Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamaki ya gama rufe sa ne ya kalli Muby yana faɗin "Kana nufin wannan gidan ne Gimbiya ta siya?"

"Matsalata da kai rashin haƙuri" Muby ya bashi amsa yana ɓata fuska.


Sun jima suna horn amma shuru babu alamar za'a buɗe gate ɗin a fusace Muby ya sauko kan dokin nasa cike da gadara yake takawa har ya isa ƙofar gate ɗin, amma sai ya dakata yana mamakin meyesa aka rufe gidan daga ciki, ko dai Afnan ta san da zuwana ne, ya tambayi kansa a zuci, kaima ka san wacece Afnan kuma ka san babu abin da baza ta iya aikatawa ba, zuciyarsa ta bashi amsa, a hankali ya koma da baya tare da nuna wasu dogaransa guda biyar ya ce "A buɗe wannan ƙofar ko ta ƙarfin tsiya"

Bada ɓata lokaci ba dogaran suka fara dukan gate ɗin kamar zasu karya, sai kuma suka dakata jin kamar za'a buɗe gate ɗin.

Daga Muby har su Ashwan da ke bayansa kallon ƙofar gate ɗin suke yi dan ganin wa zai fito, amma basu ga kowa ba ga ƙofar kuma a buɗe, cikin zafin nama Muby ya ƙusa kai ciki ba tare da tsoron komi ba ya fara kallon gidan yana gyaɗa kai dan tabbas shine gidan da aka tura masa a hoto, gaba ɗaya tawagarsa su ka mara masa baya har tsakiyar makeken gidan wanda Ashwan ya gama tsurewa da lamarin saboda shi har yanzu ya kasa yarda cewa Gimbiya tana wannan gidan, kuma ya kasa yarda cewa ita ce ta ɗauke Maimun.

Babban parlourn su ka nufa amma sai Muby ya ɗaga musu hannu alamun baya buƙatar kowa ya biyo shi.

Ashwan kam magana ma wahalar yinta yake a halin yanzu.

Cikin takunsa me masifar jan hankali ya shige parlourn amma babu kowa, daga ƙarar AC sai TV da ke magana shi ɗaya.

Ba tare da wani tunani ba ya fara taka matattakalar, da sauri kuma ya tsaya yana kallon ɗigo-ɗigon wani abu kan steps ɗin kamar jini, to me hakan ke nufi kar dai Afnan ta kashe Maimun ya faɗa a zuciyarsa, gaba ɗaya tsoro ya mamaye shi, ganin babu me bashi amsar tambayarsa ne yasa shi haurawa sama da sauri, amma duka ƙofofin ɗakin a rufe daga cikin ɗakin kana jiyo kuka da nishin mutum kamar wanda ake zare ransa.


Hankalin Muby be ƙara tashi ba sai da yaji an ƙwalla wata iriyar ƙara nan take fitilun ɗakin su ka ɗauke ƙofar parlourn ta rufe kanta, kamar marar jini a jiki haka ya koma, duk wata jijiya da ke jikinsa ta saki, amma kasancewar Muby namijin duniya ne kuma me taƙama da kansa yasa be nuna alamun tsoron nasa a zahiri ba, cikin salon iya magana ya lumshe haɗaɗɗun idanunsa masu kama da madara kafin ya buɗe baki da ƙyar ya ce "Na san cewa ke kike duk wannan haukar, saboda rashin ilimi da jahilci, ki sani cewa idan har wani abun ya sami Maimun wallahi baza kiji da daɗi ba" Ya ƙarashe maganar muryarsa na sarƙewa, dan wani hayaƙin da ya shaƙa.

Nan take ya fara ganin jiri, idanunsa sun gama rinewa, dan har cikin kansa yake jin hayaƙin, bishi-bishi ya fara gani kamar wanda ya bugu, be gama mamakin abin da ke shirin faruwa da shi ba yaji an rirriƙe shi ta baya, da ƙarfin tsiya ya fara ƙoƙarin ƙwace kansa amma ya kasa, dan mutane biyar ne riƙe da shi kuma majiya ƙarfi, bada ɓata lokaci ba aka nufi wani ɗakin da shi, har yanzu baya ganin fuskar mutanen kuma hayaƙin na shiga hancinsa sosai har yana neman ɗaukewar numfashin sa.


Cikin zafin nama ya kaiwa ɗaya daga cikinsu naushi a hanci nan take jini ya ɓalle, ba shiri su ka sake shi tare da ja baya.

Da ƙyar Muby ya samu damar dafa ginar ɗakin cikin ƙarfin hali ya ce "Gimbiya kin aikata babban kuskure a rayuwarki, kuma sai kin ɗanɗani kaɗan daga cikin azabata, bana da ra'ayi ko sha'awar zama da ke dan na tsaneki amma wannan abin da kika yi shine silar tarewarki a gidana, babban albishir ɗinda zan yi miki shine, sai kin zama baiwa kuma ƙasƙantacciya a gidana, maimakon ki kasance mata a gareni sai dai ki kasance maƙiyiyata kuma abun ƙyama...." Ya ƙarashe faɗar hakan yana sulalewa ƙasa, kusan mintuna goma ya ƙara kafin ya fita hayyacinsa, saboda jininsa me ƙarfi ne kuma Muby akwai dauriya sosai gami da jarumta.


Nan take kuma haske ya bayyane ko'ina na ɗakin.


Gimbiya Afnan ce zaune kan wata haɗaɗɗan kujera me hoton damisa, fuskarta a haɗe kamar wadda taga mutuwarta, alamun fita tayiwa samarin da ke tsaye a gurin, cikin girmamawa su ka fice tare da janyo ƙofar.


Daga can waje kuwa Ashwan da mutanen Yarima Muby sun gaji da jiran fitowar sa, tun suna ganin wasa har su ka shafe mintuna talatin a haka.

Kallon ɗaya daga cikin dogaran Ashwan ya yi kafin ya ce "Shiga ka duba mana abin da ke faruwa, a tsorace ya ce "Allah ya ja zaminka me zai hana mu shiga tare dan alqur'an a tsorace nake"

Dariya mutanen gurin su ka kwashe da ita, ganin yanda jikinsa ke rawa, murmushi Ashwan ya yi yana faɗin "Okay ba damuwa bari na duba da kaina".

Ƙofar parloun ya murɗa amma a rufe gammm, kamar wasa ƙofa taƙi buɗewa.

Dole haka Ashwan ya juyo tare da kallon dogarawan da ke gurin cikin shakku ya ce "Gaskiya ina tantama anya kuwa lafiya?"

"Nima abin da ke raina kenan, saboda yanda naga duk yanayin Yarima ya canza tun lokacin da muka fito gida" Cewar ɗaya daga cikinsu.


Kafin Ashwan ya ce uffan su ka jiyo ihu daga cikin gidan, lamarin da ya ƙara tayar da hankalinsu kenan, gashi babu halin shiga tun da ƙofar a rufe take, me kula da Yarima Muby ne mai suna Fadil ne ya ce "Nifa muryar Gimbiya naji, kamar ita tayi wannan ƙarar"

"Eh nima naji amma ka rigani magana ne" Cewar Ashwan hankalinsa a tashe, cigaba ya yi da faɗin "Allah yasa ba wani muguntar Yarima ke yi mata ba?" Ya faɗa yana mai ƙarasawa bakin ƙofar.


Nan take Ashwan ya bada umarnin bincike ko'ina na gidan, ba tare da ɓata lokaci ba dogaran su ka fara duba lungu da saƙo, wasu har cikin ruwa sai da su ka shiga, amma babu kowa.

Daga can gefe wani ya ce "Ga Maimun nan a kwance" Da gudu mutanen da ke gurin harda Ashwan su ka ƙarasa, ganin halin da Maimun ke cike ne yasa Ashwan tallafota da sauri ya nufi mota da ita, "Ina son mutane goma su yi min rakiya zan kai ta hospital, ku kuma sauran ku cigaba da bincika halin da Gimbiya da Yarima su ke" Cikin sauri driver ya ja motar su ka bar gurin.

Sauran dogarawan kuma su ka tsaya bakin gate kowa na tsoron shiga daga ciki, suna tsammanin suma haka zata iya faruwa da su.



A gefen Afnan kuwa ita kaɗai ta san dalilinta na yin hakan, lokaci kawai take jira domin ta bayyana manufarta.



Muby ko baya ma cikin hayyacinsa, shi dai yana zaune ne kamar wani marar rai, dan babu abin da yake fahimta, duk da cewar yayi ƙarfin hali sosai amma da tuni ya sume.



Agogon hannunta ta kalla lokacin ƙarfe uku na yamma ta buga, daida lokacin da wayarta ta ɗau ruri, da sauri ta kara a kunne, okay kawai ta faɗa tana mai tashi tsaye ta koma ƙarshen bed ɗin, wani abu ta ɗauko a leda tare da fesa masa.

A hankali ta koma kan bed ta rakuɓe dan jiran abin da zai biyo baya, zamanta ke da wuya ta ji buɗewar ƙofar parlourn, a lokaci ɗaya kuma ta saki ihu me razanarwa.

Muby da ke zaune a gefe ne ya miƙe a harzuƙe, dan wannan abin da ta fesa masa ne ya dawo da shi hayyacinsa, a ƙarshen gadon ya sameta a ƙudundune tana rafka ihu kamar wadda ake cire ranta, hannu ya saka da niyar cafko, Afnan na ganin haka ta yi wuffff ta damƙo shi ya faɗo kan bed ɗin, rigarsa ta hau yayyagawa da kuma yagalgalawa, kamar daga sama suka ji an banko ƙofar da ƙarfin tsiya, Sarki Shuraihu ne tsaye duk jikinsa na karkarwa ransa ya masifar ɓace, Afnan kuwa da gudu ta miƙe tare da faɗawa jikin Mahaifin nata tana mai fashewa da kuka kamar gaske, kuka take sosai tana faɗin "Baffa ka taimaka mun kasheni zai yi, ya gama lalata mun rayuwa na shiga uku ni Gimbiya...." Ta faɗa tana mai jan numfashi kamar wanda zata sume, da sauri me martaba ya riƙota yana mai faɗin "Baza ki mutu ba insha Allah har sai kinga yanda za'a bi miki haƙƙinki".

Muby da ke tsaye kamar an dasa shi ne ya sharce gumin da ya feso masa, sai a yanzu ya fahimci manufar Afnan, dama sharrin fyaɗe zata laƙamun, ya faɗa a ransa yana mai lumshe idanunsa da ƙarfi, zuciyarsa kuwa ta hau bugawa akai-akai.


Hannunta me martaba ya kama tare da fita ɗakin, Afnan kuwa sai wani ɗangesa ƙafa take kamar gaske, duk kunya ta kama Sarki Shuraihu ganin yanda ƴar tasa ke tafiya da ƙyar.

A filin gidan su ka sami Ashwan na ƙoƙarin shigowa, da sauri ya ƙaraso gurin cike da mamakin ganin Sarki Shuraihu, har ƙasa ya rusuna ya kwashi gaisuwa, a masifance me martaba ya ce "Bana buƙatar jin komi daga gareku, na san cewa kana sane da abin da yaronnan ya yiwa Gimbiya amma babu wani matakin da aka ɗauka"

"Allah ya ƙara maka nasara wallahi bansan abin da ke faruwa ba, asalima yanzu na kai Maimun asibiti itama anan gidan muka sameta a kwance duk jikinta tabon duka ne" Cewar Ashwan yana sunkuyar da kai ƙasa ganin yanda jikin Afnan ya lalace da jini ga rigar jikinta duk an yage, a ransa yake faɗin kar dai ace Yarima fyaɗe ya yiwa ƴar mutane.

Me martaba ne ya ƙatse zancen zucin da cewa "Koma menene ai abokinka ne, amma maganar gaskiya wannan karon sai kowa ya haɗu da ɓacin raina akan abin da ya aikata" Be jira abin da Ashwan ɗin zai ce ba ya ja hannun Afnan su ka fice daga gidan, dama daga shi sai mutum uku su ka shigo garin, motoci uku ne a waje suna jiransu, ɗaya daga ciki aka buɗewa Afnan ta shiga sannan me martaba ya shige ɗaya, nan take su ka bar harabar gidan, cike da girmamawa drivern ya ce "Allaha ya ja zamainka asibiti zamu nufa da ita?"


Cikin taƙama da mulki me martaba ya ɗaure fuska yana faɗin "Mu tafi gidan Sarki Ahmad domin ya fara ganin abin da ɗan nasa ya aikata" Ba tare da ɓata lokaci ba drivern ya nufi hanyar gidan.



A ɓangaren Muby kuwa tun da su me martaba su ka fita yake anan gurin ba tare ya motsa ba, shi kansa ya rasa abin da ya faru da shi, ko dai bayan sun shaƙa masa hayaƙin ne ya yi mata wani abun ko kuma sharri ne take neman laƙa masa, gaba ɗaya ya kasa bawa kansa amsar tambayar.

"Yarima me ka aikata haka?" Cewar Ashwan da ke tsaye ya harɗe hannayensa.

Mamaki ne ya ƙara kama Muby amma sai ya shafa gashin kansa yana mai lumshe idanunsa a hankali kuma ya ce "Bangane abin da ka ke nufi ba"

"Baka gane abin da nake nufi ba ko rainin hankali bayan ka gama lalata rayuwar yarinyar mutane, duk da cewar matarka ce amma hakan baya nufin ka wulaƙantata"

Cewar Ashwan ransa a ɓace, "Enough Ashwan i have enough with your talk, idan har nayi mata fyaɗe ba matata ba ce?"

"Matarka ce amma baka bi yanda addini ya tanada ba, ka sace yarinya ka ɓoye, bayan ka gama sa an yiwa Maimun shegen duka, ashe dama dalilin da ya sa ka ce ka san inda su ke kenan......." Wani irin shaƙa Muby ya yi ma Ashwan, da ƙarfin tsiya ya haɗe jikinsa da bango, duk idanun Ashwan ya zazzaro, cikin ɓacin rai Muby ya ce "Don't say another word, if not i'll definitely show you what can i do to you, kana magana ne da Yarima ɗan Sarkin Sudan ina fatar ka fahimta?" Ya ƙarashe maganar yana sakin kwalar rigarsa tare da barin ɗakin cike da izza.

Ashwan da ke tsaye idanunsa sun yi ja saboda shaƙar da Muby ya yi masa, da sauri ya bi bayansa yana kiran sunansa amma kamar bada shi yake ba, "Yarima please wannan fa ba mafita ba ce, yanzu na san me marta ba hospital zai kai Gimbiya ba, dole gida zai fara tafiya da ita domin shaidawa Sarki abin da ke faruwa, na tabbata cewa idan Alhaji ya ji wannan zancen ba ƙaramin tashin hankali za'a yi ba, sanin kanka ne Alhaji na masifar son Gimbiya"

Da ƙarfi Muny ya ce "Ashwan ya isa haka bana son surutu ka isheni da zacen wata banza" A fusace ya fice daga gidan.


Tun daga harabar gidan Sarki Shuraihu ke masifa har su ka shiga babban parlourn.


Masu tsaron parlourn ne kawai ke ciki, sai kuyangin da ke aiki, har ƙasa su ka duƙa suna gaishe su amma kamar bada su ake ba, fada su ka nufa dan sun san yanzu haka Sarki Ahmad yana can, duk inda su ka ratsa a gidan haka masu tsaron ke faɗuwa suna kwasar gaisuwa amma daga Afnan har Abbanta babu me kula su, a can suka tarar da mutane da Sarki Ahmad, a gefensa Ameer ne da Ameera cikin shigar alfarma, sun yi kyau sosai.

A ɗaya ɓangaren Sarki Ahmad ne ana fadanci, mutane masu kawo ƙorafi da sauran dogaran da ke gurin ne su ka zubawa Sarki Shuraihu ido cikin tsananin mamakin ganinsa a irin wannan lokacin, ga kuma Gimbiya a gefensa duk jikinta jini kamar ba ita ba, sai ka duba da kyau zaka ganeta.

Afnan kuwa ƙara marairace fuska ta yi tana mai matso hawayen ƙarya, da sauri wata kunyanga ta ɗauko wani babban mayafi ta rufa mata, cike da tashin hankali Sarki Ahmad ya miƙe daga kan karagarsa yana faɗin "Ina buƙatar ku bamu guri zamu gana"


Cikin girmamawa mutanen da ke gurin su ka tashi tare da ficewa, ya rage daga Sarki Ahmad sai Ameer da Ameera da ke zaune suna kallon Afnan.

Gurin zama Sarki Ahmad ya nuna musu yana faɗin "Ku zauna mana ga guri"

"Ba zama ya kawo mu ba, ina Alhaji ina buƙatar ganinsa Ameera tashi ki kirawo min shi, idan kuma a can zamu same shi ai sai mu tafi dan wannan ba maganar haƙuri ba ce dole sai an ɗauki mataki, dan ba zan haƙuri ba" Sarki Shuraihu ya ƙarasa maganar tasa ransa a ɓace.


"Ba sai an kirani ba labari ya iso kunnena a kan cewa an samu damar ganin Gimbiya" Cewar wani Dattijo da ya shigo fadar, hannunsa ɗauke da wata sandar gold irin ta sarauta, kana ganinsa ka san tsufa ya ja sosai, ba dan kuɗi da mulki ba da ko kallonsa ma baza ka iya ba, saboda zaka yi tsammin zai iya mutuwa a kowanne lokaci.


Sarki Shuraihu ne ya yi saurin isa gurin yana mai kama shi.


Bayan kowa ya zauna Dattijon ya fara magana kamar haka "Shuraihu ya hanya ashe ka dawo? masha Allah mungodewa Allah da ya bayyana Gimbiya cikin ƙoshin lafiya......"

"Ina ƙoshin lafiya kuwa bayan an gama lalata mata rayuwa" Cewar Sarki Shuraihu yana mai kawar da kai gefe.

"Tashi ku shiga daga ciki Ameera daga nan ku kira mun Mahaifiyarku" Cewar Alhaji yana mai jinjina kai, dan ya san duk abin da yasa Sarki Shuraihu ɗaga masa murya ba ƙaramin abu ba ne.


Su Ameera kuwa ficewa su ka yi dan cika umarni, bada jimawa ba Mommy ta shigo bakinta ɗauke da sallama cikin shigar alfarma sai ƙamshi ke tashi a jikinta, tayi kyau sosai cikin shigar less me tsadar gaske, a can gefen Afnan ta zauna, kamar jira take ta faɗa jikinta tare da fashewa da kuka tana faɗin "Mommy na shiga uku ya lalata min rayuwa, yanzu ina zan saka raina naji daɗi?" Gaban Mommy ne ya yi mummunar faɗuwa, ƙirjinta sai dukan uku-uku yake, kar dai ace wani ne yayi mata fyaɗe.


Rarrashinta Mommy ke yi tare da bata baki, da ƙyar aka samu ta yi shiru, Alhaji ne ya ce "Shuraihu ka barmu a duhu me yake faruwa, kuma su waye su ka sace Gimbiya?"

"Yarima ne, bayan ya sace ta ya killace ta a wani gidan tare da yi mata mummunan fyaɗe"

Kamar ɗaukewar ruwan sama haka fada ta yi shuru, idan ba ƙarar AC da sheshsheƙar kukan Afnan ba, babu abin da ka ke ji.

Kusan mintuna uku a haka kafin Alhaji ya ce "Ina Yariman yake?"

"Gani nan Alhaji"

Muby ya faɗa yana mai ƙarasowa cikin fadar, fuskarsa a haɗe tamkar wanda be taɓa dariya ba, idanunsa kuwa sun yi jajir, guri ya samu ya zauna tare da sunkuyar da kai ƙasa, kamar daga sama ya ji Sarki Ahmad ya ce "Yarima ka bani mamaki, a yau na tabbar cewa baka biyo halina ba, har zaka iya ɗaukar yarinyar da iyayenta basa ƙaunarka ka ɓoyeta dan tana matarka"

Rasss gaban Muby ya faɗi, shi yanzu baya ma da abin da zai ce.

"Magana nake yi maka dan ubanka"

Sarki Ahmad ya daka matsa tsawa.


"Abba maganar gaskiya sharri ne wannan, babu abin da ya faru tsakanina da ita"

"Idan har sharri ne dukan da kayiwa Maimun fa? dan kawai ta hanaka abin da kake ƙoƙarin aikatamun, ni yanzu ka gama da rayuwata kawai a raba wannan auren ba zan iya ba" Cewar Afnan tana mai cigaba da matsar ƙwallah.


Mamaki tsoro takaici da tsanarta ne ya ƙara dira a zuciyarsa.

Alhaji ne ya ce "Ina Maimun ɗin take?"

"Tana hospital" Muby ya bashi amsa.

Sarki Shuraihu ne ya ce "Kun gani ba, tabbas gaskiya ta fara bayyana tun da har ya san inda take, ai saika saka a kawota nan ko zata faɗi gaskiyar lamari"

"Eh ka kira a dawo da ita dan muji daga bakinta" Cewar Mommy dan ita kanta lamarin ya ɗaure mata kai, kuma ta ƙudurta a ranta idan har da gaske ɗanta ne ya aikata haka tabbas sai ta yi magana.

Waya Muby ya ciro a aljihun rigarsa yana mai danna numbern Ashwan, bugu ɗaya ya ɗaga "Ka kawo Maimun gida Alhaji na nemanta" Be jira abin da Ashwan ɗin zai ce ba ya katse wayar.


Shuru fada ta yi kowa na tunanin zuci.

Ameera da ke laɓe a ƙofa ne ta koma daga cikin gida ranta a ɓace, tana shiga ɗakin ta samu Ameer na waya da Husna, haushi ne ya ƙara cika ta ta ɗauki wayar tare da jefawa kan bed, "Meye haka Malama ina waya za ki ɗauka"

"Ina lafiya kuwa bayan Gimbiya ta laƙawa Brother sharri" Cewar Ameera tana zama kan sofa.

Kusa da ita Ameer ya dawo yana faɗin "Sharri name fa?"

"Wai ya yi mata fyaɗe, har da cewa ya daki Aunty Maimun ƙawar Aunty Munirat, yanzu haka ana jiran a zo da Aunty Maimun domin jin abin da ke faruwa, ni babu abin da ya ɓata mun rai irin wai Yarima ne yayi mata fyaɗe, gaskiya banyarda ba, na san halin Brother ba zai taɓa aikata haka ba, kaima ka san shi da girman kan tsiya, gami da taƙama yana mugun jan ajinsa" Ameera ta ƙarasa maganar tana mai dukan bayan Ameer.

Gigirga kai Ameer ɗin ya yi yana faɗin "Bamu da tabbacin abin da ke faruwa har sai ita Maimun ɗin ta zo, dan haka ki daina wani yanke hukunci"

Husna da ke sauraren abin da ke faruwa ta waya ne ta yi saurin kashe wayar jikinta na rawa, dama a lokacin da Ameera ta karɓe wayar daga hannun Ameer bata kashe ba.


Ba wani dogon lokaci aka ɗauka ba su Ashwan su ka shigo gidan, har fada su ka sami sauran mutanen ana zaman jiransu.

Da ƙyar Maimun ke taka ƙafarta duk jikinta ya yi tsami, Afnan na ganinta ta yi saurin miƙewa ta ƙarasa gurin tare da rungumeta tana mai sakin kukan ƙarya, cike da mamaki Maimun ke ture ta tana faɗin "Washhhhh" Saboda zafin da jikinta ke yi, a hankali Afnan ta matsar da bakinta daidai kunnen Maimun ta ce "Idan kina son Yarima kuma kina buƙatar aurenmu ya mutu dan ki aure shi dole ne ki yi amfani da abin da zan faɗa miki, duk abin da za'a ce miki karki taɓa yarda ki ce Yarima be yi min fyaɗe ba, magana ɗaya ce shine ya aikata idan kika ce be aikata ba, zaki rasa shi kuma zan tare gidansa, kinga kin yi biyu babu kenan, maganar dukan da aka yi miki kuwa ki san abin da zaki faɗa"

Tana gama faɗin hakan ta koma ta zauna tare da share ƙwalla a zuciyarta kuma murmushin samun nasara take.


Bayan kowa ya samu natsuwa ne Alhaji ya kalli Maimun cikin haɗe fuska alamun ba wasa ya zaunar da su ba ya ce "Me ya faru tsakaninki da Yarima, kuma waye ya yi miki wannan duka haka?"

"Yarima Muby ne, bayan ya yi ƙoƙarin aikata manufarsa a kan Gimbiya, ni kuma na hana hakan shine yasa aka kamani tare da azabtarwa"

A fusace Muby ya tashi da niyar damƙo ta, Ashwan ya tare shi yana faɗin "Meye haka kuma? dan kawai ta faɗi gaskiya"

Ƙwace jikinsa ya yi yana mai komawa ya zauna dan jin yanda zuciyarsa ke zafi, gaba ɗaya ransa ya gama ɓaci, cikin fushi Mommy ta ce "Ka bani mamaki Yarima ban taɓa tsammin haka daga gareka ba, ban taɓa shiga maganar aurenka da Gimbiya ba amma yau na shiga" Kallonta ta mayar kan Alhaji da bakinsa ya mutu ta ce "Ina neman afwa daga gareka amma a gaskiya yau wannan auren zai mutu, dan ba zan zuba ido ana tashin hankali ba, idan har ba zai sake ta ba sai dai ya canza wata uwar amma ba ni ba"

Gaba ɗaya hankalin Ashwan ya tashi dan baya son auren ya mutu, idan ka cire Alhaji da kuma Ameer da ke laɓe a ƙofar ɗakin, babu wanda baya farinciki da batun rabuwar auren, sai kuma Mommy wadda bada son ranta ta faɗi hakan ba, kawai dan nema musu sauƙi ne gaba ɗaya.


Sai a lokacin Sarki Shuraihu ya yi magana cikin farinciki ya ce "Nima abin da nake tunani kenan, bayan haka wallahi sai an hukuntashi a kan abin da ya aikata, dan ba zan yafe ba".

"Ya isa haka babu wanda zai raba aurennan kuma babu wanda zai hukunta Yarima idan ina numfashi......"


Gaba ɗayansu juyawa su ka dan ganin wadda ta yi maganar.



Hajiya ce Mahaifiyar Alhaji Shuraihu, tsaye a bakin ƙofar.

Ameer da ke laɓe kuwa daɗi ne ya kama shi, ganin Hajiya Babba, ƙarasowa ta yi ta zauna tana mai kallon Sarki Shuraihu cikin fushi ta ce "Sai da na faɗa maka cewa bana son tashin hankali, amma kana ƙoƙarin raba auren da ba kai ka haɗa ba, na san cewa idan har ka dawo sai ka yi ƙoƙarin raba auren shiyasa kana barin ƙasar nima na biyo ka". Kallon Mommy da kanta ke ƙasa tayi kafin ta ce "Ke kuma da ki ke faɗin sai dai ya canza uwa to sai ki kashe shi idan baki sonsa"

Tun da Hajiya ta fara faɗa kowa ya yi shuru a ɗakin kamar an yi mutuwa, dan daga Alhaji sai ita ke kafa doka a tsakanin masarautun a zauna lafiya.


Sai da ta gama faɗan kafin ta kalli sauran mutanen da ke fadar ta ce "Ni na yanke hukuncin sati me zuwa za'a kawo Gimbiya, wannan shine ƙarshen magana, dan haka ku fita ku bamu guri zan yi magana da iyayenku" Jiki a sanyaye kowa ya fice daga fadar, Maimun kuwa kamar ta yi hauka, ga samu ga rashi, haka ta lallaɓa ta nufi gida cike da tunanin abin da zata yi dan auren Yarima da Gimbiya ya mutu.


Wani ɗaki aka nufa da Gimbiya Afnan dan ta gyara jikinta, ɗakin ya haɗu sosai babu abin da ba zai burgeka a ciki ba, komai na ɗakin people ne hatta pentin, tana shiga ta ɗauki wani glass cup ta buga da ƙarfi kan mirrown ɗakin nan take mirrown ya tarwatse, kuka ta fashe da shi kamar wadda uwarta da ubanta su ka mutu, sosai take rusa kuka dan bata taɓa tsammanin cewa reshe zai juye da mujiya ba, duk a tunaninta a yau aurenta zai mutu amma gashi ta jawa kanta tarewa da sauri, gaba ɗaya ta tarwatse kayan ɗakin.

"Ai

Please Login or Register in order to submit comment