Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwanta ba,
ai sai ayi musu wata fassarar.
Nan da nan ta ji hankalinta ya tashi, ta fara tafiya cikin sauri, burinta ta yi sauri ta bace masa ya zo
ya rasa ta. Ta tuna ai yana da lambar wayarta zai kira ta kuma ba dadi ta kashe wayarta bayan yanzu
suka gama yin waya. Tana matukar ganin girmansa yanzu ba zata iya yi masa musu ba. Ta kula
yana yi musu komai saboda Allah, don Allah Ya halicce shi mutum mai tausayi, kulawa da kuma
son kyautatawa kowa bata ga wata alama ba bayan haka.
Bayan ta tsallaka gada sai ta tsaya a inda ya umarce ta da jira shi, ba jimawa sai ta ga ya bayyana a
kusa
da ita cikin tsaleliyar motar nan ttasa. Ya tsaya a gefenta ta bude ta shiga gidan gaba ta zauna. Ta
dube shi ta yi murmushi, shi ma ya yi mata murmushi.
Ya ce, ''Kina so ki bata ne a kasar mutane? Ke da kike kamar kifin rijiya, babu inda kika sani daga
gida sai makaranta idan kin yi nisa ne ma kike zuwa Bukit bing tang.
Sai ta yi dariya, ta ce, ''Ka kai ni tashar da zan hau motar Mantin sai in hau in je da kaina ba sai ka
wahalar da kanka ba.
Ya ci gaba da kallon titi yana tuki, yayi dan murmushi, ya ce, ''Kada ki damu, ba zan kai ki inda za
a ganmu tare ba. Sai in kai ki makarantarsu tunda a hostel suke gidajen dalibai ba nisa da cikin
makarantar sai su zo su dauke ki ni kuma sai in tafi kafin su karaso.
Ta ji sanyi a ranta, sai ta gyara zama ta saki jikinta.
Ya isa bakin wani banki ya sami waje ya tsaya, ya juya ya dube ta, ya ce.
''Ki min hakuri mintina kadan zan shiga banki na fito.
Ta gyada kai, ta yi murmushi ta ce, ''Ba damuwa sai ka fito.
Ya fice da sauri ya bar mata A.c da CD a kunne tana ji. Ta bude gidan da yake ajiyer CDs ta shiga
duddubawa can ta hango wakar da ta ke nema ta saka don wakar rannan ta yi mata dadi wato ta
'Akuri Afomsa.
Ya dan dade amma ba da yawa ba ya fito, bayan ya yi mata sallama sannan ya shigo motar ya
zauna. Ta dukar da kai ta yi masa sannu da zuwa. Ya yi murmushi ya amsa, sannan ya fara tuki. Sai
bayan
da suka yi nisa ya kula ta canja wakar ba ta da ba ce da yake ji.
Wato wakar Rihanna' mai taken 'Te amo' sai ya ji
ana Yaren 'Asanti' maimakon 'Turanci' ya kurawa rediyon ido ya juya ya dube ta, ita ma ta tsaya
tana kallonsa tana sauraron abin da zai ce mata, don
daga dukkan alamu ta ga yana shirin yin magana.
Sai ya fasa maganar ya ci gaba da duban gabansa.
Ta ji ta fara zargin kanta ko ya fi son waccan wakar ta canja masa? Nan da nan ta dauko wancan
CD na farko ta mika hannu ta danna wajen fitarwa, sai ya sa hannu ya
tare ya hana CD fitowa ya sake tura shi ciki, ya ce gaba da yi.

Ta kalle shi, sai ta sunkuyar da kanta kasa ta ajiye CD da yake hannunta suka ci gaba da tafiya ba
tare da wani ya sake magana a cikinsu ba. Sai sanyin AC mai hade da kamshin daddadan turaren
mota,
gami da sautin kida da zazzakar muryar da yake rera wakarne kadai yake tashi.
Nan da nan sai suka ga tafiyar ta yi musu sauri, kan ka ce kwabo suka isa Mantin suka gangara
zuwa cikin Legenda makarantar su Hanif. Ya sami waje ya tsaya sannan ya juyo ya dube ta.
Ya ce, ''Yaushe Hanif din zai tafi Najeriyar?
Ta ce, ''Cikin satin nan ne.
Ya ce, ''Me yasa ke ba zaki bishi ba, ku je ki ga *yan gida, kin fi so ki ba shi sako? Ta sunkuyar da
kanta kasa da alama ba shi da amsar wannan tambaya.
Ya ce ''Me da me kike so ki aikawa *yan gidan?
Ta shafa jakarta, ta ce, ''Wata ambulan ce na rubuta wasika doguwa zuwa ga Baffa da Sabitu, ina
shaida musu ina nan lafiya su kwantar da hankalinsu. Idan na gama karatu zan zo na gan su. Sannan
na ce su taimaka su je Gombe gidan iyayen Abdul-Basi
su duba Babangida da Bilal. Sannan na siyo musu wayoyi guda biyu daya ta Sabitu daya ta Baffa,
don
ina kyautata zaton an kai musu service din waya garin ko kusa da garin. Sannan na dauki kudi na je
na canja Riggit ya zama Dallar dubu biyu, zan ba shi idan ya je Najeriya ya canja ya zama naira
dubu dari uku da ashirin da wani abu, ya kaiwa su Baffa da Sabitu su yi jari, sai kuma hotunana
dana dauka a nan kasar guda goma na wanke na hada musu don su ganni ina cikin koshin lafiya.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kin yi dai-dai, gaskiya kinyi tunani, ya yi kyau hakan da kika yi.
Na ji dadi da kika yi wannan tunanin, kuma daman haka ya kama ta ki yi gara su ji motsinki akan
shirun nan da kika yi kamar ba kya raye. Yanzu za su ji dadi, kuma hankalinsu zai kwanta. Sun san
bakya tare da Abdul-Basi kuwa?
Ta yi shiru kamar mai tunani, can ta dago a hankali ta dube shi, ta ce, ''Ina kyautata zaton sun sani,
saboda daman Sabitu ya sani ban boye masa komai ba, ban sani ba ko dalili zai sa ya fada musu.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Zancen gaskiya sun san ba kwa tare, saboda Abdul-Basi har
garinku ya je nemanki, kuma ya yi musu bayanin cewar kina cikin wadanda ku ka tafi karatu
Malaysia, shima kuma daga baya ya bincika a gari
ya ji labari, kaninsa ne ya kai shi gidan Lamijo nemanki ta ce ba ta san inda kike ba yanzu, sai
Baban Hanif ya fada musu gaskiyar magana. Alh. Nasir dinma ya fada min haka Abdul-Basi ma ya
fada min, don haka kada ki boyewa Baffa komai ki sanar da shi ba ki da aure, amma kina kama
kanki, kina tsare mutuncin kanki ya taya ki addu'a.
Hawaye ya cika mata ido taf! Ta sharce da gefen gyalenta ta ce, ''Yanzu Lamijo ta ji labarin
tahowata alhalin tana zargina da mijinta?
Abdul-Sabur ya ce, ''Ah! To meye dan ta ji ai ta fi kowa sanin zaki taho daman kuma me ye abun
mamaki don ta ji kina nan? Mijinta kuwa ai ba da shi kika taho ba, kin bar mata abinta a can. Kuma
babu
wanda ya fada mata makudan kudin da Alh. Nasir yake baki ke da Hanif, ko nima ya so ya boye
min,
sai da ya ga dai na sani sannan ya sake fada min, ya ce kuma bayan Hanif da ke da Alh. Sani da ya
fara
aikowa ya baku bai taba fadawa kowa ba. Kuma ya gargadi Hanif kada ya fadawa kowa hatta
mahaifiyarsa, saboda yana da *ya*ya da yawa, duk uwarsu daban abun zai iya zama rigima idan
wata
mata ta ji ita bai bawa danta ba.
Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta sake goge hawayen idonta da alama ta ji sanyi a ranta. Ya dube ta ya
yi murmushi, ya ce, ''Babu matsala. Na
gode sosai, sai na dawo.
Ta yunkura zata bude kofar mota ta fice sai ta ji ya ambaci sunanta, sai ta waiwayo da sauri ta dube
shi.
Ya zaro kudi daga aljihunsa Dallar dari biyar ce ya mika mata, ya ce.

''Ga shi ki hadawa su Baffa na canjo musu yanzu, na zaci ba za ki hada musu da kudi ba, sai ki rike
nawa idan kuma kina ganin dukka za ki aika musu ya yi dai-dai.
Za ta ki karba ya bata rai, kuma ya ja mata kunne ba ya so duk abin da ya yi niyyar yi mata ta ce ya
bar shi. Tayi godiya ta karba.
Ya ce, ''Yaushe za ki dawo gida?
Ta ce, ''Gobe ko jibi
Ya ce, ''Magana daya za ki fada don zan dawo in dauke ki a dai-dai nan wajen inda na ajiye ki?
Ta yi shiru can ta ce, ''Jibi zan dawo.
Ya ce, ''To ba damuwa, kuma ga waya ma zamu yi,
ki gaida su Hanif. Akwai wanda nake so na gani a cikin garinnan, amma sauri nake yi idan na dawo
jibin zan gan shi. Zan je na dauko Faduwa a Putra jaya mun yi da ita karfe goma sha biyu za ta
gama.
Umaimah ta yi murmushi gami da lumshe ido, ta ce,
''To shi ke nan, ka gaida gida.
Ta bude kofar mota ta fice, yana daga mata hannu tana daga masa. Ya ja mota a guje ya fice daga
farfajiyar makarantar. Ta dade a tsaye tana mamakin irin wannan kirki da kulawa na Abdul- Sabur.
Ta ji dadi data ji yayi zancen Faduwa don daga dukkan alamu ya yarda da shawararta, ya amince
zai so Faduwa kuma ya aure ta.
''Amma fa na taya Faduwa murna da samun miji kamili. Ina fatan ni ma Allah Ya ba ni miji na gari
mai
halinsa. Inji Umaimah ta fada a zuciyarta. Yayin da ta ke kokarin zakulo wayarta daga aljihun
jakarta
zata bugawa Hanif ta shaida masa ta iso makarantarsu ya zo ya dauke ta.
Tun da Umaimah ta tafi Legenda ba ta kira Abdul ba, shima bai kirata ba har ta cika kwanaki
biyunta da la'asar tana shirin kiransa sai ta ji ya kira ta. Ya shaida mata ya shigo garin, amma ya
wuce gidan abokinsa da zai gani don haka ta shirya bayan sallar magruba zai zo ya dauke ta. Ya
tambaye ta inda zai same ta a gidan su Hanif ko a makaranta
inda ya ajiye ta?
Ta ce, zata fito ta jira shi a inda ya aje ta. Suka yi sallama suka kashe waya.
Yana idar da sallar magruba kuwa ya zo ya tsaya a inda suka yi ya dauke ta, ya iske ba ta karaso ba,
don haka ya yi zaton ko tana kan hanya don haka bai damu da ya dame ta da kira ba. Ya shefe fiye
da
awa babu ita babu kiranta. Da ya ji shirun yayi yawa sai ya kira ta, tana ta ruri ba ta amsa ba. A
masallacin Makarantar ya yi sallar
isha'i ya dawo cikin mota ya ci gaba da jira bata zo ba sai ya sake kiranta. Tun wayar tana shiga har
ya ji an kashe ta mudik. Sai ya shiga mamaki marar misaltuwa, gami da fargaba ko ba lafiya. Yana
nan a wajen har karfe goma sha dayan dare.
Ya yanke shawarar neman gidan Hanif ya je ya gani ko lafiya? Sai ya fasa zuwa saboda ya fuskanci
ba ta
so a dinga ganinta da namiji. Ya zama ba shi da wata shawara ko dubara kuma. Ya shiga tunani
anya kuwa mai ilimi da wayewa zata yi haka?
Fatansa dai ace tana nan lafiya, kuma cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Ya shiga tunanin ko kara kwana ta ke so ta yi, ko kuwa motar haya ta hau ta koma gida?
Sai wata dabara ta fado masa ya yanke shawarar ya kira Faduwa ya tambaya ko Umaimah tana gida.
Yana kiran Faduwa bugu daya wayar ta shiga, ta dauka. Ya tambaye ta tana ina? Sai ta yi mamaki
da tambayar da ya yi mata alhali da yamma nan ma
sun hadu tana gida.
Ta tambaye shi, ''Lafiya?
Ya ce, ''Idan kina gida ki duba min gidan Umaimah tana nan?
Faduwa dai ba ta daina ambaton lafiya ba.
Ya ce, ''Lafiya mana, ko kinji alamar rashin lafiya a tare da ni?

Ta yi dariya ta ce, ''Ai tambayoyin ne na ji ba irin wadanda ka saba yi min ba ne. Ya ce, ''Dubo min
ita za ki yi kawai ki fada min ko ta dawo daga Mantin?
Faduwa ta ce, ''To kashe wayar bari na gani, zan kira ka.
Ta kira wayar Umaimah a kashe, don haka dole ta katse baccinta ta tashi ta dauki mayafi ta hau
sama gidanta. Ta danna kararrawa sau daya kacal sai ga Umaimah a bakin kofa, ta bude kofar da
sauri tana
kokarin cewa Faduwa ta shigo ta zauna.
Faduwa ta ce, ''Bacci na ke ji zuwa na yi in duba in ga ko kin dawo? Na ji wayarki a kashe kuma.
Bayanin Faduwa ya ba ta mamaki, tabbas ta san akwai dalili. Sai ta yi kasake abunka da marar
gaskiya, can ta dago ta dubi Faduwa ta ce, ''Ina Abdul-Sabur?
Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Shi ya taso ni ya ce in duba ko kin dawo gida lafiya. Wai me yake
faruwa ne?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Babu komai. Kamar yadda na fada miki shi ma na fada masa yau
zan dawo, to kuma waya ta a kashe ban yi caji ba shiyasa ban fada masa na dawo ba.
Faduwa ta ce, ''Kiyi caji ki kunna ki fada masa kin dawo. Umaimah ta ce, ''Yana gidansa ne?
Faduwa ta ce, ''Ina ma na san inda yake, a waya dai ya kirani yanzu. Bari na kira na fada masa kin
dawo. Rufe gidan ki kwanta, ni ma zan je in kwanta.
Ta juya ta tafi, ta danno lambar Abdul-Sabur tana tafe tana magana da shi yayin da Umaimah ta
sankare a tsaye saboda tasan ba ta kyauta masa ba.
''Yanzu ina mafita?
Ya ya zan yi in wanke kaina daga wannan rashin ladabin da na tafka?
Umaimah ta ke wasu-wasi a zuciyarta.
Abdul-Sabur bai shigo gidansa ba sai karfe daya da rabi na dare, yayin da Umaimah ke tsaye a
dakinta tana kai kawo, ta kasa sukuni har sai da ta ji motsinsa a cikin gidansa. Tana hango hasken
fitilun da ya kukkunna yana ya kai kawo a cikin gidansa.
Bai kwanta ba sai karfe biyu da kwata sannan ita ma ta samu ta kwanta, hakarkarinta. Da kyar ta yi
bacci tana sake-saken yadda zata tunkare shi da bayanin da zai gamsu da ita, kuma da idanuwan da
zata kalle shi. Tabbas ta tabbatar ba ta kyauta masa ba.
***************
Washe gari da misalin karfe goma sha daya da minti goma sha daya Abdul-Sabur ya ji wayarsa ta
dauki
ruri. Yana zaune a falonsa yana kallon labaran CNN.
Yana dubawa sai ya ga Umaimah ce don haka sai ya gyara zama don ya ji abin da zata fada masa,
sannan ya danna wayar gami da yi mata sallama.
Shima maganin sa. Yabi ya takura mata sosai.MAKWABTAKA 33
Ya ji tana magana da kyar yayin da muryarta ke karkarwa. Bayan ta gaishe shi, sai ta fara da ba shi
hakuri, sannan ta dora da bayanai barkatai..
Da ya hada dogayen bayananta a waje daya ya dunkule ya fuskanci tana magana ne akan da ta tashi
tahowa Hanif da kawayenta ne suka cika mota guda suka ce za su kawo ta har gida, ita kuma ta kasa
fada musu akwai wanda ya ke jiranta. Sanda yake kiranta a waya tana tare da su a mota ba zata iya
amsa masa ba a gabansu, don haka ta kashe wayar.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Kada ki damu Umaimah na fahimce ki sosai, kuma na yi miki
uziri.
Hakan da kika yi kin yi dai-dai da ba ki bari wani ya zarge ki ba balle aje Gombe ana yadawa nasan
halin mutanenmu. Ki shirya da yamma ke da Faduwa za mu fita mu dan kewaya gari.
Farin ciki ya rufe ta da Allah Ya sa ya fahimce ta. Nan da nan ta amsa masa da, ''To, Allah Ya
kaimu anjimar, na gode.
Karfe biyar saura kwata a motar Abdul-Sabur suka hallara shi yake tukawa, Faduwa na gefensa a
gidan gaba yayin da Umaimah ta ke zaune a kujerar baya. Babu abin da yake tashi a motar sai
sautin kida wakar larabawa ce Faduwa ta saka ta 'Nancy' mai taken 'Yatabtab.
Tana daga zaune ta ke rawa tana bin wakar.

Abdul-Sabur ya kashe, ta sake kunnawa idan ya rage sai ta sake karawa, Umaimah na zaune ba ta
da aiki sai dariya da kyalkyalawa.
Waje-waje na shakatawa suka dinga zuwa kama daga wajen cin abincim shan ice-cream, gidan zoo
da kuma malls inda ya ce kowacce ta dauki abin da ta ke so ko nawa ne zai biya, su ka jidi kaya
kuwa. Ba su shigo gidajensu ba sai karfe daya na dare daman sun riga da sun yi sallolinsu a
masallacin 'BB
Plaza' don haka kowannensu wanka ya yi ya kwanta.
Washe gari da ya yamma sai ga Faduwa a gidan Umaimah dauke da wasu takardu a hannunta, tana
shigowa ko zama bata yi ba sai ta mika mata.
Ta ce, ''Ga form, ki cike inji Abdul-Sabur na makarantar koyon tukin mota ne, kullum da safe ko da
yamma ake zuwa. Ke da ba ki taba iya tukin mota ba watanni uku zaki yi. Kina gamawa in kin ci
jarabawa za'a baki 'driving liences'. Ni kuma da yake tsohuwar direba ce wata daya kacal zan yi a ba
ni nima nawa idan na ci jarabawa.
Umaimah ta cika da mamaki ta ce, ''Me yasa zan shiga Makarantar koyon tuki alhali ba ni da mota,
kuma ba inda nake zuwa Makarantarmu ga ta a kusa da ni? Faduwa ta ce, ''Haka dai ya ga ya dace
mu shiga kasancewar dogon hutu ne, idan ma kika zauna a
gidan me zaki yi kuma shi tuki ai yana da amfani idan ka iya din, saboda ko a kasarku nan gaba zai
amfane ki sai ki dinga tukinki ba sai kinyi ta neman direba ba. Umaimah ta ce, ''Haka ne, na gode.
Ta karbi forms din ta cike ta mikawa Faduwa.
Yayin da Faduwa ta ce, ''Ai tashi zaki yi mu je koyontukin yau za'a fara, ga Abdul din can ma a
mota
yana jiranmu.
Umaimah ta dafe kirji ta zabura ta ce, ''Wai! Tukin yau zan fara? Gaskiya Anti Faduwa tsoron mota
nake ji.
Faduwa ta kyalkyale da dariya, ta ce ''Ke *yar kauye ce har yanzu. Meye abun tsoro kuma a tukin
mota?
Ki zo mu je kada mu bata masa lokaci.
Daman Umaimah a shirye ta ke tsaf, don haka gyalenta kadai ta jawo da wayarta ta rufo gidan suka
sauko, suna shiga motar Umaimah ta gaishe shi sannan ta yi masa godiya bisa kulawar da yake yi
musu.
Faduwa ta fara ba shi labarin yadda suka yi da umaimah a sama da ta ce ita tsoron tukin mota ta
ke yi. Suka sha kyalkyala dariya su dukka ukun.
Abdul-Sabur ya shiga yi mata bayani akan ta kwantar da hankalinta ba wuya, shi tuki nutsuwa ya ke
so da kuma cire tsoro.
''Na samar muku makarantar da ba ta da nisa ko bana nan sai ku dinga takawa da kafa ko ku hau
tasi, Riggit uku ma zai kai ku. Inji Abdul. Su dukka suka amsa masa da godiya gami da fatan
alkhairi.
Ashe dai makarantar koyon tuki makaranta ce sosai, har da ajujuwa da takardun rubutu da karatu. A
koya musu a rubuce sannan a fita ayi gwaji a zahiri.
A ranar Abdul-Sabur ya jira su a mota har suka gama suka fito daga ajujuwansu suka dawo gida
tare. Amma sun yi shawara su dinga zuwa da safe ba da yamma ba, karfe tara zuwa karfe goma sha
biyu na rana.
Don haka kullum Umaimah ce ta ke saukowa, sai ta bi ta gidan Faduwa sannan su dunguma su tafi
a motar haya, ko a kafa ko kuma Abdul Sabur ya kai su, ko ya dauko su idan ya ga fitarsu.
Ku san kullum da yamma ka'ida ne sai sun fita wuraren shakatawa iri-iri, don haka kowannensu ya
daina girki abinci kala-kala suke ci a waje, kuma har su tafi da wasu gida.
Gaskiya Umaimah ta ji dadin hutun nan, ba ta taba jin dadin Malaysia irin wannan karon ba, har
kiba ta fara yi babu kashin nan rankwal-rankwal na rama. Babu sauran
hawaye a idanunta, kullum suna tare su uku, wasa da dariya kadai ne a tsakaninsu. Sai ta ji ta saba
da
su sosai ta cire jin kunya, nauyi da tsanar ganinsu da take ji ada da.

Sai ga ta gidanta ba ya rabo da mutane ku san kullum sai ta yi baki *yan makarantarsu, kuma *yan
garinsu suma suna zuwa. Su Aisha Bingyal sukan yi kungiya su ziyarce ta, ita ma da su AbdulSabur suna biyawa ta gidajensu.
A wannan sabuwar makarantar ma ta koyon tuki sai ga ta ta yi kawaye mata wasu sa'anninta, wasu
kuma sun girmeta sosai, su ma har gidanta suke ziyartarta.
Wasu kuwa kawayen Faduwa ne idan suka zo gidan Faduwa sai ta shigo da su gidan Umaimah. A
hadu a yi ta hira ana ciye-ciye ana shewa. Idan dare ya yi kuma sai ta yi zaman kiran wayar *yan
gida Nigeria, garin Gombe wato *ya*yanta,
Babangida da Bilal. Wannan dole ne kullum da daddare sai sun yi waya, kuma su dade suna yi. Ta
fuskanci dai-dai lokacin da suke gida sun dawo daga makarantar islamiyya da ta boko kuma ba su
yi bacci ba.
Sai yau Hajiyar Abdul-Basi ta karbi
wayar suka gaisa faram-faram.
Alhamdulillah, mutum rahma ne'' inji Umaimah dai-dai lokacin da ta tsinci kanta ta amsa wayoyi
har
sau shida a jejjere.
Hanif ne ya kira ta daga Najeriya ya bata hakuri saboda bai kai sakonta da wuri ba, ya tabbatar mata
kuma gobe ne insha Allah ya shirya zuwa 'Dugge' neman gidansu zai kai mata wadannan sakonnin.
Farin ciki ya rufe ta, ta yi masa godiya gami da yi masa magiya kada kuma ya sake shiga wasu
safgoginsa wadanda ya saba yi, ga shi har ya shafe wata guda cur a Najeriya bai je ya kai sakonta
ba.
Wannan karon dai ya tabbatar mata gaske yake zai je.
Allah cikin ikonSa kuwa ya cika mata alkawari, ya nemi gidansu a Dugge, ya kai mata sakon hannu
da hannun Baffanta da Sabitu ya damka.
Misalin karfe goma sha biyun rana a agogon Najeriya wanda yayi dai dai da karfe bakwai na dare a
agogon Malaysia, wayar Hanif ta shigo wayar Umaimah, shigowarta gida kenan daga gidan Faduwa
tana shirin dauro alwallar magruba. Data dauki wayar maimakon ta ji muryar Hanif tunda lambarsa
ce sai ta ji yaren fulatanci ne maimakon Hausar da suka saba yi. Muryar tsohonta ta ji, Baffa yana
ambaton sunanta cike da farin ciki
marar misaltuwa. Ta daka tsalle don murna ta fashe da kukan dadi. Fadi ta ke, ''Baffa ka yafe min.
Alhamdulillah da Allah Ya sa kana raye.
Shi ma kukan dadi yake yana hamdala da Allah ya sa tana raye tana cikin koshin lafiya. Ya shaida
mata cewar ya kasance cikin dumbin damuwa a lokacin da Abdu-Basi ya zo ya shaida musu ba ya
tare da ita.
Sabitu ma ya karbi wayar ya gaishe ta sannan ya shaida mata sun karbi sakon da ta aiko musu sun ji
dadin sakon kudin nan sosai don ta aiko musu a lokacin da suke tsananin bukatarsu saboda
al'amura sun tsananta a gare su, abincin ci ya yi musu wahala, wataran a ci, watarana a rasa a kwana
da yunwa.
Sai ta fashe da kuka don tausayinsu, sai ta sake godewa Allah da ya hore mata har ta kai matsayin
da zata taimaka musu.
Hanif ya shaida mata gari 'Dukku' suka taho don su yi waya babu service a 'Dugge' har yanzu, ko
wutar lantarki ba su da shi balle ayi cajin waya.
Sai ta roki Hanif ya siya musu layin waya ya saka musu a cikin wayoyin ya saka musu a caji ya
kuma kunna ya saka musu lambarta, sannan ya koyawa Sabitu yadda a ke yin wayar. Lokaci lokaci
sai su dinga zuwa Dukku suna kiranta suna yin magana.
Ta sake rokar Hanif ya karanta musu wasikar da ta rubuto musu.
Hanif ya aiwatar da duk abinda ta bukata. Ya sake kiranta da layin Baffa da na Sabitu suka yi
magana
da wayoyin dukka biyu. Suka sake daukar lokaci suna hira, ta sake yi musu bayani yadda za su
dinga yi da wayar suna samunta duk lokacin da suke bukatar yin magana da ita. Sun gamsu da

bayananta sosai, sannan ta ce su adana kudin da ta aiko musu, su nutsu su ga irin sana'ar data
kamata su yi dan kudin ya yaukaka ya zama babban jari, su sami na cin abinci a saukake a cikin riba
ba tare da uwar kudin ta wargaje ba.
Ta sha addu'ar fatan alkhairi, da shi albarka daga wajen Baffa da Sabitu.
Daga karshe ta yi masa godiya suka kashe waya.
Saboda dadi Umaimah ta durkusa gwiwoyinta dukka biyu a kasa ta daga hannayenta biyu sama tana
yi wa Allah godiya da ya fara warware mata matsalolinta. Ta yiwa Abdul-Sabur addu'a da fatan
alkhairi da fatan Allah Ya saka masa da gidan aljanna shi da yayi mata sanadiyyar nemo iyayenta
da *ya*yanta dan ba dan shi ba da wannan tunanin ba zai taba kawowa a kwakwalwarta ba.
Farin ciki ya hana ta daurewa, nan da nan sai ta bugawa Abdul-Sabur waya kafin ta yi masa bayani
ma ya fuskanci tana cikin nishadi. Ta shaida masa dimbun farin cikin da ya same ta yanzu a
sanadiyyar jin muryar Baffanta da kaninta Sabitu. Sai ya ji dadi shi ma a ransa, ya taya ta murna ya
kuma sake mata nasihohi masu ratsa jiki game da yadda Musulmi ya kamata ya zauna da Musulmi
dan uwansa. Ya sake gargadinta da ta zauna da kowa lafiya a duk inda take ta rike mutum da daraja
ko yaya matsayinsa yake a rayuwa, don mutum yana da daraja a wajen mahaliccinsa, ba abin
wulakantawa ba ne.
Umaimah ta yi masa alkawari zata bi duk nasihohin da ya yi mata, kuma zata ci gaba da saka shi a
cikin addu'arta bisa kokarin da

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment