Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na
suffanta ciwon na gane irin ciwon Ibrahim ne,
don haka na cire rai da shi a rayuwa.
Tun daga wannan lokaci hankalina ya yi Nigeria, na ji ina
so na zo na gana da mahaifina tunda ransa.
Saboda ban san shi ba sai a hoto, ga babu dan uwana
Ibrahim shi ne daman ya san su, wanda ko ba ran
mahaifinmu zai iya kawo ni na ga dangin ubana ko da
kuwa aurena ne ya zo.
Mahaifiyata ta dage ta ce ba zan je ba, don ba son mu
suke yi ba. Tana tsoro kada ma na zo su cuceni,
ko su hada baki su hallakar da ni, tunda ta ji labari su
*yan Nigeria suna da hadamar gado, kuma za su iya yin
komai a kan gado . Kuma ta fuskanci matansa ba sa son
mu, da akwai yadda za su yi da sun soke sunanmu daga
cikin *ya*yansa, *ya*yansu ne *ya*ya.
Na ji ba dadi don na sawa raina ina son zuwan, to amma
babban dalilin da yasa na hakura ba ni da kudin jirgi.
Muna nan haka rayuwa ba dadi, rana daya ba zato ba
tsammani zuciyar mahaifiyata ta buga, sai dai
kawai ta fadi aka dauki gawarta. Tsakaninta da yayana
shekara guda dai-dai.
Nima mutuwa ce kawai ban yi ba, saboda na girgiza, na
dimauce zan iya cewa dai na zautu tamkar kwakwalwata
ta tabu. Ta fashe da kuka mai tsanani. Ya yin da Umaima
da Abdul-sabur suka razana har suna hada baki ''Mama
ce ta mutu?
Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta tafi ta bar
ni, ni kadai a duniya. Tun daga wannan Lokaci na daina
zuwa aiki kwata-kwata.
Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta tafi ta bar
ni, ni kadai a duniya. Tun daga lokacin nan na daina zuwa
aiki kwata-kwata don ko naje shirme zan yi, yanayin aiki
na kuwa sai da nutsuwa. Babu yadda dangin mahaifiyata
ba su yi ba na je aikina nayi hakuri na maida komai ba
komai ba. Na fada musu baro-baro, ba zan je ba, tun
*yan ofishinmu na ba ni dama suna daga min kafa har
suka fara turomin da doguwar wasikar gargadi (warning
letter) cewar, ko na dawo aiki, ko a kore ni. Daga karshe
dai naga wasikar kora daga aiki,
ban damu ba daman haka nake so. Na hada *yan
abubuwan da aka ba ni na daga cikin dan abin da
Mahaifiyata ta bar min na gado,
na sayi tikiti na kaura Saudiya wajen danginta na can na
zauna da su a 'Tayif.

Bayan mutuwar Mahaifiyata na kira lambar gidanmu ta
Nigeria ina so na shaidawa Mahaifina rasuwarta, sai
matarsa ta dauka, na ce ta bashi muyi magana, ta ce min
ba ya kusa. Na shaida mata
sakon da zata fada masa, a shelake ta amsa min gami da
ajiye waya tun ban gama magana ba. Sai na kira Baffana
daya daga cikin su wanda yake zaune a Kano Baffa
Mansur na shaida masa abubuwan da yake wakana, ya yi
min alkawarin zai sanar da shi idan ya je duba shi, don
shi ma jikin ya tsananta.
Na yi kuka, kullum cikinsa nake yi har yau saboda bani da
kowa, ba ni da komai, daman dai na san Allah (S.W.T) ne
kadai gatana.
Rayuwata ta tsananta a 'Tayif' ba na ganin dai-dai duk
inda na je sai naga kaman ana min kora da hali, sun kosa
da ni. Duk da masu arziki ne abinci da sutura ba sa wuya
sai na ga suna yi min habaici game da mijinsu suna
gudun kada mazansu su ce suna sona saboda Allah Ya yi
min fara'a, hira da saurin sabo da mutane.
Duk na tsargu na fara zama mujiya a cikin jama,a.
Dole na tarkato na dawo Cairo don na tantance cewar na
wuce zama a gaban wasu. Na zo na bude gidana na
zauna, ina cin dan abin da na samo, daya kare sai na fara
shiga garari.
Egypt ba kudi ba kamar Saudiya ba komai a wadace, a
Egypt ma'aikaci mai daukar albashi kukan babu
yake yi, albashin bashi da yawa balle ni da bana aiki.
Bayan shekara ne na ga ya dace na kira na ji jikin
mahaifina tunda kozai mutu babu mai kirana ya ji hakin
da nake ciki, ina kira gidanmu, wani kanina
mai suna Salahuddin ne ya dauk wayar, sai yake
shaidamin ai mahaifinmu ya shekara da mutuwa...
Faduwa ta girgiza kai ta yi murmushin takaici, yayin da
Abdul-Sabur da Umaimah suka zazzare ido don tashin
hankali.
''Ya rasu amma ba su fada miki ba? Im ji Abdul-Sabur.
Faduwa ta fashe da kuka, ta ce, ''Ba su fada min ba,
saboda bana cikin lissafin *ya *yansa. Raina ya yi
matukar baci, na yi ta fada, a lokacin na kira Baffanaina
daya bayan daya na wanke su tas da bakaken
maganganu, na ce yanzu har Mahaifina ya shekara ya
shekara da rasuwa a kasa fada min. Sai
suka hau kame-kame wai saboda suna gudun kada
zuciyata ta buga abubuwan su yi min yawa, ga mutuwar
dan uwana da mahaifiyata, ya za a yi a fada min mutuwar
mahaifina, daman so suke a kwana biyu tukunna.
Babu abin da na ce musu, sai na kashe waya, na fi sati ina
kuka a daki ni kadai, sai da kanwar mahaifiyata ta zo ta
tambaye ni ko lafiya? Na shaida mata duk abin da ya faru.
Nan da nan ta hado taron gaggawa, kowa sai da ransa ya
baci da ya ji abin da aka yi min, suka ce ai ba za a zura
musu ido aci gaba da cutata ba, dole a kwatarmin

hakkina tunda sun nuna ba su san mutunci ba, sai an
raba abin da ya bari da ni. Suka ba ni waya na kira gidan a
gabansu na bude magana(speaker). Cikin harshen Hausa
na yi magana dasu a waya dangina basu ji abin da muka
ce ba, amma na fassara musu daga baya abin da aka ce.
Matan Babana na tambaya me da me Mahaifina ya bari?
Suka hau kame-kame wai bai bar komai ba,
duk sun kare a asibiti. Ko gidan ma da suke ciki na aro ne.
Sai na katse waya na bugawa Baffa Adamu waya,
shi yana jin larabci na tambaye shi gadon Mahaifina,
sai ya ce fili ya bari guda daya. Da na kira Baffa Mansur
kuwa shi ma a cikin harshen Larabci mukayi magana,
kowa yana ji. Sai ya ce baibar komai ba sai shaguna guda
uku a kasuwa da mota biyu tirela.
Daga jin haka mun san ba su da gaskiya, don haka aka ce
na shirya kawai na tafi Nigeria, na je na shigar da kara na
karbi hakkina. Suka hadamin kudin jirgi, amma sai da na
sami wanda ya ke da
tabbas ya san gidanmu na sokoto amma a Abuja yake a
zaune. Don haka Abuja na nufa gidan da matarsa su ma
sakkwatawa ne, unguwarsu daya da mahaifina ni kuma a
asibitinmu na sansu sun kawo dansu wata shekarar muke
waya da su har bayan sun tafi. Hira ta kawo hira suka
gane mahaifina...
Umaimah ta gyara zama ta ce,''Ya aka yi kika je?''
Abdul-Sabur ya ja doguawar ajiyar zuciya, ya gyada kai.
Ya ce, ''Ikon Allah, rayuwa kenan. Yaya ta kasance
tsakaninki da su?''
Faduwa ta tabe baki ta ce, ''Inda ranka a duniya za ka sha
kallo. Wasu mutane gani suke kamar ba
zasu mutu ba, sun kauro duniya ke nan, ba sa tsoron
Allah. Sun manta inda wancan ya je su ma za su je ne ko
ba jima ko ba dade. Da na isa Nigeria garin Abuja aka kai
ni garinmu Sokoto cikin gidan Babana. Sai ga ni a zaune a
falonsa, ga ni ga hotunansa a kusa da ni, amma baya nan.
Allah Ya yanke haduwarmu har abada.
Na ga kannene rututu, dangi kamar tururuwa kowa ya
taho ya ga Faduwa, suna murna ina murna, yayin da aka
dinga jeremin kwanukan abinci da kyaututtuka iri-iri
kamar Muhutai, atamfofi, leshina, kwarya da dai
sauransu. Kowa so yake ya yi hira da ni, kai ka ce suna
sona.
Wasu daga cikinsu kauyawa ne futik babu boko, wasu
kuwa *yan gayu ne masu kudi. Su ka ce ma idan na huta
zasu kai ni Kano, Kaduna da Abuja wajen *yan uwa
(cousins) da suke auren manyan masu kudi a can.
An ba ni su a waya mun gaggaisa na ce musu idanna na
gama da sokoto za,a kawo ni sun yi murna da jin haka.
Wasu turanci muke yi da su, wasu Larabci, wasu kuwa
hausa kawai suka iya sai mu yara.
Sai da na shafe kwanaki goma cur babu wanda ya yi min
maganar gadona, sai dai a gaisa, a yi hira

wasa da dariyaa, a tulo min abinci da kayan marmari a
gyaramin gado na kwanta in yi bacci washe gari in tashi a
ci gaba da haka. Sai na nemi a taro min kannen Mahaifina
da manyan kannena da iyayensu mata, duk muka hadu a
babban falon gidan.
Na bude baki na yi magana cikin harshen Hausa yadda
kowannensu zai gane. Na ce, na zo ne na karbi gadon
mahaifina don na kasa ganewa duk wanda na tambaya
me ya bari, abin da zai fadamin daban ne. Me ya bari,
kuma ina nawa kason?
Sai aka hau kallon-kallo, wata matarsa wacce ita tafi tsana
ta ta dinga bayani irin na rashin gaskiya, wai gidan nan
kawai ya bari duk asibiti ya cinye kudin,
an siyar da kadarorinsa gaba daya. Gidan ma ba dukka ba
dole sai an siyar da rabi an biya masa bashin da ake
binsa.
Ni kuma abin da na gida dai an gama raba shi, don naga
kowa ya kama nasa bangaren an yi toshe-toshe da likelike.
Baffa Adamu ya ce na yi hakuri na koma kasarmu idan
komai ya daidaita za a turomin da kashina.
Na fusata na ce da shi, ina fili da ka fada min yana da shi?
Na juya na dubi Baffa Mansur, da ya ce min yana da
shaguna a kasuwa, na tambayeshi. Na ce, ''Ina shagunan
da ka fada min ya bari a kasuwa da motoci? Duk ba ni da
kaso a ciki ke nan?
Na yi kuka sosai don takaici na dube su dukkansu na ce,
''To na gane abin da dukka kuke nufi, kun
cire ni daga cikin *ya*yan gidan nan, kun rabe gadon ku
banda ni. A wajen Allah ina da hakki ku ka danne, to duk
wanda ya ci kashina ko da kwayar zarra ce ban yafe ba,
zai biya ni a ranar da bashi da abin da zai ba ni sai
ladansa. In da Mutumin daya tara dukiyar da ku ka cinye
ya je dukkanmu nan zamu je, kuma ba kowa ya jawo min
wannan wulakancin ba sai shi da kansa Mahaifina da ya
nuna muku ni ba komai ba ce, kuma bai damu da ni ba.
Sai suka hau timin tsawa da fada, wai kada na yi musu
rashin kunya. Kannena har da masu cewa, za su dake ni
idan na sake yiwa iyayensu rashin kunya. Da yake
zuciyata ta kekashe ban yi shiru ba ni ma fadan na ke na
ce su zo su dake ni idan sun so ma su kashe ni.
Aka shiga tsakani aka kai ni bangaren masaukina.
Cikin dare Baffa Adamu ya aiko na zo gidansa yana
nemana. Da farko na ki zuwa sai da ya aiko matarsa
ta zo, ta tafi da ni ya dauke ni a mota ya kai ni gidan wani
dattijo, a she shine alakalin daya raba gadon. Aka
daukomin takardun da aka yi rabon gadon.
Ga sunayen magada nan, amma babu sunana,
sannan ga dumbin dukiyar da ya bari, shagunan kasuwa,
filaye da tireloli, amma babu nawa duk an
rabe musu. Wanda da ace an raba da ni da na yi sallama
da talauci. Baffa Adamu ya dube ni fuskarsa cike da

nadama.
Ya ce da ni, ''Faduwa ina tsoron ranar da zan mutu Allah
Ya tuhume ni da laifin ban fada miki gaskiya ba. Saboda
ni dai banci gadon ki ba ko sisi. Allah ba zai tuhume ni da
wannan ba, amma zai tuhume ni
da nasan komai na boye miki. Na yi ta kuka na ci gaba da
yi musu bayanin halin da nake ciki a can Egypt ba ni da
komai, ba ni da kowa.
Alkali ya ce, ''Shawara biyu zan ba ki, ki zabi wacce ta fi
miki sauki. Ta farko ko kiyi hakuri ki bar wa Allah cutar da
akayi miki, ko kuma ki nemo kudi ki dauki lauyoyi su
tsaya miki ki karbi hakkinki.
Amma ki sani za a iya shekara goma ana ta shari'ar nan
ba tare da ta kare ba.
Allah ya raba mu da son zucia.
MAKWABTAKA 13
Na tashi na fice don takaici, Baffa l Adamu ya dawo dani
gida babu abin da yake sai ba ni hakuri yana
neman gafarata. Yana sake ba ne labarin mugun hali irin
na matan babana cewar, karfi da yaji suka hana
mahaifina maganarmu, don da koda yaushe yana
maganar zaije ya dauko Faduwa ta dawo
wajensa ko ya je ya ganki, ya ba ki wani abu daga cikin
dukiyoyinsa, wanda zan ci gaba da karatu. Sai
su ce bazai je ba ni me yasa ban taba zuwa ba?
Kuma duk *ya*yan da yake da su sama da ashirin ba su
ishe shi ba sai ya je neman wata.
Dole ya hakura ya janye wannan zance na zuwa Egypt
don ba yadda zai yi.
Na ce da shi, ''Don kansu, kowa ya yi na gari zai gani.
Nawa rayuwar duniyar ta ke ne?
Washegari da sassafe na hada kayana na ce, tafiya Abuja
zan yi, daman ta Abuja na zo. Baffa Adamu ya hada ni da
babban dansa ya kai ni har Abuja gidan *yarsa Ummul
Kursim na zauna na gama kwanakina don daman wata
guda ne booking din tikitina, na komawa Egypt.
Gidan Ummulkursi ne tamkar aljannar duniya tana auren
Sanata, komai gashinan a wadace kamar ba a Nigeria
nake ba. Ta zazzagaya da ni garin Abuja na ga gidaje, sai a
lokacin nasan ashe Nigeria tana da kyau da arziki haka.
Sai a lokacin na ji zuciyata ta fara warwarewa daga
kuncin da nake ciki, ta ba ni
hakuri bisa abubuwan da *yan uwana suka yi min. Ta yi
min alkawari idan har zan iya zama a kasar nan ita kuwa
zata yi wa mijinta magana ya samar min aiki a asibiti mai
kyau inda za a biyani da kyau,
na kama gidan haya nayi zamana har Allah Ya fito min da
miji.
Na yi sha,awar shawarar nan da ta ba ni, amma na ce
mata zan koma Cairo tukunna na sanarwa dangina, na
kuma yi musu sallama.
Kafin na tahi sai da ta kai ni Kaduna wajen daya *yar

uwar tamu, ita take auren Manajan wani
babban banki, kudi kam ba,a magana. Muka dungumo
muka je Kano wajen Hajiya Lami itama kakarmu daya, ita
ma ta kafu a gidan, mijinta hamshakin dan kasuwa ne, su
dukka sun yi min
kyautar kudi da kaya.
Da muka koma Abuja a ranar da zan tafi Sanata ya yi min
yayyafin dallar, har sai da na tsorata don yawa. Allah Mai
jinkan bawanSa, Ya hana ni a can Ya bude min anan.
Na yi kukan farin ciki, gami da godiya mai dumbin yawa.
Duk da haka Ummul Kursim ba ta barni haka ba sai da ta
ba ni shaddoji da leshina dinkakku ta ce na dinga sakawa
a can, ta kara bani daloli da
yawa. Lallai ba dukka aka taru aka zama daya ba, wani
mai kirki, wani bashi da kirki, wani mai kyauta wani
marowaci. Wani mai tausayi, wani kuwa mugu ne,
haka mutanen suke ciki. Suka kaini filin jirgi suka saka ni
a jirgi na taho Cairo.
Da na ba wa dangina labari sai suka yi takaici, suka tayani
da addu ar Allah Ya saka min. Shawarar Ummul Kursim
kuwa tuni suka yi facali da ita, suka ce bazan koma
Nigeria ba, gara na hakura na yi
zamana a cikinsu.
To ba ni da zabi saboda na sallama rayuwar ma gaba
daya ba ta min dadi. Ina zaune ina canja dalolina a
hankali ina ci, talauci ya daina nukurkusata.
Na dade ina cikin rufin asiri ina kashe dalolin nan, amma
da suka dauko karewa sai hankalina ya
tashi na tabbatar zan koma gidan jiya na kashewa zai
gagare ni, don haka na koma neman aiki. A asibitin da na
yi aiki na fara zuwa na roke su, su mayar da ni sai suka ki.
Babu ta kan babban da ban bi ina roko, durkuso har kasa
kuka da hawaye suka cemin sun cike gurbina da wata, ba
su da inda za
su saka ni.
Na bazama gari duk wani asibiti da kuka sani a Cairo sai
da na mika takarduna na neman aiki, kai har ma wasu
asibitoci na wasu jihohin sai da na tuttuta wasu na je da
kaina, wasu na aika ta internate ko na ba wa wani sako ya
kai min. Amma babu wanda ya kira ni interview, don
haka babu aiki. Ina cikin hali na rashi da wahala da
fargabar neman aiki, sai dai a *yan uwana wanda ya dubi
Allah ya ba ni dan kudi, wasu sai na roka ko su ba ni ko su
hana. Babu irin wulakancin da bana gani, ga shi ba ni da
saurayi ko daya balle so na ya sa ya tallafe ni ya
kwantarmin da hankali. Ana cikin wannan hali sai na
hadu da Gaddafi, a makarantar lafiya ajinmu daya a
jami,a. Ban yi
mamakin ganinsa ba, don shima likita ne, amma tunda
muka gama karatu ban san inda yake ba.
Yana ganina ya rungume ni cikin farin ciki muka gaisa.
Hakika na ga sauyi a fatarsa da kayan da yake

sanye a jikinsa, domin tsadaddu ne, kudi ya zauna masa
matuka.
Ya tambaye ni ''ina maigida? Ina yara? Ya kuma wajen
aiki?
Sai ya ga alamar damuwa nan da nan a fuskata, jikina ya
yi sanyi don na rasa amsar da zan ba shi.
''Faduwa lapia kika sauya nan da nan?
Ya tambaye ni yana kallona cikin yanayin tuhuma.
Cikin hawaye na amsa masa dukkan tambayar da ya yi
min, amsar ita ce babu. Ba ni da uwa, ba uba babu dan
uwa, babu aiki balle *ya*ya. 'Subhanallah! Subhanallah!!
Kalmar da yake ambato ke nan.
Ya ja hannuna zuwa ga kyakkyawar motarsa muka zauna,
ya roki na share hawayena na yi masa bayanin
matsalolina.
Tunda na fara magana ya fara girgiza kai don tausayina.
Hawaye ya kasa tsayawa a idona, har na sa shima yana
zubarwa.
'Faduwa kwantar da hankalinki, zan taimaka iya karfina.
Kalmar da ya fara fada min kenan har tasa
na tsagaita da kukan.
Ya fara ba ni labarin yadda rayuwa ta yi masa kyau. Ya ce,
da muka gama karatu sai ya tafi Malaysia karatu akan
likita ya karanci kwarewa akan fannin tiyata ya zama
Sugical Doctor Consultant.
Yana gama karatu sai ya sami aiki a wani babban asibiti
anan cikin babban birnin Kaula Lumpur ana
biyansa albashi mai kyau. An bashi gida mai kyawun
gaske, ana cirewa a albashinsa har ya zama nasa. Ya dawo
gida ya yi aure ya tafi da matarsa suna zaune a can lafiya
kalau cikin so da kaunar juna yanzu yaransu guda biyu
mace da
namiji su ma har sunyi nisa a makaranta.
Ya ce washe gari zai koma Malaysia, zai karbi lambata da
photocopy din takardu da E-mail address dina ya tafi da
su, zai fadamin halin da ake ciki game da neman aiki.
Wai amma na je na fara tuntubar dangina sun yarda
sannan zai zo ya karbi takardun a ranar da daddare,
saboda washegari zai wuce. Na ce, kada ma ya damu,
babu abin da dangina za su ce ko su yarda ko kada su
yarda ni dai zan tafi saboda yanzu da na rasa babu wanda
ya dauki nauyina, babu wanda ya ke tayani yawon neman
aiki, don haka yanzu na gane zan bi duk wata hanya
wacce rayuwa zata yi min dadi idan dai ba hanyar sabon
Ubangiji ba ce.
Na ba shi adireshin gidanmu da lambar wayata, na ce
don Allah da daddare ya zo ya karba zan hada
masa su. Ya ce, ba don ma bai gama harhada takardun da
ya zo nema ba da mun tafi ya ga gidan
a lokacin, na ce masa, ba komai ya zo da daddaren. Sai na
fasa shiga neman aikin na koma gida na shiga tsara
takarduna, yadda suna gani zasu dauke ni. Na dukufa ina

addu,a ina kuka, ina rokon Allah Ya tabbatar min da
tafiyar nan, kuma Ya sa alkhairi a cikinta.
Har karfe goma na dare banga Gaddafi ba, na yi ta kiran
wayarsa bai amsa ba, sai na shiga zargin karya ya zukala
min, nan da nan murna ta koma ciki.
Sai na ji wayata tana ruri, ina dubawa na ga sunansa ne, a
guje na amsa.
Ya ce, 'Ga ni a kofar gidanki, ki fito. Na ce, ya shigo babu
damuwa. Bayan ya shigo falona na dinga jere masa abinci
da lemo da na yini ina shirya masa, don ya ji dadi ni ma
ya taimake ni.
Ya ji dadi da ganin abincin nan saboda yunwar da ta ke
addabarsa yini guda bai ci abinci ba, yana ta
yawon harhado kan takardunsa. Ya ci ya sha ya mike kafa
muka yi ta hira muna kallo talabijin har karfe daya saura,
sai da ya fara gyangyadi ya tashi ya yi haramar tafiya
bayan na zuba masa takardun da duk ya bukata a
ambulan na bashi. Ya kara ba ni hakuri a bisa bakar
rayuwar da nake ciki. Ya ba ni tabbacin zai taimake ni
insha Allahu.
Allah Sarki, abokina kudi mai yawa ya bani da lambobin
wayarsa ta gida da ta ofis na can Malaysia. Na yi masa
godiaya ya tafi, yana isa
Malaysia ya kira ya fada min ya isa bayan kwanaki biyu ya
sake shaida min cewar ya fara nema min aiki.
Abu kamar wasa an shafe watanni uku babu aiki,
hankalina ya yi matukar tashi, na dameshi da waya safe
da rana, ina rokonsa ya taimake ni. Har matarsa ta fara
kishi da ni, tana cewa wai na rabu da mijinta kada na sake
kiransa. Duk bayanin da bayanin da ya yi mata cewar ni
kawarsa ce, karatu muka yi tare, amma ba ta yarda ba,
kasan mata da kishi. Ban damu ba duk yana daya daga
jarrabawa daga Allah.
Daga karshe Gaddafi ya fitomin da sakamakon karshe
cewar ba zan iya samun aiki a Malaysia ba, sai dai idan
zan dawo karatu. Sai dai in zabi bangare daya na karanta
har tsawon shekaru biyu ina gamawa sai su ba ni aiki ba
tare da wani Cuku-cuku ba.
Na ce masa duk wannan ba matsala ba ce, amma ina zan
sami kudin da zan dawo Malaysia na yi karatu? Ina zan
sami kudin abinci da na hayar gida?
Gaddafi ya ce min, duk ba matsala ba ce, zai fada min
hanyar da zan bi na sami tallafi daga Gamnatin tarayya.
Ya turomin forms ta internate duk na cike na yi ta kaiwa.
Kafin lokaci ya yi Gamnati ta yarda zata ba ni tallafin
karatu har sai na gama. Kudin makaranta, abinci, kudin
hayar gida duk sun biya min wadataccen kudi.
Sai da komai ya kankama na shapawa dangina labari,
kadanne suka yarjemin, duk ba su bani goyon baya ba.
Na nuna musu ba neman shawararsu nake yi ba ina dai yi
musu sallama ne tafiya kamar da kasa inji mai ciwon ido.
Gaddafi ya taimaka min na sami gida, muka je makaranta

ya ya taimaka min nayi registration ina karantar
bangaren mata (Gynea). Sai na tsinci kaina cikin sabuwar
rayuwa a Malaysia tare da sababbin mutane ba wadanda
na sani a da ba.
Na yi kokarin na zubar da bakin cikin da yake damuna a
baya, na nemo farin ciki na sakawa zuciyata ba don
komai ba, sai don kawai na taimaki kaina duniya da
lahira. Na yi hakuri, nayi tawakalli na yarda Allah Yana
sane da ni, duk yadda Ya tsaro min rayuwata dole haka za
a yi.
Na yarda da kaddara, yanzu ina shekara ta biyu a
karatuna, ina gamawa ina da kujerar aikina a Subang Jaya
Hospital idan har na ci jarabawata,
wacce ba na fargabar zan fadi.
Umaimah da Abdul-Sabur sun buga tagumi suna kallon
Faduwa. Tausayinta ya cika musu zuciya,
baiwar Allah sai murmushi ta ke don tawakkali.
Nan da nan sabon tunani ya kutso zuciyar Umaimah ta
tabbatar ashe ba ita kadai ce ta ke da matsala ba a
rayuwa. Sai ta ji Faduwa ta burgeta ta da mayar da komai
ba komai ba ta ci gaba da rayuwarta cikin kawaye da
abokai tana walwala tamkar ba ta da matsalar rayuwa.
Amma ita sam ta kasa yin hakan.
''ina ma zuciyata ta sami juriya da tawakkali irin na
Faduwa? Umaimah ke fada a zuciyarta.
Faduwa ce ta katse tunaninta data ambaci sunanta. Ta ce
''Umaimah, kalle ni nan ki gani. Kinga alamar
damuwa ko fushi a fuskata? To haka kowa ya ke dannewa
ya manta da komai. Shekaruna talatin da takwas a duniya
amma banyi auren fari ba, nan da *yan shekaru zan shiga
layin tsofaffi wadanda
haihuwa zata dauke musu kuma ban haifi ko daya ba. Har
yanzu Allah Bai kawo min miji ba, ga shi ina son aure. Ya
ya na iya, sai in daina dariya ko kuma sai na tsani
mutanen da babu ruwansu, su suka
doramin? Allah ne Yake jarraba ni ya ga yaya zanyi idan
Ya doramin masifa. Insha Allah Zai yaye min ko
ban samuba a duniya Zai yaye min a lahira. Na yarda da
kaddara mai kyau ko mara kyau.
Sai ta kyalkyale da dariya saboda yadda ta ga sun tsura
mata ido suna kallonta kai kace talabijin suka saka a gaba.
Su dukka suka yi murmushi, gami da jan doguwar ajjiyar
zuciya. Abdul-Sabur ya ce, ''Ni har na rasa ma abin da
zance da ke, saboda tsabagen tausayi. Sannu Faduwa,
sannu da kokarin hakuri gami da juriya.
Allah Ya jikan nahaifanki da dan uwanki, ke kuma Allah Ya
warware miki. Wallahi ni dai ina ganinki amma ban taba
tunanin a cikin wannan halin ki ke cika ba, don ba mu
taba zama munyi yi hira irin hakaba.
Na ga dai alamar dai ba ki da miji, sai na yi tunanin ko
mutuwa ya yi ko rabuwa kuka yi yaranki na can kasarku.
Faduwa ta girgiza kai ta ce, ''Babu ko daya, haka nake ni

kadai, ba ni da kowa.
Umaimah ta ce, ''Allah Sarki, Allah Ya jikansu, mu kuma
Ya kyautata namu zuwan.
Faduwa ta share hawaye ta ce, ''Ameen, na gode.''
Su dukka sun kasa cin sandwich din, ruwan shayin ne
suka kukkurba suka

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment