Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa. Kin fi ni kyau Antina. Itama
ta fada a lokacin da take kokarin kulle kofar gidanta.
Sai suka yi dariya su dukka suka dinguma zuwa cikin
Lifter dan sauka kasa.
Suka nufi get din fita daga farfajiyar gidan kamar
Umaimah ta tambaye ta Abdul-Sabur sai ta fasa. Su na
fita sai taga Faduwa ta nufi wajen wata tsaleliyar mota
mai kyawun gaske, kalar baka mai farin
gilashi tar! Har shekin kyau take dan sabunta, ko ba'a fada
ba ka san sabuwa ce fil! Daga ledarta.
Cikin sauri Faduwa ta budewa Umaimah gidan baya, ta
shiga tana sanda gami da yiwa mutumin data iske a cikin
motar sallama. Ya amsa mata cike da fara'a gami da
juyowa a tsanake ya dube ta.
Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani sai ta cika da mamaki
tana tunanin inda ya samo aron mota dan bata taba
ganinsa da mota ba.
Faduwa ta bude gidan gaba ta zauna, ya tashi mota suka
hau kan titi suka fara tafiya.
Umaimah ta leka fuskarsa ta ce ''happy birhday''. Ya yi
murmushi ya ce Na gode. Yayin da Faduwa ta hau
magana ba kakkautawa dan ita bata gajiya da
magana.
'Eh ko A,a ko ya ce rufemin baki kin fiye surutu' Abdul ya
fada mata, yayin da Umaimah ta kunshe baki tana dariya
dan ita dariya suke bata kamar wasu *yan tagwaye. Ita
Faduwa ta cika magana, ta

fuskanci tana damun Abdul-Sabur bashi da surutu.
Suka isa wajen da ake ajiye motoci suka sami waje suka
tsaya yayin da suka firfito zuwa cikin KL plaza. Suka nufi
babban wajen cin abinci, babu abinda babu na ci abinci
kasashe kala-kala sai wanda
kake so zaka zaba. Suna zama aka kawo musu takarda
mai rubuce da duk launin abincin da suke sayarwa a
wajen. Sai kowa ya shiga cankar abinda ya fi so ya ci,
shinkafa da salad sai *yar miyar gargajiya kaji kadai
Umaimah ta zaba.
Sai Abdul-Sabur ya ce a'a yayi mata kadan sai ta kara da
wasu abinciccikan dan shi so yake a cika kan teburin
dankar da abinci da abin makulashe.
Ta yi murmushi ''ta ce to a kawo komai ma duk sai a
hadu a ci. Ma'aikata sun ga ciniki sai suka hau rawar jiki
suka garzaya a rude suka hau harhadowa, ma'aikata a
layi suke ta zuwa suna ajiye farantai da kofuna a cike da
kayan alatu. Faduwa ta zabura ta mike zata je kicin.
Abdul-Sabur ya dakatar da ita da sauri.
Ya ce, ''Kin fiye rawar kai, wa kika ga yana shiga kicin,
kowa ba'a zaune yake ba su suke zasu kawo komai ba?
Faduwa ta mike gami da tabe baki ta ce, ''Ka ga tafiyata,
kai ma ka san babu yadda za'ayi in zo waje
in zauna dam sai na motsa.
Umaimah ta tuntsire da dariya ta bi Faduwa da kallo tana
mamakin irin wannan hali nata.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya dubi Umaimah ya ce ''Kin
fara ganin halin makwabciyarki ko? Haka take
bata iya zama shiru.
Umaimah ta sake tuntsirewa da dariya ta gyara zama ta
dube shi ta ce ''Ina son halinta, tana burge ni dan tana da
kirki sosai. Dama ka aure ta, da zan so haka wallahi.
Ya yi firgigit ta dago da sauri ya dube ta cike da dinbun
mamakin yadda aka yi wadannan kalamai suka fito daga
bakinta a daidai wannan lokaci. Sai ya dan yatsune fuska
ya tambaye ta me ta ce, dan yana tunanin kunnuwansa
basu jiyo masa dai-dai ba. Data maimaita sai ya ji abun
da ta fada dazu shi ta maimata.
Ya gyara zama ya ce ''Me yasa kika yi wannan tunanin?
Ta yi murmushi ta ce, ''Kamar yadda na fada dazu tana
da kirki kuma ina tausayinta har yanzu bata
taba yin auren fari ba.
Sai ya sankare a zaune ya kasa amsa mata wannan
tambaya.
Faduwa ce ta taho dauke da babban faranti dauke da
katan kek da wukar yankawa ta zo ta ajiye a gaban AbdulSabur. Ya yi murmushi ya ce, ''Ke ni fa ba wani kek da zan
yanka.
Faduwa ta yi dariya ta ce ''Sai ka yanka yanzu kuwa.
Umaimah ta mike ta nufi kicin yayin da Abdul-Sabur ya
ce, ''Au kema kicin din zaki shigar musu irin na Yayarki?
Umaimah ta yi dariya ta kada kai ta tafi ba tare data ba

shi amsa ba. Sai Faduwa ce ta amsa masa ta ce
''Kada fa ka takurawa kanwata ka bar mu yau mu wataya
muna murna da zagayowar haihuwar dan
uwanmu.
Ya ce ''Allah Ya huci zuciyarku ban hana ku watayawa ba
ai.
Faduwa ta ciro kyamarar daukar hoto ta ce, ''Bari
Umaimah ta zo sai mu fara daukar hoto, kuma ka yanka
kek dinka. Yayana me zai hana mu bi yarinyar nan a
hankali har ta saki jiki damu sannan mu bayyana mata
manufarmu?
Abdul-Sabur ya zabura ya dubi Faduwa a gigice ya
tamabaya, ''Wacce manufa muke da ita a game da ita?
Ta yi dariya ta gyara zama sannan ta kanne ido ta ce ''Ah
maganar ka da ita mana, ni fa da gaske nake na maka
sha'awarta. Kai ka fi cancanta ka auri yarinyar nan dan
ina tausayawa rayuwarta, ta sha wahala gata marainiya.
Na yarda dakai, zaka iya rike ta amana.
Sai ya sulale ya mimmike a zaune akan kujerar da yake
zaune, ya daga kai sama saboda tsabar tashin hankali,
dimuwa, mamaki da firgici. Ya ji ko ya tsansa ba zai iya
dagawa ba saboda sanyin jiki.
Ya hau tambayr kansa da kansa.
Wai shin me yake faruwa da ni ne a yau? Yau me yake
shirin fado min cikin rayuwata ne haka? Me
yasa Umaimah ta yi min sha,awar in auri Faduwa itama
Faduwa ta yi min sha'awar ta yi min sha'awar in auri
Umaimah?
Shin mafarki nake yi ne ko idanuwana biyu? Anya kuwa
ba hade min kai suka yi ba suke shirin su waina ni ba?
Kai haba ya ma za'ayi a ce sun hada baki, yaushe suka san
juna ma? Ya zanyi kuma menene ya kamata in yi?
KARKSHEN LITTAFI NA 2..
_________(3)_____
Umaimah ta fito dauke da *yan gwangwanayen fulawar
roba a hannayenta ta zo ta jera akan tebur,
yadda teburin zai sake kayatuwa. Faduwa ta shiga
tarwatun kiran jama'ar da suke zazzaune suna cin
abinci, wai su zo su taya su yanka kek din birhday.
Masu hali irin nata na rawar kai da son wasa suka ta so
yuya guda har da wasu daga cikin ma'aikata,
ana tafi ana fadin. ''Happy birhday Abdul'' kamar yadda
suka ji Faduwa tana fada suma ita suke ta fada.
Takaici ya hana Abdul-Sabur sakat ya ji dama bai zo
wajen nan ba, a dole aka kewaye shi ana kirga daya har
zuwa goma sannan ya yanka kek, aka hau tafawa kamar
wani yaro karami. Sai Faduwa ta shiga daddatsa kek kowa
yana caka da colali yana ci. Hotuna iri-iri Faduwa ta dinga
yiwa Abdul-Sabur da Umaimah a kusa da shi, babu
abinda Umaimah take sai murmushi dan tabbas ta shaki
farin ciki a wannan fita. Bayan nan sai Faduwa ta yiwa
jama'a godiya game da yi musu tayin su zauna su ci

abinci tare da su, da yake kusan kowa an riga an kawo
masa nasa abincin kan teburinsa sai suka ki zama suka
koma in da suka fito suka zauna suka ci gaba da cin
abincinsu.
Suma su Faduwa suka zauna suka fara cin jifgin abincin
da yake jere akan teburin gabansu, daga gani abincin nan
ya fi karfin hanjinsu saboda yawa gashi kaloli dabandaban.
Duk wanda ya shigo kafin ya zauna sai Faduwa ta kirashi
tebur dinsu, ta yi masa ta yi in akwai abinda ya ke so a
ciki ya zauna ya ci ba sai ya saya ba sun saya da yawa
saboda bikin birhday da suke yi.
Abinci kadan Abdul-Sabur ya ci sai ya daina ci yana daga
zaune ya dubi Faduwa, ya juya ya dubi
Umaimah, sai ya yi sauri ya sunkuyar da kai, yayin da
kwalla ta cika masa ido yana tausayin kansu su dukka
ukun. Kasancewarsu gaba dayansu marayu ne, kuma baki
a kasar da babu danginsu. Haka su
dukka ukun bagware ne, ba su da mai kula da su,
kowannensu shi kadai a cikin gidansa kamar maye. Ya fi
tausayin matan ma akan kansa, rayuwar mace a
gurgunce ta ke muddin ta kai munzalin aure, kuma ba ta
yi ba.
Sai zuciyarsa ta shiga saka masa hanyoyi daban-daban da
zai bi don magance wadannan matsalolin
da suka addabe su.
Faduwa ta dubi Umaimah ita ma ta dubeta, gaba daya
suka tsurawa Abdul-Sabur idanu, tabbas sun ga ya sauya
yanayinsa, ya shiga halin tunani a dai-dai lokacin da suke
hayaniyarsu su kadai. Babu
wacce ta tambaye shi me yasa saboda kowacce ta san
dalilinsa na yin haka, sai dai dalilin kowacce daban, ya sha
ban-bam da na dayar.
Faduwa tasan tayi masa maganar ya auri Umaimah ta san
maganar ce ta ke yi masa zillo a zuciyarsa, ita ma
Umaimah ta san maganar data yi masa kan ya auri
Faduwa ita ce ta toshe masa a kahon zuci. Abin da ba su
sani ba shi ne, farin ciki maganarsu ta saka masa a rai, ko
kuwa damuwa, ya amince ko kuwa bai amince ba?
Shawarar da yayanke shine ya auri Faduwa Umaima
kuma ya aurawa Dan Aunty..lolx..
Ehemm. Ko ya kukagani en uwa.?
MAKWABTAKA 26
Kallon da suke yi masa shiyasa ya hanzarta farfadowa
daga duniyar tunani ya karkato hankalinsa gare su, ya
biye musu aka yi ta hayaniya da ciye-ciye. Karfe tara na
dare suka baro 'KL plaza, kai tsaye suka wuce da motar
wajen ajiye motocin da yake cikin gidansu. Yayin da suka
firfito kowannensu
cikin fara'a suke yiwa juna sallama da fatan Allah Ya tashe
su lafiya.
Faduwa da Umaimah suka nufi bangarensu, yayin da

Abdul-Sabur ya nufi na sa bangaren. A cikin lift Faduwa
da Umaimah hirarsu kawai suke yi cikin harshensu, wato
Hausa. Wasa da dariya gami da
dimbin nishadi ne ya tabbata a zukatansu.
Kaunar juna, gami da rashin jin dadin rabuwa suke ji a
cikin kalbinsu.
Faduwa ce ta ba Umaimah hannu suka gaisa gami da
rungume ta, ta sumbaci gefen kumatunta irin gaisuwarsu
ta Larabawa, a lokacin da aka zo hawa na goma sha
takwas wato gidanta. Lokacin
rabuwarsu ta zo kenan amma fa a yau. Kalmar karshe da
ta fadawa Umaimah ita ce 'Bissalam. Ta fice daga cikin lift
yayin da kofar lift ta rufe kanta,
umaimah da sauran jama'a suka karayin sama, a hawa na
goma sha tara Umaimah ta fice ta nufi gidanta fuskarta
cike da annuri, har waka take rerawa a hankali cikin
harshenta na fulatanci.
Wakar nan da suke yi a dandali ita da kawarta Matawata,
wacce suke kiran junansu kawata,
masoyiyata kuma makwabciyata.
Abun tambaya a nan shine Faduwa ce ta maye gurbin
Matawata, ko kuwa Abdul-Sabur ne?
Asuba ta gari Fadu-maimah-sabur!!!
Shigar kowannensu gida ba tare da bata lokaci ba ya yi
wanka da kuma sallar isha'i, bayan saka rigunan
baccinsu, sai suka haye gado yayin da kowannensu ya
shiga tunanin dan uwansa suna masu tunano abubuwan
da suka faru da su a
dazun nan. Haduwarsu ta zame musu tamkar a mafarki,
suna mamakin yadda haka ta kasance. Matsananciyar
shakuwa da kaunar juna nan da nan ta wanzu a ransu.
Bacci mai dadi ya kwashe su a lokaci daya, saboda sun
gaji ya hadu da mafarkai kusan iri daya, abubuwan da
suka faru dazun suke
maimaita gani a mafarki.
Umaimah ta yi firgigit ta bude ido tana mai murmushi a
fuskarta sai ta ga ashe fa a mafarki ne,
Abdul-Sabur ta yi mafarki yana yi mata magana.
Ya ce da ita, ''Umaimah kinga abin da nake fada miki ko?
Annabi (S.A.W) ya yi gaskiya da ya ce, ''dukkan musulmi
dan uwan musulmi ne''
Ta yi firgigit ta tashi zaune ta dafe kirji gami da jinjina kai
tana mai gasgata wannan maganar da ta ji a mafarki. Sai
ta yi cimak ta sauko daga kan gado ta je jikin tagar
dakinta ta daga labule ta leka gidan
Abdul-Sabur. A tsaye ta gan shi a jikin tagarsa aka yi katari
yana
kallonta, sai ta sake firgita ta saki labulen tagar da sauri
tana ambaton.
''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Anya wannan mutum ne?
Ta dade a tsaye a tsakar daki ta rike baki tana mamaki,

can ta suri filo ta fito falo kan doguwar kujera ta zauna,
bacci ya gagare ta, don haka ta tashi ta shiga kicin ta
tsaya, ta dade a tsaye sannan ta tuna kishirwa ta ke ji,
kasancewar an ci maiko dazu. Ta bude firij ta dauko
robar ruwa ta tsiyaya a
kofi ta kurba. Sai ta jiyo magana a waje kan baranda
kamar muryar Abdul-Sabur. Cikin sanda ta bude kofar da
zata kai barandar waje, tana budewa sai ga Abdul-Sabur
muraran shi ma atsaye akan barandarsa ta kicin yana mai
dubanta yana murmushi. Ya na magana amma a waya
cikin wani
yare wanda ba nata ba. Dan haka ba ta gane me yake
cewa ba, sai ta yi sauri ta tura kofar ta rufe ta gaggauta
kashe fitulun gidan gaba daya tana mai tottofa addo'o'i a
kowacce kusurwa ta cikin gidan.
Ta shige daki ta haye kan gado can cikin lungu ta
kudundune a cikin bargo tana ta makyarkyata saboda
tsoron daya kamata. Tana tunanin anya kuwa AbdulSabur mutum ne, ko kuwa aljani ne yake shigarsa don ya
tsorata ta?
Da kyar ta yi bacci bayan da ta daina jiyo maganarsa da
kuma motsin shige da fitar da yake yi a cikin gidansa. Ko
bayan da ta yi baccin ma mafarkinsa ta ci gaba da yi har
yanzu dai nasihohin yake yi mata a mafarki,
wannan karon kuma babin mace ta yiwa mijinta biyayya
yake bayani.
TIkon Allah, wannan shi ake kira boyayyen al'amari,
ko mene ne ma'anar hakan? Allah Shi Ya barwa kanSa
sani.
Asuba ta gari Fadumaimasabur.
***************
Dif Umaimah ta bace kwana biyar ma ba su sake ganinta
ba, haka ba sa jin motsinta a gidan, a makaranta ta ke yini
idan ta taso sai ta wuce Bukit bing tang ta ci abinci a
restaurant bayan ta zazzagaya malls sannan ta dawo gida
da daddare ta kwanta, ko fitila ba ta kunnawa balle a san
tana ciki. Amma koda yaushe MAKWABTAnta suna cikin
ranta, kuma ba ta da mummunan zato a kansu,
saboda ta saba da zaman kadaici, shi yasa ba ta damu ta
neme su ba.
Ranar juma'a bayan masallci tana cikin tunaninsu,
sai kuwa ta ji bugun kofa gami da jiyo muryoyinsu, babu
tantama tasan su ne sai ta rasa dalilin jin farin ciki a cikin
zuciyarta. Da sauri ta bude musu kofa bayan ta zumbula
dogon hijab.
Yadda ta ke murna da ganinsu har sun fita murna,
saboda dariyar da ta ga suna bangalawa. Ta yi musu iso
zuwa cikin falonta suka shigo suka zauna akan doguwar
kujera su biyu a jere. Ta zauna a kujerar da ta ke
fuskantarsu cike da ladabi ta duka ta gaishe su, sannan ta
koma ta gyara zama ta dube
su ta yi dariya, ta furta kalmar da gaba dayansu suka

dimauce, aka hau kallon-kallo.
Cewa ta yi, ''Kun ba ni sha'awa da na ganku a tare, Allah
Ya tabbatar da alkhairi, mafarkina ya zamo gaskiya.
Musamman Faduwa ta fi Abdul-Sabur rashin fahimtar
abin da Umaimah ta ke nufi, ga rashin wadatacciyar
Hausa, ga rashin sanin ainihin kan maganar, saboda ba ta
san maganar da Umaimah ta fadawa Abdul-Sabur ba a
kanta. Ita ma kuma yanzun nan ta sake furtawa AbdulSabur sabuwar maganarsa da Umaimah shi ne ma dalilin
da yasa ta taso shi a gaba don su zo su ganta duk da ita
ma
tana tsoron furatawa Umaimah wannan batu. Tana
gudun kada ta ki amincewa kuma ta shiga gudunsu, don
tasan halinta. Duk da Abdul-Sabur bai bata goyon baya ba
akan aniyarta ta hada shi da soyayya da Umaimah ba,
har ya kan yi fushin gan-gan idan tayi masa maganar,
amma ta san nokewa yake yana so yana kaiwa kasuwa.
Shi ma kuma ya kasa fada mata abin da yake zuciyar
Umaimah na yunkurin hada aure da ta ke yi.
Faduwa ce ta takurawa Umaimah da tambayoyi akan ta yi
mata FASHIN-BAKI akan maganar da ta yi dazun. Hausa
cikin Hausa Umaimah ta sake rikita mata kwakwalwa, sai
Faduwa ta dawo turanci dan
ta ji Hausar ta gagare ta, duk da haka Umaimah ta goce
ba ta bari ta fahimci abin da ta ke nufi ba.
Abdul-Sabur ya gane, dariya kawai yake kyakyata musu
daga karshe dai ya kawar da hirar ya shigo musu da wata
hirar wacce ta shafi kowannensu,
wato hirar makaranta da shirin fara jarabawa.
Umaimah ta mike cikin nutsuwa ta ke tafiya ta nufi kicin
dinta, ba jimawa ta fito hannayenta dauke da kwalin
lemo da kuma kofuna guda uku, ta kawo tsakiyar kujeru
(center table) ta shiga tsaiyaya
musu, ta durkusa ta mikawa kowannensu sannan ta sake
tashi ta shiga kicin.
Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta yi murmushi, magana ta
ke yi masa cikin rada.
Ta ce ''Ka ga abin da nake fada maka ko? Yarinyar nan ta
dace da rayuwarka, nutsattsiya ce ga ladabi.
Sai ya harareta ta kawai ya sunkuyar da kai, sai ta
kyalkyale da dariya.
Umaimah ce ta fito dauke da farantin tangaran da 'cake'
da biskit a cikinsa ta kawo ta ajiye a gabansu,
ta koma ta zauna suka ci gaba da hira da kallon talabijin.
Faduwa ta kurbi lemo, ta gyara zama ta ce,
''Umaimah ba ruwanki da neman MAKWABTANki ko za ki
shekara ba ki gansu ba ko?
Umaimah ta yi sauri ta dubi Abdul-Sabur, yayin da ya yi
saurin kawar da kansa gefe tamkar bai san abin da suke
cewa ba. Kunyarsa ta ke ji saboda nasihohin da ya dade
yana yi mata akan ta sauya wannan mugun halin na kin
mutane. Ta yi saurin sauya hira, amma sai Faduwa ta sake

jeho mata wata tambayar.
Ta ce, ''Ba kya neman mutane a waya ko ba ki zo inda
muke ba, sai mu dinga gaisawa a waya, koda
yake ko lambobinmu ma ba ki karba ba.
Wannan karon ma Umaimah Abdul-Sabur ta sake kallo,
yayin da yaki yarda su hada idanu, ya ci gaba da matsa
remote yana sauya tasha a talabijin.
Faduwa ta ce, ''Ba ni lambarki, ga tawa.
Ta dauko wayarta tana jiran Umaimah ta karanto mata
lambobin. Takaicin tonar asirin da Faduwa ke kokarin yi
mata ta toshe zuciyarta, ba ta so aka yi
wannan hira agaban Abdul-Sabur ba, saboda kada ya zaci
ba ta sauya ra'ayinta ba har yanzu.
Cikin sanyin murya ta ke ba wa Faduwa amsa ''Ai ba ni da
waya.
Don firgita Faduwa har da dafe kirji, ta dauki dogon salati
kai ka ce mutuwa aka yi.
Ta ce ''Kamar ya ya baki da waya? Ta bata ne ko ba ki taba
yin waya ba daman can a rayuwarki?
Umaimah ta yi dan murmushin karfin hali, ta ce ''Ban
taba yin waya ba daman can a rayuwata.
Kallo daya Abdul-Sabur ya yi musu ya juyar da kansa ya
ci gaba da kallon talabijin.
Faduwa ta zungure shi, ta ce ''Aboki, ka ji ikon Allah, wai
Umaimah ba ta da waya, a rayuwarta ma bata yi waya ba,
ko ta zaci a ruga take har yanzu?
Su dukka ukun suka kyalkyale da dariya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Matsalata da ke ke nan, kin cika
kwakwazo, meye abun mamaki don bata da waya?
Kowa fa da ra'ayinsa.
Faduwa ta ce, ''Da mamaki mana yadda duniyar nan ta ci
gaba, almajirai a cikin kauye ma rike waya suke yi balle
ita da ta ke birni. Birnin ma irin Malaysia, a Malaysia ma a
babban birnin Kaula
Lumfur, kuma a jami'a. Haba Umaimah me yasa haka, ya
ya kike da *yan gidanku, samarinki, da kawayenki?
Abdul-Sabur ya tsurawa Umaimah ido yana jira ya ji
amsar da zata bayar, sai ta ki magama ta sunkuyar da
kanta kasa, murmushi kadai ta ke yi.
Faduwa dai ba ta daina mamaki ba, haka ba ta daina yi
mata tsiya ba, har sai da Abdul-Sabur ya mike tsaye ya ce
zai tafi masallaci, ya ji ana kiran sallar la'asar.
Faduwa ta tashi ta bi shi suka fice.
Umaimah ta raka su har kofar bakin lift suka yiwa juna
godiya, sallama, gami da fatan alkhairi suka
shige lift suka tafi, ita kuma ta p dawo gida tana maijin
sanyi a ranta, kasancewar a halin yanzu tana samun baki
a gidanta, ta sami wadanda suka san da ita suka damu da
lafiyarta, wadanda zata yi hira da su har su saka ta dariya.
Bayan kwanaki biyu da zuwan su Faduwa gidanta,
ranar lahadi da yamma Umaimah ta shirya ta rufo
gidanta ta shiga gidan Faduwa don ta gaishe ta. Faduwa ta

yi matukar mamaki gami da farin cikin ganinta. Ta mike
da sauri ta rungume Umaimah ta kamo hannunta ta
zaunar da ita akan kujera. Sai a
lokacin Umaimah ta dubi mata biyu da suke zaune a kan
sauran kujerun. Ashe baki gare ta, daya
inyamura, daya *yar Malaysia. Uhum! Faduwa mai
mutane, kawayenta kala-kala daga kowacce kusurwa ta
duniya tana da kawaye mata da maza.
Umaimah ta daga musu hannu ta gaishe su, gaisuwar dai
ta hello da hi ce, don ba ta ga alamar musulunci a tattare
da su balle ta yi musu sallama. Suka amsa mata cikin
fara'a su ma yayin da Faduwa ta gabatarwa kawayenta
Umaimah, sannan ta gabatar da su ga Umaimah. Sun
jima suna hira
bayan sun ci, sun sha, Umaimah ta yi musu sallama
kasancewar magruba ta kusa. Su ma lambar wayar
Umaimah suke tambaya. Faduwa ta yi sauri ta ce, ''Ina da
ita, zan baku anjima. Saboda ta ga Umaimah ta rasa
amsar da zata ba su.
Bayan tafiyar Umaimah sun dade suna yiwa Faduwa
zancenta cewar, tana da kirki ga hankali. Sannan ta ba su
sha'awa yarinya kyakkyawar gaske kamar ba *yar Africa
ba.
Faduwa ta yi musu alkawarin zata kawo musu Umaimah
har gidajensu
wata rana.
Misalin karfe goma na safiyar wata litinin Umaimah ta
bude barandar kiicin dinta don shanya hankicin da ta
gama goge-gogen gidanta. A tsaye ta iske Abdul-Sabur shi
ma akan barandarsa yana shan iska, sun kwana biyu ba
su hadu ba ko akan hanya. Ta dan razana da ganinsa, ta yi
kamar zata koma ciki, sai ta daure, ta dake, kasancewar ta
daure kanta da dankwali duk da riga da wandon
bacci ne a jikinta, amma dogaye ne ba kanana ba. Suna
hada ido sai suka yiwa juna murmushi, ta duka ta gaishe
shi.
''Umaimah daman kina nan?
Kwana biyu kin buya.
Abdul ya tambaye ta.
Cikin kadabi ta ba shi amsa. ''Ina nan, lafiya kalau.
Ta ci gaba da shanya, ya gyara tsayuwa ya ce, ''Ba a
ganinki sosai, ko makaranta ce? Koda yake masu
ganinki suna ganinki, Faduwa ta ce kusan kullum sai kun
hadu, idan ba ta je gidanki ba, ke kina zuwa. Har ma kun
je unguwa jiya tare.
Umaimah ta yi murmushi, ta gyada kai ta ce, ''Haka ne. Ya
gyada kai, ya ce ''Yana da kyau, kuma na ji dadi
da samun wannan canjin. Ki ci gaba da yin hakan,
saboda zaman kadaici ba dadi.
Ta yi dariya ta ce, ''Insha Allah zan ci gaba da yin haka.
Ya ce, ''To na gode idan ba zaki damu ba da yamma mu
hadu a gidan Faduwa ina son magana da ke.

Sai ta ji zuciyarta ta harba nan da nan ta ji hankalinta ya
tashi, ta shiga mamakin dalilin neman ta da yake yi.
Mamaki cike a fuskarta a bayyane ta dube shi cikin
sanyayyiyar murya ta tambaye shi, ''Lafiya? Ya yi
murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Kar ki damu, ba wata
matsala ba ce face alkhairi.
Ta gyada kai a sanyaye ta ce, ''Allah Ya kaimu yammar.
Ta juta ta shiga gida.
Ta dade a zaune akan kujera tana sake-sake a zuciyarta
tana ayyano mata abubuwa daban-daban da ya sa yake
nemanta anjima a gidan
Faduwa. Ko dai maganar nan da ta yi masa za'a tayar,
wacce ta yi masa na ya auri Faduwa, yake so
ta maimata a gaban Faduwa? Idan dai haka ne ai ta
kwana gidan sauki, sai ta maimaita ba wani abu ba ne,
alkhairi ta ke so ta hada.
Daga karshe ta mike cimak ta je ta yi wanka, ta shirya ta
fito zuwa makaranta tana da darasi da
karfe goma sha biyu. Dai-dai get din gidansu ta ci karo da
Abdul-Sabur da Faduwa a cikin tsaleliyar
motarsa za su fita da alama makaranta za su tafi. Sai da
suka rage gilashin motar ta hango su,
sannan ta gane su ne, suka yi mata izini ta shigo su tafi.
Zata yi gardama Abdul ya ce ta shigo su tafi ba ya bukatar
wani bayaninta. Ta bude gidan baya ta zauna, ya ja mota
suka fara tafiya.
MAKWABTAKA 27
Daga dukkan alamu dalibai da malamai a yau sun cika da
mamaki da suka ga Umaimah tana magana
da wasu bil'adama har ma da shiga motarsu. Sai kowa ya
yi ta kallon Abdul-Sabur da Faduwa suna ta yi musu
jinjina bisa namijin kokarin da suka yi har Umaimah ta
aminta da su. Musamman kawayenta *yan Nigeria kuma
*yan garinsu suka
yi tsuru-tsuru suna kallonta suna kallon mutanen da suke
cikin mota, da alama dai sun san ba *yan uwanta ba ne,
amma kuma ga shi ta saba da su. Abdul-Sabur ya dubi
Umaimah, ya ce, ''Karfe nawa za ki tashi in zo in dauke ki?
Ta girgiza kai, ta ce, ''Kar ka damu, zan dawo da kaina, ai
ba dadewa zan yi ba yau.
Faduwa ta ce, ''To mu zauna ki shiga ki yi lecture ki fito
mu ma sai ki raka mu tamu makarantar da yamma sai
mu dawo tare.
Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce, ''Haba Aunty
Faduwa, ya za'a yi ku zauna ku jira ni kamar wata Sarki?
Ku je makarantarku. Kada ku jira ni, ni ai ba ni da nisa, na
gode Allah Ya saka muku da alkhairi.
Faduwa da Abdul-Sabur ma suka yi mata fatan alkhairi,
ya ja motarsa suka tafi, yayin da Umaimah ta juya ta dubi
dumbin idanuwan da suke kallonta.
Ta shiga karanto kula'uzai a zuciyarta don kada baki ya
kamata. Tabbas an saka mata ido a makarantar nan

hakan ya samo asali ne ta sanadiyyar rashin kula su da ta
ke yi, kuma jama'a da dama suna son shiga harkarta.
*************************
Umaimah ba ta baro gidanta ba sai bayan da ta idar da
sallar magruba. Ta ci sa'a kuwa tana shigowa
gidan Faduwa ko zama ba ta yi ba, Abdul-Sabur ma ya
shigo, Umaimah ta dube su ta yi murmushi. Ta ce, ''Ku yi
min afuwa na makara ban zo da yamma ba kamar yadda
na yi alkawarin zan zo, na yi bacci
ne ban tashi ba sai bayan la'asar sosai, shine ya sa na bari
sai da na yi sallar magruba sannan na shigo.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce ''Ba damuwa,
tunda yamma na zo muke ta jiranki ga shi na samu na je
masallaci na yi sallah nima,

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment