Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk
sun farfasa.
Umma tayi musu tsawa cikin ba cin rai ta shiga yi musu
fada tana nuna musu ba su kyauta ba.
Budar bakin Umar ke da wuya, sai ya ce 'Yauwa ga
Umaimar ki maimata abin da kika ce a kanta, ni
kuma na shiga daki na dauko kur'ani mu yi alwala mu
dukka ukun mu dafa, Allah Ya wargaza mai karya.MAKWABTAKA 22
Sai na ji wata gagarumar fargaba yadda ku ka san
zuciyata zata fito waje. Na dafe kirji cikin rawar jiki
da rawar murya na tambaye su, ''Lafiya, me na yi?
Sai Salame ta aiko min harara sama da kasa, ta murguda

baki ta sake gyara damarar da ta yi ta shirin dambe.
Ta ce, ''Kai da ita dukka munafikai ne, bakinku daya, ko
me zaku fada min ba zan yarda ba, amanata kuke ci.
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi
masibatin wa akhlif ni khairan minha.
Addu'ar da na fara fada ke nan a bayyane, yayin da na
dafe kirji da hannu daya na rike kai da hannu
daya. Kan ka ce kwabo na rikice da kuka, yayin da Umar
ma ya fara hawaye don haushin kazafin da ta
yi mana. Umma ma ta fusata ta ce, ''Duk ku yi min shuru,
Salame wacce hujja gare ki ta cewa suna cin amanarki?
Salame ta rike kugu tana girgiza idanunta mursisi babu ko
digon kunya, ta dube ni ta juya ta dube
shi. Ta ce ''Ga su nan da ran Allah ba zan musu karya ba,
ko a gabana ko a bayan idona ba su da buri irin
su ga junansu su yu hira. Bini-bini sai ta shigo in ta ga
yana nan haka sai ta tarki cewa zata je gidan Lamijo, shi
kuma sai ya ce ku shirya in kai ku. Ta madubi ma lekenta
yake sai kuma ga lambarta a wayarsa daga ta yi flashin sai
ya kira, ya fice kofar gida ya yi mata waya. Kila ma suna
haduwa a wani
wajen...
Ba ta rufe bakinta ba sai na rusa kuka na ce,
''Tsakanina da ke Salame sai Allah ya isa, kin yi mana
kazafi don ni ban taba sanin kalar lambar Umar ba, ba
mu taba waya da shi ba...''
Umar ya dube ta cike da takaici, ya ce, ''Salame, ki ji
tsoron Allah, ke makira ce, kuma idan ba ki nemi
gafarar wannan baiwar Allah ba baza ki gama da duniya
lafiya ba. Zato kike yi kawai saboda shaidan
ya yi miki huduba a zuciyarki. Waya kuwa da kika ji ina yi
ba da wata nake ba illa kanwar abokina da aka turo
bautar kasa a nan Gombe daga Kano, ba tasan kowa ba a
nan na hada ta da wata mata ma'aikaciyarmu ta samo
mata gidan haya ta zauna.
Sunanta Aisha babu abin da ya hada sunan Umaimah da
nata. Sai Salame ta sake rikicewa wai ita za mu mayar
*yar iska, marar wayo shi yasa kwana biyu idan zata
dauki wayata sai ta ga bana so, don kada ta ga lambarsa
ne.
Takaici ya sa na fice ina sharbar kuka, na bar Umma da
sulhu. Ina shiga daki na fada kan katifa ina rusa kuka,
wayata ce ta yi kara, sai na ga lambar Lamijo.
Gabana ya sake faduwa, na san labari ya isa gare ta.
Na danna a sanyaye ina sauraron abin da zata fada min,
zagi ko kuwa rarrashi?
Na ji ta cike da fara'a sai ta ce min, ''Albishir! Albishir!!
Albishir!!! Har sau uku. Na tashi na goge hawaye na dafe
kirji na kagu na ji
abin da zata fada min.
Ta ce, ''Tafiyarku ta tabbata, an gama komai. Ki shirya
gobe ke da Hanif inji Alhaji mijina zai kai ku

Abuja ku yi passport da takardunku na ainihi (original) za
ku kai federal ministry of education da autentication.
Sai na yi ajiyar zuciya mai dadi, na kumshe ido, na zabura
na ce, ''Da gaske kike?
Alhamdu lillah
ke da mijinki Allah Ya saka muku da gidan aljanna. Na
gode, na gode. Godiya nake yi mata har ta gaji da
amsawa ta kashe wayar, sai na ji zuciyata ta dan yi sanyi
daga tafasar da ta ke yi.
Na tashi zumbur na fara hada *yar jakata ta tafiya, duk
da ba ta fada min kwanaki nawa zamu yi ba,
na san dai dole zamu kwana don haka kaya kala biyu na
dauka, da katuwar ambulan da na saka takarduna na
makarantun da na yi (original certificate).
Umma na shigowa na tare ta da farin ciki, na fara shaida
mata abin da Lamijo ta fada min yanzu. Sai ta
tabe baki ta harare ni. Ta ce, ''Ni ba a zaman munafunci
da ni da cin amana, biri ya yi kama da mutum, kwana
biyu sai na jiyo ki a daki kina ta waya wanda a da ba kya
yi.
To ni lafiya nake zaune da MAKWABTANA ba zaki zo ki
raba ni da su ba. Idan kin san irin haka zaki yi ta yi, to ki
hada kayanki ki yi gaba, shegen kwashekwashe ne da
yarda irin na Lamijo ta kwaso ki daga cewa wata daya an
shude watanni uku..
Ba ta rufe bakinta ba, sai na ji jiri ya kwashe ni don tashin
hankali. Na laluba bango na jingina na zauna
na rike kai da hannayena biyu na takure ina ta addu'a
Allah Ya yi min agaji, dan na shiga garari, na shiga masifa.
Ba ni da mafita sai Allah ne kadai zai fitar da ni.
Na kasa magana don ba ni da bakin da zan yi mata
bayanin komai ta yarda da ni. Ba ni da masaniya a
bisa wayar dare da ta ce ina yi, bayan Lamijo babu mai
kirana a duniya, ni ma ita kadai nake kira.
Sabon layi ne na siya saboda MAKWABTANA da kawayena
na Kaduna suna ta kirana suna yi min
maganar Abdul-Basi, wacce ta ke tayar min da hankali,
don haka na karya layin na watsar....
Umaimah ta ci gaba da sharce hawaye. Abdul-Sabur ya
sake luntsomowa cikin tausayinta,
kallonta kawai ya tsaya yana yi, yayin da zuciyarsa ta ke
suya tana konewa.
Yayin da Faduwa ce mai karfin halin yin magana.
Fadi ta ke, ''Allahu Akbar! Sannu yarinya, kin sha takaicin
rayuwa ashe.
Umaimah ta cije lebe ta kasa ci gaba da magana, har sai
da ta dauki lokaci mai tsawo ta yi ajiyar zuciya, ta ci gaba
da cewa.
''Rayuwa ke nan tana da wahala, fatanmu dai mu gama
da duniya lafiya. Yaro ya ji dadi idan na tuna
sanda nake karama ban san bakin ciki ba. Ga uwa ga uba,
ga *yar uwa, ga dan uwa, ga kawa ga saurayina.

Ba ni da aiki sai rawa da waka, walwala da nishadi kullum
amma dubi lokaci guda Allah Ya kwace duk
wannan farin cikin ya koma kadaici, ku san kowa nawa ya
kare, ba ni da komai, ku san kowa ya tsane ni. Allah mai
yadda Ya so da bayinSa. Na gode maSa a kowanne hali Ya
bar ni a ciki.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kinyi gaskiya yarinya,
Allah Yana jarrabar bayinSa ta kowacce
hanya. Ki ci gaba da tawakkali Allah Zai yaye miki komai
da izininSa, Ya hada ki da madadinsu, Ya dawo miki da
wasu daga cikin farin cikin da kika rasa.
Umaimah ta gyada kai cikin gamsuwa, ta ce, ''Haka ne, na
gode.
Faduwa ta ce, ''Yaya na ga kuna kokarin kammala labari
alhalin ba ki gama ba mu karshen labarin ba. Yadda aka yi
kika zo Malaysia da rabuwarku da su.
Umaimah ta ce, ''Ai kawai na fuskanci Ummar Lamijo ta
gaji da zamana so ta ke ta kore ni, *yar ce
take tausarta kullum. Na shiga daki na kwanta babu barci,
sai tunani da kuka har asuba.
Na tashi na shirya da sassafe ina jiran isowar Hanif da
Babansa. Karfe bakwai da rabi a cikin gidan ta yi musu,
suka iske Umma a zaune a tsakar gida, ni kuma na gama
shara ke nen. Muka gaisa da su na dauko jakata na rataya
na durkusa na yiwa Umma sallama ta amsamin da kyar.
Sai ta dinga fada tana sake nanatawa 'a yi dai a hankali,
kuma ko me mutum zai yi yayi bisa amana.
Da alama dai surukinta bai fahimce ta ba, amma ni na
fahimci abin da ta ke nufi, tunda na zama maci amana
zan kwacewa Lamijo miji ke nan. Shi kuwa bawan Allah
hidima yake yi min saboda dansa da matarsa da yake
matukar son abin da su ke so. Muka tafi hanyar Abuja
cikin hadaddiyar mota CRB ruwan zuma, sabuwa ce Gar!
A ledarta, sai kamshi da sanyin AC ke tashi. Hanif da
mahaifinsa suna ta
farin ciki annuri fal a fuskarsu, ina baya ina yake da kyar
nake kakalo hira da dariya, amma fa hawaye
na ke sharcewa a boye. Ba mu karasa Abuja ba sai Lamijo
ta kira shi, ta dinga zazzaga magana cikin daga murya, sai
na ga ya kalle ni ta madubi yayin da ya ce bari zai kirata
idan mun isa, yana tuki ne.
Ya yi sauri ya katse wayar, tun daga lokacin na ji ya daina
magana, da alama ransa ya baci, jikinsa ya yi sanyi, sai na
shiga fargaba kada fa zuga Lamijo suka yi ta shiga zargina.
Kai tsaye muka wuce Federal ministry of education daga
shigarmu Abuja, ba mu bi layi ba muka bibbiya aka buga
mana tambari a jikin takardunmu (stamp) shaidar zamu
yi karatu a kasar waje. Sannan muka wuce Ministry of
forin affairs suma kai tsaye ya wuce da mu kasancewar
yasan wasu daga cikin ma'aikatan don ya yi aiki sosai a
wurare daban-daban a nan Abuja.
Kafin la'asar har mun gama ya wuce da mu gidansa, da

yake unguwar Asokoro. Gida ne babba da get ga wajen
ajiye motoci, manyan faluka biyu da wajen cin abinci
(dinning area), dakuna hudu
kowanne da bandakinsa sai katon kicin guda daya. Mai
aikinsa inyamuri da matarsa a boy's kuarters, su ne masu
share gidan.
An share tsaf an goge, an yi mana girki an jera akan tebur
dan sun san da zuwanmu.
Muna shiga Alhaji ya nunawa kowannenmu daki daya
nasa da bandakai a ciki, kowannenmu ya
shiga don ya kimtsa kamar wanka da sallah. Da muka idar
muka fito dinnin table don cin abinci saboda muna jin
yunwa. Kunyar Alhaji da ladabi ya hana na zauna akan
teburi daya mu ci abinci, suka yi ta rokona na ki hawa mu
ci, sai Alhaji ya ce, Hanif ya zuba min ya kai min dakina.
Na shiga daki na ci abinci yayin da nake jiyo hirarsu a
falo. Can na ji Alhaji yana Magana a waya yana cewa.
''Lamijo me yake faruwa ne, wai Umaimah ba kawarki ba
ce? Waye ya zuga ki? To ni gaskiya bana son haka, kuma
tafiyar nan kamar ta tafi ta gama tunda an gama yi mata
komai. Idan kinga ba ta tafi ba to Hanif ma ba zai je ba ke
nan. Haba me yasa ku mata ba ku da tunani ne?
Tunda abun naki har da zargi to bari na bar gidan na je
hotel na kwana. Na bar ta da Hanif su kwana, gobe zamu
dawo da sassafe har mun gama abin da zamu yi''.
Inji Alhaji yake karadi a waya shi da matarsa,
kawata, aminiyata Lamijo, a kokacin da take tuhumarsa,
ta ke zargin kada ya ce yana sona ko mu ci amanarta a
Abuja.
Sai na dafe kirji na mike tsaye yayin da na ji tamkar ba a
raye nake ba, dama na hadiyi zuciya na mutu mana na
huta. Anya kuwa lafiya irin wadannan bala'ai suke ta rufto
min?
Duk mutumin da na amincewa sai ya ci amanata. Na
tambayi kaina da kaina, yayin da nake magana a bayyane.
'Me yasa kowa ya tsane ni yanzu alhali kuwa ada kowa
yana sona?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Na durkusa ina fada yayin da kuka ya hana ni sakat, na
kasa ci gaba da cin abincin, ga yunwa ina matukar ji ko
abincin safe ban ci ba, sai dan lemo da Alhaji ya siya
mana a hanya.
Hanif ne ya yi ta kallonsa a falo yana ta nishadinsa,
amma ni kadai a dakina ina ta juyi babu barci saboda
gagarumar fargaba da kunar zuci. Yadda
na ga dare haka na ga safiya na tashi da wuri na yi wanka
na takure a lungu gado. Hanif ne da sassafe yake buga
min kofa, wai na fito na zo mu karya kumallo, Babansa ya
yi waya ya ce mu shirya da wuri ga shi nan zai zo mu
wuce Gomben.
An shirya mana abin karin kumallo na gani na fada an
jera akan dinnin table. Tura abincin nan kawai nake yi a

cikina ba don ina jin dadin ci ba, sai saboda kada yunwa
ta kashe ni ko kada Hanif ya gane ina cikin halin damuwa.
Hira kawai yake yi min cikin farin ciki da dokin zamu je
Malaysia, sai ya ce da ni ya ga kamar yanzu ban damu ba
alhali a da har na fi shi dokin tafiya. 'Eh ko 'a'a kawai nake
ta binsa da shi har muka kammala, sai muka ji tsayuwar
motar Alhaji ya iso. Ya aiko ya ce ace mu fito ba zai shigo
ba.
Muka debo kayanmu muka fito muka iske shi a zaune a
cikin mota, gaba daya ya daina wannan fara'ar tasa. Cikin
sanyin jiki na gaishe shi ya amsa min cikin sanyayyiyar
murya, muka shiga mota muka tafi.
Hanif ne kadai mai walwala da surutu ni da Babansa dai
to ga mu nan ne dai kawai babu mai son yin magana.
La'asar sakaliya suka sauke ni a kofar gidan Umma na yi
musu godiya da sallama na shiga gida su kuma suka
wuce.
Na yi mata sallama, fuskarta babu fara'a ta amsa min, na
shaida mata mun iso, ko ta kalle ni ma ta dauke kai.
Sumi-sumi na shiga dakina sai na firgita da na ga an hada
min dukkan kayayyakina da na baza a gidan a lungu daya.
Kamar takalmana, sosona daga bandaki da dai sauransu.
Katifar da na lallaye da zanin gado an jingineta a tsaye.
Daga nan jikina ya ba ni zamana ya zo karshe a gidan nan,
don haka na shiga tunanin inda zan nufa,
Abu na farko da na fara yi shi ne, na ware kayan da na fi
so kamar kala biyar na bar sauran don ban san yadda zan
iya kinkimar rusheshiyar akwatin nan na shiga gari ba. Na
zuba a karamar jaka, soso, brush da makilin gami da
takalma kala biyu. Saura na dura su a cikin babbar
akwatin na rufe na jingineta a gefe. Na shimfida katifar na
hau na zauna a hankali. Ina cikin fargaba musamman da
na ji tahowar Umma.
Tana shigowa sai ta harare ni ta harari katifarta da na
shimfida ta tabe baki ta ce, ''Umaimah, yanzu
dare ya yi idan Allah Ya kaimu gobe ki shirya da sassafe ki
koma garinku ki jira fitowar tafiyarku a can. Bana son
zamanki a gidan nan tunda kin fara jawo min fitina, ina
tsoron rayuwa, musamman *yar
autata da nake son dorewar zamanta a gidan mijinta.
Ta zaci zan razana da maganganunta sai taga ko kadan
ban rude ba. Na ce mata, ''To Umma Allah Ya nuna mana
goben lafiya, na gode ma da karamcin da aka yi min,
Allah Ya saka da alkhairi''.
Ta fice a fusace, tana fita hannuna yana karkarwa sai na
kira Lamijo don na sanar mata gobe zan koma gida. Na yi
mata godiya da sallama na roketa idan tafiyarmu ta zo ta
sanarmin ta waya. Don na ga akwai waya a Dukku zan
dinga fitowa ina kiran ta kullum ina jin labarin tafiya.
Sai taki amsa wayar, har ta fara katsewa (rejecting), ina
kira sai ta katse. Muka dinga haka fiye da sau
goma, mamaki cike da zuciyata. Daga karshe sai na tura

mata rubutaccen sako na yi mata duk wadannan bayanai.
Har gari ya waye ba ta ba ni amsa ba. Na daina kuka
saboda masifar ta yi masifa, addu'a kawai nake yi ina
neman mafita, ina so Allah Ya musanya min da muhallin
da ya fi irin wanda nake ciki daraja da kwanciyar hankali.
Na shirya na fito rataye da karamar jakata na bar babbar
a dakin. Na durkusa a gaban Umma na gaisheta..
Na ce, ''Zan tafi Sai ta hararenim ta ce, ''Ban ganki da
kaya ba?
Na yi murmushin takaici, na ce, ''Zan je na samo mai tasi
ne yanzu zan dawo. Ta tabe baki ta ce, ''Kina da kudin
motarko?
Na yi murmushi na ce, Eh Ban sani ba ko idan na ce ba ni
da shi zata ba ni ne ko ba banin zataiba, oho. Ba ni da
kudin kirki a jakata, *yan canji ne kawai wanda bai wuce
ya kai ni tasha ba.MAKWABTAKA 23
Ina fitowa na ci karo da Salame da
mijnta
Umar, har yau inajin haushin kallon
banzar
da ta yi min, ta yi tsaki da tsartar da
yawu ta
bude gaban motar mijinta ta zauna,
ta daka
masa tsawa. Ta ce, ''Ja mu je mana,
wa kake
jira?
Ya fisgi mota ya tafi suka bar ni, sai
a lokacin
na fara kuka. Ina tsaye a kofar gida
na dubi
gabas da yamma, kudu da arewa ban
san
inda zan nufa ba.
Na yi ta tafiya da kafa na nufi hanyar
tashar
garinmu da nisa sosai, amma da kafa
na je.
Sannan na tuna ba ni da kudin da zai
kai ni
garinmu.
A bakin tasha a kofar shagon wata
tsohuwar mata mai siyar da abinci da
ma'aikatanta da yawa, na zauna na
huta.
Sannan na karasa gabanta na
durkusa a
gaban Hajiyar na gaishe ta ina
hawaye,
na sanar mata ina so na dinga tayata
aiki, na
ce amma ba ni da wajen zama.

Da farko ta ki amincewa, amma da
kawarta
ta ce, ''ki dauki kyakkyawar yarinyar
nan ko
don saboda ita ma za ki sami samu
masu
saya kin san mazan nan suna da son
kyawawa. Ai wannan yarinyar kadara
ce kar
ki bari ta kubuce miki. Sai na ji
zuciyata ta
harba, na kasa gane abin da matar
nan ta ke
nufi. Nan da nan Hajiya babba ta
yarda ta
umarce ni da na shiga cikin shagon
da
kayana, sai da magriba suke tashi sai
mu
dunguma mu tafi gida.
Na shiga shagon kujeru ne da tebura
yayin
da duk masu dafa abincin sun yi
kama da
karuwai, suka hau yi min kallon
banza
saboda hassada. Dana ajiye jakar
kayana a
loko sai na koma bakin
baranda na hau kan benci na zauna,
jikina
sanyi kalau.
Daya daga cikin ma'aikatan ce ta yi
min
tsawa wai na zo na karbi abinci na
mika ciki,
ina ganin masu siya suna ta shiga
ciki na
sami waje na zauna.
Sai na tashi jikina yana rawa na karbi
farantin abincin na shiga ciki ba tare
da na
san wanda zan ba wa ba, maza ne
dankar a
ciki. Kallona suke sama da kasa, duk
da na
yafa gyale. Amma sai duk na tsargu.
Nan da
nan na juya waje na koma wajen
matar da
ta aiko ni na ce wa zan ba wa?
Ta harare ni ta ce, ''Ki ce ina Ali Ali

mai
mangyada?
Sai na koma ciki muryata na karkarwa
na
tambaya,
sai ya yi dariya ya ce, ''Zo nan *yar
shila, ga
ni nan. Zagayo nan. Na je na ajiye a
gabansa
sai na ga ya kawowa hannuna cafka,
na yi
sauri na zame, sai suka kwashe da
dariya
shi da abokansa. Su ka ce,
''Wannan sabuwar zuwa ce dai ko?
Shi yasa
ba ta san dawan garin ba.
Ali Ali ya ce, ''Haka ne, bakuwa ce
dan ko jiya
ma na zo ba ta nan. Ke yarinya ki
saki jikinki
da mu, mune
masu yi muku ciniki, gara ma ki saba
da mu
don a jikinmu zaki sami abin duniya,
don shi
kika fito nema. Idan kuwa kina
bukatar
manda sai ki bayar da gishiri.
Yana maganar yana kanne min ido
kamar
tsohon maye.
Na shiga zargin anya kuwa ban fada
mugun
hannu ba?
Anya ba a cikin karuwai nake ba?
Ai kuwa sai na tsinkayo maza suna
kaiwa
mata cafka, duk wacce ta zo ajiye
abinci sai
na ga maza suna wawurarta. Da aka
ce na
zo na kai abinci a karo na biyu sai na
sake
lullube jikina na dauki farantin
abincin na
mikawa wani Alhaji mai katon ciki da
gemu,
ga shan taba.
Yana ganina sai ya zabura ya ce,
''Wai Allah!
Wannan halittar fa daga ina? Lallai

Hajiya ta
yi tsintuwa mai kyau. Ta zo mu yi
magana ko
nawa ne zan biya don na samu
wannan
yarinya.
Ya dinga dagamin gira alamar iskanci
tsantsa a kansa.
Rana ta yi aka ce na je na zubo
abinci da zai
ishe ni na zo na ci akan baranda. Ina
kusa
da Hajiya babba ta shiga yi min
nasiha da
lallashin cewar, na kwantar da
hankalina na
saki jiki da abokan
cinikayyarmu. Na kasa gane me ta ke
nufi, in
bari maza su ringa taba ni yadda
suke
tattaba sauran ko
me...?
Abdul-Sabur ya girgiza kai yayin da
takaici ya
hana shi magana, sai cika yake yana
batsewa kai ka ce shirin dambe yake
yi.
Faduwa kuwa salati ta ke yi tana
zabura
tana dafe kirji.
Umaimah ta langwabar da kai, ta ce,
''Da na
idar da sallar la'asar sai na rataya
jakata na
zo na durkusa a gaban Hajiya babba.
Na ce, ''Ki ba ni kwatancen gidanki
zan je na
sanarwa uwar dakina cewar na sami
aiki a
wajenki''
Ta girgiza kai ta ce, ''Mai zai hana ki
bari sai
gobe ki je da wuri zai fi sauki. Na
girgiza kai
na ce, ''To, bari na yi sauri na je na
dawo
kafin ku tashi a nan kusa ne
unguwar.
Ta ce, ''To ajiye jakarki mana, tunda
yanzu za

ki je ki dawo.
Na rasa wannan wayo na matar nan,
ko da
yake bai kamata na yi mamakin
gogewarta
akan hikimomi irin haka ba, tunda ta
manyanta, kuma gashi idanunta a
bude
suke tas!
Na ce, ''Ai kayanta ne zan mayar
mata na
debo nawa, ban zaci zan sami aikin
ba zuwa
dai na yi na tambaya, yanzu da na
samu shi
ne zan je na sanar mata.
Ta ce, to na je na dawo da wuri, na
sauke
ajiyar zuciya da na ji ta ambaci haka,
na
tashi jikina yana
bari kai ka ce cafko ni za a yi, sai
sauri nake
yi kamar zan kifa ina yi ina waiwayen
baya.
Na haye acaba don ina tunanin kudin
jakata
zai ishe ni na biya shi.
''ina za ki je?
Inji Faduwa.
Umaimah ta ja fasali, ta ce, ''Wallahi
ban sani
ba, sai da mai acaba ya fara tafiya
yana
tambayata ina zai kaini?
Fiye da sau uku sannan na fara
tunanin inda
zan je.
Can na ce, ''Ka kai ni ma'aikatar ilimi
(ministry of education). Koda ya
tambaye ni
wacce unguwa ban sani ba.
Sai ya ce, ''Koda yake ita ce dai guda
daya,
bari na kai ki can...
Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya
ce, ''Me
zaki yi a ministry of education?
Tambayarsu zancen tafiya zaki yi?
Ta girgiza kai, ta ce, ''Na san mijin
Lamijo a
can yake aiki, sannan ne ina fadar

sunansa
za su san shi,
wajensa zan je na tambaye shi ranar
tafiya.
A bakin get dan acaba ya ajiye ni na
biya shi
na shiga ciki a tsorace, ina tsoron
kada a
koro ni ko ace min ba nan yake ba.
Har kasa na durkusa na gaishe da
masu
gadi, daga dukkan alamu sunji dadin
gaisuwar da na yi musu,
suka amsa cike da fara'a. Na
tambaye su shi
da cikakken sunansa Alhaji Nasir
Nafada.
Sai suka ce ''yana ciki ga motarsa
ma bai
tashi daga aiki ba.
Na ce, ''Ina ne ofisshinsa?
Suka fara kwatanta min da hannu, sai
suka
fuskanci ban gane ba, daya ya taso
da sauri
ya ce na biyo shi a baya zai kai ni
can.
Akan bene yake can ciki, ya kai ni
har cikin
ofishin gami da sanar masa, ''Alhaji
ka yi
bakuwa.
Yana dago ido sai ya ga ni ce, don
haka sai
na ga ya dan firgita kuma ya cika da
mamaki.
Ya ambaci sunana, sannan ya ce na
shigo ga
kujera na zauna. Na yi wa maigadi
godiya ya
fita ya rufo mana kofa. Maimakon na
zauna
sai na durkushe a gabansa na barke
da
kuka mai tsanani ina magana, amma
kuka
ya hana ni ya fahimce ni. Ya tausaya
min
matuka, hankalinsa ya tashi, har
kwalla ta
cika masa ido. Rokona yake na tashi
na

zauna, na daina kukan na nutsu..
Da kyar na tsagaita da kukan na tashi
na
zauna, shi ma ya zauna a tasa
kujerar yana
ta ba ni hakuri
cikin Fulatanci muke magana, shi ma
bafillace ne.
Da kansa ya ce, ''Duk na san halin da
kike
ciki Umaimah, wannan abu da ya faru
da ke
kulalliya ce aka hada miki, kawarki
Lamijo
zuga ta aka yi amma ita ai mai sonki
ce.
Na sharce hawaye na ce, ''Ummarta
ma ta
kore ni daga gidanta shi ne na zo na
shaida
maka bana gari zan koma Rugarmu
Dugge,
ga shi babu waya balle na ji ranar
tafiyarmu.
Ko zaka fada min
takamaimai ranar da zamu tafi na
dawo, ko
kuma na karbi lambarka idan har ba
zai
zama matsala ba na dinga fitowa
daga
Dugge na zo Dukku na dinga kiranka
ina jin
labarin tafiya?
Sai ya girgiza kai don tausayi, ya yi
shiru
yana kallona, har tsawon wani lokaci
mai
tsawo. Can ya dauko wayarsa ya
buga, sai
na ji ya ambaci, ''Ranka ya dade
permanent
sectery na kira ne game da maganar
tafiya
karatun yaran nan Malaysia. Ka ce a
cikin
satin nan ne wacce ce takamaimiyar
ranar
tafiyar? Saboda akwai yarinya daya a
nan
*yar Dugge ce, zata koma Ruga ba
su da

waya balle ta sani ta fito. Sai ya ce,
''Rana ita
yau ne tafiya, talata, amma ranar ake
so su
hallara a Gombe za a dibe su a mota
a kai su
Abuja su kwana litinin a sake
tantance su a
can, sannan talata su wuce.
Da ya gama wayar ya yi min duk
wadannan
bayanai, sai naji sanyi a zuciyata,
kamar
zanyi tsalle. Sai a lokacin ya ga
fara'ata shi
ma da alama ya ji sanyi a ransa.
Ya miko min lemo da ruwa ya ce, na
sha ya
shiga tambayata me ye takamaiman
tarihin
rayuwata?
Na langwabe kai na ba shi tarihina
kakaf da
inda na hadu da matarsa har zuwa
rana irin
ta yau da muka rabu da ita, wanda
bansan
dalilin
rabuwarmu ba. Sai ya girgiza kai ya
ce, ''Na
tausaya miki Umaimah, ki yi hakuri
Allah
Yana bayan mai
gaskiya. Ki yi min alkawarin idan kin
je
wannan kasar zaki kama kanki, ki rike
mutuncinki, ki yi
abin da ya kai ki, ki dawo gida lafiya.
Idan
kika yi haka insha Allah sai kin fita
daban da
*yan rugarku. Sai kin zama abar
kwatance a
garinku,
zaki zama abar alfahari ga gwamnatin
garinmu.
Idan kika yi min wannan alkawari zan
ji
dadi, kuma zan taimake ki kamar
yadda
dolena na taimaki
dana na cikina Hanif.

Sai na sulalo na durkusa a gabansa.
Na ce,
''Allah Shine shaidata, idan na tafi
can ba ka
ganina Allah Yana ganina, na yi
alkawarin
zan kama mutumcina,
abin da naje yi shi zan yi insha Allah
Baba ba
zan ba ka kunya ba.
Sai ya ji dadi ya yi murmushi, ya ce
na tashi
na zauna.
Na mike tsaye na duka na ce, ''Dare
ya fara yi
zan tafi garinmu don ba ni da inda
zan
kwana a nan.
Ya ciro bandir din kudi mai yawa ya
miko
min, sai hannuna ya hau karkarwa
don
razana da yawan
kyautar. Na yi godiya na fito akan
ranar
lahadi in fito da wuri na zarto gidan
gwamna a nan zamu taru a yi mana
jawabin
karshe.
Da na fito daga ofishin na duba kudin
*yan
naira dari-dari ne dubu goma ke nan.
Tasi
na hau ban kula masu acaba ba, na
nufi
Dukku daga Dukku na hau motar
garinmu.
Daga bakin garin acaba ne dole zai
shiga da
kai cikin rigagenmu. Ban isa
Dugge ba sai bayan sallar isha'i, sai
*yan
gida suka yi mamaki da ganina

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment