Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan ka karfafa
masa gwiwa ka da ya ga idon Dagaci ya ji nauyinsa ya amsa musu abinda suke so ni kuma in cutu.
Baffa ya dakatar da ita da hannu ya ce "Yi shiru shiga gida ki bar ni da su ni na san amsar da zan
basu.
Ya tashi da sauri ya fice Sabitu ma ya bi shi a baya, sai ta daskare a zaune tana kallon ikon Allah,
mulkin mallaka kiri-kiri ake yi musu tuntuni ashe rashin ilim ya hana su ganewa. Ta dade a zaune
sannan ta tashi ta shiga gida, ta iske *ya*yanta a tsugune a tsakar gida sunki yarda su shiga daki. Su
Nene da sauran baki sun yi fillancin duniyarnan akan su zo su zauna suka ki.
Umaimah tana shigowa suka taso da gudu suka runguma ta, ta ja hannayensu suka shiga daki.
Cikin lungu ta shige ta dinga shirgar kuka amma a wayence bata son yaran su gane. Allah Yayi dare
gari ya waye ta dawo kasarta har matsaloli sun sake dawo mata.
Idan ta dubi yaran sai su bata tausayi su ne kadai suka saka take ragawa Abdul-Basi tana gudun
kada ayi baram-baram ya hana ta ganin yaran ma gaba daya, dan kadan daga cikin aikinsa.
A haka ta daure take dan cin abincin nan dakyar take hadiyewa, saboda babu kamshin curry, bana
spies, sai karni take ji a hancinta yayin da harshenta ya gauraye da zakin kafi zabuwa babu magi,
nan da nan ta ji zuciyarta ta fara tashi kamar zata yi amai.
Su kuwa su Babangida da yake yara ne sai suka ji dadin abinci miya mai zaki cakwai.
Duk da gajiya, barci da ciwon kan da yake damunta bata so ta fara bude akwatinan tsaraba yanzu ba
amma ya zama dole ta bude taci biskit da butter tunda ta kasa cin abinci kuma ta dauko tsarabar da
ta siyowa yaranta su tafi da ita taga alama yau ita da Abdul-Basi zasu rabu baram-baram, idan aka
yi
haka kuwa ba zai sake kawo mata su ba.
Jaka guda ta cika musu da kayan sakawa, takalma da alewowi da a wata shida ma ba baza su iya
shanyewa ba duk shan da zasu yi, bayan wacce suka sha suka gaji a gidan. Duk wanda zata tafi sai
Umaimah ta zabo abin da ya dace da ita ta bata.
Tabbas haka ne duk abinda ta siyo, anan suna ganin darajarsa, tunda ba su taba ganin irinsa ba sai
taga sun barke da murna da zarar ta mika musu.
Godiya da shi albarka abun baya kirguwa suke tayi mata.
Baffa kuwa ana can ana ta fafatawa a fadar Dagaci shi da Abdul-Basi. Yayin da Abdul-Basi ya cika
da mamaki a lokacin da yaga Baffa ya fara yi masa musu, alhali a da duk abin daya fada sai ya
zauna yayi daidai.

Baffa ya murje ido bai ji nauyin Dagaci ba haka bai ji shakkar Abdul-Basi ba ya ce ba shi da
magana da Abdul-Basi sai dai da manyansa.
Nan fa gizo yake saka dan mahaifin Abdul-Basi ba zai zo Dugge ba da niyyar biko saboda sun boye
masa a lokacin da suka kori Umaimah san sun san idan yaji zai ce a dawo da ita ko ya hana auran
Zulayha. Sai da ta sami fiye da shekara sannan ya ji a gari cewar Umaimah basa tare da Abdul-Basi.
Dan haka har yau ya ki maganar zuwa bikonta,
yayi fushi ainun, don sun zubar masa da mutunci. Abdul-Basi ya san ba zai iya tarar Alhaji yayi
masa maganar bikon Umaimah ba dan haka sai ya nemi su sulhunta a tsakaninsu shi da Baffa,
amma Baffa ya kekasa kasa ya ce sai Alhaji ya zo, ko bayan ya zo din ma sai an kira Umaimahh ta
fadi ra'ayinta.
Tabbas Baffa shi zai kawowa Abdul-Basi cikas, dan haka sai hankalinsa yayi matukar tashi ya
fuskanci ba tunanin Baffa ba ne wannan mai ilimi ce ta karanta masa abunda xai ce.
Dagaci yayi amanna da bayanan Baffa cewar ya turo magabatansa. A haka aka tashi daga taron.
Cikin fushi Abdul-Basi ya shiga mota ya zauna ya aika cikin gidan ya ce Babangida da Bilal su fito
su tafi. Sai suka ki fitowa wai su sai tare da Umaimah.
Ta ji hankalinta ya tashi ta shiga lallashinsu tana yi musu dubara iri-iri tace itama gobe zata hado
kayanta ta biyo su. Suka ki amincewa, sai da karfin tsiya ta ce Sabitu ya dauke su saboda sai danna
horn din mota Abdul-Basi yake yi a fusace.
Suna kuka kamar ransu zai fita aka banbare su daga jikinta suna kiranta suna cewa "Mu a wajen
Aunty Umaimah zamu zauna. ''Su da jakar tsarabarsu a ka jifge a baya.
Yayin da Abdul-Basi ya daka musu tsawa guda daya ta wadatar suka yi kulas a lungu, amma basu
fasa kukan zuci ba. Ya ja mota ya tafi a fusace ko sallama bai yiwa Baffa ba.
Umaimah tana zaune a cikin dakinta ko rakiya kasa yi musu tayi, ta rike kai ta rushe da kuka na
takaicin rabuwa da yaranta, lallai tana cikin wani hali idan ta kwallafa son yaran nan saboda ita ta
yankewa kanta ba zata sake zama da Abdul-Basi ba shi ma kuma ba zai bata yaranta ba.
Magruba ta yi, da ta kewaya bandaki zata kama ruwa sai ta kasa tsugunawa saboda cakwalin kasa
mrtik da bawali babu siminti, *yar zana ce aka kewaye. To wannan idan ta tashi yin wanka ya za
ayi kenan?
''mishkila" inji Larabawa
Haka da daddare ta ji sauro yana gantsara mata cizo sai hankalinta ya tashi. Ta kuduri niyyar tafiya
Dukku da sassafe ta siyo shaltos da gidan sauro, ruwan swan, kayan shayi, risho food flask da duk
kayan abinci. Sai dai jama'ar Ruga su zage ta amma ba zata zauna yunwa da wahala su kashe ta ba
alhali tana dashi.
Haka kuwa akayi washe gari da safe ita da Sabitu suka tafi birni suka yi siyayya, kaya cikin bayan
mota 'a kori-kura aka zo aka jifge himilin kaya a dakin Umaimah. Ai kuwa tasha zimde da yafice a
wajen su Nene kan ka ce kwabo magana ta yadu a gari Umaimah ta siyo kayan abinci irin na turawa
ba
zata iya cin tuwo ba.
Haka tasa aka yi mata siminti a bandaki daidai inda zata dinga hawa tana yin wanka. Tabbas
gayunta ya tabbata, dan ma tana daurewa tana hakura da wasu abubuwan da kada maganar ta yi
yawa. Da generator zata siyo ta dauko me alsawa ya hada mata ta dinga yini tana kwana a cikin
fanka, dole ta hakura da wutar lantarki.
A daddafe ta shafe wata guda cur sai ta ce da Baffa zata je Gombe ta ji yadda ake ciki da zancen
tafiyarsu bautar kasa. Sabitu ne ya rakata da kayansu kala biyu suka zuba a cikin jaka.
Tana shiga birni Gombe ta sayi layi ta kunna wayarta, Hanif ta fara kira, ya ji dadi dajin wayarta
dan har ada ya fara tunanin muddin bata zo a cikin satin nan ba sai ya je Dugge da kansa ya sanar
mata maganar tafiyarsu bautar har sun yi taro sau biyu a gidan gwamnati, saura sati biyu su tafi
Abuja.
akwai Post anjima in kuna so.?MAKWABTAKA 45
Da kansa ya sanar mata maganar tafiyarsu bautar har ma sun yi taro sau biyu a gidan gwamnati,
saura sati biyu su tafi Abuja

Tana gama waya da Hanif sai ta kira kawarta Aisha Bingyal, da farko Aisha bata gane mai magana
ba kasancewar sabon layi ne yanzun nan Umaimah ta saya sai daga baya ta shaida muryar,
Umaimah Bello ce aminiyarta.
"Gani a garinku, kwatanta min gidanku" Umaimah ta fada cike da fara'a. Farin ciki ya rufe Aisha ta
ce "Fada min inda kike bari na zo kawai in dauke ki. Ko da mota kika zo?
Umaimah ta ce "Da motar haya muka zo ni da kanina Sabitu gamu nan a bakin tashar Dukku, ki zo
ki dauke mu.
"Gani nan zuwa yanzu, daman a shirye nake tsaf. Inji Aisha.
Su Umaimah suna ta tsayuwar jiran Aisha a bakin titi, sun dade suna jira kasancewar akwai tafiya
daga unguwarsu pantami zuwa tashar Dukku.
Mota kirar discoussion continious ce baka me bakin gilashi ta zo ta tsaya a gaban su Umaimah. Sai
suka tsurawa motar ido dan basa ganin cikin motar saboda duhun gilashin bata zaci Aisha ce a cikin
motar ba har sai da ta sauke gilashin motar ta leko da kai.
Ta ce "Umaimah Bello, ku shigo mu tafi Umaimah ta yi mamaki da ganin Aisha cikin wannan
daula, bata zaci *yar gidan masu kudi ba ce haka.
Umaimah ta shiga gaba Sabitu ya zauna a baya suka tafi, bayan sun gama gaggaisawa sannan hira ta
rincabe.
Aisha ta gyara farin gilashin da yake fuskarta ta dubi Umaimah tayi murmushi. Ta ce "Kin gudu
garinku ba waya kin bar ni a nan jama'arki sun hana ni sakat wai sai na kai su gidanku.
Cike da rashin fahimta Umaimah ta tambaya "Su waye kuma jama'ata?
Aisha ta ce "Na san baki san su ba amma dai idan nayi miki bayani zaki gane su, wallahi jama'a da
yawa da suka je graduation dinmu Malaysia suka gan ki suka ce suna sonki. Yanzu dai su biyu ne
suka zo suka same ni daban-daban kowanne yana son in bashi adireshi da lambar wayarki. Na ce
musu ban sani ba amma su zo ranar da zamu tafi Abuja karbo 'call up letter' mu ta bautar kasa za su
ganki.
Umaimah ta yi ajiyar zuciya jikinta a sanyaye ta juya ta dubi kaninta ta ce "Malam Sabitu ka ji wata
sabuwa kuma.
Yayi dariya ya ce "Alhamdulillah, haka ake so Allah Ya zabar miki duk wanda ya fi alkhairi a
cikinsu.
Umaimah ta dafe kai ta ce "Ai zai yi wuya in so ko dayan ne ma daga cikinsu saboda ni tuni na
dankawa Abdul-Sabur zuciyata.
Sabitu da Aisha suka dau salati a lokaci daya dan mamaki kasancewar su dukka suna da labarin
Abdul-Sabur, da yadda suka rabu.
Aisha ta fada cike da gatsali ta ce "Au anga Abdul-Sabur din ne daga in da ya bace din?
Umaimah ta harare ta ta ce "Daman bata yayi?
Aisha ta yi dariya ta ce "Kin cika abun haushi ana miki maganar mutanen da suke sonki a zahiri
kina maganar mutumin da ya tafi zai auri wacce yake so.
Umaimah, wadannan mutane manyan mutane ne, kusoshin gwamnati ne wadanda ake damawa da
su a kasa, masu kudi, masu fada aji, kuma ba yara ba ne.
Idan kika gansu za ki shaida su
daya ma kawun Khadija Jauro ne wannan yarinya fara doguwa wacce suke tare da Zainab *yan
Legenda makarantar su Hanif tai graduation dinta kuma kasashen waje yake zuwa yana shigowa da
kaya.
Ita ta rako shi ma gidan nan nemanki. Sunan sa Alh. Bilyaminu, da naga motar da ya zo da ita sai da
na tsorata saboda kyan motar, matarsa daya *ya*yansa hudu, gashi matashi ga kyau ga kudi.
Daya mutumin ban san yadda aka yi ya sami lambata ba, kwatsam na ji ya kira ni ya kwatanta min
kansa sannan na gane shi. Kin tuna wani
mutumin da ya dinga magana da masu awon kayanmu a filin jirgi, wanda ya saka koriyar shadda.
Umaimah ta yi shiru kamar mai tunani can ta ce "Na tuno shi dogo, mai kiba, wanda suke kiransa
yallabai.
Aisha ta zabura ta ce "Eh shi, shima ya ganki ya dasa. Kusan kullum sai yayi min waya ya tambaya
ko kin zo. Sai in ce masa zaki zo dai baki zo ba yanzu.

Umaimah ta girgiza kai ta ce "Gaskiya suyi hakuri ba zan iya kula su ba. Me yasa sai ni, duk a cikin
dalibai mata ga kyawawa ace sai ni kadai suka sani za su dama.
Aisha ta kyalkyale da dariya ta ce "Ai kin fimu kyau, gayu, iya tafiya da iya magana da turanci shi
yasa ya rude.
Suka sa dariya su dukkansu Aisha ta ci gaba da cewa nima na hadu da guda daya tun acan daman ya
karbi lambata sunansa Mujahid. Shima wajen kaninsa ya je Aliyu wanda yayi Inti Nilai. Amma ni
kin san ba irin ki ba ce me tsattsauran ra'ayi, ni ina son shi, magana har ta yi nisa, ya zo gidanmu
yafi a kirga.
Umaimah ta yi dariya ta ce, "Allah Ya taimaka, Ya barku tare, mu zo musha biki bayan mun gama
bautar kasa.
Aisha ta ce "Ai kin kai ni da nisa, kafin mu gama za'ayi ma insha Allahu.
Ina Hanif kaninki kuwa?
Wannan yaron ya cika surutu har da cewa zai dinga zuwa muna gaisawa, ban sake ganinsa ba.
Umaimah ta zabura ta ja wayarta ta ce, "Har kin ma tuna min, na shigo gari ban kira Baban Hanif
na gaishe shi ba.
Daman da lambar wayarsa a cikin wayar sai ta nemo sunansa ta kira. Da farko bai amsaba
kasancewar bai san lambar ba amma data ci gaba da kira ba adadi sai ya dauka. Bayan sun gaisa sai
ta gabatar da kanta nan da nan ya gane ta, yayi farin ciki da jinta a waya, ta shaida
masa ta shigo gari dazun. Yana kokarin ya ce ta zo gidan sa ta sauka a wajen kawarta Lamijo sai
tayi sauri ta shaida masa tana gidan kawarta Aisha Bingyal amma wani lokaci idan ta shigo zata je.
Baban Hanif ya yi gyaran murya ya ce "Lamabarki ce wannan?
Umaimah ta ce "Eh ita ce Baba.
Ya ce "To zan ajiye lambar, kina da labarin saura sati biyu ku tafi Abuja bautar kasa?
Umaimah ta ce "Eh an fada min, mun yi waya da Hanif ma dazu.
Suka dan jima suna hira sannan suka yi sallama kafin su kashe waya kwatsam ta ji Baban Hanif ya
furta mata wata kalma wacce ko a mafarki ba ta zaci maganar nan zata fito daga bakinsa ba. Nan da
nan ta gigice ta dafe kirji tana ta salati a cikin zuciyarta, hakika maganarsa ta firgitata kuma ta daga
mata hankali. Bata da mafita dan haka sai ta amsa da "To Baba, na amince Allah Ya tabbatar mana
da alkhairi.
Saboda ba ta isa ya nemi alfarma a wajenta ta ki yi masa ba, muddin dai bai sabawa addininta ba, ya
yi mata halaccin da babu wanda ya taba yi mata irinsa a rayuwarta ba.
Daga karshe suka sake yin sallama ta ajiye waya a sanyaye kai ka ce laka ce aka zare mata. Ta dafe
kai
da hannaye guda biyu tana ta karanta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Aisha tambaya take, Sabitu ma tambaya yake "Lafiya? Me ya ce miki?
Ta dade kanta a kife sai can ta dago ta dubi kawarta cike da damuwa.
Ta ce "Aisha ina zan saka kaina? Yaya zan yi da taron mazan nan da suka addabe ni?
Aisha ta zabura ta dafa kafadarta ta ce "Baban Hanif ma cewa yayi yana sonki ko?
Daman ni nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya.
Sabitu ya ce "Wannan shi ake kira ga akuya ga kura. Ya ya za'a yi da Lamijo kenan?
Umaimah ta ce "Kai, ka rufe mana baki maganar manya ce wannan, kawata idan muka isa gida zan
baki labari.
Sabitu ya kyalkyale da dariya ya ce "Au haka ne ma abun?
Ina cikin zamana zaki zo ki saka ni a cikin maganar.
Daidai lokacin suka iso katafaren get din gidan su Aisha, me gadi ya taso da sauri ya wangale get
sika kutsa da motar cikin gidan.
Makeken gida bangare-bangare ya kawatu da fulawowi an kewaye gidan kai ka ce Hotel ne ba gida
ba.
Umaimah ta ce "Bari mu gaisa da su Mama sai in yiwa Hanif waya ya zo ya tafi da Sabitu gidansu
tunda shi namiji ne.
Aisha Bingyal ta ce "A'a akwai bangaren baki maza ko sun kai guda nawa zasu zauna ba tare da
wani ya takurawa wani ba.

Umaimah, ku saki jikinku wannan gidanku ne babu mai gajiya da ku, muna son baki. Kin san nice
*yar auta a gidanmu dukka yayuna mata ne guda hudu duk sun yi aure.
Umaimah da Sabitu dai sai kallon gida suke suna masu annuri dan yau za su yi kwanan dadi ga
fanka ga Ac ba sauro balle kwari irin na Dugge.
Cikin katafaren falo suka fara shiga ta yi musu izini su zauna tana zuwa, ta wuce zuwa kicin ta
bawa mai aiki izinin ta kawowa baki ruwa da lemo sannan ta fito ta wuce zuwa bangaren Mamarta,
dan ta sanar da mata cewar bakin sun karaso.
Sabitu ya dubi Umaimah ya yi dariya ya ce "Adda Umaimah, Allah Ya baki kudi da ikon gina mana
gida irin wanna a birni. Ko kuma Allah Ya baki miji mai arziki mu zo mu huta.
Umaimah ta yi dariya ta dafe kirji dan jin dadin kalaman Sabitu.
Ta ce ''Allah Ya biyewa bakinka dan kanina.
Suka dinga shan lemuna kala-kala ko ruwa ba su kalla ba, suka sami kek da meat pie suka dinga ci.
Sai da suka dan jima a zaune sannan Aisha da Mamarta suka fito, Umaimah da kaninta suka silalo
daga kan kujerun da suke zaune suka kwashi gaisuwa. Ta umarcesu da su koma su zauna akan
kujera, amma suka ki zama suka ci gaba da zama akan kafet saboda kunya da girmamawa irin ta
Fulani.
Mama tana zaune, Aisha na zaune a kusa da ita.
Aisha ta ce "Mama ita ce Umaimah *yar makarantarmu da nake baki labarinta, ita ce babbar
aminiyata mai sona nima ina sonta. Suka yi dariya su dukkansu.
Mama ta ce "Ai kuwa ina shan labarin Umaimah tun daga can ai mun taba gaisawa ma a waya, sai
yau Allah Ya nuna min Umaimah *yar mutanen Dugge.
To sannunku da zuwa kawar Aisha. Ke da Yayanki ne ko?
Umaimah ta dago da sauri ta dubi Sabitu ta yi dariya ta ce "Kanina ne Mama.
Mama ta ce "Na ganshi ne kamar babba da yake namiji ne ya fi ku girma, amma kamarku daya.
Aisha ta ce "Sabitu mu je in kai ka dakinka sai ka dan huta.
Sabitu ya tashi yana biye da Aisha,
Umaimah ma ta bi su suka fice zuwa wani bangare a can waje, falo,
daki daya da bandaki, babu abinda babu tamkar dakin wata amarya. Umaimah ta bude jaka ta ware
masa kayansa kala biyu ya zuba a durowa sannan ta tafi da jakar kayanta a ciki bayan sun nunnuna
masa duk yadda zai yi amfani da kayan ciki.
Dakin Aisha suka wuce akan bene sai da Umaimah ta jinjimawa dakin saboda ya kayatu ga girma,
kai kace filin kwallo ne. Katafaren gado da kujerunsa, ga kayan kallo duk daki daya, kayataccen
bandaki
mai kyau kai ka ce na tangaren ne kamar ka kwanta ka yi bacci a ciki.
Wanka Umaimah ta fara yi sannan aka aje mata abinci kala-kala ita da kawarta suna ci suna ta hira
har suka koshi, tabbas ta tuna Malaysia a yau musamman da sanyin Ac ya ratsa ta. Bayan ci sai
kwanciya, Umaimah ta kwanta hakarkarinta akan lallausar katifa saboda gajiya, sai ta tsinci kanta
tana mai aiyanowa a ranta dama ace gidanta ne nan ita da abun kaunarta Abdul-Sabur sai ta ji
kwalla ta cika mata ido. Nan da nan ta tuno da Faduwa sai ta jawo wayarta a sanyaye ta dubo sunan
Faduwa ta kira ta.
Bugu daya Faduwa ta amsa tun kafin ma Umaimah ta yi magana Faduwa ta ambaci sunanta. Cike
da mamaki Umaimah ta tambaye ta "Ya aka yi kika san ni ce tun ma ban yi magana ba?
Faduwa ta ce "Dare da rana ina jiran in ji kiranki daga Nigeria, dan haka ina ganin lambar Nigeria
sai na san kece duk da yanzu *yan uwana suna yawan kirana daga Sokoto.
Umaimah ta ce "Kira nayi in ji yadda kike ciki. Kin haihu lafiya ko?
Faduwa ta ce "Ai na yi fushi tunda baki neme ni ba tuntuni, sai yanzu.
Umaimah ta ce "Allah Sarki Antina kin san Rugarmu ba mu da waya, yanzun nan na fito birni, na
sayi layi.
Faduwa ta ce "Na haifi *ya mace gata nan kamarta daya da ni sak, na saka mata suna Umaimah.
Sai Umaimah ta daka tsalle ta diro daga kan gado dan murna har da hawayen dadi ne yake kwarara
Ta ce "Anti Faduwa, da gaske Umaimah sunanta?

Ai kuwa zanzo har Cairo wata rana musamman dan in ga takwarata. Amma na ji dadi na gode,
Allah Ya
raya ta, Ya yi mata albarka.
Faduwa ta ce "Amin, ga Sagir ku gaisa shima yana tambayar ki, zai sake fada miki sunan baby ki ji.
Ai shi zaki fi yarda da maganarsa.
Faduwa ta mikawa maigidanta waya cikin harshen turanci suka gaisa da Umaimah ya sake shaida
mata sunanta aka saka. Ta yi masa godiya da taya shi murna, gami da yiwa jaririya doguwar addu'a.
Daga karshe ta yi sallama da su suka kashe waya.
Daidai lokacin Aisha Bingyal ta idar da sallah ta dubi Umaimah ta ce "Aminiyarki ce Faduwa ta
haihu?
Ai da kin bani ita mun gaisa, dan tana da kirki.
Umaimah ta ce "Tana da kirki sosai ma kuwa, har sunana ta sakawa *yar jaririyar data haifa,
shiyasa kika ji ina ta tsalle. Zan baki lambarta sai ki kira ta ku gaisa, ta sanki sosai, kiyi mata barka.
Faduwa da Abdul-Sabur ai aminaina ne na hakika, na ji dadin zama da su, ba zan taba mantawa da
su ba kuma ba zan daina kaunarsu a raina ba har abada.
Aisha ta yi dariya ta ce "Musamman ma Abdul-Sabur din, shi so na musamma kike yi masa bayan
na MAKWABTAKA. Suka yi dariya su dukkansu.
Aisha ta tashi daga kan abin sallah ta cire hijabinta ta linke ta zo ta zauna akan gado kusa da
Umaimah.
Ta ce "Yauwa, har kin tuna min ma da maganar Baban Hanif, kin ce zaki fada min abunda ya ce
miki.
Umaimah ta kalle ta tayi murmushi ta jawo filo ta ringisa.
Ta ce ''Uhum, ashe baki manta ba kema?
Ni ma wallahi tun dazu maganarsa ta tsaye min a rai, har na fara tunanin da ace akwai inda zan
kaura da garin nan zan bari in tafi inda ba'a taba sanina ba, zai fi min sauki.
Aisha ta harare ta, ta ce "Irin yadda kika yi mana a Malaysia za ki sake yi musu a garin da zaki
kaura?
Ai duk in da kika je dole ki sami wadanda zasu saba da ke, sai sun sanki dole, kamar yadda kika
saba da Faduwa da Abdul-Sabur.
Umaimah ta ce "Haka ne, dan gaskiya ko a mafarki ban zaci akwai ranar da zan saba da
makwabtana ba su Faduwa, sai gashi daga baya bani da tamkarsu har ban so muka rabu ba. Baban
Hanif yayi min wata magana wacce a wajena ba mai yiwuwa ba ce, kuma idan ban amince ba
tabbas ba zai ji dadi ba kuma ban kyauta masa ba.
Aisha ta ce "Me ya ce miki, cewa ya yi yana sonki zai aureki?
............
Eh cewa yayi xai aure ni, nikuma a duniya banga wanda nake so da kauna ba irin Dan Aunty...
Kuma shi xan aura...lols.
Ehem yan uba kunji dai da bakin Umaimah wanda tace xata aura dan nima bayin kaina bane a dole
xan aure ta...
Marbass Dan Aunty.
See translationMAKWABTAKA 46
Aisha ta ce "Me yace miki, cewa ya yi yana sonki zai
aure ki?
Umaimah ta ce "Cewa yayi daya daga cikin abokan aikinsu ne ya ganni ya ce yana sona, ya biyo ta
wajensa.
Hmm, Baban Hanif ya na sake maimaita min cewar Alh. Nura ogansa ne yana jin nauyinsa sosai.
Ina jin yasan halina yana tsoron kada in wulakanta masa oga. Ya dami Baban Hanif wai ya nemo
masa lambar wayata, wai idan na amince zai ba shi lambar yanzu. Nauyinsa nake ji ba zan iya cewa
kada ya ba shi lambata ba, sai na ce ba damuwa ya bashi lambar, sannan ba zan iya wulakanta
mutumin da ya kawo min ba ko da a bayan idonsa ne, sannan ba zan iya aurensa ba saboda AbdulSabur nake so.
Yaya kika ga za'ayi yanzu?

Tabbas ina cikin wani hali Aisha. Umaimah ta sulale ta kwanta saboda tashin hankali.
Aisha ta dade a zaune tana kallon Umaimah daga dukkan alamu tana jin tausayinta, sai can ta matso
kusa da ita ta dafa kanta.
Ta ce "Gaskiya sai yanzu na fara fahimtar matsalarki kawata, ba wai dan kina son Abdul-Sabur ba
ne yasa na fara jin tausayinki ba, ni na fi so ma ki cire shi a lissafinki. Naga alama cunkushewar
maneman ne da suka fara yi miki yawa, zai yi wuya ki tantance wanda ya fi a cikinsu. Yanxu haka
na turawa Bilyaminu lambarki dazun nan da muke cin abinci, ya ce zai kiraki dan ni na fi yi miki
sha'awarsa fiye da yallabai saboda shi Bilyamin matashi ne, me mata daya da *ya*ya kadan ba
kamar yallabai ba matansa biyu, sannan da tulin *ya*ya sai dai akwai tulin kudi. Ga na bangaren
Baban Hanif daga gani shima me kudi ne, dubi duk kudin Baban Hanif ya ce wancan ogansa ne ya
fishi kudi kenan, lallai akwai Naira. Ko baki aure shi ba zaki sami kudi a wajensa.
Umaimah, wannan fa ba abin damuwa ba ne, ana hada samari biyar ko goma har mai rabo ya samu
ya aura, ba abin damuwa bane. Za ki iya kula su dukka, ba dai gaisawa ba ne a waya ko kuma suzo
ki fita ku yi hira shikenan fa.
Umaimah ta ce gaba da karanta "Lahaula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim.
Dan ta shiga garari.
Wayar Umaimah ce ta dau kara bata yi mamaki ba dan ta kikkira mutane da yawa ta san yanzu an
fara sanin lambarta. Ta mika hannu a sanyaye zata dauka sai Aisha ta yi sauri ta sura ta duba
lambar,
kallo daya ta yiwa lambar ta shaida lambar Bilyaminu ce. Sai

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment