Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi mata wajen ceto rayuwarta daga kunci zuwa farin ciki.
Daga dukkan alamu Abdul-Sabur ya fi ta jin dadi,
fadi ya ke, ''Alhamdu lillah, nima na gode miki.
Tana godiya yana godiya har suka katse waya.
Allah Akbar! Allah mai musanya duk abin da Ya so Ya canzu.
********************
Tuni Faduwa ta kammala makarantar koyon tukin mota a cikin wata daya da sati daya, aka buga
mata 'driving licence' dinta aka ba ta. Har ta zamto tana tuka motar Abdul-Sabur tana kai Umaimah
Makaranta ta dauko ta, da yamma kuma ta tuka su fita yawo. Da farko tsoro ne ya hana Umaimah
kwarewa a tuki, amma gori da tsokanar da Abdul-Sabur da
Faduwa suke yi mata itace ta sanya zuciyarta ta dake ta kuduri niyyar dagewa ta koya.
Tabbas tana kokari matuka don Abdul-Sabur ya kan fito ya tsaya ta barandar baya ya ga wucewarta
a cikin motar Makarantar ita da Malamin da yake koya mata, har sun fara hawa manyan titina.
Allah cikin ikonSa a satin da zasu koma makaranta a satin Umaimah ta ci jarabawarta ta makarantar
koyon tuki, aka bata satifiket da 'driving licence.
Tana ta tsalle da murna a lokacin da ta karbo, don taya bera-bari har hotuna Faduwa ta dinga yi
mata dauke da satifiket din a hannunta. Ta sha yiwa Umaimah hotuna ita kadai, sannan suka yi da
Faduwa, Abdul-Sabur ne ya dauke su, sanan aka yiwa Umaimah da Abdul-Sabur, Faduwa ta dauke
su. A halin yanzu duk inda za su je Umaimah ce take
tuka su. Tabbas hannu ya fada sosai ma, ta san dokokin tuki ko'ina tana kai kanta har wani gari.
Don ita ta tuka su suka je har 'Mantin' Garin su Hanif, da yake hutu ya kare ya dawo daga Najeriya.
Ta je ta karbo hotunan da su Baffa suka aiko mata. Hotuna ne da yawa, bayan na Baffa da ba Sabitu
har da na *yan garinsu kamar na matan Babanta Nene da Inna, ga na kawayenta da *ya*yansu. Ta
cika da mamaki taf a lokacin data ga hotunan Matawata da Ilah, sai ta zabura ta wurgar don firgici.
''Lafiya? Faduwa, Abdul-Sabur da Hanif suka tambaye ta.
Ta girgiza kai, hawaye mai radadi ya sirnano mata.
Ta yi murmushin karfin hali. Ta ce, ''Hoton Ilah da Matawata suma suka aiko min shine yasa na
firgita.
Faduwa da Abdul-Sabur saka hau rige-rigen daukowa su gani. Tabbas mutanen ruga ne sosai,
babu digon birni a jikinsu.
Faduwa ta yi dariya, ta ce, ''Allah na tuba, Umaimah ina ke ina aure da wannan bawan Allah 'Ilah?
Ina ke ina kishi da wannan 'Matawata? Ai ko ada ma ba ajinki ba ne balle yanzu. Idan kika ga Allah
Ya yi ikonSa Ya hana bawansa abunda kake so to ka
rungimi kaddara kawai kayi hakuri, Allah Shi Ya san me yake nufi, kuma me zai faru, dan abun nan
da kake so ba alkhairi ba ne a wajenka. Da Ya hana ki auren Ilah, alkhairi ne don Ya yi niyyar

daukaka ki fiye da su. Ki yi fatan auren mijin da ya dace da rayuwarki kawai, tsakaninki da su sai
taimako na
musulunci.
Abdul-Sabur ya ce da Faduwa, ''Ke rufe mana baki, an fada miki akwai maganar kudi, wayewa ko
kyau a soyayya ne?
Ai shi so ba ruwansa da bakauye ko dan birni.
Suka kyalkyale da dariya su dukka aka ci gaba da kallon hotuna. A wata ambulan daban Umaimah
ta
buda, nan kuma hotunan *yan Gombe ne wato na Bilal da Babangida kowannensu an yi masa shi
kadai, sannan da wanda aka yi musu a tare su biyu. Sun girma sosai, kuma da kyan kamarsu tamkar
a gaban mahaifansu su ke. Kamarsu daya sak tamkar uwa daya uba daya.
Umaimah ta dafe kirji ta rushe da kukan dadi, sai ta sumbaci hotunan gami da daga ido sama ta
godewa Allah da Ya raya mata *ya*anta, basu tagayyaraba bayan tahowarta.
Su Abdul-Sabur ma suka karbi hotunan suka kalla tabbas sun taya ta murna, yaran sun ba su
sha'awa,
kyawawan *ya*ya gaba daya sun juye kamannin Umaimah.
Faduwa mai son yara sai ta hau rungume hoton tana sunbatar hotunan.
Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin talikai, mai kowa mai komai.
****************
Da sati ya zagayo ranar Alhamis da yamma Umaimah tana daura alala a kicin dinta, saboda Faduwa
ma ta tarki yin Alalar don Faduwa tana son alala sosai, amma ba ta iya yi ba. Tana ta sauri ta gama
ta zuba ta kai mata ita da Abdul-Sabur.MAKWABTAKA 34
Ta ji ana bugun kofar gidanta da karfi ana kada kararrawa ba adadi. Da sauri ta fito daga kicin a
gigice tana zaton ko ba lafiya ba. Ta fara lekawa ta huda kafin ta bude don ta ga ko waye, Faduwa
ta gani duk a gigce ta ke, amma tana fara'a daga dukkan alamu alkhairi ne ya kawo ta.
Cikin gaggawa ta bude kofa, kafin ta ce wani abu Faduwa ta yi caraf ta rungume ta tana tsalle.
Umaimah dai dariya ta ke taya ta gami da tambayar ta, ''Lafiya? Me ya faru? ''
Albishirinki? Inji Faduwa.
Umaimah ta ce ''Goro fari tas-tas.
Faduwa ta ce, ''Sai kin ba ni goro zan fada miki.
Umaimah ta yi-ta yi Faduwa ta fara fada mata inyaso ta dauko mata goron. Faduwa ta ce, gaskiya
sai an
ba ta goro zata fada, don albishir din babba ne. Umaimah ta cika da mamaki matuka, ta ce, ''To, bari
na je daki na dauko miki goron sai ki fada min.
Ta shiga dakinta ta yi diri-diri ta rasa ma me zata dauko mata. Ta rasa mene wannan abu da Faduwa
ta ke ja mata rai kafin ta fada mata.
A zuciyarta ta ke magana, ''To ko Abdul-Sabur ne ya amince zai aure ta, shi yasa ta ke murna? Haka
ne ma labarin, ina jin ya fada mata ni na ce ya dace ya aure ta shi yasa zata yi min albishir.
Ta jawo jakarta ta bude ta dauko kudi Riggit dari biyu, wanda ya yi dai-dai da naira dubu tara, ta
kawo mata. Faduwa ta karba, sannan ta cewa Umaimah ta rufe idanunta. Tunda ta kagu ta ji sai ta
yi sauri ta rufe idanunta.
Faduwa ta ce, ta miko hannayenta duka biyu.
Umaimah ta yi yadda ta umarce ta. Da faduwa ta saka mata abu guda biyu kowanne hannu guda
daya sai ta umarci Umaimah ta bude idanunta ta gani.
Da ta bude ta duba sai ta kasa fahimtar abin da Faduwa ta ke nufi. Mukulli ne guda biyu a kowanne
hannunta.
Ta tambayi Faduwa cike da rashin fahimta,
''Mukullan me ye wannan? Faduwa ta ce, ''Mukullan motocinmu ne ni da ke kowa daya.
Umaimah ta turo baki ta ajiye mukullan akan tebur ta ce, ''Anti Faduwa, wallahi kin cika son wasa.
Wacce irin mota kuma, ya za a yi ki ce mukullin motata? Na dora abinci akan wuta bari na je na
duba kada ya kama.
Ta shiga kicin da gudu ta ci gaba da daura alala tana jefawa a cikin ruwan zafin da yake a kan wuta.

Faduwa ce ta sake debo mukullai ta biyo ta kicin ta ce, ''Wallahi da gaske nake mukullan motarmu
ne.
Umaimah ta tsaya tana kallonta tana mamakin irin wannan son wasa da tsokana na Faduwa.
Faduwa ta ce, ''Na ga alamar har yanzu ba ki yarda da ni ba, to gama daura alalar ki zo mu sauka
kasa
sai ki ga zahiri.
Umaimah ta gama sannan ta dauko gyalenta ta biyo Faduwa kasa. Kai tsaye Faduwa ta shige wajen
da aka tanada don ajiyar motoci. Ta je ta bude wasu motoci guda biyu iri daya, sai dai bambancin
fenti. Saboda mamaki sai Umaimah ta kame a tsaye
tana kallon Faduwa da motocin da aka fi hawan irinsu a Malaysia 'persona' Har yanzu da ragowar
kokonto a cikin zuciyarta, tana ganin kamar wasa Faduwa ta ke yi mata.
''Me yasa Abdul-Sabur zai yi tunaninya saya mana motoci?
A wanne dalili? Umaimah ta ke fada a cikin zuciyarta.
Faduwa ta ce, ''Zabi daya wacce kala kika fi so,
baka ko ruwan tokar? Cikin rawar jiki Umaimah ta ce, ''Duk wacce kika zabar min.
Faduwa ta ce, ''Ki dauki ruwan tokar tunda na fiki haske, sai in dauki bakar.
Ta mikawa Umaimah mukullin motarta a hannu yayin da Umaimah ta ji tamkar a mafarki, wai yau
ita ce a kasar waje, har ta mallaki mota wanda tunda take a rayuwa ta ke matukar sha'awar duk
macen data ga tana tuki. Bata taba saka ran zata yi mota ba a rayuwarta. Duk da dan Adam ba ya
fitar da rai da samun rahamar Ubangiji. Allah Yana iya mallakawa bawanSa mulki, dukiya, lafiya
ga wanda Ya so, kuma Ya hana idan Ya so.
Umaimah ta yi tsalle ta kankame Faduwa suka hadu suka sha tsalle-tsalle suna murna su biyu.
Yayin da
tsurarun jama'ar da suke wajen suka jeru suna kallonsu, su ma fuskokinsu cike da murna sun
fuskanci abun alkhairi ne ya same su. Da yake Faduwa duk ta sansu sai ta dinga jawo su tana sanar
musu yau aka yi musu kyautar su. Ba ta fadi wanda ya saya musu ba, amma dai ta ce su zo gidanta
gobe da yamma zata yi gagarumar liyafa.
Faduwa da Umaimah ne suke tsaye a kofar gidan Abdul-Sabur suna kwankwasawa. Da alama ba ya
zaune a falo saboda sai da ya jima kafin ta bude.
Daga dukkan alamu ma daga wanka ya fito saboda jikinsa a jike da ruwa yake, yana sanye da
doguwar riga jallabiya.
Yaune karo na farko da Umaimah ta tako bangarensa (block) ballantana ta shigo gidansa. Ya yi
matukar mamaki da ganinta, kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da hakan. Ya yi musu iso suka
shiga suka zazzauna a falo, yayin da ya nemi izininsu sannan ya shiga daki ya saka kayansa riga da
wando (jeans & T.Shirt) ya fito ya zauna tare da su. Suka gaishe shi sannan Faduwa ta fara bayani.
Ta ce, ''Abdul ka fadawa Umaimah da bakinka ko zata yarda saboda na ga alama har yanzu ba ta
gama yarda cewar wadannan motocinmu ne ba, kai ka sayo mana.
Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya, ya ce,
''Umaimah, me ye abin mamaki?
Ai tunda ku ka daure ku ka koyi mota, mallakar motar ba wahala ba ce tunda basu da tsada a
Malaysia. Ni na ga ya dace in ba wa kowaccenku ku huta da hawa motar haya, tafiyar kafa ko hawa
jirgin kasa.
Umaimah ta silalo daga kan kujera ta durkusa ta yi masa godiya, gami da dogayen addu'o'i na fatan
alkhairi. Yayin da Faduwa ma ta silmiyo daga kan kujera ta durkusa itama a gabansa ta rangada
godiya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Haba-haba meye haka? Ya za ku durkusa min kamar wanda na ba ku duniya?
Allah na tuba nawa motocin nan suke da har za ku dinga irin wannan doguwar godiya? Ku tashi ku
zazzauna. Fatana Allah Ya kiyaye tsautsayi da asara.
Suka amsa da, ''Amin''. Suka koma suka zazzauna.
Faduwa ta ce, ''Ina gayyatarka liyafa (lauching) din bude motocin gobe a gidana da yamma. Zaka
iya

gayyato abokanka guda biyu ku zo tare. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''A'a Faduwa ba na son
bidi'a. Me abun hada liyafa don kin yi mota?
Kin ga abin da yasa wataran ba ma shiri ko, kin cika rawar kai. Umaimah me ya kamata ku yi?
Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Godiya ga Allah.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa, haka ya kamata a yi ba holewa ba.
Faduwa ta zabura ta ce, ''To liyafa ba ciyar da Musulmai ba ce a sami lada?
Abdul-Sabur ya ce, ''Party za ki hada sosai da kek, da kunna disko na san sai kin cashe. Bayan
haduwa da mata da maza a waje daya wadanda ba muharramanku ba. Ni dai ganina tunda mu dukka
ukun nan mun sauke alkur'ani, mu kwana a daren yau muna karatu har sai mun sauke kur'ani. Mun
ci
sa'a kuwa yau alhamis ce daren juma'a, mu godewa Allah da Ya ba mu lafiya, arziki da zaman
lafiya. Sannan mu yi wa iyayenmu da *yan uwanmu musulmi da suka mutu fatan neman gafara da
aljanna ya kuma kai mu a sa'a idan tamu mutuwar ta zo. Mu yi fatan Allah Ya raba mu da sharrin
karfe
lafiya, Allah Ya sa a tuka su lafiya, a rabu lafiya.
Sai kuma mu yiwa kasarmu ta gado addu'a, wato Nageria fatan zaman lafiya da yalwal arziki da
wadata, mu yiwa sauran kasashenmu addu'a kamar su Ghana, Cairo da Malaysia kasashen
musulunci Allah Ya kare Musulmi da addininSa Musulunci.
A ganina haka ne kadai hanyar da zamu bi mu godewa Allah ba tare da mun saba maSa ba. Sannan
kafin ku fara hawa motar kowaccenku ta dafa saman motarta ta yi wannan addu'a
''Allahumma inni as'aluka min khariha wa khaira ma fiha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa'uzu bika
min sharrinha wa sharri ma fiha wa sharri ma jabaltaha alaihi.
''Ya Allah ina neman alkhairinta (mota) da alkhairi da yake tare da ita da alkhairin da Ka halicceta
akai
kuma ina neman tsarinKa daga sharrin ta da sharrin da yake tare da ita da sharrin da Ka halicce
ta akai.
Su dukka suka yi amanna da maganarsa, suka gasgata shi.
Umaimah ta mike tsaye ta ce, ''To karfe nawa za'a fara saukar kur'anin kuma a ina zamu hadu? Don
zan je duba tukunya na dora abinci.
Faduwa ta ce, ''A gidanki za'a taru bayan sallar isha'i na ga kina da kur'anai da yawa, idan mun ci
alala sai mu fara karatun. Abdul kada ka ci abincin dare yau ka zo gidan Umaimah ka ci alala daga
gani
zata yi dadi, saboda ta sha hanta da kwai ga albasa da attaruhu.
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ban cika son alala ba da dai danwake ne. Umaimah ta yi caraf ta
ce, ''Zan yi maka danwaken yanzun nan kuwa, ka zo ka ci.
Ya yi murmushi, ya ce, ''Na kuwa gode. Bari na je masallaci na yi sallar magruba da isha'i daga nan
sai na yi sallama da gida don karatun zai kai mu har asuba kun ga daga can sai mu yi jam'i mu yi
sallar asuba. Sannan kowa ya tafi gida yayi bacci da safe.
Ina fatan dai babu wanda ya ke da lecture ko test da sassafe gobe a Makaranta?
Su dukka suka ce ba su da lecture balle jarabawa.
Umaimah da Faduwa suka fito daga gidan Abdul-Sabur suka nufi gidajensu yayin da shi kuma ya
shiga bandaki ya dauro alwala dan Almuru (Magaruba) ta kawo kai, ya rufo gidansa ya nufi
masallaci.
Karfe takwas da rabi bayan sallar Isha'i Abdul-Sabur ya biya ta gidan Faduwa ko zama bai yi ba,
ya iske ta a shirye tsaf sanye da hijabinta ta idar da sallar isha'i dan haka sai ta rufo gidanta ita ma
suka
dungumo zuwa gidan Umaimah.
Bugu daya suka yiwa kofar sai ta zo ta bude musu.
Babu shakka sun yi farinciki da ganin Umaimah,
domin yadda ta karbe su da farin ciki. Ta tsaftace gidanta kal-kal-kal ko kwayar tsinke babu a kasa.
Kai ka ce harshe aka saka aka sude tiles din gidan.
Kamshin turaren wuta tururu daga shigowarsu kamshin ya daki hancinsu.

Umaimah sanye ta ke da riga da siket na material,
sannan ta saka dogon hijabi daga dukkan alamu daga sallah ta idar da carbi a hannunta. Kan dinning
table kai tsaye ta wuce da su inda ta tsara shi ta kawata da food flask da jugs na alfarma,
ga farantai da cokulla a gefe.
Daman su dukka ukun tsananin yunwa suke ji, sai suka zauna gaba dayansu kowa ya jawo
farantinsa
da cokali. Umaimah ta bubbude kowanne flask sai kamshi tururu ya daki hancinsu. Alala ce a flask
daya, dan wake a daya flask din, yayin da daya flask din hadaddiyar shinkafa ce 'fried rice' tasha
curry, hanta, peas da karas. Yayin da flask din karshe farfesun kaza ne mai romo da yawa an dafa da
dankalin turawa sun hadu sun dahu luguf sai
kamshi suje yi.
Dogon kofi (Jug) daya, kunun aya ne sannan daya kofin markadaddiyar kwakwa ce da abarba aka
tace aka zuba (coconut da pineaple) aka zuba dan sukari a ciki. Tabbas Yau Umamaimah ta yi musu
komai, saboda ta dafa musu abun da suke so. Sai ga Faduwa da ta ke son alala kawai ta buge da cin
shinkafa da danwake. Haka Abdul-Sabur da yake son dan wake ya hau cin alala da shinkafa gami
da farfesu da dankalin da aka jejjefa a cikin romo. Suka ci suka sha gami da yiwa Umaimah
doguwar godiya da jinjina bisa iya dafa zazzakan girki. To meye matsalar da zaisa abinci ya ki yin
dadi?
Da suka gama ci Umaimah ta kwashe kwanuka ta kai kicin ta wanke, sannan ta dawo suka matsar
da tebur din da yake tsakiya (center table) suka zazzauna akan kafet suka buda kur'anai. Izufi
ashirin-ashirin suka rarraba, Umaimah zata fara daga kasa, Faduwa daga sama, yayin da AbdulSabur ya dauki tsakiya.
Faduwa ta yi hamma gami da yin doguwar mika ta dubi Abdul-Sabur da Umaimah, ta ce, ''Anya
kuwa ba zamu bar saukar nan ba sai gobe da safe ba, da na ci abincin nan sai jikina ya mutu bacci
kawai nake ji.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ba ki isa ba, sai kin yi karatunan, kina gyangyadi ruwan sanyi zan watsa miki.
Kina so ki bari shaidan ya yi miki huduba, idan abun Allah ne sai ki dinga rauni, amma da party ne
ko za a kwana ba kya gajiya.
Faduwa ta dauki dogon salati, ta ce, ''Har haka na zama? Irin wannan shaidar zaka yi min?
A'uzubillahi minal shaidanir rajim, mu fara karatu na kori shaidan. Umaimah ta sha tuntsira dariya,
suka yi salati goma gafiyayyen halitta (S.A.W) sannan suka fara karatu babu wanda ya sake yin
magana a cikinsu . Ayar Allah kawai suke ta ragargazowa. Ba su sauke ba har sai da suka kai asuba.
Allah Ya amsa mana addu'o'inmu, Ya biya mana bukatunmu na alkhairi, amin!!
***************
Ranar lahadi da yamma Abdul-Sabur Faduwa da Umaimah suna zaune a wajen shakatawa na
jenting high land, wani gari ne mai nisa 51km daga KL. Wajen yin wasanni ne iri-iri da shakatawa,
wajen akan tsauni yake babu abinda kake hangowa daga sama sai fulawowi da ruwan teku.
Ga liluka wasu akan tsauni wasu a can kasa.
Yawancin mutanen da suka fi yawa a wajen turawa ne masu zuwa kasar musamman dan shakatawa.
Su Umaimah na zaune akan kujeru da tebur shake da kayan ciye-ciye kamar; gasassun kaji,
meatpie,
cake, gogguru, lemuka kala-kala. Tun daga karin kumallo na safe babu wanda ya kara cin abinci a
cikinsu, saboda haka yunwa ce take ta addabarsu,
suna zuwa sai suka hau yin maganinta. Abdul-Sabur ba ya kiwar kashe kudi komai ya tashi saya sai
ya jifgo da yawa, yadda zai ishe su, su ci har su bari.
Don haka har nauyi da kunyarsa suke ji wani lokaci su yi kokarin fitar da kudi za su biya sai ya
hana su.
Ransa yana baci da duk wacce ta aikata hakan daga cikinsu, don haka ma suka daina damuwa da sai
sun dauko jakar kudi don babu abin da zai bari su saya da kansu. Sannan ya gargade su da su daina
yi masa godiya duk abin da ya yi musu yana yi musu ne saboda Allah.
Wai! Wai! Wa ya ga garabasa?

Tabbas cikin *yan watannin nan Umaimah da Faduwa sun yi kiba sun kara jawur saboda ciye-ciye
da kwanciyar hankalin da suka samu.
Abdul-Sabur din ma a dalilinsu yana samu ya ci abinci sosai sabanin da da yake ci shi kadai ba ya
iya ci da
yawa.
Mutum rahma ne inji masu iya magana, hira suke yi sosai ta shakuwa. Umaimah ta dubi Faduwa ta
juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Wani lokaci ma sai in ji farin ciki ya yi min yawa, saboda na duba,
na hanga a halin yanzu
babu abin da yake damuna na kuncin rayuwa ko akwai abin da na rasa ma kadan ne, shima ban
daukesa a matsayin damuwa ba. Allah Shine abin godiya, shi kadai Ya cancanci a godewa a koda
yaushe.
KU DAN HUTA ANAN SAI ZUWA GOBE DA YARDAR ALLAH A KWAI CI GABA
INA GAYYATAR KU XUWA SHAFINA NA FACEBOOK DOMIN SADA XUMUN TA DA
FADAKAR DA JUNAMAKWABTAKA 35
Faduwa da Abdul-Sabur suka yi murmushi,
Faduwa ta ce, ''Gaskiya ne kanwata babu abin da yake damuna ni ma yanzu a duniya. Iyayenmu da
suka
rigamu gidan gaskiya muna yi musu addu'a Allah Ya kai rahma kabarinsu, amma na cire damuwa
da bakin ciki daga cikin zuciyata.
Son Sagir da talauci da yake addabata a baya sun gushe. Saura watanni uku in kammala karatuna, a
take ina da upper ta aiki. Albashi mai tsoka, gida da motar hawa duk
kyauta za a ba ni. Miji kuwa na hakura da nemansa, idan Allah Ya yi zan yi aure, in lokaci ya yi zan
yi,
idan kuwa ba ni da rabon aure a duniya ina addu'a Allah Ya tayani tsare kaina da kama mutuncina
har
karshen rayuwa.
Tausayinta ya rufe Abdul-Sabur da Umaimah. Ya girgiza kai ya ce, ''Ki ma daina irin wannan
magana za ki yi aure insha Allah ki hayayyafa, fatana ace kafin ma ki karbi takardar aikin naki a
hannu ki
sami mijinki a hannu kin ga dai-dai ke nan.
Faduwa da Umaimah suka amsa da, ''Amin, amin Ya rabbi.
Abdul-sabur ya gyara zama ya yi murmushi ya dubi Faduwa, ya ce, ''Ai ni da ina so ki ba ni
adireshin Sagir idan na je Cairo in neme shi mu zauna inji yadda za'a yi a yi komai in dai zai yiwu.
Faduwa ta harare shi, ta ce, ''Ka ji shi da tsokana ko,
shekaru nawa da rabuwarmu ya taba nemana? Ai in mahaifiyarsa na raye auren nan da kyar zai
yuwu, sai dai ikon Allah. Nasan ma ya yi aurensa ya manta da ni. Don ni ma gaskiya da kyar zan
iya zama da Sagir yanzu, saboda na sake wayewa nasan daraja da martabar kaina yanzu, ba wai na
fi karfinsa ba ne, a'a na ga yadda ake kula da
tarairayar mace, bana tunanin Sagir zai iya yi min irin wannan tarairayar dana gani.
Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''A ina kika ga tarairayar mace? Ai matan Malaysia su
suke fita su nemo abincinsu, yaransu da manyansu kowa aiki yake yi dan ya ciyar da kansa. Kin
manta sai kiga mata da miji da *ya*yansu sun je cin abinci restaurant kowa ya ci ya biya nasa?
Faduwa ta ce, ''Na san da wannan amma ni yanzu na ga inda namiji yake tarairayar matarsa, sai ya
burge ni haka nake fata in auri irinsa.
Abdul-Sabur ya tabe baki ya ce, ''Ke kike leke-lekenki har kika hango wannan daman shegen yawo
gare ki, gidajen kawaye iri-iri.
''Eh anyi yawon, Faduwa ta fada a fusace.
Umaimah ta kyalkyale da dariya, daman ita ba ta da aiki sai dariya idan ta ji sun fara irin wannan
fadan nasu.
Abdul-Sabur ne ya katse dariyar da take kyakyatawa, nan da nan dariyar ta koma fushi.

Da ya ce, ''Ke kuma Umaimah idan na je Nigeria zan je har Kaduna mu zauna da Abdul-Basi idan
kuma Ilah kika fi so zan je Dugge mu gana. Kada ki ji tsoron Matawata, zan yi mata nasiha ku
zauna lafiya.
Faduwa ta kyalkyale da dariya, har da tsugunawa yayin da Umaimah ta ji wani kululun takaici ya
dira
a cikin zuciyarta, kuma ba ta sha'awar auren Ilah ko kadan balle Abdul-Basi. Sabuwar rayuwa ce ta
bude don haka ba ta so ta waiwayi baya. Takaici ne sabo fil ya ke dirgo mata a kahon zuci har ta
tuna dacin da suka dandana mata a rayuwarta ta baya su dukka biyun.
Abdul-Sabur ma ya yi ta dariya daga karshe ya shiga lallashinta yana ba ta hakuri, don yaga da
gaske take ta yi fushi, har ta daina cin abincin.
Dariyar da Faduwa ta ke kyakyata mata ita tafi tunzura ta sai da Abdul-Sabur ya roki Faduwa ta
daina yi mata dariya kada ta sa ta kuka. Da faduwa ta ki dainawa sai ya ce, ''Zan je Nigeria in hada
ki da
Alhajin Birni.
Nan dai aka rincabe da Faduwa da Abdul-Sabur suka hau zolayar juna. Umaimah ta sami abin
dariya, tana ta kyakyatawa.
Abdul-Sabur ya saka hannu a aljihun wandonsa ya ciro wasu kananan katina guda biyu masu kyawu
da kyalkyali kai ka ce da ruwan gwal aka yi rubutun. Ya mikawa Faduwa daya, Umaimah ma guda
daya. Sai suka yi sauri suka karba suka karanta, daga dukkan alamu ba su fahimci ko katin mene ne
ba. Ba na gayyatar aure ba ne, haka ba na liyafa ba ne. Abin da za su iya gani shi ne 'Graduation
Ceremoney.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya gyada kai a lokacin da ya ga duk sun zuba masa ido suna neman karin
bayani daga gare shi.
Ya ce ''Me ye ba ku gane ba? Katin gayyata ne na bikin yaye mu mun gama karatun PhD za a bamu
satifiket. Lokaci ga shi nan an rubuta karfe goma na safe, waje ga adireshin nan da sunan hotel din
'J.W MaRRIOTT HOTEL'. A bukit Bing Tang. Sai kun nuna katin nan za a barku ku shiga, shi ne
ya sa na
karbo muku. Ku yi kokari ku fito da wuri gobe, tara da rabi ta yi muku a can. Tafiyarmu ba zata
zama
daya ba saboda ni a cikin makarant zan kwana, tun karfe bakwai na safe zamu shiga taro (meeting),
sannan a raba mana riguna da huluna (graduation gown) a zuba mu a doguwar motar makaranta a
kawo mu can.
*Yan uwa da abokan arziki za su zo daga kasashe daban-daban, ni dai ku ne *yan uwana kuma
dangina, in kuka makara ba ku zo ba shikenan na zama ba ni da kowa, babu mai daukana a hoto a
lokacin da ake mika min satifiket.
Faduwa da Umaimah suka zabura suka hada baki, ''Ah haba zamu zo mana.
Abdul-Sabur ya yi

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment