Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsananin son
juna. Sai na ji garin ya fita a raina ma gaba daya,
gara na koma Kaduna. Na shirya na tafi ba tare da hutu
ya kare ba...
Abdul-Sabur ya yi shuru yana kallonta, can ya ce,
''Amma me ta ce masa? Anya kuwa ba hadaku ta yi ba?
Umaimah ta ce, ''Hadamu ta yi mana, ba abin da na fada
mata ta je ta fada masa ba. Ashe ce masa ta yi na ce ya
fita harka ta, ni yanzu ba ajinsa ba ce, sai dan boko. Wai
na ce me zanyi da almajiri, gardi mai bara?
Faduwa ta ce, ''Subhanallahi. Ita kuwa a wanne dalili ta yi
miki haka?
Kafin Umaimah ta yi magana, Abdul-Sabur ya ce,
''Hassada don ita ba ta da saurayi?
Umaimah ta runtse ido ta zubo da hawaye mai zafi ta ce,
''Ashe ita ma sonsa ta ke. Yadda ta ke zuga ni haka a can
bangaren ta ke ta binsa tana min kazafi kala-kala, har da
cewa, an zubar min da ciki a birni.

Har sai da ya ji babu abin da zai yi da ni sannan ta yi
kokarin cusa kanta wajensa, ba shi da zabi don babu
yadda zai yi, amma zancen so ni ce kadai macen da yake
so a duniya. In ba rashin wayewa ba me yasa ba zai kira
ni ya zaunar da ni ya tambaye ni ba, ko ya aiko
mahaifansa su bincika?
Ni kuma da yarinta sai nayi ta boyewa Yafindona ko ta
tambaye ni idan taga ina damuwa sai in ki fada.
Shekara ba ta dawo ba aka zo min da labarin anyi auren
Matawata da Ilahna. Suma ne kawai ban yi ba, amma na
gigice, sai da Nasiba ta rike ni dan da faduwa zan yi. Kuka
muke ta yi ni da Nasiba tun Yaya Abdul-Basi yana ba mu
hakuri, har ya ji haushi ya kwakkwayemu, ya ce, ni da
nake karatu ina ni ina
maganar saurayi a kauye, almajiri dan Ruga? Ina ma
auren zai yiwu?
Ni da zuciyata ne kadai muka san halin da muke ciki,
wannan bakauyen almajirin ya fi min samarin Birni sai
dubu, don shine farin cikina. Duk tsananin bacin ran da
nake ciki idan na ga Ilah sai na ji sanyi,
don zai lallashe ni ya ba ni labaru masu dadi.
Wannan shi ne cin amana da musgunawar da
MAKWABTANA suka fara yi min a rayuwa....
Umaimah ta sa gefen hannunta ta sharce hawaye mai
radadi.
''Yi shiru daina kuka. Inji Abdul-Sabur da Faduwa, Su ma
tausayinta ya rufe su.
Ta ce, ''Ban koma garinmu ba, har sai da na shiga aji
hudu na sakandire shi ma ba zuwan dadi ba ne, kawai
Yaya Abdul-Basi ya ce mu zo gida ana nemanmu, ashe
Yafindonmu ce ta rasu.
''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Inji Faduwa da AbdulSabur, yayin da kuka ya barkewa Umaimah.
Ta dade tana yi kafin su lallashe ta, ta ci gaba da labarin.
Ta girgiza kai ta ce.
''Da aka yi sadakan bakwai dole muka shirya zamu koma
Kaduna, saboda watan haihuwar Nasiba ne,
ta samu ciki da kyar ya zauna mata.
Ilah ya zo ya yi min gaisuwa a tsaitsaye, amma Matawata
ga ni ga-ta, a jikin zanar gidan su Ilah ta ki yi min magana.
Ciki ne ma da ita a lokacin, har wata rangwada ta ke yi
tana shafa cikin. Wai har na
zama abar zolaya a wajen Matawata duk amincin da ke
tsakanina da ita.
Zuciyata sai ta yi ta tafasa idan na jiyo masoyina Ilah da
aminiyata Matawata suna hira a gidansu. Tunda a gidan
iyayensa aka ba su daki, mu kuma katangar gidan mu
daya don haka ana jiyo hirarrakin da ake yi a tsakanin
gidajen biyu.
Muka koma Kaduna muka yi jugum-jugum cikin
damuwa, mu dukkanmu. Bayan sati uku dai-dai da
rasuwar Yafindo sai haihuwa ta tasowa Nasiba aka kaita

asibiti. Allahu Akbar haihuwar ta zo da
matsala, likitoci suka yi iya kokarinsu wajen ceto uwar da
*yar abu ya ci tura..
Sai kuka ya hana Umaimah ta ci gaba da magana.
Faduwa ta zabura ta ce, 'Ba dai ta rasu ba?
Umaimah ta gyada kai cikin kuka mai tsanani. Ta ce,
''Yayata Nasiba ta rasu ita da *yar cikin dukka.
Sai Faduwa ta rungume ta ita ma kukan ta ke taya ta don
tausayi. Abdul-Sabur ya yi ta girgiza kai
kalmar ''Sorry-sorry. Kadai ya ke ambato.
Umaimah ta matse hawaye ta gyara zama ta ci gaba da
cewa, ''Na yi kuka, har yau ina kan yin kuka amma ba
zasu dawo ba, sun tafi, sun tafi kenan. Na damu matuka,
amma sai Yaya Abdul-Basi ya fi ni damuwa, har na fi shi
tawakkali, shi har sai da aka yi ta rike shi don ya rike
makara ya ki ya saki, da za a saka ta a kushewarta. Ta sha
addu'a kuwa a wajensa, ya ce, ''Nasiba, ke ce matar da na
taba so, nake so, kuma zan dauwama ina so a duniya. Ki
sani GANGAR JIKINMU ce kawai zata rabu, amma ruhin
mu yana tare..''
Hawaye ya yi ta kwaranyowa daga idanuwan su dukka
ukun. Har zuwa lokaci mai tsawo kowannensu yana
matsar hawaye, sannan Umaimah ta ci gaba da magana.
''Aka kai Babangida Gombe wajen kakarsa wato Hajiyan
Abdul-Basi, ni kuma da kayana kacokan aka dawo da ni
Dugge, sai kunci ya karu. Na dawo gidanmu dakin
Yafindo bata duniya, sannan babu kawata abokiyar hirata
Matawata, babu masoyina mai saka ni farin ciki, wato,
Ilah.
Allah Ya sa Sabitu ya zo a lokacin, da shi kadai nake hira
na dan ji dadi, don shi kadai ya rage min a
duniya, daga shi sai Baffana. Baffa kuwa ya tsufa, ciwociwo kala-kala. Kishiyoyin Yafindo Inna da Nene suka saka
ni a gaba suna ta yi min habaici wai karya ta kare dan
birni ya dawo kauye.
Kullum sai su yi ta zafuta ta da dungure kai, dole sai na
fito daga daki na taya su surfe da girki. Na ga
tashin hankali don na manta yadda ake surfe da cin
gabza. Yaya na iya, dole na yi ta cusawa cikina duk abin
da na samu, don kada yunwa ta kashe ni.
Matawata ta haihu, yawanci ma a gidanmu aka yi girkegirke da taron *yan suna, sai na yi mamaki
da na ji sunan jaririyar, wai MARIYA, sunan Yafindona ne
don dai nasan danginsa kakaf da nata babu Mariya. Ba su
gayyace ni ba suna haka tashin hankali ya hana ni fitowa
daga daki, sai kuka nake yi yadda ku ka san na tsaga kasa
na
shige ta rufe ni na huta don tashin hankali.
Hakika na ji haushin cin amanar da aka yi min, na shiga
zargin ni ce ban sani ba watakila tuntuni ma suna son
junansu. Kamshin suyar naman rago da dan Akuya har
cikin

dakina, amma ko hanji ba a san min ba, raina ya yi ta
biyawa. Babban tashin hankalina ma shi ne
gulmata da aka dasa kungiya-kungiya ana ta yi,
wai na ki auren bakauye na koma birni, ga shi na rasa dan
birni na dawo kauyen,
Ilah ya yi aurensa yanzu bakin ciki zai kashe ni na ma kasa
fitowa cikin jama'a. Su Nene ne masu kara zuga
magulmatan, koma dai mene ne na fauwalawa Allah
komai, Shi ne mai sakayya.
Ba'a yi watanni shida ba kuwa Allah Mai komai da kowa
sai da Ya yi min sakayya a bisa abubuwan da duk aka yi
min...
Faduwa ta dafa kirji tare da yin ajiyar zuciya, ta ce, ''Me
ya faru da su?
Umaimah ta yi nata takaitaccen murmushin, ta ce,
''Uhum, Allah ba azzalumin bawanSa ba ne. Ashe tunda
Ilah ya auri Matawata ba ya jin dadin zama da ita, bayan
rashin son da yake yi mata ta cika makirci da hada
husuma. Ta hada shi da *yan uwansa saboda fada da take
yi da matansu, ta raba shi da abokansa ta dawo tana hada
iyayensa fada.
Kullum ba ta shiri da surukarta rashin kunya ta ke yi mata
sosai, shi kuma Baffansa yana bin bayan Matawata don
haka sai a yi ta rigima, Ilah mai hakuri ne yana zaune ba
ya magana duk abin da
zata yi ba ya iya tsawatar mata. Mahaifiyarsa har kuka ta
ke tana cewa, ta yi asarar haihuwa, idan
har danta zai auro macen da zata yi mata rashin kunya a
gabansa ya kasa magana. Allah kada Ka tsayar da ni ranar
shaida, an ce bokaye ta ke bi ta shanye shi, ba ya ganin
laifinta sam! Amma Allah Ya fi ta, sai kuwa aka kama ta da
laifin kwartanci ita da tsohon saurayinta lawwali.
Gari gaba daya sun shaida, har aka rakota gida da waka
ana ga kwartuwa.
A take Ilah ya yi mata saki uku, ina daga dakina nake jiyo
komai. Ban fito ba ma balle ace tsegumi sai na ji a raina
ban ji dadin wannan bakin al'amarin ba. Domin dukkan
musulmi dan uwan musulmi ne, Allah Ya rufa mana asiri,
Ya sa mu gama da duniya lafiya, Ya sa mu fi
karfin zuciyarmu.
Abdul-Sabur da Faduwa suka amsa da ''Amin''.
Umaimah ta kurbi ruwan sanyi ta dago da ido ta dube su,
ta yi murmushi don ta ga sun kammala
hankalinsu kacokam a kanta, ita suke kallo.
Ta ci gaba da cewa, ''Ai ba'a yi wata ba sai na ji an ce ga
Ilah can da Baffana a wajen Baffana suna maganata a
aure, Ilah har yana kuka yana bada hakuri.
Na ji zuciyata ta fusata na kudiri niyyar duk wanda ya kira
ni akan maganar sai na fadi ba dadi, kuma
ba zan yarda ba, don a lokacin ko ganinsa bana son yi.
Ina cikin tunani ne na ji Baffana ya kwallamin kira,
na saka hijabina na fito na same su a zaure. Na durkushe

a gefe na gaishe su, sai Baffana ya fara bayanin.
Ya ce, ''Ga Ilah ya dawo daman makircin Matawata ne ya
raba ku. Na girgiza kai na ce, ''Baffa ka yi min afuwa ka
bar maganar nan, don maganar nan ba mai yiwuwa ba
ce. Na hakura da Ilah tuntuni, ya je ya auri wata.
Wato sai da ya rasa Matawata zai tuno da ni? Ai ba a 6ari
a kwashe dukka.
Nan fa Baffana, Ilah da Baffansa suka hau dogon fillanci,
ni wata kalmar hakurin ma sai a ranar na taba jinta a
fullanci. Suka yi ta magiya Ilah yana sake fada min duk
abubuwan da ya faru tun farko.
Wai ashe sanda na aike ta wajensa sakon da ta fada masa
daban ne ba wanda na fada mata ba ne, cewa
ta yi na ce na fi karfinsa yanzu, ya cire ma maganar aure
a tsakaninmu. Sai ya ce tace min ya gode tunda
wulakancin da zan yi masa kenan.
Sai ni kuma ta dawo ta ce min, ya ce, me zai yi da ni na je
birni na zama *yar iska ragowar maza? Sai a lokacin ya
fadi duk abubuwan da ta fada masa a kaina, ni ma na
fada muka gane Matawata ce munafuka, sai zuciyata ta yi
sanyi na amince zan aure shi. Muka watse daga zauren
kowannenmu
cike da farin ciki.
Dare, Safe, da yamma Ilah yana wajena, koda yaushe sai
ya zo zance, hade da hidimomin da ya
saba yi min tuntuni. Kamar: atamfa ce, mangoro, rake,
kaji da dai sauransu.
Ita ma Matawata tana jiyo hirarmu da shewarmu daga
zaurensu, don gidanmu ne a tsakiyar nasu.
Bakin ciki ya rufe ta, ta rasa inda zata saka kanta.
Rannan har da fitowa tana zage-zage tamkar
mahaukaciya, yara kuwa suka hau yi mata wakar
kwartuwa. Idan aka yi sata ko kwartanci a kauye ka shiga
uku, gara ma ka bar garin zai fiye maka
sauki.
Muna ta shirye-shiryen aurenmu Ilah ya siyo siminti ya ce
zai sumulce bangon dakina sannan ya yi dabe a kasa,
saboda na saba da gidajen birni. Muka shiryawa kanmu
rayuwar jin dadi ta aure, irin tamu ta talakawa dai, har
yake cewa yana so ya koma Kaltingo da zama wani Alhaji
da ya zauna a gidansa ya ce zai bude shago ya dinga jire
masa.
Muna tunanin nan da wata uku a yi aurenmu.
Allah Mai yadda Ya so da bawanSa, ashe dai Ilah ba mijina
ba ne har abada.
Faduwa da Abdul-Sabur suka zabura suka ce, ''Shi ma ya
rasu?
Umaimah ta matse hawaye ta ce, ''Ilah bai rasu ba,
har yanzu yana nan a raye, koda yake yanzu ban san halin
da suke ciki ba. ''To me ya faru? Abdul-Sabur ya tambaya
cike da zumudi.
Ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa, da alama dai tana jin

ciwon tuna abubuwan da suka faru da ita ne a baya.
Faduwa ta shafa kafadarta tana jijjigawa, kamar me
lallashin jariri. Kalmar, ''Ma'alesh, ma'alesh''. Ta ke ta
ambatowa, ma'ana 'yi hakuri'.
Umaimah ta dago da jajayan idanuwanta ta dube su, ta
ce, ''Kun san me ya faru? Baban Abdul-Basi
ne ya dawo wajen Dagacin garinmu aka kira Baffana aka
yi shawara, wai na maye gurbin Yayata marigayiya.
Ma'ana na auri Yaya Abdul-Basi, babu wanda bai amince
ba a cikinsu. Kwatsam ni da Ilah muna zaune wannan
bakin labarin ya zo mana muka gigice nan da nan sai
kuka ya barke mana.
Mun yi tunanin guduwa ma dai muka fasa, Ilah ya yi min
nasiha ya ba ni hakuri, na yi iya kokarina a
fasa auren nan aka fi karfina.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ba kya ganin auren
Abdul-Basi ya fi miki Ilah, tunda Abdul-Basin
kin san shi, kin san halinsa, yana da kirki?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba maganar kirki muke ba
kadai, maganar so da shakuwa shi ne aure.
Faduwa ta ce, ''Haka so yake ba ruwansa da kudi ko
birni''.
Umaimah ta ce, ''Son da nake yi wa Yaya Abdul-Basi na
*yan uwantaka ne ba na aure ba, Ilah kuwa shi ne farin
cikina, shi ne abinda nake tunawa na ji dadi a zuciyata.
Daga dukkan alamu Yaya Abdul-Basi ma ba ya son hadin
nan, an fi karfinsa ne, babu yadda zai yi.
Amma shi ma ya kasa cire Nasiba a ransa.
Aka tarka ta mu aka yi auren aka dawo da ni gidan nan
dai na Nasiba, ba a dawo da Babangida ba
wajena, saboda Abdul-Basi ya mayar da ni makarantar
boko, aji biyar. Yana kai ni da safe na dawo a motar haya
idan an ta shi, sai dare yake dawowa.
Bai taba kusanta ta ba, wata da watanni ina dakina yana
dakinsa. Ina tunanin Ilahna yana tunanin
Nasibarsa. Ya fada min baro-baro cewar shi fa Nasiba
yake so har yanzu, da zata dawo su zauna da ya fi masa.
Ni ma na fada masa da zai sake ni na koma wajen Ilahna
na zauna da ya fi min zama a gidansa.
Bai damu ba nima ban damu ba da maganar da muka
fadawa juna saboda kowa gaskiyar abin da yake ransa ya
fada ke nan.
Ba ya damuwa da girkina, balle kwalliyata, haka ni ma ba
na damuwa da na yi masa komai.
'Zo na kai ki makaranta, ungo kudin makaranta, karbi
kudin cefane. Shikenan maganar da ta ke hadamu. Hakan
ya fiye min dadi a rai ni kuwa. Daga baya ya fara warewa
yake yawan shiga harka ta, yawan jana da hira da kai ni
unguwanni wuraren shakatawa. Ya mayar da ni islamiyya,
ranar asabar da lahadi yake kai ni ya dauko ni, ya dawo
da yi min home work da dai sauran kulawa.
Ni ce nake ta baudewa don ban fitar da ran komawa

wajen masoyina ba Ilah. Da ya dau hutu
ya kai ni gidansu Gombe, muka ga Babangida, ya girma
yana zuwa makaranta. Daga nan na roke shi
ya karasa da ni Dugge, kai tsaye ya ce 'a'a idan dai su
Baffa ne zai je ya gano su ba sai na je ba' wai shi
nan da tsiya kishi yake, ya san Ilah nake so na je na gani.
Na yi ta kuka da ihu har sai da surukata ta ce, ya tashi ya
kai ni garinmu na kwana biyu sannan ya
koma ya dawo da ni. Ya dinga harbamin harara da ya ga
ina murna a mota saboda tsananin kishi.
Ai kuwa mun kai musu goma ta arziki, kayan abinci, ya
diddika da atamfofi, gidanmu da gidan Dagaci. Da aka
gama gaggaisawa sai Abdul-Basi ya tafi ya barni. Kudi mai
yawa na kunso na kawowa
tsohona a dunkule a boye na ba shi, ya yi ta mamaki yana
tambaya ta ina na samo kudin nan?
Na shaida masa kudin makaranta ne da ragowar kudin
cefane nake tarawa. Ya yi godiya ya shi min albarka ya
yiwa mahaifiyata da yayata addu'a Allah Ya sada su da
rahama.
Na gyara zama na tambaye shi Ilah, sai na ga ya girgiza
kai ya tabe baki, ya ce, 'Ilah sai addu'a Allah
Ya hadashi da jarababbiyar mata!. Ina jin haka gabana ya
yanke ya fadi, na ce, 'Lafiya?
Baffana ya yi shiru can ya dago ya dube ni, ya ga yadda
na dimauce. Ya ce, 'Ki rike mijinki, ki rabu da
Ilah ba mijin da zaki yi tunanin za ki aura ba ne.
Sai na sulale kamar zan kwanta na sume don fargaba.
Baffa ya ce, ''Yarinyar nan Matawata auren kisan wuta ta
yi na sati uku ta fito ta yi idda ta dawo wajen Ilah, yanzu
haka suna tare tana gidan na ji ance ma wani cikin ne da
ita. Don haka ki je ki kama mijinki ki manta da Ilah a
rayuwarki.
Na matse hawaye na ce, ''Idan Allah Ya so Baffa na
hakura da Ilah a rayuwata.
Na koma daki a sanyaye sai na ji dama Yaya Abdul-Basi
bai tafi ba na bishi mu koma, don bana son
garin ko kadan.
Matawata ta ji labari na zo, washegari da sassafe ta shigo
gidan ta same ni har kofar dakina ta zazzage min habaici
iri-iri. Wai Ilah nata ne duk naci da sihirce-sihircena dole
na hakura na bar mata shi.
Ban rama ba ta yi ta gaji ta tafi.
Wasika doguwa da ajami Ilah ya aiko ,in da daddare yana
mai ba ni hakuri da yi min fatan alkhairi, ya kuma roke ni
da na taya shi da addu'a, rayuwarsa tana cikin kunci don
bai yi sa'ar abokiyar zama ta gari ba.
Ban gama karantawa ba ma na yayyaga na zubar a shara.
Ban yarda na hadu da shi ba har na yi mako a garin,
sannan Yaya Abdul-Basi ya zo ya dauke ni muka tafi. Tun
a hanya ya ga alamu ina cikin damuwa, da ya dame ni da
tambaya sai na rushe da kuka. Na

shaida masa Ilah ya sake mayar da Matawata a dakinsa.
Wani dogon tsaki na ji ya ja, sannan ya watso min wata
hargitsattsiyar harara.
Ya ce, 'Idan bai mayar da ita ba ke zai saka a dakin?
Wallahi Umaimah ki rufawa kanki asiri, ki sani fa kina
kona kanki ne, da auren wani a kanki amma
kike tunanin wani katon banza, har kina kishi akan ya
maida tsohuwar matarsa. To ina ruwanki?
Ya shiga yi min nasihohi masu ratsa jiki ya ce, gara ni da
shi dukka mu yi wa kanmu fada mu manta da Nasiba da
Ilah mu fuskanci sabuwar rayuwa, Allah ne kadai Ya san
dalilin da Ya raba mu da wadanda muka fi so, Ya hada
junanmu.
MAKWABTAKA 19
Tun lokacin na yiwa kaina fada, na
nutsu na
fara kokarin cusawa raina zama da
AbdulBasi a matsayin miji na, shi ma haka.
Sai
bayan ma da na
gama sakandire sannan muka
budewa
kanmu sabuwar rayuwar jin dadi da
son
juna.
Abdul-Basi ya dawo yana sona
tamkar
Nasiba, don na juye ta sak! Da na yi
kiba, ni
ma na cire Ilah a
raina, na daukeshi a matsayin
munafiki na
barshi da Matawata can su karata da
bakin
munafincinsu...
Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya
ce, ''Ya aka
yi kika zo nan kasar kika baro
masoyinki
Abdul-Basi a can?
Sai ta yi murmushi karfin hali, ta ce,
''Kai ma
tun da ka ganni a nan kasar alhali
ina da
aure a can kasan
sai dai idan da wata matsala ne.
Kuma ai da
sauran kuka wai anci gumba an hana
maye,
me aka yi a hawa bishiyar bare a
tsinko

reshenta?
Sai Abdul-Sabur da Faduwa suka
hada
idanu.
Sannan Faduwa ta dafe kirji, ta ce,
''Me ya
hada ku?
Umaimah ta tabe baki ta ce,
''MAKWABTANA
ne suka hada mu,
MAKWABTAKA! ''Kamar yaya? AbdulSabur ya
tambaya cike da fargaba.
Umaimah ta yi shuru kanta a sunkuye
a
kasa, kamar me tunani. Can ta dago
ta dube
su, idanuwanta a cike da kwallah.
Ta ce, 'Na kasance mai saurin yarda
da
amincewa mutane, na saba da
Makwabtana
da *ya*yansu tun lokacin marigayiya
don
haka nake jinsu tamkar dangina.
Kamar yadda na fada a baya gidaje
takwas
ne a farfajiyar, sama da kasa guda
hudu. Mu
muna sama
kasanmu kuma wata mata ce mai
suna
Hajiya Ladidi, *yan garin Minna ne
aiki ya
kawo mijinta Kaduna, suna yaren
Nufe da
*ya*yanta hudu ta girme ni harta
kusan
haifata ma.
Sai gidaje biyu da suke fuskantar
namu
wata beyarabiya ce amma
musulmace mai
suna Zulaiha Senegal. Tana zuwa
Senegal
tana dinko kayan mata da maza
shaddoji da
yadiddika tana siyarwa *yan siyasa
da
matan masu kudi. Tana ji da gayu da
rawar
kai tana abu kamar wata budurwa

alhali ta
ajiye karatan *ya*ya guda uku.
Samari maza
guda biyu har daya ya gama
sakandire ya
shiga jami'a,
daya ya na daf da gama sakandire,
sai mace
ita ce a sakandire aji uku. Ta rabu da
baban
yaran tun suna kanana ta zo ta kama
haya ta
ke kasuwanci, ta ke kula da
*ya*yanta.
Ba laifi matar tana da kirki da yawan
fara'a
da jan mutane a jikinta, bakinta rairai-rai
saboda iya magana, don haka
gidanta
kullum a cike da mutane yake, mata
da
maza, kawayenta da kawayen
*ya*yanta,
*yan uwanta da *yan uwan tsohon
mijinta
zuwa suke yi tana maraba da kowa.
Ta ja ni a jiki sosai muka saba tun
lokacin
Nasiba,
shakuwarmu ta fi yawa a lokacin da
na
dawo ni kadai, ba ni da abokiyar
shawara
sai ita. Gidaje hudun kuwa da suke
gefenmu, gidan wasu kabilu ne ba
musulmai ba ne, wa da kani, daya
sama
daya a kasa da matansu, ko na ce
dadironsu,
wadannan ba ma harka da su. Sai
dayan
ginin Hajiya Bishra a kasa, mijinta ya
mutu
ya bar ta da yara,
amma fa duk ta aurar da *ya*yanta.
*Yan
mata biyu ne suka rage mata
sa'annina ne,
Nana da Wahida,
suna neman gurbin karatu a Kaduna
Polytechnic.

Sai saman su wata amarya ce ba su
dade da
tarewa ba, mai suna Bara'atu ta riga
ni aure
har ta haifi
*yan biyu. Ita ma kawance muke yi
na
hakika kamar yadda mai gidanta
Kamal da
maigidana suke yi saboda su dukka
banki
daya suke aiki.
Duk wani sirrina, na gidanmu can
Dugge
dama tsakani na da mijjina da kawata
Bara'atu nake tattaunawa saboda na
yarda
da ita.
Mijina sai ya yi ta jiyo maganarsa ya
rasa
daga inda magana ta ke fitowa. Ban
tashi
ganewa ba har sai da abu ya kwabe,
a
lokacin da bazan iya gyarawa ba...
Kamar yaya? Abdul-Sabur ya tambaye
ta cike
da rashin fahimta.
Cikin jimami Umaimah ta ce,
''Matsalata da
Bara'atu ke nan, sai ni da Zulaiha
Senegal.
Auntyna nake kiranta koda yaushe
sai na
dauki kayan abinci kamar idan zanyi
wainar
shinkafa ko alala, to ban iya sosai ba,
ita take
koya min. Ko ta shigo da kanta har
gidana ta
koya min, ta koya min yadda zanyi
magana da miji, da yadda ake tafiya
da kissa
gami da kisisina. Na dauke ta tamkar
*yar
uwata Nasiba, saboda yadda ta ke
nuna min,
sai na zaci tana sona.
Abdul-Basi ya fara min fada akan na
dinga ja
da baya da Makwabtana, dan ya ga
na bawa

Makwabta gaskiya fiye da shi mijina.
Ni kuwa a wajena dole ne na shiga
makwabta saboda zaman gidan ya yi
min
yawa ni kadai, ga yawan dauke wuta
haka
ga mijina baya dawowa sai karfe
takwas ko
tara na dare tun karfe bakwai na
safe. Idan
ma na zauna ni kadai tunani ne ya ke
addabata na yi ta kuka. Da jimamin
rashin
mahaifiyata ko *yar uwata zan ji ko
kuma da
takaicin cin amanar da Matawata ta yi
min ta
raba ni da wanda nake so?
Makwabta nake shiga in sha hira,
suma su
shigo min, amma a ce a raba wannan
karfaffan zumunci
ba zai yiwu ba. Don haka ban ji
maganar
Abdul-Basi ba, na ci gaba da huldata
da su.
Muna nan a haka na samu ciki, na
haifi dana
santalele, mai kama da mahaifinsa,
aka saka
masa suna Bilal.
Abdul-Sabur da Faduwa suka bude
baki don
tsananin mamaki. Tambayarta suke
yi, ''Au
ashe kin
taba haihuwa?
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Ina
da
dana yana can a gidansu.
Abdul-Sabur ya ce ''Ke kuwa me ya
raba ki
da mijinki da danki kika taho kika bar
su?
Umaimah ta ce ''Kaddara ce wacce ta
riga
fata,
kaddara ta sanadin amincewa
MAKWABTAKA
da na yo. Kafin na yaye Bilal sai na
sami wani
cikin, ni dai tun daga wannan lokacin

na
rasa kan mijina, sai na ga kamar ya
daina
sona, ya tsane ni. Ya daina shiga
harkata,
kullum sai ya dawo gida a koshe ya
ce ya ci
abinci a waje. Ashe ni ce ban sani ba
Zulayha
Senegal ta kwace min mijina, tun
baya biye
ta har ya fara.
Ashe tunda magruba ya ke dawowa
sai ya
shige gidanta a can zai ci abinci, ya
yi kallo,
ni kuwa ina
cikin duhu idan babu wuta ina
jiransa ya
dawo ya tayar min da janareto don ba
zan
iya tayar da shi
ba, ya yi min tauri. Ban san wainar
da ake
toyawa ba MAKWABTA duk
sun sani babu wacce ta fada min, sai
dai
suna gefe suna tausayamin, idan
suka ganni
a gidanta, ko
suka ganta a gidana. Ni ma dai na ga
a
lokacin ta fiye bugun cikina ta ji irin
zaman
da nake yi da mijina, ban boye mata
ba na
fada mata irin canjin da na ga ni
daga
wajensa, sai ta yi murmushin
mugunta.
Ta-kai-ta-kawo sai in zo in ganta a
kicin dina
tana min barbaden magani a cikin
kwanukan abincina.
Rannan kuma na kama ta ta budamin
gas
cooker wajen da ake ajiye silinda ta
jefa min
wani abu, ashe laya ce. Matattakalata
duk
ruwan rubutu ne idan na fito nake
gani, sai

na yi ta mamaki, amma
kuma ko kusa zuciyata ba ta taba yi
miin
zargin tana bi na da sharri ba. Kuma
ban
daina kula ta ba.
Wata ranar asabar da safe cikina ya
tsufa ina
son na je na nemo mai aiki a
unguwar Dosa,
wata Hajiya Balaraba babar kawata
ce ta ke
samowa, ta yi min waya ta ce an
kawo masu
aiki da yawa na zo na
dauka.
Kasancewar watan haihuwata ne gani
da
karamin da bai fi shekara daya da
rabi ba,
ba ya tafiya ma a
lokacin sosai, ga shi daf da watan
azumi za,a
fara aiki zai yi min yawa dole na sami
mataimakiya.
Na dade da fada masa zan nemi mai
aiki, ya
kuma yarda, sai na sanar masa a
safiyar ya
zo ya kai ni na dauko mai aikin. Ya
daka min
tsawa ya ce, ba zai kai ni ba.
Na shiga yi masa bayani cikin ladabi
duk da
haka ya ce, ba zai je ba sai dai ni na
je. Na ce
ya ba ni
kudin tasi drop na je na dawo, ya ce
ba zai
bayar ba.
Na duba jakata na ga kudin dari biyu
ne
kawai, ba zasu ishe ni daukar tasi
zuwa da
dawowa ba. Sai na kuduri niyyar
hawan
acaba na yi sauri na je na dawo, in
yaso Haj.
Balaraba sai ta ba ni na dawowar. Na
ce to
ya rike min dana na je yanzu na
dawo. Abin

mamaki sai ya daka min tsawa.
Ya ce, ''dauki danki ki tafi da shi, ba
zan rike
ba nima ina da wajen zuwa. Kuma ki
tafi da
makullanki
don bazan jire miki gida ba. Na

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment