Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita ba, halinta ɗaya ne shine bata ƙaunar talaka, ina son ka koyawa kansa ƙaunarta koda ma ace ita bata sonka" Murmushi Muhseen ya saki sannan ya ce "Insha Allah Hajjo zan yi abin da kika ce, dama ni bana ƙinta, ita ce ke janye jikinta daga garemu".


Satin Afnan ɗaya aka gama komai na school ɗinta, a sati ɗaya kullum sai sun yi faɗa da Alhassan shi ko baya ɗaga mata ƙafa dan mugun tsoronsa take yi, akwai ranar da ya tashi yimata dukan tsiya, tun daga ranar take shayinsa daga ya kafa doka bata takawa kuma Brother sama Brother ƙasa, dan Alhassan akwai son girma, yau ta kama Monday kuma a yau zata shiga school ɗin da ta fara, tun ƙarfe shida na safe ta shirya cikin wata arniyar duguwar riga irinta ƴaƴan sarakuna milk colour, kana ganinta ka san babu inda zaka ƙushe ta, agogon hannunta ya sha ado wanda take haɗa shi da wayarta, wata Alkyabba black ta ɗora sama me laushi ta kwanta kan rigar, tun da ta fara saukowa ƙamshin turarenta ya fara baje babban parlourn har ta sauko inda su Hajjo da sauran mutanen gida ke zaune, Muhseen da shima school ɗin yake ne ya tsaya jiranta dan su tafi tare, saɓanin Alhassan da ya riga ya wuce dan shima a school ɗin yake, Mubina da masu kula da Afnan na tsaye dan ta ce a tare zasu tafi, da fara'a ta gaishe da Hajjo, itama Hajjon murmushin ta mayar mata "Gimbiya uwar Gimbiyoyi, takawarki lafiya me nisan kwana gabanki alkhairi bayanki alkhari, sannu da fama sarauniyar kyawawa ta duniya wa zai ja da ke ya kwana lafiya" Tun da Hajjo ta fara kirari Muhseen ke dariya, Afnan kuwa sai wani karairaya take ita ala dole ana yabonta, "Hajjo ni zan tafi sai na dawo, ina fatar an haɗa min motocin da na umarta ko?"

"A dawo lafiya, batun motoci kuma ki samu masu aiki a waje, wai baza ki ci abinci ba kafin ki tafi?" "Hajjo dan Allah barni yau azumin lada nake yi"

"To Allah ya bada lada" Cewar Hajjo. Har ƙasa Su Mubina suka rusuna tare da gaisheta ko kallon banza basu samu ba ta nufi hanyar fita.

Muhseen kuwa tashi yayi daga zaunen da yake, ƙananan kaya ne sanye a jikinsa ya masifar yin kyau, sosai kamanninsu ya ƙara fitowa, "Sai ki jirani mu tafi ke nake jira tun ɗazu amma kin yi kamar baki ganni ba"

A kasalance ta juyo sannu a hankali ta sauke idanunta kansa "Kaga nayi kama da wadda zaka fita tare da ita?"

"Shikenan ki tafi idan Yaya ya dawo zan faɗa masa kin ce kar na tafi school tare da ke" Haɗe fuska Afnan tayi kamar zata yi kuka ta ce "Mu tafi idan ka tashi" Bata jira abin da zai ce ba ta fice daga parlourn, Mubina ma bayanta suka bi har inda aka baje motocin kusan guda ashirin masu mafisar kyau da tsada, kowacce mota na ɗauke da tambarin GIMBIYA GIDAN MULKI, waro ido Muhseen yayi ganin yawan motocin, ko shi da Alhassan basu taɓa zuwa da mota biyu ba, iyaka su shiga ɗaya a tare dan ko Driver basa son ya kai su.

"Sister me kuma za'a yi da motocinnan? kamar masu zuwa wani taron biki" Banza tayi masa tana mai shigewa ɗaya daga ciki, su Mubina ma biyu suka shiga, Muhseen na ganin haka ya buɗe wadda Afnan ta shiga shima ya shige, kallonsa tayi cike da jin haushi ta toshe hanci "Meye haka? dallah malam ka canza wata mota"

Murmushi Muhseen yayi yana faɗin "Yaya zan faɗawa ko" Tun kafin ya ƙarasa magana ta ce Drivern ya wuce. Nan take motocin suka bar harabar gidan.


Ba wani tafiya suka yi ba aka iso haɗaɗɗar makarantar wadda ita ce ta ɗaya a garin Chad, idan kaga mutum a ciki tabbas ba ƙaramin arziƙi iyayensa ke da ba, tun daga gate ɗin School mutane ke jiyo ƙarar motoci kamar za'a tashi makarantar, wani irin ƙura ce ta baɗe gaba ɗaya filin School ɗin, a can gafe Alhassan ne kan wata farar kujera hannunsa ɗauke da book yana karatu, sarai yaji ƙarar motocin amma be ɗaga kai ba, sai lokacin da ya ji wata matashiya da ke gefensa na faɗin "Wacece kuma Gimbiya? kinga wai Gimbiya gidan Mulki" Ta ƙarasa maganar tana taɓa wata ƙawarta da ke gefe, sai a lokacin Alhassan ya ɗago kansa dan ya san tabbas Afnan ce, ita ce kawai zata yi wannan abin, daidai lokacin da Muhseen ya fito motar, mamaki ne ya kama Alhassan har ya ƙurawa motocin ido, kusan mintuna biyar bega fitowar Afnan ba.

Masu kula da ita su biyar da Mubina ne kusa da motar ga rana na dukansu, dan shi Muhseen ya daɗe da shigewa cikin school ɗin, haka ta ƙara shuɗe mintuna biyar bata fito ba, a lokacin gaba ɗaya makarantar labari ya cika cewar an samu wata sabuwar ɗaliba ƴar sarki, kafin ka ce me mutane sun zagaye gurin ana jiran ganin wacece Gimbiyar, sai a lokacin Afnan ta gama waya da me martaba, ta glass ɗin take hango mutane zube ana jiran fitowarta, wani killer smile ta saki tare da buɗe hand bang ɗinta ta ciro wani black glass ta kafa, har a lokacin Alhassan idanunsa na kan motar, ƙafa ɗaya ta sauke ƙasa tana bubbugawa, ba tare da ta fito ba, wata irin shewa da ihu mutanen da ke jiran fitowarta suka yi dan ganin tsananin kyawun ƙafarta da kuma takalman da ke ƙafar tata, mintuna uku ta baje a haka sannan ta zuro ƙafa ɗaya tana mai fitowa cikin salon ƙasaita gami da gadara, ba mutanen da ke gurin ba hatta Alhassan sai da ya tsorata da ganin kyawun da tayi, gaba ɗaya makarantar babu wata macen da ke da kyau da kuma aji kamarta, cikin iya tafiya ta fara taka ƙasa, da sauri Mubina suka mara mata baya, tare da karɓar jakar hannunta, nan fa mutane suka rinƙa jayewa ana bata hanya, sai cewa suke yi ƙanwar Alhassan da Muhseen ce tun da ga mugun kamar da suke yi, ganin yanda take tafiyar ne yasa Alhassan girgiza kai yana mai ɗauke kai gefe, a ransa ya ce zamu haɗu gida ne sai kin faɗa min wanda ya baki damar zuwa da motoci fiye da goma a school.

Dirrect office ɗin shugaban makarantar ta nufa, tun daga nesa Security ya bata hanya ta shige.

Ba tare da ya bata izinin zama ba ta zauna kan wata kujera da ke kallonsa ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, shugaban makarantar da zai kai shekaru arba'in ne ya ɗago yana mai gyara zaman farin glass ɗin da ke fusarsa "Gimbiya Afnan Mulki right?" Ya tambaya yana murmushi, yamusta fuska Afnan tayi kamar dole ta ce "Yes ina fatar an gama arranging komai na karatuna ko?"

"Eh komi ya haɗu ga takaddunki har class ɗin da zaki zauna yana ciki" Miƙa mata dakaddun yayi ta karɓa tana tashi tsaye.

"Gud job" Ta faɗa a gadarance lokaci ɗaya kuma ta fice daga office ɗin, lashe baki yayi tare da sakin wata dariya, a ransa ya ƙulla abubuwa da dama a kanta.



A ranar babu wanda be san Afnan ta shigo chool ɗin ba, kowa tsoronta yake hatta ƴaƴan masu kuɗin da ke ji da dukiya tsoron tunkararta suke, ƴanmata kuwa ƙawance suke son ƙullawa da ita amma babu wacce taga fuska, ƙarfe biyar aka tashi, motocin da suka kawota kuwa suna harabar school ana jiranta.

Alhassan kam tun ƙarfe huɗu da rabi ya isa gida, kan farar kujera ya zauna zaman jiran Afnan dan ya gama ƙudurtawa sai ta faɗa masa wanda ya aiketa fita da motoci da yawa haka, rana ɗaya kawai har ta nunawa kowa ita wacece.


Tun daga nesa ta hangesa zaune gefen ƙayataccen lambun da ke gidan, haɗe fuska tayi tana mai ba su Mubina umarnin su shige daga ciki, ta jima sosai a motar kafin ta fito cike da gadara ta nufi parlourn "Keeeee...." Alhassan ya ƙwala mata kira, fuskarsa babu alamun wasa, jikinta kuwa ya fara rawa dan tsananin tsoro amma sai ta ƙara ɗauke fuska dan gudun kar ya rainata.


ƘASAR SUDAN
..................
A ɓangaren Maimun kuwa tun da aka saki Afnan zaman gidan ya daina yi mata daɗi, gashi Muby be sake zuwa ba, so biyar tana komawa gurin bokanta amma kullum magana ɗaya yake faɗa mata, wai Yarima zai zama nata ita kaɗai, shiyasa ma take jin dama-dama, yau kam ta ɗauri aniyar zuwa gidan sarautar dan ganin abin da ke faruwa, sosai ta caɓa ado kamar me shirin zuwa party, ɗaya daga cikin motocin gidan ta hau dan bata ma son Driver ya kaita.

A babban parlour ta sauka amma babu kowa dan haka ta nufi part ɗin Mommy, a can ta sami Ameera da Mommy, Maimun kuwa kamar wata munafuka ta fara matso ƙwalla, tana mai zama kusa da Ameera babu batun yin sallama ko gaisuwa "Ameera ina Brothernki? dan Allah ki kira min shi wallahi na gaji da zama ni ɗaya" Ta ƙarasa maganar cike da makirci, Mommy ce ta ce "Zo nan ƴata daina damuwa yau zai koma gida, tun da yana da iyali" Maimun na jin haka daɗi ya mamaye mata zuciya, kusa da Mommy ta koma har wani sunne kai take yi "Na gode Mommy amma shi Babyn yana ina?"

"Me martaba ya aikesa amma yanzu zai dawo, yana zuwa zaku tafi kin ji?" Ɗaga kai Maimun tayi alamun eh, sallamar Ameer ne ya katse musu zacen, ganin yanda ya shigo kamar wani zararre ne yasa Mommy faɗin "Kai lafiya? ka shigowa mutane kamar an koro ka"

"Mommy ina lafiya kuwa yau satin Gimbiya ɗaya a ƙasar Chad, wallahi hankali ya tashi kuma da auren Brother a kanta" Ameer ya faɗa yana mai zama gefen bed, a zabure Maimun ta ce "Aure kuma? bayan ya saketa"

Kamar Ameer zai shaƙe Maimun ya ce "Sannu Aunty ya gida"

"Kaima sannu ka amsa min tambaya ta" Ta faɗa a zafafe, shima a faɗacen ya ce "Aure dai da kika sani, yau sati ɗaya da Brother ya maida Gimbiya ɗakinta, kinga maƙiya sai dai su mutu, dan aurensu haɗin Allah ne"

Mommy ce ta daka ma Ameer tsawa "Tashi ka fita tun kafin na ɓata maka rai shashashan yaro kawai, wanda be san arziƙi ba" Miƙewa yayi yana hararen Maimun tare da ficewa daga ɗakin, "Mommy dan Allah ki ce ƙarya yake yi, ba zan iya zama da Gimbiya ba" A ruɗe Maimun ke jijjiga Mommy tana magana kamar ba sirukarta ba, Ameera da tun ɗazu bata ce komi ba ne ta ce "Aunty ni kaina na tsani shegiyar Gimbiyar nan, duk laifin Alhaji Babba ne shine yasa Brother zuwa har ƙasar Sengel wai ya dawo da matarsa, kuma ya je amma ta ce baza ta dawo ba, ashe ta wuce ƙasar Chad ma" Kamar Maimun zata yi ihu ta ce "Shikenan na shiga uku ni Maimun yanzu sai da aka haɗa wannan auren"

"Ihun me ki ke yiwa mutane haka? duk kin cika mana gida da hauka" Cewar Muby yana shigowa ɗakin, nan take tasha jinin jikinta dan ta san halinsa, yana sanye ne cikin wani ɗanyen yadi me laushi maroon colour ya masifar kyau musamman da ya ɗora hula dark maroon, gashin kansa ya sha gyara fuskarsa sai wani haske take amma ya ɗan rame, ƙamshin turarensa me ɗan karen daɗi ya gama baje ɗakin, "Yawwa Yarima kamar ka san kai nake jira, zo ka zauna a nan" Mommy ta faɗa fuskarta babu alamun wasa, ganin haka ne yasa shima zama cike da biyayya, Maimun kam ganin yanda ya ƙara kyau ne yasa jarabarta ta taso, har wani matse ƙafa take yi.


"Ina sauraronki Mommy Allah yasa ba ƙarata aka kawo ba" Ya faɗa yana gallawa Maimun harara, "A a ba ƙararka aka kawo ba amma magana zan yi maka, ka san cewa dai kana da aure kuma haƙƙine a gareka ka kula da matarka, duk tsawon lokacin da ka ɗauka ashe Maimun na gidanka, nayi tsammin tana gidan iyayenta sai yanzu da take sanar da ni, dan haka ka tashi ka koma gidanka bana son jin wata magana" Cikin ladabi ya ce "Ina neman afwa in Allah ya yarda za'a kiyaye"

Cewar Muby kansa na ƙasa.

Daɗi ne ya kama Maimun har ta kasa ɓoye farincikinta, "Kafin ku wuce sai ka sanarwa Abbanku da Alhaji" Mommy ta faɗa.


Noke-noke ya fara alamun akwai magana a bakinsa, lura da hakan yasa Mommy ta ce "Idan kana da magana kayi idan kuma baka da sai ku tashi ku tafi"

Lumshe kyawawan idanunsa yayi a hankali ya ce "Dama maganar Fadila ne ina son naje ƙasarsu dan Allah Mommy kar ki ce a'a"

Wani ƙololon baƙin ciki ne ya dirarwa Maimun, wannan ai cin fuska ne a gabana yake maganar wata.

Jin abin da Mommy ta ce ne yasa Maimun saurin kallonta fuskarta cike da kishi, "Zan yi magana da Me martaba na san zai barka ka tafi" Godiya Muby yayi sosai kafin suka fice daga part ɗin, ba wani jimawa suka yi ba dan daga Alhaji har Me martaba fushi suke da shi, a harabar gidan ya samu Ashwan yana ƙoƙarin zuwa part ɗinsa, "Ina zuwa haka malam?" Muby ya faɗa yana nunawa Maimun motar da zata shiga, ba musu ta shige cikin iyayi.

Sun jima sosai da Ashwan suna tattauna, daga ƙarshe ya faɗa masa shifa son Husna yake yi, gara ya fito tun wuri kafin wani ya riga shi, dogon tsaki Muby ya ja gami da faɗin "Kai ka rasa wadda ka ke so sai ƙaramar yarinya salon ka ja mana raini, kana ganin yanda Yayarta take balle ita ƙanwar"

"Koma dai menene so be san hakan ba, kuma ni na gani ina son kayana, idan zaka mun hanya kayi idan baza ka yi ba ka mana fatan Alkhairi amma ba ƙushe abin da Allah ya halatta ba" Ashwan ya faɗa cike da yaƙini.

"Ai sai kayi fa, wallahi babu wani hanya da zan yi maka, ni kaga tafiya ta" Cewar Muby yana shiga ɗaya daga cikin jerin motocin da ke gurin, Maimun da ke jiran shigowarsa ne ta ɓata fuska ganin ya shige wata motar.

Motocine guda talatin suka ratsa unguwar tare da nufar gidan Yarima Muby, tun da suka shiga gidan take binsa a baya tana kiran sunansa, amma yayi mata banza ɗakinsa ya haura tare da danna key, a masifance ta ƙaraso bakin ƙofar tana bubbugawa "Baby ka buɗe ƙofar nan dan Allah, wannan rashin adalci ne yau auremmu kusan sati uku ba wani alamar zaka sauke haƙƙin da ke kanka, ka buɗe ƙofar nan idan har ba fushin mahalicci kake son fuskanta ba" Tun lokacin da Maimun ta fara masifa yake jinta, ya ma kasa tashi daga kwancen da yake balle ya samu damar buɗe mata, tunaninsa ɗaya Fadila ya kasa cireta a rai, ga wannan Afnan ɗin ta bar ƙasarsu balle ya koma roƙonta a kan ta dawo ko zai auri burin rayuwarsa.

A haka Maimun ta gaji tare ba komawa nata ɗakin, ita kam yau ta ƙudurta koma me zai faru sai ya bata haƙƙinta, tana shiga ta ɗauko wani gari na kayan mata ta zuba cikin ruwa har da girgizawa kafin ta kurɓeshi tasss, musamman ta aika maganin a kawo mata shi daga Abuja, ba ƙaramin tada tsimi maganin ke yi ba, shiyasa ma tana shan shi ta kwanta dan kar ya taso mata sosai.

Tun da ya tafi sallar isha be dawo gidan ba sai goma na dare, gaba ɗaya parlourn a hargitse kamar ba mace ba, sanye yake cikin jallabiya fara me taushi hannunsa ɗauke da cazbaha, kansa ya sha gyara sai sheƙi yake, tun daga ƙasa ya fara kiran sunanta amma shuru, a fusace ya nufi part ɗin da aka kai Afnan lokacin da take gidan, a parlour ya sami ɗaya daga cikin masu aikin ta fito kitchen "Ke...." Ya dakatar da ita, a sukwane ta ja burke tare da rusunawa cike da girmamawa ta gaishe shi, shuru yayi na minti ɗaya kafin ya ce "Meyesa baku gyara part ɗin Maimun ba?"

"Allah ya baka nasara ita ce ta ce kar wanda ya sake zuwa part ɗinta, abinci ma mutum ɗaya ce ke yi mata"

"Gobe da safe ku shirya Driver ya maida ku masarauta"

"Insha Allah Yarima" Ta faɗa kanta a ƙasa.

Ficewa yayi daga part ɗin yana mai janyo ƙofa.

A parlourn ya sami Maimun wannan karon.

Sanye take cikin wata ƴar iskar riga da kaɗan ta wuce mazaunanta, babu abin da be nuna ba a jikinta, sai uban ƙamshin da ke tashi a jikinta amma babu gyaran gida.

Kallo ɗaya yayi mata ya haura masa.

Bayansa ta bi tana kiran sunansa "Baby wai meye haka ne? duk ajinnan nawa da ɗaukar kai na sauke ina nuna maka soyayya amma baka gani, please ka dakata ka bani haƙƙina wallahi a matse nake idan ba mutuwa ka ke son nayi ba" Yana jinta amma ya shige ɗaki da sauri ta rufa masa baya, ganin haka yasa shi juyowa da mamaki "Lafiya ki ke bina a baya?"

Ɗan marairaice fuska tayi kamar wata tsohuwar mayya ta daƙale ido "Kai nake ra'ayi please Baby ka daina mun haka mana" Da ƙarfin tsiya ya janyowa ta faɗo jikinsa, tun kafin ya yi wani abun ta haɗe bakinsu guri ɗaya, sai wani shafa masa jiki take yi har ta sauka gefen fuskarsa, janyeta yayi a jikinsa cike da takaici ya ce "Ina son na baki haƙƙinki amma hakan baya mun daɗi, meyesa ki ke zaƙewa ne haka? nifa a tsarina ina son cikakkar mace me aji da kamun kai amma ke ko ɗaya baki da" Ya faɗa yana mai matsawa gefen hasken ɗakin ya kashe, kan bed ya kwanta tare da kashe bed side lamp, kamar wata mayya haka ta rarrafa kan jikinsa, shuru yayi mata tana duk abin da taga dama, sosai hankalinsa ya tashi har jikinsa ya fara rawa, jin yanda ta ɗora hannunsa kan mazaunanta, Muby ko be san lokacin da ya chakumota ba, harhaɗata ya fara gami da murzata son ransa, gaba ɗaya ya rasa natsuwarsa, ya jima sosai yana yalyalata, kafin ya yi watsi da kayan jikinsu, amma ya sha mamakin yanda wasa da jikin Maimun be wani yi masa daɗi kamar yanda ya yi da Afnan ba, wata irin ƙara me firgitarwa Maimun ta saki tare da saka dukkan ƙarfinta tana turesa, jin wani irin mugun zafi ya shigeta amma ina Muby be ma san tana yi ba, kuka ta fara iya ƙarfinta har tana buge hannunta kan bed, so uku tana sumewa amma ya kasa saurara mata, dama can ba ƙaramar wahala yake da lalurarsa ba, tun abun sha ɗaya saura har ƙarfe biyar na asuba kafin ya samu natsuwa, a lokacin Maimun ta suma kusan so shida, a kasalance ya matsa gefen bed yana mai sauke nannauyan numfashi, kusan mintuna ashirin yana kwance a lokacin an fara kiraye kirayen sallah, numfashin da yaji an sauke a bayansa ne yasa shi ɗago kansa, sai yanzu yaga halin da Maimun ke ciki, saurin kunna haske yayi.

Jallabiyarsa da ke gefe ya zura da sauri ya tallafota ganin idanunta sun wani luhu-luhu, gaba ɗaya fuskarta ta sauya kamar ba ita ba, zanin bed ɗin kuwa ya gama ɓaci, toilet ya nufa da ita tare da haɗa ruwa me zafi, yana sakata ciki ta saki wata irin ƙara tana mai ƙara zubewa a sume, wani irin bugawa zuciyarsa yayi, hankalinsa ya gama tashi duk ya fita hayyacinsa, da sauri ya kunna pampo ya zuba mata ruwan a fuska, wata ajiyar zuciya ta sauke tana mai fashewa da kuka, muryarta ciki-ciki ta ce "Na shiga uku ni Maimun dan Allah kar ka kasheni, wayyyo na tuba ka yafe min wallahi ba zan ƙara zuwa kusa da kai ba" Haɗe fuska yayi jin abin da take faɗi "Idan kika ƙara magana sai na sake yin wani" Shuru Maimun tayi jikinta na rawa dan a halin yanzu wani irin sarawa kanta yake, cikin ruwan ya bar ta ya koma ɗakin tare da cire bedshirt ɗin ya sauya wani.

Koda ya shigo ya sameta a yanda ya barta, malama ki ƙarasa wankan ni zan tafi masallaci, a bazata ya ji ta ce "Ban iya wankan tsarki ba fa" Dafe kai Muby yayi cikin mugun jin haushinta ya ce "Wankan tsarkin ne baki iya ba?" Ɗaga masa kai tayi alamun eh.

"Zan koma parlourn ƙasa na gyara jikina, duk kin wani lalata min jiki, akwai wadda zata shigo ta taya ki" Ficewa yayi ba tare da ya ƙara kallonta ba.


Be jima da fita ba wata kuyanga ta shigo cikin waɗan da aka kawo gidan, amma ita tana da ɗan shekaru, sosai ta ƙara gasa Maimun kafin ta koya mata yanda ake wanka tsarki, babu abin da Maimun ke yi sai zagin matar wai ta kalle mata jiki.

Da ƙyar take taka ƙafa duk taku ɗaya sai ta saki ƙara, da haka har ta koma ɗakinta tana shiga ta saka masa key, tare da cire key ɗin.

Sai da rana ta fito ya shigo gidan, yau ji yake kamar an yi masa kyauta, sosai yaji daɗin jin Maimun a matsayin budurwa, wanka ya ƙara shiga kafin ya shirya cikin wani Boxer iya gwuiwa da ƴar ƙaramar T-shert ruwan toka, turare ya feshe jikinsa da shi tare da gyara gashin kansa, haka kawai ya fasa zuwa office yau.

Saurin dafe mararsa yayi da ta murɗa masa, wani irin mugun feelings ne ya taso masa kamar wanda yasha wani maganin, a sukwane ya nufi ɗakin Maimun, koda ya murɗa ya ji a rufe, a daddafe ya koma nasa ɗakin ya ɗauko wani key, cike da dauriya ya buɗe yana mai kunna kai ciki.



ƘASAR CAMEROUN
.............
Kwanan Fadila uku a kwance, kullum cikin maganar zuwa ƙasar Sudan take, a haka har ta warware, yau satin ta ɗaya da samun sauƙi.

Kuma ta tashi da niyar zuwa ƙasar, babbar fadar gidan ta nufa, tun daga nesa dogaran suka fara isarwa Me martaba da zuwan ƴar tasa.

Cike da shagwaɓa ta shige cikin fadar, Mahaifinta na ganinta ya bada umarnin kowa ya basu guri, kusa da shi ta zauna tare da ɗora kanta kan cinyarsa "Dad barka da wannan lokacin"

"Barka Shalele ya ƙarfin jikin naki? ina fatar Jakadiya ta baki abinci ko?"

"Yes Dad ta bani, yawwa dama ina son na shiga ƙasar Sudan yau" Fadila ta faɗa tana ɓata fuska, hannunta ya kama cikin so da ƙaunar ƴar tasa ya ce "Shalele ba wai bana son zuwan naki ba ne, mutuncinki nake son karewa" Itama hannun nasa ta kama tare da faɗin "Dad ka san cewa Mom bata da kishiya ko?" Ɗaga mata mai yayi alamun eh, murmushi ta kuma yi kafin ta ce "Shiyasa nake son zuwa Yarima ya saki matayensa gaba ɗaya har munafukar Maimun ɗin"

Kallonta me martaba yayi cike da damuwa ya ce "A a kar ayi haka Shalele, baki ganin cewa hakan zai janyo tashin hankali tsakanin masarautun"

"No Dad idan har ba so kake na illata kaina ba, kawai ka saka a tanadar min jirgi yanzunnan, kafin na shirya a haɗa mun masu rakiya" Ta ƙarasa maganar babu alamun wata tarbiya.

"Shikenan za'a yi abin da kike so, je ki gama shirin naki"

Mahaifin nata ya faɗa yana murmushi.

"Yawwa Dad that's why nake sonka" A hankali ta tashi tare da barin fadar.






*GIDAN MULKI*

*By*

*Asmeetar Hydar*







P. 12






ƘASAR CHAD
............................................................................
A ɓangaren Afnan kuwa ganin ya miƙe tsaye ne yasa ta tsaya jikinta na rawa, yana ƙarasowa ya kama hannunta tare da matsewa da ƙarfi, gimtse idanunta tayi jin wani zafin da ya shigeta, amma sai ta buɗe idanuwan nata a hankali ta sauke kansa, shima

Please Login or Register in order to submit comment