Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

goma sha hudu a sama sannan suka
isa Cairo da misalin karfe shida na asuba agogon Cairo,
sannan aka kwashe su a motoci aka rarraba su a Hotels. Saboda yawansu ma a Hotel daban-daban
aka rarrabasu, dan sai sun shafe awanni goma sha biyu sannan zasu taho Nigeria. Duk daki daya
mutane biyu aka rarraba, Umaimah da kawarta Aisha dakinsu daya, bata ga Abdul-Basi ba daman
ba nemansa take ba. Bata ga Lamijo da mijinta ba amma taga Hanif shi da abokinsa Bashir Wada, a
kusa da dakinsu ma suke. Burinta kawai ta shiga dakin ta kwanta saboda gajiya da bacci, sai bayan
data yi bacci ya ishe ta sannan suka yi wanka da salloli suka sauko suka ci abinci. Saida yamma
karfe biyar aka kawo motoci aka kwashe su zuwa jirgi
da karfe shida na yamma jirgi ya tashi zuwa Abuja,
tafiyar ba nisa sosai awanni uku da rabi ne kacal, suka isa Abuja da karfe goma na dare a birni
tarayya ta yi musu.
.
Plz in barar addu,ar ku bani da lapy Ngd
MAKWABTAKA 43
ABUJA, NIGERIA
Suka ci sa'a kuwa suka sauka da kayansu gaba daya kafin su iso dogayen motocin gidan gwamnatin
garinsu sun zo sun jeru reras suna jiransu a filin jirgi, suna fitowa sai suka duru a ciki su da kayansu
a ka zarce dasu katafaren Hotel. Aka rarraba su mata dakunansu daban, maza ma dakunansu daban,
mutane uku-uku. Daliban ne kadai aka kai wannan Hotel din sauran kowa ya
tafi ya kama nasa da kudinsa masu gidan *yan uwa ko abokai suka tafi can.
Ta san Abdul-Basi gidan Yayansa ya tafi wato Abdul-Badi.
Washi gari da sanyin safiya suka shirya suka shiga motocin suka nufi garinsu Gombe, nan danan
suka
isa, abinka da motoci masu lafiya.
GOMBE, NIGERIA Suna shiga garin sai suka gan shi kamar anyi gobara haka mutanen garin duk
sun yi baki-kirin,
amma ba baki suka yi ba haka garin ba ayi gobara ba, illa sun saba ganin jajayen fata da dogayen
gininnika kamar gidajen tangaran.

Gidan Gwamna aka zarce da su sai suka iske gidan a cike da masu taryarsu, Umaimah bata damu da
duba nata *yan uwan ba ta san babu mai zuwa mata duk da dai su Baffa sun san tana tafe amma ba
suyi da ita za su zo ba.
Gagarumar liyafa aka shirya musu a gidan Gwamna, aka yi dafe-dafe iri-iri aka zazzauna akan
kujeru da suke babban dakin taron da yake gidan gwamnati, tare da mai girma Gwamna aka ci. Da
aka ci, aka sha, sai ya yi musu jawabin maraba gami da yaba musu bisa kokarin cin jarabawa da
kowannensu yayi sannan ya gode musu da cika masa alkawarin da suka yi suka je can basu yi wani
abu na rashin da'a ba.
Dalibai uku maza biyu, mace daya suka tashi suka yiwa mai girma gwamna godiya bisa dawainiyar
da
ya sha yi da su har suka kammala karatunsu na tsawon shekara uku bai taba gajiyawa ba.
Daga karshe aka umarci kowannensu ya dauki kayansa ya tafi gida, za'a neme su nan da wata daya
da rabi zasu tafi bautar kasa. Abuja za su yi bautar kasarsu dan haka acan zasu karbo takardunsu
wato 'Call up letter.
Umaimah Bello ce ke tsaye a farfajiyar gidan gwamnati tana kallon kawayenta da abokananta suna
ta tururuwar shiga cikin tsala-tsalan motocin iyayensu.
Allah Sarki, ita kuwa bata da kowa da ya zo daukar ta a mota, ta na tsaye tana ta zulumin yadda zata
yi. Shawara take ko dai ta fita ta je ta samo tasi ta zo ta kwashi kayan akaita har Dugge,
amma anya kuwa jami'an tsaro zasu bar dan tasi ya shigo wannan gida?
Gashi kayan kuma ba zasu dauku ba da sai ta kinkima zuwa bakin titi ta hau mota amma saboda
yawansu da nauyinsu ba zata iya ba.
Tana cikin wannan tunani sai ta ga Hanif a gabanta.
Ya ce "Ke muke neme tun dazu, Baba ya ce ki zo ki shiga mota mu tafi gidanmu ki kwana gobe sai
a
kai ki gida.
Sai ta ji gabanta ya fadi nan da nan muryarta ta dauki rawa dan ba zata iya zuwa gidan Lamijo ta
kwana ba har abada.
Ta ce, "A'a na gode, yanzu nake so in tafi gida, Hanif ka taya ni yiwa Baba bayani dan ya fahimce
ni, ba kin bin ku nayi ba.
Hanif ya ce, "To ina motar da zata kai ki gida?
Umaimah ta ce, "Yanzu nake tunanin ko bakin titi zan fita in nemo tasi?
Ko kuma kayan zan baka ka tafi min da shi ni kuma sai in tafi tasha in dauko mota in zo gidanku in
dauka amma gidanku ba gidan Lamijo ba zaka kai min dan gidanku ya fi kusa da tasha.
Hanif ya ce, ''Nifa bana so in ji kina maganar motar haya, ke fa babbar yarinya ce. Kina da mota a
Malaysia taki ta kanki a kasar ku a ganki a motar haya. Ki zo mu je gidanmu kawai ki kwana gobe
da wuri zan tashi in kai ki Dugge da kaina.
Umaimah, ta girgiza kai alamar bata amince ba,
wani takaici ya rufe ta data ji wannan bayanai na Hanif, kai da jin bayanan Hanif ka san da sauran
kuruciya a kansa, da kuma gata da yayi masa yawa bai san wahala ba, shi dai magiya yake yi mata.
Tabbas tun yanzu Umaimah ta san ta fara tozarta a kasarsu.
Kamar daga sama ta ji wata murya ta kira sunanta,
muryar ta yi mata kama da muryar data sani tana kuma matukar kewar mai muryar, amma bata
zaton bayyannar mai muryar a halin yanzu kuma adaidai wannan lokaci. Ta waiga da sauri ta dubi
inda sautin yake fitowa tabbas mai muryar da take tunani ne. Baffanta ta gani a tsaye, Sabitu da
kuma
Ilah cikin yagulallun rigunansu, kai kace daga bakin kura aka kwato kayan jikinsu, basu yage ba
amma sun kode sunyi yaushi. Daman ta san za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, duk da ta aiko
musu da makudan kudi ta san ba zasu saki jiki su ci ba, boyewa zasu yi su cigaba da wahala daman
ita suka saba yi. Ta ji hankalinta yayi matukar tashi data gansu cikin wannan hali dan ma wai sun yi
wanka sun caba ado zasu shigo birni taryar babbar bakuwa daga kasar waje.
Cike da mamaki gami da farin ciki mabayyani ta ruga da sauri kai tsaye wajen Baffanta ta nufa ta
kankame shi su dukka suna kukan murna, ta rike hannun Sabitu shima

hawayen murna yake, sannan ta juya ta kalli Ilah duk ya tsufa saboda talauci ga *ya*ya, ga masifar
Matawata.
A sanyaye ta ambaci sunansa ''Hamma Ilah, ina wuni.
Ya yi murmushin dadi, yayi caraf cike da murnar ganin amaryarsa ya ce, ''Lafiya Umaimah, sannu
da dawowa. Sai suka ji ana ta matsa 'horn' din mota a bayansu nan da nan suka waiwaya, mota
dankareriya kirar BENZA suka sake tabbatarwa da su mai motar yake, amma ba su gane ko waye
ba saboda gilashin motar a rufe kuma bakin-kirin basa ganin cikin motar. Ko daya sauke gilashin
motar, ya zare bakin gilashin da yake fuskarsa sai suka shaida shi.
Abdul-Basi ne ya bayyana muraran a gaban su.
Ta dukar da kai kasa ya ce, ''Baffa, ina wuni. Ku shigo mota in kai ku gida.
Baffa, Sabitu da Ilah sai suka zubawa Umaimah ido suna jiran su ji abunda zata ce. Ta kuwa sha
kunu tana harararsa zuciyarta cike da tsantsar tsanarsa,
ta cije baki ta juya ta dubi Baffa ta girgiza kai.
Ta ce ''Kada ku shiga motarsa tunda ba shi ya kawo ku ba.
Aka yi carko-carko na kallon-kallo tsakanin Umaima da Abdul-Basi daga dukkan alamu yana
mamaki yadda Umaimah ta waye har ta fara yi masa musu. Sai ya sauke gilashin kujerun bayan
motarsa,
sai ga Babangida da Bilal sun bayyana. Su ma aka hau kallon-kallo da su da su Umaimah, da farko
yaran basu shaida ta ba. Sai ta ji wani farin ciki ya lullubeta, ta runtse ido dan ta tabbatar ba'a
mafarki take ganinsu ba sannan ta bude ido ta tabbata zahiri take ba'a mafarki ba, ta yi murmushi ta
ambaci sunayen yaran.
''Baku gane Anti Umaimah ta Malaysia, ba na fada muku a waya nace zan zo ba?
Sai suka gasgata ita ce suka fara tafa hannu da ihu suna tsalle, yayin da suka yunkura zasu bude
kofa su rugo wajenta, Babansu ya dakatar da su.
Ya ce ''Ku koma ku zauna zata zo.
Yana so ya nuna mata idan ta isa da Baffanta shima ya isa da *ya*yansa. Aka jima ana kallonkallon,
har yanzu su Umaimah na tsaye a inda suke haka Abdul-Basi da *ya*yanta suna zaune a cikin mota.
Sai fullanci ya hargitse tsakanin Baffa da Sabitu suna rokarta data manta da abubuwan da yayi mata
a baya ta dubi albarkacin yara ta yafe masa.
Wanne miji take da shi yanzu a duniya wanda ya wuce shi, mutumin da ya rike ta tun tana karama,
ya dauki nauyin karatunta har ta zama mutum. Ba dan tubalin karatu (firamare da sakandire) daya
bata ba ada a ina za ta sami ilimin da har zata sami damar tafiya kasar waje ta yi karatu?
Ita kuma tana fada musu irin wulakanci da korar karen da yayi mata a lokacin daya tabbatar bata da
kowa din sai shi.
Baffa yana hawaye a zuciye ya jawo hannunta ya tura ta cikin mota kusa da *ya*yanta ta rushe da
kuka ta rungume su. Baffa ya shiga kusa da Umaimah ya zauna, Sabitu ya zauna kusa da Baffa,
dukkansu a gidan baya, yayin da Ilah ya ja burki ya tsaya cak. Baffa ya leko ta windo ya ce da Ilah
ya
shiga gaban mota ya zauna. Ilah ya ce su tafi kawai ba zai shiga motar ba zai taho a motar haya.
Da alama dai kishi ne ya ke zakularsa, wannan shi ake kira da 'ta leko ta koma kenan' har da ya fara
murna Umaimarsa ta rabu da Abdu-Basi zasu daidaita gashi ya dawo, har su Baffa sun fara goyon
bayansa. Aka hau galle-gallan harara a tsakanin Ilah da Abdul-Basi yayin da Umaimah ke
tsakiya tana kallon ikon Allah da mamaki marar adadi.
Kishi kumallom maza!!!
Baffa dai har yanzu magiya yake yiwa Ilah don ya shigo motar, ya ce in dai ka dauke ni uba kamar
yadda ka dauki Jani to ka shiga mu tafi.
Umaimah ta ce, ''Hamma Ilah, yi hakuri ka shiga mu tafi kada ka damu.
Nan da nan ya ji sanyi a ransa. Sai yayi amanna da maganarsu, har da tafiyar takama yake yi saboda
ko a yanzu Umaimah ta gwada wanda ta fi so a cikinsu shi ta zaba, ya zo ya bude gidan gaba ya
zauna basu daina gallawa juna harara ba har
yanzu.

''A ina kayanki suke?
Abdul-Basi ya tambayi Umaimah a gadarance ba tare da ya juyo ya kalle ta ba.
Ta turo baki tayi masa nuni da hannu ba tare da tayi masa magana ba, ya ja mota ya tafi kusa da
kayan. Da yake babbar mota ce tana da katon but yana daga zaune bai fita ba sai ya bude but ya kira
wasu kartai ma'aikatan gidan gwamna masu jidar kaya a cikin but. Nan da nan suka dinga cicciba
suna sakawa har suka gama, ya zaro naira dubu ya basu.
Abdul-Basi ya yi addu'ar tafiya, ya zaro bakin gilashi daga aljihunsa ya saka, ya daga gilashin
windunan mota sama, ya kunna Ac gami da sautin kida a hankali, ya fisgi mota ya kama hanyar
Dugge.
Gudu yake ba kakkautawa, bai sake
magana ba kuma babu mai yin magana a cikin motar, sai muryar Babangida da Bilal ne ke tashi,
suna ta yiwa Umaimah hira kala-kala, tana biye musu suna hira amma gaba daya hankalinta a tashe
yake. Ganin Abdul-Basi da tayi ya ruguza mata lissafi gaba daya amma ta ji dadi ya kawo
mata *ya*yanta, tun daga cikin mota ta fara zakulo musu tsarabarsu ta alawoyi masu dadi da tsada
sai suka ji sun kara sonta dan suna kaular alewa sosai.
Suna shiga Dugge sai Umaimah taga yara da samarin garin kacokan sun firfito waje suna daga mata
hannu daga dukkan alamu taryarta kowa ya fito yi sai farin ciki ya rufe ta, tausayinsu ya kamata
saboda ta gansu har yanzu a gidan jiya babu wani ci gaba a tare da su. Sai taga garinsu ya zama
tamkar wanda aka cisu a da yaki, bututu da su a cikin yashi. Amma bada yaki aka ci garin ba tsabar
talauci ne daman can ma haka suke, dan ta saba ganin titina dodar da kwalta, fitulu da dogayen
gininnika, a garin fararen fata garau-garau. Ta dinga addu'a a zuciyarta Allah Ya taimaki Africa da
garinsu Dugge, su sami ci gaba suma su ji yadda a ke ji a kasashen da suka ci gaba. Amin.
Ta sauke gilashin kasa ta leko da kanta tana ta daga musu hannu, sai yanzu suka hangota dan da
duhun gilas yasa basa ganin komai suna ganinta sai murna ta karu. Yara suka biyo motar a guje har
kofar gidansu suna fadin ''ga Umaimah daga turai'' tana fitowa daga mota sai suka ganta ta juye jar
fata ta zama tamkar balarabiya jajawur a cikin bakar abaya, ta yi kyau, ta yi kiba, sai kamshin turare
take. A haka ta dinga rungumar yara kaca-kaca da su, duk wacce ta ci sa'a Umaimah ta taba ta sai ta
ji tamkar an yi mata gafara dan ta sami babban rabo a duniya, sai ka ji
suna cewa kamshinta ya shafe ni, su dinga shinshina kayan su.
Mata suka dinga leke ta saman katangu ko zana suna kallon Umaimah, sai rike baki ake saboda
mamakin wannan canjawa da ta yi. Har sai da ta gaji da gaisawa da jama'a ta shiga gida, yuu!
Kungiya guda aka bita ciki.
Nene da Inna da murna suka fito suka rungume Umaimah tabbas yau sun san ba karamar daukaka
Allah Ya yi musu ba da Ya sa suka auri Baffa wanda ya haifi wannan galleleliyar yarinya
Umaimah, ba
karamin abun alfahari ba ne a ga Umaiman ta wuce kowanne gida ta shigo gidan da suke.
Subhan Allah,
sai Umaimah taga gidansu tamkar turken shanu, dakinta tamkar kejin kaji wai dan ma saboda
zuwanta Baffa yasa an yabe shi da jar kasa, an share, an shinfida sabuwar leda da sabuwar katifa
karama, ga sabon labule. Su Sabitu suka dinga jidar manyan jakunkunanta suna saka mata a daki.
Babangida da Bilal suka rirrike Umaimah wai ba za su shiga dakin nan ba itama ba zata shiga ba sai
dai ta zo su tafi gidansu, dadi ya rufe Abdul-Basi yadda zata ji zuciyarta ta karaya saboda yara ta
koma gidansa.
Nene tana rawar jiki ta yiwa Baffa da Abdul-Basi shimfidar tabarmar kaba a zaure, ta kawo musu
dakwalkwalin ruwan sha a kwanan
sha, ko ba'a fada ba Abdul-Basi ba zai iya shan wannan ruwa ba da ruwansa na roba a mota.
Umaimah ta dinga lallashinsu yaran dakyar suka shiga dakin a bisa sharadin ana jimawa zasu fito su
tafi da ita.
Mata, yara da manya kowacce ta wanko kafa ta zo yiwa gimbiya Umaimah sannu da zuwa har da
masu guzurin abinci, wasu dafaffiyar kaza, wasu fura da nono aka jere mata a gabanta, sai godiya
take tana ta gaisawa da mutane har sai da ta ji ba dadi, kanta ya fara ciwo saboda ta dade
rabon data ji rin wannan hayaniya, gida ya cika dankar kai ka ce gidan biki ne.

Kowacce mace a dangi da MAKWABTAN Umaimah sun hallara a gidan amma banda Matawata, ta
kulle kanta a daki ita da *ya*yanta ta hana su fitowa, sai cizon yatsa take tana kai kawo daga
wannan
bango zuwa wancan bango, zama balle kwanciya sun gagare ta saboda bakin cikin dawowar
Umaimah musamman Ilah ya shirya ya je har Gombe taryar ta. Daman ta san da wanan maganar
har yanzu yana son Umaimah, ya fada da bakinsa ba zai daina sonta ba har abada. Ko bayan ransa
yana fatan Allah Ya hada su a aljanna su zauna tare.
Duk da ta rufe kanta a daki babu abinda bata jiyowa daga gidan su Umaimah, shewa kawai ake yi
ana yiwa Umaimah kirari ana yabawa da kyawun da ta tsatso a can, har ma ana kwatantata da ta
zama tsoka daya a miya dan ita ce *yan asalin garin ta farko data taba yin karatu mai zurfi kuma ma
ba akasar nan ba a kasar waje.
Rashin sani yafi dare duhu bata san kuncin da Ilah yake ciki ba a yau har ya fi nata saboda yaga
alamar Abdul-Basi da gaske biko yake nema. Ya kasa zaman gida ya kaura gaba daya bakin rafi ya
zauna yana lazimi.
Hehehehe..
Duk naku wasa ne kallon ku kawai nake naga iya gudun ruwan ku.
Dan Umaimah ta dan Aunty ce..MAKWABTAKA 44
A lokacin da Umaimah take fama da baki a cikin gida, Abdul-Basi ya tara dattijai masu fada aji a
gari
cikin zauran gidan, yana yi musu bayanai da basu hujjoji da zasu yarda dashi a tilastawa Umaimah
ta koma gidansa.
Daga duk alamu ba alfarma ya ke nema ba illa shi ne zai yi musu alfarma saboda ya na ganin su
kidahumai babu boko, ba wayewa, ga talauci, na masara da dawa kawai suke nema.
Baffa da Sabitu suna gefe ba su ce komai ba daga dukkan alamu ba su yi amanna da bukatunsa ba.
Abdul-Basi ya kula da haka sai ya tuno wata hanya wacce zai bi ba sai ya bi ta wajen Baffa ba
kuma ita
ce hanya mafi sauki da zai cimma burinsa, daman ta inda a hau tanan ake sauka ba da Baffa suka yi
magana ba, da Dagaci suka yi magana tun a lokacin auren Nasiba dan haka da ya gama dandankawa
dattijai na goro sai ya dunkulo kudi mai dan yawa ya ajiye a gaban Baffa da Sabitu ya mike tsaye ya
ce
zai je ya gaida Dagaci.
Da kafa ya tafi ya bar bar motarsa a kofar gidan,
yana fita Baffa ya juya ya kalli *yan uwa da abokansa na zaune a wannan zauren ya ce, ''Kada ku yi
gaggawar amsawa Abdul-basi, yanzu ba ra'ayinmu za'a bi ba ra'ayin yarinya za'a bi tunda ita ce ta
zauna da shi ita ya wulakanta kuma ya wahalar, ita ce kuma nan gaba zata zauna da shi dan haka sai
abun da ta zaba za'a yi.
Wasu daga cikinsu suka gasgata da maganarsa,
wasu kuwa suka ce ba zai yiwu ba, ba za'a bi ra'ayin yarinya ba, dan ba ita ce ta haife su ba su suka
haifeta. Ko dan tayi ilimi tayi kudi shine zata gagari manya?
To in shi ba zai iya tsawatar mata ba saboda ta aiko masa da makudan kudi yayi jari su zasu iya
tsawatar mata.
Surutai dai barkatai suka dinyi suna fada harda kumfar baki.
Sabitu ya kufula ya bude baki zai yi magana, Baffa ya hana shi. Haka aka tashi daga taro barambaram
Baffa da Sabitu ne kawai suka rage a zaune a zauren.
Baffa ya ce Sabitu ya shiga gida ya kira masa Umaimah, shigar Sabitu gida ba dadewa sai ga shi da
Umaimah sun bayyana a gaban Baffa.
A gigice ta fito yayin da zuciyarta ta dinga dukan uku-uku ta san maganar dai ta Abdul-Basi ce.
Fargabar da take yi ita ce wanne hukunci Baffa ya yanke akan maganar, tafi kyautata zaton Baffa
yana goyon bayan Abdul-Basi yin hakan kuwa da Baffa zai yi ba karamar matsala zai tayar mata ba,
dan ba zata bi ra'ayinsu ba. *Ya*yanta suna makale da ita suka zazzauna.
''Baffa lafiya na ganku a cikin damuwa?

Umaimah ta tambaye shi cike da rikicewa.
Ya dago a hankali ya dube ta tabbas har yanzu babu annuri a fuskarsa. Ya gyada kai ya ce,
"Umaimah na shiga matsanciyar damuwa akan maganarki da Abdul-Basi, yana son ki koma
gidansa, dangina da abokaina suna son ki koma.
Yaya kike gani?
Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Baffa, ka tuna a sanda Abdul-Basi ya kore ni, kunya nake ji wani
ma ya ji abunda yayi min. Kai kanka ma kasa fada maka nayi ina ta rufewa ina ganin kamar zai zo
ya
mayar dani. Ya juya min baya bai sake waiwayata ba balle yasan wanne hali nake ciki. Alokacin
koda na fito da maganar wadannan mutanen nan da kake kiransu *yan uwanka, abokanka babu
mutum daya da zai iya tashi ya je ya cewa Abdul-Basi bai kyauta ba, ya zo ya mayar dani. Daga
masu murna da surutu, suna yada zance, sai wadanda za suyi dariya suce Allah Ya kara, babu
wanda yasan wahalar da na sha, na dinga garari a garin Gombe har hannun karuwai na kusa fadawa,
Allah ne Ya kiyaye ni ka tambayi Sabitu duk na bashi labarin yadda aka yi.
Baffa zamani ya canja, kan mage ya waye, ka rabu da ra'ayin mutane ka yi abunda ya dace da kai.
Maganar gaskiya ita ce Abdul-Basi yayi sha'aninsa in yi nawa ba zan iya aurensa ba, dan zamanmu
a
yanzu ba zai yiwu ba.
Baffa ya nisa ya ce, "Bakya tausayin yaran nan da suka shaku dake, ki duba kiga yadda suka
rirrikeki basa so ku rabu.
Umaimah ta dubesu ta sirnano da hawaye mai radadi ta ce, ''Rayuwarsu, cinsu, shansu da kariya duk
yana hannun mahaliccinsu. Shi Ya rayasu a lokacin da suna kanana basu ma kai haka ba na tafi na
bar su, ina kuka suna kuka Abdul-Basi ya rabamu. Duk inda suke ina yi musu addu'a kuma zata isa
gare su, duk daren dadewa za su zo inda nake.
Baffa ya girgiza kai ya ce, ''Bakya ganin zan zama abin tsana a wajen Dagaci da sauran jama'ar gari
idan na bi bayanki?
Yanzu ma an yi min gori wai dan kin yi ilimi, kin yi kudi, kin aiko min da jari shiyasa bana iya
tsawatar miki.
Umaimah ta ce, "Abun da na gama fada maka fa kenan, ka bi ra'ayinka ka rabu da mutane dan
mutane ba'a iya musu. Su je suyi magana har su gaji su daina babu abinda zai shafe mu.
Duhu ya gushe haske ya zo, kai yanzu ya waye, talauci ya tafi. Babu abinda yanzu wani zai iya yi
maka wanda bazan iya yi maka shi ba, daga Abdul-Basi har Dagaci balle
abokanka. Ka toshe kunnuwanka, ka rufe idanuwanka, ka zamo baka ji baka gani su je su ce duk
abunda zasu ce.
Sabitu ya kyalkyale da dariya ya yi tafi ya ce, ''Yayi daidai Adda Umaiman, maganarki haka take.
Baffa ya girgiza kai ya ce ''haka za ki ci gaba da zama a cikin Rugar nan ba aure, ko birni zaki je ki
kama gida ba aure ki zauna?
Ai sai a zage mu.
Umaimah ta gyara zama yayin da ciwon da kanta ke yi ya sake tsananta ta ce, "Ba'a kaina mace take
zama a gidansu ba idan aurenta ya mutu ba, har zuwa ranar da Allah Zai aiko da wani mijin ayi
aure.
Me zai hana ni zama a gidan nan tunda anan Allah Ya rubuto min, anan aka haife ni harna girma,
anan zan zauna inci gaba da rayuwata irin ta da. Ba zan koma birni da zama ba duk da cewa ya
kamata in fara aiki sai in hakura da aikin, nima nasan bai kamata a ce ina zaman kaina ba a can. Ni
dai zan
hakura da duk wani jin dadi da zan samu in dai sai na koma gidan Abdul-Basi.
Baffa ya ce, ''A tsakanin Rugagen nan wanne namiji kike gani zai iya tunkararki da maganar aure?
Kowa gudunki zai yi saboda kinfi karfinsu babu mai iya aurenki. Idan Ilah kike so har yanzu shima
yana sonki, amma kinsan halin Matawata, kin kuma san irin tashin hankalin da aka yi a baya.
Umaimah ta yi murmushin takaici ta dubin yaran da suke kwance a jikinta ta yi magana cikin
harshe turanci ta ce su tashi su shiga gida zata shigo itama yanzu.
Yara masu hankali da jin magana suka tashi cimak suka shiga gida.

Ta dubi Baffa ta juya ta dubi Sabitu ta ce, ''A yanzu ba ni da wanda nake so a duniya irin AbdulSabur,
shine kadai namiji daya da halayyarsa suka yi min, kuma wanda zan iya zama da shi in yi masa
biyayyar aure.
''Waye Abdul-Sabur?
Baffa da Sabitu suka hada baki suka tambaye ta.
Ta yi mumushi kuma hawaye ya cika mata ido ta gyara zama ta fara basu labarin Abdul-Sabur. Ta
fara da fayyace musu asali, yare, da kuma kasar da ya fito, ta fada musu a inda suka hadu da yadda
akayi suka hadu, yadda aka yi suka saba da dalilin da ya sa ta fara sonsa da yadda kyawawan
halayensa suka saka take marmarin aurensa sannan ta fada musu yadda suka rabu.
Sai suka tausaya mata saboda suma sun san ta rasa Abdul-Sabur din data ke so.
Baffa ya ce, "Zaki ki auren mutumin da kike da shi a hannu saboda mutumin da baki da tabbacin ko
zaki sake ganinsa a rayuwarki ba? Kuma har ya fada miki da bakinsa ya tafi ya auri *yar uwarsa.
Dadin dadawa kuma bai ma san kina nan kina sonsa ba, dan haka ko yana sonki ba zai yi garajen
nemanki ba.
Ta sharce hawaye ta gyada kai ta ce, "Wannan haka yake, ko ban same shi ba na tabbata shi nake so
kuma zan sami wani makamancinsa amma ba Abdul-Basi ba.
Kafin ta rufe bakinta suka ji sallama suka daga kai gaba daya suka kalli me shigowa, Musa ne daya
daga cikin fadawan Dagaci, ya duka ya gaishe da Baffa ya shaida masa ana kira a fada.
Baffa da Umaimah suka zurawa juna ido can Umaimah ta juya ta dubi Musa Ta ce "Malam Musa,
ka je ka ce gashi nan zuwa Ya fice da sauri da sauri, ta dubi Sabitu ta ce ''Ka raka shi

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment