Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana"

Ya faɗa yana zare mayafin da ke jikinta, doguwar riga ce less me kyau pink colour, a gaban rigar akwai flowers red wanda ya sauko har ƙasa, sosai kayan suka fito da ita musamman da ya janye mayafin da ta ɗora sama, Afnan kam rufe ido ta yi tana jiran abin da zai yi mata, a hankali ta ji saukar numfashinsa kan wuyanta, wani rin yanayi ne ke shiga jikinta amma ta kasa buɗe ido balle ta san abin da yake yi, cikin hikima ya janye zip ɗin rigar sannan ya sauketa ƙasa, ɗan ƙaramin pant ne black ya yi saura dan ko bra bata saka ba, wani irin mugun numfashi Muby ya ja wanda yasa Afnan tsorata har ta buɗe idanunta, sosai kunya ta kamata ganin ya zubawa na shanunta ido har yana shiɗewa, saurin rufe idon ta kuma yi tana murmushi.


Pant ɗin ya janye yana mai shafa mararta cike da ƙwarewa, gurin da aka yi ɗinki kuwa ya bushe sai dai har yanzu da saura, tana jin ya kai hannu ta yi saurin miƙewa zaune tana waro ido duk firgici ya bayyana kan fuskarta "Bana so please ka maida mun kayana, na fasa komawa gidanka ma" Ta faɗa a shagwaɓe, laƙace mata hanci Muby ya yi yana mai saukowa kan be ɗin "Babu abin da zan yi miki, kawai zan rage zafi ne" Wata drower ya buɗe tare da ɗauko wani glass Box golding me kyau tamkar zinari, kusa da ita ya koma fuskarsa ɗauke da murmushi "Ga wannan kyauta ce daga gareni"

Da fara'a Afnan ta karɓa "Meye shi ɗin?"
"Ai sai ki buɗe za ki gani"

"No kaine zaka buɗe min" Ta faɗa a shagwaɓe, babu yanda Muby ya iya dole ya buɗe glass ɗin, agogo ne ciki me masifar kyau da tsada wanda duk son kwalliyar da Afnan ke da bata taɓa ganin irinsa ba, sai kuma Biza zuwa Dubai, cikin tsananin farinciki Afnan ta rumgume sa tana godiya "Mijina Allah ya ƙara arziƙi me amfani, amma nawa wannan agogon ya yi mun kyau fiye da tunaninka"

"Na san cewa zai yi miki kyau shiyasa ma na ɗauko shi, kuɗin ba yawa Million ɗari ne kawai"

"Wow thanks so much, kyautar meye wannan"

"Baby tambayoyin naki sun yi yawa, kin mance ranar na sha daɗina, nikam inda na san haka ki ke da tun ranar da aka ɗaura aurenmu zau ɗauko kayana"

"Uhmmm..., Allah ko?"

"Eh mana, ko yanzu ƙarawa zan yi"

"Aa ni ban warke ba fa, idan ba so ka ke na ƙarasa ba" Cewar Afnan tana dariya.

Ƙura mata ido ya yi ganin yanda dariyar ta yi mata kyau sosai, ga wani juyi da na shanunta ke yi idan tana motsa jikinta, ganin ya zuba mata ido ne yasa ta fara ƙoƙarin mayar da kayanta, shigewa jikinta Muby ya yi tare da shafa bayanta cike da sha'awa ya ce "Bayan na ce miki a matse nake, ki bari na more ko kaɗan ne ba zan yi komi ba, kawai daɗi zamu ji tare"

"Amma ba za ka mun wani abun ba ko?"

"Eh ba zan yi ba"

Sarrafata ya shiga yi tamkar ya samu kayan wasa, ba ƙaramin rikita Afnan ya yi da salonsa ba, wannan karon ita ce me sambatun ma dan har janyosa take wai ya shiga daga ciki, shi ko tausayinta ne ma ya kamasa dan ya san idan har ya shige tabbas ɗinkin zai ƙara lalacewa, cikin ƙwarewa ya gamsar da su gaba ɗaya, Afnan kam ƙanƙame shi ta yi tana sauke numfashi kamar zata shige jikin nasa, ga wani sanyi da daɗin da ke bi duk wani sashe na jikinsu, sai a yau Muby ya ƙara tabbatar da cewa ya yi wasa a baya, dan komi na jikin Afnan daɗi ne da shi.

Sai da suka yi wanka kafin suka koma kan bed, Muby ne ya kalleta sai kuma ya bushe da dariya har yana riƙe ciki, ɗan ɓata fuska Afnan ta yi "Meye kuma haka?"

Tawul ɗin da ke jikinta ya kama kamar zai cire, Afnan ta wani ƙara matsowa dan ita haƙiƙanin gaskiya tana buƙatar ya ƙara yi, "Kin gani ko Babe gaskiya kin fini jaraba, ɗazu sai wani shige mun ki ke har da ƙara janyoni fa"

"Eh ɗin na janyoka ba kai ne sai wani rikitamun lissafi ka rinƙa yi ba, nifa ɗazu na yi tsammanin a sararin samaniya muke, gaskiya romance duniya ne, amma wancan abin da ka mun ranar wallahi babu daɗi sai azaba"

"Waya faɗa miki babu daɗi? ai shine sarkin daɗi kawai dan farkon yi ne, amma daga kin saba za ki zama ƙwararriya har ma ki rinƙa bibiyata"

Ƴar dariya Afnan ta yi tana ƙara shigewa jikinsa "Nikam ban ji wani daɗin ba, kawai wannan ma is okay"

"Tom na ƙara yi miki irin wannan ne?"

Cikin alamun kunya ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana ɗaga kai sama alamun eh.

Dama abin da Muby ke so kenan, ai kuwa ya cigaba daga inda ya tsaya, sosai suka ƙara gamsuwa kafin bacci me daɗi ya ɗauke su rumgume da juna, kana kallon fuskokinsu ka san cewa ba ƙaramar soyayya ce kwance ba, sai ma kaga yanda wani killer smile ke fita daga fuskar ta su.


Washe garin ranar tun sha biyu na rana Mubya ya hana kowa shan iska a gidan kan cewa zai tafi da matarsa, haka ko aka yi duk kayan lefenta su Ameer ne suka tafi da shi akwati hamsin ne daidai waɗan da ke cike da kaya masu mugun tsada, haɗuwar kayan kuma ba'a magana.

Motoci ɗari ne ke take musu baya wannan karon har da su Me martaba gurin kai amarya, ta haɗe cikin wata bugaggar doguwar riga wadda zata kai kimanin dubu ɗari bakwai, riga ce wadda kana gani ka san sai cikakkun ƴaƴan sarauta ke iya sakawa, a saman rigar ta ɗora alkyabba har tana jan ƙasa, fuskarta na ɗauke da simple makeup me jan hankali, Muby na gefenta cikin tasa shigar da haɗaɗɗun wando da riga na sarauta kalar kayan jikin Afnan, shima ya ɗora alkyabba har da rawani sai murmushi ke sauka kan fuskarsa tamkar sabon ango, tun daga farkon arean zaka tabbatar cewa ba ƙaramin haɗuwa gidan zai yi ba, Afnan da ke gefen Muby ne ta ɗan matsa kaɗan yanda zai ji ta ce "Mijina wannan unguwar ta yi mun kyau, amma akwai nisa da gidansu Mommy fa" Shima rage muryar ya yi tare da faɗin "Eh hakane saboda bana son idan ina shan daɗina su rinƙa jin kukanki"

Tsoro da fargaba ne suka bayyana kan fuskar Afnan, lokaci ɗaya ruwan hawaye ya ciko mata ido dan baza ta mance da wahalar da ta sha da farko ba.

Har aka iso bakin gate ɗin bata sake cewa komi ba, gate ɗin da ke gidan guda uku ne masu rikitaccen kyau tamkar ba a duniya ba, gaba ɗaya ƙofar gidan electric ne, ga flowers haɗaɗɗu green colour, Afnan kam ta kasa magana dan tsarin ba ƙaramin tafiya da ita ya yi ba, gates ɗin guda uku ne suka ɗage sama, cikin ƙanƙanin lokaci motoci ɗari suka kunna kai daga ciki, duk inda ka duba electric ne da CC Camera, faɗin yanda gidan ya haɗu kuwa babban aiki ne, hawa biyar ne wanda kowanne hawa ɗaya na ɗauke da masu kula da shi, duk inda ka duba flowers ne da bugaggun motoci masu masifar tsada, ginar gidan kuwa tambarin sarauta ne ta kowanne gefen, kai hatta gidansu Afnan be kai kyau da haɗuwar da wannan ya yi ba.

Akwai gurin wasar dokuna me kyau da girma, lokacin da suka shiga parlor kowa da ke gurin kasa magana ya yi, dan babu wanda ya san Muby ya haɗa waɗannan kayayyakin, ba ƙaramin haɗuwa parlourn ya yi ba musamman ƙofar shiga daga ciki.

Kuyangin da ke shige da fice ne suka baje musu kayan motsa baki, sun jima suna fira wanda Afnan kam kasa magana ta yi, sai dai kallonsu har wani Dogari ya yi sallama, tare da rusunawa ya kwashi gaisuwa, bayan sun amsa ne yake shaidawa Muby cewar akwai masu nemansa a waje.

Cike da taƙama ya ce "Su waye da baza su shigo ba?"

"Allah ya ba ka nasara ƴan maula ne, tun ɗazu nake korararsu amma sun ce baza su tafi ba sai sun ganka, yau kwanansu uku suna zuwa nemanka"


Mamaki ne ya kama Muby amma sai ya ce "Ka tafi ina zuwa"

Me martaba ne ya dakatar da shi da faɗin "Ka ce su shiga daga ciki"

Cikin girmamawa Dogaren ya amsa yana mai ficewa.

Mintuna biyu tsakani wasu mutane biyu suka shigo kamar waɗan da aka fiddo daga rami, ɗayar ma sai wari take ga wasu kurajen da ya ɓata mata fuska, Dogarai goma ne ke tattare su dan kar su taɓa jikin wani, Muby ne ya ce "Daga ina bayin Allah" Bushewa da dariya ɗayar matar ta yi tana faɗin "Ni ce na yiwa Yarima magani ya tsani matarsa, ni ce na yiwa Yarima magani saboda ya auri ƴata"

Sai da ta gama dariya kafin ta kuma cewa "Gimbiya ta haukace ni ce sila, Gimbiya ta zama marar lafiya ni ce sila, yanzu haka ina neman inda zan same su ko zan kashe su da kaina, saboda natsani ganinsu a tare, be dace da Gimbiya ba, ya fi dacewa da kyakykyawar ƴata"

A fusace Alhaji ya miƙe tare da dakawa Dogaran da ke tsaye a gurin tsawa "Ku fice da wannan azzalumar makirar a gidannan"

Fadila na ganin haka ta faɗi ƙasa tare da rushewa da kuka.




*GIDAN MULKI*


*By*

*Asmeetar Hydar*








P. 27







"Dan Allah ku yafe mana, haƙiƙa mun cuceku musamman Gimbiya, ki yafe min ni da Mahaifiyata, wannan ita ce ƙaddaramu domin a halin yanzu Mahaifina ya kore mu a gidansa, duk wasu ƴan tarkacemmu ya ƙwace"

Afnan kam tausayin Fadila ne ya kama ta, a hankali ta ƙaraso gurin da niyar ɗaga ta, wuffff Muby ya riƙe mata hannu yana girgiza kai "Baza ki taɓa wannan mushirikar ba, duk kin mance da abin da suka aikata miki, har ciyon hauka suka saka miki fa, kuma ki ke tsammanin zan barki ki isa kusa da su"

"Amma......"

"Shhhhhhh....bana son jin komi, ki koma ki zauna please" Dubu ɗari ya ciro daga aljihun rigarsa ya jefa musu, da hanzari Fadila ta karɓa tana godiya, ƙeyersu aka tasa a gaba tare da fitar da su daga gidan, ɗaya daga cikin masu tsaron gidan Muby ya kira fuskarsa a haɗe "Waye ya nuna musu gidannan?"

Jikinsa na rawa ya ce "Wallahi ranka ya daɗe a can gida suka fara zuwa, sai muka kore su wannan gidan kuma bamu san wanda ya nuna musu ba, yau kwana uku kenan suna zuwa bakin gate"

"Zaka iya tafiya" Muby ya faɗa yana maida kallonsa kan Afnan da ta haɗe fuska tun lokacin da ya ce ta koma ta zauna, ita ala dole ta yi fushi.

Sai da su Alhaji Babba suka yi masu nasiha sosai me ratsa jiki, Afnan kam sai a yanzu ne take jin kamar ta koma gida, tun kafin nasihar ta yi nisa har ta fara kuka, Mommy na gefenta tana aikin rarrashi, sai misalin huɗu na yamma suka bar gidan, har inda jerin motocin da suka zo Muby ya rakasu, Afnan kuwa sama ta haura cike da ɓacin rai, dan har yanzu fushi take wai Muby ya hanata zuwa kusa da Fadila, tana shiga ƙayataccen ɗakinta ta rufe ƙofar.


Sai da ya yi sallar ƙarfe huɗu kafin ya dowa gidan, ya yi bugun duniyarnan amma Afnan ta ƙi buɗe masa ƙofa, sai ma ƙara dunƙulewar da ta yi kan bed.

A bisa dole ya koma nasa room ɗin.


Kwanansu Uku a haka amma Afnan ta hana Muby ya ganta, duk abin duniya ya ishe sa, itama haƙuri kawai take amma tana muradin ganinsa, a kullum sai ta tsantsara masa lafiyayyen abinci me masifar daɗi, be taɓa tsammanin ta iya abinci haka ba, dan kwanaki uku ya saba da girkin nata, haka zai shigo parlourn ya tarar da ƙamshin turarenta duk da cewar bata ciki, abinci kuwa iri-iri sai wanda ya zaɓa.

Yau ma kamar kullum kwana huɗu kenan da tarewarsu, a bakin ƙofar ɗakinta yake tsaye yana yi mata magana amma ta share sa sai ma cewa ta yi "Dan Allah ka tafi bana son ganinka, a gaban su Mommy ka rinƙa yi mun ihu da faɗa dan kawai zan taimaki waɗan da suka cuceni, kar fa ka mance shi ɗan adam idan ya yi maka sharri ka saka masa da Alkhairi wannan faɗin fiyayyen halitta ne, to me zai sa ka hanani? yanzu a haka zasu ƙare rayuwarsu? ɗan kuɗin da ka basu ne ka ke tsammanin zai ishe su, ka tafi kawai ka barni bana buƙatar sake ganin fuskarka"

Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, ita yanzu gidansu ma take son komawa dan wata irin kewar su Fulani ne ke damunta, ga son ganin Baffanta da ta mance ranar da ta yi magana da shi, sosai tausayinta ya kama Muby ya san cewa be kyauta ba, a rayuwa duk wanda ya jefe ka da sharri ka rama da khairan, tabbas Gimbiya tana da gaskiya, "Shikenan na yarda na yi laifi, amma ki fara buɗe ƙofar da Allah"

A fusace ta kuma cewa "Just go please i said i don't want to see your face"

"Alright tun da baza ki haƙura ba sai ki cigaba da fushin naki, ba zan sake roƙonki ba"

Muby ya faɗa yana barin gurin a harzuƙe, parlourn ya koma dan wani irin zafi zuciyarsa ke masa, kan daining ya duba amma babu ko abincin da ya saba ganin ta yi masa, dama ko ya gani ya ƙudurtawa ransa ba zai ci ba, ficewa daga gidan ya yi dan kiransu Ashwan na shigowa.

A bakin gate ya same su sai dariya suke, Ashwan ne ya ce "Ango an sha ƙamshi, wai haka ake yi? ko gayyata babu"

"Mtss! yanzu ai kun zo shikenan"

"Hakane amma sai mun ci abincin amarya kafin mu haƙura"

Cewar Yusuf yana dariya, murmushin takaici Muby ya yi be san lokacin da bakinsa ya ce "Wai fushi take da ni, dan kawai taga ina ƙaunarta" Bushewa da dariya Ashwan da Yusuf suka yi, dan yanda Muby ya yi maganar kamar wani maraya, Ashwan ne ya ce "Nikam ka fara nemo min number Husna kafin na ba ka shawarar da zaka amfana"

"Wai wacce Husna? bayan na faɗa maka baza ka janyo mana raini ba, kuma suna soyayya da Ameer, nima kwanannan na samu labari"

Cikin mutuwar jiki Ashwan ya ce "Allah sarki wallahi bansaniba kuwa, shiyasa ranar da na tambayi Ameer number ta, naga yana haɗe fuska ashe soyayya suke yi, gaskiya na haƙura amma ba ƙaramin so nake yiwa Husna ba"

"Hmmmm me zai hana ka auri Musleema itama fa ba laifi dan gaskiya yarinyar ta haɗu, tun da naga kana son haɗa alaƙa da Gimbiya" Yusuf ya faɗa yana kallon Ashwan.

Ɗan kaɗa kai Ashwan ya yi kafin ya ce "Ka san ban cika son raini ba, Allah ya sa bata da ɗagin kai, so ɗaya na taɓa ganinta ranar da suka zo da Gimbiya nan ƙasar"

Muby ne ya ce "Duk ku gama wannan shiriritar ku bani shawara wallahi ba zan iya jurewa ba, ina son Baby sosai kwana huɗunnan kamar zan yi hauka, baccin ma na saba yi a jikinta"

Matso kusa ka ji wani sirrin, cewar Ashwan yana kama hannun Muby, sai da suka gama maganganunsu wanda ba ka jin abin da suke faɗa, mota suka shige tare da barin ƙofar gidan.


Afnan kuwa sai da ta tabbatar ya fita kafin ta fito parlourn sanye cikin ƙaton hijab ɗinta, wayarta da ke ƙara ne ta ɗauka tana sakin murmushi, daga can ɓangaren Alhassan ne ya ce "Amarya an sha ƙamshi har an mance da babban Brother ko?"

"Yanzu kai Yarima Alhassan kana tsammanin ka girmeni ne? a rana ɗaya fa aka haife mu Allah ba zan raga maka ba"

Dariya Alhassan ya yi kafin ya ce "Lallai Gimbiya wuyanki ya isa yanka, ni duk ba wannan ba ki tura aiport a tarbo su Husna har da su Eaha sun iso ƙasar ta ku"

Tsalle Afnan ta daka saboda murna, "Wai dama zasu zo shine basu faɗa mun ba, amma su Fulani fa? da Hajiya kuma ya kamata Mubina ta zo dan ba laifi na yi kewarta" "Aa daga su Esha sai su Husna Fulani ta ce baza ta samu zuwa ba, Muhseen ma ya ce sai idan su Hajiya zasu zo zai biyo su" "Okay fine bari na tura a ɗauko su" Cewar Afnan tana kashe wayar, kichen ta koma a gaggauce ta ɗora tumatir sannan ta fitar da naman kazar da ke Frigde, ɗaya daga cikin masu aikin ta kira tare da bata umarnin ta kira mata Driver, ba ɓata lokaci Drivern ya shigo parlourn cikin girmamawa ya rusuna yana mai kwasar gaisu "Aa dan Allah ka miƙe tsaye daga yau bana son kuna rusunawa idan za ku gaida ni, yawwa dama ina son ku haɗa motoci goma zuwa aiport zaku tarbo min wasu baƙi"

"An gama ranki ya daɗe amma a bamu number idan muka tafi zai yi mana sauƙin gane su" Numbern Muslima ta bashi sannan ya fice daga parlourn, masu aiki mata su biyu ne aka kawo mata daga gidansu Muby, cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙara gyara gidan sai ƙamshi ke tashi, kasancewar daga airport zuwa gidan akwai jayewa ne ya sa kafin su iso har Afnan ta haɗa musu lafiyayyar shinkafa da miya wadda ta sha spyciss, ba ƙaramin daɗi abincin ya yi ba, naman kaza ta tafasa bayan ya dahu ta soya tare da flower, a gefe ɗaya ta baza perpesun naman rago, da haɗaɗɗen dambun nama wanda ya tashi gaba ɗaya gidan, daga bakin parlourn kana jin ƙamshin girkin nata, Afnan macece wadda ta yi masifar iya girki dan Fulani bata sakar musu jiki kan abinci ba, duk wani girkin zamani sai da ta koya musu, Halima kuwa a gurinta take zuwa koyon girki dan Fulani bata banbanta ƴaƴanta da ƴaƴan Mama ba, amma su Bilkisu kam basa zuwa part ɗin balle su koya, shi kansa Muby be taɓa tsammanin Afnan zata iya girki haka ba.

Fruits ta yanyanka tare da zuba madara da kuma Flavor sai kayan ƙamshi, ta saka a Fridge, perpesunta da ke kan Gas ne ta ƙara dubawa sannan ta haura sama dan ta yi wanka kafin ya ƙara dahuwa.

Sai da ta ƙara gyara ɗakinta me ɗauke da bed uku ba ƙaramin girma ɗakin yake da ba, musamman Wadrop ɗinta da zai kai rabin bangon ɗakin, cikin ƙaramin lokaci ɗakin ya ɗauki ƙamshi, har ta ɗora tawul ta tuna cewar ɗakin Muby ba mai gyara masa, da sauri ta zura hijab tana mai nufar room ɗin.

Babu abin da zaka nema na rayuwar duniya da baza ka samu a ciki ba, shima bed uku ne royal me tsinannen kyau irin na ƴaƴan sarauta, ba wani lalacewa ɗakin ya yi ba dan Muby akwai tsafta sosai, minti biyar ya ɗauketa gurin gyara komi na ɗakin, ƙamshi kawai ke barazana a ɗakin, toilet ma ta gama tsaftace shi tasss ta yi mopping ko'ina, Ac ta kunna kafin ta fito daga room ɗin, a gaggauce ta koma kichen dan duba perpesun da ta bari kan wuta, lokacin da ta fara jiyo motocinsu Husna na shigowa harabar gidan, da sauri ta kira ɗaya daga cikin masu aikin, cikin girmamawa ta ce "Allah ya ba ki nasara gani"

"Yawwa abincinnan nake son ki haɗa mun, ina buƙatar ganin komi ya yi need and before na fito wanka ki haura da komi parlourn da ke hawa na uku, sannan ki yiwa baƙina jagora zuwa sama"

Cikin biyayya ta amsa da "Insha Allah"

Komawa ɗaki Afnan ta yi dan ta samu yin wanka, duk jikinta ya fara ciyo dan ba wani son takura jikin nata take yi ba.


Ba ɓata lokaci ta haɗa komi yanda aka umarceta, su Easha kuwa tun daga Compound suke kallon tsarin gidan, ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, har suka shigo tsararren parlourn suna magana kan gidan, me aikin ce ta yi musu jagora har zuwa parlorurn sama, Muslima kam kasa haƙuri ta yi tana faɗin "Wai ina ɗakin Gimbiya ne?"

Me aikin ce ta ce "Mu tafi na nuna miki, amma ta shiga wanka ne"

"Aa ki barta kawai, zamu jira har ta gama"

Kayan sanyi na alfarma aka zube musu na kece raini, snacks kuwa aready akwai shi a gidan.

Wayar Husna ce ta yi ƙara da sauri ta ɗaga ganin sunan Ameera, "Aunty Ameera kun iso ne?"

Daga can ɓangaren Ameera ta ce "Muna parlorun ƙasa amma babu kowa, kuna ina ne?"

"Muna Upstairs na uku bari na sauko sai na taho da ku"

Ameera na dariya ta ce "No ai ɗazu mun zo gidan bari mu ƙaraso, ko dai kina son ganin Ameer ne"

Kunya ce ta hana Husna magana dan su Easha na kallonta, Ameera kuwa ta kashe wayar tana mai cewa Ameer "A sai mu haura suna daga sama" Cikin hanzari Ameer ya miƙe kamar zai tashi sama dan murna, ya sha wankan manyan kaya irin na ƴaƴan sarauta, sai ƙamshi ke tashi, Ameer ma ba ƙaramin kyakyawa ba ne dan zaka iya saka shi na biyu a gefen kyawawa.

Tun da suka shiga parlourn Husna ta kasa zama sai kallon juna suke har Afnan ta shigo sanye cikin wata bugaggar less navy blue me kyau da laushi, riga da skit ne ya karɓi jikinta sosai, hips ɗinta kuwa sai motsawa suka kamar ita ke juya su, ta saƙala mayafinta blue a wuya me ɗan girma, fuskarta ɗauke da simple makup wanda ya karɓi kayan jikinta, agogon da Muby ya siya mata ne ta saka tun daga nesa ƙellinsa ke haska parlourn, cikin farinciki Husna ta tashi suka rumgume juna, kamar zata ɓalla mata baya, kawai jin suka yi an ce "Kai so ki ke ki ɓalla min bayan mata"

Kowa da ke ɗakin kallon su Muby suka yi tsaye a bakin ƙofa, haɗe fuska Afnan ta yi tana faɗin "Yaya Ashwan ku shigo daga ciki mana" Ƙarasowa daga ciki suka yi tare da zama, bayan sun gama gaisawa ne Afnan ta kira me aiki ta baje musu abincin da ya tashi kan gaba ɗaya ƴan parlourn, daining table ɗin me zaman mutun ashirin ne dan haka anan suka sauke gajiya, Muby ya wani ƙurawa Afnan ido kamar zai haɗiyeta, duk wanda ya kai spoon ɗaya a baki sai ya jinjina kai saboda daɗin da abincin ya yi, Ameer kam sai ɓata fuska yake ganin Ashwan a gurin dan ya yi tsammanin zai iya kiran Husna a gefe ya faɗa mata sirrin zuciyarsa, abin da be saniba shine tun da suka shigo Ashwan ya ƙurawa Muslima ido kamar ya samu Tv, sai yanzu yake ganin tsantsar kyawun da Allah ya yi mata, a ɓangaren Muslima kuwa ta lura da kallon da yake yi mata, tana ganin ya ɗago take sakar masa murmushi dan itama ta kamu tun daga shigowarsa, suna gama cin abincin suka koma kan kujera aka ɗora fira daga inda aka tsaya, Ameer kam parlourn ƙasa ya koma shi da Husna, Yusuf ya ja Ameera harabar gida, ya rage daga Ashwan sai Easha da Muslima, Afnan da Muby kuwa im banda kallon kallon ba abinda suke yi, miƙewa tsaye ta yi tare da kallon Eaha ta ce "Zo mu barwa su Yaya Ashwan guri dan na lura da kallon da masoyan ke yiwa juna" Ɗauke kai Muby ya yi daga barin kallonta, har suka bar parlourn, kan daining ya koma yana mai latsa wayarsa.

Ba ƙaramin zafi Afnan ta ji ba ganin Muby ya nuna halin ko in kula gare ta, amma sai ta share tana faɗaɗa murmushinta dan kar Easha ta fahimta.

Ɗaya daga cikin ɗakin da ke

Please Login or Register in order to submit comment