Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tafi zai samo min makarantar sakandire ta
kudi na karasa karatuna, tunda har na
kai aji na hudu a can, kuma ya fuskanci ina da kokari, ina
magana da Turanci sosai.
Ita kuma Khausar tunda ba ta yi nisa a karatu ba zai
samar mata makarantar koyon sana,a ta koyo ta dinga yi.
Sai Ummana Fuse ta ce a saka ta a makarantar koyon
rinin kamfala, amma babu makarantar anan kusa sai a
Abrkan ake yi. Sai dai idan ta koma gidan kanwarta
Umma Aisha da ta ke unguwar Dukuma ya fi kusa da
Abekan.
Shikenan sai aka tsayar da wannan shawara kafin ya
koma England sai da ya tabbatar na fara zuwa makaranta,
Khausar ta khaura gidan Ummna Aisha da ke Dakuma da
zama, tana zuwa Abekan koyon kamfala.
Ya yi mana alkawarin zai dinga aiko mana da kudin
makaranta (school fees), da kudin motar zuwa da
dawowa har mu gama. Abu daya ne ba mu ji dadi ba, shi
ne da aka raba mu ni da Khausar domin tunda muke a
rayuwarmu ba mu taba rabuwa ba.

Ta yi ta kuka kullum ana ba ta hakuri haka ni ma idan na
shiga bacci, sai na yi ta kuka ni kadai don
tausayinta, bata da kowa sai ni na rage mata, haka ni ma
ita ta rage min. Koda yake muna ganin kakarmu mai
tausayinmu muna jin dadi, sai kadan daga cikin dangi
masu kula mu kamar su Uncle Hamza da ya zo ya
taimake mu. Duk wanda ya taimaki wani Allah Zai
taimake shi...''
Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Ya ya aka yi kuma?
Abdul-Sabur ya yi dan murmushi, ya ce, ''Suna kiran
motar hayarsu Bus da suna Toro-toro, kullum sai na hau
toro-toro na tafi makaranta idan an taso na hau na dawo
gida. Na ga bambanci tsakanin karatun Kano da na Accra,
a Kano na fi *yan ajinmu kokari, tunda na shiga
makaranta daga firamare har zuwa sakandire ni ne
monita dan kokarina,
amma a Accra ni nake zuwa na karshe a ajinmu har ana
tunanin a mayar da ni ajin baya. Allah Ya taikama
Malamin ajinmu ya ce a kyale ni ya ga alamar ina da
kwazo da saurin koyo, watakila idan na dage na saba da
*yan ajin zan yi kokari.
Turancin su daban da namu, domin su suna kwaikwayon
irin na turawa ne sosai ba kamar anan Nigeria ba da
kowa yake yin yadda ya ke so.
Hausawa suna turanci kamar da Hausa suke magana,
Yarbawa suna yi kamar da Yarbanci, haka Igbo da sauran
kabilu (broken English).
Idan ka ji dan Ghana yana Turanci sai ka rantse a Turai ya
girma, saboda kowacce kalma suna furta
ta dai-dai da yadda Turawan suke furtawa.
Tabbas yadda Malamin ajinmu ya fada haka ne, rashin
sabo, fargaba da gane turancinsu ne ya sa na zama komabaya a ajinmu ba wai rashin kokarin ba ne. Amma da
shekara ta zagayo sai warware
gaba daya na rikide, ni da *yan ajin ake damawa.
Da muka gama aji hudu muka wuce aji na biyar nan ne
na gagari maza, ba ma matan ajin ba. Mu uku ne muke
gumurzu akan karbar na daya. Idan na tashi daga
makaranta da yamma sai na tafi 'Zarbarma Land' sunan
unguwar ke nan, akasarin *yan unguwar Zabarmawa ne,
ma'ana daga kasar Niger suke. Suna sana'ar canjin kudi,
wasu na siyar
da albasa, leda da fina-finan Hausa ko pure water.
Ko na je unguwar Zango nan kuma *yan Nigeria ne, a
nan ne za ku ga masu bara kutare, makafi da guragu. Nan
na ke samun abin yi irin su dako, ko jiran shago ko tallata
kaya a cikin kasuwa na je na
zazzagaya na yi ciniki na kawo a sallame ni da dan kudi
kalilan na ci abinci, na rago sauran na ba wa
kakata ko na boye na ci abinci a makaranta idan an fito
break....
Faduwa ta girgiza kai alamar tausayi, ta ce, Allah Sarki, ina

kanwarka Khausar, a wanne hali ta ke ciki a can unguwa
mai nisa Dukuma?''
Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya ce,
''Tana can tunda ta je sai da ta shekara ba ta zo
unguwarmu ba, ni ne dai duk sanda na bushi iska nake
zuwa na ganta, haka kakarmu tana kokarin zuwa. Idan ta
samo kwancen atamfofi sai ta zuba a
leda ta je ta kai mata.
Rayuwar Khausar abin tausayi ce a can, gida ne da yake
cike da *yan mata, *ya*ya da jikoki na Ummana Aisha.
Wasu *yan makaranta, wasu babu karatun, wasu ustazai
wasu kuwa *yan iska. *Yan mata sunfi goma don haka sai
rigingimu da
tsegungumi, sun tsani Khausar, sharrace-sharrece kalakala idan an rasa wani abu ace ita ta dauka ayi ta zaginta
ana dungureta. Sai daga baya aga abin ko a kama wacce
ta sace a cikinsu Haka kowacce ta ke ciyar da kanta, don
haka dole Khausar ta fita nema. Kudin motar zuwa da
dawowa Abekan ba ya da matsala Uncle Hamza ya
turowa Ummana Aisha tana ba ta, sai na siyen abinci ne
da na zirga-zirga don daga makarantar wani lokaci suna
hawa toro-toro su je wasu unguwannin koyon aiki kamar
unguwar Nima,
Guinea kwanakir ko Mamubi. Suna yini acan tun daga
safe har marece.
Ina iyakacin kokarina wajen kawo mata agaji da *yan
kudade, biredi ko fanke da zata dinga yaga tana ci a duk
lokacin da ta ji alamar yunwa zata yi mata illa.
Rayuwa kenan, komai mai wucewa ne, dadi ko wahala....
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ne, babu abin da yake
dauwamamme a duniya.
Ya ce, ''Khausa ta rame saboda kewa ta, ga tsangwama da
rashin wadataccen abinci. Sai na bata shawara ta dinga
zuwa kasuwa tana rini ranar asabar da lahadi sai ta dan
adana kudin da ta samo ta dinga cin abinci a makaranta.
Da kai na na kai ta wata karamar kasuwa da ake kira
Malata, anfi siyar da gwanjo a kasuwar, anan na samar
mata aiki a shagon wata mata mai suna Mrs. Ibrahim don
bana so na kai ta shagon maza saboda lalata.
Ghana ba kamar Nigeria ba ne, inda ADDINI da AL'ADA
suka saka kunyaa idon mutane, sukan rike mace a bainal
nasi ba komai ba ne. Don haka zinace-zinace ya yi yawa,
saboda arna sun fi yawa.
Da farko Mrs. Ibrahim ta ki yarda ta dauke ta aiki data ji
an ce sai asabar da lahadi kadai zata dinga
zuwa, ta fi son wacce zata dinga zuwa kullum. Na dinga
rokar ta har da durkusawa a kasa ina zubar da hawaye
ina cewa ta taimaka mana mu marayu ne kuma baki ne a
kasar dan bamu da inda zamu je mu sami wani aikin in
ba a wajenta ba. Nan danan ta ji zuciyarta ta karaya sai ta
tausaya mana ta amince.
Sai na ji hankalina ya kwanta dan naga hankalin Kausar ya

kwanta, ta kuwa ci sa'a ta hadu da uwar daki mai kyauta
da tausayi. Tana bata lada fiye da kudin aikin yadda ta
dauke ta. Allahu Akbar!
Rayuwa kenan Allah Yana bayan wanda Ya dogara da Shi.
Shekara biyu ne daman ake yi a makarantar koyar
kamfala, Allah cikin ikonSa Khausar ta kammala, aka bata
satifiket dan haka Ummana Fuse ta daukota, ta dawo da
ita gidanta sai farin ciki ya kama mu. A waya na shaidawa
Uncle Hamza cewar Khausar ta kammala makaranta tana
neman jari za ta dinga yin rinin a gida. Ummana Fuse ta
karbi waya ta sake yi masa bayani ta roke shi daya sake
jurewa ya ci gaba da taimakon mu, dan mu marayu ne
Allah zai taimakesa shima.
Ya ce babu matsala, Khausar ta rubuta abubuwan da take
bukata da yawan kudaden dan ya turo mata da kudin.
Akwai wani bangare a gidanmu tsohon waje ne,
bangarensa na gado ya ce ya bata aro ta dauka sai ta
dinga yin rinin a ciki.
Daya turo mata da kudin sai muka dauko masana suka
tona mata ramukan, muka je kasuwa muka
hado duk abubuwan da ake bukata a wajen rinin.
Ni da Ummana Fuse sai muke dan taya ta duk da bamu
san yadda ake yi ba amma muna taya ta da miko
wannan, zubo wancan kamo wadancan.
Idan tayi rina ta buga kamfalu kamar turmi goma ko
ashirin sai ta kai kasuwa ta sararwa masu shagunan da
suke sayar da atamfofi, shaddoji da kamfalu. Khausar ta
zamo ita take bani kudin abinci idan zan tafi makaranta a
lokacin ina ajin karshe ina shirin fita. Muka zamo ba'a
sauke tukunya a gidan Ummana Fuse abincin safe, rana
da na dare duk muna dafawa saboda cinikin kamfalar da
Khausar take samu.
Hankali a kwance nake ta karatu yadda ya kamata dan
haka na ci jarabawa sosai fiye da tunanin mutane. Daga
cikin darussa guda tara da muke yi na ci A1 shida, B1
biyu C1, kuma sciences na yi. Koda na fadawa Uncle
Hamza abunda na ci a jarabawa sai ya yi farin ciki ya
kuma yi min alkawari zai nemar min makaranta a jami'a
mai kyau a Ingila sai in karanci Medicine ko Engineering.
Farin ciki ya lullubemu, Ummana Fuse ta ce nayi shuru
da bakina kada na fadawa *yan uba da sauran *yan uwa
masu hassada sai dai kawai suji tafiya. Na ja bakina na yi
shuru inajin *yan hassada
kuwa suna ta surutai wai mu ne tsintacciyar mage an ci
jarabawa an rasa kudin shiga jami'a. Da aka
fada maka Hamza zai iya biya maka kudin jami'a ne?
Wanan me shegiyar rowar? Ummana Fuse ta ce in yi
musu shuru kada in ce komai.
Allah cikin ikonSa shekara na zagayowa Uncle Hamza ya
yi waya ya ce in hada takarduna in kai gidan abokinsa zai
kai masa Ingila, ina rawar jiki na hada na kaiwa abokin.
Bayan tafiyar abokinsa da watanni uku sai ya turo min da

komai na tafiya kamar tikiti da biza aka tabbatar min na
sami shiga jami'ar Cambridge da take cikin Ingila.
Na yi sallama da kakata da kanwata ina kuka suna kuka,
makiya suka sha takaici a lokacin da na zaga dangi ina
mai musu sallama tafiya ta tabbata. Na tafi Ingila karatu
cikin kwanciyar hankali, sai dai matsalolin da ba'a rasa ba
daga matarsa da *ya*yansa ba sa so na, saboda tsabar ba
su saba ganin bako a gidansu bakar fata ba, da kuma
yahudancin da yake cikin ransu. Ko kudi ko kaya
zai ba ni, sai dai da dubara kuma a boye, saboda matar
sai ta hana shi baro-baro a gabana. Kun san Nasara bai
iya boye-boye ba da gulma, gar da gar suke abubuwansu.
Ban damu ba saboda na saba da irin wadannan
tsangame-tsangwame a baya. Karatuna na saka a gaba
don shi zau fishshe ni. Da zaman ya gagara ma sai na
shawarci Uncle Hamza nace ina so na koma zama a cikin
makaranta a rukunin gidajen dalibai da yake cikin
makaranta. Ina so mu zauna
gida daya da abokina Usman shima dan Accra ne.
Uncle Hamza ya yarda ya biyamin duk abin da na bukata
na kudin haya, kayan abinci da dai sauransu.
Lokacin wayar hannu ba ta wadata ba sosai a Accra, sai
dai na kira wani gida a kusa da gidan su Ummana Fuse na
ce a kira su, bayan mintuna ashirin sai na sake kira mu yi
magana da su. Kullum
suna cemin ba su da wata matsala kasancewar aikin rinin
kamfala ya karbi Khausar, an fara saninta ana ta kawo
mata aiki, suna samun na
cefane. Amma duk da haka idan na sami mai tafiya ko
kuma transfer ta banki sai na kundige rabin kudin da
Uncle Hamza ya ke ba ni na tura musu,
don su sake jin dadin rayuwarsu. Kasancewar akwai
ayyukan yi a England da na gane gari, sai na dinga fita ina
yin ayyuka irin na awannin nan a biya ni.
Kamar ba da abinci a hotel, goge-goge da share-share a
ofisoshi, duk ranar da ba ni da darasi.
Alhamdulillahi na samu kudi mai yawa a wannan harkar,
saboda na iya aikin karfi, kuma ba ni da girman kai.
Sabanin abokaina *ya*yan masu hali,
wadanda iyayensu ne suke turo su karatu sun kuma jifgo
musu dukiya mai yawa saboda gata,
kada ma *yan Nigeria su ji labari sun fi kowa irin wannan
wadaka da kudi.
Ina turawa su Khausar kudi masu yawa da kayan sakawa
daga English wears har atamfofin super
Hollanda yayin da mahassada suka shiga aikinsu na
hassada da yada labarun karya.
Wai sai dai idan ba karatu na je ba, damfara nake ina turo
musu da kaya da kudi haka. Idan su Khausar suka fada
min sai na yi dariya na ce su rabu da su, kuma su toshe
kunnuwansu ko sun ji su ki ji.
Abinka da Babba sai Ummana Fuse ta shiga yimin

nasihohi tana cewa, kada na yarda na biyewa abokan
banza na fada harkar banza. Kada na sake na yi sata ko
damfara dan na turo musu da kudi, su rinin kamfalar nan
ma ya ishe su, su ci abinci.
Na yi mata rantsuwa bana banayin wannan harkar inda
ina yi da Uncle Hamza ya sani tuntuni, kuma da zai sanar
da ita koma ya koro ni gida. Kuma can kasa ce mai tsaro
kana yi za,a kama ka, na'urorin daukar hotuna a ko'ina.
Khausar daman a bayana ta ke, tasan halina don haka ba
ta damu da sharci-fadin mutane ba, ita ce
mai hana Ummana Fuse zato.
A waya suke fara fada min cewar, Khausar ta sami saurayi
yana so ya aure ta, sunansa Isah. A Accra yake zaune yana
sana'ar siyar da gwanjo, amma dan asalin garin Kita ne
dan Yaren Aibe.
Umaimah ta ce ''duk kasar Ghana ne? Ya ce ''Ai garin Kita
nan ne ma asalin Ghana dan dai yanzu garin duk babu
mutane sosai ruwa ya cinye su,
saboda suna da katon teku wanda ya ke fita har kasashen
turawa.
Akwai gidajen tarihi da suke wajen idan ku ka je zaku ga
jinin bayin da turawa suka kashe, idan bayin suka yi
gardama ko rashin lafiya, ko idan
suka yiwa mace baiwa ciki sai su harbe ta anan dan basa
son su haihu da su. Ban bawa Khausar goyon baya ba,
don ban cika son auren Accra ba, dama zata sami dan
Kano mana ta aura ta dawo gida don ni har yanzu ban
fitar da ran zan kaura gida ba, don tarbiyar Ghana ba ta yi
min ba, ga su da nuna kabilanci.
Da na ji maganar aure tana kara kankama sai na fito
baro-baro na fada musu ra'ayina cewar, bana so a yi
auren nan, na fi so ta auri Bakano. Haba sai Ummana na
Fuse ta hauni da fada, ta zage ni tas har
da koke-koke a waya, wai dama har yanzu ba na
kaunarsu, su dangin mahaifina, na fi son dangin
mahaifiyata duk wahalar nan da ta yi da mu dama
niyyarmu mu gudu mu bar ta wata rana? Kun san tsoho
da rikicewa, yanzu ya lauya maka magna.
Hankalina ya tashi na shiga lallashi ina gyara lafazina.
Da kyar dai ma samu ta huce da ni, don da ta daina zuwa
ta dauki wayar ma idan na bugo sai dai Khausar ta zo.
Daga baya ma na hada musu wayar a gidan (land line)
suka huta zirga-zirgar daukar waya gidan mutane
kullum....
''Ya yi dariya.
Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai, ta ce ''Kai!
Me yasa ba ka so kamwarka ta yi aure alhali ta yi shekara
ashirin koma fiye da haka tunda ba karatu take yi ba ai
gara auren.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya yi dariya, ya ce ''Haka ne,
na gode da wannan tambaya taki. Ina da dalilaina masu
yawa. Kinga macen Ghana dole ta fita nema don idan ma

baki da sana'a ko aiki babu mai auranki. Na tabbata
yaron da yake son Khausar ya zo wajenta ne a dalilin ya
ga tana da sana'a, tana samun kudi, kuma ga ni Yayanta a
turai, ina turo musu da dukiya. Da ace ba ta da komai ba
ma zai zo ba.
Haka idan an yi auren raba dai-dai za a dinga yi ta yi wani
aikin ciyarwar, ya yi wani shima. A lokacin ne ma zata fi
zagewa tana yin rini tun karfi don takai masa wadataccen
kudi.
Na biyu, tarbiyar yaran da zata haifa ba zata yi kyau ba,
saboda al'adunsu kamar babu musulunci a ciki.
Na uku, bana so na tafi na bar ta ita kadai a kasar, na
santa da mako, tuni zata gigice ta rame da koke-koke don
ba ni da ra'ayin sake zama a Accra kuma,
idan bana turai to ina Nigeria, Abuja da Kano.''
Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Ashe ba ka auri *yar
Ghana ba?''
Ya tuntsire da dariya, ya girgiza kai, ya ce, ''Ban auri *yar
Ghana ba. Ina can suka fadamin an saka rana,
don haka suna bukatar kudi masu yawa saboda shagalin
bikin da ake a can ya baci. Bidi'a ce zallah.
Umaimah ta ce, ''Ai daman ko a Nigeria al'adar auren
Hausawa gidan mata suna shan wuya, bayan
kayan daki da gara. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, can
mata ba sa
kai kayan gara, duk miji ne zai yi. A inda suke kashe kudi a
wajen shagalin biki ne sai a fi sati mata suna daukar girki
ba na wasa ba, kuma mai dadi da nama cusu-cusu. A biki
dole ne ka yanka sa ko shanu, rago ko raguna, bayan kaji.
Saboda bikin ne mata suke hada kungiya
(meeting) suna taro duk karshen wata suna tara kudi ana
ajiyewa don idan biki ya kama wata a cikin kudin da aka
tara za a siya mata abubuwa don ta rage nauyi.
Suna fara aiki ranar juma'a da daddare a yi kunshi nan
ma taro ne za a yi mata tuli a kan kujeru a kofar gida,
abinci kala-kala, iyayen amarya dole su sayiwa *yarsu
leshi mai tsadar gaske ta saka a wannan rana. Washe gari
asabar sai a yi Ashadi shima amarya sai ta canza kaya
tsadaddu kamar kala uku ko biyar. Duk sai da na kundige
wadannan kudade na aiko musu suka sha shagalinsu, na
bita da addu'ar fatan fatan alkhairi.
Da na kammala karatun degree dina da kaina na biya na
wuce na yi masters dina. A lokacin na mallaki gidan haya
babba ni kadai, da motar hawa.
Sai dai naje ofishin Uncle Hamza na gaishe shi a can dan
kiyayyara tayi tsamari tsakanina da iyalansa har babban
dansa ya ja min kunne kada in sake zuwa gidansu, idan ya
sake ganina sai ya harbe ni.
Don haka sai na fadawa Uncle Hamza sai dai na dinga
ganinsa a ofis ko kan titi.
To yawanci ma sai ya zo ya same ni a makaranta ko a
gidana mu yo maganar da zamuyi, don so yake idan na

gama karatu ya gutsuro wasu daga cikin dukiyarsa ya
fara aikena Indonesia da Swizerland ina saro masa
shaddoji, leshina na mata da huluna sana'arsa ke nan.
Amma ya lura *ya*yansa da matarsa suna kacaccala
masa dukiya sai ya je kasuwa ya tarar sun je sun karbe
ciniki bada izininsa ba.
Haka kuwa akayi, ina gama karatu ya hadani da wani
Ishaya babban yaronsa dan Nigeria ne shi ma, muka je
kasashe uku ya nunamin wuraren sa suke saro kaya.
MAKWABTAKA 16
Zuwana cikin shagon sai na ruguza cutar da suke yi masa
wajen lissafin bogi, na saka musu ido don ba su isa su yi
min wayo ba, na fi su ilimi. Sabanin Uncle Hamza wanda
bai yi makaranta ba. Bakin jini na yi sosai a wajen
ma'aikatan dan suna ganin ba karamin tauye musu
rayuwa nayi ba, sun daina samun kudin cuta. Da akwai
yadda zasu yi da sun kawar da ni daga doron kasa.
Ganin wannan riba mai yawa da Uncle Hamza ya yi sai ya
sake yarjewa da ni ya fi so na kasance tare da dukiyarsa.
Ya sa na zo muka zauna muka tattauna abin da za a yi
kowa ya ji dadi tsakanin ni da shi. Ya ce, kada na damu da
sai na yi aiki, duk tafiya daya idan aka saro kaya sai a bari
a siyar sannan a raba gida hudu.
Shi kashi biyu, ma'aikatan kashi daya, ni kashi daya. Na yi
murna da jin haka, don kudin da zan dinga samu ya fi
albashina na watanni shida ma.
Na amince na yi godiya muka ci gaba da yin haka.
Sai a lokacin da na karbi ribata ta farko na shirya na taho
Accra ganin gida, shekaruna shidda rabona da gida. Na ga
Ummana Fuse ta kara tsufa yayin da Khausar ta yamutse
saboda wahala, ba ta jin dadin auren,
azzalumin miji ta samu yana yi mata wayo tana nemowa
yana karbewa.
Duk sun yi mamaki da ganina, na girma na yi kyau,
na yi fari kal, ga wata kasumba da na tara. Ina isowa na
tari sabuwar motar da na auno tun ban zoba na turo, a
ita na ke yawo gidan *yan uwa da abokai. Sai kallo na ake
ana sha'awar ni'imar da Allah Ya yi min a rayuwa,
mahassada suna ta
surutai, babu abin da ba su ce ba. Sane nake yi, damfara,
yankan aljihu da dai sauransu haka suke cewa. Ban damu
ba, don ko sauraron su bana yi.
Uncle Hamza ya yi bakin jini a wajen dangi
makusantansa, wadanda suka fini kusanci da shi.
Wai har ya dauko bare ya saka shi a harkar arziki su bai
dauki *ya*yansu ba. Nan fa kowacce ta fara
buga masa waya tana balokoko da magiya ita ma ya turo
ya kai danta England.
Dogon turanci yake musu, bayanai ne kawai da lallashi, a
cikin bayanan nasa kuwa ba zai yiwu ba ne kawai su yi
hakuri.
Kaina da kafata na yi ta taimakon dangi mabukata, suna

ta godiya, masu kushewa suna karba sai dai
idan na tafi su zaga. Na canja fasalin gidan kakata, na
canjawa Kanwata ita ma duk abubuwan da ta ke da
bukata. Na kara mata jari, na kuma bata hakuri gami da
yi mata nasihohi akan ta yi hakuri ta ci gaba da biyayyar
aure. Na kira mijinta muka gaisa, na yi masa kyauta mai
tsoka, sannan na yi masa wa'azi cikin siyasa akan ya sani
mace kiwo ce Allah Ya ba shi, Allah zai tambaye shi yadda
ya yi da ababan kiwon nan da aka ba shi a ranar tsayuwa.
Ya fahimci abin da nake nufi, shi ne ya rage sosai zaluncin
da yake yi mata,
daman dai ba su taba haihuwa ba, saukinta kenan.
Na koma England harka ta sake budewa, na samu Uncle
Hamza yana samu, ina murna yana murna
haka muka yi da bawan Allah nan har tsawon shekaru
biyar. A lokacin ne hassadar iyalansa ta fito baro-baro
*ya*yansa suka zo har ofishina suka cakume ni suka fito
da ni, wai na bar musu dukiyar mahaifinsu ya tsufa yanzu
zasu ci gaba da kula da ita.
Babu yadda zai yi a gabansa na harhada na fice yana
hawaye, ina hawaye. Ya san kawai rusa shi zasu yi, tunda
duk *yan shaye-shaye ne su da uwarsu.
Uncle Hamza ya koma gida ya zauna ya zuba musu ido sai
abin da suka kawo masa yake karba, sai lokacin ya ga illar
auren Ahlul-kitabi, nasara asarar duniya.
Oho, sunyi ta banza don ni duk ribata da ake ba ni suna
boye a banki, kuma na riga na san hanya
nasan mutanen kamfanin su ma sun san ni.
Da jarin na je na kawo kayan na canja gari na bude
shagona a can. A hankali aka gane ni, nima na sami masu
siya. A hankali na sami ma'aikata da teloli.
Amma kafin na fara sai da na je na shawarci Uncle Hamza
ya ce ya ba ni izini na yi, ya yi min fatan alkhairi.
Sai a lokacin na sami nutsuwa nake zuwa Accra akai-kai,
wani zuwa dana yi na iske auren Khausar dai ya ki
yiwuwa, sai da suka rabu ta dawo gida suka zauna da
Ummana Fuse. Na ma fi jin dadi da aka yi haka, ga shi ba
haihuwa suke yi ba, sai rigima kullum, har dukanta yake
yi. Na ba ta shawara ta koma makaranta ta yi yaki da
jahilci, ta kudi ce ana koyar da kowanne darasi da
Turanci tsabarsa kuma ka sami kwali mai daraja kamar
kowacce sakandire. Ta yarda ta shiga ta fara daga aji daya
na sakandire, don ta iya aikin firamare.
Ina can dai a Ingila, na sami labarin daga Khausar cewar
ta yi hutun makaranta, sai na yi musu biza ita da
Ummana Fuse, na turo musu kudi suka sayi tikiti suka zo
suka same ni a Ingila.
Wata guda suka shafe tare da ni ina ta yawatawa da su,
duk wani wajen shakatawa sai da na kaisu.
Kwanakin su biyu a gidan Uncle Hamza, sannan suka
dawo gidana. To a wannan zuwanne abokina Shamsu dan
Nigeria garinsu Minna, Niger State banufe ne. Ya ga

Khausar kanwata ya ce yana sonta, shima tare muka yi
karatu yana aiki a Abuja, amma yana zuwa Ingila akaiakai. Sai na ce, a,a ba zai yuwuba, shi da ya ke saurayi bai
yi auren fari ba, ita kuwa bazawara ce duk da ma ba ta
taba haihuwa ba. Ya girme ni nesa ba kusa ba, ba yaro ba
ne, don alokacin ya yi shekara arba'in. Ita kuwa ba ta
wuce talatin ba.
Ya ce, shi dai yana sonta, zai aureta kuma. Sai na ga ita
ma ta karkata da sonsa. Ban hana ta ba, na fi kowa farin
ciki idan har za a yi auren saboda nasan Shamsu na san
halinsa, yana da kirki ga rikom
addini. Uwa-uba dan Nigeria ne a can zai zauna da ita,
wanda shi ne ra'ayina daman tuntuni.
Da ta ji na ce Nigeria zamu wuce daga nan ni da su
Khausar, sai ya yi murna don kawai za'ayi ta, ta kare,
ma,ana idan ya biyo mu Nigeria sai ya kai ta iyayensa su
ganta a tsayar da maganar aure ko ma a daura kawai
tunda gani ga Ummana Fuse, ga dangin mu a can. Mun
riga shi iso Nigeria san nan ya biyo mu daga baya. A waya
ya sanar da ni ya iso Mina, na ba shi adireshin inda zai
same mu. A gwarzo muka sauka, sun sha mamaki da
ganinmu,
don sun zata ma ba ma raye. Tun sanda Baba Mukhtar ya
kai mu ya dawo babu wanda yasan halin da muke ciki. Sai
muka zama tamkar taurari abin haskawa a kauyen nan.
Aka dinga tururuwar zuwa ganin mu ana kawo mana
abinci kala-kala. Kannena Hassana da Usaina su na fi
damuwa da na gani, Alhamdulillah suna cikin rayuwar
rufin asiri kasancewar mahaifinsu tsayayye ne me neman
na kansa ne. Na siya musu kayan sakawa da kayan
kwalliya kai ka ce lefe ne suma aka hada

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment