴan duniya tana mai bin bayan mijin nata.



ƘASAR SUDAN
............................
Muby kuwa yana ganin abin da Maimun ta masa ya sauko daga kan bed ɗin ransa a mugun ɓace, ba tare da ya ce komi ba ya fice daga ɗakin, tana ganin haka ta sauke ajiyar zuciya a fili ta furta "Ni babu wani daɗinka da nake ji, haba dan Allah ka wani mannewa mutum kamar maye daɗi ai sai Alhaji Fahad, mtsssss" Ta ja dogon tsaki tare da saukowa ta rufe ɗakin.

Yana jinta lokacin da ta rufe ɗakin nata, sosai mamaki ya ƙara kama sa, ya san cewa Maimun dai a budurwa ya sameta, to me hakan ke nufi tsoronsa take ne ko kuma ta daina yarda da shi ne.

A haka ya koma nasa ɗakin cikin nazarinta.

Asubar fari ya farka, ba tare da ɓata lokaci ba ya shige toilet dan ɗauro alwala, yana fitowa ya saka farar jallabiyarsa me ɗan karen kyau, ga wani ƙyalli da take yi kamar zinari, turare ya fesa masu ƙamshin gaske sannan ya nufi masallaci.


Afnan kuwa tun ƙarfe huɗu ta farka, gaba ɗaya ta hana kowa bacci a part ɗin, duk wanda ya nufi gurinta kuwa dukansa take, sosai haukar ta ƙara yawa ga wasu ƙurajen da ke fitowa a jikinta masu zafi, duk fuskarta ta gama lalacewa da su, har wani duhu ta yi kamar ba ita ba.

Duk masu aikinta sun tausaya mata matuƙa, musamman kukan da take yi, ga guje-gujen da ta rinƙa yi tun ɗazu, a haka har takwas na safe ya buga, lokacin Muby ya shigo gidan dawowarsa daga masallaci kenan, dirrect part ɗin Maimun ya nufa be san abin da ke faruwa da Afnan ba, kamar wancan lokacin haka ma yau ya rinƙa jin wani irin nishi daga ɗakin nata, har zai shiga kuma sai ya fasa yana mai nufar room ɗinsa, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga wanka, kusan mintuna talatin ya fito ɗaure da tawul, gashin kansa ya gyara kafin ya shirya cikin haɗaɗɗen yadi me masifar kyau blue me taushi, shigar ƴaƴan sarakuna ya yi dan har da rawani a kansa, yana son zuwa masarauta dan case ɗin matasan da ya kama, idanunsa kawai ake gani sai kuma gashin girarsa kaɗan me yawan gaske, ƙamshin turarensa ya gama baje room ɗin, cikin tafiyar ƙasaita ya sauko ƙasan, ba tare da ya nemi Maimun ba ya nufi part ɗin Afnan.

Shi kansa Muby hankalinsa ya tashi da ganin jikinta, tabbas ya san cewa wata cutar ce matasan suka laƙa mata, idan kuwa hakane babu wata mafita face ya rabu da ita, ya gama ƙudurtawa ransa rabuwa da ita, a fusace ya kira masu aiki idanunsa sun gama rinewa ya ce su kamata da ƙarfin tsiya ayi mata wanka dan ba zai iya taɓa jikinta ba.

Afnan na kuka da ihu haka suka kamata tare da nufar ɗakin nata da ita, a parlour Muby ya zauna yana mai dafe kansa da ke sara masa, lallai koma me zai faru ya faru tabbas rabuwa da ita shine mafita, abincin da ke kan dianing ma kasa ci ya yi dan ƙyanƙyamin da yake ji na Afnan, dole haka ya bar gidan.



Motoci ashirin ne suke take masa baya masu masifar tsadar gaske, shi ko yana cikin wata arniyar mota fara me tambarin YARIMA GIDAN MULKI, hannunsa kuwa news papper ne wanda aka kawo masa yau, a nan yake ganin abin da ya faru da Fadila da kuma abubuwan da ta aikata ita da Mahaifiyarta, godiya ya yiwa Allah da ya sa be aureta ba, wata irin muguwar tsanarta yake ji a halin yanzu, wanda shi kansa ya kasa gane dalili.


Su na isa Gate man ya wangame musu wakeken Gate ɗin, nan take motocin suka kunna kai ciki, Muby ya jima zaune a motar yana tunanin yanda zai ɓullowa lamarin, a ransa yake faɗin, na san idan na ce zan rabu da ita a gaban su Alhaji tabbas hanani za su yi, sosai ya shiga tunanin shin ya sawwaƙe mata ne tun kafin ya shiga gidan ko kuma ya bari a gaban iyayensu, dan ba zai iya zama da ita ba.




*Ku bibiyeni a next page dan jin wannan chakwakiyar, shin Sarki Shuraihu zai kori ahalinsa kamar yanda Mama ke buƙata? Ya maganar Nabeelah wace magana ce take son faɗawa Yarima? Wai Yarima Mubarak zai samu damar sakin Gimbiya Afnan tun a waje, ko har sai ya shiga ciki ne? menene silar fitowar ƙurajen da ke jikin Gimbiya, duk amsoshin tambayoyinnan za ku samu a next page insha Allah, ina buƙatar sharing da kuma sharhi fiye da yanda ake yi a baya*




*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*










P. 19



Kallonsa ya maida kan wasu Dogarai goma da ke ba Flowers ruwa, alamu ya yi musu da su ƙaraso, cikin biyayya suka iso tare da rusunawa, duk da cewar yana jin yanda suke gaidashi amma sai ya ƙara haɗe fuska yana faɗin "Ina matasan da na ce a rufe?"

Ɗaya daga cikinsu ne ya ce "Allah ya ba ka nasara ai tun jiya Me martaba ya bada umarnin a tafi da su Police station, Waziri ya tsaya sosai kan case ɗin har zuwa shiga kotu"

"Sarki ya samu labarin abin da suka aikata ne?"

"Eh Allah ya ba ka

Please Login or Register in order to submit comment