Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su haɗe yawu dan sun san tafi ƙarfinsu, ganin sunan gurin shopping ɗin ne yasa ta zare ido da ƙarfi ta furta, "PRINCE MUBY SHOP....."

A fusace ta maida kallonta kan drivern da ya kawo su ta ce "What the heck? da umarnin wa ka kawoni wannan gurin?"

Jikinsa na rawa ya faɗi ƙasa kan gwuiwoyinsa yana neman tuba, ko kallonsa bata yi ba ta shige motar tana faɗin "A canza min gurin shopping in the nex three munites"

Tun kafin ta gama magana driver ya juya kan mota tare da nufar cikin gari, wani gurin aka kaisu shima ba laifi sai ƴaƴan manya ke zuwa amma ko kaɗan be kama ƙafar kyawun na Prince Muby ba.


Dogarai goma ne su ka shige kai tsaye tare da busa sarewa, ai kuwa mutane su ka fara fita kamar ana korosu, ƙa'idar Afnan kenan duk zata yi shopping to tabbas sai kowa ya fita idan ba haka ba mutum ya karɓi hukunci.

Sai da kowa ya gama fita kafin su ka shimfiɗa carpet red me laushi da tsantsi, dogarai kuwa su ka jera ana watsa mata flower's me tsananin kyawu, Husna kuwa na bayanta har su ka shiga daga ciki.

Ta daɗe a ciki tana sayen kaya, can ta fara jiyo hayaniya daga waje ana ƙoƙarin hana wata budurwa shiga amma ta ce dole sai ta shiga ba bu wada ya isa ya hanata, kallon wulaƙanci Afnan ta watsawa matashiyar, sannan ta yima dogaran alamu da su kwaso kayan da ta saya, cikin tafiyar gadara ta iso gaban budurwar wadda zata kai kimanin shekaru ashirin da biyar, a kasalance Afnan ta ce "What did you just said? idan har ba kunnuwa ƙarya su ke min ba naji kamar kina faɗin dole sai kin shiga daga ciki, bayan kuma kinsan cewa the Princess and the Queen of Beauties na ciki tana shopping, waye ubanki a garinnan?" Afnan ta ƙarasa maganar cikin tsawa, duk da cewar matashiyar ta tsorata amma hakan be saka ta karaya ba, "Ni ba ƴar kowa ba ce amma inada daraja da kuma kima...."

"Just be quiet, don't say another word here, if not i'll make you regret it"

Afnan ta ƙatseta rai ɓace, yawu ta tattara ta tofa mata tare da tunkuɗata gefe, tana mai barin gurin, nan take masu tsaronta su ka rufa mata baya aka bar budurwar nan tsaye tana share yawun da aka tofa mata, kafin ka ce me motocin sun shallewa ganinta.



Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana gaba ɗayansu su ka fito cikin shirinsu na zuwa ɗaurin aure.


Me martaba, Afnan, Fulani, Halima da kuma Husna, sai dogarai da ke take musu baya, kowannensu cikin kayan sarauta musamman Afnan gaba ɗaya jikinta kayan sarauta ne, hatta takalman da ke ƙafarfa, a cikinsu ba bu wanda ya saka kayan ƙasa da dubu ɗari biyar, Afnan kuwa abaya ce ta larabawa me tambarin sarauta a gaban rigar sai alƙibba ruwan toka, kamar yanda dukkaninsu da alƙibba a jikinsu, me martaba ne aka buɗewa wata firgitattiyar mota ƙirar Camaro, mai masifar kyau ɗauke da tambarin sunan SARKI SHURAIHU, a tare su ka shiga motar da Husna, sai Fulani da Halima mota ɗaya su ka shiga ƙirar Ferrari wadda kana gani ka san kuɗi sun yi kuka, motar nada tambarin FULANI GIDAN MULKI, mota biyu kuwa kunyanginsu mata ne su ka shiga.



Afnan da ke gefe tana jiran su gama shiga ta maida kallonta kan driver alamun ya rufe motar da ya buɗe mata, a gadarance ta ce "Ka maida tambarin sunana a ɗayar motar can ita nake son shiga" Ta nuna wata santaleliyar mota mai matuƙar kyau ƙirar Bughatti divo, wadda har tafi ta me martaba kyau da ɗaukar ido, nan take drivern ya cika umarni. Ahankali motocin su ke ratsa unguwa-unguwa, duk unguwar da su ka gifta sai kaga kowa na shigewa gida, idan ma a hanya ne matsawa mutane su ke a gefe, har su ka isa katafaren gidan wanda ya gaji da haɗuwa, tun daga waje aka canza salon busa algaitar alamun Sarkin sarakai ya ƙaraso, gaba ɗaya mutane sun cika ƙofar gidan tun daga layin unguwar har bakin gate ɗin, motocin Sarki Shuraihu guda ɗari biyu ne su ka shige daga cikin gidan sarautar, Sarki Ahmad ne ya fito tare da muƙarrabansa cikin taƙama har inda baƙin nasa su ke, da fara'a suke gaisawa da kuma sakin fuska amma fa kowa da abun da yake tunani a zuciyarsa, har babban parlourn gidan aka sauke su tare da baje musu kayan motsa baki, abinci kuwa kala-kala har da na ƙasashen waje, ba bu abin da zaka nema a cikin abincin da aka kawo musu ka rasa, amma ko kallon arziƙi be samu ba.


Afnan kuwa har ila yau tana zaune cikin mota ba bu alamar zata fito, ta kai mintuna ashirin a ciki tana latsa wayarta kafin ta sako kafarta ɗaya waje tana kaɗawa, tun daga nesa ya hangi mutum cikin mota amma baya iya ganin fuskar waye, ya daɗe a haka yana son ganin wanda ze fito amma har ya baje mintuna goma a haka, sanye yake cikin wando da riga masu masifar kyau, ya aza alƙibbar maza a sama, kalar ruwan ganye, hular kansa ma kala ɗaya da alƙibbar, takalman ƙafarsa black sawu ciki, amma daga bayan takalman a buɗe, komai na jikinsa akwai tambarin sarauta, gashin kansa ya sauko har bayan wuyansa baƙi siɗiƙ kamar na larabawa ne ya ƙara ma shigar tasa kyau, dogo ne me ƙirar majiya ƙarfi, yanada lue-lue eyes ɗauke da gashi luffff, hancinsa har yana ƙoƙarin tsere bakinsa, gashin girarsa kuwa gamewa ta yi gaba ɗaya, sai dai yana gyarawa akai-akai, ɗan ƙaramin bakinsa kuwa ɗauke yake da pink lips ba bu wani surki da wata kala, fari ne sosai kuma irin farin da ba bu ja a ciki, yana da wushirya tsakinin haƙoransa masu haske, amma ba sosai ka ke ganin wushiryar ba, sai idan ya yi dariya ko kuma yana faɗa to a lokacin ne zaka ga ta fito da kyau, yana da ƙwarjini da ke sa kowa a gidan tsoron sa, baya dariya ko kaɗan idan kaga dariyarsa to tabbata da Mahaifiyarsa ce, Prince Mubarak kenan matashi ɗan shekaru talatin, me ji da mulki da kuma taƙama, baya son raini kuma baya buƙatar a shiga rayuwarsa shiyasa a kullum yake keɓance kansa, idan kaga yana magana to Friends ɗinsa ne su ka zo, Ashwan da Yusuf, suma ƴaƴan masu kuɗin garinne ana ji da su a garin, kuma ana damawa da su, ba bu inda Prince Muby zai shiga a garin Sudan ba tare da mace ta nemi soyayyarsa ba, mata har faɗa su ke a kansa, amma shi ko in kula dan be ma san suna yi ba.





A masifance ya nufi gurin motar da niyar ganin wanne ɗan rainin hakali ne haka tun ɗazu a cikin mota, kasa matsar da ƙafarsa ya yi ganin Afnan ta fito cikin tafiyarta me jan hankali, nan take surar jikinta ta faɗo masa a rai, sarai ta gansa amma sai ta yi kamar bata san yana gurin ba, ƙamshin turarensu ne ya haɗe guri ɗaya tare da bada wani ƙamshi mai daɗin shaƙa.


Ta gabansa ta wuce kuyanginta na tattara mata alƙibbarta, har ƙasa su ka rusuna suna gaishe shi, amma ko kallon banza basu samu ba, kamar daga sama ta tsinkayo muryasa yana faɗin "Shi mulki iyawa ne, wani ko ya gwada ba ze yi masa kyau ba, da za ki sauke ji da kai da taƙama ki gaisheni ina ganin hakan zai fiye miki"

Yamutsa lips ɗinta ta yi kamar zata tanka masa sai kuma ta cigaba da tafiya kamar bada ita yake ba, da ƙarfi tsiya ya kaiwa iska naushi yana lumshe kyawawan idanunsa, dan ya tsani shariya a rayuwarsa, "Har ni zata nunawa mulki? ai tun da ta shigo gidannan yau sai na koya mata hankali" Ya faɗa yana bin bayanta.


A babban parlourn ya same su a zaune, can gafe ya hangeta zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, kallon su Sarki Shuraihu ya yi a ɗan girmame ya ce "Allah ya ja zaminka sannunku da zuwa, ya hanya?" Fulani ce kawai ta amsa cikin fara'a amma Sarki Shuraihu kuwa sai da ya ɗan karkarta kai gefe cike da izza ya ce "Alhamdulillah, ya muka sameku?" Sosai ran Muby ya ɓace ganin kallon ƙasƙancin da aka yi masa amma saboda yana da wani ƙudiri a ransa sai ya ɗan saki fuska da faɗin "Lafiya ƙalau"

Tashi ya yi daga rusunawar da ya yi yana kallon Fulani dan ya san ita ce kaɗai zata sa Afnan ta yi abin da yake so, "Mami dama yunwa nake ji, please a bawa Gimbiya abinci ta kawo min part ɗina" Kallon rainin hankali da kuma tambaya Afnan ta yi masa, jin abin da ya ce, har ta buɗe baki da niyar magana sai taji Fulani na faɗin "To ba damuwa zata kawo maka yanzunnan"

"What! zan kai masa abinci? amma idan har mutanen da ke cikin parlourn nan sun saurari sunan da ya kirani da shi ai sun san cewa nafi ƙarfin na kai masa abinci"

Kallonta ta mayar gefen da Muby ke tsaye tana faɗin "Gimbiya....., shine sunan da ka kirani amma ka ke tsammanin zan kai maka abinci, ina kunyangar ka take? me kula da ɓangaren abincinka, kaga nayi kama da wadda zata ɗauki abinci a hannunta?".

Ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da jujjuya jikinta, ganin tana neman raina masa hankali ne yasa ya daka matsa tsawa ransa ya masifar ɓace ko ba bu komi, iyayensu na parlourn, cikin masifa ya ce "Umarni nake baki ba shawara ba idan har kina tsammin ban kai matsayin ba to karki kawo, ni kuma sai na nuna miki nawa matsayin tun da a cikin masarautata ki ke ba taki masarautar ba, bayan haka ke matata ce dole za ki bi umarni na"

"Really.......?" Ta faɗa tana tafa hannu, alƙibbar jikinta ta gyarawa zama kafin ta motsa lips ɗinta a hankali ta ce "Zamu gani kuwa idan kaine ko kuma ni ce" Ta ƙarashe maganar tana zama kan kujerar da ta tashi.


Jin abin da ta ce ne yasa shi ficewa a fusace kamar namijin za ki.

"Ai sai ki tashi ki kai masa abincin ko"
Fulani ta faɗa ba bu alamar wasa a fuskar ta, baki Afnan ta buɗe da niyar magana amma sai Fulani ta kawar da kai alamun bata son jin komi.

Dan dole ta miƙe tare da kallon wata kuyangar da ke gefe a tsaye a hankali ta ce "Ina abincin nasa yake?"


Cike da girmamawa kuyangar ta ɗauko wani basket me zube da kayan abinci iri-iri, ta miƙa mata, "Ni sa'arki ce da za ki bawa abinci? dallah Malama ki riƙe har mu isa part ɗin nasa"

"A a Gimbiya ki karɓi abincinnan bana son dogon zance" Fulani ta faɗa cikin gajiya da magana, ba dan tana so ba haka ta karɓi abincin ta fice cike da taƙama.


Sarki Ahmad ne ya kalli Fulani cikin sakin fuska ya ce "Ina ganin cikin ƙa'idar auren nasu ba bu dole a ciki, ai da kin barta tun da ta nuna baza ta tafi ba"

Murmushi Fulani ta yi kafin ta ce "Ai wannan ya zama dole tun da da aurensa a kanta, dan haka dole ta bi umarninsa"

"Tana jin maganarku ne dama?" Sarki Ahmad ya tambaya yana gutsura tufar da ke hanunsa, da mamaki Sarki Shuraihu ya ce "Me ka ke nufi da tana jin maganarmu?"

Fulani ce ta yi saurin ƙarɓe zancen da faɗin "Kana kallo fa mijinta ya aiketa amma ta nuna baza ta tafi ba, shi yake nufi ba komi ba"

"Meyesa ki ke son kareni? bayan na faɗi abin da ke raina, Gimbiya bata jin maganarku musamman kai da ka ke mahaifinta, idan ba haka ba yau wata ɗaya da aurensu amma kun kasa kawo mana amarya, wannan dalilin kawai ya isa na ce ita ce ke baku umarni"


Sarki Ahmad ya ƙarashe zancen yana murmushi, sosai maganar ta ɓatawa Sarki Shuraihu rai amma sai ya dake gami da juriya ya ce "Idan kuwa haka ne to tabbas Yarima ma baya jin maganarku, kamar yanda ka faɗa watansu ɗaya da aure ba'a kawo muku amarya ba, haka kuma shima mijin be nemi a kawo masa ba saboda umarninsa ku yake bi" A fusace Sarki Ahmad ya miƙe zai yi magana sai kuma ya fasa gami da komawa ya zauna, ransa ya masifar ɓace jin abin da Me martaba ya faɗa masa, sallamar wata budurwa ce tasa dukkaninsu maida dubansu gareta, shekarun matashiyar ba zai wuce ashirin da ɗaya ba, fara ce sol me kyau kamanninta ɗaya da Prince Muby, amma sai dai ya fita kyau nesa ba kusa ba, a bayanta wani matashin yaro ne wanda shigar kayansu iri ɗaya da yarinyar, kuma kamanninsu ɗaya kana ganinsu ka san ƴan biyu ne.


Kusa da Sarki Ahmad su ka zauna cike da girmamawa su ka gaishe da Fulani da me martaba, Husna ce ta kalli matashin yaron fuska ɗauke da fara'a ta ce "Ameer barka da wannan lokacin" Murmushi ya yi kafin ya ce "Mutanen Senegal ya hanya"

"Hanya lafiya ƙalau, Ameera sannu ko?"

Husna ta faɗa tana kau da kai gefe, wadda aka kira da Ameera ne ta ɗan taɓe baki kafin ta ce "Kema sannu"

Fulani da ke kallon yanayinsu ne ta girgiza kai, tana mamakin yara ƙanana ma sun san abin da ke tsakanin masarautar Sudan da masarautar Senegal, Allah ya kawo ƙarshen wannan zaman, Fulani ta faɗa a ranta tana mai ɗaukar tufa ɗaya cikin kayan abincin da aka kawo ta kai baki.





Tun da Afnan ta shiga part ɗin take jiyo warin sigari na tashi har yana neman saka ta amai, hanci ta toshe tare da aje basket ɗin kan wani makeken table na gold, hotonsa da ke gefe ta kalla yana cikin shigar ƙananan kaya wando blue da riga red, sai glass ɗin da ya saka me ɗauke da tambarin sarauta, ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin a ranta ta ce, mutum ko'ina sai ya nuna shi ɗan sarauta ne neman a sani, juyawa ta yi da niyar fita daga parlourn sai ta ji saukar hannun mutum kan kafaɗarta ana yi mata tafiyar tsutsa, da sauri taja da baya tana ƙare masa kallo.


Daga shi sai ɗan ƙaramin tawul duk surar jikinsa a waje, gashin ƙirjinsa ya yi kwance gwanin sha'awa, hannunsa ɗauke da sigari yana zuƙa kamar daga gare shi aka fara sarrafa ta, "Subhanallahi me nake shirin gani haka?"

Afnan ta faɗa tana nuna sigarin da ke hannunsa, gashin kansa ya shafa tare da lumshe ido wanda hakan ya zamar masa jiki ya ce "Abun da idanunki su ka gane miki, ki zuba mun abinci yunwa nake ji" Ya ƙarasa maganar yana zama kan wata arniyar kujera me zaman mutum ɗaya, wadda idan ka zauna zata zauna idan ka jingina zaka kwanta, kana ganin kujerun da ke parlourn ka san cewa ƙaryar wani babban attajiri ya saye irinsa, dan ba ƙananan kuɗi aka kashe a kansu ba.


A hankali ta motsa lips ɗinta kamar wadda magana ke yima wahala ta ce "Uhmmm ina ganin ka mance wadda ke tsaye a gabanka ne shiyasa ka ke faɗar hakan, Mubarak Ahmad Mulki, baka kai matsayin da zan zuba maka abinci ba, kawo maka da nayi ma ba a son raina ba ne" Tsayuwa ta gyara cike da izza gami da ji da kai ta ce "Umarnin Fulani ne..."

Sigarin da ke hannunsa ya zuƙa da ƙarfi, tare da fesarwa gefe idanunsa sun rine kamar garwashin wuta, nan take jikinsa ya fara rawa zufa na tsatstsaƙo masa tsananin ɓacin rai, kallonta ya yi a karo na biyu da rinannun idanunsa ya ce "Idan har baza ki zuba mun ba a ɗakinnan za ki kwana dan bazan buɗe miki ba, idan kuwa ki ka kwana anan kinsan abin da zai biyo baya".


Jin abin da ya ce ne yasa ta komawa da baya da niyar fita daga parlourn, da sauri ya ɗauki wani remote da ke kan table ya danna, yana sakin murmushin mugunta.


Afnan kuwa ganin ƙofar parlourn a rufe ne yasa ta juyo a fusace kamar wadda zata iya dukansa ta ce "Na san kaine ka rufe ƙofar nan dan kawai neman magana, a halin yanzu magana ma wahalar yi nake, ka buɗe mun ƙofa na fita ƙamshin turaren ɗakinnan be yi min daɗi ba, idan har ba so ka ke nayi amai a ciki ba".

Lumsassun idanuwansa ya rufe na ɗan wani lokaci, sai kuma ya miƙe tsamm kamar wanda aka tsikara ya nufi hanyar ɗakinsa yana faɗin "Duk lokacin da ki ka gama shawara ki sameni da abincina a ɗaki".

Ya ƙarashe maganar yana shigewa daga cikin ɗakin.


Da ƙarfin tsiya ta ƙwalla ihu tana faɗin "Wallahi baka isa ba na fika taƙama, na fika mulki na fika dukiya da ƙarfin iko, na wuce saninka, yau zaka ga taurin kaina sai ka san da wadda ka ke, a masu kula da ni ma baza ka kama darajar mutun ɗaya ba, ba bu abin da ka ke da face girman kai, mulkin da ka ke taƙama da shi ma baka iya ba".

Ta ƙarasa maganar tana dukan wani ɗan ƙaramin table na glass da ƙafa, nan take ya tarwatse a tsakiyar parlourn.


Muby da tun lokacin da ta fara magana yake bakin ƙofa a tsaye yana kallonta ne ya fara takowa a hankali inda take a tsaye, yau ta gama ɓata masa rai dan kalamanta sun shige shi, kai ko a mafarki ba'a taɓa samun wanda ya tozarta shi irin yau ba.


Ganin yana matsota ne kuma fuskar nan tashi a haɗe yasa gaba ɗaya tsoro ya mamaye zuciyarta, amma saboda kar ya rainata yasa itama ɗaure fuska tana nuna sa da tsaya baki na rawa ta ce "Ka daina matsoni da wannan ƙazamin jikin naka, bana son ƙamshin turarenka irin na ƴaƴan talakawa".

A fusace ya nufota yana faɗin "Yau kuwa sai kin lashe jikin da ki ka kira da ƙazamin jiki".




*GIDAN MULKI*


*By*


*Asmeetar Hydar*









P.2





Taku ɗaya ya damƙota tare da janyota ta faɗo ƙirjinsa, "Washhhhhhh, bayana" Ta faɗa tana dafe bayan nata, sannu a hankali ya ke lumshe lue-lue eyes ɗinsa yana buɗewa, "Me ki ka ce, ƙazamin jikina ko?" Ya tambayeta yana mai goga hancinsa a kan nata hancin, kawar da kai gefe ta yi jin warin sigarin da ke bakinsa, kamar me ciyon magana ta karkata baki tana faɗin "Please live me alone, wallahi bakinka warin sigari......" Saurin haɗe bakinsu ya yi tun kafin ta ƙarasa, sosai take turesa tare da nadamar abin da ta faɗa masa, ya kai kusan mintuna biyar a haka yana sarrafa harshenta cikin bakinta, Afnan kuwa duk ta jiƙe da gumi, jira kawai take ya saketa ko zata yi aman da ke damunta, a rayuwarta ta tsani sigari balle warinsa.


Jin yanayin jikinsa na neman sauyawa ne yasa ya yi jifa da ita gefe, kamar jira take nan take amai ya kwace mata, sosai take zuba amai kan sofa kamar zata amayar da hanjin cikinsa, duk kayan jikinta sun ɓace.

Kallon mamaki yake binta da shi da kuma tuhuma, lumshe kyawawan idanunsa ya yi yana mai gyara ɗaurin tawul ɗin da ke jikinsa ya ce "What does that mean? the smell of cigarettes makes you vomit, or you are pregnant?"

"Pregnant...?" Ta tambayesa cikin mawuyacin hali.

"Yes ciki shi nake nufi, idan shine kuwa sai ki je neman ubansa"

A fusace Afnan ta miƙe da ƙyar har jiri na neman kadata ta ce "You are very stupid, kuma baka san me ka ke faɗi ba, na tabbata cewa shayeshayen da ka ke ya taɓa maka ƙwaƙwalwa"

Saurin ƙatseta ya yi da faɗin "Did you just call me stupid?"

"Yes you are?" Ta bashi amsa a gadarance.


Gashin kansa ya shafa yana lumshe ido, sai kuma ya damƙe tawul ɗin da ke ƙugunsa da ƙarfin tsiya ya yi jifa da shi gefe tare da nufar inda take gadan-gadan.

Afnan na ganin haka ta yi saurin ɗaukar wata kwalbar turare, ta buga a tiles nan take kwalbar ta fashe, cikin masifa ta nuna shi da kwalbar alamun kar ya ƙaraso.

"If you add one more step here i will do something for you that everyone will regret in this house". She said that in confirmation.


Ko sauraronta be yi ba ya faɗa kanta, cikin zafin nama ta janye gefe tare da yanka masa kwalbar a bayansa, wata razananniyar ƙara ya saki yana dafe gurin ganin jini na zuba sosai, tana ganin haka ta jefar da kwalbar gefe jikinta na rawa kamar za ka ce ƙyet ta tsere.


Ana cikin haka ta hangi remote ɗin ƙofar a ƙasa, da sauri ta ɗauka tare da dannawa, cikin gudun da bata taɓa yi ba ta fice daga parlorn har tana haɗa steps gurin sauka hawa na ƙasa, kamar wata me taɓin hankali haka ta shigo babban parlourn da su Fulani ke ciki, sai dai wannan karon su Sarki Shuraihu basa nan shi da Sarki Ahmad, amma Mahaifiyar Muby wadda su ke kira da Mommy na zaune.


Dattijuwa me kyau fara da ita, sanye cikin atamfa me tsadar gaske an yi mata aikin duwatsu na gold a gaban rigar, wuyanta da hannunta na sanye cikin sarƙa da ƴan hannu masu masifar tsada har wani sheƙi su ke tsabagen hasken su.

Da sauri matar ta miƙe tana kama hannun Afnan da ke tsaye jikinta na karkarwa, cikin alamun tsoro Dattijuwar ta ce "Lafiya Gimbiya me yake faruwa ne? na ganki haka kamar an koroki"


Cikin sauke ajiyar zuciya a kai akai, ta ce "Sai ki je ki tambayi ɗanɗanki da yake neman yi mini fyaɗe, amma ba ni ba"

Ta faɗa tana ƙwace hannunta, cikin ɓacin rai Fulani ta daka mata tsawa "Kina da hankali kuwa? surukarki ce fa, ko ba komi ta haifeki shine ki ke faɗa mata magana haka"

"Fulani please, ku tafi ku duba yaronnan kafin ya mutu, dan gaskiya ba zan zuba ido ya yi min fyaɗe a banza a wofi ba, tun da ya zama bunsurun mata" Cewar Afnan tana barin parlourn cike da takaicin lalacewar da jikinta ya yi da amai, da kuma abin da Prince Muby ya yi mata.


Da sauri su Fulani su ka nufi part ɗin Muby cike da tsoron abin da zasu tarar, suna isa Mommy ta tura ƙofar amma a rufe, bugun duniyar nan ta yi amma Muby yaƙi buɗewa, dan dole su ka koma tare da mamakin abin da yasa be buɗe ƙofar ba.


A parlourn su ka ci karo da Sarki Ahmad cikin shirin ɗaurin aure, ya sha babban riga me kyau da tsada a gaban rigar akwai tambarin sarauta, Mommy ya kalla matarsa cike da murmushi ya ce "Lafiya na ganku haka? kamar an yi mutuwa" Fulani ce ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mommy alamun ta faɗa ko ta yi shuru, ɗaga mata kai Mommy ta yi alamun ta faɗa masa.

Kalllonta ta mayar kan Sarki Ahmad tana faɗin "Allah ya ja zamaninka akwai abin da ke faruwa tsakanin Gimbiya da Yarima, amma kuma ta kasa sanar mana, gaskiya ina tsoron abin da zai je ya dawo, saboda shi kansa Yarima yaƙi buɗe mana ƙofa, ba bu irin magiyar da bamu yi ba amma a banza". Fulani ta ƙarasa maganar tana sunkuyar da kai ƙasa, hankalinta ya masifar tashi dan ta san halin Gimbiya sarai zata aikata abin da hankalin kowa zai tashi a masarautar.

Ba tare da Sarki Ahmad ya ce uffan ba ya nufi part ɗin Yarima, dogaran da ke hanya sai faɗuwa su ke suna kwasar gaisuwa cike da girmamawa, a bakin ƙofar ya sami Muby na ƙoƙarin fitowa daga parloun,

Please Login or Register in order to submit comment