Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauki
dana
na tafi jikina a sanyaye ina ta hawaye
ina jin
bakin cikin wulakancin da ya tarki yi
min, da
kyar nake tafiya ga ciki ga goyo,
nauyi jikit.
Na fara jin alamun nakuda dan
lokacin
haihuwar ya cika. Na wuce gidan
Zulayha
Senegal na iske ta tana ta caba ado
sai na ga
ta yi min kallon banza. Na gaishe ta,
na
shaida mata na kawo mata Bilal ta
rike min
zan je unguwar Dosa yanzu zan
dawo, zan
dauko mai aiki....
Ban rufe bakina ba ta ce, ''dauki
danki ki tafi
da shi, nima unguwa zan je.
Na fice a sanyaye na nufi titi na tare
dan
acaba na hau. Banda kuka babu abin
da
nake yi. A gaban mai babur aka saka
Bilal
duk da ya yi kankanta a zaunar da
shi a nan
babu yadda zan yi, tsinin cikina
bazai bari na zaunar da shi a gaba
na ba,
haka ba zan iya yin goyo ba.
A lokacin ana taron siyasa a garin,
kowanne
titi a garin Kaduna motoci ne (go
slow). Don
haka sai muyi mintuna talatin akan
titi daya
kafin mu matsa gaba.
Kwatsam ina kan babur a cikin rana
ni da
dana, da mai acaba mun galabaita.

Juyawar
nan da zan yi,
sai na ga galleliyar motar Zulayha a
gefena,
koda na sake wurga ido itace a gefe
namiji
ne yake tukawa.
Sun yi luf a cikin AC babu ruwansu
da kura,
zafi, balle hayakin *yan acaba, dariya
suke yi
suna hira
da shewa, har da tafawa da hannu.
Ko da na
dubi mai tukawar sai na ga AbdulBasi ne.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Na
dinga
fada a bayyane, yayin da dan acaban
ya
gigice, ya fara tambayata ko lafiya?
Na barke da kuka, yayin da jikina ya
dau
karkarwa cewa nake, ''Ga miji na can
da
MAKWABCIYATA suna cin amanata.
Zulayha ce ta fara ganina, muka hada
ido, sai
ta zunguro Abdul-Basi ta nuna ni ga
mu nan
a kusa da su, muna daf da su. Sai
jikinsu ya
yi sanyi suka kasa hada ido da ni.
Mun jima kafin a bada hannu, su ka
ja da
gudu suka tafi suka bar mu a baya
muna
gurgurwa. Na ga masifa a ranar, na ji
kamar
na hadiyi zuciya na mutu. Dan
acaban ya yi
ta yimin nasiha yana bani hakuri,
suna
gabana ina hango motarsu, hanyar
kawo
suka yi da alama garin ma zasu bari
gaba
daya.
Gudu muke yi kawai a hanya, to ni
dai ban
san me ya faru ba, sai na ji mu gijif!
Mun

watse a titi, mun yi karo da wani
babur din
mun fadi. Na fadi a kan cikin nawa,
yayin da
dana Bilal aka cilla shi a gefen titi ya
fadi. Ya
kurje a fuska da kafafuwa, ni ma
fuskata,
gwiwoyin hannu da kafafuwana duk
jini.
Dan acabar ya karye, ya yin da daya
mai
acabar ya suma. Nan dai na mike
tsaye wuriwuri ban damu da ciwon da yake
jikina ba,
dana kawai na ke nema. A can gefe
aka
tsinto min shi, jini gaje-gaje na rushe
da
kuka na rungumeshi....
Umaimah ta fashe da kuka, yayin da
tausayinta ya lullube zuciyoyin
wadanda ta
ke ba wa labarin.
Faduwa ta ce, ''Sannu *yar uwata,
ashe kin
sha wuya ke ma?
Umaimah ta nisa ta sa toilet paper ta
share
hawaye, ta ci gaba da cewa.
''Alhamdu lillah a kowanne hali nake,
sai aka
fasa tafiyar unguwar Dosa, aka kawo
motar
asibiti (ambulance) aka zuba mu a
ciki, an
sace min jakata, waya ta na hango
akan titi
har wani ya dauke na karbi abuna.
Wayar
Abdul-Basi nake ta yiwa flashing don
ba ni
da kudi a wayar, amma ya ki kira na.
Na yi flashin fiye da sau goma ina so
na
sanar masa mun yi hatsari, muna
asibiti ya
ki kira na, da na dame shi ma ya
kashe
wayarsa.
Su Bara'atu na yiwa flashing suka

kira ni na
sanar musu halin da nake ciki, na
fada musu
sunan asibitin.
Suka gigice ba jimawa kuwa sai gata
da Haj.
Bishra sun zo, ni dai ta dana nake yi,
ban
damu da kaina
ba. Babu dinki a raunin sai dai aka
wanke
ciwukan aka saka mana auduga da
iodine.
Mun sha zafi, aka
ba mu allurai da magunguna duk
kyauta. Sai
aka zo maganar dan cikina suka ce
ya bugu,
amma na
koma asibitin da nake awo na ga
likita ya yi
sauri a fitar da jaririn.
Bara'atu da Haj. Bishra na sa su
tsayar mana
da me tasi, muka hau muka kama
hanyar
gida. Fadi suke,
''Umaimah ma tafi gida kuwa ba
asibitin da
kike awo ba zamu je? Saboda
maganar dan
cikin nan naki. Ki kira mai gidan ki
fada
masa halin da kike ciki mana.
Sai suka ga na barke da kuka, suka
gigice
ainun,
suna tambaya ta, da kyar na iya fada
musu
abin da idanuwana suka hango min,
wato
Zulayhat Senegal
da mijina Abdul-Basi a mota suna
tafe suna
hira da shewa. Sai na ga sun hada
ido sun
sunkuyar da kai kasa,
da alama dai sun san komai, don na
ga ba
su yi mamaki ba.
Bara'atu ta fara magana, sai Aunty
Bishra ta

dinga zungurarta, wai ta yi shiru. Na
ce, ''Au
daman har da abin da zaku iya
boyemin? Me
kuwa za ku boye min bayan na gani
da
idona?
Sai Bara'atu ta gyara zama ta dinga
ba ni
labarin abubuwan da suke faruwa
wanda
ban san da su
ba. Tun ina fahimtarta har na gigice
na fita
daga hayyacina, na dora hannu aka
na
mimmike a cikin
tasi kamar wacce zata sume. Ga ciwo
a
fuskata, ga kuka ina yi, ga dana yana
nasa
kukan saboda azabar ciwo...
Faduwa ta ce, ''Me suka fada miki?
Umaimah ta goge hawaye, ta ce,
''Labarin
dawowar da yake yi da wuri ya shige
gidanta ya ci abinci, ko ya dauketa
suje
restaurant su ci. Da yadda ta ke zuwa
ofis
dinsa daga dukkan alamu kuma suna
neman juna. Yanzu haka wannan fitar
da
suka yi garin su Zulay zasu je Zariya
maganar aurensu, ni ban sani ba,,,,,
Abdul-Sabur ya ce ''Allah Sarki, da
kin yi
hakuri kin zauna da ita. Me ye
kishiya? Ko
wacce ta zauna da halinta.
Umaimah ta tabe baki ta ce, ''Ban ki
zama da
ita ba ita ta fitar da ni dole, Ya zan yi
tunda
an kore ni?
Faduwa ta ce, ''Ya aka yi da cikin a
ranar?
Umaimah ta sake goge hawaye, ta
ce, ''Ba
muje asibitin ba, gida na je na
kwanta ni da
dana, MAKWABTA suna jinyarmu. Su

AbdulBasi ba su
dawo ba sai karfe goma sha daya na
dare.
Ya shigo yana bata rai don kada ma
na yi
masa maganar dazu. Sai ya tsorata
da yaga
ciwon jikinmu, ya shiga karkarwa.
Ban iya yi
masa magana ba sai Bara'atu
ce ta ba shi labari. Ya fito da makulli
ya
kinkimi Bilal ya ce, ta kamo ni mu je
asibiti a
sake bincikarmu musamman ma dan
cikin.
Haushinsa kawai na ke ji, muka duru
a mota
har da Bara'atu muka je. Muna isa
saiga
Zulayha ita ma ta
biyo mu a motarta, ban san wanda ya
fada
mata ba ma. A gigice ta hau kissa da
kisisina, wai ita tausayi. Likita yayi
scanning
a cikina ya ce, ''Baby ta mutu a ciki,
za su ba
ni gado zuwa gobe a yi tiyata.
Cikin dare nakuda ta taso da kaina na
haifi
*ya ta fara jawur mai kyan gaske,
amma ba
ta da rai.
Kwanana uku a asibiti a kwance, abin
takaici
Zulayha ce a kaina ita ya barwa kudin
komai,
tunda shi yana ofis sai dare yake
zuwa su
tafi gida tare,
sun daina boyemin komai ma a
gabana ake
hirar soyayya, wasa da dariya.
Abincinta
nake ci, haka dana a hannunta yake
kacokan
ita ke kula da shi.
Na yi kuka, na sha takaici, ba yadda
zan yi
sai kallo da ido.

Bara'atu na sake dora min da wasu
bayanan
ma da ban sani ba, ashe an dade ana
cin
amanata. Su ma MAKWABTAn abin
da suke
takaici
ta girme shi, ya fi ta kyau, ya fi ta
ilimi ba
ajinsa ba ce. Me zai yi da tsohuwar
*yar
duniya? Kanta har da farar fufura, shi
da
yake da mata kamar ni fara, yarinya
mai
kyau da ilimi?
Amsar ita ce ta fini iya duniyanci,
bariki zalla,
wayo, iya tattali da rashin kunya, sai
kuma
asirai da ta dogara da shi, ta haka ya
fara
sonta.
Aka sallamo ni na dawo gida zan
karbi dana
sai ta hana ni, wai na bari sai na
gama jego
tukun na ita
zata kular min da shi. Tsabar kissa
ce da son
jan ra'ayin Abdul-Basi ba don Allah
ba ne, na
hakura na bar sa. Ta goya shi ta
sauke, ta yi
masa rawa, ta kai shi kantina siyayya
kalakala.
Uban kuma sai ya yi ta jin dadi.
Wata asabar suka shirya a motarta
shi da ita
suka tafi Gombe wajen mahaifansa,
zai
gabatar da ita a matsayin amaryar da
zai
aura. Kudin cefane kawai ya wurgo
min kan
cinyata, ya ce mu mun tafi
Gombe sai goben za mu dawo.
Na san da ita za su tafi, na daure ban
tambaye shi ba balle na yi korafi, ya
samu
damar yi min rashin

mutunci. Ya kada kai ya fice da jakar
kayansa. Na tafi wundo da gudu ina
lekensa,
na ga ya shige gidanta fiye da
mintuna
ashirin, sannan suka fito a tare, ashe
shaddar jikinsu iri daya ce. Ita ta
dinko
musu daga Senegal sun yi kyau, sai
kamshi
suke yi.
Ina saka ran za su miko min dana
kafin su
wuce,
sai na ga har da shi da kayansa suka
shige
mota, an yi masa kwalliya shi ma. Na
manta
rabon da na ga dariyar Abdul-Basi
amma
tunda suka shiga mota suka fara hira
da
dariya, har da kyakyatawa.
Na sake bin daya wundon da gudu
don na
ga fatarsu daga get, to ko na gani ma
ba
komai zai kara min ba banda
tsabagen
takaici da kunar zuci. Suna tafiya na
sulale
na zauna na dora hannu aka na
surnano da
wasu zazzafan hawaye mai radadin
fita.
Kafin hawayen ya diro kasa sai na ga
Haj.
Bishra a tsaye a gabana, na yi sauri
na goge
hawayena ina
kokarin wayancewa. Sai ta ce, ''Kada
ma ki
bata hawayenki *yata, ki kwantar da
hankalinki, ki saka musu ido kawai,
komai ya yi farko zai yi karshe. Da
yarinta
jikinki shi yasa kike amincewa kowa
alhali
ana cutar da ke.
Ba Zulayha kadai ba, duk wasu da
kike
mu'amala da su a gidan nan sai kin

yi takatsan-tsan, kuma kin rufe bakinki, kin
boye
sirrinki.
Ba ta fada min ba dai baro-baro
saboda
gudun haddasa husuma a matsayinta
na
babba, amma
tabbas na san akwai wata magana a
kasa.
Sai ta tashe ni tsaye ta zaunar da ni
akan
kujera ta ci gaba
da yi min nasihohi masu kwantar da
hankali,
sai na ji dan sanyi a raina. Na yi
mata godiya
ta tafi na kasa cin abinci, shi ya sa
ban dafa
ba. Daga lemo da biskit sai ruwa na
yi ta sha,
a lokacin ina da kiba
tunda na yi wannan ramar har yau
ban
mayar da jikina ba.
Da na tuna da son da Alhaji surukina
ya ke yi
min, sai ban damu ba nasan da kyar
zai
amince ya bar Abdul-Basi ya yi
wannan
auren. Mahaifiyarsa ce dai na ke
zaton zata
amince, don duk abin da *ya*yanta
suke so
shi ta ke so, ba ta hana su. Na
dukufa ina ta
addu'a ina kuka akan Allah Ya dawo
da
hankalin mijina kaina, don na ga ba
ya sona
yanzu.
Bara'atu kawata, makwabciyata ta
shigo
gidan da yamma da sababbin gulma,
ita ba
kwantar min da hankali ta zo ta yi ba,
irin na
Haj. Bishra, sai ma tayar min da
hankali ta
sake yi. Mijinta ne yake sanar

mata da komai, duk hirar da suke yi
da
Abdul-Basi akan Zulayha. Wai shi
Zulayha ta
fiye masa ni, gara ya auri babba mai
hankali
wacce ta san tattalin miji ba irina ba,
raino
kadai yake yi. Ni ma na saki baki
na yi ta fada mata irin wulakancin da
yake yi
min,
Allah Sarki! Kuruciya dangin hauka.
Ba su dawo ba sai washegari lahadi,
da
daddare ya dawo gida bai yi min
bayanin
komai ba ya shige dakinsa ya kwanta
kamar
yadda ya saba, ya raba daki da ni
yanzu. Da
sassafe ya fice wajen aiki ko kudin
cefane
bai bani ba, ina sallah na ji fitarsa.
Misalin karfe goma da rabi na safe na
ci
kuka na gaji, na fito barandar waje na
tsaya
ina mai kallon gidan Zulayha, sai
kawai na yi
ido hudu da
Babangida dan gidan Yayata a zaune
akan
kujera,
dana Bilal akan cinyarsa. Yana
ganina ya
zabura ya ce, ''Aunty Umaimah''. Bilal
ma ya
hau tsalle da
murna da ganina.
Na yi matukar razana da ganin
Babangida,
na dafe kirji na ce, ''Lah yaushe ka
zo?
Ya ce, ''Ni da Abba muka zo jiya, ai
na dawo
Kano gaba daya za'a saka ni a
makaranta a
nan. Anti Zulayha ta ce min ba kya
nan ni
daman a wajenki zan zauna''
Sai ya mike da sauri ya ajiye Bilal

yana shirin
ya zagayo wajena. Sai na ce, ''Ka
taho da
Bilal shi ma.
Ya dauko shi suka taho, a falo na jiyo
muryarta ta ce, ya koma ya zauna
babu inda
za su je. Sai na ji
shiru ba su zagayo ba. Na fusata
ainun na
kwalla kiran sunansa, amma kiri-kiri
matar
nan ta hana shi amsawa. Ban dauki
gyalena
ba sai na fita na shiga gidan haka
nan. Na
iske su a zaune a gabanta sun yi
tsuru-tsuru,
kana ganinsu kasan a takure suke.
Ita kadai ce a gidan yaranta duk sun
tafi
makaranta.
Na yi sallama sam ba ta amsa min
ba, na
wuce kai tsaye na dauki Bilal na
kama
hannun Babangida na ja, ai kuwa sai
ta rike
shi ta ja.
Ta ce, ''Ki tafi da danki, wannan dai
ba ke
kika haifa ba, kuma ba ke kika ba ni
ba,
Kakarsa ce ta ba ni da
ubansa, don haka sai a bar min
dana.
Na auna mata harara, na ce, ''Kin
manta
wace ce ta haife shi? Idan kin manta
ki tuna,
dana ne, dan yayata ne uwa daya uba
daya,
don haka ni na fi cancanta na rike
shi ba ke
ba.
Sai ta sake shi ta gyada kai, ta ce,
''dauke su
ki tafi da su, na ji *ya*yanki ne amma
ki sani
daukar
*ya*yan nan da kika yi daga wajena
zai zai

janyo miki bacin ran da za ki
dauwama da
shi bai gushe ba. Ni Haj. Zulayha ba
a ja da
ni, yaro bai san wuta ba sai ya dafa
ta. Idan
kin san wata ba ki san wata
ba, da sannu za ki banbance zuma
da
madaci.
Na sake auna mata harara na ce,
''Allah Ya fi
ki ai, duk abin da ya same ni daga
Allah ne
ba dai mutum ba. Ta rike baki tana
mamaki,
sai ta gyada kai, ta ce,
''Au har kin yi baki? Kin yi wayon yi
min
rashin kunya? Tabbas sai na zame
miki
duhu a cikin rayuwarki, sai kin yi dana-sani
da ba ki zage ni ba.
Na ja wani dogon tsaki ba tare da na
tanka
mata ba, na fice da *ya*yana muka
shiga
gidana. Sai na ji sanyin kasurgumin
bacin
ran da nake ciki da na ganni da
yarana suna
taya ni hira.
Amma ina mai tsananin mamaki da
takaicin
kawo Babangida a dalilin Zulayha ba
a
dalilina ba. Babu
irin magiyar da ban yiwa Abdul-Basi
ba tun
farkon aurenmu ya dawo da
Babangida
wajena, amma fur! Ya ki sai ga shi
yanzu ya
dauko shi tun kafin ma ya aure ta ya
damka
mata shi.
Na san halin kissa da kisisinar
Zulayha ta yi
musu dadin baki ne shi yasa suke
ganin ita
zata iya rike

su alhalin nan gaba wahalar da su
zata yi.
Na san zata fadawa Abdul-Basi zai yi
fushi
da ni amma ban zaci har zai yanke
min irin
wannan hukuncin ba....
Sai ta dafe kai ta surnano da hawaye.
Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Ba dai
dukanki
ya yi ba akan haka?
Kafin ta amsa Abdul-Sabur ya amshe
da
cewa. ''Ba dai saki ya baki ba?
Umaimah ta sharce hawaye mai hade
da
majina, ''Ina fita tayi masa waya
wajen
azahar sai ga shi a
gida. Na yi mamaki da ganinsa daidai
wannan lokacin. A fusace ya fado
mana cikin
falon, muna
cin abinci. A gigice muka mike don
tsorata,
ya daka min tsawa ya tambaye ni.
''Me ya kai ki gidan Zulayha kika
zage ta?
Na ce, ''Ban zage ta ba, ni karya ta ke
yi min''
Ya dakamin tsawa, ya fada cike da
fusata,
''Ita ta ke yi miki karya? Sa'ar ki ce?
Daman
ta ce kin zama
fitsararriya, don haka ki kwashi yaran
nan ki
mayar da su, amma ki durkusa ki ba
ta
hakuri kada ki sake shiga gidanta.
Na tambaye shi har Bilal din ma a
wajenta
zai zauna? Ba saboda rashin lafiya
ba ne aka
ba ta ba,
yanzu kuwa ai na warke ni zan rike
dana.
Sai na ji ya kwashe ni da mari dau!
Na
durkushe na rike kunci. Ya fada cikin
kakkausar murya.

''Daga yau idan ina magana kina yi
sai na
saba miki.
Banza! Ballagaza, saunar mata.
Yaushe aka
gama rainonki da zaki iya rainon
wasu?
Yaushe kika
gama sanin ciwon kanki balle ki san
ciwon
wani?
To tunda bakyajin maganata ki shirya
kayanki gobe na saki a mota ki koma
Dugge
can ki zauna a gidanku, sai ki yi
musu
fitsarar a kauye, ba a nan ba. Dama
tsiyar
bakauye ke nan, ya zo birni ya sha
jar miya ya nuna maka ya fi ka iya
tafiya a
kan tiles.
Na ji kamar almara, na kasa kuka, na
kasa
magana.
Ya ja hannun yaran suna ta tsala
kuka, har
da ihu ya kai su wajen Zulayha,
sannan ya
shiga motarsa
ya koma ofis. Sai a lokacin na fara
rusa kuka
ni kadai a daki, amma na tsorata da
maganar kora ta da ya yi, na san
tonan
asirina ya zo idan ya sake ni na
koma Ruga
da zama.
Har dare jikina rawa ya ke yi, ina ta
addu'ar
Allah Ya huci zuciyarsa kada ya dawo
da
fushi ya sake ni. Ya dawo tunda
magruba,
na ga tsayuwar motarsa amma ba
gidana ya
shigo ba, gidan Zulayha ya shiga
inda ya ci
lafiyayyen abincin da ta dafa masa.
Ni kuwa da yake bai bar min kudin
abinci
ba, sai na dafa shinkafa da wake da

mai da
yaji, dan na ga yana sonsa. Na
kakkalato
kudi na aika aka siyo min salad da
tumatir
da *yar albasa na yayyanka masa
don na
burge shi. Bai shigo gidan ba sai sha
dayan
dare.
Na durkusa na gaishe shi ya yi banza
da ni
kamar bai san da wanzuwata a gurin
ba, na
yunkura zan je na dauko abinci, sai
ya ce
dawo nan, bana son abincinki
munafuka.
Na tsorata da jin wannan kalma da ta
fito
daga bakinsa. Na dawo na durkusa,
sai ya
fara zayyano min maganganu kalakala na
tsakani na da shi,
amma ya ji maganar nan a waje a
ofis ma
aka fada masa. Sai jikina ya hau rawa
na ce,
''Ni ban fadawa kowa ba.
Ya daka min tsawa ya ce, ''Ki fada
min da
wacce ku ke hira a gidan nan idan
bani nan,
ko kuma yanzu
na yi kasa-kasa da ke, bakar makira
kina
tafiya a sum-sumke, amma sai tsabar
bakin
munafurci da tozarci.
Can na tuno aminiyata Bara'atu ce
kadai
nake irin wannan hirar da ita. Sai na
ce, ''Na
san dai mu kan
yi hira da Bara'atu.
Ya ce, ''To zamana da ke ya kare
tunda ba
kya iya boyemin sirrina. Bara'atu kike
fadawa ita kuma ta ke kwashewa ta
fadawa
mijinta, shi kuma ya je ofis yana

yadawa ga
abokan aikinmu.
Na yi ta ba shi hakuri, na ce, ''Ba zan
kara ba.
Ya yi banza da ni, ya shiga daki sai
ya fito
min da farar takarda mai kunshe da
bakin
sako. Na bude
na karanta tun a gabansa, saki daya
ya
rubuta min, wanda tunda nake a
rayuwata
ban taba jin tashin hankali ba sai irin
na
ranar. Allah Ya sa ban manta
ambaton
innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ba.
Na yi ta
fada ina mai-maitawa kamar yadda
malamin
islamiyyarmu ya ce mu dinga yi da
zarar
mun hadu da bala'i. Ya damke
gashina ya
kai ni dakina ya ce, na fara hada
kayana
gobe da safe zai saka ni a mota na
tafi
garinmu.
Ina makyarkyata ina hada kayana a
lokacin
na nemi hawaye na rasa, saboda
masifa ta yi
masifa, tashin hankalina rabuwa da
karamin
dana Bilal ga Babamgida da aka
dauko shi
daga gidan tarbiyya,
wajen rufin asiri aka kawo shi wajen
wahala, inda za a iya gurbata masa
tarbiyya,
shi ma zan fi so da an bar shi a
Gombe ya fi
komai a gare ni.
Yana ta zagina ta uwa ta uba, yana
ambaton
albasa ba ta yi halin ruwa ba, ban yi
halin
Nasiba ba, ba don albarkacin Nasiba
ba ai da
tuni ya sake ni.

Alhali na fi yi masa biyayya ma akan
Nasiba,
na fi ta wayewa da sanin tattalin
miji...
Abdul-Sabur ya kumbura ya yi
suntum kai ka
ce Abdul-Basi ne a gabansa, ko
Zulayha sai
harare-harare yake zuciyar nan na ta
tafasa
don takaici. Faduwa kuwa sai girgiza
kai ta
ke, kira ta ke,
''Lahaula wala kuwwata illah billah.
Umaimah ta zubo da hawayen takaici,
ta ce,
''Na kwana ban runtsa ba a zaune,
ina ta
sake-saken inda zan nufa don ba zan
iya
zama a tsakiyar Matawata da Ilah ba,
ga
gulmar gari, ga tsangwamar matan
uba, ga
talauci da rashin lafiyar mahaifina
babu
kudin magani.
Daman Abdul-Basi ne mai siya ya
aika masa,
ni ma na tara dan kudi na kunshe
idan na je
na ba shi, yanzu duk babu mai ba
mu.
Gari ya waye na tashi na yi wanka na
yi
sallah tun da asubah. Sai da na jima
da
kimtsawa sannan na ji
Abdul-Basi ya shiga wanka, misalin
karfe
shida da rabi, bakar abaya na saka a
jikina
sai na zindimo bakin hijabi na fice da
sauri
na nufi gidan Bara'atu zuciyata tana
ta
tafasa. Ba su bude gida ba ma ni na
kwankwasa, na san sun tashi tunda
mijinta
ma Ma'aikacin Banki ne. Ta yi
mamaki da
ganina, gami da hawaye face-face a

idona.
''Lafiya Umaimah? Ta tambaye ni a
dan
duburce Na ce, ''Na zo ne na yi miki
sallama
na kuma yi miki godiya. Na ji abin da
duk
kika fadawa mijinki shi kuma ya je ya
yada a
ofis har Abdul-Basi ya zo ya sake ni
a dalilin
haka. Amma wallahi Bara'atu kin ba
ni
mamaki, ban taba tunanin
MAKWABTAKA
takan iya komawa cuta ba. Yanzu
duk yadda
na dauke ki a gurina ki rasa abin da
zaki
saka min da shi, sai ki kwashe duk
maganar
da muka yi da ke ki fadawa mijinki,
shi
kuma don rashin lissafi kamar shi
namiji wai
ya buge da kwasar maganar mata
yana
kaiwa gurin aiki.
Sai ta hau fada da daga murya don
mijinta
ya ji ya fito. Ta na cewa, ''Kamar
yaya, me
kike nufi? Ni da mijina munafukai ne
ke
nan? To mun fada din ke dai kawai
kishi ne
ya dame ki za a auro miki wayayyiya
*yar
birni, kin tsorata za ki gudu, amma
mu ina
ruwanmu? Idan ma na fada ni na
gayyatoki
kizo ki fada min?
Surutai dai da cin mutunci ya yi ta
fitowa
daga bakin Bara'atu, na yi kasake ina
kallonta cike da tsananin mamaki,
makwabciyar da na amincewa ce yau
ta ke
min wannan tonan sililin.MAKWABTAKA 20
Na tuno cin amanar da Matawata ma ta yi min na hado
da cin amanar da Zulayha ta yi min, sai na ji a raina na

tsani duk wani MAKWABCINA. Na kudira a raina har
abada ko gaisuwa babu tsakanina da MAKWABTANA, haka
na dai na ba da hakkin MAKWABTAKA..
Umaimah ta fashe da kuka mai cin rai.
Abdul-Sabur ya yi doguwar ajiyar zuciya, ya gyara zama
ya ce, ''Ke wanne sirrinsa ne kika barbaza a
waje wanda ya ba shi haushi haka har da saki?
Kin san fa maza ba sa son kananan maganganu irin na
mata, amma shi ma ai duk wannan bai kai ga saki ba.
Umaimah ta ci gaba da kuka, abin da kuwa ba ta sani ba,
kukanta yana tayar da hankali ga duk mai raunin zuciya.
Sai suka shiga rarrashinta suna mika mata toilet paper
tana ta sharcewa.
Sai can ta nisa ta ci gaba da magana, ''Allah Sarki kuruciya
mai dadi, rashin sani ya fi dare duhu. Ba
wani abu na fada ba wanda ya wuce hirar da nake ba ku
yanzu. Hirar garinmu na ba ta, ta kuruciyarmu da waken
dandali. Da hirar yanda Abdul-Basi ya hadu da yayata
Nasiba har aka yi aure, dawowata wajensu da zamana a
wajensu, da shiga makaranta. Don ita bata san Nasiba ba
a lokacin ba a yi mata aure ba, ba sa gidan, wadan da
suka zauna da Nasiba sun bar gidan. Kuma da bakinta ta
tambaye ni wai wacece Nasiba
da ta ke jin su Haj. Bishra suna ta maganarta, wai an ce
yayata ce? Shi ne na bata labari, na hada mata da labarina
da Ilah da Matawata sai kuma labarinsa da Zulayha a
lokacin da maganar cin amanar da ake yi min ban sani
ba. Ita ma Bara'atun ta ke karamin da abubuwan da
idanuwanta suka gani, ko wanda mijinta ya jiyo a ofis ya
fada mata.
To amma ka san magana idan ta zamana ta koma ta
gulma, to yadda za'a jujjuya ta sai ka ji ba iri daya ba ce
da yadda ta ke tun fil'azal.
Yadda Kamal mijim Bara'atu ya je yake fada a ofis cewa
ya yi, Abdul-Basi dan birni ne, dan masu kudi da sarauta a
Gombe, amma saboda neman kyau ya shiga Ruga ya
auro mai tallar nono Nasiba Yayata
ke nan, wai don ta haifa masa kyawawan *ya*ya.
Da ta rasu ya koma nacewa kanwar bayan shi ya rike ta
ya ce sai ya aure ta, ba ta sonsa, tana ta wulakanta shi ya
yi ta cusa kudi aka raba ta da saurayinta da ta ke matukar
so mai suna Ilah, ta zo
gidan ba ta sonsa. To burinsa ya cika ya sami fararen
*ya*ya, amma fa duk maza ne ya fi son *ya mace don ta
kawo masa jari.
Kun ji yadda aka juya zancen, kuma dai shi ma ya tsane
ni ya fasa zama da ni akan Zulayha shi ne ya sa ya yi saki,
amma ba don maganar nan kadai ba.
Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Tabbas haka ne, nima abin
da zan fada kenan kika riga ni.
Abdul-sabur ya kurbi lemo ya ce, ''Haka ya ke yanzu na
fuskanci maganar. Ya dai so ya sake ki ne ya rasa dalili,

kuma ba ya so ace ya sake ki a dalilin zai yi aure.
Umaimah ta langwabe kai gefe, ta ce, ''Sai na ji Kamal
yana magana da Abdul-Basi a waya, wai ya zo gidansa ya
fitar da ni ga shi nan na zo gidansa ina ta takalar matarsa
da fada. To shi ba ya son tashin hankali, ya za a yi na zo
gidansa na tayar musu da hankali da sassafen nan?
Sai na ji muryar Abdul-Basi yana kwalla min kira a bakin
matattakalar gidan. Na fito da sauri jikina yana rawa.
Bayanai nake yi masa cewar ni ba fada
na zo na yi da ita ba, sallama zan yi mata.
Ai kuwa ban rufe bakina ba na ji ya rufe ni da duka ta
ko'ina, yana zagi yana jana ya wurga ni a cikin mota. Da
gudu MAKWABTA suka kawo min agaji,
amma ina! Har ya kulle ni a mota. Haj. Bishra har da
hawayenta ta shiga yi masa fada tana cewa, ''Haba AbdulBasi kashe yarinyar na kake so ka yi bayan cin amana da
cin mutuncin da Zulayha take mata a gidan nan tana
hakuri, kuma har da duka da zagi?
Sai ya balbale ta da rashin kunya, wai babu ruwanta da
iyalansa. Ina daga cikin mota na bude mata takardar
sakin da ke kunshe a cikin rigata. Ta gilas ta karanta, sai ta
fashe da kuka ta shiga gida.
Kalmar karshe da ta fada kafin ta tafi ita ce, ''Ki yi hakuri
Allah Zai musanya miki da miji mafi aikhairi.
''Insha Allah''. Inji Abdul-Sabur.
Faduwa ta ce, ''Kayanki fa, ya bari kin koma kin dauko? Ta
ce, ''Eh, gidan amaryarsa ya shiga ko in ce
farkarsa don ba a yi auren ba suke holewarsu. Ta lalata
shi, salihin mutum ne Abdul-Basi, ban taba
jinsa da neman mata ba, amma sai ga shi kowa ya san
abin da suke aikatawa da Zulayha Senegal.
Yana shiga na bude kofar da gudu na hau samana Allah
Ya sa bai kulle ba na jawo katuwar akwatina da na shirya
ta tun cikin dare na ratayo jakata mai dauke da tarkacen
kayan kwalliyata na fito, har nazo matattakala zan sauka
na tuna takarduna na firamare da sakandire, da na
diploma da na yi akan na'ura mai kwakwalwa (computer)
suna cikin akwatin da yake ajiye muhimman takardunsa
na garzaya da gudu na dauko a cikin ambulan na cusa su
a cikin riga don idan ya gani zai kwace tunda ya yi niyyar
yin mugunta, baya son ci gabana.
Ina saukowa sai na ji an ambaci sunana, wata *yar
karamar murya daga kan barandar Zulayha. Na daga kai
da sauri sai na ga Bilal dina ne ya tashi daga barci daga shi
sai pampers.
Yana murna yana tsalle yana fadin, ''Ga Umma''
Sai Babangida ya fito da gudu ya ce, ''Aunty Umaimah ina
za ki je na ga kin dauko akwati?

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment